SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 1

SILAR GIDAN AIKI
CHAPTER 1
Yarinyace da bazata wuce 13 years ba na hango tana Tafe, rik’e da Yar jakanta a hannu tana Kuka gwanin ban tausayi, Ga uniform dinta duk ya 6ace saboda ruwan da ake, kuka takeyi sosan gaske me ratsa duk wani zuciyar Mai tausayi, Ahankali ta karaso gidan da take aiki ta buga gate taji a kulle, samun waje tai daidai gate din ta tsugunna har sanda, Tafara tinani barkatai, sanyin ya ratsa jikinta sosai abun tau say I +

Ruwan ya dauke kenan Sannan me gadi yazo zai tafi Sallar la’asar sannan ya bude Kofar

Yana bude kofar har ya tsorata saboda yanayin daya ganta be azama mutun bane, amma yasan ba kowa bane illa Nazeefa, nan Take yace”_ Subhanallah…Nazeefa nazeefa, a tsorace ta mik’e tace Baba me gadi Ina wuni

Ya amsa da lafiya lau Ashe Kin taso shine ko ki buga gate, Muryanta yai kasa kasa saboda kukan da tasha tace” inata bugawa naji baka budeba sai yasa na zauna anan, Kallonta yai cikin Tausayi yace” kiyi hakuri ki shiga ciki, Ta kalleshi tace” Hajiya nanan ne? Yace” tananan bata dade da dawowa ba

Gabantane ya fadi tace” OK, Shiga gidan tai da Sallama tun daga window Hajiya ke kallon Nazeefa, Tace Wannan yarinyar!!!Hajiya ke hangota ta window tace wannan yarinyar kamar mayya sai na gyara mata zama tunda bazata bi umurnin da nace mata ba +

Nazeefa tana shiga dakinta direct ta wuce ta chanza kaya, Jikinta in banda rawan Sanyi ba abun da yakeyi, Pallow ta fito tai Addu’a Sannan ta nufa dakin hajiya Asma’u

Kallonta tai daga Sama har kasa, A ranta tana mamakin taurin Kan karamar yarinyar nan da duka shekarunta befi 13 ba, Nazeefa tsugunnawa tai a gabanta tace Hajiya na dawo akwai wani aikin ne, Kallonta tai taga bakinta na rawa alamar Zazzabi tadan tausaya Mata tace” ba Wani aikin jedai ki huta, a ranta tace” Alhamdulillah

Mik’ewa tai ahankali hajiya dai ta kalleta tace” zo ki amsa maganin nan, Tazo ta amsa paracetamol guda 2 tace kisha saura kuma taurin kanki yasa ki jefar,

Nazeefa tai murmushi tace” Hajiya zansha in shaa Allah, hajiyar batace Mata komai ba, itakam nazeefa tasa kai ta fita ranta a sanyeye at least tadanji dadin yanda Hajiya ta amsa Mata harda Bata magani, lalle kam hausawa sunyi gaskiya in jumma’a zatai kyau tundaga laraba ake ganeta

Nazeefa ta fito kenan ta shiga kitchen ta dakko pure water zatasha magani kenan Saiga *Mubin* first born din Hajiya da a kalla zekai 20years, hararta yayi yace” Dan ubanki ban hanaki zuwa kitchen dinnan ba, kalleki kazama dake zaki dinga taba mana kayan kitchen,

sunkuyar dakai tayi tace” kayi hakuri, yace would you keep quite ko Sai nayi ball dake, da yake tanadan jin turanci yasa tai sumi Sumi ta fita daga kitchen din

Tana fita yabi bayanta da kallo yace” Shigiya aranshi kuma yace idan fa ta kara girma za’ai hot beb anan, tsaki yayi ya bude fridge ya dakko lemon ya nufa dakinsa

**********

Nazeefa tana shiga daki ta kulle kanta, Kuka ta fara me taba zuciya gashi ba wanda zai lallasheta hakanan taci kukanta ta gama, magrib nayi tai abun da zatai tasha magani ta kwanta tun 8:00PM
Washe gari tun asuba Nazeefa ta tashi ta daura ruwan zafi, Tana cikin kitchen ne sai ga Hajiya ta shugo ta dubeta tace” Har kinji saukin ne? +

Kallonta tai idonta a kumbure alamar taci kuka tace” Eh Hajiya naji Sauki, Hajiyar ta ce” to Allah Kara sauki nan dai ta Dan kakkama mata Sukai gama break fast ta shirya zata tafi L.E.A primary school da aka sata

Tafito da sauri a harabar gidan taci Karo da mubin Robar abincin data boye tun jiya da aka dafa taliya da miyar manja da yasha kifi Ya subuto a hannunta ya fadi Sai kan kayar Mubin

Faeeza da faee kannanshi suna zaune a cikin motor suka hango dramar da akeyi, Faeeza tace tab yau yarinyar nan ta shiga uku kuwa, Faeez ya harareta yace to sai me? Kawai mutun be mistake a rayuwa? Faeeza tace to kaimun shuru malan

Mubin Yana ganin kayanshi ya baci Ya saukar mata da wasu zafafan Mari a fuskanta, Yaja hijab dinta yace” ke bakida hankaki KO? See what you did to me this morning,

Kuka kawai Nazeefa ta fara dan marin ya shigeta sosai, Batasan Sanda tace Sorry ba, Ya daka Mata tsawa yace Sorry for your self! Ya shiga daki

Jin hayaniya yayi yawane Hajiya ta fito Dan ganin meke faruwa, a bakin kofar shiga daki taci karo da mubin, Ganin kayanshi a 6ace yasa tasan me ya faru

Mubin ko saboda bacin rai yace” Mum kingani ko Wallahi sai na balla yarinyar ne, be jira yaji me zatace ba yai shigewarsa dakinshi ya chanza kaya, Nazeefa kuma tana tsaye a wajen ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, Hajiya ta karaso wajenta tace sai ki shiga motar ya rage miki hanya Dan nasan kunyi latti dukanku,

Kamar zataje bazata shiga, Sai kuma tai shuru ta tunKaro motor, sit din baya ta bude taga Gefe books din shine dayan site din kuma kannanshine twins *Faeeza da faeez* Dan haka ta bude sit din gaba tai zamanta,

Faeez face sorry Nazeefa, ta juyo da jajayen idonta ta kalleshi tace” bakomai Dan Allah ka tayani bashi hakuri,

“Faeez yace karki damu”

Mum na tsaye ya fito fuskarshi a murtake yace Hajiyata sai mun dawo, Tace to Allah ya tsare ya kikaye hanya yace Ameen,

Key yasa ya bude motor

Ya zauna kenan ya duba right hand dinshi yaga nazifa a zaune, Yasan aikin Hajiyarsune Gyada Kai yayi yace OK, bece komai ba me Gadi yazo ya bude masu get ya fita ya saita hanya

Faeez ne yace” yaya please kayi sauri munyi latti Wallahi, Harararshi yayi ta cikin Madubi, Sai ya gama bakinshi yai shuru,

Seda yazo bakin titi yai parking Ya kalle Nazeefa yace” to malama Sauka,

Tai karfin hali tace” AI makaranta akace ka kaini, Wani Shu’umin dariya Yayi yace” makaranta ko?

Ta daga Kai tace Eh

Yaga alamar da gaske ba sauka zatai ba yace” Dan ubanki ki fitan mun a mota, jin ya zage ubantane tai zuciya tace motor banza, Ta fita ta buga kofar da Karfi!!

Gaba dayansu binta da ido sukai

Mubin ko a ranshi yace” A sauka lafiya

Yan biyu kuma basuji dadin abunda yai mataba gaskiya, Nan ya seta motarshi ya fara gudu Dan both of them sunyi latti Dan shi ma kanshi yanada lectures 7:30 gashi yanzu 7:50 yaushe yaje ya sauke kannanshi balle har ya wuce dan haka ya Kara gudu da karfi

*********

Nazeefa kuma tunda aka ajiyeta ta share hawayenta KO banza yau ta gomama Mai, tafiya take a kasa abun tausayi gashi slippers ne a kafarta gashi garin anyi ruwa kafar tai datti sosai, Ta kalle kanta Tace” Ya Allah ka rabamu da wahala Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page