FETTA CHAPTER 24

FETTA CHAPTER 24 

Ganin tana neman fad’uwa Fetta tayi saurin rik’e ta, “Lafiya?, meke damun ki?”, Tayi k’arfin halin cewa “Kaina ke ciwo”, Tana dafe gefen kanta dake masifar sarawa tamkar ana buga mata guduma, Ta zaunar da ita kan kujera tana mata sannu, Suraj kallo d’aya ya mata bai sake duban ta ba, Yana faman jijjiga Mimi. “Bari na tafi”, Ta fad’a tana mik’ewa, “Zaki iya kai kan ki gida?”, Fetta ta tambaya cike da damuwa, “Kar ki damu zan iya”, “Allah ya k’ara sauk’i”, Ta amsa da “Amin” Bata san ina take jefa k’afarta har ta kawo bakin motar ta, ta bud’e ta shiga, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” Take maimaitawa, Da k’yar ta tayar da motar ta nufi gida, cike da tsananin tashin hankali, bata bi ta kan mutanen dake falo ba, ta nufi d’akin ta, tasa key ta rufe, jakarta ta cillar da mukullin mota saman gado, ta hau zagaye d’akin, “Tabbas shine, ko shakka babu shi ne, bazan tab’a manta tabon da ke hannun shi ba”, Hawaye masu zafi suka zubo mata, “Taya zan fara sanar da Fetta waye Suraj?, taya zan sanar da ita ?”, Ta fad’a cikin d’aga murya, ta fad’a kan gado tana fashewa da matsanancin kuka. Fetta jikinta yayi sanyi da yanayin Yasmeen, tana kyautata zaton ba ciwon kai kad’ai ke damun ta ba, amma kuma ba a haka ta shigo ba, meya canza ta suddenly, Suraj ya katse mata tunani “Karb’e ta, zan fita”, Tasa hannu ta karb’e ta, d’aki ya shiga, ya sake fesa turaruka ya fito, “Allah ya bada sa’a” Ta fad’a cikin sanyin murya, “Amin”, Har ya kai k’ofa ya juyo yace “Ba zaki mun rakiya ba”, Ba musu ta mik’e ta raka sa harabar gidan, Driver ya taso da sauri ya bud’e masa mota, Ta koma cikin gida, tana mamakin sabon salon da ya tsirfu dashi.

Wayarta ta jawo ta kira Yasmeen taji jikin ta, Yasmeen wacce fuskarta tayi jajir tsabar kuka jin k’arar wayarta, da k’yar ta iya d’ago kanta da ya mata nauyi, tayi receiving, “Hello Yasmeen ya kika je gida?, ya jikin ki?, “Da sauk’i Alhamdulillah”, Ta fad’a murya a dashe, “Dan Allah ki fad’a mun meke damun ki, nasan ba ciwon kai kad’ai bane, kuma ciwon kai ba zai sa kiyi kuka har muryar ki ta dashe ba”, Ba zata iya fad’a mata ba, ba zata zama silar rugujewar farin cikin ta ba, a yadda ta hango soyayyar Suraj a k’wayar idon ta, ba zata zama silar jefata a wani yanayi ba, Ta katse mata tunani “Kinyi shiru, ba zaki gaya mun ba ko, you can’t share your problems with me, baki d’auke ni yar’ uwar ki kamar yadda kike fad’a ba”, “Tamkar jinina haka nake jin ki Fetta, ki yarda dani babu komai”, Fetta ta kashe wayar cike da takaicin rashin sanar da ita. Yasmeen tabi wayar da kallo, tana ji wasu hawaye na zubo mata, gara kiyi fushi dani Fetta akan na gan ki cikin damuwa da tashin hankali, i can’t bear to see you in pain, rayuwar k’uncin da kika yi a baya ta isa, bana so ki sake wata. Fetta ta kasa natsuwa, tana son tasan damuwar Yasmeen ko zata iya taimaka mata, haka take jin ta tamkar yar’ uwarta ta jini, wunin ranar sukuku tayi shi, Ana sallar isha’i Suraj ya dawo, ya tarar da ita tana sallah, Mimi na sashen Hajiya tunda yamma ta aiko aka karb’e ta, Shima alwala yayi ya gabatar da sallah, Ta idar tayi folding sallaya, Ta koma falo ta zauna, yana idarwa ya biyo ta falo, “Sannu da zuwa”, “Yawwa” Ya amsa yana zama kujerar kusa da ita, Ledar da ya shigo da ita, ya bud’e shawarma ce, ya d’auki d’aya ya mik’a mata d’aya, Tace “Thanks”, Duk da dad’in da tayi, rabi taci, ta ajiye saura, Suraj ya lura da sanyin da tayi, bai tambayeta dalili ba. Daren ranar ma sai da suka raya shi, idan yana tare da ita sam baya iya controlling kansa, Fetta bata hana sa. 3:00 na dare STORY CONTINUES BELOW Bilkisu ce a wani k’aramin d’aki, babu kaya a jikinta, tana zagaye wani kasko dake fitar da hayak’i, had’e da wari marar dad’i, sau bakwai tana zagaye wa, ta duk’a ta bud’e baki, hayak’in na shiga ciki, sai faman tari take, idonta ya cika da hawaye, Sai da garwashin ya mutu, ta d’aura zani ta fito, Aunty Jummai na tsaye bakin k’ofa tace “Sannu, karb’i wannan ki shafe fuskar ki da kan ki dashi”, Wasu ruwa ne masu kalar fitsari a cikin k’aramin galoon, ta karb’a ta zuba a hannu, ta shafa, Aunty Jummai tayi murmushi tace “Saura k’iris”, Bilkisu tayi dariya tana nufar d’akin ta. Suraj tun 6 ya fita, zai je lagos a ranar ya dawo, Baya jin zai iya kwana can.

Fetta tana so ta kira Yasmeen taji lafiyar ta, haushin ta ya hana, a ganin ta babu wanda yafi cancanta ta fad’a ma matsalar ta sama da ita, bata b’oye mata matsalolin ta, meyasa ita zata b’oye mata. Feena ta fito super market, rik’e da ledoji a hannu, Wani saurayi ya bi ta, ta bud’e mota zata shiga, Yace “Yan mata”, Ta juyo ta kai dubanta gare sa, numfashin ta ya tsaya cak na wucin gadi, kyaun sa da had’uwar sa ya tafi da imanin ta, Murmushi ta mishi, Yace “Am sorry na tsayar dake samun titi, ko zaki iya bani number ki”, Ya mik’a mata wayar sa k’irar 11pro max, ba musu ta karb’a ta saka mishi, Yayi murmushi yace “Thank you, sai na kira ki”, Ta mayar masa murmushin tana d’aga kai, Cike da farin ciki ta koma gida, tayi babban kamu, bata tab’a had’uwa da saurayi mai kyawun sa ba, ga kuma naira. Alhaji Tambari yace baya so a d’auki lokaci na auren Tasleem da Bello, an saka biki nan da sati uku, Yaba Kawu Lamid’o kud’ad’en masu yawa yace su k’ara ayi hidima yasan ba wani kud’i ne dashi ba, kuma zai basu gidan da zasu zauna, ya samar wa Bello aiki ya rik’a karb’ar albashi mai tsoka, baya son yar’ sa ta wahala, Kawu Lamid’o da Gwaggo murna kamar ta kashe su, irin auren da suke so dan’ su yayi kenan, auren jari, ya samu suma su samu. Bello yana shirin fita, Karima ta rako sa tana masa Allah ya tsare ya bada sa’a, Kiran Kawu Lamid’o ya shigo wayar sa, sai da gaban sa ya fad’i, bai d’auki wayar ba, sai da Karima ta koma ciki, baya so tasan halin da ake ciki, ta shiga damuwa, “Abba ina kwana?”, “Lafiya lau, mun kai k’arshen maganar auren ka da Tasleem, sati uku masu zuwa, ba yardar ka nake nema ba ko shawara, nan da sati biyu ka dawo gida”, Bai jira cewar sa ba ya kashe waya, zufa ta karyo masa, tsananin tashin hankali ya rufe sa, rikici ne babba ke tunkaro rayuwar sa, ya zai yi da Karima, ba k’aramin tashin hankali za’a yi ba idan Kawu Lamid’o ya gano ya auri Karima, zai iya cewa ya sake ta, ba zai iya rabuwa da ita ba, raba shi da ita tamkar raba shi da rayuwar sa ne, “Ya Allah” ya furta. Feena saurayin da ya karb’i number ta, ya kira ya bayyana mata soyayyar sa, ba tare da wani jan aji ba ta amince, Sunan sa Fahad, ya fad’a mata auren ta yake son yi, Karon farko a rayuwar ta da taji tana son aure, komai nashi ya mata, ya fad’a mata baya son a d’auki lokaci, a cikin satin nan zai turo iyayen sa, baya so wani ya mishi overtaking, Hakan ya mata dad’i sosai, ko banza ta huta da maganar Hajiya kan ta fitar da miji, da bikin Su’ad ma yan’ uwa nata sa mata baki, k’anwarta ta riga ta aure. Bayan kwana uku

Fetta shiru bata ji daga Yasmeen ba, ta ajiye haushin ta da take ji gefe, ta kira taji a kashe, hankalin ta ne ya tashi, Allah yasa lafiya, Suraj ta samu a falo yana kallon news, Mimi na hannun sa yana shan yoghurt, Murya a sanyaye tace “Dan Allah ina so naje na duba Yasmeen yau kwana uku ban ji daga gare ta ba”, “Ki shirya nayi dropping d’in ki, ki saka hijab”, Tace “Toh”, Minti biyu ta fito cikin shiri sanye da hijab iya gwiwa ya mata kyau sosai, Suraj ya zuba mata ido, kafin ya mik’e ya d’auki mukullin mota, ya fita, tabi bayan sa. Gaban mota ta shiga, shi ke driving, yau ce rana ta farko da suka shiga mota tare, motar shiru, sai k’ira’ar Sudais dake tashi, bakin gate d’in su Yasmeen yayi parking, “Ki kula da kanki, kar kije ko’ina ko bakin gate ban yarda ki fito ba, ki ajiye wayar ki i will call you idan na dawo”, Ta amsa da “Toh”, Ta bud’e murfin motar ta fita. A falo ta tarar da k’annen Yasmeen, suna kallo, suka gaisheta ta amsa tana tambayar su Ina Yasmeen, D’ayan su ya amsa “Tana d’aki” ya karb’i Mimi, yarinyar akwai farin jini duk wanda ya ganta sai yaji yana son d’aukar ta. Da sallama ta tura k’ofar d’akin ta shiga, Yasmeen wacce tayi nisa a tunani bata ji shigowar ta ba, sai ji tayi an dafa ta, tayi firgigit, ganin Fetta tayi faking smile, Kallo d’aya zaka mata kasan tana cikin damuwa, Zama tayi kusa da ita tana kamu hannun ta, “Ashe baki d’aukeni yar’uwa ba kamar yadda kike fad’a, a zatona idan kina da damuwa ni zan fara sani, kina tunanin hankali zai tab’a kwanciya sanin kina tare da damuwa, Dan Allah kiyi proving d’ina wrong ki gaya mun damuwar ki Yasmeen”, Ta k’arasa tamkar zata yi kuka, “Ba haka bane Fetta, ko kad’an ba haka bane, ki fahimce ni Dan Allah”, “Idan ba haka bane yaya ne, taya kike so na fahimce ki Yasmeen, idan ba so kike nima na shiga damuwa fiye da taki ba, ki gaya mun meke damun ki” Kanta ta shiga girgizawa tana hawaye, Fetta ta matse hannayen ta tace “Ki sanar dani Dan Allah”, Yasmeen wani sashen na zuciyar ta na son sanar da ita, yanayin da wani sashe ke hana ta, “Ki fad’a mata tasan da wane mutumin take tare, b’oye mata shine babban kuskuren da zaki yi, ranar da ta gane gaskiya ba zata tab’a gafarta miki ba na b’oye mata, Fetta bata yi deserving Mutum irin Suraj ba” Zuciyarta ta fad’a mata, “Ki fad’a mun please Yasmeen”

“Zan gaya miki, amma ki mun alk’awari ba zaki bari ki shiga damuwar da zata tab’a lafiyar ki ba, zaki zab’a mai karb’ar k’addara a duk halin da tazo miki, idan kika sa damuwa a ranki bazan tab’a gafartawa kaina ba”, “In Shaa Allah ba zan yi ba”Yasmeen bakinta taji ya mata nauyi, tamkar an d’auke dutse an danne harshen ta dashi, tunanin yadda Fetta zata ji maganar take, bata son ta zama silar rugujewar farin cikin ta, Fetta ta katse mata tunani “Ki sanar dani, kina k’ara saka ni a damuwa”,+ Cikin sark’ewar murya tace “Su..ra..j ya….”, Tamkar wacce aka shak’e ta kasa k’arasawa tana haki, “Ki sanar dani Dan Allah, me Suraj yayi wani abu ya same shi”, Ta fad’a tana jijjiga ta, Sam ta manta shi yayi dropping d’in ta yanzu, Yasmeen ta damtse idonta tana dafe k’irjin ta tace “Yana d’aya daga cikin yan’ fashin da suka kashe su Daddy, shine ogan su” Zuciyarta tayi mummunan bugawa, kanta yayi masifar sarawa, ta saki Yasmeen tana ja da baya, komai na d’akin juya mata yake, zuciyarta ta kasa yarda da abunda kunnen ta suka jiye mata, kanta ta shiga girgizawa tana fad’in “No ba Suraj d’ina ba, wallahi ba shi ba ne, you are mistaken kice mun ba shi bane Yasmeen, wallahi ba shi ba ne” Yasmeen hawaye take ta kasa cewa komai, sai jin fad’uwar Fetta tayi, da sauri tayi kanta, da sauri tayi kanta, tana rik’o ta, ta zama mutum mutumi, sai fad’in take “Ba shi ba ne, wallahi ba Suraj ba ne”, Yasmeen dana sanin sanar da ita take, yayin da wani b’angare na zuciyarta ke sanar da ita hakan shine daidai, Zame jikinta tayi daga rik’on da Yasmeen ta mata tace “Ki fad’a mun wacce hujja kike da na cewa Suraj ne”, zuciyarta ke mata d’aci, tana jin tabbas sharri ake mishi, ba zai tab’a zama cikin yan’ fashin da suka kashe Addani ba, Yasmeen na matsar k’walla, Daren da abun ya faru na dawo mata a k’wak’walwa da ido, “A lokacin da aka harbi Ya Sadeeq, na shiga ihu, wanda hakan yasa ogan su sa hannu ya rufe mun baki, Idona na kan hannun shi, ina jin tsananin tsanar shi da duk wanda suke tare, tabon da na gani a hannun shi, shi na rik’e wanda nasa a raina duk inda na gani zan gane, ranar da Suraj ya k’arbi Mimi wurina, naga tabon a hannun shi, shine wallahi shne”, Ta k’arasa da fashewa da matsanancin kuka, Fetta jikinta ya shiga kyarma, tana jin wani zafi cikin k’ashin ta tamkar ana gasa ta cikin oven, zufa ke keto mata duk da sanyin Ac dake d’akin, ba zata iya misalta yadda take ji ba, Amma zuciyarta ta kasa gaskata Suraj dan’ fashi ne mai kisan kai, “Bazan tab’a yarda da hakan ba, har sai nayi bincike na tabbatar da hakan”, Ta fad’a tana jin d’aci cikin bakin ta, Yasmeen ta rik’o hannun ta tace “Na yarda kiyi bincike, kuma ina fatan hasashe na ya zama ba gaskiya ba, ina hango mutumin kirki a tare da Suraj, taya za’a ce ya kasance dan’ fashi”, “Shine abunda ke d’aure mun kai Yasmeen, zuciyata ta kasa yarda da hakan amma ina tsoro, ina tsoro ya zama gaskiya, ina tausayin Mimi”, Ta fad’a tana jin karyewar zuciya, da tsananin tsoro da fargaba, Yasmeen ta kama hannun ta tana k’ok’arin comforting d’in ta. Suraj yana ajiye Fetta ya nufi gidan marayun sa, ya duba lafiyar su, tare da tambayar matsalolin su, office d’insa ya zauna, Yana lissafin abubuwan da yaran ke buk’ata, Pass 6 ya fito daga gidan marayun, ya nufi gidansu Yasmeen. Zaune suke jingum ita da Yasmeen, kowane yayi nisa a tunani, k’arar wayarta ya fargar dasu, Ganin Suraj ne, k’irjinta ya duka, jiki a sanyaye, ta d’auka, “Ki fito ina bakin gate”, Bai jira cewar ta ba ya kashe, Ta kai dubanta ga Yasmeen, “Yazo zamu wuce”, Tasowa tayi ta kama hannun ta, “Ki mun alk’awari Dan Allah bara kisa damuwa a ranki ba, zaki cigaba da walwalar ki har ki gano gaskiyar komai”, Fetta ta numfasa tace “Ba zan miki alk’awaro rashin damuwa ba, amma In Shaa Allah zan yi yak’i da zuciyata wurin ganin damuwar bata tab’ani ba, kema ina so kiyi k’ok’arin yin haka”, Tayi nodding kai tace “In Shaa Allah”

Bakin k’ofar falon su ta mata rakiya, ta koma ciki, Mahmoud brother Yasmeen har mota ya musu rakiya saboda Mimi, Tamkar wacce k’wai ya fashewa a ciki ta bud’e murfin motar ta cigaba, tsoro da fargaba ne a tattare da ita, Tun shigar ta motar bata kalle shi ba, shima bai bi ta kanta ba har suka kawo gida, Ita ta fara fita, d’aki direct ta shiga, ta kwantar da Mimi, ta shiga toilet ta d’auro alwala, Ta gabatar da sallar magrib, Suraj masallacin dake had’e da gidan ya tsaya yayi sallah kafin ya shigo, A kitchen yaji motsin ta, Ya nufi kitchen d’in, abincin dare take k’ok’arin had’awa, “Baki gaji ba?” Ya fad’a yana kafeta da ido, Ba tare da kalle shi ba tace “Eh”, “Ok ki dafa taliya shi zai fi miki sauk’i”, Ta mishi nodding kai, Ya juya ya fita, Duk da zuciyarta bata yarda ba, tana cike da tsoro da fargaba, ko a mafarki bata fatan hakan ya kasance gaskiya. Cikin minti 45 ta kammala, ta jera akan dining table, Ta d’auko ruwa da drink ta ajiye, Taji muryar sa “Zubo ki sauko k’asa muci”, Taji kamar tace masa ta k’oshi, sanin halin sa tursasata zai yi kuma bata son wani dogon surutu, Ta d’auki plate tayi serving, Jiki a sanyaye ta ajiye gaban sa, Kusa dashi ya nuna mata ta zauna, Ta zauna, “Oya fara ci”, Fork ta d’auka ta d’ibo zata kai bakin ta, kalaman Yasmeen ya dawo mata “Yana d’aya daga cikin yan fashin da suka kashe shine ogan su”, Sakin cokalin tayi, k’irjinta na duka, A rud’e yace “Are you ok?”, Sai a lokacin ta ankara da abunda tayi, Tayi k’arfin halin cewa “No ba komai, sub’uce mun yayi”, Kanta sunkuye k’asa, “Kalle ni”, Ta d’ago kanta but ta kasa had’a ido dashi, Hannu yasa ya tallabo fuskarta, yana had’e idonsu cikin na juna, Zuciyarta taji tamkar zata fasa k’irjinta ta fito, wani tsoro ke sake shigar ta, Tayi saurin damtse su, “Tell me meye matsalar meke damun ki?”, Kasa ko da k’wakk’waran motsi tayi balle ta bashi amsa, sai jikinta dake kyarma, Rungumota yayi jikin sa, Yana jin yadda take kyarma, Damuwa ta lullub’e sa lokaci d’aya, ya sake matse ta jikin shi, Bata bar kyarma ba, d’umin jikinsa da take ji na k’ara mata fargaba, gangar jikin ta na son raba ta da gangar jikin sa, yanayin da zuciyar ta ke hanata, tana jin buk’atar d’umin jikin nasa. Feena da zuwa Hajiya zancen Fahad ba k’aramin farin ciki tayi ba, Tayi addu’ar Allah ya tabbatar da alkhairi, “Ki sanar da Ya Suraj cikin satin nan zasu turo”, Hajiya tace “Ohh ni ko kunya baki ji”, Dariya tayi tace “Kaii Mama”, “Eh mana Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi”, Ba kunya ta amsa da “Amin” Su’ad satin amarcin ta tayi shine ba wani tarairaya balle jin dad’i, kwata kwata sau biyu ya kusance ta, shime cewa yayi bai ji ta daidai ba, wai anya tayi gyara kuwa kafin aure, Ranar tayi kukan bak’in ciki da takaici, Kullum ya fita tun safe sai cikin dare yake dawowa, ita kad’ai a gida kamar mayya, babu dan’uwan sa ko d’aya da ya taba kawo mata ziyara, Yau ma har d’aya na dare bai shigo ba, zaune take jingum tana yi tana duba agogo, har bacci ya soma d’aukar ta taji k’arar bud’e k’ofa, ta mik’e tace “Baby ina ka tsaya yau, kasa duk hankalina ya tashi”, Ko kallo bata ishe sa ba ya wuce ciki abun sa, wani k’ulloton bak’in ciki taji ya tsaya mata a wuya, “Haka dama aure yake, soyayyar iya waje ce kawai”, Ta fad’a kan kujera tana shafewa da kuka mai cin rai. Kiran sallar isha’i yasa ya raba jikin sa da nata, Yana mik’ewa, “You take care, zanje masallaci”, Tayi nodding kai, Ya fice, Jiki a sanyaye ta mik’e ta shiga d’aki, ta nufi toilet, alwala tayi ta gabatar da sallar isha’i, akan sallayar ta zauna tana addu’o’i, wanda rabi akan Suraj ne kar ya zama d’aya daga cikin yan fashin da suka kashe Addani, Har ya dawo ya tarar da ita, zama yayi kan gado ya jawo sytem yana operating, bayan minti biyu yana kai duban sa gare ta, Ta kishingid’e a wurin tamkar mai bacci, bata son doguwar magana na had’a su da Suraj, kallon sa ma bata cika son yi ba, tsintar kanta take da tsananin fargaba.+

Tasowa yayi ya d’agata tamkar baby, ta sake langab’ewa kamar mai bacci, ya d’aura ta kan gado, ya gyara mata kwanciya tare da jan bargo ya rufe ta, ya koma gefe yana cigaba da operating system. Duk wani motsin sa akan kunnen ta, but idan ka kalleta zaka rantse bacci take, Ya kammala abunda yake, ya rufe system d’in ya ajiye, ya gyarawa Mimi kwanciya, yaja bargo ya rufe cikin mintunan da suka gaza goma bacci ya d’auke sa. Fetta sam bacci ya k’auracewa idon ta, tunani da damuwa suka taru suka dababaiye ta, kalaman Yasmeen ke mata yawo a k’wak’walwa. Dare ya tsala sosai, baka jin motsin kowa sai haushin karnuka, Bilkisu ta fito daga k’aramin d’aki, d’aure da zani, tana tari, idonta na zubar hawaye, “Umma ni gaskiya na gaji da wannan hayak’in, wallahi kamar zan suk’e”, Aunty Jummai ta dafa kafad’arta tace “Kiyi hak’uri daga gobe shikenan, ko kin fara hak’ura da komawa gidan Suraj ne”, Ta jinjina kai tace “Tabb ai har abada bazan hak’ura ba, kwanakin nan har mafarki nake na koma, muna zuba soyayya”, “Hakan ne zai kasance” Aunty Jummai ta fad’a cike da tabbaci, Bilkisu tayi dariyar farin ciki. Kiran sallar asuba a kunne Fetta da sam bata runtsa ba, ana cewa bacci b’arawo a daren jiya bai sace ta ba, Dubanta takai kan Suraj dake bacci hankali kwance, ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ta kalli Mimi wacce itama ko motsawa bata yi ba, yarinyar sam bata da rigima. Toilet ta shigo ta d’auro alwala, fitowar ta yayi daidai ta tashin sa, idon ta ya sauka cikin nasa, Ta d’auke kanta tana k’arasawa cikin d’akin ta d’auki sallaya, Addu’ar tashi daga bacci ya karanta ya mik’e, ba b’ata lokaci yayi alwala, ya fice zuwa masallaci. Dawowar sa masallaci ya tarar da missed calls na Rabi’u, yabi kiran, “Hello Ranka ya dad’e ina kwana?”, “Lafiya”, “Maganar aikin jiya”, “Ina fatan komai ya tafi daidai”, “Eh Ranka ya dad’e”, “Ok gani nan zuwa”, Hankalin Fetta gaba d’aya ta tattara kan wayar da yake, but idan ka kalleta zaka d’auka hankalin ta na kan Qur’anin dake gabanta, A gaggauce ya shirya bai tsaya breakfast ba, Ya fita, yau ko samun damar ce mata ya fita bai yi ba, “Saurin me yake?, meye ya tafi daidai?”, Ta jefowa kanta tambayoyin da bata da amsar su. Qur’anin ta rufe ta ajiye mazaunin sa, ta nad’e sallaya, drawers da tasan yana ajiye takardu ta bud’e ta shiga dubawa, files guda biyu ta gani da d’an k’aramin littafi, Ta jawo takardun dake cikin file d’in, rubuce rubuce ne na gidan gonar sa, d’ayan ta bud’e takardu ne na gidan marayun sa, Taja tsaki tana mayar dasu, k’aramin littafin ta d’auka zata bud’e, Mimi ta fara kuka, Ta ajiye ta d’auke ta.

K’arfe bakwai na safe Karima ta kammala karin kumallo, ta jere musu a tsakiyar carpet, Tayi serving d’insu ita da Bello, loma biyu yayi yace “Ya k’oshi”, Da kallo tabi sa “Meke damun ka?, kwana biyu naga ka canza”, Faking smile yayi yace “Ba komai, wurin aiki ne al’amura suka yi yawa”, “Toh Allah ya shige maka gaba”, Ta fad’a ba dan ta yarda ba, Ya amsa da “Amin”, Bello a kwanakin nan ya rasa natsuwar sa, damuwa ta samu wuri tayi gini a zuciyar sa. Suraj ne tsaye da cup mai d’auke da lemo a falon guest house d’in sa, Yayi sip d’aya yace “Bravo wannan karon kayi k’ok’ari Rabi’u, Alhaji Badamasi yau zaki yi kuka da idon ka, kayi dana sanin abubuwan daka dad’e kana shukawa”, Yayi dariya mai nuna farin ciki, Rabi’u yace “Baka ga idon sa ba, kamar an kama shi yayi satar gyad’a”, Suraj ya kwashe da dariya, Rabi’u kallon mamaki yabi sa dashi, a tsawon shekarun da suka yi, bai tab’a ganin dariyar sa haka ba, “Zan ninka ma albashin ka”, Rabi’u ya shiga zuba godiya, Ya umarce sa ya tafi, Ya zauna kan kujera yana cigaba da shan lemon sa. Fetta bata samu duba littafin ba, Hajiya ta buk’aci ganin ta sashen ta, yarinyar abokin Baban su Suraj ce tazo, wacce zata yi sa’a da Fetta, A falo ta tarar da Samee na kallo, ta gaisheta, ta karb’i Mimi, duk cikinsu ita kad’ai ke d’aukar ta, Cike da ladabi ta gaishe da Hajiya ta amsa, “Waheeda ce yar’ abokin marigayi jiya suka dawo nan kusa damu da mijinta, a Abuja suke aka mishi transfer wurin aiki”, Da sakin fuska Fetta ta kai dubanta gareta tace “Sannu ya gida?”, “Lafiya lau”, Ta karb’i yaron dake hannun ta wanda zai girmi Mimi da kad’an, “Ya sunan sa?”, “Waleed”, “Allah ya raya”, “Amin” Hajiya tace “Kije da ita b’angaren ku, a can zaku fi sakewa”, Fetta tayi murmushi tacewa Waheeda su je, Waheeda bata da wuyar sabo, ta saki jiki tana ta ba Fetta labari, wacce itama ba laifi ta saki jiki da ita, ta yaba da hankalin ta, sai gab da magrib tace zata wuce, suka exchanging number wanda Waheeda ta buk’aci haka, ta mata rakiya har bakin gate, “Sai kinzo ina jiran ki”, Fetta tayi murmushi tace “In Shaa Allah zan shigo”, “Allah ya yarda”, “Amin”, Ta koma ciki. Tana shiga, Suraj ya rufa mata baya, bata so dawowar sa yanzu ba, taso ta duba littafin d’azu, Da sakin fuska tace “Sannu da zuwa”, Ya amsa da “Yawwa”, Yana zama kan kujera, D’aki ta wuce, Tv ya kunna ya kamu tashar labarai, anan yake ganin ansa abunda ya faru da Alhaji Badamasi, yayi murmushi, yana jin nishad’i. Bayan sallar isha’i ya shiga b’angaren Hajiya, take sanar dashi zancen Fahad, ba k’aramin farin ciki yayi ba, Ya nuna goyon bayansa akan su turo, a shirye suke, Hajiya tace “Ba za’a sa nan da wata uku ko hud’u ba, naga baka dad’e da hidimar Su’ad ba”, Murmushi yayi yace “Dukiyata gaba d’aya mallakin ku ce, saboda ku nake tara ta, bana jin k’yashin kashe muku ko nawa ne, duk abunda kuke buk’ata a duniyar nan in dai bai fi k’arfina ba zan muku”, Sosai taji dad’in furucin sa tace “Allah ya maka albarka, ya tsare ka da dukkanin sharri”, Ya amsa da “Amin” Su’ad ce zaune jingum, abun duniya ya isheta, kallo take amma sam hankalinta baya kai, wayarta ta soma ringing, ganin Feena ce ta d’auka, Bata tsaya sun gaisa ba tace “Sis guess what?”, “Me?”, “Gobe za’a zo neman aurena”, “Allah ya sanya alkhairi”, “Ya naji bakya farin ciki”, “Kaina ke ciwo”, “Ko dai na kusa zama mother”, “Uhmm ni sai anjima”, Ta kashe wayar a ranta tace “Baki san ya auren yake ba shiyasa kike zumud’i, sai kinji dama baki yi ba”, Suraj da Fetta na zaune falo suna kallo, shi ya buk’aci zaman ta, tayi k’ok’arin daidaita natsuwar ta da b’oye damuwar ta, ta yadda ba zai gane ba, Waya ya kira yace “A mishi booking flight na zuwa lagos gobe da safe”, Fetta taji tana so tasan harkokin sa na can, but taya? Zuciyarta tace “Hanya d’aya ce ki bi sa”, Tana tsananin son bin sa, dan gudanar da bincinken ta, zata jure duk wata bak’ar magana da zai jefa mata, Cikin dakewa tace “Dan Allah ina so nabi ka”, Da mamaki yake kallon ta, at the same time yaji dad’in furucin ta, yana buk’atar zama lagos na kwanaki, rashin su a kusa ke hana masa zama, “Ki shirya gobe by 7 zamu tafi”, Bata tsammaci amincewar sa da wuri ba, sosai taji dad’i, Tace “Nagode”, Da hannu ya mata alamar tazo ta mishi tausa, da biyu yayi, yana buk’atar ta ya fake da tausa, ba musu ta shiga yi masa, daga nan suka zarce duniyar ma’aurata. 6:30 na safe Fetta ta shirya tsaf, ta had’a kayanta da na Mimi a akwati d’aya, k’aramin littafin ta faki idonshi ta d’auka tasa can k’asan akwati, Sun shiga sashen Hajiya su mata sallama, ta tashi sallar asuba bata koma ba, taji dad’in ganin tare zasu tafi, Haka ya k’ara tabbatar mata suna zaman lafiya, Text message ta turawa Yasmeen da Aliya cewa sun tafi lagos, Yasmeen na gani tasan yana cikin shirin Fetta na yin bincike, Aliya kam murna tayi sosai, har tana sanar da Mallam yaji dad’i tare da musu addu’ar zaman lafiya mai d’aurewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page