RAI BIYU CHAPTER 12

RAI BIYU
CHAPTER 12
Tare da Siraj suka shigo a lokacin Jibril na zaune saman kujerarsa yana kallon ƙofar shigowa office ɗin.
Tun da suka haɗa ido da Mustapha zuciyarsa take ta raya masa wani akansa, Siraj ne ya nuna masa gurin zama a cikin kujeru dake gaban teburin Jibril suna facing ɗinsa, domin Jibril in banda kallonsa babu abunda ya ke. Mustapha ya miƙa masa hannu. +

“Sunana Mustapha Faruk Turaki”

Jibril ya daɗe yana kallon hannunsa sannan ya miƙa masa.

“And…?”

Mustapha ya yi mamakin ganin yadda yake amsa masa kamar baya maraba da mutane, sai dai be nuna masa komai ba ya ɗora akan abunda ya kawo shi.

“Na zo ne akan wani gida da yake guiwa, wanda ka siya ta hannun Malam Haruna”

“Me gidan ya yi maka?”

“Be min komai ba, ance min ka siye gidan ne milion ɗaya ni kuma zan baka 1.5 million ka mallaka min gidan”

Jibril ya yi murmushi tare da kwantawa saman kujerarsa yana lilo tare da wani shegen murmushi.

“Waya faɗa maka ni na siya gidan?”

“Malam Haruna ne ya faɗa min, naje gunsa ina son na siye gidan sai yace min wani ne ya siya sunansa Jibril, amman ya ce be san waye Jibril ɗin ba, yaro ne ko babban na buƙaci gani ka, yace bashi da number ka sai da ta wanda suka yi cinikin domin ya bar number akan idan mutunen gidan su tashi a faɗa masa, na buƙaci ya bani number wanda suka yi cinikin ne sai ya bani number wannan Siraj ɗin, ni kuma na kirashi sai ya yi min bayanin ba shi ya siye gidan ba kai ka siya kuma shi baya da wani abu da zai yi sai dai na yi magana da kai”

Hannu Jibril ya kai yana wasa da wata ƙwallo da ake saman teburinsa mai ruwan zinari wance aka ɗora saman wani abu mai kama da turmi.

“Amman miyasa zaka siya gidan har 1.5 million?”

“Saboda kai da ka siye gidan ka bawa waɗanda suke cikin gidan kwanaki su tashi, that’s why na ke son siye musu gidan”

Siraj ya haɗa ido da Jibril sannan ya kalli Mustapha ya ce

“Kana da alaƙa da ƴan gidan ne da har zaka siye gidan da kuɗi da yawa haka, gidan da be wuce dubu ɗari shida ba?”

Mustapha ya watsa masa wani shegen kallo tare saboda yadda yaga sun maida shi ƙaramin yaro.

“Mr gida na zo siye ba bincikar alaƙata da ƴan gidan na zo ku min ba”

Jibril ya yi murmushi yana ciagaba da juyawa saman kujerar.

“Come on tell me boy maybe i can help”

Mustapha ya maida dubansa gurin Jibril jin irin isgilancin da yake masa, yanzu kan zuciyarsa ta fara raya masa akwai dalilin da ya sa Jibril ya siye gidan.

“Ban girmi ka karani boy ba? Name what ever you want zan baka am not here to play a game”

Jibril ya miƙe tsaye yana dariyar ƙeta ya nufi gurin window sa yana faɗin.

“In banda kai daƙiƙi ne baka taɓa tsayawa ka yi tunani ba, baka taɓa tambayar kanka dalilin da yasa ka na siye wannan gidan ba? Taya zan zuba har milion ɗaya na siye gidan dubu ɗari biyar sannan ka zo ka ce na fansar maka ni ba a min wasa da kuɗi sai dai ni na yi ma wasu wasa! Mu kamfaninmu baya siye da siyar da gidaje ni ma kuma ba sana’a ta ba ce, so wannan gidan akwai dalilin da yasa na siye shi, so walk out of my office ba zan siyar ba”

Mustapha ya tashi tsaye yana murmushi.

“Zuciya na raya min ka siye gidan nan ne saboda wata manufa is that the reason yasa ka basu lokacin tashi? Kuɗin ka be amfane ka ba Mr Billionaire, tun da har zuciyarka zata raya maka siye gidan talakawa kuma ka takura musu bayan kasan babu su da inda zasu koma me suka maka ne?”

STORY CONTINUES BELOW


Jibril ya ƙyalƙyale da dariya daga inda yake tsaye ba tare da ya juyo ba ya ce.

“Na siye gidan ne saboda na isa na siya, ni mijin Nawwara ne idan ma akan ta kake wahalar da kanka so ka daina yaudarar kanka”

Mustapha ya yi murmushi tare da zuba hannayensa aljihu.

“Her ex-husband dai Nawwara bata da wani miji a yanzu”

Jibril ya juyo yana kallon Mustapha murmushin da ke fuskarsa yana dusashewa, can kuma sai ya fara dariya.

“Yeah yeah it Funny am laughing, amman bari na faɗa maka wani abu ka bar irin wannan wasan i don’t play when it comes to Nawwara”

Mustapha ya nufo kamar yadda Jibril yake doso inda yake.

“Kana son zaka saketa? Ƙarya so kake mata tun da har ka iya siye gidan da suke ciki dan kawai ka takura mata, a haka ake so? Ko dai jikinta kake so ne huh? Da nine na samu damar auren Nawwara ko ƙuda ba zan bari ya taɓa ba balle har ya kai ga na saketa ko da kuwa kullum ruwan zafi take zuba min a jiki, but look at yourself ka yi arzikin aureta amman ka saketa ooph so sad maybe rabona ce shiyasa ka saketa” 2

Cewar Mustapha yana wani abu da fuska kamar mai magana da ƙaramin yaro yana murmushi, cikin zafin rai Jibril ya kai masa bugu a fuska ya sake kai masa wani a gefen baki, cikin zafin nama Mustapha ya ɗago zai rama sai Siraj ya yi saurin riƙeshi ya jashi baya, hakan ya bawa Jibril ƙara kai amsa wani dukan a baki sai jini ya fara zuba. 1

“Abraham”

Siraj ya ƙwalawa PA ɗin Jibril kira sai gashi cikin ɗakin da sauri.

“Riƙe min wannan”

Da sauri ya Siraj ya saku Mustapha ya nufi Jibril ya riƙe shi yana faɗin.

“Take him out”

Ganin Abraham ɗin ba zai iya fitar da shi shi kaɗai ba, yasa Siraj ya saki Jibril ya nufi Mustapha suka fitar da shi tare.

Juyowa Jibril ya yi ya nufi teburinsa ya buge System ɗin da ke saman ta faɗi ƙasa.

“I need to see her, we need to talk zan bata haƙuri zan yi komai akan ta, ba zan bari wani ya ɗauki muhallin na a zuciyarta ba”

Komawa ya yi gaban teburin ya ɗauki wayarsa ya danna number Abbah, yawo ya riƙa yi cikin office ɗin zuciyarsa na mugun bugawa, a ƙarshe ya samu tsayawa jikin window saboda Abbah ya yi picking.

“Afternoon Abbah”

“Afternoon Jibril ya aiki?”

“Alhamdulillah, Abbah we need talk”

“About?”

“Nawwara Abbah na gano inda take”

“Ai nasan zaka gano inda take, shiyasa na ce ban yafe maka kaje ƙofar gidansu da sunan neman gafararta ba, kai yanzu dan baka da kunya sai kaje ƙofar gidansu har ka iya haɗa ido da ita? Mu muka zaɓa maka ita lokacin da zaka aureta ka butulce ma umarninmu ka ce kai ba haka ba yanzu kun rabu miye na bibiyar yarinyar mutane?”

“Na tuba Abbah Wallahi na tuba”

Ya duƙa har ƙasa kamar yana gaban Abbah.

“No ban yarda ba”

“Abbah ko dan na nemi gafararta ba, ina da buƙatar na tambayi abunda yake cikin maybe ta haihu, you know how i love to see my carbon copy Abbah kasan yadda na ke son haihuwa”

“Sai ka ƙara aure ka yi haƙuri har Allah ya baka”

“Abbah kasan na yi aure ba ɗaya ba amman Allah be bani haihuwa ba, taya Allah zai bani haihuwa bayan na yi masa butulci”

STORY CONTINUES BELOW


“Sai ka yi haƙuri”

Abbah na faɗar haka ya aje wayar. Sai Jibril ya miƙe tsaye yana cizon lips ya wulgarda wayar ƙasa iya kar ƙarfinsa, kamar mahaukaci ya fara bugun ginar gurin da duka hannayensa har sai da jini ya fitowa ko wannensu sannan yaja baya yana haƙi.

Zinatu ce ta shigo office ɗin da sauri hankalinta tashe ta doso inda Jibril ya ke.

“Miya same ka haka?”

Zata taɓashi sai ya yi baya yana ɗaga mata ɗayan hannunsa.

“Don’t touch me, na yi ma kaina alƙawarin ba zan sake taɓa wata mace ba sai Nawwara, wata mace kuma ba zata sake taɓa ni sai ita”

Mutuwar tsaye ta yi a gurin ta, kamin ta juyo ta kalli Siraj da ya shigo yanzu.

“Miya faru kuma? Zinatu go and call doctor please”

Kainta kaɗa sannan ta juya ta fice jikinta a sanyaye. Siraj ya nufo Jibril yana faɗin

“Be kamata ka tada hankalinka akan wannan gayen ba”

“You don’t know what Love is you have no idea how i feel so karka faɗa min wannan maganar”

“Ina ƙoƙarin faɗa maka wannan gayen be isa ya ƙwace Nawwara daga hannunka ba har sai idan kai ka so”

“Kasheshi zan yi Siraj babu wanda ya isa ya so Nawwara sai ni kaɗai ne wanda Nawwara zata so sai ni”

Siraj ya kai hannu ya dafa ƙirjinsa.

“Baka buƙatar kashe shi, sai idan kasheshi zaka yi da ranshi babu wanda ya isa ya yi gasa da kai Jibril sai idan ka so”

Wata kujerar da ke gefe Jirbil ya nufa ya zauna yana ta sauke ajiyar zuciya, wani haushi yake ji da baƙincikin da be shaƙe Mustapha ba. 3

*** *** ***

Misalin huɗu da rabi ina zaune tsakar gida ni da Inna muna tattauna abunda ya faru a ɗazu. Kamar daga sama sai muka ji sallamar Zinatu daman na ji tsayar mota a waje sai dai ban ɗauka mai motar nan zata shigo ba.
Na yi mamakin yadda na ganta fuska a sake kamar ba ita, cike da walwala ta gai da Inna sannan ta kai min duka irin na wasa.

“Ke ƴar gari gurinki na zo”

Cike da mamaki na tashi ina dariya na nufi ɗakinmu sai ta biyoni, bayan ta zauna saman katifar mu sai na fita na ɗebo mata ruwa na dire mata gabanta.
Sai ta ɗauke ruwan ta maiyar gefe ta fuskance ni ta ce.

“Nawwara ranar da kika mari Ogan mu, abun ya ban mamaki, abu na biyu kuma ya matsa akan yana son ki dawo aiki wai sai ya mugun wulaƙantaki, shine na ke son na san wace irin gaba ce a tsakaninku har haka duk da yake na ji ya kiraki da matarsa amman abun ya ɗaure min kai”

Murmushi na yi a zuciyata ina cewa ki ce gulma ce ta kawo ki kenan. A fili kuma sai na ce

“Babu wata alaƙa fa, kawai ya taɓa hannuna ne ni kuma bana son yadda maza suke taɓa ni shiyasa na mare shi”

“Amman miyasa ya kira ki matarsa?”

Ido na ƙura mata ina ta tunanin abunda zan ce mata, ban sani ba ko shine ya aikota ko kuma ta zo ta san wani abun ne.

“Shi ya kamata ki yi ma wannan tambayar, ai na yi zaton ke ɗin budurwarce ko ƙanwar da har kika yi unƙurin rama marin da na masa”

Ɗan murmushi ta yi.

“Nawwara kenan, ai ban za ci akwai wata alaƙa tsakaninki da shi ba shiyasa na yi hakan domin be kamata ki mari babban mutun kamar shi ba”

“Gaskiya ne, ke ma be kamata ace kin biyo ƴar talaka har gida kina bugun cikinta ba” 1

Miƙewa ta yi tsaye tana cigaba da murmushi ta dafa ni.

“Anyway daman na zo ne akan na baki shawara akan karki yarda ki koma aikin nan domin kuwa Jibril na shirya wulaƙantaki ba kaɗan ba”

Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleni

“Da ni ce ke ba zan taɓa yarda na haɗa ido da mutumen da ya wulaƙanta ni ba balle har ya kirani kariwa kuma na yarda na kula shi, Wallahi ba ayi irin wannan mijin ba”

“Sai kuma aka yi rashin sa’ah zuciyar Nawwara da ta Zinatu ba iri ɗaya ba ce” 1

“Ai ba zasu taɓa zama ɗaya ba har a bada ni dai shawara ce kawai na baki domin bana son ya cutar da ke”

“Tau na gode Ummu ta gaida Aisha”

Daga haka ta juya ta fice, ni ɗauki ruwan da bata sha ba na fice da su daman na san ba zata sha ba tun da ƙyamarmu take.


MUSTAPHA POV.

Gudu ya ke kamar zai tashi saman ko da ya iso gida kamar baya cikin hayyacinsa saboda ɓacin rai. Shi kansa be san iya adadin horn ɗin da ya yi ba kamin a buɗe masa gate, abunda ya tashi hankalin Hajiya ta fito a firgice tana kallon yadda ya faka mota kamar wani mahaukaci.

“Son what happen to you?”

Ta faɗa tare da nufar inda yake tana kallon fuskarsa hankalinta a tashe.

“Wani ne ya yi min haka saboda Nawwara Mom”

Hannayenta biyu ta kai ta riƙe fuskarsa tana kallon yadda gefen bakinsa ya soma kunbura ga fuskarsa ma tayi ja sosai abunka da mai farar fata.Bayan an gama wanke masa hannun aka bashi wani magani da zai sha, sannan likitan ya ɗauki box ɗinsa ya fice daga office ɗin zuwa chemist ɗin dake kamfanin kasancewar yana aiki a ciki ne. +

“Siraj ka sake aikawa yarinyar da saƙo ko kuma ka kirata”

“Ya kamata mu bata time Jibril, idan har kana son Nawwarar nan ta yi aiki tare da kai kuma ta yarda ta yi aikin dole ne sai ka nuna mata cewar kai ma Namiji ne, rayuwarka ta baya dole sai ta fara aikin a kanta ya yadda zata gamsu aikinne dai kuka yi ba wani abu ba, matuƙar ka ce zaka kwanta ta hau ta takaka zata yi maka abunda baka tsammani kuma daga ƙarshe mu zo bamu samu abunda muke so ba”

Shiru ya yi tana nazarin kalaman Siraj yasan yana da gaskiya wani ɓangaren, a halin yanzu ya san Nawwara ba zata taɓa yarda ta yafe masa kai tsaye ba, kuma taya zata gane ya canja da gaske yana sonta idan har kusance ba idan kuma har be bi shawarar Siraj ba yasan babu kusanci a tsakaninsu domin zata yi ta nesantarsa ne.
Ganin Yadda Jibril ya natsu ya bawa Siraj damar cigaba da bayaninsa.

“I zuwa yanzu ya kamata mu dakata daga tura mata da saƙon neman ta dawo aiki ko kuma kiran da kake mata mu ɗaga mata ƙafa na ɗan wani lokaci”

“Baka san yadda na ke ji ba Siraj idan naji sunan yarinyar nan ji na ke kamar na runtse ido na buɗe na ganta a gabana, Siraj ina neman duk wata hanya da zan nuna mata da gaske na gyaru kuma ina sonta, abu na ƙarshe ba zan bari wannan wawan ya shiga zuciyarta ba”

“Ka yi haƙuri da sannu komai zai wuce, ka bata ɗan lokaci kaɗan, amman fa dole sai ka zama namiji domin ba zai yiyu ta riƙa maka wannan cin kashin ba”

“Idan kuma bata dawo ba fa?”

“Zata dawo na tabbatar zata dawo saboda tana tunanin ɗaukar fansar abunda ka yi mata ta hanyar wulaƙanta a gaban ma’aikanta, ai ta yi na ɗaya ka ƙyaleta dole zata yi ƙoƙarin yin na biyu har zuwa adadin da take ganin zata gallaza maka, idan kuma ba ta dawo ba sai mu bi wata hanyar ta dabam”

Ya saka hannunshi aljihi ya ciro ƙaramin hoto ya miƙawa Jibril.

“Ga wannan Abraham ya bani wai Nawwara ta manta shi lokacin da ta shigo office ɗin nan, ina tunanin yana da muhimmanci sosai a gareta”

Hannu Jibril ya miƙa ya karɓa yana duba, yasan ba Nawwarsa ba ce amman wacce ke cikin hoton tana kamada ita sosai, ajiyar zuciya ya sauke ƙana ya ce.

“Idan har Nawwara ta furta kalmar so gurin wannan yaron ko? Ba makawa kisa ya tabbata akansa” 2

Miƙewa ya yi tsaye ya fice daga office ɗin maganganun Mustapha na ɗazu suna ta masa yawo akai, yanzu kan bashi da babban maƙiyi kamar Mustapha domin duk mai son Nawwara a gurinsa maƙiyinsa ne indai namiji ne.

MUSTAPHA POV.

“Sai yaushe zaka ga ne Nawwara nan ba ajin ka ba ce Son? Dan me zaka bar wani ya yi maka haka akan macen da ko a mafarki be kamata ta zama budurwarka ba balle matarka ba, na je ɗazu na ma mahaifiyarta jan kunne akan karta sake bari ƴarta ta kula ka idan ma wani maganin ne tau ta yi gaggawar karyashi”

Ya janye hannayenta dake fuskarsa ya riƙe yana nuna mata tsantsar damuwa a fuskarsa.

“Haba Mom a maimakon ki taimaka min gurin neman soyayyarta sai kuma ki ɓata abun? Kin ce kina so na miyasa ba zaki so abunda na ke so ba? Wallahi yarinyar nan bata min komai ba, kawai Allah ya ɗauki sonta ne ya ɗora min dan ya jarrabe, dubi ki ga fuskata kin san dalilin da yasa na dawo gida yanzu? Saboda na nuna miki wannan abun ki san ba ni kaɗai na ke son Nawwara ba, kuma ki taimaka min wajen neman yafiyarta da soyayyarta, na je gurin wanda ya siye gidan da suke ciki ne akan ya fansar min amman sai yake nuna min kamar ya fini son Nawwara saboda shi mahaukaci, ni kuma na yi alƙawari ba zan taɓa bari ya auri Nawwara ba, ba zan hanata Nawwara son wanda zuciyarta take ƙauna ba, amman ba zata taɓa zaman aure da wani ba sai ni, saboda ta haka ne kawai zan iya gane cewar ta yafe min” 1

STORY CONTINUES BELOW


Hawaye ya fito a idanuwan Mahaifiyarsa ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallonshi.

“Shikenan sun gama juye min kan yaro, s8n gama da kai Mustapha ba zaka taɓa jin abunda zan faɗa maka ba”

“Ke kuma ba zaki taɓa gane abunda na ke nufi ba…!”

Yana kaiwa nan ya sake mata hannu ya nufi part ɗinsa.

*** *** ***

Bayan na aje ruwan da bata sha, sai tambayarta da kuma abunda ta faɗa min ya dawo min a rai, ya aka yi ta san Jibril ya wulaƙanta har haka? Ko dai shi ya faɗa mata ne? Idan har shi ya faɗa mata wannan yana nufin shi ya turota kenan? Amman taya zai turo ta bani shawara akn karna koma aikin kuma.

“Lafiya kuwa Zinatu ta zo?”

Ya ɗago daga tunanin da na ke na kalli Inna ina ƙirƙiro murmushi tare da nufar inda take zaune na zauna.

“Ba komai ta zo ne akan aikin nan wai yau ban je ba na faɗa mata se gobe shine wai bata son ina wasa da aikin ne”

“Nawwara be kamata ace kina ɓoye min wani abu ba, ni fa mahaifiyarki ce, bana son noƙe-noƙen nan da kike haka kuka yi ke da Habiba har ta Allah ta kasance”

Rumgumata na yi ina murmushi.

“Wallahi Inna maganar aikice ta zo ta bani shawara, babu wani abu kin ji na rantse miki”

Hakan yasa hankalinta ya kwanta, ni kuma na zari Hijabi na nufi gidansu Jidda.
A tsakar gidansu na sameta kwance saman tabarma ta yi rufa da zane da alama bata jindaɗi duk ta rame kamar ba ita ba. Da mahaifiyarta muka fara gaisawa sannan na nufi inda take hankali a tashe, hannu na kai na taɓa jikinta sai na jishi da ɗan ɗumi.

“Tun yaushe ne baki da lafiya?”

“Shekaranjiya, maleria ce ke damuna”

“Allah ya baki lafiya, Wallahi ban sani ba sannu”

Kai ta gyaɗa min sai ta miƙo hannunta ta kama nawa hannu ta jimƙe a sosai ta lumshe ido sai hawaye, a take hankalina ya tashi ji nayi kamar itama tafiya zata yi ta barni ban san lokacin da na fara nawa kukan ba, sai Maman Nura tasa mana dariya wai daman mu ƴan raki ne idan muna ciwo. Ban bar gidan ba sai da na yi sallah magariba a nan, ko da na dawo gida kaina na ta ciwo saboda kuka da na yi a gidansu Jidda.

Da kaina na labartawa Inna rashin lafiyar Jidda, ita ma kanta bata jidaɗi ɓa domin ta san yadda na ke da Jidda kuma ta san irin halin da Jidda take shiga idan bani da lafiya.

“Zata ji sauƙi ai kin san maleria yanzu yadda take ma mutane balle Jidda da rakin tsiya, Allah ya sauwaƙe sai gobe zanje na dubata”

“Amin amman gaaskiya tana jin jiki domin ta rame sosai jikinta kuma da zafi kamar ba a mata allura ba”

“Allah ya bata lafiya, ai malaria yanzu sai an sha allura sosai ake tashi”

Na tashi cikin rashin kuzari na nufi ɗakinmu. Washe gari da wuri na tashi kamar kullum bayan su Sakina sun tafi makaranta ni kuma na shirya cikin wata doguwar rigar yadi na yi ma Inna sallama tare da faɗa mata zanje gurin aikin sannan na saka Hijabi na fice. Gidansu Jidda na nufa dan duba lafiyar jikinta, una tafe ina ta mamakin tun jiya ba mi yi waya da Bilal ba be kirani ba ni kuma ina tsoron kiransa saboda ban saba ba kuma ban san hali da yake ciki ba, sai dai gaskiya a kwana biyu nan da ya saba min da kiran yasa ni jin babu daɗi.

Na yi mamakin ganinta ƙofar gidan tare da Mustapha suna magana duk da ban san mai suke magana akaiba na samu kaina da tsoro sosai saboda sanin wanene Mustapha.
Daga ita har shi ido suka ƙura min ganin irin kallon tuhumar da na ke musu, ba ma kamar shi da natsu guri ɗaya kamar na rikice da ganina.

STORY CONTINUES BELOW


“Kin san waye Mustapha a unguwar nan Jidda karki yarda ya yaudareki”

Na faɗa ina kallon Jidda da idonta ke cike da ƙwalla, shi kuma sai ya yi saurin girgiza kai yana faɗin

“Wallahi ba abunda kike tunani ba ne Nawwara”

Ni kuma na watsa masa wani shegen kallo.

“Mi na ke tunani miye bana tunani? Kasan na san waye kai ka gwadani baka samu ba shine zaka dawo gurin ƙawata? Ko kuma bayan ka gama da ita ne ka dawo kaina?”

“Babu komai a tsakanina da shu Nawwara nan ma ya zo ne saboda ke…”

Cewar Jidda hawaye na mata zuba.

“Saboda ni ko? Ki cigaba da biye masa har ya kaiki ya baro, waya sani ma ko ya lalata miki rayuwa kema”

Ina faɗar haka sai na juyo na kamo hanyar dowowa, zuciyata cike da zargi kala-kala. Sai da na yi nisa sosai na kai bakin titi ina ƙoƙarin tare Napep sai ga Mustapha ya sha gabana da Mota ya fito da sauri ya fuskance ni.

“Wallahi ba abunda zargi ba ne, na canja na Nawwara Wallahi na miki alƙwari ba zan sake yin wani abu marar kyau ba”

“Ka dawwama a cikin abunda kake aikatawa ko kuma ka tuba babu ruwan Nawwara a ciki wannan farincikin iyayenka ne da kuma masoyanka, Kuma dan Allah ka fita daga hanyata mahaifiyarka ma ta yi mana cin mutunci saboda kai tace muna zugaka kana ci mata mutunci akan gida, dan Allah ka ƙyale karka sake jamin wani bala’in gida dai zamu tashi mu bar maka abunda very soon In Shaa Allah”

“Ba ni na siye gidan ba Nawwara, wani ne ya siya sunansa Jibril ya ce shi mijinki ne”

Mamaki ne ya cikani.

“Ina ka ganshi?”

“Malam Haruna ne ya faɗa min na je na sameshi yace shi mijinki ne”

“Daga kai har shi baku da hankali, Kuma na faɗa maka ka fita hanyata” 1

ina kaucewa ya sake shan gabana.

“Nawwara mi zan yi ki yafe min mi zan yi ki yarda da ni? Faɗa min ko minene zan yi Nawwara ki yafe min?”

“Zaka iya dawo min da Habiba?”

“Wanda ya mutu baya dawowa kuma…”

Sai na tari Numfashinsa.

“Tau ba zan taɓa yafe maka ba” 1

Ina faɗar hakan na kauce na cigaba da tafiyata na bar shi nan tsaye yana kallona fuskarsa kamar wanda zai fasa kuka.

Na yi sa’ar samun Napep da wuri, ko da na isa gurin aikin takwas da ƴan mintuna, tun a bakin gate na haɗu da Amina abokiyar aikina, a tare muka ƙarasa ciki muka rubuta suna tare har tana cemin yau kan munyi latti ita tama daina ganina kwana biyu ina wasa da aikina, nikan dariya kawai na yi na ɗauke kai na nufi gurin aje Hijabina sannan na muka shiga ciki tare.

“Khadija Musa Kafinta”

Daf da za mu shiga lifted na ji an kirani sai muka waigo tare, wata ƙabila ce ta kira sunan nawa tana sanye da suit.

“Please Follow me”

Sai da muka haɗa ido da Amina sannan na bita ita kuma ta shiga Lifted, wata lifted muka nufa muka shiga tare sannan ta danna 5 lifted ta rufe muka fara tafiya. Ni dai ban kalli inda take ba itama bata ce da ni Uffan har muka isa sannan ta fita nima na fita muka doshi wani gurin daban.

Ina hango inda na bi shekaranjiya na shiga office ɗin Jibril na yi tunanin kalwaɗowa zata yi mu shiga office ɗin sai naga mun iso wani ƙaton ɗaki mai cike da computers da kuma files.
Muna shigowa sai matar ta juya ta fita wannan abokin nasa ya miƙe tsaye yana ɗaukar documents ɗin dake gabansa ya yi min magana ba tare da ya kalleni ba.

“Congratulations Miss Nawwara, kin samu baban promotion zuwa office ɗin Oga Jibril you’re now his new PA, Rabi zata zo ta miki bayanin komai” 2

Mamaki ne na cikani new pa haka kawai bayan bana da dogon karatu?

“Amman ban yi wani zurfin karatun da za a bani wannan matsayin ba”

Kamar daga sama na ji muryar da nafi tsana a duniyar nan wato muryar Jibril ashe yana bayana ta gurin kujerar da ke farkon shigowa, ni ban ma san da shi ba kasancewar ban kalli gurinba tun da na shigo idona yana kan abokin nasa.

“Shi kuma ga damar baki idan kuma ba zaki yi ba you can leave” 1

Ba yabo ba fallasa ya faɗi haka ya kana ya miƙe tsaye suka fice tare da abokin nasa suka barni nan tsaye ina mamaki.Wata kyakkyawar mace ce ta shigo mai far’ar fuska da kuma ta ruhi domin kuwa muna haɗa ido da ita sai naji kamar na santa, hannu ta miƙa min. +

“Sannu sunana Rabi Ismail”

“Nawwara”

Na faɗa ina miƙa mata nawa hannun.

“Zo muje zan nuna yadda aikin naki yake”

Tana gaba ina biye har muka isa office ɗin Jibril, a gaban computer ta fara isa ta nuna min yadda zan danna na buɗe ƙofar farko ta shigowa, sannan muka ƙarasa ciki ta nuna abubuwan da zan yi da zarar na iso da safe, sai kuma abubuwan da Jibril yake buƙata da kuma tsarin yadda zan jera masa komai.

“Aikinki ne ki sanar da shi idan zai yi meeting kamin lokacin ya cika, da zarar ya shigo da wuri saki sanar shi duka abubuwan da zai yi, wayarsa da ke nan office ke zaki riƙa amsa ta, idan wani na buƙatar ganawa da shi ke zaki tabbatar da tsaro kuma ke saki saka time, yanzu kan ba zaki tashi aiki ba sai 4:00pm, kuma dole ne ki shigo 8:00am, masu kowa ƙorafi ko wani bayani na cikin kamfanin nan ke zaki kula da su shi kuma sai kije ki masa bayani a tsanake, aikinki ne gogewa da kuma gyara ɗakin nan, idan na shigo dole ne zaki tashi ki gaishe kuma ki tambayeshi abunda yake buƙata” 1

Ya juya ta ɗauko wata leda dake saman teburinsa ta miƙa min.

“Wannan kuɗi ne naira dubu ɗari biyar zaki siye tufafin da zaki saka masu kyau saboda Oga baya son ana saka tufafi marar rsada musamman yanzu da kike new PA ɗinsa, wannan kuma makullin gida ne dake Abdullahi Fodio Road a gidan zaki zauna komai akwai a ciki” 1

Na sauke ajiyar zuciya ina kallon makullin data fiddo daga aljihunta tana miƙa min.

“Daman idan mutun ya fara aiki haka kuke masa a wannan kamfanin?”

“A’a Karamci ne kawai irin ya Oga Jibril ina tunanin kina da muhimmanci a gareshi sosai shiyasa”

“Ki bar kuɗin ki aje makullin kuma ki faɗa masa ba zan yi aikin ba” 1

“Amman miyasa?”

Ban bata amsa ba na juyo na yi tafowata zuciyata na ta raya min abubuwa da dama, idan har na yarda na yi aikin nan tau Jibril ya ƙwareni kuma duk wulaƙancin da ya yi ya tashi a banza kenan, taya mutun zai wulaƙanta ni sai kuma na dawo na fara aiki a tare da shi? Ya samu danar wulaƙanta ni saboda kuɗin da yake da su, yanzu kuma sai na yarda ya yi amfani da kuɗin ya maye gurbin abunda ya aikata? Lallai ni wawuya ce.

Haka na ke ta tunanina har na iso reception na ɗauki wata a inda na aje tare da Hijabi na saka na nufi ƙofar fita ba tare da na saka lokacin da na tashi ba. 1

“Nawancy”

Da sauri na juyo jin muryar Bilal, sai na sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake min.

“Ashe kin shigo?”

“Ee amman yanzu zan koma”

“Har kin gama aikin ne?”

“Ee yau baka kirani ba, duk na damu”

Ɗan murmushi ya yi muna fara takawa tare yana faɗa min akwai abunda ya ɗauke masa hankali.

“Amman ko minene ai ya kamata ka min ko da massage ne”

“Haka ne am sorry my dear ba zan sake ba”

Hango Jibril da na yi a tsaye a gate ɗin garden yasa na washe haƙura ina kallon Bilal.

“Ma yafe maka ammam karka yarda ka ƙara”

“Allah ya Huci ran sarauniya ba zan ma sake ba”

Haka mike tafiya tare muna firarmu sai dai yadda na ke dariya sai ka ɗauka wani labarin ban dariya ne yake ba ni.
Muna dosar gate Jibril kuma ya doso cikin kamfanin tare da mutumen da suke magana tare.

STORY CONTINUES BELOW


“Good Morning Sir”

Bilal ya faɗa cikin girmamawa a lokacin da Jibrilya kawo kusa da mu, ni kan ko kallonsa ban yi ba har sai da na ji maganar da ke fitowa daga bakinsa.

“Miye tsakaninka da wannan yarinyar?”

Ƙasa Bilal ya yi da kansa ya kasa amsawa kamar mai tsoro sannan ya buɗe baki xai yi magana sai na yi karaf na karɓe duk da ba ni ya tambaya ba.

“Wanda zan aura ne”

Sai ya juyo kaina ya kalli fuska a ɗaure ya ce

“Bamu gina wannan kamfanin domin masoyaba, idan zaku yi soyayyarku sai ku yi ta a can waje nan kam domin aiki muka ɗaukeku dan haka bama buƙatar ganin wani abu daya alaƙancin soyayya a nan. Ku wuce gurin aikinku” 1

Kallona Bilal ya yi ya sakar min murmushi.

“Sorry Nawancy zan kira ki”

“Okay Dear I love you” 1

“I love you too”

ya mayarmin da martani sannan ya juya ya koma ciki. Ina kallon yadda Jibril ya ɗauke kai ya haɗe yawu da ƙarfi, ya saka hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma ya jimƙeshi sosai.

“Wuce kije office”

“Ba zanyi aikin ba”

Na bashi amsa kai tsaye, sai ya ɗaga kafaɗunaa alamar ko a ajikinsa. Ni kuma na kama hanyar fita daga harabar kamfanin.

Ina cikin Napep kira ya shigo wayata da fari na ɗaukar Jibril duk kasancewar baƙuwar number ce, hakan yasa na ƙi ɗauka, sai dai har na isa gida ba a daina kiran ba da zarar ta tsinke sai a sake kira ni kuma na ƙi na ɗaga. Ko da na shigo Inna na wankin tufafinta na sakawa, da sauri na cire Hijabina na aje na tsuma hannayena cikin wanki ina faɗin ta cire nata.

“Amman dai yau ma kin yi saurin dawowa”

“Na gama aikin ne da wuri”

“Bayan fitarki Ɗansandan nan ya zo be tararda ke ba ya ce zai sake dawowa”

“Ya yi wata magana ne?”

“Cewa Ya yi suna nan suna cigaba da bincike amman yana son ganawa da ke, ya kuma tambayeni akan yadda muka tararda Babanku lokacin da muka je duba shi”

“Uhmm su dai suka sani”

“Wayarki tana ƙara”

“Barta a can kiran bashi da muhimmanci”

Na faɗa ina ɗauraye kayan da ta fara wankewa, a hankali na ji ta kira sunana.

“Nawwara? Kwana biyu nan kin chanja kamar akwai abunda ya ke damunki, ki daina barin damuwa a ranki ki riƙa sanar da ni abunda ya kamata na sani tun wuri”

Na tsayar da abunda na ke na kalleta.

“Babu komai Inna, kawai ina tunanin Noor ne da makomarsa”

“Makomar Noor tana hannun Allah da kuma shi kansa, ki daina damuwa da matsalarsa idan ya girma zai nemi mahaifinsa da kansa ko kuma shi mahaifin nasa ya nemeshi, amman ki daina damuwa arzikinki Noor na mijine ba mace ba”

“Amman ni Inna ina ganin kamar ba zan iya ƙyale Noor yaje gurin mahaifinsa ba, bayan wulaƙancin da ya masa ya yi min sai kuma ace na yarda na bada ɗan gaskiya ba zan iya bari Noor ya kusanci wannan mugun mutumen ba”

“Ko da ya gane kuskurensa ya nemi yafiyarsa? Ba a shiga tsakanin ɗa da uba Nawwara yanzu kin ga duk wannan abun Noor be san da shi ba aiko abun farincikin ki idan har yau Allah ya kawo babansa ya nemi ɗansa da kansa”

Idona ya cika da ƙwalla.

“Amman Inna kamar akwai ƙwaruwa a ciki, ku kuka raini yaron nan sai kuma a ɗauka a miƙawa uban bayan uban be san darajarsa? Gaskiya ni ba zan iya yafe masa ba”

“Ban ce ki yafe masa ba kuma ban ce karki yafe masa ba, amman bashi ɗansa kan dole ne indai har ya buƙaci haka, yara su tashi a gidan iyayensu maza yafi daraja da ƙima fiye da iyaye mata, ke kanki zaki fi jindaɗi na san ba zaki so Noor ya yi agolanci ba, saboda ba ko wane uba ne yake son a kawo masa ɗan wani a gida ba, ba duk miji ba ne zai so ki ya so ƴaƴanki, ni kuma ba burina ki yi ta zama a gida ba bana da natsuwa Nawwara har sai kinyi aure kin zauna ɗakin mijinki”

“Amman ai be zo karɓan ɗansa ba kwata-kwata be taɓa sakashi a ido ba, kuma irin wannan mutumen kike goyon bayan na bashi ɗansa?”

Na faɗa ina kuka, ji nake kamar da gaske rabani za’ayi da ɗana.

“Misali ne kawai na ke baki, ba wai na tabbatar zai zo ba ne, amman zuwansa yana da muhimmanci Nawwara domin zai wanke zargin da mutane suke miki, kuma Noor zai san waye ainahin ubansa na gaskiya”

“Ni gaskiya zan maida Noor gurin Gwaggonsa”

“Wace Gwaggonsa kuma? Zumuntar uwa suka haɗa ko ta uba da zaki ɗauki yaro ki kai mata saboda kawai kin auri yayanta? Faɗa min abunda kike ɓoyewa Nawwara ko shine yake kiranki?” 1

“Ni ma ban sani ba, amman Inna Noor zai iya rayuwa ko babu babansa a kusa da shi ko da ma ace Ubansa ya mutu”

“Allah ya kyau”

“Amin”

Na amsa ina kuka sosai har da mazina. Ban gama wankin ba sai da aka yi azahar, a lokacin su Sakina suka dawo makaranta, Noor da ciwo a ƙafarsa wai yaje buga Boll ya buge da dutse har jini ya fita.
A ranar ba tare da shi suka je Islamiya ba saboda ciwon ƙafan, da suka dawo ne suke labarta mana wai yau sun yi babban baƙo a makarantar su har ya saka gasar karatun sirratul nabiy wacce ta yi ta ɗaya za a bata gida ta biyu kuɗi dubu ɗari biyar ta uku kuma dubu ɗari biyu da hansin, kuma su uku kawai aka zaɓa Sakina sai wasu ƙawayenta biyu. 1

Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta har tana addu’ar Allah yasa Sakina ta ci, ya yinda ni kuma na ke ta tunanin kamar ba gasar Allah da Annabi ba ce. 1

JIBRIL POV.

Shi kansa ya san ya cancanci a yaba masa akan namijin ƙoƙarin da ya yi na ɗauriyar sauraren kalma mai tsada da Nawwara ta furtawa Bilal. Sai dai tun daga lokacin baya jin sukuni har yanzu, kalmar kawai yake ta ji a kunnensa tana masa yawo kamar wanda zai haddace sautinta.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” 1

Shine abunda ya fi furtawa a duk lokacin da yaji abun ya haye masa zuciya. Safa da marwa yake ta yi a ɗakin ya kasa natuwa guri ɗaya.

“Am so so sorry Naj am so so sorry please forgive me”

Ya furta yana janye hannun rigarsa sai ga sunanta shimfiɗe a ɗamtsensa da tattoo, shafa gurin ya shigayi ya lumshe ido sai ga hawaye.

“I love you so much bana son na zama wani kalar mutum Ya Allah help me”

Zaunawa ya yi bakin gado yana ta tunanin abunda zai fissheshi, can ya miƙe tsaye ya saka hannunsa ɗaya ya saka aljihu ya fiddo wayarsa ya danna number Nawwara, haka ya jera mata kira biyar bata ɗaga ba sai ya sake kira na shida ya bar wayar saman madubi ya fita zuwa kitchen ɗan haka wa ƙansa tea.

“Hello Momina tana banɗaki idan ta fito zan faɗa mata” 1

Noor ne yake maganar sannan ya katse kiran jin ba a amsa masa ba, a daidai lokacin Jibril ya dawo ɗakin ɗauke da kofin tea, wayar ya sake ɗauka ya duba sai ya ga anyi picking, da sauri ya sake kira sai aka kashe ya sake kira aka sake kashewa sai kawai ya yanke shawarar aika mata da saƙon karta kwana wato sms.
Da kansa ya tsara rabutun ya tura mata sannan ya jefar da wayar ya miƙe tsaye ya nufi window yana ta kurɓa tea ɗin zuciyarsa na mugun zafi, ji ya yi ba zai iya jurewa ya aje kofin ya nufi wani ɗakin, da shigarsa ya ɗauko wani akwati ya buɗe ya ɗauki ƙwanƙwaƙo ƙarami ya buɗe sai ga cocaine cikin wata farar leda da sauri ya ɓasge ledar ya zuba garin a hannu yana shaƙa kamar ba gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page