IN SO YAKI NE CHAPTER 1

IN SO YAKI NE CHAPTER 1

  MALEEK HOLDINGs Wuse zone 5 Abuja 8:40am “Feenah kiyi sauri ki yi concluding presentation sheets d’in nan bamu da lokaci, duba kiga time in har Boss ya shigo to kwarankwatsa zai sauk’e a kan mu! Ku kuma me kuke yi har yanzu a nan? Please remove those files from there they should be at His office by now, wai meyasa kullum se na maimaita magana d’aya?! Ke kuma Asiyah barin tuna miki Boss yana buk’atar strong coffee d’in shi ne lokacin da ya iso fresh and hot! Ban san me kike yi a nan ba har yanzu, zai fi miki ki je ki kama aikin ki” Duk wad’annan maganganun Mubeenah Ali ce take yi, wanda ta kasance Personal secretary na Mr SURAJ ABDOUL-MALIK, wanda ya kasance sanannen attajiri, trendsetting industrialist,and businessman. MAITAMA DISTRICT…. Tiriri ne kawai ke tashi a bayin hakan ya maida bathroom d’in dishi dishi se k’aran zubar ruwa da kuma k’amshin shower gel dake tashi, a tsanake ya fito ya zari towel ya d’aura sannan ya nufi k’ofa, Makeken d’aki ne mai tsarin gaske, baka jin motsin komai se k’arar news dake tasowa daga TV, kayan shi na shimfid’e kan gado saida ya dad’e yana kallon su kafin ya nufi gaban madubi, bayan ya gama shafa mai ya gama fesa body spray ya d’auki comb ya taje lallausan gashin kan sa sannan ya ja ya tsaya na d’an wasu mintina daga bisani ya d’auki kayan ya kintsa waistcoat d’in shi ya saka a saman long-sleeved shirt d’in sannan ya rataye jacket d’in a hannu kafin ya feshe jikin sa da daddad’an french perfume. Agogon sa ya sak’ala sannan ya d’auki wayar sa ya nufi k’ofa. Cikin nutsuwa yake sauk’o wa daga stairs d’in tuni masu aikin gidan suka jeru gefen dining table kowanne kai a k’asa har ya kammala had’a files d’in sa dake kan side table ya gama, sannan ya nufi table d’in tsaya. Jiki na rawa d’aya daga cikin ma’aikatan ya ja masa kujera kafin nan tukunna ya zauna tsabar mulki. “Goodmorning Master” suka had’e baki wajen gaida shi amma as usual ko ta kan su bai bi ba balle yasan suna yi. Newspaper ya d’auka yana duba headlines yayinda masu aikin suka fara serving d’in shi, green tea ya kurb’a sannan ya cigaba da duba jaridan. Daga d’ayan wing d’in stairs d’in take sauk’owa cikin takun k’asaita, kyakkyawar mace ce first class, sanye da doguwar riga bak’i mai golden embroidery, kallon cin mutuncin da take wa ma’aikata ma kad’ai ya isa ya nuna cewa ita crook ce. Tana k’arisa wa dining section ta ja kujera ta zauna gefen Suraj wanda bai san ma ta iso ba, fuskar shi newspaper kawai take duba. Cikin salo ta sa hannu ta janye jaridar tana shu’umin murmushi ta ajiye a gefe kafin tace “Ohhh sweety! Look abincin ka zai huce why don’t you eat while its still ho…oo..ot”. Ta yi maganar idanuwan ta cikin nashi. Ganin yanayin idanuwan Suraj ya isa ya baka amsar cewa Meenah tayi crossing boundaries, duk wajen saida suka firgita ganin yanda Suraj yayi watsi da abincin dake kan table d’in at once sannan ya fisgo Meenah har saida k’irjin su ya doki juna, “OUCH!! careful sweety you are hurting mee”!. Cewar Meenah in a romantic tone. Suraj ya janyo ta suka bar dining section d’in zuwa living room kafin yayi wurgi da ita cikin Lallausan cushion d’in dake wajen ya d’aura k’afa d’aya kan kujeran rai a dak’ile ya nuna ta da yatsa yace “Ina tunanin baki da fahimta! I’ve warned you times without numbers to stay away from me! Why are you so stubborn? Me ya dame ki da cin abinci na? It’s my food and i will decide whether to eat it hot or cold! You have no right to do so!” Wani Shu’umin murmushi Meenah ta saki kafin ta mik’e daga cikin kujeran ta matso kusa da shi romantically ta chafke rigar shi, idanuwan ta cikin nashi hancin ta na gugan nashi ta ce “I am your wife Suraj….i have full rights to do what i want and decide whats best for you! I remembered a saying (strike the iron while it’s hot) so i’m just trying to imply that! Whats the big deal?”. Sake fisgo ta yayi jikin shi ya chafke gashin kan ta kafin yace “ki fita a harka na, na gaya miki if not i will skin you alive!” Yana kai nan ya hankad’e ta gefe yana gyara rigar shi, matsawa Meenah ta sake yi kusa da shi ta rad’a masa magana a kunne “Fushi da sassafen nan bai dace da kai ba Darling, bana son na ganka a wannan yanayin tell me what can i do to make you just happy?” Murmushi Suraj yayi ya shafa fuskar ta kafin ya had’e rai yace “Now you are talking! All i want is that you stay away from me! Ki fita a harka na, let me live my life the way i want and you live yours but don’t come near me or my belongings” in kin yi haka babu wanda zai kai ni farin ciki.” Duk maganganun da yake yi tana tsaye gaban shi ta nad’e hannuwa a k’irji tana murmushi yana gama rufe baki ya juya zai tafi Meenah ta fisgo hannun shi yana juyowa ta had’e lips d’in ta da nashi tayi kissing Suraj har saida ta cije masa leb’e yayi jini. Tun k’arfin sa ya fisge ta daga jikin sa ya kaura mata mari a kumatu, tuni Meenah ta rik’e kumatun ta tana murza wa tana shu’umin murmushi yayinda Suraj ya juya ya fice a fusace. Driver na tsaye a jikin motar yana jiran fitowar Suraj. A fusace ya fito ya bud’e k’ofa ya jefa jakar sa sannan ya dubi driver’n yace “Bani makullin motar!” Driver jiki na b’ari yace “Amma Master!” “GIVE ME THE DAMN CAR KEY!” Suraj ya fad’a a tsawace driver bai san lokacin da ya mik’a makullin motar ba, wafcewa Suraj yayi ya shige motar ya sa key ya tada motar ya fice daga gidan…… ******* ******* ******* @MALEEK HOLDINGS.. 9:30am…. A fusace ya fito daga motar makullin ma wurgi yayi da shi a fuskar wanda yake parking motocin yayinda wani d’an saurayi ke biye da shi rik’e da Briefcase d’in Suraj d’in. Tafe yake yana gyara jacket d’in sa fuskar sa babu annuri ko kad’an, tun daga reception yake shan gaisuwa amma ko ta kan su bai bi ba ballantana ya amsa gaisuwar. Da sauri take bin bayan shi kamar zata yi tuntub’e hannuwan ta rungume da files. Duk saurin da take yana kallon ta daga glass d’in gaban sa don haka ya tsaya chak, ita ma ja tayi ta tsaya tana jiran me zai aikata. Agogon shi ya duba kafin ya juya ya kalle ta yace “Miss. Mubeenah, could you please just take your time? Calm down, just hand over the files and schedules i will handle everything, you look worked out already”. Kai Mubeenah ta girgiza tace, “Nnn….No lafia k’alau nake Sir i will handle everything!” Mak’e kafad’a Suraj yayi kafin ya juya yacigaba da tafiya, lift suka shiga ya kai su third floor na building d’in inda Office d’in Suraj yake. Wani card Mubeenah ta saka a k’ofar tuni ya bud’e Suraj ne ya fara shiga se Mubeenah sannan Saurayin ya shigo ya ajiye masa briefcase d’in sannan ya taya shi cire jacket d’in sa ya rataya masa a clothes rack kafin ya fice. D’agowa yayi ya dubi Mubeenah a tsaye yace “menene Schedules d’in yau?” “Sir, Yau kana da meeting da CEO na CLOVE ENTERPRISES, by ten am, sannan zaka sa hannu a wad’annan tender files d’in, su ne files mafi muhimmanci worth billions yanzu haka letter of guarantee muke jira” “oh! And one more thing! An aiko katin gayyata na dinner daga Honourable Sufyan Khalil, its his wedding anniversary today. Kuma kai da Mrs Maleek are invited.” Jin ta k’ira sunan Meenah yasa ya tuna abubuwan da suka faru just moments ago kafin ya fito, nan take ran shi ya b’aci ya sa hannu ya sassauta necktie d’in shi kafin ya bugi table da hannun sa yace “LEEAVE!!” Mubeenah bata fahimci me yake nufi ba tace “sorry???” Mik’e wa yayi yace “I said leave my cabin ASAP!” ba shiri ta kwashi takardun ta sannan ta juya zata fice. Hot coffe d’in da aka kawo mishi ya d’auka yayi wurgi da shi a k’asa saida kofin ya tarwatse kafin ya ce “Mrs Maleek my foot!!!” Tsorita Mubeenah tayi bata san lokacin da ta zame ba har ta kusa kai wa k’asa taji an rik’o ta, rik’o mai k’arfi, zare idanuwa tayi tana kallon kyakkyawar fuskar shi kafin ta daidaita tsayuwar ta, har lokacin hannun sa guda yana sak’ale a kunkumin ta suna fuskantar juna yayinda files d’in suka yi iya shawagin su suka zube. “AMEER! In kun gama romantic scene d’in naku then let’s get back to business cos i have no time to waste!”. Suraj ne yayi maganar yayinda ya tsare su da idanu. Kumatun Mubeenah Ameer ya sumbata kafin ya rad’a mata a kunne “Sorry dear wife, it’s obvious yau an tab’o Suraj, you go, i’ll handle him.” Kai ta jinjina kafin ta bi gefen Ameer ta wuce. Kallo Ameer ya bi ta dashi kafin ya juya ya maida duban shi ga Suraj wanda ya bashi baya tun tuni yana kallon harabar company d’in……. Da murmushi Ameer ya tako zuwa kusa da Suraj shima ya dubi faffad’an harabar companin daga gilashin windon sannan ya dafa kafad’ar Suraj yace “Me ya faru haka Bro? Yau naga yanayin ka ya sauya” Suraj bai ce komai ba ya cigaba da tsayuwa, Ameer yayi k’asa k’asa da murya yace+ “duk da cewa ma de kullum haka kake ” Hararo shi Suraj yayi sannan yace “Me kake cewa?” Ameer ya mak’e kafad’a ya kad’a kai kafin yace “No! Babu abunda nace! Ko kaji nayi magana? I said nothing really!…” Kai Suraj ya girgiza yace “No i heard you say something Ameer don’t fool me!”. Ameer ya sosa kai yace “Look Suraj, akwai abubuwa da dama da suke faruwa around us that muna so mu sauya su yanda muke so but wasu lokutan babu abunda muka iya, we can’t really do anything about it. Situation d’in ka kamar haka yake, nasan baka buk’ata ko k’aunar Meenah a rayuwar ka, na sani cewa auren ka da Meenah was against your wish sannan kuma ka aure ta ne saboda farin cikin Mom ,amma wata gaskiyar itace ya kamata ka cigaba da rayuwa, you have to move on with your life. It’s obvious that Layla da kake b’ata lokacin ka a kanta ta riga tayi moving on with her life, ka tuna cewa ita da kanta ta nemi da ku rabu, sannan after all the love you had for each other she didn’t give you even a pint of chance, bata baka dama ba ko da kwaya d’aya tak, Suraj it’s been SEVEN YEARS! Ya kamata ace ka mance da abunda ya faru a baya that is your past, Layla is in your past just try and give Meenah a chance she is your future.” A hankali Suraj ya juyo ya dubi Ameer kafin yayi murmushin dole ya kad’a kai yace “Ameer bazaka fahimta bane, har yanzu na kasa accepting cewa Layla ita ne ta nemi in sake ta, Layla bata ma san me duniya take ciki ba, bata tab’a making decision a kanta ba, i agreed to divorce her back then but now i need her more than anything! Na sani cewa Meenah mata ta ce kuma we have been married for three years now, Amma ko a mafarki ban tab’a jin son ta ba, she is nowhere compared to Layla she is very cunning i cant even trust her Ameer ban ga ta inda zan fara bawa Meenah dama ba!” Kallon shi Ameer yake har ya kammala maganar sa kafin ya fuskance shi yace “Why Suraj?…….. Why exactly can’t you give her a chance? Kana tunanin bazata baka farin cikin da Layla ta baka ba? Bai wuce shekara d’aya ba da wasu watanni ka san Layla but Meenah! You were married for three years! Shekaru uku Suraj, afterall Layla jiya ce a wajen ka she was your yesterday, but MEENAH! Meenah is your today! Suraj all i am saying is give her a chance, ka bata dama ta sa ka farin ciki ko ba don mu y’an uwan ka ba kayi don Mom. Na tabbata da yau tana raye a duniya ita ma abunda zata so kenan, she would have wanted the same thing!” Suraj ya dafa kafad’ar Ameer ya girgiza kai yana hawaye yace “Ameer i am sorry, amma abunda kake so in yi a iya rayuwa na babu abu mafi wahala a gareni kamar shi, wannan zuciyar bazata tab’a zama mallakin Meenah ba, bazata tab’a buga wa meenah ba. Sorry Brother”. Ameer na jin haka ya sauk’e hannun Suraj daga kafad’ar shi yayi murmushin takaici “Suraj nasan bani da kwarewa a wannan fannin, amma suraj a matsayin mu na family a gun ka dole mu shiga wani hali in har kana cikin damuwa, shekara bakwai amma ciwon da kake da shi a zuciya bai warke ba se yaushe zaka bashi daman healing? Bazan tursasa maka ba cewa dole kaso Meenah, i just wanted you to try , make efforts in life and move on, kawai ka sani cewa, no matter what, no matter how Ni da Habeeb will always be there for you”. Murmushi Suraj yayi sannan ya rungume Ameer.. Cikin Salo ya bud’e k’ofar yana waya, turus yayi ya tab’e baki kafin ya katse wayar da yake yi ya jingina da k’ofa yana kallon su. Ganin sun dad’e a haka yasa HABEEB ya yayi gyaran murya yace “Wow! Two brothers emotional and all! What did i miss?”. “HABEEEB!” Suraj da Ameer suka k’ira sunan shi cike da mamaki kafin ya k’arisa suka rungume juna duk su ukun. Suraj ne ya zame jikin shi yace “wai me hakan kuke yi duk kun mak’ure ni? Gosh shin kun san yanda nake jin yunwa kuwa? Ban wani yi proper breakfast ba na fito gaskiya ina buk’atar abinci”. Dariya suka sa baki d’aya kafin Suraj ya d’auki jacket nashi da wayar shi suka fice. Tare suka fito daga lift d’in se hirar su suke gwanin ban sha’awa. Habeeb ya ja ya tsaya chak kafin ya ce “Wait a minute! Suraj yau ban ga Sister in-law ba ina Mubeenah ta shiga? Na san ta da aiki.” Ameer ya bushe da dariya kafin ya dubi Suraj yace “Let me tell you, yau a karon farko Boss yayi unleashing anger a kan Mubeenah, and it’s not fair at all, matata fa ba ita ta b’ata maka rai ba, now you have spoiled her mood already” Zare ido Habeeb yayi ya dubi Suraj. Shi kuwa Suraj dafe goshin sa yayi kafin yace “Look Ameer i am so sorry wallahy ba da niyya na yi ba, kun san me? Meenah ta fara wuce gona da iri! Imagine har tana da kwarin gwiwar had’a lips d’in ta da nawa tayi kissing, i mean what kind of a woman force herself on a man? Na kasa gane wanne irin rashin zuciya ne da ita.” Dariya Ameer da Habeeb suka yi kafin Ameer yace “But Suraj Meenah did the right thing, baka da niyyar nuna mata k’auna, you don’t even give her a chance saboda haka ko da nine ita ina samun slight sarari i will take advantage of it”. Habeeb ya sake sa dariya yace “kayi gaskiya Ameer Bro! Afterall Body no be wood”. Duk har shi kanshi Suraj saida suka yi dariya, Suraj bai sake cewa komai ba don yasan baza su daina tsokanar shi ba in aka cigaba da maganar don haka ya wuce gaba suka bi bayan shi suna dariya. Kan ta ya d’au zafi tana ta rubuce-rubuce bata ankara ba taji an rufe files d’in dake gaban ta. A tsorace ta d’ago, ganin Suraj ne yasa ta mik’e tsaye kai a sunkuye tace. “Sir? Kana buk’atar wani abun ne?” Murmushi Suraj yayi yace No Mubeenah, nazo in baki hak’uri , i am truly sorry about my attitude towards you earlier, You now many times a lot of things happen that are beyond your understanding but there’s nothing you really can do about it, wannan yasa nayi miki tsawa duk da ba kece mai laifin ba i am just helpless.” Nad’e hannu Mubeenah tayi a kafad’a ta ce “Hmm!…. Zan yafe maka amma bisa sharad’i, accept my condition and you are forgiven!! Simple as that” Ta k’are maganar da rik’e kunkumi Suraj yayi murmushi ya tab’e baki kafin yace “Anything for my Sister in-law!”. Ba wani abu me wahala bane gobe in Allah ya kai mu kai da kanka zaka mana breakfast, na farko Orange Milkshake na biyu Banana Sushi na uku kuma sandwich. Duk abunda na k’irga favourites d’ina ne, in ka amince zaka yi you are forgiven in kuma ka k’i then am sorry to say appology not accepted”. Zare idanuwa Suraj yayi kafin yace “WHAT?!!” Sannan ya juya ya dubi Ameer da Habeeb su kuwa suka tab’e baki gami da mak’e kafad’a, sake kallon Mubeenah yayi yaga ta tsare don haka yace “Fiiiine! Na amince zan yi, afterall i have to do it for you to accept my appology.” Kai Mubeenah ta jinjina tace “yesss”…… 4:30pm A tare suka shigo main parlour su uku, shiru kake ji babu alamar wani a ciki. Ameer zubewa yayi kan kujera yana sassauta necktie d’in shi “Why is the house so quiet? Ina masu aikin nan ne?” cewar Habeeb shima yana k’ok’arin zama. Suraj yana daga tsaye shima se cewa yayi “wa yasani ne? Who knows what cunning games that woman is playing?.” Habeeb ya dube shi kafin yace “Excuse me…? Which woman? what game? Ameer ya bushe da dariya ya ce “Look Habeeb, Suraj yana magana ne akan Meenah, His wife am i right Suraj?.” Harara Suraj ya watsa musu duk su biyun sannan yayi murmushi ya wurga wa Ameer jacket d’in shi duk suka hau dariya. A hankali ya murd’a k’ofar ta bud’e, turus yayi ganin gown d’in ta shimfid’e a kan gadon sa, k’arisa wa yayi cikin d’akin idanuwan shi kan gown d’in. K’aran ruwa ya ji daga bathroom hakan ya tabbatar mishi Meenah ce a ciki. “How dare she gather the courage to enter my bedroom!” Cewar Suraj a fusace har dunk’ule hannu yayi daidai lokacin Meenah ta bud’e k’ofa idanuwan ta cikin nashi tana sake wannan shu’umin murmushin nata wanda yafi komai spoiling mood d’in Suraj, k’arisa wa tayi daf da shi tace “Oh! Yau ka dawo da wuri, Suraj d’in da na sani yana shigowa ne kawai lokacin da zai kwanta me ya faru yau?” Hannun ta ya damk’a tun k’arfin shi ya matso da ita jikin shi ta yanda babu wanda zai tantance numfashin sa a cikin su sannan yace “Uban me kike yi a nan? Wa ya baki izinin shiga min d’aki? Tell me who gave you the right to barge into my room without my permission?” Murmushi tayi sannan ta kwace hannun ta daga rik’on da yayi mata kafin ta sa hannuwan ta biyu ta sak’ale wuyan shi tace “Miji na ne kai, d’akin ka d’aki na ne, in fact kai kanka mallaki na ne saboda haka i can come in duk lokacin da naga dama kuma in fita lokacin da naga dama! Besides ina da dalilin shigowa d’akin ka, shower na ya daina aiki so i taught i could maybe use your bathroom kafin a gyara nawa”. Cire hannuwan ta yayi daga wuyan shi yace “Nice try! Duk sauran d’akunan gidan bakiga wanda ya dace ki shiga ba se nawa! I know you Meenah, i know exactly how cunning you are! You are doing this to get my attention and trust me you won’t succeed”. Dariya tayi ta juya tana tsane gashin kanta da towel ya bita da kallo cike da takaici. Da gangan ta saki towel d’in jikin ta tana kallon shi daga madubi “Oops!” Shine kalmar da ya fito daga bakin ta. Suraj ko d’ar bai ji ba ganin ta da yayi a wannan yanyin se ma wucewa da yayi zuwa bathroom kai tsaye ta bi shi da kallo tana dariya. Yana shiga band’akin ya banke k’ofar, ita kanta Meenah saida ta firgita, a fusace ya kama shirt d’in jikin shi duk buttons d’in suka b’alle yayi wurgi da rigar bayan ya duk’unk’une ta. Ruwa ya sakar wa kan shi ya had’e goshin sa da bango yana sauk’e nannauyan numfashi “wai me wannan matar ta d’auki kanta? Tana tunanin don ta nuna min jikin ta zan so ta ne? What kind of a woman forces herself on a man like that? How disgusting!! No bazan kyale ta ba ta fara wuce gona da iri”. Towel ya janyo ya d’aura ya fice a fusace fuskar nan babu masakar tsinke, kwance ya iske ta a kan gadon shi tana danna waya, k’are mata kallo yayi har lokacin bata sa kaya ba “What the hell are you still doing nude in my room? Wai ke baki da kunya ne, have you no shame at all?” Fisgo ta yayi ya d’auki towel ya wurga mata a fuska sannan ya juya kai gefe ya nuna mata k’ofa “Wanka kika zo yi kuma kin yi, don haka ga kayan ki d’auka ki fice min a d’aki, dabarar ki bata yi aiki ba a wannan karon, try hard next time” Faffad’an k’irjin shi ta kalla kafin ta matsa daf da Suraj tayi murmushi sannan ta yi hugging d’in shi faracen ta tasa tana yagunin shi a baya tsabar yanda ta rik’e shi. Tun Suraj na iya tsayuwa kan k’afafun sa har ya kasa ya fad’i kan gado garin kokawar fisge ta daga jikin shi. “Meenah what are you doing??!” Ya fad’a da kyar kafin ya hakad’e ta gefe ya tashi zaune kansa a cikin hannuwan sa kamar zai yi hauka. Mik’e wa yayi ya sure ta bai tsaya ko ina ba se bakin k’ofa ya dire ta sannan ya rufe k’ofar sa ya koma ya d’ebo kayan ta ya watsa mata ya sake banke k’ofar ya rufe se huci yake yi “What’s wrong with this woman! Why is she behaving this way all of a sudden?” Suraj ya fad’a kafin ya d’auki kwalbar turaren shi yayi wurgi da shi ta window har saida glass d’in ya tsattsage nan abubuwan da Meenah tayi masa suka fara dawo masa haka ya dinga wurgi da kayan d’akin hatta wayar sa bata tsira ba. “How dare you Meenah!! Baki da wannan hurumin Layla is the only one who has rights over me! Bazan bari ki kwace wannan damar ba!”.. Daga bayan shi yaji muryar Habeeb yace “But she’s not here!!” Juya wa Suraj yayi ya kalli Habeeb dake ta kallon yanda d’akin ya birkice “Suraj Laylar da ka bawa wad’annan rights d’in ta rabu da kai mafi munin rabuwa shekaru bakwai da suka wuce! To be frank ban yi expecting zaka sake ambaton sunan ta ba ma, after all she has put you through, she didn’t even give you a chance, ko da sau d’aya bata baka daman yi mata bayani ba, just like that ta fice daga rayuwar ka, sannan here is another woman, all meenah wants is a chance from you, dama kawai take buk’ata ka bata ta saka farin ciki yet baka fahimta, yanzu haka Layla ta cigaba a rayuwar ta, who knows where she is? Its obvious that baka ma cikin tunanin ta, and…..” Habeeb bai gama magana ba Suraj yace “Bro please! Kar ka fara, lucky for you baka tab’a shiga yanayin da na shiga ba kuma bana maka fata ka shige shi, barin Layla da nayi ta tafi shine babban kuskuren da na tafka a rayuwa, because rashin nata shi yake k’ara min kewar ta a koda yaushe, i know wherever she is she still love me! Na san tana so na”. Kai Habeeb ya girgiza yace “I hope so”. Na zo ne daman in tuna maka anjima anniversary party d’in da aka gayyace mu, Meenah was also invited, Suraj zan rok’e ka alfarma, zaku je wajen ne a matsayin ma’aurata ban damu ba duk tsanar da kayi mata atleast ko dan saboda pressMedia try and act as a love couple atleast kar kuje kuna nuna musu true colours d’in ku, sannan as for d’akin ka in na fita zan turo masu aiki su tattare” Habeeb yana kai nan ya juya ya fice Suraj ya koma gado ya zauna yayi tagumi, duk good memories da yayi sharing da Layla su suke dawo mishi, ya d’ad’e zaune har masu aikin suka shigo sannan ya fice daga d’akin ya nufi wani flat d’in dake gefen nashi….. ****** ******* ****** Cike da bak’in ciki da takaici tayi wurgi da gown d’in nata kan makeken gadon dake d’akin nata, cije leb’e tayi kafin ta hankad’e duk kayan kwalliyan dake gaban madubin ta tana kallon fuskar ta a madubin tana huci se kace macijiya *No! No!!….. Suraj Abdoul-Maleek you have crossed all your limits!! Amma nayi maka alk’awari se na samu abunda nake buk’ata daga gareka by Hook or by crook i will fulfill my dreams….” Hawayen ta share sannan sa saki murmushi kafin ta duba agogo taga lokaci sannan ta ciro wata kwaya daga drawer ta bushe da dariya tace “Suraj you humiliated me in your house but i will make sure you get humiliated at the party tonight!!, this will be my only chance to come closer to you! Yau zan cimma buri na bazan bari wannan damar ta wuce ba!”. Tana kai nan ta bud’e purse d’in ta ta jefa kwayar a ciki ta rufe sannan ta d’auki gown d’in ta, ta bud’e wata k’ofar ta shige. ****** ****** ******* ******* Nnamdi Azikwe international airport 6:30pm… “Woman! Kina b’ata min Lokaci you better hurry up! If possible ki d’auki wannan good for nothing y’ar taki kuyi sauri, i don’t have time to waste! We are here for a very high profile party! So ki daina shashanci ki d’ago k’afa!” Matar da ya k’ira da Woman kyakkyawa ce ajin farko haka ma d’iyar ta dake biye da ita wanda zata kai ak’alla shekaru bakwai, kamar zata yi kuka haka ta d’auki yarinyar ta rungume sannan ta fara jan trolley d’in ta jiki na b’ari, Allah yasa ma y’ar ba me girman jiki bace sosai amma duk da haka matar na ji a jikin ta. Suna isa jikin motar ta dire yarinyar sannan ta bud’e mata k’ofa ta shiga ita ma ta shige. Driver ya gama loda kayan a booth sannan ya dawo ya shiga motar ya tuk’a suka bar Airport d’in…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page