IN SO YAKI NE CHAPTER 5

IN SO YAKI NE CHAPTER 5

  Kufce hannun shi yayi ya fice da gudu ya bi hanyar da yaga ta nufa, nan take Habeeb ya yunk’ura zai bi bayan shi Ameer ya rik’e shi yana girgiza masa kai “Habeeb please! Let them meet, ka bari su had’u in kayi k’ok’arin hana Suraj a yanzu tabbas zai sake birkice wa ne kawai besides in Allah yayi zasu had’u baka da ikon hana wa, ni a gani na ya kamata ka kyale su it’s up to them su yi sorting out matsalar su.”+ A fusace Habeeb ya hankad’e Ameer tun k’arfin shi sannan ya had’a shi da bango yace “How dare you Ameer! Why don’t you understand cewa barin Suraj ya had’u da Laylah tamkar ya yanki ticket d’in barin duniya ne? Me kake tunani idan Suraj ya fahimci cewa Laylar da ta kasance tashi ce shekaru bakwai da suka wuce yanzu ta yi mishi fintinkau, mi zai faru idan ya fahimci cewa matar da yafi k’auna yanzu ta dawo a matsayin matar babban mak’iyin shi Muhseen? Ko da yake kai me ka sani game da soyayya? All you know is to hurt people, bazaka fahimci dalilin da yasa nake hana Suraj ganin Laylah ba, besides dama chan da kanka ka damu.” Habeeb na kai nan ya fice daga d’akin yana neman Suraj Tamkar an sara shi gida biyu haka Ameer yaji kalaman Habeeb ba shiri ya fara zubar da kwalla jiki ba kwari ya d’auki makullin motar shi ya fice ba tare da b’ata ko da dak’ik’a d’aya ba….. Durk’ushe Habeeb ya hango shi, dan haka ya yi saurin k’arisa wa wajen shi ya dafe kafad’ar shi hakan yasa Suraj yayi saurin d’ago wa ya dubi Habeeb d’in. Mik’ewa yayi da murmushin sa zai yi magana Habeeb ya katse shi ta hanyar cewa “Kayi abunda kaga ya dace, now it’s my turn, ga key d’in motar ka jira ni a ciki zan taho da Meenah we are going home”. Habeeb na kai nan ya juya ya bar wajen Suraj ya bi shi da kallo domin yaga b’acin rai k’arara a fuskar shi , hankan ne ma yasa bai furta ko kalma ba ya rik’e makullin ya nufi parking lot na asibitin. Saida Habeeb ya gama siyan magungunan da likita 6a rubuta sannan ya fito Meenah ma ta biyo shi Habeeb ya tada motar suka tafi….. Kamar yanda cikin su babu wanda ya yi magana haka ma b’angaren Ameer yana ta tuk’i kamar wanda zai bar garin Abuja, abubuwan da ya aikata a baya tunanin su ke ta faman farautar sa babu shiri ya ja birki ya tsaya ya bugi sitiyarin motar sannan yace “kaicho!! Habeeb yayi gaskiya amma ya kamata ya gane cewa mutum yakan sauya kuma d’an adam Ajizi ne, abunda na aikata a baya nayi nadamar su bai kamata yayi min magana the way he did ba, zan je in same shi se muyi magana a tsanake i’m sure d’azu ranshi ne a b’ace” Nan take Ameer ya juya kan motar ya nufi hanyar gida. Ko da ya iso dare yayi dan haka yayi sallah a masallaci ya shige gida “Gobe inshaa Allah ma had’u da Habeeb d’in”…….. Wutar d’akin ya kashe ganin barci yayi awon gaba da khadijah, fice wa yayi ya tsaya a balcony yana kallon sashen Ameer, se lokacin ne kalaman shi suka fara dawo masa. Dafe goshin sa yayi cike da takaici yace “What have i done?! Na tabbata na bak’anta wa Ameer rai yau dole naje na bashi hak’uri, amma yanzu tara ma ta wuce, in Allah ya kaimu da safe zan same shi, na tabbata zai fahimci situation d’in da yasa nai mishi hakan.” d’aki ya koma ya kwanta da kyar ya iya runtsa wa…… Fitowan Suraj daga wanka kenan yaji ana kwankwasa masa k’ofa “Come in”. Ya fad’a ba tare da ya kalli inda k’ofar take ba yacigaba da tsane ruwan kan shi. Magungunan shi ta ajiye da orange juice sannan ta juya zata fita Sakin towel d’in hannun shi yayi ya chafko hannun ta sannan ya fisgota jikin shi yace “nagode da kulawa”. Murmushi tayi tace “It’s nothing, besides hakk’i na ne in kula da kai da kuma lafiyar ka as your wife”. Murmushi yayi ya matse ta a jikin shi yace “fine then, nima se ki bani chance na baki hakk’in ki, from today we will live under the same roof , a gado d’aya sannan as my wife, i will not complain, i will not nag, sannan ba zamu b’oye wa juna sirri ba daga yau” Hawaye ne ke gangaro wa daga idanuwan ta yasa hannu ya share ya girgiza mata kai. Murmushi tayi tace “Thank you Suraj” ta rungume shi. Da kyar ya iya d’ago hannun shi yayi hugging d’inta shi ma har karkarwa hannuwan suke ya k’ank’ame idanuwan shi yana sauk’ar da numfashi. Sun dad’e a tsaye kafin ya janye ta daga jikin shi ya kashe mata ido d’aya yace “hug d’in ya isa haka in de ba so kike mu kwana a haka ba Meenah dear” dariya tayi har tana blushing ta sake shi tace “Bani five minutes ina dawowa” Kai kawai ya jinjina ya bita da kallo har ta fice sannan ya furzar da iska daga bakin shi yace “Ya Ilahy! What’s wrong with me? Wannan dare de Meenah tayi shi cike da farinciki gashi ta samu kusantar Suraj ba tare da fargaba ba na wulak’ancin da ya saba yi mata a baya. Shi kuwa Suraj duk moment da yayi spending da Meenah a wannan daren tamkar reflection d’in dararen da ya yi spending da Laylah yake gani……. @Maleek Holdings 8:45am Bak’ar Mota SUV ce aka yi parking driver ya fito ya bud’e k’ofar, k’afar sa d’aya kawai ya jefo waje yana daga cikin motar yana waya daidai lokacin Mubeenah suka fito tare da wasu maza biyu ita ma ta sha dogon jacket bak’i tayi rolling da peach mayafi ta rungume wasu files wanda daga ganin su kasan suna da muhimmanci ba kad’an ba. Daga main entrance suka tsaya shi kuwa Suraj saida ya kammala abunda yake a motar sannan ya fito yana sa button d’in jacket d’in shi wanda hakan ya fitar da Murd’ad’en figure d’in shi mai d’aukar hankali, da sauri wani daban ya sa hannu a motar ya d’auko jakar Suraj da wasu manyan takardu ya ja ya tsaya, shi kuwa driver ya koma ya ja motar zuwa inda yake parking. Suraj bai saurari gaisuwar da ake masa ba ya nufi inda Mubeenah ke tsaye “Good morning sir”. Ta furta da murmushin ta, “Morning” ya amsa a tak’aice sannan ya saki killer smile yace “mintina nawa ya rage kafin board meeting?” agogon hannun ta ta duba sannan tace “kana da atleast mintina goma sha biyar Sir” kai ya jinjina sannan ya shige gaba suna biye da shi a baya. Har zai wuce ta gaban ofishin Ameer sai kuma ya dakata, mabud’in k’ofar ya murd’a sannan ya sa kai. Tsaye ya hango shi ya bada baya yana kallon waje daga tafkeken window dake ofishin, wayar shi ma sai ringing take amma baya ji dan haka ne Suraj ya k’ariso ciki ya tura k’ofan yace “Prince! Ya dai? Daman ka shigo ne??” Ba tare da Ameer ya juyo ba ya share guntun hawayen dake fuskar shi sannan ya yi faking murmushi yace “Yass! Na shigo already, i have a lot of paper works da nake son k’arisawa kafin board meeting” Juyo wa yayi ya dubi Suraj sannan yace “please have a seat yanzu zan gama se mu fita, coz ina son ka sa hannu a wasu daga cikin papers d’in” Duk maganganun da Ameer yake yi Suraj yana kallon fuskar shi yana k’ok’arin gano b’acin rai dake kwance kan fuskar tashi, shi kuwa Ameer yana ta bud’e wasu files ko zama bai yi ba Mik’ewa Suraj yayi daga kujerar sa ya zaga inda Ameer ke tsaye ya haye saman table d’in ya zauna sannan ya ce “What happened prince? You looked angry, pale and hurt wani ya maka wata maganar ne wanda ya b’ata maka rai? Ko dai saboda abunda na aikata ne jiya a asibiti? Look Broo i am truly sorry ba da gangan nayi ba, ban sani ba ko idanuwa na ke min gizo but i’m sure na ga Laylah a asibitin Ameer in behaviour na ne ya bata maka rai am so sorry please…” Kai Ameer ya girgiza yace “Suraj come on! Ka duba wad’annan papers d’in suna da muhimmanci a meeting d’in you have to sign them ASAP. Sannan ka daina wani bani hak’uri ni baka b’ata min rai ba saboda in my own opinion ya kamata ka had’u da Laylah in har da gaske ne ita ka gani because na san kana da tambayoyi wad’anda ita kad’ai ne amsan su”. Kai Suraj ya jinjina sannan ya k’arbi takardun ba tare da furta kalma ba ya fara bibiyan su, d’aya bayan d’aya yana rantab’a hannu. Ana haka ne Habeeb ya shigo da sallamar sa Ameer ko kai bai d’aga ba har suka gama maganganun da zasu yi da Suraj Se lokacin Suka d’ago idanuwan su suka had’e, irin guilty kallon da suka yi wa juna ne yasa Suraj ya fahimci cewa akwai matsala. Mik’ewa Suraj yayi yace “It’s time guys mu tafi ko?” Ameer ya d’an saki murmushi yace “you two should carry on, barin kintsa in taho” Suraj ya dubi Habeeb yace “Alright let’s go Habeeb”. Shima Habeeb se cewa yayi “Kai kaje Suraj zan yi magana da Ameer se in taho”. Shiru Suraj ya d’an yi na wasu dak’ik’ai sannan yace “Fine then..” ya juya ya fice amma basu san cewa yana cabinet na gefen na Ameer ba kuma yana kallon su sannan yana jin maganganun da duk zasu yi saboda jikin shi ya bashi akwai abunda suke b’oye masa… Habeeb na k’arisawa daf da Ameer ya kasa d’aga kai ya kalle shi Rungume shi yayi kafin ya iya furta kalmar “I AM SORRY”. Cikin rawar murya. shima Ameer hannu yasa yayi hugging d’in shi yace “It’s okay bro ai ya wuce, besides laifi na ne ya kamata na fahimci cewa duk abunda kake yi domin lafiyar Suraj kake yi, domin farin cikin shi, we are brothers baza mu yi fad’a over such trivial matter ba, kaga yanzu Suraj yana suspecting akwai matsala a tsakanin mu kuma he won’t rest har sai ya nemo sanadin matsalar so we have to be careful” STORY CONTINUES BELOW Janye jikin shi Habeeb yayi daga jikin Ameer sannan ya sauk’e wata nannauyan ajiyar zuciya ya dubi Ameer yace “Ameer tsoro nake kar Suraj ya fahimci cewa wannan lamarin muke b’oye masa, me zai faru idan ya gano cewa Laylah tana nan a wannan garin, tana tare da mu a wajen party, sannan ita ce ya gani a asibiti ba gizo bane. Ba ma wannan ba how will he react when he realises Laylah tayi aure? Auren ma kuma da mutumin da ya fi tsana MUHSEEN ALI ! Yanzu bashi da wani right a kanta ballantana hope?” Bazamu iya handling d’in shi ba a in har ya shiga wannan yanayin, shi yasa nake a tsorace Ameer, Am sorry na fad’i maganganu masu d’aci a gareka” Kai Ameer ya kad’a sannan yace Habeeb duk fa nisan jifa k’asa zai dawo, B’oye wa Suraj batun Laylah da kake yi ban ce kayi laifi ba amma tabbas Suraj zai had’u da Laylah and there is nothing we can do to stop that, Kar ka manta Muhseen da Suraj manyan business men ne had’uwar su bazai yi wuya ba, ko ka tuna cewa Laylah ma tana wajen party kamar yanda ka fad’a? Wani event d’in zai iya taso wa and they might meet. Abunda yafi kawai shine in hakan ta kasance zai fi kyau d’ayan mu yana tare da Suraj because in ya birkice ni kaina kasa gane kanshi nake. Muhseen kuma bazai zauna shiru ba tunda Laylah matar sa ce”. “Kayi gaskiya” cewar Habeeb ya sake cewa “shikenan, Allah ya rufa asiri”. Da murmushi Ameer ya amsa “Ameen” suka kwashe files d’in suka fice daga office d’in zuwa conference room inda za’a yi meeting d’in “Ji yayi kamar an fisge zuciyar shi daga k’irjin shi an dab’a mata wuk’a ya kai kusan mintina biyar yana rik’e da k’irjin shi ya rufe idanuwa, d’aya bayan d’aya maganganun su Habeeb ke yawo cikin kwakwalwar shi, ko da ya bud’e ido baya ganin komai se uban duhu, saida ya daddafe bango ya nufi k’ofar fita, Cabin d’in shi ya wuce direct ya shige bayi, ruwa ya kunna ya dinga watsa wa a fuskar sa har saida ya samu daidaito sannan ya dakata ya d’ago kai yana kallon yanda fuskar shi tayi pale gashi idanuwan shi sun yi ja se uban ciwon kai dake addaban shi. Da sauri ya fice daga bayin ya dawo table d’in shi, farin glass ya d’auka ya zira a idon sa saboda yanda idanuwan suka ka’da suka yi ja sannan ya d’ebi wasu files ya fice…… Kusan awanni biyu meeting d’in ya k’are Suraj bai bi ta kan su ba ya fice daga company d’in ma gaba d’aya su ma kowa is busy babu wanda yabi ta kan d’an uwansa….. SHERATON ULTIMATE HOTELS Abj. A parking lot yayi parking sannan ya fito daga motar yana k’arewa k’iran Hotel d’in kallo sannan ya ciro wayar shi daga aljihun jacket nashi ya kara a kunne “Sufyan….i am here. A ina zan same ku?”. Jim kad’an ya ajiye wayar sannan ya doshi mashigar hotel d’in Wata ma’aikaciyar wajen ce ta tunkaro shi da fara’ar ta “Mr Suraj Abdoul-Maleek??” “Yes i am Suraj” Da murmushin ta tace “This way sir”. Ba ko b’ata lokaci ya bi bayanta har zuwa wani dank’areren executive suit a nan ta ja ta tsaya bayan ta danna door bell. Wani security ne ya bud’e k’ofar sannan ya k’ura wa Suraj ido har saida ya jiyo muryar Muhseen yana cewa “Let him in”. Suraj bai saurari me security zai ce ba ya wuce ciki da takun k’asaita. Daga Sufyan har Muhseen mik’e wa suka yi murmushin yak’e shimfid’e a fuskokin su, shima Suraj da yake player ne murmushin ya sakar musu, cike da fara’a suka amsa sannan suka bashi waje ya zauna. Tun da suka fara maganar Partnership deal d’in hankalin Suraj baya jikin shi don kawai jin su yake amma jifa jifa yakan d’aga ido yana dube dube kamar yana wani CID. Da gudu take bin Tasleem har tana neman fad’uwa, ita kuwa Tasleem se gudu take hannun ta rik’e da wayar Laylan “Tasleem stop! Ki tsaya nace… Ya ilahy. Tasleem ki tsa…..” Turus suka yi su biyun ganin Muhseen ya kafe su da ido kamar zai had’iye, ta tabbata in da ba don yana da bak’i ba da babu mai karb’an su a gidan nan. Da sauri ta figo Tasleem a hankali tace “Dubi abunda kika ja mana, mu koma ciki kafin Mr grumpy ya taso.” Idanuwan sa na yin arba da fuskar ta yaji tamkar an tsikare shi da allura bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba, lab’ban shi na karkarwa amma sun kasa furta sunanta se zufa yake tamkar mara gaskiya. Muhseen ne ya mik’e ya nufi inda Laylah suke don har sun juya zasu bar wajen “Wait” Ya umarce su da su dakata Gamgam Tasleem ta damk’e hannun Laylah tana b’ari ita kuwa Laylah janyo y’ar ta tayi jikin ta tarungume sannan ta juyo duk da cewa ta kasa had’a ido da shi tsabar tsoro. Hannu yasa a hankali ya d’ago fuskar ta aikuwa suna ido hud’u ya daka mata wani mugun Harara ya damk’o hannun ta da k’arfin gaske cikin salon da babu wanda zai fahimta chan k’asan mak’oshin sa yace “Na sha fad’a miki in ina da bak’i ki kula da y’ar ki but what did you do? You end up insulting me by appearing like this”. Ya rik’e rigarta yana nuna mata sannan yace “Ki jira hukuncin da zai biyo baya! Sannan act properly in kika yarda fuskar ki ta nuna alamun damuwa sai na gurje fuskar taki da takalmi nah, useless woman!” Yana kai nan se ya saki murmushin yak’e ita ma hakan tayi, sannan ya shafa kan Tasleem yace “come on sweetie, tafi d’akin ki kar kiyi troubling mom”. Da gudu Tasleem ta wuce d’aki ta rufe k’ofa shi kuwa ya rungumo Laylah daga kunkumi Ya ce “Mr Suraj Maleek.. Had’uwar mu rannan was not quiet pleasant ban samu daman introducing matata ba Meet my better half Mrs Laylah Rasheed”. Maganganun Muhseen Suraj jin su yake tamkar zuban ruwan sama, domin kunnuwan shi basa iya banbance kalma da kalma idanuwanshi kuwa ko kyafta wa baya yi ga bugun zuciyar shi da ke tsere da juna. Tun da taji Muhseen ya furta sunan Suraj bata yi k’asa a gwiwa ba ta d’ago nan take, rau-rau tayi da idanuwa ta kuma kasa d’auke su daga kan fuskar shi, ji tayi tamkar tana zube wa k’asa domin yanda k’afafun ta suka d’au kyarma, hannu ta sa ta dafe k’irjin ta da shi da kyar take fusgan numfashi tsabar yanda zuciyarta ke bugawa Da kyar Suraj ya iya controlling emotions d’in shi ya saki wani murmushin takaici yace “H…..hy Mrs Muhseen it’s a pleasure meeting you” Ita kam maganar ma ta rasa yanda zata fara da kyar ta saki murmushi wanda bashi da maraba da kuka. Fisge jikinta tayi daga rik’on da Muhseen yayi mata kai a k’asa tace Zan je in k’arasa parking” Bin ta Muhseen yayi da kallo har ta shige yana shu’umin murmushi……. A daddafe ta k’arisa d’aki ai kuwa tana tura k’ofa ta ranta da gudu tayi bayi, rufe k’ofar tayi sannan ta jingina a jiki se lokacin ta saki wani dunk’ulallen kuka hannuwan ta a k’irjin ta a hankali take zame wa har ka kai k’asa, sautin kukan ta kad’ai ya isa yasa kaji tausayin ta, tuni ta sauya tamkar wanda aka yi wa mutuwa. Da dishashiyar murya take fad’in “Why Suraj? Mi yasa….. Me yasa zaka dawo after all those years? Bayan kai ka zab’i ka barmu ni da Tasleem? Shin ka dawo ne kaga halin da na shiga? Have you come back to see how i am suffering? I hate you Suraj i soo much hate you! Me yasa zaka dawo yanzun bayan duk wad’annan shekarun? Na neme ka duk inda nasan zan same ka amma na gaza samun ka, me yasa se yanzu? Bayan nayi aure me yasa ka makara Suraj?”……. Duk maganganun da muhseen suke masa babu d’aya da yake shiga kunnuwan sa, ji yake kamar ya burma a guje ya fice daga gidan domin in har ya k’ara b’ata lokaci zuciyar shi tarwatse wa zata yi don haka kamar an tsikare shi ya mik’e yana duba agogo. “Sorry guys, ina da lunch meeting da wasu bak’i, ya kamata in tafi, Sauran documents d’in next week zamu sa hannu to finalise the deal, yanzu kam zan tafi na gode da karramawar ku. One more thing! Ranan saturday akwai dinner da muka yi organising with family at my mansion, zan yi farin ciki in kuka zo along with your families, consider this my special invitation, in mun yi hakan zamu k’ara sanin juna, we will get to know each other well. Please do come.” ya k’ak’are maganar da murmushi, shima Sufyan murmushin ya saki haka ma Muhseen sannan a tare suka ce “Of course we will definatly come”. Hannu suka yi shaking sannan Suraj ya fice…. Muhseen ya dubi Sufyan yace “Akwai abunda ban fahimta ba, Suraj shi da kanshi was against wannan partnership d’in amma se gashi kwatsam ya nemi inda muke da kanshi, something is fishy Sufyan i don’t trust him! Tabbas akwai abunda ya taka.” dariya Sufyan yayi yace “kayi gaskiya, ni kaina nayi mamaki da ya k’ira ni yace zai zo maganar partnership sekace ba shine yayi mana rashin mutunci ba a wajen party.” Kai Muhseen ya jinjina yace “Tabbas! But in yasan wata bai san wata ba, in da ace ya san irin takun da muke shirya masa da bazai kawo kansa nan ba da zancen wannan partnership d’in. Bai san cewa this is the beggining of his doom ba, amma ance rashin sani yafi dare duhu. Duk suka bushe da dariya…. **** **** ****** ***** Ya dad’e yana zaune cikin motar shi a parking lot na hotel d’in. Kuka ne , dariya ne? Ya ma rasa emotion da zai yi portraying a fuskar shi “You’ve changed a lot….” ya fad’a yana murmushi. Ya cigaba da cewa “You are not that young girl anymore, not that childish anymore you are now a fully grown woman, so beautiful as always, you are now a very responsible young woman. Ina ma ace zan iya komawa shekaru bakwai da suka wuce da na sauya komai ya dawo daidai… Da na…….” “KEEEEEEE” Bai k’arashe maganar ba saboda wani uban k’ara da yaji bai ankara ba yaji motar shi ta k’ara gaba ta bugi wata motar dake ajiye. Kad’an ya rage Suraj ya wuntsilo waje saboda k’ofar motar shi ba a rufe take gaba d’aya ba. Kafin kace me ma’aikatan tsaron wajen sun taho cikin sauri, Suraj suka duba suka ga lafiyar shi domin sunga lokacin da ya kusa fad’owa zuwa waje, Sannan aka yi k’ok’arin bud’e d’ayan motar, Daga gani kasan cewa a buge take, da kyar ta iya d’aga k’afa hannun ta rik’e da purse ja, d’ayan hannun nata kuwa shi tasa ta janye ba’akar doguwar rigar ta wanda ya sha ado da stones kusan rabin jikin ta daga k’asa ana gani, bata da wani k’iba, sedai kam kyakkyawa ce ga wani uban hips, mayafin kanta ma reto yake a kafad’ar ta ko a jikin ta, ba tare da ta damu da abunda ta aikata ba, kutsa wa tayi ta cikin mutanen ta wuce tana surutai ta nufi mashigar Hotel d’in. Har ta b’ace Suraj bai bar kallon inda ta bi ba, a fusace ya juya ya kalli lights d’in motar shi yaga yanda ta tarwatsa masa bayan mota sannan ya maida duban shi ga ma’aikatan “Sir! Are you alright? We are really sorry for the inconvinence you have faced” wani daga cikin ma’aikatan ya furta. Kai Suraj ya gyad’a yace “No! Wanne irin alright? this is my favourite car! Dubi irin ta’asar da ta tafka…… Wacece ita da har zata tafka irin wannan b’arnar sannan without saying sorry ta wuce tayi tafiyar ta, tsoron ta kuke ne? Wannan shine karo na farko da na shigo Hotel d’in ku sannan this is the kind of welcome i recieved, tarba ta musamman! Where is your manager? Ina so inyi magana da manager yanzun nan!” Kafin kace me sun hau bawa Suraj hak’uri har shi kanshi manager d’in da aka k’ira shi haka ya dinga pleading. Suraj yace “Zan hak’ura amma i must have a word with her in ba haka ba i will sue this…….. Kafin ya k’arashe maganar manager ya had’e hannuwa biyu yace “No Sir please, please kar ayi haka. Matar da ka gani ba zama take a wannan hotel d’in ba, tana tare ne da Mr Muhseen Ali, she is a VIP sannan tana da access na flat d’in da yake anytime. And sorry to say, Mr Muhseen yana d’aya daga cikin important customers namu, Sir zaka iya magana da ita but please ranka shi dad’e…….. Suraj bai saurari me manager zai ce ba ya juya ya nufi hanyar shiga hotel d’in a karo na biyu.. Lift ya shiga ya danna numban floor d’in da Muhseen suke, yana tsaye yana jira lift ya isa se buga wayarshi yake a tafin hannun sa yana cije leb’e tsabar masifa…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page