RAI BIYU CHAPTER 10

RAI BIYU

CHAPTER 10
Khadija shine sunan da mahaifina ya saka min, sai ya yi min alkunya da Nawwara, duk da kasancewar ba ni ce ta farko ba, ƴaƴƴuna hudu maza duk basu tsayaba sai ni da nazo a ta biyar kuma mace.
Bayan ni sai da mahaifiyata ta shekara biyar sannan ta haifi Habiba, a lokacin Mahaifina yana ta faɗi tashin rayuwa na nema mana abunda zamu ci. +

Ba zan kira kaina da kyakkaywa ba, sai nasan ni ba mummuna ba ce, abunda kawai zan iya shaidar kaina da shi shine na ɗauko fari da kuma dogon hancin mahaifiyata kasancewarta fulani, gashin kan ba a magana na girata ma askewa nake balle kuma na gadon bayana dake ƙayatarda mai kallo.

Siye da siyarwar na fatoci, Sana’ar iyaye da kakkanina ce sana’ar wacce mahaifina ya buɗe ido ya samu kansa a cikinta har muma muka zo muka tarar anayi, kowa ya tashi a gidan ana buɗa masa shago ko kuma a haɗashi da wanda zai riƙa masa ja gaba kan sana’ar har ya kafa tashi.
Kusan zan iya cewa sana’ar bata karɓi mahaifinmu ba, tun lokacin da ya fara ba riba ba kuɗi, wani lokacin har kuɗin wani sai sun shiga ciki su ƙi fita, duk lokacin da mahaifinmu ya siyo fata da zimmar saidawa sai karaya ta sameshi wacce zata zama silar da ba zai iya maida kuɗin ba, yayyunsa da Yakumbo da kuma Hajiya Lamtana Allah ya jiƙanta sai suka ɗauki karan tsana suka ɗora ma Ramatu wato mahaifita, a ganinsu ita ce bata da ƙashin arziki, sukan ce wai can kamin ya aureta a lokacin da yake saurayinsa yana sa’arsa lafiya sai da ya aureta sannan komai yaso ya lalace.

A lokacin ina ƙarama amman abun yana min zafi sosai saboda yana damun mahaifiya sosai, har na riƙa kallonsu a matsayin maƙiyanmu wanda har yau shine a zuciyata, domin a lokacin a gaban idonmu suna faɗa wai uwarmu mai farar ƙafa ce wanda hakan suke tunanin ba komai bane ko kuma mu bamu kula ba alhalin yana mana zafi sai dai bamu isa mu nuna ba kasancewar gidan taro ne, ko tari kayi sai anji, Babban gida irin gidan nan ne da kakanni suke siye sai iyaye da jikoki su taru a gidan kowa ya keɓe wani ɓangare nasa ya kafa nasa iyalin.

Lokatuta da dama takan keɓe ita kaɗai ko kuma da mu tayi ta kuka tana roƙon Allah ya bawa mahaifina wani aikin duk da bashi da wani karantun zamani a wacan lokacin, muna haka wani maƙocinmu Malam Buba kuma abokin Baba da yake yawan zuwa Abuja ya faɗa ma Mahaifimu cewar wani attajirin mai kuɗi a garin Abuja yana neman mai masa gadi kuma ya ce baya buƙatar kowa sai bahaushe ɗan’uwansa, Malam Buba ya kasance yana masa gadin wani babban kamfanin siyer da kayan alatu ne dake can garin Abuja.

Muna zaune gida ranar wata talata, bayan mun gama cin kwaɗon ƙanzo, sai Baba ya shigo da far’arsa yana labarta mana abunda Malam Buba ya faɗa masa, Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta, a nan suka yanke shawarar ba zasu sanar da Yakumbo da Hajiya ba saboda sunsan ba zasu bari yaje ba, sai suka haɗa kai da Malam Buba ya faɗa musu Babanmu zaije Abuja ya kai fatune saboda ana bukatarsu a can, sun yi na’am suka masa addu’ah da fatan nasara, sai Baba ya karɓi fatun bashi da sunan idan yaje can zai aiko da kuɗin.

Ranar da zai tafi munyi kuka sosai ni da Inna har ma da wasu mutanen gidan saboda muna ganin kamar ba zai dawo ba, tafiya nisa kuma har garin Abuja garin da a wacan lokacin muke ɗaukarsa kamar wata ƙasar dabam.
Bayan wata ɗaya da tafiyar mahaifinmu sai gashi ya dawo cikin shigar mutunci da kamala, sai dai ya ɗanyi rama kaɗan ya kuma yi haske, ya labarta mana komai yake muna nan cikin ranshi wannan tunanin ne ya hanashi ƙiba, har ma yake faɗa mana cewar mai gidansa ya ware masa wani ɓangare na gidansa ya bashi ya ce ya ɗauko iyalansa su dawo nan kuma ya zo mana da kuɗi mai yawa.

Ba ƙaramin yaƙi akayi ba kamin Hajiya ta yarda ta barmu aka tafi da mu, a nan ma sai da ya yi mata wata ƙaryar cewa ya canja sana’a yanzu yana siye da saida takalma ne na fatu har ma ya ce mata hayan gida ya kama a ƙauyen Abuja acan zai zauna da mu ya cigaba da sana’arsa.

Amaina huɗu a mota kamin mu sauka zaria, aka siya min abinci da ruwa na cika cikina ni da Habiba sannan muka cigaba da tafiyar, ko da muka shiga garin Abuja ina bachi, sai da motar ta tsaya sannan Inna ta tasheni muka koma can wani ɓangare na tashar, Baban mu ya ari wayar wani ya kira Alhaji ya sanar masa mun iso domin ba a shiga da wani abun haya a unguwar.
Dare ya yi sosai har Baba ya yanke shawarar zuwa gurin abokinsa Malam Buba mu kwana a can sai ga ƴan komisho sun zo suna neman Malam Musa Kafinta, a nan suka haɗa mu da mutumen yanayin yadda Baba ya gaisa da shi sai ya tabbatar da cewar ya sanshi, ashe direban Alhajin ne.
Ni da Inna duk da tsoro muka shiga motar saboda ganin Babbar motar kamar wannan wacce ni dai zan iya rantsuwa hannuna ma be taɓa kaiwa akanta, amman yau zan shigeta. Ina ta rabon ido har muka iso wata kyakkyawar unguwa. Idona be ƙara buɗewa har sai da muka iso cikin ƙaton gidan dake cike da ababen more rayuwa.

STORY CONTINUES BELOW


Iyalan mutumen ne da Alhajin shi kansa suka fito suna tarbonmu, har yake bawa Baba haƙuri akan rashin ɗaukoshi da wuri wai yaje meeting ne kuma sai ya manta sai da ya dawo gida sannan ya tuna.
Cikin Falonsu muka shigo sai suka saka mai aikinsu ta kwashi kayanmu ta kai BQ, mu kuma suka kawo mana abinci da abin sha.

Cikin sati ɗaya muka sake da ƴan gidan kasancewarsu mutane da suka san darajar ɗan’adam tun daga Hajiyar gidan har yaranta, Ƴaƴanta maza biyu manya sannan mata uku ɗayar tana aure sauran biyu kuma a lokacin suna karatune, sai ƴar ƙaramar ƴarta Salima, wacce ta kasance ta shida a cikin yaranta takwas.

Shaƙuwa sosai da sosai ta shiga tsakanina da Salima, har ta kai zuwa makaranta ne boko ne kawai yake rabamu, kasancewar ni bana zuwa bokon sai dai islamiya Alhaji Dahiru wato mahaifinta ya sakani Islamiyarsu.
Duk ƙarshen wata Baba yake zuwa gida duba Hajiya, wani lokacin kuma sai dai ya yi mata aike a haka muka kwashe shakara ɗaya a gidan Tsohon ambasadan nigeria a ƙasar London, muka zama kamar ƴan gida, shaƙuwa sosai ke ƙara shiga tsakanina da Salima, da kuma Babban yayanta Jamal, shi yake koya min karatu duk da ba a sani makaranta ba a lokacin, Jamal mutum ne mai son jama’a da far’a, har ta kai idan be ganni ba sai ya aika an kirani, bayan ya gama koya min karatu sai ya ce na yi masa gatana, ba laifi a lokacin na iya zuba gatana har da wacce ba’a taɓa yi ba, haka zai zauna ya yi ta saureren shirme na wani lokacin har da Hajiyarsu. Shi ya fara yaba ƙwazo na sai ya yi ma mahaifinsu magana aka sakani a makarantarsu Salima, na kashe kuɗi sosai gurin samo transfer dake nuna daga wata makarantar na ke, sannan aka samu sa’a aka sakani aji ɗaya da Salima, Habiba kuma aka sakata wata maƙarantar wacce ƙannen Salima suke yi.

Tare muke zuwa mu dawo, mu tafi islamiya tare, wasa-wasa sai na tattara kayana suka na koma ɗakinta da zama, a lokacin Inna na da cikin Sakina, komai a iri ɗaya muke da Salima bana da ƙawa sai ita itama bata da ƙawa sai ni, idan ba a ganta ba sai an tambayeni haka itama.
Ta ɓangaren Jamal kuma soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk a lokacin ban san miye so ba, na kan samu kaina da tunaninsa da kuma rashin jindaɗi a duk lokacin da baya gida.
Muna daf da ƙare makarantar secondary school ni da Salima Hajiya ta samu labarin cewa Baba gadi yake a wani gida, babu irin bala’in da bata mushi ba cikin har da zance zata tsine masa gidan be dawo ba, wai Inna zata kaishi ta baro yana biye zancen mace. A dole tasa Baba ya tattara ya koma gida sai dai be zauna gidan ba sai ya kama haya kusa da su inda muke zaune har yanzu.

Ni kuma a aka barni nan da sunan idan na gama zana jarabarwar za a maidani gida, bayan mun gama jarabarwa ta fito ta yi kyau, a lokacin ne ɗan wani mai kuɗi ya fito neman auren Salima, Alhaji Dahiru ya yi na’am ya sallama masa bisa sharaɗin zai jirata ta yi karatu na gaba, a lokacin shi kansa yaron be kammala karatunsa da yake ba.

Bayan sati ɗaya da faruwar haka sai Ya Jamal ya fara min zancen aure, ni kuma ina ta tsoro saboda ina ganin kamar iyayensa ba zasu yarda ba, sai na nuna masa bana son shi, duk abunda muke a tsakaninmu ne iyayensa basu sani ba, har Salima ma tada zame min jinin jiki ban taɓa labarta mata ba, shi ma kuma be taɓa nunawa kowa ba.
Bayan takadun mu sun fito sai Alhaji Dahiru wanda muke kira da Daddy ya turo mu gida ni da Salima, bayan ya cika mana bayan mota da abinci, a lokacin an haifi Sakina har ta soma wayo.

Watan mu ɗaya muka garin Abuja saboda sabo sai zaman sokoto ya yi ma Salima wuya, ni kan ban so haka ba, sai dai babu yadda zan yi tun da mun zo tare dole mu koma tare, bayan mun koma sa sati ɗaya na sake dowa, Alhaji Dahiru ne yasa ka Ya Jamal ya rakoni har gida, sai dai wannan karon tafiyar Jirgi muka yi saboda Ya Jamal ya ce ba zai iya bin mota ba zuwa sokoto.

Kwanansa ɗaya ya koma, ni kuma na zauna a nan har na tsawon wata uku a lokacin Mahaifina yana sana’ar siyar da itace a ƙofar gida, wata rana mu cinye ribar wata rana kuma Allah ya buɗo mana, haka muke ta faɗi tashin rayuwa ga masu neman aurena sai fitowa suke. Kwatsan Alhaji Dahiru ya kira ya ce a sanar min ya samo mana gurbin karatun lafiya a ƙasar burtaniya wato London, cikin sati ɗaya na shirya na koma Abuja, duk wani shirye-shirye ina can aka yi shi, bayan kamar wata ɗaya da ƴan ƙwanaki aka kammala komai, sai da na koma gida na yi bankwana da su Inna a lokacin ne Yakunbo ta so tanani zuwa saboda a ganinta kamar za a siyar da ni ne ko wani abu makamancin haka.

Kamar na mafarki na fara karatu a City, University of London, a ƙasar da ban taɓa mafarkin zuwa ba, ƙasar da nake ji a labarai da kuma jaridu, burtaniya ƙasar turawa ce wacce bata da matsatsi akan addinin kowa a wacan lokacin, ba ko yaushe nake irin shigarsu ba wato shigar ƙananan kaya, nafi saka doguwar rigar atamfa ko abaya sai na samu ƙaramin ɗankwali ko hula na yi rolling kaina da shi. 1

Ɗakin mu ɗaya da Salima da kuma wata tsohuwar ɗaliba makarantar wato Farida, wacce ƴar asalin hijar bauchi ce, cikin ƙanƙanen lokaci muka saba da Farida duk da kasancewar ba gurin karatun mu ɗaya ba. Ranar da muka fara zuwa lab wani babban likita muka tarar ɗan Nijeria dan asalin garin Kaduna, wato Doctor Jibril Bashir Makama, sai da ya fara gabatar mana da kansa sannan na soma bamu darasi tare da nuna mana wasu abubuwan a zahiri.
Tun da idona suka sauka akansa sai ya tafi da imani da duk wani tunani da natsuwata, Jibril na da kyau da ba zaka iya tantanshi aa cikin ƴaƴan turawa ko larabawa, fatarsa fara ce fes ga shi da tsaye hancinsa ya sauko a ƙasan hancin an yanka masa madaidaicin baki, fuskarsa na ɗan faɗi, yana da manyan ido sai dai ba fararene ba, suna da surkin ja ƙaɗan, a gefen wuyansa tattoo ɗin taurara ne aka jera masa har cikin bayansa.

Hankalina baya kan abunda yake ƙoyar da mu yana kansa, duk wani ƙyabtawar idonsa ƙirgawa nake, ina haɗɗace yadda bakinsa yake motsi da turansa da yake watsowa kamar baturen burtaniya, duk bayan daƙiƙu sai na lumshe ido saboda ƙamshin turarensa da ya cika lab ɗin. Murmushi nake masa ba tare da na san ina yi ba, har sai da ya katsa min tsawa.

“You deaf…”

A firgice na dawo hayyacina cike da kunya, ƙasa-ƙasa na ke kallon wata abokiyar karatuna Katherine Williams wace ke sonim dariya ita da wasu da dake kusa da ni.Tun daga lokacin bana da tunani sai na shi, mafarkina ma nasa ne, duk wani abu da zai kusantar da ni gareshi na kanyi ƙoƙarin aikatashi, duk hanyar da zan ganshi ita na ke bi, duk da na lura da babu ruwansa da sha’anin kula wasu matan na daban hakan yasa na fara tunanin ko yana da mata ne.
Salima kanta ta lura da yadda nake ta rawar jiki da son ayi zancesa, idan kuma wata macen ta kalleshi sai naji kamar naje na shaƙeta, a gurin Salima na ke samun labarinsa, kasancewar ta sanshi farin sani wai ɗan abokin Daddy ne, na yi mamakin da ban san shi ba duk tsawon zaman da na yi a gidan, duk da kasancewar na san Mahaifinsa amman ban taɓa kawowa zuciyata cewar shine ɗansa ba, sai dai duk wani mummunan hali nashi na wulaƙanci da rashin son mutane ta hanyar Farida na ke jinsa saboda ta rigamu zuwa makarantar duk wani abu da ya danganceshi ta san shi sosai. +

Salima ce take labarta min cewar Jibril shine ɗa na uku a gurin Mahaifinsa, kuma ɗa na farko a gurin mahaifiyarsa kasancewarta Amarya, yana da Step mother wacce ita ce ke da ƴaƴa da yawa kuma ita ta riƙashi a hannunta ya tashi, a gurin haihuwarsa Allah ya karɓi ran mahaifiyarsa wannan yasa mahaifinsa yake sonsa kuma yake tausayinsa domin ko da Jibril ya buɗe ido be san mahaifiyarsa ba sai step mother.

Wata ranar da muka yi practicing akan thigh surgery, ya yaba min sosai kuma ya nuna jindaɗinsa akan yadda na maida hankali sosai, a ranar kasa bachi nayi saboda farinciki duk bayan minti ɗaya zuwa biyu uku fuskarsa na ke gani.
Hakan yasa na ƙara maida hankali akan karatuna, da muka samu hutu sai muka soma shirin ziyarar gida kasancewar dkanmu munyi marmarin gida saboda haka muna samun hutun muka shirya muka dawo gida.
Bayan mun dawo Abuja da kwana biyu na fara shirye-shiryen zuwa gida sokoto domin ganin iyayena, ranar da anje gurin kitso na dawo sai Daddy ya aiko yana kirana.

A ɓangaransa na sameshi tare da Momi Aisha wato Hajiyarmu, da sallama na shiga bayan na gaishesu sai na maida kaina ƙasa ina wasa da carpet zuciyata cike da son jin dalilin kiran nawa, da farko na yi tunanin akan tafiyata ne sokoto ko kuma karatu.

‘Wata ƙila zai ce na haƙura har sai mun sake samun wani hutun ne ko kuma wani abun’

Haka na yi ta saƙe-saƙe na kamin na ji abunda Daddy yake faɗa.

“Nawwara ko akwai wani wanda kike so? Ko kuma iyayenki suke son haɗa ki da shi?”

Na yi mamakin da ya yi min wannan tambayar, a take Jamal ya faɗo min a raina na fara tunanin ko ya faɗawa Daddy wani abun ne, ko shiyasa tun da na zo ban ganshi ba. Cikin natsuwa da ladabi na ɗaga kai na kalleshi na ce

“A’a babu Daddy”

“Mashallah”

Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciyar da ke nuna ya jidaɗin hakan, ya gyara zamansa yana fuskanta ta sannan ya ce

“Alhaji Bashir Makama aminane a tare muka taso tare muke duk wani abu da ya shafi siyasa ko kasuwanci, sai dai shi be cika zama a garin Abuja ba shiyasa ba ki wayeshi sosai ba, yafi zama Kaduna wato mahaifarsa sai kuma garuruwan da yake gabatar da kasuwancinsa.
Few days ago mun tattaunada shi akan ɗansa, yana son haɗa zuri’a da ni, ni kuma na duba a cikin ƴaƴana na ga babu wacce ta dace da shi sai ke, na yi hakan ne ba dan komai ba sai dan sama miki rayuwa mai kyau da nagarta, na san idan har kika auri ɗansa zaki ji daɗi sosai, saboda yaron yana da aiki ba irin ƴaƴan masu kuɗin nan ba ne shashashu kuma yana son yaronsa sosai, matsalar sa ɗaya baya son zaman da yake a waje kuma baya son yarinyar da yake tare da ita”

Sosai na ji babu daɗi duk da bani da wanda zan iya fitar a lokacin na ce gashi shi nake so, amman hakan yasa ni jin babu daɗi, sai dai ban yarda na nuna masa ba domin na san ba zai min abunda zai cutar da ni ba.

“Ai kin san Alhaji Bashir ko? Ɗan sa da yake waje yana aiki, ta hanyarsa ma Daddy mu ya samo muku gurbin karatun, ba zaki rasa sanin Jibril ba dan ance makarantar ku yake koyarwa, kuma a can zamu zauna sai kin gama karatun sannan ku dawo gida gaba ɗaya”

STORY CONTINUES BELOW


Wannan karon Momy ce take maganar da ta kwantar min da hankali kuma ta saka ni farinciki, cikin nuna tsantsar ladabi na ɗago na kalli Daddy na ce

“Ba zaka taɓa yi min abunda zai cutar da ni ba, ni kuma ba zan taɓa butulce maka ba, ko wuta ka kunna kace naje na shiga zan iya shiga na ƙone kaina balle aure, fatana Allaj yasa haka shine alheri”

Ya ji daɗin farucina har ma yasa min albarka shi da Momy sannan na taso zuciyata cike da farinciki fal na dawo sashenmu, jikin har rawa yake na labartawa Salima abunda ake ciki, ita ma tayi farinciki sosai sai da nayi mata alƙawari karta faɗawa kowa kuma karta nunawa Daddy ina sonsa, ita kuma ta yi min alƙwarin haka.

Bayan kwana ɗaya muka yi shirin zuwa sokoto ni da Salima wannan karon ma jirgi muka bi, Inna ta yi farinciki ganin sosai ni kaina ban san na canja ba sai a wannan lokacin na yi mamaki da Inna ta ƙara haihuwa ba tare da ƙara wasu shekaru biyar ba, kuma ace har anyi sunan Jamila ba a faɗa min ba. 
  Dare muke rayawa ni da Salima muna labarta Inna da Baba rayuwar waje, Habiba kan ta shige cikina tare muke kwana a shinfiɗa ɗaya, a wannan lokacin ne na samu damar ziyarar abokaina da muka taso tare ciki wasu kuma da muka yi makarantar islamiya da boko a tare kamin tafiyata Abuja, cikin har da Zinatu da Baraka da kuma Jidda a lokacin duka muna unguwa ɗaya kamin su Zinatu su koma kware road gawon nama.

Wasu basa yarda ina karatu a waje saboda suna ganin mahaifina ba kowa bane, kuma ba kowa ne mai arziki ba ne zai iya yi mana yadda Daddy ya yi mana. Inna ta labarta min yadda ake ta tsigumi a unguwarmu wai saboda kwaɗayin abun duniya zai siyar da mutuncin ƴarsa ya yarda naje na yi karatu bayan na secondry da aka ce na yi, a cewarsu wai yaƙi ya yi min aure jira yaƙe sai na gama karatun sai mai kuɗi ya zo ya aureni.

Ni kaina maganar bata min daɗi ba kuma daman nasan za a samu haka, mutane ba zasu taimakeka idan kuma wani ya tallafawa rayuwarka sai koma gefe suna zagi da ganin hakan be dace ba. 
Sai da muka yi sati biyu a sokoto ana sauran kwana uku mu koma Abuja, Baba ya shigo ya same ni a ɗaki a lokacin ina ni kaɗai ya soma labarta min maganar da Daddy ya yi masa, ganin na ƙi cewa komai yasa ya kira Inna suka sakani a gaba akan ina son haka ko bana so domin shi ba zai yarda ayi min auren dole ba.

Ni kuma na yi shiru ban amsa ba, hakan ne ya tabbatar masa da ina so ɗin kamar yadda Annabi ya faɗa shirun budurwa shine amsarta.

“Amman yasan ke ba ƴar Alhaji ba ce ko? Saboda bana son ayi abu daga baya ya dawo na rashin daɗi”

“Wallahi Baba ban sani ba, amman na san ba zai rasa faɗa masa ba”

“Idan ma be faɗa masa ba ni zan buƙaci.ya faɗa masa, ƙara yasan ko wacece gudun kar sai anyi abu wani abu ya biyo daga baya, kuma ina son yasan mu talakawa ne iyayenki ba masu kuɗi ba, idan ya ji zai iya aurenki a haka walillahil hamdu idan kuma ya ce ƴar mai kuɗi yaƙe so sai mu jira Allah ya kawo miki na gari”

“Hakan shi yafi Allah ya zaɓa miki alheri”

Cewar Inna, ni dai ban ce komai ba, Allah kawai na ke roƙo ya zaɓa min abunda ya fi alheri. Bayan mun koma Abuja Momy take faɗa min wai cikin satin nan Jibril ɗin zai dawo dan haka na shirya tarbonsa a kowane lokaci, a lokacin hutunmu sauran sati uku ya ƙare. 
    Shiru-shiru Jibril be zo ba, da sunan ganin matar da zai aura, hakan ya tabbatar min da cewar shi ma baya son auren wata ƙila shi ma an masa yadda aka min ne, wato haɗi.

A week later Momi ta ce na shirya ni da Salima zamu je area 1 gurin abokin Daddy mu ƙarɓo saƙo, duk kalar tufafin da na saka sai Momy tace ba su yi ba naje na canja, kuma ni kawai take cewa ba da Salima ba, daga ƙarshe sai ta shigo ɗakinmu da kanta ta zaɓa min tufafin da zan saka kuma tasa na canja kwaliyar fuskata na feshe jikina da turare sannan ta kira direba ta ce ya kaimu.

Na samu kaina da faɗuwar gaba sanin gidansu Jibril ne zamu je, sai dai ko da wasa ban kawowa raina cewar zan je mu gaisa ba ne, iya abunda na zata zamuje karɓo saƙo ne wata ƙila yana nan shiyasa take son na yi kwalliya ta yadda ko da ya ganni ba zai raina ni ba, amman abun mamaki bayan mun isa gidan mun gaisa da Hajiya Zainab Step mother ɗinsa sai aka nuna min wani falo wai na shiga zamu gaisa da Jibril.

Na ji babu daɗi duk da kasancewar ina sonshi amman sai nake ganin kamar hakan be dace ba, shi da yake namiji ya kasa zuwa ya ganni sai ni da nake mace za a ce naje mu gaisaz, ba zan iya mata musu ba tunda ita a tunaninta Momy ta faɗa min haka tun gida.

Da sallama na shiga muryata can ƙasa-ƙasa, amman be amsa min ba kuma be ɗago ya kalleni yana ta aikin dannar wayarsa fuskarsa a haɗe kamar baƙin hadari, his perfume make me feel comfortable har na zauna duk da be min izinin zaman ba. 
From head to toe ya kalleni sannan ya jinginar da kansa yana taɓe baki ya ce

“Ke kuma haka tarbiyar gidanku take? Mata su suke zuwa fira da kansu? What kind of woman are you, kin cika arha da yawa gaskiya abun har cikin gida” 2

“Ni ma ba a faɗa min da kai zan gana ba, saƙo aka ce min zan karɓa shiyasa yazo da ko mayafina baka isa ka gani a gidan nan ba”

Ba bashi amsa kai tsaye, sai ya tashi zaune yana taɓe baki tare da cigaba da kallona.

“Really? Kuma kika ci kwalliya haka? Kina tunanin zan ga kyauki ne ko? Mutumen da yake son ki zai yaba kyauki, amman ba ni ba dan ni kamar baƙin maciji nake ganin ki, ki taimaki rayuwata baiwar Allah ki ce baki so na, Wallahi zan biyaki ko nawa kike so”

“Kai miyasa ba zaka taimaki rayuwata ka faɗawa mahaifinka cewar baka so na ba”

Still bakinsa a mere ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa a aljihu ya nufi window.

“Ban san ko sau nawa zan faɗa masa ya yarda ba, Wallahi na faɗa na ƙara duk wata mace da ba Aisha ba bana son ta, amman mahaifina ya tsaya kai da fata akan sai na auro wata, ya neman min auren ƴar Alhaji Dahiru ne saboda yana yaba tarbiyar gidan kuma yana son zumuncinsu ya ƙara ƙulluwa, after that you’re not his biological daughter, jin wannan yasa Mahaifina ya ɗaga min ƙafa, amman Alhaji Dahiru ya dage akan shi yana son ayi, har da cewar wai baya son auren ya ɗauki lokaci.

Aurena da ke baiwar Allah ba alheri ba ne, domin ni dai har ga Allah bana son ki, lemme ask you some questions, shin zaki iya auren namijin da ya taɓa kusantar wata mace kamin ke? Zaki auren Namijin da ya taɓa sanin wata mace kamin ke? Zaki iya zama da namijin da zuciyarsa da gangar jikinsa duk na wata macen ne? Could you?”

Na girgiza masa kai.

“No i couldn’t, ba zan iya auren namijin da ba be san ƙimar zaɓin iyayenshi ba”

Ya matso kusa da ni cikin ɓacin rai, ya riƙa fuskata ya soma magana cikin murya mai amsa amo biyu.

“how dare you, ke iyayenki sun san ƙimarki ne zasu barki hannun wani saboda ƙwadayin abun duniya, bayan baku haɗa komai da shi ba daga gadi! Wallahi duk kika aure kin saka rayuwarki cikin matsala sai kin ƙwammace kiɗa da karatu, duk wanda ya ce zai raba ni da Aisha ba zai sha da daɗi ba”

Ya ciro wayarsa da ɗayan hannunsa ya nuna min hotonta da ke gaban wayarsa, yana matsar min fuska iya ƙarfinsa, a nan na fara kokuwar kuɓucewa amman na kasa.

“Wannan matar ta fiye min ke sau dubu ɗari, dan haka karki yaudari zuciyarki kar kwaɗayin abun duniya yasa ki salwantar da rayuwarki ni da ke kamar RAI BIYU ne wuta da ruwa ba zamu taɓa haɗuwa ba, you bitch…!”

Yana kaiwa nan ya wulgar da ni saman manyan cushion, ya yi ficewarsa cikin zafin rai. Ni kuma na tashi zaune da sauri ina taɓa bakina da nake tunanin yama fara jini saboda zogin da yake min.

Na kusan minti goma a falon sannan na fito ina ta ƙoƙarin ɓoye abunda ke fuskata. Ban tararda Salima a falon ba, sai Hajiya Zainab da yaranta ƴan mata da ke ta min kallon uku saura kwata. 
   
“Direba zai maida ke gida, Salima ta koma tuni saboda an kira Daddy ku ba lafiya”

Gabana ya faɗi sosai, miya samu Daddy ina ta tambayar kaina har na fito harabar gidan na nufi inda direba yake, na shiga bayan motar sai ga wata budurwa ta zo da jakunkuna ta saka min a motar sannan direba ya kama hanyar gida da ni, tun kamin mu isa gida na fara hawaye saboda tunanin abunda ya sami Daddy da kuma baƙin cikin abunda Jibril ya yi min.
Ganin Motar Anty Mairo da Zubaida wato manyan ƴaƴansa guda biyu a harabar gidan ya ƙara tayar min hankali, cike da fargabar abunda ya samu Daddy na fita motar na nufi cikin gidan.

A falon Momy babu kowa sai ƴar aikinta Suwaiba, ban tsaya komai ba na nufi part ɗin Daddy. Mamaki ne ya maye gurbin tashin hankalina, sai ya zo akasin tunanina da kuma furuncin step mother ɗin Jibril cewar Daddy ba shi da lafiya.

A sanyaye na shigo falon idona kan Daddy dake making call yana murmushi, ban ankaro da ban yi sallama ba sai da Anty Zubaida ta hankarar da ni ta hanyar amsa min da.

“Wa’alaikissalam”

Saurin share hawayen fuskata na yi na yi sallamar duk da kasancewar na kai tsakiyar falon. Sai duk suka haɗa baki gurin amsa min ciki har da Momy. Cike da mamaki na zauna kusa da Anty Zubaida ina cigaba da kallon Daddy.

“Nawwara har kin dawo?”

Cewar Momy.

“Eh ko da na fito Salima ta dawo gida ko da na fito Hajiya tace min Salima ta wuce wai Daddy ba lafiya”

“Ee na kirata na ce ta dawo gida jikin Daddynta ya tashi amman da sauƙi daman jinin ne ya hau amman ya sauka”

Ajiyar zuciya na sauke na kalli Daddy da ya aje waya a kunnensa ina masa ya jikin.

“Alhamdulillah, ya kika baro can ina fatar kina son shi?”

Har na buɗe baki na yi magana sai Momy ta yi karaf ta karɓe.

“Kana maganar tana son shi Alhaji wace mace ce zata kalli Jibril ta ce bata son shi, ai Hajiya ta kirani ta faɗa min sun fahimcin junansu sosai kuma shima ya yaba da ita sosai”

Ƙasa na yi da kaina saboda bana son ƙaryatata ko kuma na kunyata ta a gaban ƴaƴanta akan wannan zancen da ba haka yake ba.

“Maa Sha Allah, haka muke so Allah ya tabbatar da alheri a ciki, mahaufinsa ma ya faɗa min yana son a ɗaura masu aure kamin ta koma makaranta albashi idan ta kammala sai ayi bikinsu”

Jin wannan maganar ta Daddy yasa idanuwa cika da ƙwalla. Anty Zubaida da Anty Mairo suka shiga tsokanata har ma da Salima, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na tashi da gudu na bar falon.

Ɗakinmu ma dawo na zauna bakin gado ina ta kuka, wata zuciyar na raya min na kira Baba na faɗa masa wata na cewa a’a, tabbas a lokacin ina son Jibril amman rashin aurensa shi zai fi min alheri tun da har ya nuna min akwai wacce yake so.
  Ina ta tunanin mafita sai ga Momy ta shigo ɗakin tare da Salima tana faɗin.

“Kun saka min ƴa kuka bari na rarrashi abata”

Tana zaunawa kusa da ni sai ta kore Salima daga ɗakin da sunan zata rarrasheni, Salima na fita sai ta canja fuska ta kalleni

“Iyakar halacci Nawwara mun miki ke da iyayenki, ashe ko ba mu cancanci komai ba sai kyakkawan sakamako, kin dai san Alhaji ba zai miki zaɓin da zai cutar da ke ba, kuma wannan auren da kike gani idan har kika aureshi ke da danginku duk kun warke, ƙin yi wannan auren zai ɓata abotar Daddynku da shi na tsawon  shekaru ashirin, idan kuma kika yarda kika aureshi tam kamar kin zuba babban jari ne a dukiyar gidan nan da kuma ta gidanku, domin mahaiɗinsa na cikin masu kuɗin da ake ƙirgawa da su a africa ba ma Nigeria kaɗai ba”

Na ɗaga kai na kalleta cikin muryar kuka na ce

“Amman Momy baya so na yana da wacce yake so, kuma ya faɗa min matuƙar na yarda na aureshi sai na yi nadama”

“Ai nasan baya son ki, daman taya za’ayi Namiji kamar Jibril ya so mace irin ki? Yaron da yake ganin ƴaƴan turawa da larabawa, kuma ɗan da magana kawai zai yi ma kuɗi su faɗo ƙasa sai kalli ƴar talaka irinki ya ce yana sonta? Ke ni fa Salima na so a bashi amman Alhaji yaƙi wai wani ya riga ya bada ita ba zai ce ya fasa ba saboda wannan, amman idan kika yi haƙuri da sannu zai fara sonki har ya kyautata miki, ke ko be so ki dole zai kyautata miki domin su masu kuɗi matuƙar suna auren mace dole ne su kyautata mata domin dukiya bata musu zafi.

STORY CONTINUES BELOW


Nawwara karki yarda ki faɗa ko ki nunawa Alhaji cewar baki son zaɓin da ya yi miki domin hakan zai iyasa zuciyarsa ta buga ya mutu gaba ɗaya, dan Allah ki yi min alƙawari zaki auri Jibril albashi idan daga baya kika ga zaki fito sai ki ce ya sakeki, kuma kin ga waje ma zaku zauna kina karatunki shi yana sha’aninsa”

Ta ƙarasa tana riƙe hannuna cike da magiya. Kai kawai na iya ɗaga mata alamar na amince ba dan raina ya so ba, har ga Allah ni kaɗaina ina ganin kamar idan ban auri zaɓin Daddy ba ban masa halacci ba.

Bayan fitarta Salima ta shigo tana zolayana, yadda ta ga ina kuka ya tsorata ta har ta soma tambayar ko wani abun ne ni kuma na amsa mata da ba komai.

A haka na jure na kauda kaina daga duk wani abu da zai nuna bana son auren saboda kar ran Daddy ya ɓace, su kuma sai hidimar ɗaurin auren suke har ana daf da ɗaura aure Baba be daina min magana akan idan bana sonsa na faɗa ba, amman na ƙi na faɗa, ni dai kawai na ɗaukarwa kaina alƙawarin zan jure ko ma minene saboda na zama ƴar halak a gurin Daddy da Momy. 
   
Ana cikin haka ne Ya Jamil ya samu transfer gurin aiki zuwa Jos, ni kaina na jidaɗin haka nasan idan ya yi nisa da ni zan fi samun sakewa.
Sai da ana sauran kwana biyu ɗauren auren Jibril be taɓa kirana ko a waya ba, kuma be je ya gaishe da Baba ba, sai dai Mahaifinsa ya tafi tare da muƙƙarabbansa suka gaishe da Baba, komai a ɗaurin auren a nan Abuja aka yi saboda haka sai ranar da aka ɗaura min aure sannan mahaifina ya ga fuskar mijin ƴarsa kasancewar ya samu halarta tare da wasu ƴan’uwansa.

Na ji ni daban a cikin wani yanayi marar misaltuwa a wannan ranar, bana farinciki kuma bana baƙinciki ni dai kuka kawai na ke kukan da ban san dalilinsa ba, ganin haka yasa Momy ta kaini ɗaki ta ja min kunne akan na daina kukan kar mutane su zargi wani abu, haka na wanke fuskata na keɓe kaina a ɗaki har sai da ka ce na fito ga Baba can zamu gaisa.

Babu wata gaisuwa da na yi da dashi sai ta kuka kuka na yi sosai har sai da shi ma na saka shi kuka, ya yi min nasiha sosai akan rayuwa da kuma zamantakewar aure, ya faɗa min yanzu na tashi daga ikonsa na koma ikon wani, hakan yasa na ji ni cikin wani babban ɗaki mai nauyi. 
Washe gari ma da zai koma sai da ya kirani shi da ƴan uwansa suka zagaye ni suna min huɗuba mai ratsa jiki.

Kwana biyu da ɗaura min aure aka kwantar da ni a babbar asibitin Abuja saboda rashin lafiyar da ya taso min, a wannan ranar ce Jibril ya hau jirgi ya bar ƙasar nan, har na yi jinyar na gama be taɓa kirana ba sai dai mahaifinsa da wasu Sisters na sa sun zo duba ni da kuma step mother ɗinsa, Mahaifinsa ne ya fi nuna min kulawa da damuwa, su kan kamar daman sun zo ne by force.

Bayan an sallameni da kwana biyu Salima ta fara shirin zuwa makaranta, ni kuma Daddy ya hana ni da sunan wai ba zan koma ba sai na ƙara jin sauƙi, ni kuma ban musa musu ba na amince, ina ji ina gani Salima ta koma makaranta ni ina nan.
  
Yana lura da yanayi na sosai, har ta kai wata rana ya kirani a ɗakinsa ya tambayeni ko dai bana son auren ne, sai an kasa amsa masa, ya yi min nasiha akan haƙuri da halin Jibril wai daman yasan za a samu haka saboda baya son auren kwata-kwata babu zancen aure a gabansa, wannan yarinyar ce kawai yake kulawa ita kuma ba ƴar mutunci ba ce zaman kanta take wannan dalilin ya saka mahaifinsa ya ƙi yarda ya aureta, a ranar yake labarta min cewar Jibril ne ya hana na koma makaranta wai ya ce be bada izinin na koma makaranta ba.

Ranar na yi kuka sosai har sai dai na raina kaina, mutumen da ba zai iya kirana ya tambayi tafiyata ba shi ne zai ce bada umarnin kar a barni na koma karanta kuma a ƙyaleshi saboda kawai yana taƙama da kuɗi.

A haka na kwashe wata shida a ban koma makaranta ba, idan kuma nunawa Momy ina son anje gida gurinsu Inna sai ta ce min ba haka ba, wai ba zata bari na tafi bada izinin mijina ba. Tun daga ranar da aka ɗaura min aure da Jibril duk wata sai Alhaji Bashir Makama ya aikowa da Momy kuɗi ya ce a bani amman bata taɓa bani ko naira ba, bata ma taɓa faɗa min ko nawa ba ne tana dai faɗan min ya aiko saboda kawai na yi masa godiya.

Tun da Jibril yasa ƙafarsa ya bar ƙasar nan be sake waigo Nigeria ba, kuma be taɓa ɗaukar waya ya kirani ba, wani daga familynsa be taɓa zuwa da sunan ganina ko duba lafiyata ba. 
Da wannan baƙinciki na ke kwana na ke tashi ban taɓa nunawa kowa ba, sai dai hakan be hana Daddy damuwa ba, wata rana bayan na gama haɗa abun karyawa mun sai ya aiko yana kirana, ko da na shiga sai na samu Momy tare da shi, guri na samu na zauna na natsu ina ta sauraren abunda yake faɗa min.

“Na gaji da wannan halin na Jibril, ba zai yiyu ya ce ba zaki koma makaranta ba, kuma baki tare ɗakinki ba, tun da ya tafi be ma kira ya tambayi lafiyarki ba, dan haka na faɗawa mahaifinsa idan ba zasu iya tanƙwara ɗan su akan abunda suke so ba, ni ba zan cutar da ƴata ba, na faɗawa mahaifinsa idan har yana ganin rabuwa da ke shine maslaha tam mu muna maraba, kuma ina fatar wannan hukuncin ya yi miki”

Kamin na ce wani abu sai Momy ta yi karaf ta ce.

“Haba Alhaji yaran zamani ai sai an yi haƙuri, karka yi maganar raba auren su ko shekaran jiya na tambayeta ta faɗa min ita tana son mijinta, kawai ka yi ta musu addu’ah”

Kallo ɗaya na yi mata na ɗauke, wata ƙila tana min haka ne saboda ni ba ƴar ta ba ce, Daddy kan tuni ya gama gamsuwa da bayaninta, jiki a sanyaye na taso na fito daga part ɗin Daddy.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page