FETTA CHAPTER 20

FETTA CHAPTER 20

b Fetta tayi wanka ta canza kaya zuwa marasa nauyi, suna hira da Yasmeen bacci ya d’auketa, Ganin tayi bacci Yasmeen tace “Lallai Fetta duk gajiyar ce, bari na tashi na tafi”, Ta sumbaci baby a goshi, Ta fice. + Suraj da sallama ya shiga falon, Samee kad’ai ya tarar tana kallo, “Yaya ina wuni?”, “Lafiya lau”, “Ina Fatima?”, Tana d’akin k’asa, “Toh me take a can?”, Ya tambayi kansa, Fetta tayi nisa a bacci bata ma san Hajiya ta shigo ta d’auki baby ba, Mamaki ne ya cika sa ganin tana bacci, yayi tapping k’afar ta, Ta bud’e ido ta zube su a kan shi, Gira ya d’aga mata alamar “Ya dai?”, Kanta ta kawar gefe, “Me kike anan baki je kin gyar sashen mu?” (Part d’in a gyare yake yace hakane dan kar ya fito direct ya tambaye ta), “Hajiya ta buk’aci zamana a nan”, Murmushin gefe baki yayi a ransa yace “Ba zai yiyu ba”, Ya fice, Ta gyara kwanciya ta cigaba da baccin ta, A d’aki ya samu Hajiya, Tana goye da baby, Gefen ta kud’i ne tana k’irgawa, “Mamana yau kece da goyo”, Tayi dariya tace “Jikalle ai yar’ gata ce dole tasha baya”, Yaji dad’in ganin yadda take son yar’ sa amma dole taso jinin sa saboda soyayyar da take mishi. Yayi shiru yana tunanin yadda zai b’ullo mata da maganar, Can ya nisa yace “Mum kawota muje mu kwanta, ki huta”, “A’ah barta, idan ba kuka tayi ba, tana nan tare dani”, “Idan dare yayi fah, muka shige”, Murmushi tayi tace “Ohh na manta na fad’a maka Fetta na nan har sai tayi arba’in”, Bai san lokacin da yace “Saboda me?”, “A k’aida haihuwar farko mace gida take zuwa sai tayi arba’in, ni kuma Fetta ya’ na d’auketa shiyasa na buk’aci zaman ta nan”, “Toh Mama meye difference na nan da sashen mu, ta zauna a can mana”, Hajiya ta girgiza kai, Zai sake magana, ta katse shi “Bana son musu Suraj”, Yayi shiru cike da takaici, Hajiya kad’ai ta isa ta mishi haka, ko kad’an baya iya tsallake maganar ta. Tasleem ke ta faman dialing number, yayi ringing har ya tsinke ba’a d’auka ba, wannan shine kira na shida tayi, Sai da ta kusa tsinkewa aka d’auka, Ta sauke ajiyar zuciya’ “Ya dai, ina jin ki”, “Ina ka ajiye wayar ka ina ta kira ba’a d’auka”, “Kin ga na gaji da baki information akan mai gidana, ina ganin haka tamkar cin amanar sa nake bayan halaccin sa gareni, besides bansan me kike dashi ba”, “Haba Rabi’u na gaya maka wallahi son shi nake, ba zan tab’a cutar dashi ba”, “Naji amma ki nemi wani ba zaki k’ara jin komai daga gare ni ba”, Ya kashe wayarsa ya sata reject list, Tasleem ta shiga kiran sa yana sa failed, Tsaki tayi tare da cillar da wayar cike da takaici, “Kije gidan sa ko zaki samu wani bayani” Zuciyarta ta fad’a mata, Wani b’angare yace “Idan aka kama ki fah”, “Ba zan bari a gane ni ba”, Wayar ta d’auka ta yafa mayafi ta fice, A bakin main entrance na gidan tace ma mai taxi ya tsaya, D’aya daga cikin securities ya taso ya tambaya “Lafiya”, Tace Matar Suraj take tambaya tana nan, “Ai sun koma 9ja”, Gabanta ya fad’i da k’yar ta iya cewa “Ok thank you” Mai taxi ya mayar da ita unguwar da ya d’auko, “Ya zama dole na koma nigeria, na kawar da babyn nan a doron k’asa, shine babban katangar da zai hana ni shiga gidan SURAJ”, Idon ta sun rine sunyi jajir, zuciyarta ta riga ta bushe komai zata iya aikatawa. Tana shiga gida, wayarta ta lalubo ta shiga net tayi booking flight na komawa 9ja, sai nan da 8days ko zata samu, Wani haushi ya sake turnik’e ta, tayi booking ta cillar da waya gefe, Tana sak’e sak’en yadda zata shiga rayuwar Suraj ta zama matar sa. Suraj daga sashen Hajiya mota ya shiga ya nufi gidan gonar sa, Masu aikin dare suka shiga gaishe sa da mishi sannu da zuwa, Da sakin fuska yake amsa su, Office d’in sa ya nufa, Ya buk’aci ganin Rabi’u,Bukar da Sabeer, “Sannu da zuwa Ranka ya dad’e”, Suka fad’a a tare, “Yawwa”, Ya kai duban sa ga Sabeer “I hope kayi clearing mess da kayi”, Yace “Eh ranka ya dad’e”, “This should be the last time haka zai faru”, “In Shaa Allah za’a kiyaye”, Bukar ya nisa yace “Sir ina ganin kamar akwai spy a cikin mu”, Suraj yace “How is that possible?”, “Duba da yadda abubuwa ke tafiya this days”, “Ina so ka gano mun ko waye”, “Ok Ranka ya dad’e”, Da hannu ya musu alama su tafi, Suka fice. Shiru yayi yana nazarin maganar Bukar, idan kuwa aka gane ko waye sai ya gwammace mutuwar sa da hukuncin da zai fuskanta, Wani file ya jawo yana dubawa, Ya dad’e gidan gonar sa kafin ya koma gida. Washegari tun k’arfe bakwai, Aliya tazo gidan, ita ta d’aura ruwan wankan Fetta da jaririyar ta, Ta ma babyn wanka, Ta kai ma Fetta nata band’aki tayi, Ta dama mata kunun masu jego tasha, Suna zaune d’aki, baby na shimfid’e na bacci, Suraj yayi sallama ya shigo, Aliya ta amsa, Fetta kanta na sunkuye k’asa tace “Ina kwana?”, “Lafiya lau” Ya amsa, Ya zauna gefenta, ya d’auki baby, Aliya ta mik’e ta fita, Zuba mata ido yayi yana k’are mata kallo, Kwanakin nan wani kyau yaga ta k’ara mishi, ko dai haihuwa nasa mace ta k’ara kyau, Lallausan hannun sa taji saman nata, Bata janye ba haka bata ce masa komai ba, Ya shafa hannun cikin wani salo yace “Jibi mai lalle zata zo ta miki”, Nodding kai ta mishi gaba d’aya ya sakar mata da wata kasala, “Ba ki da baki ne”, Ya fad’a tare da matse hannun, Da sauri taja hannun tare da sakin k’aramar k’ara, Ya rik’e shi gam, “Me ke damun sa yau, mutum kamar mai juji”, Ta fad’a a ranta, Ya saki hannun ya maida duban sa ga yar’ sa yana jin k’aunar ta, “Allah ya miki albarka ya haskaka rayuwar ki”, Ya sumbaceta a goshi, Fetta dake gefe ta amsa da “Amin” Murya k’asan mak’oshi, Yasmeen tun daga bakin k’ofar falo take sallama, Direct d’akin ta nufa, Ganin Suraj a ciki tayi saurin juyawa, Hakanan yake mata kwarjini bata son had’uwar su. Su’ad da Feena suka fito a tare sun ci kwalliya, Suraj ya fito d’akin yaci karo dasu, tun dawowar sa sai yanzu ya saka su a ido, A tare suka duk’a suna gaishe sa, Wani banzan kallo ya watsa musu, “Dan uban ku sai yanzu zaku gaishe ni, me kuka taka na rashin zuwa ku ga Fatima da baby”, Cikin rawar murya suka ce “Wall….”, Tsawar da ya daka musu yasa suka yi shiru “Na lura da take taken ku, duk wacce ba zata daraja matata ba ko ta nuna k’iyayya ga jini na wallahi wallahi…..” Yayi shiru tare da cije lips na k’asa, Sun tsorata matuk’a, “Gidan uwar wa zaku je?”, Feena murya na rawa tace “Bikin k’awar mu”, “Daga yau kar na sake ganin k’afar kowacce a ciki waje idan ba makaranta zaku ba, shima driver zai rik’a kai ku”, Ya wuce, Kamar su tsunduma ihu saboda bak’in ciki, birthday na saurayin Feena zasu je, Haka suka koma d’aki cike da takaici da bak’in ciki, Feena na matsar k’walla tace “Gaba d’aya ya b’ata mun plan, ace birthday bangis banyi attending ba”, Ta buga k’afa hawaye ya shiga zirya kan kumatun ta, Su’ad tace “Ni babban bak’in cikina hana mu driving, wai driver zai rik’a kai mu school ba hanyar da zaka samu ka fita, outing da muke zuwa da Adnan ya datse”, Feena kuka ta cigaba da yi, Su’ad na mita. Aunty Jummai ta shigo gida a gajiye lik’is k’afar ta tayi duk’un duk’un, Bilkisu dake zaune tsakar gida tana shan iska tace “Sannu da zuwa Umma ina fatan an dace”, Tayi murmushi tace “Sosai an dace, sai dai mu jira sakamako”, Bilkisu tayi dariya tace “Kai ina sonki Ummana”, Atamfa ta fito da ita daga cikin leda, Tace “Kinga atamfar nan, ya tsaface ta, tana d’aurawa zata haukace, wannan kayan ana sawa jaririyar zata mutu”, Bilkisu ta buga wani tsalle tare da juyu tace “K’arshen ki Fetta ya kusa zuwa”, “Tashi ki shirya, mu tafi gidan, bari na watsa ruwa” Aunty Jummai da Bilkisu zaka rantse da Allah suna farin ciki da haihuwar Fetta( Mugu bashi da kama), Aunty Jummai hadda su goya baby, wanda hakan na cikin shirin ta, Fetta tayi murna da kayan barka da suka kawo mata, A gidan suka wuni, sun fito zasu wuce, suka hango Suraj ya fito daga sashen shi, Bilkisu tamkar zata had’iye shi tsabar kallo, Suka tsaya suna jiran ya k’araso, Yana ganin su ya d’auke kai ya shige mota, Bilkisu kamar zata suk’e tsabar haushi, Aunty jummai taja hannun ta tace “Kwantar da hankalin ki, ba da dad’eww ba zai zo hannu” Yan’uwa da abokan arzik’i nata zuwa barka, Kowa yazo sai ya kawo abun arzik’i, Aunty Yelwa da Kawo Sule ma sun zo, Hajiya ganin bata ga Karima ba, Tace “Ina Karima?, kwana biyu na daina ganin ta”, Mutanen dake wurin yasa Aunty Yelwa cewa “Tana gida, kwana biyu bata jin dad’i”, “Allah sarki, Allah ya bata lafiya yasa zakkar jiki ce”, “Amin”, “Zan zo In shaa Allahu na duba ta”, “Allah ya yarda”, “Amin” + Professional mai lalle tazo ta tsantsanrawa Fetta ja da bak’i, ba k’aramin kyau yayi ba, Suraj already ya biya ta, a instagram yayi coming across page d’in ta, Yayi mata magana yana so tama matar shi, ba k’aramin dad’i taji ba ganin Suraj ne. Kowa yaga lallen sai ya yaba, Yasmeen tace “Gaskiya yayi masifar kyau, kin ganki kamar wata sabuwar Amarya, Fetta yar’gatan Suraj da kanshi ya samo miki mai lalle”, Ta wurga mata harara, “Kin dace miji, muma Allah ya samu a dashen ki”, Wani banzan kallo ta watsa mata, Ta kamo hannun ta tace “Wallahi Fetta, Suraj yayi nisa a sonki, girman kai ne ya hana shi fitowa ya bayyana miki, a sannu zai furta, zaki ce na gaya miki”, Fetta ko kad’an bata yarda da zancen Yasmin ba, ta d’auki komai da yake mata saboda babyn sa ne da Hajiya. Tace “Uhmm yawwa ina ta so na tambaye ki, wai ya maganar case d’in su Alhaji”, Yasmeen ta nisa tace “Tuni aka rufe case d’in, yan sanda sunyi bincike sun kasa gane komai”, Fetta da damuwa d’auke a fuska tace “Allah yabi su Addani hakk’in su Allah ya tona asirin ko su waye”, Yasmeen ta amsa da “Amin, Fetta ina tsananin kewar iyayena wani lokacin na kan ji tamkar nabi su, meyasa wad’annan mutanen basu da imani a ran su, sun tarwatsa family a dare d’aya”, Ta k’arasa da hawaye, Fetta tace “Gara ke Yasmeen kina da dangi, bani da kowa, bansan kowa nawa ba, Addani shi kad’ai ne gatana, sun rabani dashi, sun kashe shi, taya zan gane dangina?, ban tab’a jin tsanar halitta ba kamar wanda suka kashe Addani, bazan tab’a gafarta musu ba”, Ta fashe da kuka mai tsoma zuciya, Yasmeen kasa lallashin ta tayi, sai ma taya ta da tayi. Suraj tun daga bakin k’ofa yake jiyo shesshek’ar kuka, Hankalin sa ne ya tashi, ya k’arasa ciki, Yasmeen na ganin sa ta tashi ta fita, Fetta da ta kifa kanta kan cinya tana kuka, Ya d’ago ya rungume tsam a jikin sa, Har cikin ransa yake jin kukan ta, A hankali ya furta “Me aka miki?, Me ya saki kuka?”, Kasa bashi amsa tayi sai kukan da ta cigaba, Lips d’inshi na k’asa ya ciza yace “Please kiyi shiru you are hurting me”, bai san sanda ya furta haka ba, Fetta mamakin furucin sa tayi, Kukan ta tsagaita, hawaye na ambaliya kan kumatun ta, Ya d’ago ta yasa hannu yana share mata hawaye, “Tell me what makes you cry?” Ya kafeta da ido, Kanta ta sunkuyar k’asa, cikin sanyin murya tace ” Ina tuna Mahaifina ne, i want to meet my family”, “Addu’a zaki rik’a mishi ba kuka ba”, Tayi nodding kai, “Ina family naki suke?”, “Nijar”, “A wane gari”, “Ban san komai a kan su ba, Mahaifina bai tab’a gaya mun ba”, Tausayin ta yaji for the first time ya kama shi, “In Shaa Allah watarana zaki had’u dasu”, Tayi nodding kai, “Ina baby?”, “Tana wurin Umma”, Sam bai lura da lallen ta ba, wanda shine dalilin sa na zuwa d’akin yaga mai lallen tayi yadda yace tayi. Ya mik’e har ya kai bakin k’ofa, “Ina neman alfarma d’aya a wurin ka”, Ya juyo yana kallon ta ba tare da yace komai ba, “Dan Allah a sawa baby Zainab sunan mahaifiyata”, Juyawa yayi ya fice ba tare yace komai ba, Har ga Allah sunan Hajiya yake so ya saka, Fetta ta sauke ajiyar zuciya tace “Allah yasa ya amince”, Babban burin ta yaranta sunci sunan mahaifiyarta da Mahaifin ta. “Wane irin aiki ne wannan da ya hana ka waiwayar gida” Kawo lamid’o ya fad’a cike da fad’a, Bello yace “Kayi hak’uri Abba In Shaa Allahu cikin satin nan zan shigo”, “Allah ya kaimu”, “Amin”, Kawo Lamid’o ya kashe wayar tare da yin k’wafa. Karima ta ajiye tray na abinci a gaban shi, ta zauna kusa dashi, “Cikin satin nan In Shaa Allah zanje Kano, Su Abba sun matsa a kan naje”, “Allah ya kaimu”, Ta fad’a murya a sanyaye, “Ya naga kamar baki ji dad’i ba”, Murmushin takaici tayi tace “Ka gode ma Allah iyayen ka na neman ka, suna son ganin ka, tunda nasa k’afa na bar gida ba wanda ya k’ara nema na”, Cike da tausayin ta ya jawo ta jikinsa, ya rungume, “Su Kawo na son ki, watarana zasu neme ki”, Tayi murmushin takaici a ranta tasan bara su tab’a nemanta ba, basu damu da ita ba, da halin da take ciki ba, bata tab’a ganin iyaye irin su ba. Shirye shiryen suna ake, kai kace bikin aure za’ayi, Ma’aikatan gidan nata faman aikin wasu na yanke-yanke su cabbaje, wasu na gyaran kaji, wasu na had’a zob’o da kunun aya, kowa da aikin da yake, Aliya na b’angaren masu aikin tana kula da ayyukan, wani kuma tasa hannu. Bayan sallar magrib, Suraj ya shigo d’akin Fetta janye da akwati, “Kayan fitar suna ne, ki gwada idan akwai wanda ya miki kad’an ko yawa, kiyi magana a mayar a gyara”, “Nagode Allah ya saka da alkhairi ya k’ara bud’i da dauk’aka”, Sosai yaji dad’in addu’o’in ta ya amsa da “Amin” Yasmeen ta kira ta tayata duba kayan, Akwatin shak’e take da kaya, Laces tsadaddu guda biyu d’inkin riga da skirt stone work, shadda getzner guda d’aya d’inkin ta ya masifar yi kyau, sai atamfa super d’aya holland d’aya, da wani tsadadden material, Duka kayan charass a jikin ta tamkar an gwada ta, “Wallahi Fetta kin more miji, ki kwanta kiyi ta bacci kawai”, Fetta murmushi tayi dan har ga Allah taji dad’i sosai bata d’auka zai mata haka ba, Kwanakin nan kulawar da yake nunawa a kanta, yasa ta fara tunanin maganar Yasmeen gaskiya ce yana sonta, “Wannan ai ko matar gwamna sai haka”, “Kai Yasmeen”, “Wallahi Allah, Allah dai ya barku tare ya kauda shaid’anin mutum da aljani”, Cikin zuci ta amsa da “Amin”, Sallamar Aunty Jummai ta katse musu hira, suka amsa a tare, Ta shigo tana washe baki, Fetta ta tsinci kanta da fad’uwar gaba, “Mai jego ana lafiya”, “Lafiya lau”, “Dama na lek’o naga kina lafiya, ina jika ta?”, “Gata nan”, Ta d’auke ta tana fad’in “Amma ba’a mata wankan dare ba”, “Eh”, “Bara na mata”, Ta shiga toilet ta had’o ruwan wanka, Tayi mata, ta shafe ta da cream. Tana washe baki tace “Ina kayan da na kawo mata, ina so na saka mata naji dad’i”, Fetta bata kawo komai a ranta ba, Ta bud’e akwati ta d’auko, ta mik’a mata, Aunty Jummai cike da farin ciki ta karb’a, Overall ce pink mai kyau, ta shiga k’ok’arin saka mata. Suraj yayi sallama ya shigo d’akin, Aunty Jummai ta washe baki kamar gonar auduga, “Suraj kai ne, ya gida?”, “Lafiya”, Ya amsa, Ya juya kallon sa ga Fetta, “Ki zab’o kaya kala uku masu kyau, da za’a saka mata, mai hoto yazo za’a mata pics kafin na suna”, Aunty Jummai na washe hak’ora tace “Ai ga d’aya a hannu na sai dai ta d’auko kala biyu”, Ba tare da ya kalleta ba yace “Bara suyi ba”, Yasa hannu ya karb’e ta, + Aunty Jummai wani abu taci ya tokare mata wuya bak’in ciki, haushi da takaici suka dabaibayeta lokaci d’aya, Ta kasa b’oye haushin ta wanda sai da ya bayyana a fuskar ta, Dress mai kyau ya saka mata, ya fita da ita, da sauran kala biyu a hannu. Fetta ta kalli Aunty Jummai taga yadda ta b’ata rai tace “Kiyi hak’uri Aunty gobe idan ya dawo da ita sai a saka mata”, Aunty Jummai tayi fuskar tausayi ta marairaice murya tace “Hak’uri ai dole ne, tunda ya raina nawa kayan”, “A’ah ba haka bane Aunty, hotuna za’a mata shiyasa”, Tace “Uhmm”, Tana k’ara nuna rashin jin dad’in ta, wanda yasa Fetta ganin duk ba’a kyauta mata ba, Yasmeen na gefe na danna waya bata ce komai ba. Suraj ana gama hotuna, ya wuce da ita sashen shi, Ya kwanta tare da d’aura ta saman k’irjin shi, a haka bacci ya d’auke su. Aunty Jummai tayi ta jira, ya maidota ta saka mata kayan, ganin har goma da rabi, yasa suka wuce ita da Bilkisu, wacce tun zuwan su tana wurin Hajiya tana fadanci, hadda gyaran mata d’aki da wanken toilet. 11:15pm Kukan ta ya tashe sa, yayi saurin mik’eww yana jijjigata, Ya nufi sashen Hajiya, Fetta wacce fitowar ta daga wankan kenan tana d’aure da towel, ya shigo d’akin, Ido ya zuba yana kallon ta, Skin d’inta na glowing, Yana kallon cinyoyin ta, sai da ta tsargu da irin kallon da yake mata, Yanayin da ya fara jin sa yasa shi kawar da kai, Ya mik’a mata baby, Ta karb’eta, ba tare da sun cewa juna komai ba, Ya juya ya fita cike da tunanin ta a ransa. Washegari tun da suka tashi sallar asuba babu wanda ya koma bacci, aka shiga hidima, Aliya ma tana idar da sallar asuba tazo gidan, Mallam ya bata jarka ta zamzam da yayi addu’o’i yace ta kaiwa Fetta, A d’aki ta sami Fetta tana breastfeeding baby, tana jin shigowar Aliya, tayi saurin zare ta, tana jan riga, Aliya ta kalleta ta girgiza kai tana mamakin kunya irin nata, “Ina kwana Umma?”, “Lafiya lau, ya kwanan ku?”, “Lafiya lau”, “Ga zamzam Mallam yace ki rik’a sha kina shafe ma jikin ki ke da yar’ki na kariya ne daga dukkan sharri”, “Toh nagode Allah ya saka da alkhairi”, “Amin”, “Bari na tashi naje wurin ayyuka”, Ta fad’a tana mik’ewa, Fetta tayi bayanta da kallo tana jin k’aunar su, banda su da bata san a wane hali take yanzu ba, Sun zame mata tamkar iyayen ta. Feena rik’e da waya tana kiran wayar bangis a karo na ba adadi, yayi ringing har ya tsinke bara a d’auka ba, Ta cillar da wayar cike da takaici, Idonta ya ciko da k’walla ta kalli Su’ad dake kwance tana chatting, Tace “Bangis fushi yake dani, har yanzu baya d’aukar waya ta”, Su’ad ta nisa tace “Am facing the same problem, Adnan yana so mu had’u na gaya mishi Ya Suraj ya hana, yayi fushi, tun d’azu ina mishi magana babu reply”, “Hmm naku mai sauk’i ne yazo gida mana”, “Wai yana jin kunyar su Hajiya” Feena tayi shiru tana nazari can tace “Yes! yau suna zamu iya fakar idon mutane mu fita mu dawo ba’a sani ba”, Su’ad ta bata hannu suka tab’a tace “Exactly”, “Tashi muje muga bararojin can kafin ya waiwayo mu”, Suka mik’e, Su’ad ta jawo ledar kayan jarirai, Hajiya ta basu tace su ba Fetta a matsayin su suka siya. Mai make up ke yi ma Fetta kwalliya, Yasmeen na zaune gefe tana d’aukan pics, “Wannan ai sai ki kwashe kyan kwalliyar, ki bari a gama mana”, Cewar Fetta, Yasmeen tayi dariya tace “kwantar da hankalin ki, kyau ne zaki yi shi, nasan fargabar ki kar Suraj yaga baki yi ba”, Harara ta watsa mata, Mai make up tayi dariya. Su’ad da Feena suka shigo ba ko sallama, Yasmeen ta d’auke kai tamkar bata gamsu ba, “Sannun ku”, Suka fad’a, Fetta da sakin fuska tace “Yawwa”, Jaririyar dake shimfid’e kan gado, Feena ta d’auka kamar su ta gani da Suraj, Tace “Wannan baby mu ta biyo anci sa’a”, Su’ad ta kalleta tace “Aiko sak Ya Suraj”, Fetta murmushi tayi, Yasmeen tace “Da ta biyo Fetta kuwa da tafi haka kyau, dan muma ba daga baya ba”, Dariya suka tuntsire da ita, Su’ad ta mik’e tace “Bari na tashi kafin dariya ta kashe ni”, Ta ajiye ledar dake hannun ta tace “Gashi a sawa baby”, Feena ta mik’e tabi bayan ta, Yasmeen taso mayar musu martani, Fetta ce ta hana ta. Sa biyu da rago biyu aka yanka, Yarinya taci suna Zainab, Marok’a nata faman wak’e wak’e kai kace bikin aure ake, Suraj yasha shadda wagambari d’inkin tazarce yayi kyau sosai, kamar wani sabon ango. Fetta taci ado cikin shadda, tayi kyau sosai ba kace ta haihu ba, Ta fito tamkar Amarya, Duk wanda ya ganta sai yace tayi kyau, Aliya tace “Mashaa Allahu Fetta kin ganki kuwa”, Tayi dariya, “Kin kyauta da aka saka sunan mahaifiyar ki”, Baki ta washe cike da farin cikin jin yasa sunan Mahaifiyar ta, Wayar ta dake hannun ta, ta mishi text, ta tura, Ta nufi d’akin Hajiya, ta aiko tana neman ta. Yana tsaye harabar gidan, yana ma masu decoration bayanin yadda zasu yi, k’arfe hud’u za’ayi walima, Wayar sa tayi k’ara, ganin sunan Fetta yayi appearing ya duba, “NAGODE ALLAH Y SAKA DA ALKHARI DA KA SAKA SUNAN MAHAIFIYATA, YADDA KA FARANTA MUN, ALLAH YA FARANTA MAKA YA HASKAKA RAYUWAR KA” Murmushi yayi da jin dad’in addu’oin ta, ya mata reply da “AMEEN” Ya kashe wayar ya cigaba da yi musu bayani. Hajiya kad’ai ta tarar a d’aki, ta durk’usa ta gaishe ta, Ta amsa da sakin fuska, “Walimar da za’ayi anjima nace ko akwai k’awayen ki da zasu zo?”, “Eh wanda mukayi secondary tare ne, sai masu siyan laces”, “Toh dama ina so naji ne dan a ware musu wurin zaman su, da kuma kaya da za’a raba”, Fetta tace “Toh”, “Zaki iya tafiya”, Ta fice zuwa d’akin ta, Safiya ce dan haka mutane da yawa basu hallara ba, yan uwa ne na kusa ke ta hada hada, Aunty Jummai, Aunty Yelwa da Gwaggo matar kawu lamid’o duka suka gidan kowacce ta k’ure a daka. Fetta shigar ta d’aki kenan, Suraj ya rufa mata baya, Jin mutum a bayan ta, ta juyo a tsorace, Yadda ta tsorata yaso bashi dariya, Ya gumtse, yana bin ta da kallo, tsananin kyan da yaga tayi yasa ya kasa d’auke idon shi daga kallon ta, “You look beautiful”, First time in her life da taji ya yaba ta, Kasa yarda tayi da abunda kunnen ta suka jiye mata, Ido ta zuba mishi tana kallo cike da mamaki, Gira ya d’aga mata alamar ya dai, tayi saurin sunkuyar da kai cike da kunya, Ji tayi ya jawo ta ya manna da jikin sa, kafin tayi wani motsi ya had’e bakin su wuri d’aya, ya shiga bata hot kisses, K’afafun ta taji bara su d’auke ta gaba d’aya ya saukar mata da kasala, Tayi baya ta fad’a kan gado, Ya fad’a kanta ya shiga romancing d’in ta, kasa hana shi tayi, sai ma martani da ta shiga mayar masa, Yana k’ok’arin saka hannu a pant d’in ta, tayi saurin ture shi, Idon sa lumshe yana maida numfashi, Kunya taji ya kamata, tayi saurin shigewa toilet, Kusan minti biyar yana haka, yana jin sa a wani yanayi, wata masifaffan desire na damun sa, yaja tsaki tuna bata da tsarki, Haka ya mik’e jiki sanyaye ya bar d’akin, Fetta wanka tayi, gaba d’aya ya jagalgalata, jan baki dake lips d’in ta ya shanye tas, make up na fuskar ta ya b’aci, ta wanke tass, Ta fito, Zaune da shigowar ta kenan tace “Me zan ganj haka?”, “Wanka nayi, na fara staining”, “Shine kika b’ata make up d’in”, “Ba da yamma za’a k’ara wani ba”, “Ina fatan Suraj ya ganki”, “Ban sani ba” Dariya Yasmeen tayi tace “Ah ya gani, tunda ya gani ai shikenan”, Bata tanka ta ba, ta d’auko cream tana shafawa, Zuciyarta cunkushe da tunanin Suraj. Anyi gagarumin suna wanda zaka rantse bikin aure ne, shima na masu naura, Fetta tasha kyau da yar’ ta Zainab wacce za’a rik’a kira da Mimi, Hajiya tayi shiga ta alfarma, Aliya ma tayi kyau sosai, Mai wa’azi tazo ta sharara wa’azi kafin aka saki Dj, kowa ya shiga rawa, Su Feena hotuna kad’ai suka yi suka faki idon mutane suka fice, Anci an k’oshi, an raba soverniers, kowa ya yaba walimar, ana ta sawa jaririya albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page