RAI BIYU CHAPTER 11

RAI BIYU

CHAPTER 11

A nawa tunani Momy tayi min haka ne tun farko saboda kar na auri ɗanta, yanzu kuma bata son a kashe auren ne saboda dukiyar gidansu Jibril tasan duk wulaƙancin da zai min ni ba ƴarta ba ce saboda haka wannan ba zai taɓa damunta ba, babu wanda zai fi jin zafi jin zafin ɗa kamar uwar da ta haifeshi, ni kaina da Mahaifana ne ce zan iya fahimtar da su kuma su fahimta, amman wannan duk abunda zan yi sai dai su kalleshi a a matsayin butulci. +

Duk da maganar da Daddy ya ce yi ya sai da aka kwashe wata ɗaya har da kwanaki rana ɗaya Momy ta kirani wai na je na shirya yau Jibril zai zo ganina, gabana ya faɗi sosai har na ji ina ma ba zai zo ba har abada domin na san zuwan nasa ba alheri ba ne.

Wanka na sake na saka wasu tufafin kwaliya kan ban yi ba, mai ma dan ya zamin ne jikine yasa na shafa, daman ta saka mai aikinmu ta shirya masa abinci da lemu haɗin gida. Haka na zauna tun sha biyu na rana har magariba be zo ba kuma be kira ba, misalin goma sha na dare Momy ta shigo ɗakina wai na taso gashi can ya zo, Ba musu na tashi na cire kayan bachi dake jikina na ɗauki atamfa na saka da mayafi na saka takalmi na fito jikina a sanyaye na nufi part ɗin baƙi.

Tun a bakin ƙofar falon ƙamshin turarensa ya daki hancina hakan yasa gabana faɗuwa, da sallama na shiga falon amman be amsa min ba sai dai idonsa na kaina har na zauna a kujera na soma miƙo masa gaisuwa a kufile, nan ma be amsa ba, sai wani shan ƙamshin yake ya tsare fuskata da kallo kamar mai neman munina.

“Saboda ke Daddyna yasa na dawo garin nan, saboda ke ya cilasta min dawo wa da aiki a nigeria gaba daya, ke dan Allah ba ki jin kunyar yadda ake ta turaki gurin namiji kamar ni?”

Ɗagowa na yi na kalleshi kallon mamaki da takaici ina ma zai san abunda ke zuciyata da ya taimakamin ya rabu da ni, akwai tsantsan tsoro da fargaba a tare da ni a wacan lokacin shine abunda yake ta cutar da ni sai kuma zurfin ciki da ya zame min hali.

“Zuwanka da rashin zuwanka duka ɗaya ne a gurina, ni dai ina neman izininka zan koma makaranta”

Be ci komai daga abunda Momy tasa aka kawo masa ba, sai ya tashi tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni har jikinsa na shafar nawa ya matso da fuskarsa kusa da tawa ta yadda ni kaɗai zan iya jin abunda zai fito bakinsa sannan ya kalleni ya na ƙara haɗe fuska ya ce.

“Ba aure kika zaɓa ba? Tam zaman aure zaki yi babu ke babu karatu har a bada, ai baki san waye Jibril ba kina da butaƙar sanin wanene tuƙunan”

Yana kaiwa nan ya tashi tsaye na saka hannunsa aljihu ya ciro kuɗi ya watsa min.

“Ga tsiyarki nan”

Ni kuma na miƙe tsaye ina kallonsa na ce

“Tsiyarka dai, tsiyar da ta saka baka ganin kowa da mutunci, na ji ni ƴar talaka ce kuma ni talaka ce amman haka ba zai baka damar ka yi min duk kalar wulaƙancin da ka ga dama ba, kuɗi kawai kake da shi Jibril ni kuma na ɗara ka da tarbiya da biyayya”

Murmushin gefen fuska ya yi ya taɓe baki.

“Fine, zamu gani”

Daga haka ya fice, ni kuma na koma cikin gida ko inda kuɗin suke ban kalla ba, zuciyata cike da ƙuna.

Tun daga wannan lokacin be kuma sake zuwaba sai da aka sake yin wata ɗaya sannan ya kira Momy a waya yana tambayar lafiyata shi ma kuma na san cilasta masa aka yi, bayan ya tambayi Momy aka kawo min wayar sai ya kashe ba tare da ya ce da ni komai ba, a ranar n samu Momy na yi mata bayani akan bana son Jibril kuma bana son zaman aure da shi sai ta muna min na yi haƙuri komai zai wuce da zarar na tare a gidansa, ganin bata goya min bayan rabuwa da shi ba yasa na samu Daddyda kaina na kuka masa halin Jibril da abunda na ke hangowa a zamantakewar auren da zamu yi, amman sai ya bani haƙuri saboda a tunaninsa saboda na daɗe a gidana ne yasa nake wannan tunanin shi ma sai ya kasa fahimta ta, wannan ƙorafin da na kaima yasa ya kira mahaifin Jibril ya yi masa magana akan tarewar mu.

STORY CONTINUES BELOW


A cikin watan nan aka yi kawo lefena kayan masu kyau da tsada, bayan sati ɗaya aka yi walimarta Daddy ya aika da ƙaramar mota aka ɗauko Mama da wasu daga ƴan’uwanta da kuma ƴan’uwan Baba.
Ranar da akayi walimar aka kaini gidansa bayan anyi min huɗuba sosai ciki har da Mama da take ta kukan rabuwa da ni, ni kaina ba zan iya misalta irin kuka da na yi a wannan ranar ba. Tun tara na dare aka kaini gidansa amman abokansa basu shigo da shi ba sai ƙarfe goma sha biyu, su kansu kamar sun sam baya son auren suka mana addu’a suka fice tare da wasu ƙawayena.

Misalin ƙarfe ɗaya na dare ya bar gidan, ban saka shi a ido ba har garin Allah ya waye, haka na kwana na wuni be shigo gidan ba har sai da aka kwana huɗu tsoro duk ya kamani saboda ƙaton gida ne gashi ni kaɗai ke ciki sai ƴan aiki da safe ne kawai ake aiko mana da abinci daga gidan Momy, yau ma da yake rana da huɗu ne ba a kawo ba ni na girka da kaina. Sai a ranar na biyar ya shigo shi ma kuma tare da budurwa Aisha, a gidan suka wuni suka kwana idan yana buƙatar wani abun ko kuma tana buƙata sai ya aiko min da saƙo a waya na tashi na yi musu, ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba zan taɓa nuna masa ina jin zafin abunda yake ba, ba kuma zan taɓa saɓa umarnin iyayena na cewar na yi duk abunda ya saka ni.

Ranar da na gaji da zama gida na fita maƙota, gidan wata matar na shiga wacce gidanta ke kusa da nawa sosai, ba laifi matar tana da son mutane da far’a Cikin ƙanƙanen lokaci muka sabu har ta kai gidan naje gidanta sai dare zan dawo shi ma kuma idan mijinta ya dawo, ita da kanta ta fara fahimtar irin zaman da nake da miji har ta tambaye ni na labarta mata kaɗan sai ta bani shawarwari akan na daina biye masa kuma na nuna wayeta sosai saboda shi yana shiga ƙasashen turawa ne dole idonsa zai buɗe da yawa.

Gaskiya Ummi Faisak na da kirki na koyi abubuwa da dama a gunta ciki har da girki da kuma iya kwalliya, sai dai ban taɓa gwada ko ɗaya ba saboda na san irin mijin da na ke aure.
Wata rana ina gidanta har dare sai gashi ya kira ni na ce masa ina maƙota yanzu zan so, ko da na fito sai na same shi bakin titi yana jiran ƙarasowata shi da wani abokinsa, ina isowa ya wanke min fuska da mari da har sai da na ga wasu ƙananan taurari, har abokinsa ya yi ƙoƙarin riƙeni saboda tangal-tangal da na yi zan faɗi, abun mamaki sai ya fara faɗa da abokinsa kamar zai cinye sa wai taya zai yi ƙoƙarin riƙa masa mata ai ko baya so na yasan zafina na matarsa kar an ya sake masa haka.

A ranar na wuni da zugin marin shi kuma ya wuni yana ta mitar fitar da na yi, hakan yasa ya kulle kitchen kuma ya karɓe wayar da ke hannuna, wai naje gurin matar da nake zuwa ta bani abinci. Daga lokacin kullum da yunwa na ke wuni na kwana sai ya ga dama zai dauko wani abun ya bani jiki na rawa na karɓa na cinye, sai na koma abar tausayi, da na masa laifi kaɗan sai ya dakeni kamar wata ƴarsa, yana yawan shigowa da Aisha ta kwana a gidan ko ta wuni yasa na dafa musu abinci na kai musu ruwan wanka idan sun gama sai naje na ɗauke kwanukan, sai dai duk da haka ko da wasa be taɓa sakewa Aisha fuskar da zata rainani ba baya bari ta sakani aiki ko ta faɗa min wata maganar marar kyau idan ma an wulaƙanta a gidan to shi ne kawai yake da wannan damar.

Wata rana ina zaune falo cikina na kukan yunwa, shi kuma yana ɗaki sai gashi ya fito ya jefo min wayata wai zan yi waya da Mama, sannan ya juya ya fice daga falon.

“Babanki ba lafiya Nawwara, kuma bamu da komai, shine na ce idan da wani abu a hannunki ki aiko mana dan Allah, ko abinci sai mu siya”

Shine abunda Mama ta roƙa ni kuma na ce mata zan aiko mata, bayan na kashe wayar na soma raira kukan da ban san ta inda yake fito min ba, ina haka abokinsa ya shigo hakan ba ƙaramin ɓata ran Jibril ya yi ba saboda ƙananan kayana ne jikina kuma abokin nasa ya ganni, ya yi min masifa sosai har da dukana ya yi akan haka.

Muna cikin wannan halin Daddy ya yi rashin lafiya ya rasu, sai komai ya koma min sabo domin ganin Babu Daddy ya bawa Jibril damar azantar da ni da kalar azabar da yake so, sai dai bayan rasuwar Daddy sai Mahaifinsa ya kira ta wayarsa ya riƙa tambayata ko da wani abun ni dai ban taɓa faɗa masa ba.
lokacin da Ya Jamal zai koma Jos sai ya biyo inda na ke dan mu gaisa, kamar ƙaddara sai ga Jibril ya dawo a ranar na sha duka wai akan me zan shigo masa gida, ya yi faɗa da Ya Jamal sosai har Ya Jamal yake masa faɗa akan yadda ya maidani kamar wata tsohuwa saboda wahala.

Na sha fama a gidan Jibril ga shi baya son Sallah akan lokaci idan kuma na tasheshi sai ya yi ta masifa da ni, wata rana sai kamo tashar musulunci dake cikin receiver wa’azi wani babban malami yake akan irin azabar da ake ma masu wasa da sallah da kuma halin da suke shiga tun nan duniya, da gangan na cika murya dan yaji ashe kuwa saƙon ya isa dan tun daga wannan lokacin be sake wasa da sallah ba, wani lokacin da asuba har tashi na ke na tarar da ya riga ni tashi.

Abun da na lura da shi Jibril yana da rayuwar turawa saboda zama da ya yi a can tun yana da ƙurciya har girma, gaba ɗaya rayuwarsa ta turawace, sai dai a wannan lokacin Jibril ba ya cin goro ma balle taba, rashin ilmin addinin islamiya ne yake ta cutar da shi, idan ina karatun ƙur’ane ya kan natsu yana saurarena musamman da asuba, akwai ranar da ya taɓa tambayata wai waya koya min karatu manyan surori haka na ce makarantar islamiya, daga ranar kuma be ƙara tambaya ba, ni kuma na maida tashar wa’azi ta zamo abar saurarena kullum, sai dai hakan be hana shi zalunta ta ba, be kuma hana shi yin fasiƙanci da Aisha ba, be kuma sanya shi ciyar da ni ba, ni dai iya abunda zan iya shidunsa da shi shine kishi, Jibril yana kishina sosai dan ko abokansa baya bari su gan ni, idan kuma wani ya yi magana da ni ko ya nuna kulawarsa akaina ranar zai wuni yana masifa kamar ya cinye kansa.

Haka na bi na lalace ba ƙarfin yau bare na gobe, wata rana mahaifinsa ya aiko da mota aka ɗauko ni aka kaini gidansa, muka gaisa ya ɗauki wayarsa ya kira Jibril yana zuwa ya fara masa akan yadda ya ga na lalace sai Jibril ya yi tunanin ko na faɗa masa wani abun ne, bayan ya sallame ni da kuɗi mai yawa muka fito ni da Jibril na shiga motarsa muka kama hanyar gida.

Sai da ya tabbatar na yi nisa da gida sannan ya faka motarsa ya fisgoni da ƙarfi ya jefar a gefen titi ya koma cikin motar ya yi tafiyarsa ya bar ni a gurin. Haka na zauna a gurin har aka kira magariba sai da wani mutun ya zo zai wuce ya tsaya ya tambayeni na nemi ya taimaka min ya taimaka ya ɗauko ni a motarsa ya kawoni gida, a ranar sai da Jibril ya mareni kuma ya yi min duka mai kyau. Washe gari sai ga Momy ta zo gidan ta karɓu kuɗin da Daddynsa ya bani, ni dai na roƙeta akan ta raba biyu ta aikawa Baba rabi duk da nasan ba zata yi ba.

Jibril ya kan kirani da ko wane irin suna, idan na yi masa wani abu ba dai’dai ba sai ya ce min annoba ko baƙin maciji, yana yawan faɗar cewar ya fi son mutuwarsa da ni. Tun da ya aureni be taɓa bari naje gida ganin Baba ba, gidan momy kawai na yake kaini shi na kuma da dare yake kaini bayan ƴan mintuna ya ce na taso mu dawo gida.

Ranar da zamuje raka daddynsa zuwa airport ya mareni a bainar jama’a saboda kawai na zubar da ice cream ba da gangan ba, aiko ranar ya sha faɗa a gurin mahaifinsa har sai da ya raina kansa.
Bayan mun dawo gida ya wuce ɗakina na yi kuka har na gode Allah, daga nan bachi ya yi gaba da ni ina cikin bachin na soma jin ana shafani, hakan yasa na farka a firgice ina ihu, sai ya ji haushin ihun da na yi ya mare ni ya riƙa ya jefar ƙasa har sai da kaina ya bugu da madubin gadon, sai kuma ya taso ya doso inda na ke gadan-gadan ya dake fiskgata ya jefa saman gadon.
A ranar Jibril ya maidani cikankiyar mace, da safe ni na taimakawa kaina na shiga banɗaki da kaina na haɗa ruwa na yi wanka sannan na ɗora da alwala na fito a wahalce na yi sallah. +

Da safe be shigo ya tambayi ya na tashi ba duk da yasan halin da ya barni, ban fito daga ɗakin ba sai tara da rabi na safe kai tsaye na nufi kitchen sai na samu ya aje min makaroni da mai da tumatir da sauran kayan da zan sanrafa na dafa makaroni ɗin, cike da tausayin kaina na dafa makaronin ɗin ne na dawo ɗaki ina ta aikin kuka. 4

Haka nake wuni na kwana babu ruwan Jibril da ni a gidan, tun daga ranar kuma be saki kuni da sunan zamantakewar aure ba, idan baya nan gidan Ummu Faisak na ke zuwa na zauna musha fira ta haka nake samu na cika cikina da abincin gidanta, ban taɓa labarta mata irin yadda Jibril yake azabtar da ni ba, sai dai tasan irin zaman da nake a gidan ko da yaushe tana ƙoƙarin koya min abubuwan da zan yi na burge Jibril ko kuma na janyo hankalinsa akaina.

Ranar wata lahadi yana zaune gida na same shi a garden inda yake zaune yana hutuwa na risina har ƙasa na roƙoshi akan ya taimaka ya sake ni, amman ya ƙi har ma ya soma iƙirarin shi yanzu ya fara zama da ni, sai dai ya taimaka min ya ba ni makullin kitchen, daga ranar kullum abinci kala uku na ke girkawa wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ko kallonsa ba ya yi.

Yana zaune falo shi da abokinsa ni kuma na nufi kitchen saboda miyar da na ɗora karta ƙone, ina nufar kitchen ina jin yadda yake faɗawa abokinsa wai Aisha tana da ciki and he’s so happy and excited akan cikin da aka samu babu aure, ina kitchen ɗin na tarar da ni ya shaƙe ni yana tambayar ina Hijabina taya zan fito haka babu mayafi a gaban abokinsa, da kansa yaje ɗakina ya ɗauko min Hijab na saka sannan na wuce ta gaban abokinsa, har abokin yana zolayarsa wai shi yana ganin matan wasu amman shi ba a ganin nasa.
Ma samu sasauci sosai daga lokacin da ya bani makullin kitchen ɗin saboda kullum zan girka na ci, sai dai wata rana sai na gama girkin na ji bana so ko kuma na ji wannan na ke so bana son wannan abu a kaɗan sai amai, nan da nan zazzaɓi ya rufeni haka na kwashe kwana uku ina fama da rashin lafiya kamar zan mutu amman ko da rana ɗaya Jibril be taɓa shigowa ya duba lafiya na ke ba.

Ranar da na samu sa’ida na ɗaure na fito falo saboda na gaji da zaman ɗaki, ranar sai ya shigo ya sameni falo yadda ya ga na rame shi kansa ya bashi tsoro, da kanshi yana zo yana tambayar me ke damuna cikin nuna halin ko in kula saboda kawai na ce be damu ba. 2

Bayan na faɗa masa ya ɗauko min roba ya ce na yi fitsari sai kuma ya ɗibi jinina, ya bani wasu magunguna. Washe gari sai gashi ya dawo cikin gidan a rikice kai tsaye ɗaki na ya nufa.

“Ina kika samu ciki?” 2

Shine abunda ya fara tambayata fuskarsa na nuna tsantsar ɓacin rai da ke tare da shi, ni kuma na ɗago kai a hankali na kalleshi na maida kaina domin bana iya amsa masa.

“Ni ban shirya haihuwa yanzu ba, saboda haka ki san yadda zaki yi da cikin nan, daga yin abu sau ɗaya sai ace ciki ya shiga, zubar da shi zan yi ko kuma ya zama ƙarshen auren mu”

Ni dai uffan ban ce da shi ba ina ta aikin kuka, ban san miya aikata ba bayan kwana biyu ya shigo ɗakina ya bani lemu ina sha hankalina ya ɓace ban farko ba sai da aka kira assalati. A week later ya ɗauki ni zuwa gidan Daddynsa ashe ya kira Baba ni ban ma sani ba sai da muka isa, a falon ya yi min tozarci da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ya tozarta ya yi min ƙazafi a gaban Mahaifina da mahaifinsa ya fiddo wasu hotuna na tsiraici tare da wani ya nuna musu kuma ya yi min ƙazafin cewar na aikata zina da wani a waje kuma da aurensa. 2

Ban iya cewa komai ba sai aikin kuka, har ga Allah ban san inda ya samo wannan hoton ba amman ni dai nasan babu wani namiji da wata mu’amala ta taɓa shiga tsakaninmu sai shi amman ya juya baya ya murje ido ya ce ba nashi ba ne, a ranar na riƙa hannunsa na riƙe shi akan ya karɓi cikin nan sai ya tureni yana faɗin taya zai karɓi cikin da ba nasa ba.

“Ni kan ban haifi ƴar iskaba kuma na san irin tarbiyar da na bawa ƴata”

Shine abunda Baba ya faɗa, Shi kuma ya sakeni saki uku mahaifinsa ya ce idan an saki mace a lokaci ɗaya kamar saki ɗaya ne dan haka ya maida aurensa ya yi haƙuri, sai kawai ya ce ya sani saki ɗaya ya sake ni saki biyu ya sake ni saki uku saboda kawai kar na koma gidansa sai Baba ya kama ni muka fito daga gidan, gidan aurana na koma na ɗauke duk abu na wa mai muhimmanci daga nan kai tsaye muka nufi tashar mota, sai dai ba mu kawo sokoto ba sai washe gari saboda ko da muka taso yamma ta yi sosai a zaria muna kwana, dawowata ta bawa kowa mamaki musamman da aka fahimcin ina da ciki sai aka fara zancen cewar ba aure na je yi ba iskaci naje yi wasu kuma su ce daman haka sai ya faru tun da Baba ya nuna kwaɗayinsa a kan abun duniya, har ma da masu cewa babu makarantar da na tafi. Baba ne yake ta dawainiya da ni shine ci na shana har na haihu da ƙarma ƙarama ya samo aka yanka rago ranar suna, yaro ya ci suna Muhammad Noor.

Bayan na haihu Inna ta ce ya faɗa masa sai azo a auna jininsa da na yaron amman Baba ya ce ba zai yi ba, ai namiji idan ya girma shi zai nemi ubansa, kuma yasan komai daren daɗewa sai Jibril ya dawo gurin ɗansa. Da wannan na zauna a gida ina rainon ɗana har ya cika shekara biyu da wasu watanni, a lokacin ne muka fara sabo da Bilal saboda gaisuwar arziki da take haɗa ni da shi, abotarmu da Jidda kuma ta ƙullu sosai, a gunta na ke jin labarin ai mahaifin Zinatu yana ɗaukar aikin local government har da masu ssce, haka na ɗauki takarduna naje gidansu Zinatu neman ta yi ma Babanta magana akan aikin amman sai ta tsaya tana kallona har ma da zolayata wai ina karatun da aka ce ina yi a waje har tana dariya, daga baya take faɗa min cewar mahaifinta ya ce sai masu degree yake ɗauka.

A hanyata ta dawowa daga gidansu na haɗu da da Faruk, tun daga unguwar yake bina har sai da na iso gida sannan ya yi min magana, ya kuma gabatar min da kansa ni kuma na faɗa masa ko wacece ni ban ɓoye masa komai.
Daga nan sai alaƙa mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninmu har ta kai ga neman aure duk da ban so haka ba Baba da Inna suka buƙaci na aureshi tun da har ya nuna yana son aurena. Faruk mutum ne mai hallaci da kawaici yana so na tsakani da Allah, da kansa ya ce na daina cewa Noor babansa ya mutu saboda na yi masa ƙarya tun farƙo na faɗa masa cewar Baban Noor ya rasu ne, wasu mazan basa yarda mace ta yi aure da ƴaƴan wasu a gidansu amman shi kan ba zaka taɓa gane cewar ba shine ya haifi Noor ba, duk abunda ya kamata uba ya yi ma ɗansa shi yake ma Noor ba dan kuma baya da ƴaƴanba, domin yana da aure har da yara biyar, sai dai yana aiki ne a sokoto amman mutumen kebbi ne, acan yake zaune da duk familynsa, sai ya bar ni nan, ita kuma yana zuwa can inda take a kebbi. Iyayensa basa jindaɗin zama da matarsa irin matan nan da basa ragawa uwar miji da ƴan’uwanta ko kaɗan duk da ba guri ɗaya suke ba, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa ta buƙaci ya maidani kebbi kusa da ita saboda ta yaba da tarbiyata a ɗan zuwan da muke ina gaisheta.

Sai ya tattara ya maida ni a kebbi tare da Noor, su kansu family ɗinsa suna son Noor kamar ɗansa yan’uwansa haka, ga mahaifiyarsa tana mugun so na ni da ɗana saboda ina kyautata mata sosai, ɓari na biyu a gidan Faruk amman Allah be bani haihuwa ba, aiko ranar na ga gata a gurin danginsa da shi kansa kamar su haɗeni saboda tausayi. Muna haka kwatsam labarin mutuwarsa ta same mu sanadiyar haɗarin motar da ya yi a hanyarsa ta zuwa sokoto gurin aikinsa.

A ranar nima sai da na yi kamar zan mutu saboda kuka, a nan gidan na yi taƙaba na gama familynsa suka riƙe Noor kamar yaron da muka haifa saboda sun ga babu yaro a tsakaninmu kuma basa son alaƙarmu ta yanke gashi Noor ya ɗaukesu a matsayin yan’uwan mahaifinsa. Bayan na gama wankan taƙaba na dawo gida. 2

A duk lokacin da suka samu lokaci sukan kirani ko kuma su zo duba Noor, bayan na dawo sai Bilal ya maida Noor kamar abokinsa kullum zai zo gidanmu kiran Noor da wannan alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu muna girmama junanmu sosai ni da shi, sai dai iyayenaa basa son alaƙar da ke tsakaninmu ko ƙaɗan saboda sunan ganin ni bazarawa ce kuma da ɗan da ake zargin shege ne shi kuma saurayi mai mutunci, wannan dalilin yasa na ƙi bashi wata dama da zai nuna min soyayya.

Har kuma tsawon lokacin Momy bata taɓa kirana ba, ni ma kuma ban kira ta ba, Ya Jamal ma sau ɗaya ya taɓa kirana be ƙara ba, Salima ce kawai muke yawan gaisawa akai akai ita kaɗai ta san na haifi Noor kuma na nemi ta min alƙwarin ba zata faɗawa kowa ba, duk da nasan sai ta faɗawa Momy amman Jibril be san yana da ɗa ba da ni ba. 4

BACK TO STORY….

Tuna irin rayuwar da na yi aba ya hanani bachi har garin Allah ya waye. 2

‘Baka cancanci yafiya ba Jibril kuma hanyar da zan rama abunda ka yi min ita ce ta hanyar yin aiki tare da kai kamar yadda ka buƙata’ 10

Shine abunda zuciyata take ta raya min ni kuma ina nanatawa kaina cewar ba zan taɓa yafe masa ba…

YANZU LABARIN ZAI FARA…😄
Bayan ya baro part ɗin Hajiya sai ya dawo ɗakinsa ya zauna saman kujera ransa a jagule ya dafe kansa yana sauke ajiyar zuciya. +

Shi kansa yasan Nawwara ba zata taɓa kula shi ba, yasan ba zata taɓa ƙaunarsa ba, gani yake ya cancanci ko wace irin jarrabawa amman ban da ta son Nawwara, yarinyar da ya wulaƙanta ƙanwarta sai kuma yanzu ya zo ya ce yana son ta.

Miƙewa ya yi tsaye ya nufi gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa, tunani yake abunda zai aikata wanda zai cire masa son Nawwara amman ko sunanta ya tuna sai gabansa ya faɗi.

“Allah na san na aikata laifi mai girma Allah kaine mai yawan gafara mai tausayi Allah ya yafe min, Allah ka musanya min wannan jarabar ta son Nawwara zuwa wata Allah indai wannan ba ita ce ajalina ba”

Shine abunda ya ke faɗa idonsa cike da ƙwalla.

“Son…”

Ya juyo da sauri jin motsin mahaifiyarsa, sai ya zauna gefen gado, ita ta ƙaraso kusa da shi ta zauna ta dafa shi

“Son ka yi haƙuri da abunda Daddynka ya yi maka ka kwantar da hankalinka ka ji?”

“Bana da kwamciyar hankali Mom tun daga lokacin da Allah ya jarrabe ni na zama silar mutuwar wata kuma Allah ya jarrabe ni da son macen da ba zata taɓa so na ba, kullum kuma ina tunanin abunda zai faru da ni gaba, ina jin kamar ajalina yake kusa da ni saboda wannan tunanin da rayuwar da na shiga ba zata taɓa bari na rayuwa mai tsowo ba”

Ta yi saurin rumgume shi tana ƙoƙarin kuka.

“No Son no ka daina zancen mutuwar nan, ka daina saka kanka damuwa akan abunda ba kai ka aikata ba, yarinyar nan ba kai ka akasheta ba su suka kashe ƴarsu so stop blaming yourself, Nawwara kuma ka cireta a ranka ba ta dace da kai ba, so kawai take ta yi amfani da wannan damar ta wulaƙanta ka”

Be damu da hawayen da ke zuba a idonsa ba ya ce.

“Mom Wallahi ba ni na sakawa kaina son yarinyar nan ba, ban san yadda aka yi son ta ya shiga raina ba duk wata hanya da zata cire min son ta nemanta na ke amman na kasa samu”

“Zamu samu Son ka kwantar da hankalinka”

Ya ɗago yana share hawayensa tare da ɗaga mata kai.

“Bari Ikram ta kawo maka abinci ka karya anjima za mu yi magana”

Nan ma kai ya gyaɗa mata, sai ta shafa masa kai cike da so da kuma ƙaunar ɗan ta.

“Allah ya maka albarka”

Ta tashi tayi ta fice, bayan kamar mintuna goma sai ga Ikram ɗauke da kwanonin abinci ta shigo ɗakin da sallama ta aje masa a gabansa.

“Ba zan iya cin abincin nan ba Ikram”

Ya faɗa yana kwantar da kansa saman gadon saboda zazzaɓin da yake jin ya fara taso masa.

“Idan baka ci Mama zata damu”

Cewar Ikram tana buɗe wasu plates, sauƙowa ya yi ƙasa ya zauna ya tsurawa Ikram ido kamar mai karantar abu a fuskarta.

“Ikram zaki iya aurena…?”

Ɗago kai ta yi da sauri ta kalleshi har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta yi shiru ta ɗaga masa kai alamar Ee.

“Amman miyasa Nawwara ba zata iya so na ba”

“Ni da ita akwai banbanci, ni na rayuwa a cikin gidan nan ita kuma ta rayu a gidansu, kana da kyau da isar da kowace mace zata ce tana son ka, sai dai ita a halin yanzu ba soyayyace a gabanta ba, duk macen da aka yaudareta ko aka yaudari wani nata ita ma zata ga kamar wani zai yaudareta ne, babu yadda za ayi Nawwara ta kula balle ma har ya kai ga ta so ka, saboda abunda ka aikata ma ƙanwarta, kullum da wannan abun zata riƙa kallonka ko da kuwa wata mace ka yi ma balle kanwarta.

STORY CONTINUES BELOW


Sannan akwai banbancin tarbiya a tsakanin kai da ita da kuma gata, kaga duk wannan abun da aka aikata iyayenka goyon bayanka suke suna ƙoƙarin nuna maka baka da laifi, i’m sorry to say idan har ka biyesu zasu iya rabaka da Ubangijinka duk da kuwa suna iyayenka, saboda suna kallo kana aikata zina kuma suka ƙyale saboda gudun ɓacin ranka, ƙara ma Momy wata rana tana maka magana amman baka ji, Allah ya ce kar mu kusanci zina balle har mu aikata ta, kai ko ya aikata adadin da baka san iyaka ba, kasancewar nan da muke ɗaki ɗaya ba shi da kyau Ya Mustapha domin idan mace da Namiji suka kasance su kaɗai suka kaɗaice to sheɗan ne na ukunsu, amman wannan be taɓa zuwa a ran Momy ba balle kuma kai da ace hankali ko kuma sha’awarka ta kwaɗaita maka ni da yanzu ka gama da ni kuma ba za ayi komai ba saboda kai ɗan gata ne.

Ka misalta kanka Ya Mustapha da ace kana aikata zina da wannan yarinyar ne Allah ya karɓi ranka mai zaka faɗawa Ubangijinka? Kamar kaina da bawa ka ce karya aikata abu kaza wata rana sai ka sameshi da tsabama Umarninka har ma ya yi maka sata kuma ka kamashi dumu-dumi wane irin hukunci zaka yanke masa?”

Tun da ta fara maganar jikinsa ya yi sanyi hankalinsa ya tashi tun da yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa ya faɗa masa gaskiya kamar Ikram, yana sauraren wa’azi amman be taɓa natsuwa ya yi aiki da shi ba. Hawaye yake hawayen da ke nuna nadama da tashin hankalin da ke fuskarsa.

“Miyasa baki faɗa min wannan ba tuntuni? Da kin tunatar da ni da yanzu ban faɗa wannan halin ba”

“Ko da na faɗa maka zaka faɗa saboda ƙaddaraka ce a haka, kuma a lokacin na san ba zaka saurareni ba saboda ba zaka taɓa ganin munin abunda kake aikatawa ba, ban ga sha’awa ga abincin da zan wanke hannu na ci ba wani yazo hannunsa da datti ya ci wani ma yazo hannunsa da datti yasa ya ci ni kuma na zo na sake saka hannu na ci, sam babu kishi kuma babu imani ga duk mutumen da yake aikata Zina, ban san miye daɗinta ba balle kuma ribarta, saboda yawan mata da kuma yawan wasu ɗabi’u na ɗan adam Allah ya halattawa maza auri mace sama da ɗaya amman kai kaba ma yi auren ba ka faɗa a zina kana neman hallaka kanka, a wannan halin da ka shiga a yanzu ina tunanin shiriyarka ne yazo, dan haka ka yi ta istigifari kana neman Allah ya yafe maka abunda ka aikaka kuma ka yi ma Allah alƙwarin ba zaka taɓa komawa a cikin wacan ƙazamin halin ba, ka yi ta aikata dik wani abin da ka san zai kusantar da kai ga Ubangijinka”

Ya gyaɗa mata kai alamar gamsuwa.

“Amman Nawwara ba zata yafe min ba ko?”

“Zata yafe maka matuƙar kana kyautata mata, kuma kan tuba tuban gaske sai Allah ya dafa maka ta yafe maka har ma ta so ka idan ƙaddarar sonka yana cikin ƙaddararta”

“Idan kuma so na baya cikin ƙaddararta fa?”

A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce.

“Zai iya zama son ka yana cikin tawa ƙaddarar…!”

Da sauri ya miƙe tsaye ya share hawayensa daman tun ba yau ya lura da take-taken Ikram da ke nuna alamar tana son shi.

“Ki ɗauki abincin idan na fita waje zan ci, na gode sosai Sis”

Yana faɗar hakan ya nufi banɗakinsa dake cikin ɗakin, murmushi ta yi murmushin da ke nuna rashin jindaɗinta sannan ta kwashe kayan ta fice.

bayan ya fito wankan ya ɗauki wayarsa ya nemo number Jidda bugu uku ta ɗaga muryar a sake har wani zaƙi take ƙara mata.

“Hello Mustapha”

“Ya kike?”

“Lafiya ƙalau”

“Kina gida?”

“Ee ina gida lafiya?”

“Lafiya ƙalau, kawai ina son ganinki ne akwai wata magana mai muhimmanci da na ke son mu yi da ke idan babu takurawa kuma idan kina free”

STORY CONTINUES BELOW


“Aiko bana free dole zan samu time dominka, faɗa min yaushe zaka zo i mean time?”

“Yanzu nan gani nan har na yi wanka”

“Okay sai ka shigo”

Yana aje wayar ya nufi gurin da tufafinsa suke ya buɗe, cikin ƙanƙanen lokaci ya shirya cikin manyan tufafi riga da wando na shadda, sannan ya fito ya nufi gurin motarsa ya shiga sai ƙofar gidansu Jidda.
Waya ya buga mata sai gata ta fito ba ɓata lokaci fuskarta ɗauke da kwalliya sai ƙamshin turare take kamar sabuwar amarya, motar ta buɗe ta shiga kasancewar be fito ba ne yana daga ciki zaune. Front seat ta zauna tana ƙara miƙa masa gaisuwa ciki kashe murya fuskarta ɗauke da murmushi, bayan sun gaisa ya koro mata da bayanin da ke tafe da shi.

“Jidda ko kin san wanda yake da gidansu Nawwara da suke haya?”

“Ee Malam Haruna ne yana nan gaba da su kaɗan, ya aka yi?”

“Na je gurinta ne sai take zargin ko nine na siye gida na saboda ance an siye gidan”

“Haka nima na ji amman ban san waya siye ba”

“Ai nasan Malam Haruna zan masa magana na ji wanda ya siya sai ya fansar min. Am Jidda ina son ki faɗa min duk wani abu da Nawwara take so da wanda bata so da kuma taimaka min akan duk wani abu da zai ƙara kusancina da ita na san ke zaki iya daboda kinfi kowa saninta”

Ta kalleshi Jiki a sanyaye.

“Saboda me?”

“Saboda ina ƙaunarta son ta na ke Jidda wannan dalilin yasa na ƙulla abota da ke”

Tafiyar daƙiƙu biyar zuwa shida numfashinta ya yi sannan ya dawo jikinta har ta iya jiyo bayanin da Mustapha yake koro mata. Be ɓoye mata komai ba daga irin son da yake yi ma Nawwara da kuma abunda ya aikatawa Habiba, ko da ya ƙarasa bata labarin kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro. Lumshe ido ta yi ta haɗeye yawu sai hawaye suka sauko mata, hawayen da ita kanta ba san na minene ba na tausayin Habiba ko Nawwara ko kuma kanta ko Mustapha, wani baƙon al’amari ya ziyarceta labarin ya zo mata banbaragwai domin Nawwara bata taɓa labarta mata wannan ba, sai dai yanzu ne ta gano dalilin tsanar da Nawwara take yi ma Mustapha. 2

“Please help me…”

Ya faɗa cikin muryar kuka. Sai ta kalleshi tana kukan kamar yadda shi ma yake yi.

“Zan yi tunani akwai, ina da buƙatar natsuwa bana iya banbance komai a yanzu”

Tana faɗar hakan ta buɗe motar ta fita ta shiga gida da sauri tana kuka. Ya kusan minti talatin sannan ya bar ƙofar gidan zuciyarsa na mugun ƙona ya nufi gidan Malam Haruna.

*** ***     ***

Anya zan iya aiki tare da Jibril kuwa? Mutumen da ya wulaƙanta ni zan iya bashi wannan damar ta kusanci da ni?
Yes zaki iya, ga dukan alamu ya gane kuskurensa yanzu kan ya san ƙimarki tun da har zaki maresa a gaban jama’a ya ƙyaleki, yanzu ne ya fi dacewa ki nuna ko wacece ke, yana da kyau yasan ba wacan Nawwarar ba ce this is the time da zaki rana abunda ya yi miki kuma the same time da zaki nunawa Bilal son gaskiya kike masa, kuma idan har ban yi aiki da shi ba na gallaza masa hakan zai bashi damar da zai riƙa bibiya ni da familyna.

Da wannan tunanin na tashi yau ina ta son tsayarda matsaya ɗaya akan na yi ko kar na yi. Su Sakina sun kama hanyar makaranta Inna kuma na bachinta kamar yadda ta fara dabuwa kanta a yanzu da bachin rana, ni kuma na fito na gyara tsakar gidan na yi wanka sai na shirya cikin koriyar atamfata ta roba, jin na yi bana ƙaunar zama gidan dan haka na saka Hijabina na ɗauki wayata na nufi Babban gida daman na kwana biyu ban leƙa ba. 
Ina cikin tafiya wayata ta yi ƙara alamar saƙo, da fari na yi zaton mtn ne ashe Bilal ne ya aiko min da saƙon barka da safiya.

_Morning text does not only mean good morning. It also means, I think about you when I wake up, I love you._

Wani kalar farinciki ne da annashuwa suka nemi inda zuciyata take suka mamayeta, at that time phone ɗin ta nokia @360 ta yi ringing da number nan da aka saba kirana da idan wacce sai na ɗauka sai ayi shiru aƙi magana. Kamar ba zan ɗauka ba sai kuma na daure na ɗauka a tunani na Mustapha ne ashe Jibril.

“Kai wai wane irin shashasha ne? Akan ne zaka riƙa kirana ne wahalalle”

“Dan Allah ki yi haƙuri Wallahi na kira ne kawai na tambaya idan zaki zo aikin saboda na ga baki shigo ba yau”

“So kai ne ko? Daman kai ne kake kirana ka ƙi magana ko?”

“I just want to hear your voice”

Ya faɗa muryarsa a ɗaƙile, ni kuma na ja tsaki na kashe wayar ma gaba ɗaya, saboda ya ɓata min rai. Ban wani daɗe Babban gida ba kasancewar ban tarar da Yakunbo ba domin a ɗakinta na ke shiga na kwanta saboda rashin hayani, mun ɗan yi fira da wasu cousins ɗina mata, sannan na taso na nufo hanyar gida.

Ina shigowa gida na tarar da Inna ta rafka uban tagumi tana kallon ƙofar shigowa, da sauri ma ƙarasa kusa da ita.

“Inna lafiya”

“Mahaifiyar Mustapha ta zo gidan nan ta min cin mutunci, kuma ta gargaɗe ni matuƙar baki ƙyale ɗanta ba sai tasa an ci mana mutunci, har tana iƙirarin wai mun yi ma ɗanta magani mun zugashi yaje ya ci mata mutunci”

Faɗuwa na yi zaune shi ƙenan mu dan muna talaka ba mu da gata kowa ya ɗauko shararsa sai ya juye akan mu wai mai muka yi mutanen nan ne…?

JIBRIL POV.

Lilo yake ta yi  da kujerarsa hannunsa dafe a kai ya lumshe ido, sai shaƙar ragowar cocaine ɗin dake hancinsa ya ke. 
Siraj ne ya turo ƙofar office ɗin ya shigo riƙe da wasu takardu a hannunsa.

“Kana ta takurawa kanka Jibril yarinyar ba zata zo ba, ɗazu fa nan ka kirata amman ta kashe maka waya, akwai mata da yawa fa a garin nan da ma wajen gari be kamata ace kana damun kanka akan ƴar talakawa ba…!”

Da mugun ƙarfi Jibril ya daki teburin dake gabansa har wasu abubuwan suka zube ƙasa, ya kalli Siraj cikin wani irin ɓacin rai ya ce.

“Oh s*** how many times do i have to tell you ka daina faɗin wani abu marar daɗi akan yarinyar nan ne, baka san wacece ita ba ka daina saka bakina a kan maganarta, you’re just my friend so stay where are you”

Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya nufi window yana huci tare da busar da iskar bakinsa. Siraj ya tsorata sosai da yanayin Jibril duk zamansu tare be taɓa masa haka ba sai yau, cikin sanyin jiki ya ce.

“Akwai wanda yake son ganinka”

Ba tare daya juyo ba ya ce.

“Yana da appointment da ni ne? Idan yana da ayi cancelling bana buƙatar ganin kowa a yanzu sai NJ, na faɗa maka idan ma wani abun ne akan aikin nan zaka iya wakiltata”

“This one is important too, ya zo ne akan maganar gidan nan da ka siya na su Nawwara, ni ya kira na faɗa masa inda kake ya zo PA ya hana shi ganinka, so shiyasa ya ƙara kirana ya matsa yana son ganinka”

Da sauri Jibril ya juyo yana kallonshi da idonsa da suka kaɗe sukayi ja.

“Waye shi?”

“Ban sani ba ya ce dai sunanshi Mustapha” 5

“Bar shi ya shigo”

“Ka faɗawa PA ɗinka ya barshi ya shigo domin yana reception yana jira”

Daga haka Siraj ya juya ya fice, Jibril kuma ƴa nufi telephone ɗinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page