RAI BIYU CHAPTER 9

RAI BIYU
CHAPTER 9
Bayan Inna ta amsa sallamar ta je ta ɗauko hijbinta ta saka sannan ta ƙarasa ƙofar gida suka gaisa da shi. Sama-sama na ke jiyo firar da suke har Inna na faɗin Innalillahi, kamar na unƙura na tashi sai kuma wata zuciyar ta ce na zauna tunda maganar manya ce ake ko ma minene idan ta zo ai zanji, sai dai jikina na ta raya min ba abun daɗi ba ne. +

Sun ɗan ɗauki lokaci suna maganar daga bisani na ji muryar Inna tana roƙon a tausaya mana shi kuma yana faɗin babu yadda zaiyi. Bayan sun gama maganar Inna ta dawo cikin gida jikinta a sanyaye fuskarta kuma na nuna alamun damuwa.

“Lafiya Inna miya faru?”

Zama ta yi kusa da ni tana nuna min kuɗin dake hannunta.

“Wai an sai da gidan ya kawo mana ragowar kuɗin hayarmu na wata takwas kuma wai sati ɗaya wanda ya siye gidan ya bamu” 1

Kamar daga sama aka jefo maganar haka na jita cikin kunena, zuciyata ta hau bugawa da hauri na zaro ido hannuna a ƙirji na ce

“Sati ɗaya kuma? Waya siye gidan ne?” 1

“Oho”

Ta faɗa idonta cike da ƙwalla, furucin da na yi na ɗazun ne ya fito da Sakina, Jamila da kuma Noor da gudu suka nufo inda muke zauna suna ta rabon idon da son jin abunda muke tattaunawa.

“Inna miya faru?”

“Tashi zamu yi Sakina an saida gidan”

Inna ta amsata cikin wani irin kalar murya marar daɗi.

“Tau ina zamu koma, waya siye gidan hala?”

Jamila ta tambayi Inna.

“Allah masani”

Dukansu ɓata fuska suka yi da alama suma maganar tashin be musu daɗi ba domin sun saba da unguwar anan haifesu ga ƙawaye da ƴan’uwa kusa da su taya zasu jidaɗin tashin? Idan muka tashi ina zamu koma ? Babban gida ko ina?

“Haya yanzu tsada take ina ma zamuje a bamu ɗaki ban sani ba, babban gida ma idan muka ce zamu zauna babu guri tun da duk sun kame ɗakunan waya ma zai bamu haya da dubu ashirin datara da suka rage mana na ragowar kwanakinmu kai Innalillahi wannan rayuwa daga wannan sai wannan”

Cewar Inna hawaye na zuba a idonta, ni kuma na kalleta na ce

“Ko dai karin kuɗin hayar yake so?”

“Na tambayeshi yace aa shi ai ya riga ya siyar da gidan” 1

Na yi shiru inata nazari wannan wane irin saida gidana ne ba a shigo ciki anga yadda gudan yake ba kawai sai muji labarin an siye shi kuma wai sati ɗaya mu tashi? Lallai wannan daga gani shiri ne, kuma ba zai wuce Mustapha ba shine kawai na ke zargi. 1

“Inna ki kwantar da hankalinki zan koma aiki idan aka biyani kuɗin aikin sai mu haɗa da wannan mu kama wani gidan haya, zan roƙeshi ya yi mana haƙuri har ƙarshen wata zamu tashi mu bar masa gidansa”

Na faɗa ina kallon Inna sai Sakina ta ce

“Ko kuma a faɗawa Ya Bilal”

Na katsa mata tsawa.

“Ke wane irin Bilal kuma Wallahi duk wacce taje cikinku ta faɗa masa sai na ɓata mata rai, haka kawai sai mu ɗauki lalurar duniya mu aza masa, shi ma ai yana da tashi lalurar”

Haka muka wuni gidan shiru-shiru kamar wanɗanda aka yi ma mutuwa duk jikinmu ya yi sanyi, tsoron kwana da muke ji a gidan sai ma ya cire mana saboda hankalinmu ya karkata kan wannan matsalar.
Bayan sallah magariba Inna tace naje Babba gida na faɗa musu halin da ake ciki, ba musu na tashi na ɗauki Hijabin da na cire wanda na yi sallah da shi na saka na kama hannun Jamila muka nufi ƙofar fita.
Abun mamaki muna fitowa muka dami Mustapha a tsaye kamar daman can mu yake jira, kallon kallo muka riƙayi da shi, idonsa narau-narau fuskarsa abun tausayi kamar mai shirin yin kuka, ni ko babu komai a idona sai wuta mai tsananin ci a lokacin da ta ga maƙiyinta.

STORY CONTINUES BELOW


“Guri….guri…gurin.. inna na..zo Daddy ne ya aiko…ni-“

Haka maganar ta riƙa taƙe mishi kamar marar gaskiya, ni kuma abun sai ya bani mamaki kuma ya sakani murmushin takaici.

“Like seriously? Wai Mustapha ko baka san gidansu Habiba ba ne? Baka san ni yayarta ba ce?”

Sai ya amsa min da sauri.

“Na sani! Zan iya rantsewa da Allah ni ban taɓa kula kina cikin unguwar nan ba sai da kika mareni, daga lokacin da kika mareni sai na sa aka min bincike kanki a maimakon na tsargu sai na samu kaina da tausayin halin rayuwar da kuke ciki kuma na yi nadamar abunda na yi ma Habiba kasancewarta ƙanwarki, a lokacin da ta sameni ta bani haƙuri akan karna cutar da ke ina ta shirya abunda zan miki na rama abunda kika min amman sai zuciyata ta hanani saboda tausayinki da take, kin fini kwarjini da ƙima Nawwara kuma ke jaruma ce na gano haka ne daga lokacin da kika ɗaga hannunki kika mareni bayan kuma ba dake nake faɗan ba siya kika yi, wannan ya karantar da ni wani abu a rayuwata lalle ni a idon wasu ba kowa bane tun har mace kamarki zata iya ɗaga hannu ta mareni a bainar jama’a, bayan ko ƴaƴan masu kuɗi basu taɓa unƙurin nuna min ko da yatsa ba balle kuma harara.
Na rasa natsuwata daga lokacin da labarin mutuwar ƴar’uwarki ya same ni, mutuwar Habiba ta canja ni Nawwara, ta tunatar da ni abubuwa da dama da na manta i understand the distance between right and wrong, ta kuma ta sanar da ni abubuwan da ban sani ba a rayuwar duniya, if i begin to tell you how terrible i feel for what I did to your family Nawwara you will find a place in your heart to forgive me, da ace kun sanar da ni tana da ciki da na karɓi cikin kuma na ɗauki nauyin komai na ta, but it too late labarin mutuwarta kawai ya sameni ba a faɗa min dalilin mutuwarta ba amman ni na san cikine saboda ance ta yi zubar jini, Nawwara i’m looking forward to corrected all my mistakes, i made a mistake because I am only human dan Allah Nawwara ki yafe min”

Ta yanayin muryarsa nake fahimtar hawayene suke zuba a idonsa, domin duhu ya sauko bana iya ganin fuskarsa da kyau, sai dai na fahimci hawaye yake kamar yadda nima nake tunawa da ƴar’uwata.

“It’s too early to ask my forgiveness Mustapha, i know you are here to play a game with me too”

“No don’t get me wrong, i know it too early i’m sorry i shouldn’t talk about this, ga wannan ko zaku buƙaci yin wani abu da shi”

Jamila na ganin damin kuɗin da ya miƙo min ta juya da gudu ta koma cikin gida. Ni kuma na yi murmushi ina share hawayena.

“Baka ba kanka dariya ba? Tsayawa kana magana da ni be isa yasa ka ji kunyar kanka ba? What kind of stupid are you Mustapha? What make you think zamu karɓi wani taimako daga gareka? Wannan ne yasa ka turo aka kwashe mana komai kuma ka siye gidan da muke ciki just to humiliate us? Or to force us accept your apology? What kind of person are you?” 1

Na faɗa cikin kuka, har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya yi shiru kamar mai nazari, isowar Inna ce tasa ni saurin share hawayena.

“Lafiya Nawwara?”

“Lafiya ƙalau daman Zakkace aka fitar shine Daddy ya ce a kawo muku”

Shine ya amsata yana miƙa mata kuɗin, ni kuma na yi karaf na ce.

“Karki karɓi kuɗin nan Inna, kuɗin maƙiyinki ne, shine mutumen da ya yi ma Habiba fyaɗe ya yi sanadiyar rabaki da farincikinki kuma shi ya turo mana ƴan fashin nan ya siye gidan da muke ciki saboda kawai mu karɓi taimakonsa…” 1

Mutuwar tsaye Inna tayi na ɗan wasu mintuna sannan taja hannun Jamila da Sakina ta mayar da su cikin gida ni kuma ta ce da ni.

“Nawwara shiga gida”

Ba musu na juya na shige cikin gida sai ta maida ƙofar ta rufe, duk muka yi ɗaki har ita, na yi tsammanin zan ga hawaye ko makamancin haka a idon Inna amman ban ga komai ba muryarta ce kawai take iya karantar da ni damuwarta.

STORY CONTINUES BELOW


“Daman na yi zaton shine ya aiko da ƴan fashin nan, kuma na san babu wanda zai saye wannan gidan sai shi, amman ban taɓa tsamanin shine ya lalata min rayuwara ƴa ba…” 1

Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciyata, daga ni har ita bamu kwana cikin daɗi ba a wannan daren gashi zuciyata na ta saƙa min zuwa gurin aikin ko kuma na haƙura.

*** *** ***

JIBRIL POV.

Jingine yake jikin kujerar dinning hannunsa saman kofin tea yana ta zagaye bakin kofin ya gagara sha, babu abunda yake tunani sai rayuwarsu ta baya da Nawwara.

Yana jin lokacin da take waya da Inna Inna na faɗa mata zata so har Abuja ganinta ita kuma tana ta ɗauki da murna, amman sai ya haya ya nuna mata sam baya son sanin family ta.

“Kina jindaɗi kin auri mai kuɗi ko? So that ki kawo min su a gida ko? Ni ke na aura ba iyayenki ba dan haka bana buƙatar ganin kowa a gidana”

Matsowa ta yi kusa da shi kamar zatayi kuka.

“Jibril ya kamata ka san iyayena suma kuma su sanka, ko lokacin da za ayi aurenmu ƙin zuwa ka yi ka gaishesu, bayan kuma an yi auren sau ɗaya suka taɓa ganinka ba zasu tantance ka ba…”

Tsawa ya katsa mata ya shaƙe wuyanta.

“Na faɗa miki bana buƙatar ganin kowa anan, ba iyayenki ba har abokanki bana da buƙatar ganinn kowa karki kuskura kawo min kowa a nan, annoba kawai…” 2

Tuna wannan yasa shi sauke wani dogon numfashi har yana buɗe baki.

“Taya zan tunkaresu yanzu? Ya Allah help me”

Ya faɗa yana kallon Siraj da ya shigo yanzu riƙe da file a hannunsa.

“An gama komai mum nika masa kuɗin gidansa ya sayar mana ya bamu takardu mun bashi kuɗi kuma mun faɗa masa sati ɗaya muka ba ƴan hayan” 2

“What…?”

Ya ture kofin tea ɗin ya miƙe tsaye.

“Sati ɗaya ya yi nisa Siraj a basu kwana biyu ko uku, miyasa baka da tausayi ne baka san halin da nake ciki ba i can’t live without her” 4

Siraj ya matso kusa da shi ya dafa kafaɗarsa.

“Cool down my friend, Nawwararka ta dawo aiki yau da safen nan” 6

Jibril ya juya baya yana lumshe ido tare da jan sauran cocaine ɗin dake hancinsa.

“Joke apart Siraj”

“i’m not joking, yanzu aka kirani wacce ake aikawa saƙon ta dawo aiki ta dawo amman bata da uniform na ce a bata sabo”

“Oh my God”

Ya furta ya nufi bedroom ɗinsa da sauri yana cire vest ɗin dake jikinsa. Siraj kuma ya bishi da kallo yana taɓe baki.

*** *** ***

MUSTAPHA POV.

Yafi ƙarfin waya ɗaya a tsaye ƙofar gidan bayan Inna ta rufe gidan, sannan ya kama hanyar gidansu yana tafiya da ƙafa kamar yadda ya zo zuciyarsa cike da mamaki, daman sai yanzu Nawwara take faɗawa Inna kenan Habiba Nawwara kawai ta faɗawa bata faɗawa Inna ba.
Ko da ya isa gida jikinsa a mace ko part ɗin mahaifiyarsa be leƙa ba ya yi shigarwasa part ɗinsa, sallah isha’i a cikin ɗakin ya yi ta. Tunani Nawwara ne ya tsaya masa a rai har garin Allah ya waye be bachi be ko zo kusa da idonsa ba balle ya ɗauke shi, be taɓa samun kansa cikin irin wannan halin ba sai a yanzu.

Kamar sallah isha’i itama sallah asuba a cikin ɗakinsa ya yi ta, yana ta roƙon Allah ya yi masa sauƙin abunda yake ji a zuciyarsa. Misalin sha ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta shigo ɗakin sai ya yi saurin juyawa kamar mai bachi. A aladar shi tara na safe yake fitowa su yi breakfast goma ya shirya ya wuce gurin aiki amman yau ga shi har shaɗaya na safe bata ji ɗuriyar ɗanta ba dole ne ta duba tun da taga motarsa ta tabbatar da yana gida.

“Son…”

Ta kira sunansa a hankali tana zama saman gadon kusa da shi. Juyowa ya yi ya kalleta ba tare da ya amsa ba. Jan da idonsa suka yi suka kumbura ya tashi hankalinta sosai, da sauri ta kai hannu ta taɓa kansa.

“Baka da lafiya ne your temperature is so high, miyasa same ka, bari na kira likita” 1

Tana miƙewa tsaye sai ya riƙa hannunta.

“Please tell me Mom ya zakiji idan kika rasa ni?”

“What…?”

Ta dawo ta zauna tana masa wani razanannen kallo, shi kuma ya tashi zaune yana kiran amsarta.

“Zan haukace Son, ƙara dai ni na mutu kai ka rayu, kai kaɗai gareni fa bani da kowa sai kai i can’t afford to lose you, don’t talk about this please, you have no idea how mother could feel if she lose her own child, her happiness, kai kaɗai gareni Son ka daina kawo zancen mutuwa a yanzu”

Razani, tsoro da fargabar da ya ganin a fuskar mahaifiyarsa ta karantar da shi halin da mahaifiyar Habiba take ciki.

“Ba zasu taɓa yafe min ba losing a father, mother, child is unforgettable pain ba zasu taba yafe min ba” 1

Ya furta idonsa na kallon window ɗakinsa. Sai mahaifiyarsa ta kama hannayensa.

“Su wa?”

“Ƴan’uwan Habiba”

“Wace Habiba?”

“The woman i raped”

“When… How”

“Yarinyar da tazo gurinki neman kuɗi kika hanata, ni na yi mata fyaɗe na bata kuɗi and now she’s dead”

Hankalinta ya ƙara tashi.

“Fyaɗen da kayi mata ne silar mutuwarta? Taya?”

“Ciki tayi iyayenta suka je zubar da cikin garin zubar da cikin ta rasu”

Ta yi saurin riƙa fuskarsa dan bata son tashin hankalin ɗanta ko kaɗan.

“That’s the point Son ba kaine silar mutuwarta ba karka matsawa kanka, su sukaje zubar da cikin ƴarsu suka kasheta” 3

“Amman ni ne silar cikin” 1

Shiru ta yi tana ta tunani babu yadda ba tayi ba akan ya daina neman mata amman yaƙi ita kanta abun yana damunta amman gudun ɓachin ransa yasa take ɗaga masa ƙafa ga kuma ubansa da ya tsaya masa kai da fata akan yadda duk yadda yake so a gari ga taka wanda duk ya yi masa ba dai-dai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗora hannayenta saman kafaɗarsa ta ce

“Son kai ne Sila amman idan ka roƙi Allah zai yafe maka, kuma hukunci za a masa sai dai ayi maka mukuncin wanda ya yi zina su kuma iyayenta ayi musu na kisan kai, zan toƙa maka Allah ya yafe maka kuma kaima ka roƙa Allah ya yafe maka”

“Amman Mom su iyayenta ba zasu yafe ba, musamman yayarta Nawwara”

“Idan Allah ya yafe maka ko da su basu yafe maka ba babu komai, kawai ka natsu na daina wannan halayyar” 2

“Na daina Wallahi Mom, amman idan Nawwara bata yafe min ba i will never ever being in peace and happiness, because i love her…” 8

Kamar wacce akayi ma shocking haka ta ɗauke hannayenta daga kafaɗar Mustapha tana kallonsa baki sake.Bayan su Sakina da Jamila sun wuce makaranta ni kuma na shiga gyaran gida, ina tsaka da wanke-wanke wayata ta ringing kamar ba zan ɗaga ba saboda bana son tashin idan ina aiki har sai na kammala, sai kuma na cire kuiya na miƙe tsaye na nufi saman window inda wayar take na ɗauka, Bilal ne ke kira da gangan na tsaya masa yanga har sai da ta kusa tsinkewa sannan na ɗaga cikin muryata mai nuna tsatsan babu ruwana. +

“Assalamu Alaikum”

“Nawancy i’m glad muryarki na fara ji yau da safen nan”

“Baka je aiki ba?”

“Yanzu zan wuce ɗan leƙo waje na ganki”

“Bilal duk na yi datti aiki nake yi”

“Ai nafi son ganinki da dattin kin fi kyau, leƙo mana ke kaɗai nake jira”

Babu yadda na iya dole na amsa masa da tau na ɗauki Hijabi na saka na leƙa waje da fuskata a she yana nan daf da ƙofar gidan jikingine yana jiran fitowata.
Murmushi na sakar masa ina kallon yadda suit ɗin jikinsa ya karɓesa ya fito da kyausa chocolate skin ɗinsa sai shining take kamar wani sabon ango. Shi ma murmushin yake min yana nuna min wani bafulatani dake tsaye da jarkokin ruwa a wheelbarrow.

“Ragowar ruwan da aka zuba mana a cikin gidane Mama ta ce a kawo muku”

“Na gode sosai Allah ya saka da alheri”

“Amin”

Ya faɗa ni kuma na juya da nufin komawa cikin gidan domin nunawa mai amalanken inda zai zuba ruwan, sai kawai na ji Bilal ya kirani.

“Nawancy”

Ina juyowa sai kawai ya kanne min ido ɗaya sannan ya kama gabansa yana tafiya kamar ba shi ba.
Nikan dariya ma abun ya bani wani lokacin Bilal yana min abu kamar wani ƙaramin yaro, hakan kuma ba ƙaramin ƙara min son kasancewa da shi nake ba. Komai na cikin gidanmu sai da aka ciki har muka bada sauran jarka biyu maƙota kasancewar ruwan ya yi mana yawa, hakan ne ya tabbatar min da cewar ba Mahaifiyarsa ce ta siye ruwan ba shine dai ya siya ya yi mata kamfen, taya ma zata siya mana ruwa haka kawai. 1

Bayan mai ruwan ya gama juyewa na koma na cigaba da wanke-wankena zuciyata na ta shauƙin begen Bilal, alƙairinsa nake ta tunawa da kuma irin son da yake yi ma Noor da kulawar da yake bamu, lallai idan har rayuwarsa zata kasance a haka har abada to kuwa matarsa ta yi dacen mijin da zai taimaka mata ta tashiga aljanna, domin ni kan nasan ba ajina bane domin babu yadda za’ayi mahaifiyarsa ta barshi ya auri bayan ta yi iƙirarin wayo kawai nake masa wai na yi aure har biyu kuma da yaro kuma na ce zan auri ɗanta shi da yake saurayi ƴan uwansa ma basa so mahaifinsa ne kawai be ce komai ba shi ma kuma ina tunanin baya ra’ayin haka.

‘Amman tun da shi yana son ki ina ruwanki? Ai da shi zaki zauna ba da iyayenshi ba’

Wata zuciyar ta tambayeni, har ga Allah idan har na ƙi auren Bilal saboda iyayensa zai iya ɗaukar na yi masa butulci ne kawai domin shi baya la’akari da wannan shi di kullum maganar ɗaya ai shi dai yana so na, na san ko da na aureshi ba zai taɓa bari kowa ya wulaƙantani ba kuma zai maida Noor kamar ɗansa.

Haka nake ta saƙe-saƙe na ina aikin har na gama na shiga wanka na fito ina ta tunanin alfanun auren Bilal domin ni dai har yau ban hango wata illa auren Bilal ba idan har iyayensa zasu amince ya aureni ɗin, sai dai kawai na shirya fuskarta familynsa masu uban yawa da cecekuce.

Abaya na saka na ɗauki ɗankwalin abayar na yafa akai na, na saka baƙaƙen talkami sai dai fuskata bata da wata kwalliya domin ko hoda ban shafa ba bayan man da shafa, na ɗauki jar jakata na saka wayata a ciki na nufi ɗakin Inna, ina shiga sai na sameta har yanzu tana bachi, daman na san za a rina tunda jiya ta raya dare da tunanin Habiba a duk lokacin da na farko zaune na ke ganinta saman carpet ta rafka tagumi nasan wannan ba zai rasa nasaba da maganar da na faɗa mata ba jiya lokacin da Mustapha ya zo. Tashin na ta ya zame min dole ne domin bana son na je aiki ba tare da ta sani ba, dan haka na taɓata a hankali na tasheta har ta buɗe ido sannan na faɗa mata zan tafi, addu’a tayi min da fatan nasara ni kuma na fice ina amsawa da Amin.

STORY CONTINUES BELOW


Kamar ni ake jiran an fito sai na samu motar kamfaninsu Jibril a tsaye direban yana neman yaron da zai aika, yana ganina ya yi saurin fitowa cikin ladabi ya miƙa min wasiƙar ni kuma na karɓa ina wani shu’umin murmushi na yi sighing sannan ya wuce ni kuma na jefa takardar a jakata na kama hanyar zuwa gurin aikin.

Ko da na isa bakin gate ɗin kamfanin, ƙarfe tara ta yi har da rabi, da fari guards ɗin dake bakin gate ɗin sun tareni a da na nuna musu id cart ɗina da ya rage ban ƙone ba a cikin kayan aikim kamfanin sai suka bani dama na shiga bayan sun tambayeni dalilin saka Uniform ɗin sai nan faɗa musu uniform ɗin ya ƙone ne, da na shiga kamfanin sai na nufi gurin da aka tanada domin aje wasu abubuwan da mutun yake shigowa da su wato wani ɗan katon cabinets ne da aka tana domin ma’aikatan gurin su riƙa aje komai na su idan sun rufe sai su tafi ta makullin. Wayata da jakata na aje bayan na kulle na nufi reception na rubuta sunana da kuma lokacin da na shigo sannan na yi musu complain ɗin bana da uniform sai suka ce na wuce kawai.
Da kunnena na ji lokacin da ɗayan yake sanar da zuwana a telephone da halshen nasara wato turanci.

Yadda na tarar da gurin ya tabbatar min da wata ta fanshe a aikin, domin alamu sun nuna wata ta yi mopping ɗin kamin zuwana. Amman hakan be dame ni ba na ɓa ɗaure mayafin abayata a kaina na ɗauki bokiti da mop na fara aikina mutane dake ta kai kawo a gurin na ta kallona domin sun san an yi mopping ɗin gurin ni kima na zo ina ƙara yi.
Irin ƙamshin turaren da naji lokacin da muka zo tare Bilal irinsa na ƙara ji a wannan karon, ƙamshin turaren dana tsana a duniya wanda ke haddasa min ciwon kai a duk lokacin da na jishi.
Ko da wasa ban yarda na juya ta baya da nufin ganin mai ƙamshin ba, duk da jikina ya bani akwai mutun tsaye a bayana. Mutane dake gurin da waɗanda zirga-zirga na ga duk sun fice ɗaga gurin kamar ƙyabtawar ido wata ƙila da kai ya yi musu magana da su fita domin ni ban ji kalma ko ɗaya ba, kawai dai na hango yadda duk suke shiga natsuwarsu daga bisani kuma naga sun tashi sun fice da sauri kamar wanɗanda aka kora.

Hakan yasa na juyo sai idanuwana suka sauka cikin nasa, hakan yasa ni haɗe fuska kamar baƙin hadari, na wulgarda abunda ke hannuna na nufi ƙofar fita, sai ya biyoni da sauri yana kiran sunana. Juyowa na yi a fusace ina jiran jin dalilin kiran sunan, shi kuma ya gagara cewa komai bakinsa sai rawa yake idonsa na yawo saman fuskata. Ganin ba shi da abun cewa yasa na juya na cigaba da tafiya lifted na nufa shi kuma yana biye da ni sai kiran sunana yake mutane dake gurin kowa yaja baya ganin ya nufo lifted waɗanda suke cikin office’s kuma na kallonmu kasancewar duk office’s ɗin glass door ne na ciki yana hango na waje kamar yadda na waje zai iya hango na ciki, kallon mamaki suke ganin yadda ya biyoni yana kirana ni kuma naƙi na tsaya.

Daf da zan shiga Lifted ya miƙa hannunsa ya riƙoni.

“Nawwara ki saurare ni mana….!”

Tassss na yi ƙarfin halin wanke masa fuska da mari mai kyau, har sai da ya lumshe ido, komai da ke hawa na uku sai da ya tsaya kasancewar ma’aikatan dake aikin gurin suka ɗauke hannayensa masu tafiya kuma suka tsaya cak suna kallon ikon Allah. 3

“Karka sake kuskuren kai Hannunka ka taɓa min jiki, ka ɗauka nima kamar sauran ƴan matanka nake ko? Karuwai masu binka? To ni ba ƴar iska ba ce kar hannunka ya sake taɓa jikina shashasha kawai”

Har lokacin da nake masa wannan furucin be buɗe ido ba, ni kuma ban fasa faɗa masa abunda nake so ba, a gurin baka jin ƙarar komai sai na muryata da kuma sautin takun talkamin Zinatu wacce ta doso inda muke rai a ɓace, tana ƙarasowa kusa da mu ta ware hannu zata rama marin da na yi ma Jibril sai ya yi saurin buɗe ido ya yi karaf ya riƙe mata hannu.

“Don’t…”

Ya faɗa cikin muryarsa dake amsa amo biyu. Cike da tsananin mamaki Zinatu ta kalleni da kalleshi ta ce.

“Baka ga abunda ta yi maka ba?”

“She’s My wife….”

Ya faɗa rinannun idanuwansa da suka kaɗe suka yi ja suna kaina, ni kuma na yi murmushin takaici na tattara yawun bakina na tofa masa a fuska.

“Tuuff Allah ya tsare Nawwara da zama matar Jibril, matar da ka kira da annoba yau ita kake kira da matarka? Matar da kace ganin baƙin maciji ya fi maka ganinta, matar da ka ce baka ƙauna bata dace da kai ba yau ita kake kira da matarka? Matar da ka wulaƙanta ka fifita karuwa akanta? Matar da ka kira mashiririciya ƴar talakawa ita kake kira da matarka? Matar daka zalumta ka dannewa haƙƙi ita kake kira da matar da baka son abokanka su ganta yau ita kake kira..”

“Enough….!”

Ban ƙarasa ba ya katsa min tsawa idonsa cike da ƙwalla wasu kuma sun ganganro zuwa kumatunsa. A maimakon na yi shiru sai hakan ya bani damar cigaba har ma da nuna shi da yatsa.

“Ba irin da bane Jibril, Nawwara da ka sani a baya ba ita ba ce a yanzu, tirr da kai Jibril, tirr da haihuwar ɗa irinka, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata, azzalumi macuci maha’inci, wanda be san komai ba sai zalinci da cin amana” 1

Hawaye nake ina faɗin wannan maganar kamar yadda shi ma yake hawaye kamar ba gobe, a ada ne na faɗa masa wannan maganar dukana zai yi har sai na faɗi uban da ya aikoni, amman abun mamaki sai ya faɗi saman gwuiyoyinsa ya fashe da kuka yana ƙoƙarin riƙa ƙafafuna abunda ya bawa kowa na gurin mamaki.

“Ki yi haƙƙuri Nawwara dan Allah ki yafe min…”

Da gaske hawaye yake kamar yadda nima nake hawaye na tsanarsa da kuma tuna irin zalumcin da ya yi min. Mutume nan ne ya shigo wanda ya taɓa shigowa a wacan lokaci da nake cikin office ɗinsa, shi ne ya yi ma duka ma’aikatan dake gurin magana suka fice da sauri ciki har da Zinatu da jikinta ya gama yin sanyi da mamaki.
Sai kuma rage daga ni sai Jibril sai kuma wannan mutumen, baya baya nayi sai Jibril ya matso da sauri ya rumgume min ƙafafu yana kuka kamar ba shi ba.

“I’m sorry Nawwara i’m so sorry”

“Haƙuri kake bani da gaske ko Jibril?”

Ya yi saurin ɗago kansa yana gyaɗa min kai a tunaninsa zan haƙura ne.

“Waya faɗa maka zan yafe maka? Miyasa zaka yaudari zuciyarka da abunda ba zai taɓa zuwa maka ba? Nawwara will never ever ever forgive Jibril for what he did to her, indai har wannan ne yasa ka riƙa aikamin wasiƙar aiki to ka daina wahalar da kanka”

Ya yi saurin miƙewa tsaye ya riƙa fuska yana girgiza min kai.

“No no no ba haka ba ne Nawwara i just want be close to you i need..”

“Close to epidemic? Close to black snake…”

Ya yi saurin rufe min baki yana kuka kamar ƙaramin yaro.

“Nawwara please…”

Hannu nasa na janye hannunsa ɗaga baki na ce

“Na tsaneka Jibril na tsani duk wani masoyinka, na tsani farincikinka kukanka shine farincikina na tsaneka Allah ya wandaranka”

Na juya cikin kuka na danna lifted ta buɗe na shiga, ina jin yadda yake ƙoƙarin riƙoni abokinsa ya hanashi. Ko da na fito reception kowa kallona yake nasan baya rasa nasaba da hawayen dake zuba a idona. Gurin dana aje jakata na nufa na ɗauka ina hawaye na fice.A hankali ya yi parking ya fito daga motar kamar marar lakka ya nufi part ɗin mahaifiyarshi.
Tana hakimce saman kujeara ya shigo jiki ba ƙarfi kamar marar lafiya, gaba ɗaya sai ta tattara hankalinta ta maida gunsa tana kallonsa har ya zauna a kujerar dake gefenta na dama. +

“Son na yi ta kiran wayarka kashe, tun da ka fita baka dawo gida ba sai yanzu hankalina duk ya tashi, kuma ka kashe duka wayoyinka”

“Ina Office”

Ya amsa mata cikin muryar dake nuna tsantsar damuwarsa. Tashi tayi takoma kusa da shi ta zauna tana ɗaga bayansa.

“Duk tsawon lokacin nan kana office? Haba son miyasa zaka riƙa wahalar da kanka kana damuwa ga abunda har ga Allah baka da laifi? Bafa kai ka kashe yarinyar nan ba dan mai zaka damu kanka su suka kashe ƴarsu da kan su” 2

Juyowa ya yi ya kalleta.

“Momi ke kika siye gidansu Nawwara?”

“What why would i?”

“Lokacin da naje gidansu Nawwara ta yi wani furuci da ke nuna an siye gidansu kuma an basu kwanaki kaɗan su tashi ke ce ko Momi?”

“Wato Mustapha har gidansu yarinyar nan kake zuwa fira? Yarinyar da basu da tarbiya ga shegen hassada ya yi musu yawa, dan Allah ka cire yarinyar nan a ranka Wallahi ba ajinka ba ce” 2

“Da ace ni na sakawa kaina son ta da na cire shi cikin sauƙi ba tare da kanki kin sani ba, na yi iya ƙoƙarina na ganin cewar na gujewa soyayyarta amman sai na kasa, babu yadda za’ayi na sakawa kaina ƙaunarta Momi Allah ne ya saka min” 2

Ya miƙe tsaye ya zuba hannayensa a ajihu.

“Please Mom ki maida musu da gidansu, kuma karki sake yin wani abu da zai takurawa rayuwarsu, idan har baki tayani neman yafiyarsu ba to be kamata ki ƙara ɓata min suna a gurinsu ba” 2

Yana kaiwa nan ya nufi ƙofar fita cikin yanayi marar daɗi, Hajiya ma miƙewa ta yi tsaye ta bishi da kallo har ya fice sannan ta ce

“Wato revenge ɗin da zata ɗauka ta haɗa ni da ɗana ko? Uhmm Wallahi Nawwara kin deɓo ruwan dafa kanki, duk kika ce zaki shiga tsakanina da ɗana bake ba kaf ɗanginku sai na hana musu zama lafiya, kuma Wallahi ɗana ba zai taɓa aurenki ba ƴar matsiyata kawai” 6

faɗa take tana huci tsabar jin zafin ɗanta ya kamu da son Nawwara. Ɗakin ta nufi tana da bala’i har su Zarah da Ikram suka fito ɗaga ɗakinsu jinyo muryarta tana matsifa. 5

***  ***      ***
Around eight am kowa ya hallara a dinning ɗin cin abincin safe ban da Mustapha, hakan be damu Hajiya ba domin ta san halin da ɗanta yake ciki, sai kawai ta cigaba da jera kayan abincin tare da su Ikram da kuma Ma’u mai aikinta. Fitowar Alhaji ne yasa Zara dake ɗaki fitowa domin yin breakfast ɗin, ganin babu kowa a kujerar Mustapha yasa Alhaji ya kalli uwargidansa ya ce

“Yau ma ba zai yi breakfast ɗin ba?”

Ikram ta yi karaf ta ce

“Ai daman sai tara yake karyawa”

Hajiya kuma ta taɓe baki tana cigaba da haɗawa Mijinta tea ta ce

“Ai ina ganin tsakanin jiya da yau in ban da ruwa babu abunda Mustapha ya ci, ko jiya be fita aiki ba sai sha biyu na rana be dawo gida ba sai da isha’i”

Kallon rashin fahimta Alhaji ya yi mata yana ɗaukar tea da ta aje masa ya kurɓa

“Saboda mai?”

“Uhmm saboda yarinyar nan mana”

Wani dogon tsaki Alhaji yaja ya kalli Ikram a fusace ya ce

“Jeki kira min shi wannan ai iskancin banza ne”

STORY CONTINUES BELOW


Da sauri Ikram ta tashi ta nufi ƙofar fita, bata ɗauki dogon lokaci ba sai gata ta dawo falon tare da Mustapha dake cikin shigar kayan bachi.

“Good morning Dad”

Ya faɗa murya can ƙasa-ƙasa kamar wanda baya son magana.

“Seat”

Alhaji ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar da ya yi masa ba, ba musu Musyapha yaja kujera ya zauna yana fuskarta Daddynsa, mahaifiyarsa taja kujerarta ta zauna tana kallon ɗanta a natse Alhaji ya fara magana ta yadda ɗan nasa zai fahimta.

“Mustapha ka daina damunka kanka nayi imani har ga Allah baka da laifi akan wannan lamarin, saboda ba kai ka kasheta ba iyayenta ne silar mutuwarta. And a part from her sister ka aje shi a gafe domin ba tsararka ba ce, idan ma aure kake so ka nemo ko ƴar wani gidace ni zan aura maka ita amman ba dai wannan yarinyar ba” 2

Sauke idonsa ya yi ya kalli tea ɗin da Ikram ta aje masa a gabansa sannan ya sake data kai ya kalli mahaifinsa ya ce

“Dady ita kaɗai ce macce da nake so”

“No Look Son yarinyar nan ba ƴar gidan mutunci ba ce sannan aurenta biyu fa kai kana sauranyinka ka ce zaka aureta, after that yaron dake hannunta yanzu ana zargin shege ne fa bashi da uba, wasu ma na cewa babu wani aure da tayi zaman banza ta yi abuja ta dawo da ciki sai wannan auren da ta yi na biyu, ba ƴar gidan tarbiya ba ce Mustapha ƙara ka auro ƴar mutunci kuma ƴar gidan mutunci” 2

Mahaifiyarsa ya kalla domin yasan ita kaɗai ce zata iya faɗawa Daddynsa wannan maganar, kallon mahaifinsa ya sake yi

“Amman ina fatar Momi ta faɗa maka ni na lalata ƙanwarta ko?”

Alhaji ya yi saurin girgiza kai.

“No no son ba kai ka ɓata ta ba, daman can yarinyar lalatacciya ce, mahaifinta ma ance sata ya yi da aka mashi aka masa shegen duka har ya mutu….” 2

Zarah dake aikin tsire baki tayi karaf ta ce.

“Wallahi sam yaran gidan nan basa da mutunci ko kaɗan”

Tsawa Mustapha ya katsa mata.

“Idan ana maganar tsakanin Uba da ɗa ki daina saka bakinki a ciki”

Momi ma ta katsa masa tsawa.

“Ta daina saka bakinta iya ba ƴar’uwarka ba ce? Wai mi yake damunka ne Mustapha?”

“Nima ban sani ba, kawai ni dai abunda na sani zuciyata na son Nawwara” 2

Ya amsa mata da cikakiyar gaskiyarsa, shi kansa a yanzu ba zai iya ayyana abunda yake damunsa ba, kawai dai yana samun kansa cikin wani kalar yanayi da be taɓa samun kansa a cikinsa ba. Alhaji ya buga tebur ɗin da ƙarfi

“Ba zaka aureta ba Mustapha, ana nuna maka hanya kana ba haka ba, ka bar ganin kai kaɗai na haifa zan iya shafe labarinka a doron ƙasa matuƙar ka zaɓi yarinyar can ƴar nasara mutunci”

Miƙewa ya yi tsaye ya nufi ƙofar fita ba tare da wata kalmar ta ƙara fitowa daga bakinsa ba.

“Could you see this?”

“Na gani, ni gani nake kamar ba banza suka barshi ba, dan ni ban taɓa ganin yarimyar da Mustapha ya zo ya ce min yana so ba duk wanda na gansu tare zai ce abokiyar aikinsa ce ko  abokiyarsa, amman be taɓa buɗe baki ya ce min ga wacce yake so ba sai wannan zagalar, duk yabi ya canja saboda wata ƴar iskar yarinya, jiya ma haka ta zugoshi yazo ya rufeni da masifa wai na siye gidansu, ni kuma ban san na siye wani gida ba wata ƙila so take ya ɗauki maƙudan kuɗi ya ɗanka mata”

“Bari ai zamu saka ƙafar wando ɗaya da shi”

“Da shi kuma? Sai dai da su ai su suka susuta naka yaro, shi kaɗai fa Allah ya bamu idan ka saka ƙafar wando ɗaya da shi ai abun akan mu zai koma”

STORY CONTINUES BELOW


Ƙwafa ya yi ya cigaba da shan tea ɗinsa yana ta huci.

***         ***          ***

JIBRIL POV.

Be bar kamfanin ba sai tara na dare, ko da ya isa gida jikinsa da mugun nauyi kamar wanda ya yi wani aiki, bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower ya lumshe ido yana sauraren yadda tsanyin ruwa ke ratsa jikinsa. 1

‘Nawwara will never ever ever forgive Jibril for what he did to her’

Shine abunda ke ta masa yawo a cikin kai, zuciyarsa na wani irin zafin, sai goma har da kwata sannan na bar bathroom ɗin cikin yanayi marar daɗi. 
  Vest ya saka da ɗan guntun wando, be shafa mai ba amman ya shafa turare, sannan ya fito parlour ya haɗa ma kansa tea ya zauna saman cushion yana kallon hoton nawwara Tea ma sai ya gagara sha. Yana zaune gurin har shaɗayan dare ta buga be ko motsa daga inda yake ba. Siraj ne ya turo ƙofar falon ya shigo hannunsa riƙe da takardu masu yawa, ɗakin karatun Jibril ya nufa ya aje takardun sannan ya dawo ya zauna kusa da shi yana faɗin.

“Gaskiya yau Jibril ka bani mamaki, wai su waye iyayen yarinyar nan ne da har zata wulaƙanta a gaban jama’a ka ƙyaleta?” 1

Sai a yanxu ya gincira saman kujerar yana cigaba da kallon hoton Nawwara.

“Maruƙar haka zai sa ta yafe min, zan jure har sai ta yarda da na yi nadama kuma na tuba”

“Wannan ba revenge ba ne, it’s an embarrassment, ko ma mi kayi mata baka cancanci ta yi maka wannan tuzarcin ba, su fa mata ba a ƙyalesu hakan ya bata damar cigaba ne, gaba ɗaya yau ak kamfanin nan kai aka wuni ana magana wannan ai tozarci ne”

Murmushi Jibril ya yi ya kalli Siraj ya ce.

“Data mareni a gaban mutane na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta airport, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a gaban iyayena, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a bakin titi na jefar da ita na yi tafiyata, at least now na san yadda mutun yake ji idan aka disgashi gaban jama’a”

Siraj ya juyo yana fuskarta shi da kyau ya ce.

“Kana da banbanci da kowa Jibril be kamata ka auna kanka da sauran jama’a ba, weather you like or not abunda yarinyar nan ta yi maka bata kyauta ba”

Miƙewa Jibril ya yi tsaye ya nufi window falon yana faɗin.

“You’re my new tight friend Siraj, bana son kana faɗar wata kalma marar daɗi a kan nawwara, saboda hakan zai sa na tsane ka ita kuma na ƙara ƙaunarta, zan iya jure ko wani kalar wulaƙanci daga Nawwara matuƙar hakan zai sa ta yafe min, soyayyata da ta rasa a can baya ita nake son nuna mata a yanzu, kulawar da na gagara bata a da, ita na ke son bata a yanzu.

Na wulaƙanta yarinyar sosai Siraj irin wulaƙanci da ban taɓa tsamanin Allah zai jarrabeni da son kamar haka ba, a gaban idonta na ke shigowa da budurwa a gidanta kuma ta dafa mana abinci ta haɗa mana ruwan wanka, ta san fasadi muke aikatawa amman haka be taɓa damunta ba, ko da yana damunta bata taɓa nuna min ba. Idan ta dafa abinci sai ta kawo min tana jiran na yaba mata amman sai na kushe wani ko ci ba zan ba, idan ta yi kwalliya tana jiran na yaba mata ba zan kalleta ba, ban taɓa riƙa hannunta da nunan sha’awaba sai idan zan hukunta ko kuma na doketa, idan mahaifina ya tambayeta ko akwai wata matsalar sai ta ce masa babu komai muna zaune lafiya…” 2

Hawaye ya zubo masa sai yasa gefen hannunsa ya shafe yana cigaba da kallon titi kasancewar window yana fuskantar titi ne.

“Lokacin da na gano tana da ciki, sai na saka mata maganin bachi a lemu ta sha, da tayi bachi sai na cire mata tufafi na ɗauki hotonta na kai ayi editing aka haɗa da na wani, da gangan na sa aka ɗauko min mahaifinta aka zo da shi garin abuja na tarasu da mahaifina na ce cikin da ke jikinta ba nawa ba ne ga wanda ya yi mata shi nan, i’m very fool Siraj can you imagine na ɗauki hoton mamata na haɗa da hoton wani saboda kawai bana son ta kuma ban shirya haihu da ita ba a wannan lokacin…” 10

STORY CONTINUES BELOW


Ya zuba hannayensa aljihu hawaye na ta masa zuba, sannan ya sauke ajiyar zuciya.

“A gaban mahaifinta da mahaifina na nuna waɗancan hotunan kuma na ce na saketa saki uku, sai mahaifina ya ce min saki uku idan aka yi su a take a matsayin saki ɗaya suke dan haka na yi haƙuri na maida matana, jin wannan yasa nace na sake tsaki ɗaya tsaki biyu tsaki uku, a ranar Nawwara ta riƙe min hannaye tana roƙon na rufa nata asiri na karɓi cikin nan, wannan roƙon da ta yi min sai yasa mahaifina ya yarda cewar ba cikina ba ne. 2

A ranar mahaifina ya tabbatar min da sai na yi nadamar abunda na yi mata, saboda yana ganin ta bi maza ne domin kawai na kasa bata kulawa, ashe da gaske zan yi nadama. Bayan na rabu da ita mace huɗu na aura suka kasa zama aure da ni, wasu basa mutunta ni kamar yadda take, wasu kuma su nuna min suma ƴaƴan manya ne ba zasu iya abu kaza da kaza ba, daga lokacin na fara kewar Nawwara, kuma duk wannan auren da nayi babu wacce ta taɓa samun ciki da ni, kuma ba dan bana haihuwaba ba dan ina da wata matsala ba sai dai isgilancin da na yi Allah ya jarrabe ni,  sai bayan na yi aure na biyar ashe ita ba ɗana ba ne ban ganr haka ba sai da na auna jininsa, gudun afkawa cikin wata matsalar sai step mom ɗita ta aura min ƙanwarta, sai da tafiya ta tafi sai na gano kasheni take son yi ta ci gado tun da bana haihu ita kuma tana son haihu amman bata son fita ta bar ɗaular gidana, sai ta saka min guba a abinci shine ciwon da har yanzu yaƙi warkewa a jikina, bayan na rabu da ita na dawo na cewa mahaifina ina son naje gidansu Nawwara, sai ya ce min shi ba babu ruwansa kuma ba da yawun bakinsa ba, saboda na kunyatashi na tozarta shi kuma na ci amanarta bayan shi ne silar aurena da ita, daga ƙarshe ya ce be yafe min na taka ƙafata ƙofar gidansu Nawwara ba, tun daga lokacin sai tunaninta da halin damuwar da na saka ta ya riƙa damuna, wani lokacin na kan rufe kaina ni kaɗai a ɗaki ina kukana amman babu mai bani haƙuri saboda mahaifita bata raye. 2

Komai nawa sai ya tsaya cak, idan naje asibiti bana iya komai sai tunani da damuwa, wannan ne ƴasa Abbah ya dawo da ni kamfaninsa na nan sokoto saboda na rage damuwa, na jidaɗi da Abbah ya yi min haka ko ba komai ni ma zan yi rayuwa garin da Nawwara ta taɓa rayuwa, lokacin da na zo na haɗu da kai, na saka nemanta sai ka ce min ta mutu kuma iyayenta ma sun mutu, daga lokacin na yafe farinciki da walwala a tare da ni.” 3

Ya juyo ya kalli Siraj sannan ya ce

“Nawwara ce kawai macce da ta samu ciki da ni ta hanyar halak, Nawwara ce kawai take kula da ni kamar mahaifiyar da ta haifeni, Nawwara ce kawai zuciyata ke ƙauna, ko a can baya ba ƙaunarta ne bana yi ba kawai dai ina ganin ta shigo rayuwata ne a lokacin da be kamata ta shigo ba. Dan haka karka sake faɗin wata mummunar kalma akan Nawwara, na zan iya tukararta kai tsaye ta yafe min ba, amman idan muna zama a guri ɗaya ita da kanta zata fahimci halin da nake ciki ta yafe min, i need to work with her, i need to be close to her” 5

Yana kaiwa nan ya share hawayensa ya nufi Bedroom ɗinsa, ya bar Siraj a tsaye yana jinjina lamarin.

***         ***         ***

Kukana ya yanke tun kan na iso gida, sai dai hakan be hana mahaifiyata fahimtar ina cikin damuwa ba, ga shi na dawo da wuri ban daɗe ba.

“Lafiya kika dawo yanzu?”

“Lafiya ƙalau kawai faɗa muka yi da wani na mareshi sai suka ce na dawo gida”

“Faɗa kuma? Da namiji miya haɗa ku”

“Na goge gurin ne sai yazo yana min masifa har da riƙa hannuna na ni kuma na mareshi” 1

“Tau kin kyauta kin yi abun a yaba miki kowa ya yi miki ba dai dai ki riƙa hannu kina marensa kinji Allah ya miki albarka” 1

Na san baƙar magana ta yi min wacce ke nuna bata jidaɗin abunda na yi ba.

“Amman Inna ni ce nai gaskiyafa”

“Idan kina da gaskiya sai ki ɗaga hannu ki mareshi wata ƙila ma ya girmeki, duk wani hali da ba naki ba Nawwara yanzu kin ɗauka kin ratawa kanki, wannan zabin zuciyar na Habiba ke aka saukewa shi? Ita tafi sai masifar ta dawo kanki, wannan ba halinki ba ne Nawwara, kuma ba tarbiyar gidan nan ba ce”

“Yi haƙuri Inna na miki alƙwari ba zan sake ba”

Na faɗa idona cike da ƙwalla, domin ni kaɗai na san halin da nake ciki, ita kanta da tasan wanda na mara da bata min wannan masifar ba. Ɗakinmu na wuce na ci kuka sai da na gode Allah sannan na fito.
  Bayan sallah magariba, Bilal ya kirani a waya ya sanar min yana waje, na ɓata lokaci kamin na fita saboda na san maganar da zai min ba zata wuce ta abunda ya faru yau ba, sallama na yi masa amman be amsa min ba sai ya jefo min tambaya.

“Ance min kin kirashi da azzalumi, shi kuma ya baki haƙuri har ya yi iƙirarin kiranki da matarsa, shine Baban Noor ko Nawancy” 2

Na gyaɗa masa kai

“Shine”

“Daman kin san nan kamfaninsa ne kike aiki?”

“Ban sani ba sai yau”

Wani dogon numfashi yaja ya sauke.

“Na yi farinciki da ya gane kirkurensa, ko ba komai Noor zai san mahaifinsa na gaskiya”

Na yi saurin girgiza masa kai idanuwa cike da ƙwalla.

“Ba zai sani ba Bilal ba zan iya bashi Noor ba, be san zafin ɗana ba, be san yadda na yi na haifi ɗana ba, be san wahalar da na sha kamin da bayan na haifi ɗana ba, ko sau ɗaya ƴan’uwansa ba su taɓa biyo sawunna su duba lafiyar ɗana ba, Noor be cancanci Uba irin Jibril ba, Dan Allah dan girman Allah karka faɗa masa ina da ɗa zai iya raba ni da ɗana Bilal”

“Ba zan faɗa masa ba, amman dole wata rana zai gano, lokaci yana zuwa Nawancy zaki koma ke da shi kamar ba ayi ba” 2

Ya faɗa muryarsa na nuna tsantsar damuwar dake cikin ransa.

“Ba zamu koma ba Bilal, babu wanda zuciyata take so take ganin ƙimarsa kamar kai, kai kaɗai ne mutun da zan tuna na yi murmushi, Wallahi kai kaɗai zuciyata take ƙaunara Bilal” 5

“Ina jin tsoron faruwar wani abu Nawancy”

“Babu wani abun da zai faru, sai idan ba son aurena kake ba, ba son ƙwarai kake min ba, daman can zaka biye abunda mutane suke cewa ka gujeni”

“Ba zan taɓa gudunki ba Nawancy, ina ƙaunarki sosai” 1

Ya faɗa yana ƙoƙarin kai hannu ya share min hawayena sai na yi saurin saka nawa hannun na share, sai kawai ya saka min dariya.

“Na jidaɗin wannan abun ko ba komai kin nuna min yadda kika so na”

Ni kuma sai na cire talakmena na gwaɗa masa a hannu har sai da ya yi ƙara.

“Ka daina taɓa ni da wannan hannun”

“Nima ba son raina yake taɓa ki ba, kawai dai shi ɗin ne ya damu sai ya taɓa ki, amman ranar da zai taɓa halalinsa zan ga bakin da ya isa ya hana shi” 5

Na zaro ido ina mamakin kalaminsa, sai ya kannemin ido ɗaya yana murmushi. Mum yi firar da ta ɗebe min kewa fira irin ta masoya firar da ta gusar min da duk wani tunani da damuwa har sai da na dawo cikin gida. Bayan na yi sallah isha’i na ci abincin dare kaɗan saboda kar Inna ta gano abunda yake damuna.

Dakimmu na dawo da zimmar bachi amman sai na kasa rayuwar da na yi a abaya ta dawo min…

FLASH BACK…….

_______________________________________

I can’t wait na ji tarihin Nawwara zamanta da Jibril.. 💃

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page