RAI BIYU CHAPTER 18

RAI BIYU
CHAPTER 18
SIX MONTHS LATER…

Rayuwar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba ita na ke a yanzu, ni kaina ina canjin da na yi a jikina da kuma ruhina, na zama RAI BIYU a gurin mutum biyu Noor da Jibril, na yi fadi tashin rayuwa kamin na kawo yanzu, na yaki zuciyata kuma na yi nasara akan kudirina.

Komai ya canja a yanzu wa zai yarda da ni idan na ce ina rayuwa da Jibril a matsayin kanwa kuma abokiya, ni kaina na kan yi dariyar kaina kamin mamaki ya biyo baya, na zauna a matakin da ban taba tsammanin zan zauna ba, na shiga na fita na gyara rayuwar da na fi tsana a duniya abunda ko a mafarki ban taba tsammanin afkuwarsa ba, a yanzu Jibril ba shi wani madubi ko kuma tsarin rayuwa sai nawa, dukan wani abu daya shafi kamfaninsa da rayuwarsa ko kuma ta Noor da ni yake shawara kamin ya aiwatar da shi, hakan yasa kara tsanar da Siraj ya ke min har bayan son ganin sai dole, gashi case din da muke a kotu ashe yayarsa ce da ke aure nan domin a asalinsu su yan kaduna ne, shi kansa be taba sani ba sai da muka yi zaman kotu na hudu aka je da shi muka hadu, akwai nasara sosai a shariyar ta mu kasancewar Dpo ya tsaya kai da fata wajen ganin an yi mana adalci kuma an bi maka hakkin mahaifinmu, gaskiya na yaba da irin kokarin da dpo yake mana hakan ya kara tabbatar min mana cewar ba duka yan sanda marasa na na gari ba, domin a cikin bata garin ana samun na gari a cikin na garin kuma ake samun bata gari, Inna ma ta yaba da kokarin shi duk da ita tafi maida hankalin akan cewar wai so na ke, ni kan ina ganin kamar dai yana yi dan Allah kawai domin ni ai yasan an samin rana, duk da wani lokacin haka kawai xai kirani a waya ya ce fira yake son muyi ko ya ce yana son jin muryata, sai dai duk wannan firar da muke a waya Bilal be sani ba da sai ya kusa hadiye zuciya saboda mugun kishina da yake ko da yake na lura kamar ya fi kishina akan abunda ya shafi bangaren Jibril, kamar yadda shi ma Jibril yake nuna min kinshinsa na banza a duk lokacin da na ambaci Bilal a gabansa ko kuma na yi waya da shi, ni kuma na kanyi hakan ne saboda ya daina wahalar da kansa yana kusa kansa gareni domin na dade da zama matar wani.

Na yi nasarar shiga na kanannade duk wata hanya da zata sa Siraj ya samu wani abun a karkashin Jibril, idan zuwa wani aikin ne ko taro ni kaina na ke cilasta Jibril zuwa, kuma na sa ya karbe komai nasa da yake hannun Siraj duk da be so haka ba, har ta kai ta kawo idan ban ga dama ba Siraj ba zai iya ganin Jibril ba indai a office ne, da fari Jibril da shi kansa Siraj din sun zarge ni da shiga tsakaninsu na neman rabasu, sai dai nasarorin da Jibril ya yi a cikin watan nan shida ba tare da Siraj ba yasa na fahimci shi kadai ma zai iya ba sai tare da wani, ko da wasa ban taba fadawa Jibril cewar Siraj yana masa Zagon kasa ba, sai dai na kan yi kokarin nuna masa haka ta hanyar wasu abubuwan da Siraj yake yi, tare da Rabi muke komai ita take sanar da ni duk wani kudiri na Siraj ni kuma sai na yi kokarin Jibril aikatawa, Jibril bw taba yarda da ni sosai ba kamar lokacin da na daukeshi muka je bypass da kansa ya ga kamfanin da Siraj yake ginawa wanda be taba fada masa ba, hakan yasa shi ma na ya fara ja baya da shi har suka soma samun sabani saboda rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu Jibril yana ganin be kamata ace Siraj ya boye masa abu mai muhimmanci kamar haka ba, shi kuma Siraj yana ganin Jibril ya dauki amana ya bani har ina shiga tsakaninsu.

Jibril ya sake shiga rayuwata a karo na biyu, na sake jiki da shi irin sakewar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba, ya canjawa Noor da Jamila makaranta daga makarantar gwanati zuwa Imam international school, da school bus ake kawo su kuma a dauke su da safe, shakuwar data shiga tsakanin Noor da Jibril a yanzu har mamaki take bani lallai na yarda da aka ce yara sun fi sabawa da iyayensu maza. Sakina kuma ya maida Khalifa International School wace ke can kusa da Polytechnic bypass, dukan wani abu da za’a ci a gidan daga aljihun Jibril yake zuwa, idan na yi magana yace dansa yake yi ma, ni kuma na kan bashi damar hakan ne saboda nima na samu damar shiga cikin tasa rayuwar, ni ce na yi ruwa na yi tsaki a rayuwar mutumen da na fi tsana a duniya, bana da matsala a yanzu sai ta mutum biyu Bilal da kuma Siraj, na rasa yadda zan yi na fito kai tsaye na nunawa Jibril irin kudirin da Siraj yake da shi akansa, ina son nayi masa yadda zai fahimta ne kuma ya kamashi dumudumu amman na rasa yadda zan fahimtar da shi.

STORY CONTINUES BELOW

Sai Bilal da ya kasa fahimta ya kasai daina zargina duk kuwa da kasancesar an saka ranar aurenmu a yanzu, zuciyarsa ba raya masa kamar ina son Jibril ne, ga kuma ta bangaren Familynsa har yanzu mahaifiyarsa fushi take dashi ta kasa sakewa da ni saboda bata son auren, gashi tana ganin kamar saboda ni aka kore shi aiki daman mahaifinsa ne ya tsaya kai da fata akan maganar har aka saka ranar auren.
Ko ranar da aka kawo tufafin sakawata sai sa yan’uwansa mata suka yi ta Maganganun kamar na habaici, ni dai ko kadan hakan be dame ni domin iya abunda na sani Bilal yana so na ni ma kuma ina son shi so kiyayyar yan’uwansa ba zata dame ni ba, domin ina jin a jikina zan iya canja musu rayuwa su soni ta hanyar kyautata musu da kuma yi musu biyayya.
Ban tsammaci Bilal zai zuba min lefe kamar haka ba, domin kala talatin da biyu ya yi min kamar wata budurwa babu abunda be saka ba a cikin lefen, da na masa magana sai ya ce wai daman ya dade da siye ya aje ba a yanzu ya siya ba, baya aikin komai a yanzu sai tsaron wani shagon computers suna biyanshi kullum, amman ya yi applying a cbn da kuma aikin kaki har guda biyu, sai dai aikin naija sai a hankali za ka yi applying dauka sai na manta ma, baya son komawa kamfanin Jibril aiki kamar yadda nima bana so saboda kar Jibril ya dauka cewar Bilal da kamfaninsa kawai ya dogara. Ban taba sanin cewar Bilal yana da zafin kishi ba sai a yanzu, domin ko kallona ya yi sunan Jibril yake kira wai ai daman yasan ina son shi ni kuma wani lokacin har dariya yake bani domin idan ya bata rai abun baya masa kyau.

Yau ta kama Friday ina dawowa aiki na zauna na shiryawa Bilal Snack saboda yana ciki favorite dinsa musamman ma idan ni nasa yana ci sosai, sai da magariba na gama sai na yi wanka na shirya cikin wata jar kamfala, ta karbeni sosai saboda jan abu yana fitar da farin mutum, sai na bi jikina na fashe da turare sai na dauki blue mayafi na saka, na dauki wayata na kirashi bugu biyu ya daga.

“Hubby ina nemanka yanzu”

“Me za ki ban?”

“Sai zan baka wani abu kawai na ke da ikon ganinka?”

Na fada kamar zan fasa masa kuka.

“Gani nan zuwa”

Yana fada ya kashe wayar, haka yake mina yanzu zuwa fira ma sai yaga dama saboda kawai yana fushi da ni wai ala dole ni soyayya na ke da Jibril, ko kadan bana ganin laifinsa domin na san ko a littafi ba za a samu namijin da zai yarda ya kyale matar da zai aura tayi aiki karkashin wani ba a
Wai dan kawai da taimaki rayuwar danta.
Ta bangaren yan uwansa ma nasan ba a rasa masu masa magana domin abokansa da yake zuwa da su wani lokacin sukan zolayeni da Maganganun marar dadi ko kuma na bugun ciki domin kawai su ji abunda zan ce, amman ya toshe kunnuwansa domin kawai ya bani damar cin ma kudirina har shi yake kokarin kare ni wani lokacin.

Bayan kamar mintuna talatin sai gashi ya aiko min sako wai na fito yana kofar gida, ni kuma na yi murmushi na dauki snack din na kira Noor ya rika min lemun kwakwa hadin gida da na yi masa muka fito tare fito Noor na aje jug din yaje da gudu suka rumgume juna.

“Uncle Bilal i miss you”

“I miss you too Noor”

“Wannan Saturday data wuce ka ce zaka zo kaje da ni yawo kuma baka zo ba”

“Mantawa na yi but dis weekend zamu je”

“Gobe ko? Gobe weekend fa”

Bilal ya dafe kansa.

“Oh na manta tau gobe za muje”

“Thank you”

Ya fada har da tsalle, sai kuma ya tsaya yana kallon bakina da shi yadda muke gaisawa, ganin hakan yasa na umarce shi da ya wuce cikin gida.

“Ga snack din da na maka”

Sai ya kawarda kai baya ma son kallon snack din.

“Bana jin cin komai a yau”

STORY CONTINUES BELOW

Hakan yasa ni jin babu dadi amman sai na daure na dauki daya na mika masa a hannu.

“Dan Allah ka ci da kaina na hada maka”

“No na koshi yanzu na gama cin indomie”

“To ga lemun kwakwa nan da kaina shi ma na hada”

“Ai ko baki fahimtar hausa ne?”

“Na fahimta dan Allah Bilal ka daina fushi da ni, na san ka yi hakuri ni kaina ba dan raina yana so nake aikin nan ba, kuma na yanke shawarar aje aikin a wannan week”

Ya kalleni

“Saboda mai?”

“Saboda ya kamata na aje, na yi iya kokarin da zan yi na taimakon Jibril, sai dai na bishi da addu’a kawai, kuma kaga aurenmu sauran wata uku a wannan lokacin ne ya kamata na aje aikin ai”

Murmushi ya yi ya soma wasa da yatsun hannunsa.

“Har yanzu kina son Jibril ko Nawwara?”

Kallonshi na yi jin tambayar banbaragwai da kuma yanayin yadda ya kira sunana kai tsaye ba kamar yadda ya saba kira ba.

“Wannan kuma wace irin tambaya ce Bilal?”

“Tambaya ce dai kamar ko wace tambaya amsarki kawai na ke so”

“Idan har baka so ba aikin nan Bilal ba zan yi ba”

“Na isa na hanaki? Ban riga na aureki ba Nawwara balle na gindaya miki wasu sharadodi, so ban isa na hanani aiki tare da Jibril ba, idan ma na yi kokarin hanaki sai Inna da ke sun ga laifina”

“Babu wanda zai ga kaifinka saboda kana da cikakken iko a kaina, be kamata ka zargeni ba Bilal”

“Mi zan yi bayan zarginki Nawwara? Jibril first love dinki kuma karya kike yanzu ki ce min babu son shi a cikin zuciyarki, na san yana son ki sosai kuma zai yi komai dan ya ga ya same ki, ya fini kudi na sani kuma ya kyautata musu da abunda ni ba zan iya ba”

Idanuwa sun cika da kwalla kalamansa sun ratsa zuciyata cikin rashin jindadi na hadeye yawun da ke bakina na ce

“Jibril ya fika kudi amman be fika karbuwa a zuciyata ba, Jibril ya wukanta ne Bilal irin wulakancin da wani da namiji be taba ma mace ba, kuma a yanzu kake zargin zan iya aurensa? Bayan an saka mana rana da kai mika dauki iyayena ne zasu canja magana ta da kai saboda kawai Jibril ya fika kudi?”

“Idan har baki son shi dan me za ki taimaki rayuwarsa? Har ku kuma kuna zama kamar wasu masoya, dan Allah Nawwara baki ji kunyar kanki ba?”

“Da ka nuna min baka so tun farko da ban yi ba, dukan abunda na ke ma Jibril ko kuma na yi masa na yi ne saboda Noor idan ya gyaru Noor zai amfana idan kuma ya lalace Noor ne zai tagaiyara miyasa ka kasa fahimtata ne?”

“Saboda Noor ko? Komai ma ai saboda Noor ne Nawwara i understand”

Yana fadar hakan ya saka hannayensa aljihu ya wucewarsa ya barni nan tsaye ina faman hawaye.

JIBRIL POV.

Daker yake numfashi saboda nauyin da zuciyarsa ta yi masa, daman yanzu abun ya zame masa kamar jiki idan yau be yi ba gobe sai ya yi, sai dai duk wannan abun be taba yarda ya yi gaban Nawwara ba, idan har suna tare abun ya taso masa sai ya kulle office dinsa ko kuma ya bar kamfanin ya dawo gida.
Daker ya unkura ya tashi ya nufi bathroom yana shiga sai aman jini yau kan be yi shi da yawa ba kamar yadda ya saba, sai da ya wanke bakinsa sannan ya bude cabinet ya dauko wasu kwayoyi ya hade tare da ruwa sai ya juyo ya fito daga bathroom ya zauna saman kujera ya lumshe ido yana sauke numfashi a hankali.

Nawwara ce kadai macen da yake gani idan ya rumtse idonsa, duk da a yanzu ya sadakar ba zata taba zama tashi ba, yana ji a jikinsa kamar ba zata sake rabarsa, but he’s happy da ta yi aiki da shi ta maida da shi cikakken namiji, dukan wani canji daya samu a rayuwarsa yasan ta dalilin Nawwara ne, domin be yi zaton zai iya daina shan cocaine ba amman gashi yanzu komai ya zama tarihi, and now he can read Quran duj da be yi nisa sosai a ciki ba amman ya san bakin domin kullum Malaminsa yana zuwa yana koya masa har ma da wasu littafan na daban da kuma bayani akan sallah da wasu abubuwan na addini, shi kansa a yanzu yana jin dadin rayuwarsa Saboda yana jin ya kara kusanci da Ubangijinsa hakan yasa ba janye dokan hana saka hijabi a kamfaninsa domin a yanzu ya fahimce babu komai a cikin addininsa sai rahama da jinka ga gata da addinin musuluncin yake ma ko wane musulmi, bashi da wata matsala ta rayuwa a yanzu sai tunanin Nawwara da ya zame masa kamar abinci, idan suna office har baya son su rabu saboda kewarta da yake komai ya zo masa kamar a mafarki ace Nawwara ce ta sake jiki da shi suna aiki haka, but a duk lokacin da ya tuna zancen aurenta da Bilal sai yaji kamar ya hade zuciya ya mutu, wannan tunanin ya yi tasiri a zuciyarsa da har ya zurfafa masa ciwon dake damunsa, a iya yanzu ya sadakar kuma ya yarda rayuwarsa ba mai tsawo ba ce a duniya, saboda matsala da cocaine ya haifar masa da kuma yawan tunanin da yake a baya ga kuma wanda yake a yanzu, wannan yasa shi yin saku saku da rayuwa. Wani lokacin yana kan kamar ya samu Nawwara ya fada mata hakan sai dai yasan ba zata fahimta ba kuma zata zargeshi da cewar saboda yana son bata alakarsu da Bilal ne, wannan yasa ya danne komai ya barwa zuciyarsa sai kuma mahaifinsa da Siraj da suka san da matsalar.

STORY CONTINUES BELOW

Kalaman da ta yi masa yau a office na cewar zata aje aikinta a wannan satin mai zuwa ne suka haddasa masa ciwon kai har ya abun ya sauko a zuciyarsa, kullum sai ya kirga kwanakin da suka rage na aurenta da Bilal kamar da shi za a daura auren. Ji yayi yana da bukatar ganin dansa domin a yanzu shine kawai farincikisa, a duk lokacin da Noor yake kusa da shi yana jin dadi sai ya dinga jin kamar Nawwara ce a kusa da shi.

Unkurawa ya yi ya tashi cikin karfin hali ya koma bathroom ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki wayarsa da car keys ya fice daga dakin.

Har ya fito harabar gidan be daina jin zafin da zuciyarsa take masa ba. Haka ya shiga motar ya dauki hanyar da zata kaishi gidansu Nawwara. A kofar gidan ya yi parking sannan ya dauki wayarsa ya kira Nawwara, bata dauka ba har ta katse sai ya sake kira haka ya jera mata kira hudu ba tayi picking sai ya fita daga motar ya je kofar gidan ya buga, sai gata ta fito hawaye shabe shabe a fuskarta.

“Dan Allah dan girman Allah karka sake zuwa kofar gidan nan Jibril da sunan ganina, yanzu yanzu Bilal ya bar gurin nan da ya tararda kai ai ba zai ji dadi ba, saboda kai yau na fada min magana marar dadi, kuma na fada maka cewar komai ya kare a yanzu, tun da zaka iya komai da kanka shiyasa nima zan aje aikin saboda na samu damar kula da Bilal da kuma kaina”

“Ina son ganin Noor ne shiyasa na zo”

“Idan kana son ganinsa ka sanar da ni zan sa a kawo maka shi har gidanka, amman a i zuwa yanzu ka daina zuwa nan sai na yi aure”

“Okay Nawwara ba zan sake ba, and ki bawa Bilal hakuri akan abubuwan da suka faru, na san mun shiga hakkinsa but yanzu komai ya wuce”

Ba tare da ta sake cewa komai ba ta juya ta koma ciki, shi kuma ya cikama bakinsa iska ya busar sai ga Noor ya zo da gudu, sai Jibril ya risina kasa ya shafa fuskar dansa sai kuma ya rumgume shi ya lumshe ido.

‘Ni na jawa kaina komai saboda haka dole na yarda da rashinki’

Ya fada a ransa, a fili kuma sai ya dago fuskar dansa ya kalleshi ya ce.

“Dukan abunda Nawwara ta yi da wanda na yi mun yi ne saboda kai Noor, ina son ko da bana raye ka kasance mai alfahari da ni a matsayin ubanka”

“Ni ban gane abunda kake cewa ba”

“Zaka gane wata rana, ina son ka zama mai biyayya ga Mahaifiyarka ita ce zata rayu da kai har ka girma, na yi farincikin da na rayu da kai Noor ina son ka sosai” 1

Ya rumgume shi idanuwansa cike da kwalla, sosai da sosai yake shakar kamshin jikin Noor, domin haka na masa dadi yana jin kusan da dansa sosai.

“Noor zamu je yau ka yi weekend gidana ko?”

“Ee amman Uncle Bilal ya ce zai je da ni yawo gobe Saturday”

“Yaushe ya zo?”

“Dazu”

“Okay, idan kun dawo sai na aiko a dauko min kai ka ji”

“Okay Daddy Momy har da cake ta yi ma Uncle Bilal”

Wani irin daga kai ya yi ya sauke numfashi saboda yadda maganar ta sokeshi.

“Okay je cikin gida ni zanje gida kar dare ya yi”

Ya sumbanci goshinsa.

“Goodnight”

“Goodnight”

Noor ya fada yana daga masa hannu sannan ya shige cikin gida, shi kuma ga mike tsaye ya jingina da motarsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Ya samu thirty minutes a gurin sannan ya bude motaraa ya shiga cikin rashin dadin rai. 1

*** *** ***
NAWWARA POV.

Na farka yau cikin rashin dadi rai saboda abunda ya faru jiya, sam ban jidadin yadda Bilal ya kasa fahimta ta ba, duk da nasan kowa waye dole ya zargi wani abu a tsakaninmu, amman komai ya kare a yanzu ba zan sake bari wata alaka ta shiga tsakanina da Jibril ba da har zata sa Bilal ya zargeni.

Na dade a kwance kasancewar yau weekend har su Noor da Jamila suka dawo daga islamiyar safe ban tashi ba ba dan kuma ina bachi ba sai dan ina jin jikina da rayuwata babu dadi, ina son na labartawa Inna sai wata zuciyar ta hanani saboda na san ba komai ya kamata ace iyaye sun sani ba musamman a abunda ya shafi fada a tsakanin ma’aurata ko kuma masoya, har sai idan ya kai ya akwo mun kasa shawo kan abun. Wayata na dauka na aika masa da sakon barka da safiya amman be maido min da amsa ba, hakan yasa na kirashi sai be yi picking ba. 1

Tashi na yi na fita tsakar gida na gyara ko ina sannan na shiga na yi wanka na shirya cikin bakar abaya, Inna ma ta kula da yanayin da na ke cikin na rashin dadin rai, sai dai bata min magana ba, wata kila ta fahimci akwai abunda ya shiga tsakaninmu da Bilal jiya da dare saboda na dawo ina kuka duk da kasancewar ta tambaye dalilin kuka na ki fada mata.

Misalin sha daya da rabi Bilal ya kira ni ina picking ya ce

“Ki shirya ma Noor gani nan zuwa”

“Tau, har yanzu fushi kake da ni ko?”

Sai kawai ya kashe wayar, ni kuma na ja dogon numfashi na sauke na tashi na fita. Ko da sha biyu ta yi da kwata Bilal na kofar gidanmu yana jiran Noor, ban san miyasa ba na samu kaina da rashin jindadin fitar shi tare da Noor duk da sun saba fita amman yau ina jin daban gashi gabana sai faduwa yake, wata kila saboda bana cikin dadin rai ne ko kuma wani abun ne daban oho. Da kaina na riko hannunsa na kaiwo shi kofar gida, saiga wayar da ke hannuna ta yi ringing Jibril ya kira, daman yakan kira da safe ya yi waya da dansa haka ma da dare idan zai kwanta sai dai yau yayi ranar kira domin har sha biyu ta gota ko da yake yasan yau weekend ne Noor baya suwa school. A nan na mika masa wayar ya gaisa da Jibril sannan Bilal ya rika hannunsa ba tare da yace da ni komai ba suka tafi Noor nata dariya yana dago min hannu.

Cikin gida na dawo na dora girkin rana, sannan na dauko tufafin Inna da suka yi datti muka soma wankewa ni da Sakina muna fira sama sama, sai dai faduwar gabana na ta karuwa, ina jin kamar na yi kuka kuma ba dan a min wani abun ba.
Da la’asar Jibril ya aiko da dare bansa a daukar masa Noor sai na fadawa direban cewar basu dawo ba, daman idan suka fita wani lokacin har isha’i suna kai wa basu dawo ba, direban na wuce da kamar minti biyar sai ga Bilal ya kirani a waya hankalinsa a tashe.

“Nawwara Noor ya dawo?”

“Aa kun dawo ne?”

“Bayan fitar mu be dawo ba?”

“Aa be dawo ba, lafi… “

Kamin na tambaya ya kashe wayar, ni kuma jikina ya yi sanyi na soma ambaton Allah a hankali

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”Jina yi kamar bana da karfi a jikina na kasa shanyar da na ke, sai na zauna a gurin gabana nata faduwa.

“Nawwara”

Inna ta kirani saboda ta lura da yanayina, sai na kasa amsa mata saboda kukan da ya cika min zuciya nasan ina bude bakina zai fito.

“Lafiya miya faru? Dawa kike waya?”

“Bilal ne, tambayata yake wai Noor ya dawo”

Na fada ina ta kokarin danne kukana.

“Kamar ya? Ba tare suka fita ba”

“Tare suka fita”

“Amman shine zai kira ya tambaya ya dawo bayan kuma ya san tare suka je? Wane irin rainin wayo ne wannan?”

Cewar Sakina tana matse zanen Inna.

“Wata kila wani abun ne ya faru, ina ji jikina ba dadi”

“Tun jiya na lura da ke sai dai nasan matsalar bata wuce tsakaninki da Bilal ba shiyasa ban yi magana ba, sabodana bana son ina yawan shiga fadanku, amman babu abunda zai faru da Noor Inshallah”

Ajiyar zuciya na sauke ya share guntun hawayen da ya zubo min na tashi na koma bakin kofar dakinmu na zauna, Sakina ta cigaba da wanke kayan. Haka muka zauna shiru har aka kira magariba Bilal be sake kirana ba gabana kuma be daina faduwa ba. Bayan na sallah isha’i na dauki waya na zimmar na kira Bilal sai kuma nake ganin rashin dacewar hakan, saboda ya saba fita da Noor su kai har dare basu dawo ba, dan me yanzu zan soma kiransa ai sai ya zargeni yace ko dan munyi fada ne, haka na maida wayar muhallinta na aje, kamar Inna ta san abunda ke raina sai kawai na ji ta ce 1

“Karki ji kunyar kiranshi Nawwara, ki kirashi mana ko muma hankalinmu zai kwanta”

Ba musu na daga wayar na kira number Bilal amman har ta gama ringing be dauka ba, haka na jera masa kira hudu be daga ba, daga baya kuma sai naji wayar a kashe, hakan ya kara fadar min da gaba, ina kokarin fadawa Inna cewar wayarsa a kashe take sai ga sakon Jibril ya shigo.

_Nawwara Noor ya dawo? Ina son gani dana zan aiko da mota yanzu_

Ni kuma na yi saurin mayar masa da sakon cewa basu dawo ba, sai ya sake aiko min da wani

_Dan Allah karki shiga tsakanina da dana Nawwara na roke ki, kiyi min duk abunda zaki min amman karki hana min Noor_

_Idan sun dawo zan fada maka_

_Gani nan zuwa na dauki dana_

_Aa karka zo_

Bw sake cemin komai ba, nasan be yarda da ni bane yana ganin kamar ina kokarin hana masa Noor ne.

“Inna na ta kira na kira be daga ba daga baya kuma sai aka kashe wayar”

“Allah dai yasa lafiya”

Cewar Inna ni kuma na amsa da Amin, kamin mu hada baki gurin amsawa Jidda da ta shigo a yanzu kamar marar lafiya, ina kallonta na san ba lafiya ba, sai dai ban kawo cewar maganar Noor bane saboda a tunani bata san sun fita ba. Kasa gaisawa ta yi da Inna sai kawai ta sakar min ido hawaye ya soma mata zuba

“Ke lafiyar ki?”

Na tambaya ina dafata.

“Nawwara”

Sai kuma ta yi shiru kamin ta cigaba.

“Dazu da Bilal ya fita da Noor wai ya tsaya da shi a AGG MALL ya siya masa chocolate shine sai yaga wani abokinsa suka tsaya gaisawa, wai Noor ya fito daga ciki ko da suka gama gaisawan ya nemeshi ya rasa”

Nina mike tsaye da sauri Inna kuma ta dinga furta

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”

Sakina kuma ta dora hannu saman kai tana kiran

STORY CONTINUES BELOW

“Mun shiga uku”

“Yanzu ina shi Bilal din yake?”

Inna ta tambaya hankalinta a tashe.

“Yana can gidansu, wai besan yadda zai fada muku ba shiyasa be zo ba tun dazu, nima yanzu yake fada min kuma ya ce ya bada report gurin yan sanda da gidan radio”

Ni dai ban iya cewa komai ba ban da hawayen da nake, muna haka naji tsayawar mota a kofar gidanmu wanda hakan ya tabbatar min da cewar Jibril ne kuma daman yana kusa da unguwar a lokacin da ya kira.

“Ga Jibr.. Il nan… Yace tafiya zai yi da Noor”

Na fada muryata na rawa.

“Ki fita ki fada masa gaskiya dole ne ya sani”

Inna ta umarceni, tashi na yi na fita ina hawaye, nasan Jibril ba zai yarda ba amman ya zama dole na fada masa, ko da na fito yana jingine jikin motarsa yana danna wayarsa da alama ni zai kira.
Fitowata tasa ya dago kai ya kalleni yanayin yadda na ke tafiya na doso shi yasa ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata.

“Karki fara min complain ba gurinki na zo ba Wallahi, kawai zan dauki dana ne kuma nasan idan ban zo da kaina ba ba zaki bari taje ba, and i need to be with my son”

“Jibril…. Noor …… Noor”

Na kasa magana saboda kukan da ya ci karfina. Ya sakar min ido sosai yana son jin abunda zai fito daga bakina.

“Noor ya bata….”

“What? How?”

Na kasa magana sai kuka na ke.

“Look Nawwara, idan ma kin shirya hakan ne dan ki samu nisanci da ni to wannan ba hanya ba ce, dan zan iya jure komai ban da rashin Noor, dan Allah ki canja tsari”

“Wallahi ba wasa na ke ba Noor ya bata”

Ya tsaya kallona dan tabbatar da zancen da nake gaskiya ne ko akasin haka.

“Kamar ya Noor ya bata bata ya bata ya bata as how?”

Ya tambaya yana mai daga murya tare da hannyensa sama, ni kuma sai kuka na ke ina ta kokarin rufe baki.

“Ki daina wannan banzan kukan naki ki fada min yadda aka yi dana ya bata”

Na razarana sosai saboda yadda ya katsa min tsawa da kuma irin bacin ran dake cikin muryarsa.

“Da suka fita da Bilal shine suka tsaya Agg mall siyen chocolate sai ya nemi Noor ya rasa”

Ya yi dariya marar sauti

“Ki ce Bilal ya sace min yaro ya siyar ko kuma ya boyeshi ya nemi kudin fansa”

“No Bilal ba zai yi haka ba, Wallahi Bilal ba zai taba cutar da Noor ba”

“To wa zai cutar da shi waya batar da shi a yanzu?”

Ya fada a tsawace.

“Wallahi Bilal ba zai cutar da Noor…”

Hannunsa ya daga zai mareni sai kuma ya kaiwa gilashin motarsa bugun yana wani irin huci.

“Akan dana zan iya taba kowa Nawwara kuma kowa da kowan nan har da ke, idan kin san wani abu ne kula da Bilal tau ki gaggauta kanwace shi tun wuri”

Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya bar ni nan tsaye ina aikin kuka, sai ga Sakina ta fito da gudu ta nufi hanyar Babban gida, ni kuma na juya na koma, ko da na shiga Inna na ta buge bugen waya tana kuka kamar yadda Jidda take.
Ko da tara na dare ya yi gidanmu ya cika da jama’a makota da kuma yan uwa, maza suna suka shiga gari inda ake sa ran za a ganshi har Agg mall din anje amman ba a ganshi ba, ko da Baba Sulaiman ya aika Sakina ta kira masa Bilal sai ta dawo ta fada mana cewar wai yana police station an tafi da shi tun dazu, kowa yayi mamakin wanda zai kulle Bilal a wannan lokacin sai da Baba Sulaiman da Inna suka fada cewar Jibril ne, a ranar duk wanda yake cikin gidan nan ya tabbatar da cewar Noor yana da Uba.

STORY CONTINUES BELOW

Ni da Inna da Mama turai da Baba Sulaiman da Sakina da kuma Jidda muka kwasa muka je station din, daidaikun mutanen unguwa suka bimu saboda gulma. Mun tararda Jibril a can sai mahaifin Bilal da mahaifiyarsa tana ta kuka, sai wani kanensa daya.

“Ina Bilal din yake?”

Inna ta tambayi Mahaifinsa sai ya amsa mata cikin rashin dadin rai.

“Yana can ciki sun ce ba zasu fito da shi ba, tun dazu muke a nan tsaye babu irin rokon da ba mu musu ba”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”

Cewar Inna, ni kuma na doshi gurin Jibril sai yayi saurin tashi ya fice daga station din, da gudu na bishi ina kiran sunansa daker ya juyo ya kalleni fuskarsa babu annuri.

“Minene”

“Wallahi ba Bilal ba ne ya sace shi”

“Ke kika sace shi”

“Wallahi ba Bilal ba ne, dan Allah ka kyale kasan yan sandan nan basa da mutunci zasu iya ji masa fa”

“Ke ta Bilal kike ni kuma ta da na nake, babu ruwana da alakarku ya fito min da da na ya zauna lafiya”

Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya barni nan tsaye.

Wasa wasa aka kwashe kwana uku ana abu daya, Jibril ya ki bari a saki Bilal saboda yana zargin shi ya batar masa da da, ita kuma mahaifiyar Bilal da yan uwansa suna dora laifin akaina, a ganinsu ko da da gaske Bilal ya batar da Noor ai be cancanci a ayi masa irin wannan wulakancin ba, har fade take wai danta be taba zuwa cell ba sai dalilina, babu irin magiyar da bana ma Jibril amman kullum maganarsa daya Bilal ya fito masa da da, ni da shi baka iya tantance waye ya fi shiga damuwa, sai dai Jibril ya fini shiga tashin hankalin sosai saboda haukacewa yake kokarin yia kan neman dansa, har mahaifinsa sai da ya zo har sokoto saboda wannan maganar Noor, kullum mafarki na Noor sai dai har yanzu zuciyata bata zargin Bilal. Ranar talata ranar da mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir ya yasa a kashe maganar gurin yan sanda muna station mu dukanmu Jibril ya saka Bilal gaba yana masa magiya har da kukansa.

“Dan Allah dan Annabi Bilal ka fada min inda da na yake? Idan kudi kake so ka fada min zan baka ko nawa ne, kuma Wallahi na maka alkawari ba zan bari a ama ka komai ba, amman Noor shi kadai ya rage min ka tausaya min Bilal dan girman Allah”

Bilal ya kasa magana sai hawaye yake, gaba daya kamaninsa sun canja.

“Wallahi Bilal be dauki Noor ba”

Na fada cikin kuka, sai mahaifiyar Bilal ta kwatse ni.

“Ke dan Allah can rufewa mutane baki, baki fada tuntuni ba sai yanzu tsohuwar munafuka, ko da yake Allah ya kara ai kai ka ce ka ji ka gani”

Ban kara mata magana ba, har muka fito station din, muna dawowa gida sai ga Jibril ya iskoni har gida be tsaya a waje ba ya shigo cikin gidanmu da sallama ba tare da ya nemi uzinin shiga ba, ban tabbatar da irin ramar da yayi ba sai a wannan lokacin idanuwansa sun fada sosai. Gaban Inna ya je ya risina yana hawaye kamar karamin yaro

“Inna na rokeki ki saka Nawwara ta fada min wani abu akan batan da na, shi kadai ya rage min a duniyar nan, yau kwana hudu kenan ba a ga Noor ba, duk wanda ya dauke ke Noor rayuwarsa yake so ba kudi na ba, da kudi nane da yanzu an kira an ce na bayar, babu inda ban duba ba, babu irin binciken da ban sa anyi ba amman an kasa ganin Noor”

Inna ta kasa ce masa komai, ni da nake zaune nesa da ita na kalleshi cikin hawaye na ce

“Ban san komai a akan batan Noor ba, idan kuma baka yarda da ni ba, zaka iya sakawa a kulleni kamar yadda ka yi ma Bilal”

STORY CONTINUES BELOW

“Na rasa mahaifiyata Nawwara a lokacin da ban san miye duniya ba, ban sani ba ko zan iya jure rashin Noor”

Haka kawai ya fada ya mike tsaye ya shafa kansa ya fice. Sai da ya fice sannan Inna ta ce

“Miyasa baki fada masa gaskiya akan abokinsa ba? Mai yiyuwa shi ya sace Noor”

“Idan kuma ba shi bane fa Inna? Sai mu dauki laifin mu dora masa? Mai yuyuwa yan satar mutane ne suka sace shi ko kuma yan garkuwa da mutane sai mu dauki laifin mu dora masa?”

“Amman idan ba a bullowa wannan matsalar da wuri ba zata iya zama babba, kina da dalili da hujja mai karfi ta zargin wannan mutumen kuma shi kadai ya rage a yanzu wanda zamu iya zargi” 1

Tabbas ni kaina zuciyata a yanzu Siraj take zargi, amman ina cikin kwankwanto saboda kar na yi zargi na jefa rayuwarsa cikin matsala daga karshe kuma ya zama ba shi din ne ba. Ina jin kewar da na sosai kullum mafarkinsa na ke yadda muke rayuwa da shi a cikin gidan yana ta min gizo a ido wani lokacin har ji na ke kamar yana kirana.

JIBRIL POV.

Daga gidansu Nawwara kai tsaye ya nufo gida har ya iso be daina hawaye ba, zuciyarsa kuna bata daina kuna ba, nan da nan ya fara tarin jini sai da ya saka tissue ya goge, babu wanda idanuwansa suke son gani kunnuwansa suke son jin muryarsa a yanzu irin Noor, daman tun kamin faruwar hakan jikinsa yake masa ba dadi ashe na rabuwa da dansa ba, rabuwansu na karshe ya tuno lokacin da yaje daukarsa yace Bilal zai fita da shi, rumgumar da ya yi masa ya dingajin kamar yanzu yake masa ita.

“Ina kake Noor ina kake?”

Ya tambaya yana buga sitarin motarsa yana kuka sosai kamar makaramin yaro.

“Miyasa nake ta rasa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwata ne? Miyasa ne? Allah karka karbi rayuwar da na a yanzu da na fi bukatarsa Allah kada ba basu damar cutar da shi Allah ka kubutar min da dana”

Kamar zai fadi haka ya fito daga motar yana kuka be damu da ma’aikatan gidan su ga kukansa ba shi dai matsalarsa da isheshi. A falo ya zauna yana ta misalta irin yadda Noor yake idan ya zo gidan, sai kuma ya dauko wayarsa ya bude gallery yana kallon hotunan Noor da kuma wanda suka yi tare.

“Wa zai min haka a duniyar nan? Mina tarewa wani? Bilal mi na maka? Oh Allah”

Ya mike tsaye yana share hawayensa, a dare kasa bachi yayi kamar dai ko wane dare yana ta aikin sallah da rokon Allah ya fito masa da dansa, kudi mai yawa ya diba ya bawa Malamin nan mai koya masa karatu akan yasa a yi masa addu’a Allah ya bayyana masa dansa.

Yana zaune yana shan ruwan tea kamar kullum domin tun da abun ya faru baya cin komai sai ruwan tea maganinsa ma ya daina sha. Sai ga Kiran Abbah ya shigo wayarsa cikin yanayin damuwa ya daga.

“Assalamu Alaikum”

“Wa’alaikassalam Jibril ka zo gida yanzu nan ina jiranka”

“Okay”

Yana kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bedroom ya canja kayan jikinsa daga jallabiya zuwa kananan kaya, a gaggauce ya fito saboda yasan yau Abbah zai bar sokoto yasan dalilin kiransa ba zai wuce ya fada masa Maganganun hakuri ba.

Ko da ya isa Abdullah fodio road ya tararda Abbah tare da wani bako, bayan sun gaisa sai Abbah ya gabatar masa da shi.

“Ga Dsp Sani Muazu nan na fada masa komai akan case din Noor, abunda yasa na ce kasa a saki Bilal saboda a bullo masa ta wata hanyar, tun da har ya kwashe kwana uku a station da duk irin wahalar da ake bashi be fadi gaskiya ba zai taba fada ta hanyar tsiya ba, so wannan dsp ya san yadda xai bibiyi Bilal har a gano gaskiyar lamarin”

STORY CONTINUES BELOW

“Thank you Abbah”

Abbah ya dafashi.

“Ka kwantar da hankalinka Jibril Noor dinka yana nan lafiya kalau, kuma za a gano shi da yarda Allah duk wani bayani sai kanyi masa ni yanzu zan wuce”

Sai da Abbah ya koma ciki yayi yan mintuna sannan ya fito Jibril ya raka shi har gurin mota suka yi sallama dan baya jin xai iya binsa har airport, bayan Abbah ya wuce ne Jibril ya dawo ya cigaba da yi ma Dsp bayani akan abunda ya sani a game da Bilal sai Dsp ya nemi hoton Bilal da addirensa da komai nasa.
Suna haka wayar Jibril ta yi ringing yana dubawa ya ga Number Siraj cikin sauri ya dauko a tunaninsa ko zai sanar da shi wani abun ne, domin shi ma ya damu sosai akan batan Noor duk wani shiga da fita da ake tare da shi ake yinsa.

“Hello Siraj”

“Jibril kana ina ne?”

“Ina nan Abdullah Fodio Road lafiya?”

“Nawwara ce ta kirani a waya tana kuka tana min magiya wai na fada mata inda danta yake”

“What? Ita da kanta?”

“Yes ita ce ni abun ya bani mamaki ne”

“Kana ina ne? ”

“Ina gida”

“Bari naje na sameta”

Yana kashe wayar ya mike tsaye yana kallon Dsp

“Taso muje can inda zamu samu hotonshi”

Tare suka fito sai Dsp ya shiga motar Jibril suka nufo gidansu Nawwara. Sai da ya tsaya nesa da gidansu Bilal ya nunawa dsp gidan sannan ya karaso kofar gidansu Nawwara, kiranta ya yi ya sanar mata yana kofar gida yana son magana da ita sai ta ce ya shigo ciki.

Ko da ya shigo ya sameta tsakar gida tana aikin kuka duk ta rame ta yi baki sosai kamar ba ita ba, sai da ya gaisa da Inna sannan ya zauna saman tabarmar da Inna ta shinfida masa yana kallon Nawwara har cikin ransa yake jin kukanta.

“Ki yi hakuri Nawwara dan Allah ki daina kukan nan kina tada min da hankali”

“Jibril Siraj ne ya sace Noor”

Ta fada cikin kuka.

“What?”

Ya kalli Inna sai kuma ya maida dubansa gurin Nawwara a tunaninsa bakinciki ne yake son taba ta.

“Listen Nawwara…”

“Wallahi ba karya na ke ba, shi ya kade Noor kuma yana cikin plan dinsa kashe Noor da ni da kuma kai”

“Okay na ji shikenan zan masa magana”

“Ba hauka na ke ba Jibril ka tambayi Rabi ka ji ita ta fada min komai, shiyasa na koma aiki tare da kai nasa ka karbe kamfanin daga hannunsa ya dawo hannunsa shine yake kiran Abbah ya fada masa komai saboda ya lalata maka rayuwa yasa ka fara shan cocaine, kuma shi ya kade Noor da mota lokacin da suka taso makaranta, Noor ya ganshi shiyasa ya ki yarda su yi ido hudu da Noor saboda karya nuna shi”

“No Nawwara Bilal ne ya kade Noor”

“Ba shi ya kade ba, lokacin da Noor ya yi hadari Bilal yana kamfaninka yana aiki, shine duk ya tsara wannan Jibril ka karda da ni, Rabi ce ta fada min komai idan bata fada min ba babu yadda za ayi na sani”

Wayarsa ya dauko ya kira Rabi tana dauka ya ce.

“Duk inda kike ki zo ki same ni yanzu nan gidansu Nawwara”

Be tsaya jiran abunda zata ce ba ya kashe wayar ya kira Siraj.

“Siraj ka zo nan gidansu Nawwara gani nan na iso”

Nan ma kashe wayar yayi sannan ya kalli Nawwara.

“Siraj ba zai min haka ba, babu dalilin da zai sa Siraj ya sace Noor”

“Wallahi da gaske nake Siraj ne ya sace shi”

Siraj ya riga Rabi isowa duk da kasancewar ta fishi kusa da unguwarsu Nawwara, bayan ya shigo cikin gidan ne sannan Rabi ta iso, Nawwara na ganinsu ta mike tsaye tana hawaye

“Rabi fada masa gaskiya fada masa abunda kika fada min akan Siraj”

Rabi ta nuna kanta.

“Ni Kuma? Mina fada miki ne?”

Nawwara ta girgiza kai.

“Karki min haka dan Allah ki fadi gaskiya”

“Gaskiyar me zan fada? Ni ban san komai akai ba”

Inna ta matso kusa tana kallon Rabi da mamaki ta ce

“Yar nan ki ji tsoron Allah ki fada gaskiya, ke fa kika sami Nawwara a cikin gidan a nan kika fada mata cewar Siraj so yake ya kashe Jibril da ita kuma shi ya kade Noor”

“Haba Inna da girmanki be kamata ki yi wannan maganar ba, bata dace da ke ba, ni gaskiya ban san komai a kai ba”

Jibril ya kalleta

“Look Rabi ki fada mana gaskiya”

“Sir Jibril ban san komai a kai ba, idan ma wani abun ne ai kai zan sama na fadawa gaskiya ba Nawwara ba”

Faduwa Nawwara ta yi kasa tana kuka da tureturen kasa kamar mai aljanu, hakan yasa Jibril zargin tana kokarin fita hayyacinta ne. Sai ya kalli Siraj

“Siraj yi hakuri dan Allah ka je gida yanzu zamu kaita asibiti Rabi ku wuce kawai”

Siraj da tuni gumi ya gama keto masa ya juyo a firgice ya fice, sannan Rabi ita ta fice hankalinta sam baya jikinta.

Sai Dsp nan ya kira Jibril gefe yana tambayarshi alakar da shi tsakaninsa da Siraj, Jibril be boye masa komai ba ya fada nasa sannan Dsp ya bi bayan Rabi. 1

NAWWARA POV.

Ba zan iya cewa ga halin da na ke ciki ba, ni dai nasan bayan abunda ya faru a gidanmu Inna da Jibril sun kawo ni asibiti shi ma sama sama nake gani kamin Jibril din ya shigo ya yi min allura, sai yanzu da na farko sai na ke ganin komai kamar a mafarki hudun da na hango a window ne ya tabbatar min da cewar dare ya yi domin ko da abun ya faru da safe ne misalin tara zuwa goma.

Tashi na yi zaune sai naga drip a hannuna, tunawa da Noor yasa idanuwa cika da kwalla, dakin babu kowa sai kayan tea da dan karamin freezer, ina haka Jibril ya turo kofar dakin ya shigo.

“Sannu”

Ya fada yana cire min drip din a hannu.

“Ka yarda da ni Jibril Wallahi Siraj ne”

“Na yarda Nawwara”

Ya fada sannan ya cire safar hannunsa ya shi ya shiga hada min tea. Wayarsa ce ta yi ringing sai ya aje hada tea da yake ya yi picking.

“Eh miya faru? Da gaske? Okay gani nan zuwa”

Haka kawai na ji ya fada sai ya juyo ya kalleni.

“Anga Noor police sun tafi da shi asibitin Uduth za a duba shi”

Da sauri na sauka saman hospital bed din hankalina a tashe.

“Jibril zan je”

Tare muka fita, a waje muka hadu da Inna sai duk muka dugunduma gaba daya muka nufi Uduth din dake gawon nama.
Kamin a isa har jin na yi kamar na runtse idona na ganni gaban asibitin. Muna isa parking space din na asibitin na bude na fito da sauri ni da Inna sai dai duk da haka jibril ya rigamu isa Emergency din kasancewarsa Namiji kuma ya hada da gudu, muna isa muka tararda Dsp din nan na dazu tare da wasu yan sanda sanye da uniform. Muna isa sai ya tare mu wai Jibril kawai zai shiga ya ga Noor ba tare da ni ba.

“Kamar ya ni ce mahaifiyarsa fa”

“Na sani amman shi zai shiga”

Zan kara magana Inna ta rike ni ta ce ta Jibril din ya shiga, sannan ta shiga kiran yan’uwa tana sanar musu a waya. Jibril ne ya fara shiga ni da Inna muka tsaya ina ta jin kamar na yi tsalle na shiga na gani. Muna haka Jibril ya fito a daya daga dakunan dake Emergency din fuskarsa da hawaye, kamin ya karaso kusa da mu ya zame kasa ya fadi yana kokarin rike wata kofa dayan hannunsa na danna da zuciyarsa. Wani irin nauyi zuciyarsa ta yi masa har ta kai kafafunsa ba sa iya daukarshi, yadda ya ga Noor yana ta masa yawo a idanuwa, but Nawwara da ya hango ta fadi zaune tana hawaye, sai tausayinta ya lullube masa zuciya, a kokorin mikewa ya yi tsaye ya tunkareta yana kokarin buye damuwarsa.

“Ya mutu ko?”

Ta tambaya cikin rawar muryar da kuka ya dakishe mata ita.

“No lafiyarsa kalau” 1

Ya fada yana kokarin tare hawayen da suke son zubo masa. Daukar Numfashi Nawwara ta fara yi idanuwansa na kokarin rufewa kamar wacce za a cirewa zuciya. Inna kuma ta dora hannu saman kai ta fashe da kuka tana rika Nawwara.
“Help us please”

Jibril ya fada yana karasawa kusa da ita, hankalinsa a tashe dan shi a yanzu ba nata yake ji ba na Nawwara yake ji, sai wasu Nurses suka zo da gudu suka rikata suka dauketa suka dorata saman gado suka nufi wani bangare da ita, shi kuma ya juyo ya dawo dakin da Noor yake kwance kamar gawa likita biyu ya tarar a gurin sai Nurse daya da ta mika masa wasu takardu Jibril ya saka hannu sannan suka dauki Noor din suka fita da shi zuwa dakin tiyata.

Jinginawa Jibril ya yi da kofar gurin ya lumshe ido hawaye suka zubo masa, zuciyarsa na ta raya masa kamar Noor ba zai rayu ba, an yanka masa ciki da wuka har hanjinsa sun bayyana ga gefen fuskarsa ma ya kumbura. Sai da ya share hawayensa sannan fito daga dakin ya nufo gurin da Dsp din yake wani irin bakinciki da bacin rai na fisgarsa. 4

“Dsp taya haka ya faru? Na fada maka idan har kun gano inda yaron nan yake ku fada kamin ku yi komai”

Dsp be ce masa komai ba sai da suka fito daga Emergency din sannan ya kalleshi ya ce

“Aikinmu muke yi Jibril da ace na tsaya kiranka da wata kila yaron nan be rayu ba, domin a can cikin daji muka dauko shi, can cikin arkilla tanki can cikin dajin nan dake saman dutse”

“Ina Siraj din yake?”

Ya tambaya yana sauke ajiyar zuciya.

“Yana can station nasa a tsare shi, karka damu da wannan”

“Rabi fa?”

“Am sorry jami’an mu gawarta kawai suka samu” 5

“How”

Ya tambaya a rude.

“We don’t know yet but idan komai ya laba zamu bincika”

Kansa ya daga sama ya kalli taurari zuciyarsa na mugun quna.

“Siraj…”

Sai yasa yatsansa ya share hawayen da ke gefen idonsa. Juyowa ya yi ya dawo ciki, tafiya yake amman ji yake kamar ba taka kasa yake ba, numfashinsa ba ji yake kamar ba a jikinsa yake ba, yana karasowa kofar Emergency Inna na isowa cikin tashin hankali.

“Noor ya mutu ko?”

Dsp ne ya shiga mata bayani Jibril kuma ya doshi dakin tiyata yana safa da marwa, gabansa sai faduwa yake.

Awarsu biyu a dakin tiyatar sannan suka fito da Noor unconscious, da sauri Jibril rika gadon da Noor yake ya kai hannunsa ya taba gefen wuyansa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Daya daga cikin likitan biyu da suka masa tiyata ya san Jibril farin sani saboda sun yi aiki a tare asibitin Abuja, shi ya dafa Jibril ya ce

“Ka kwantar da hankalinka, tiyata ta yi kyau sai dai ka masa fatar samun sauki” 4

Kai kawai Jibril ya iya dagawa ya saki gado ya rike ginin gurinsa saboda mugun ciwo da zuciyarsa take, daker ya mike tsaye daidai ya bi bayan Nurses din har suka isa icu suka canjawa Noor gado saka dora masa oxygen sensor sannan suka masa wata allura a hannu mai hade da drip, sannan likitan ya dauko wani abu mai guda biyu mai kamar iron ya hada shi ya goga sannan ya kurga 1 2 3 ya danna gaban Noor dai dai zuciyarsa.
Sai ga Noor ya numfasa da mugun karfi sai kuma ya lumshe, numfashinsa ya shiga nunawa a sensors. 3

STORY CONTINUES BELOW

“Al-hamdulillah”

Shine abunda Likitan ya fada da duka Nurses din kasancewarsu musulmai. Wani irin lumshe ido Jibril ya yi ya bude bakinsa kunshe da godiyar Allah.

NAWWARA POV.

ban san iya awa nawa na yi a sume ba ni dai na farka na ganni saman gado oxygen na sanye a fuskarta, abunda ya faru ne ya soma dawo min zuciyata na ta nuna min cewar da na ya mutu. Ban san akwai mutum a kusa da ni ba har sai da na fara hawaye.

“Am sorry Nawwara Noor yana nan raye an masa tiyata kuma an yi nasara”

Kallo daya na yi masa na kawarda fuskata, sai na rika kokarin sauka saman gadon.

“Babu inda zaki iya zuwa a yanzu karfe uku na dare ne, kuma babu wani karfi a jikinki a yanzu, Inna tana tare da Noor ni ma bata san ina nan ba, Sakina aka sa ta kwana da ke tana waje”

“Ya mutu ko?”

Na tambaya ina kuka duk da nasan amsar ba zata min dadi ba amman ina da bukatar jinta, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.

“Be mutu ba”

“Dan Allah karka boye min Jibril ka fada min gaskiya”

“Zan raka ki yanzu ki ganshi”

Saukowa na yi daga kan gadon duk da babu kwarar kuzari a jikina, sai dai na samu gwarin guiwar tafiya ne saboda jin cewar zan ga Noor ne hakan ya tabbatar min da cewar basu kashe shi ba kenan. Hankalina ya tashi sosai lokacin da na ga halin da Noor yake cikin, duk kokarin da Inna da Mama Turai suka yi na hana ni kuka hakan be yi tasiri ba sai da kuka sosai kamar Noor din ya mutu ne.

“Ina aka ganshi? Waya masa haka?”

Na tambaya ina kallon Jibril a zuciyata kuma ina jin cewar zan iya daukar ma dana fansa a kan duk wanda ya yi masa wannan abun. Be bani amsa ba sai ya juya ya fita ni kuma na bishi duk da babu wani kuzari a jikina Inna ta biyoni tana kirana sai ya juyo ya daga mata hannu alamar ta bari hakan yasa ta juya ta koma.
Haka na cigaba da binsa har muka koma dakin da aka kwantar da ni wanda ya kasance babu kowa a dakin sai ni da shi.

“Siraj ne”

Ya fada ba tare da ya kalleni ba.

“Amman da na fada maka karyata ni ka yi, da ace ka dauki mataki tun a lokacin da haka be faru da Noor ba, amman sai ka maida ni mahaukaciya”

Kallona ya yi da idanuwansa da suka rine suka yi ja sosai saboda kuka da kuma bacin rai ya ce

“Kin riga kin kira Siraj kin tuhume sa, ni kuma na kirashi tare da Rabi ne saboda na tabbatar da abunda kike fada, da ace na sa ana rike Siraj a lokacin nan da har yanzu Noor be bayyana ba, da ganga na kai shi asibiti saboda ya yarda cewar haukace take son kama ki, amman ban boyewa Dsp komai ba a game da Siraj, hakan yasa ya bi bayan Rabi saboda ni da shi duka mun lura da yanayinta, da ace ban turki Rabi a wannan lokacin ba da ba zata taba fadin gaskiya kamar yadda ta yi a yanzu ba, ashe all this while Rabi ta san inda Noor yake amman ta kasa fada saboda tana tsoron abunda zai biyo baya, Siraj ya bata yarda shiyasa ya fada mata inda ya aje Noor, and Nawwara na san idan har Rabi bata fada miki ba babu yadda za ayi ki san wani abu daya shafi kanfanina ko kuma rayuwata kuma na san idan har bata fada ba babu yadda za ayi Inna ta goya miki baya, i do believe you sai dai babu yadda za ayi na nuna hakan a gaban mutumen da na daukeshi kamar dan’uwa, Rabi da kanta ta fadawa Dsp inda Noor yake a lokacin da komai ya kure saboda isha’i ta yi a lokacin kuma ta fadawa police cewar rayuwarta tana cikin hatsari, but ko da suka je sun yi latti an riga an kasheta, Noor kuma suka same shi a cikin gidan da ta fada musu an yanka masa ciki” 1

Hannu nasa na rufe bakina saboda kukan da ke son ya ci karfina, sai na rika gadon na zauna ina kuka a hankali.

“Komai ya faru saboda ni Nawwara”

Ya fada yana hawaye tare da danne kukan da ke son kubuce masa.

“Rabi ta rasa ranta saboda ni, an yanka cikin Noor saboda ni, kin sake shiga tashin hankali saboda ni, da ace ban dawo rayuwarki a karo na biyu ba da duk haka be faru da ke ba, kina da gaskiya Nawwara, kina da dalilai na ki na, a duk lokacin da na kusance ki sai wani abu marar kyau ya faru da ke, ni ne silar lalacewar rayuwarki a karon farko, na dawo a yanzu da tunanin zan iya gyarata na saka miki farinciki saina sake bakanta miki wanda ba hakan raina ke so ba, but komai ya kare yanzu.

Na miki alkwari daga ranar da Noor ya ji sauki ya tashi, ba zaki sake sani a idanuwanki ba, balle na dame ki ba zaki sake kuka da ni ba, kowa ma ba zai sake kuka da Jibril ba, zan tafi wata duniyar wacce babu wanda na sani kuma babu wanda ya san sai na yi rayuwa a can har ta Allah ta kasance, saboda ciwon da ke jikina yana tabbatar min da cewar mutuwata tana kusa da ni a yadda na ke ji a zuciyata na san ko da wane irin lokaci zata iya bugawa na mutu, ina tsoron sake kusantarku ke da Noor wai Nawwara saboda kar wani abun ya same ku… Ki yi hakuri da duk abunda ya faru, but no matter what Nawwara har gobe ina son ki, ko da na mutu a yau na mutu da ciwon son ki ina son ki san wannan, ina son zuciyarki ta gansu cewar ni masoyinki ne ba makiyinki ba” 5

Yana fadar hakan ya juya ya fice be damu da ya share hawayen da suka bata masa fuska ba, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da tausayinsa da na kaina da kuma na Rabi da Noor…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page