MAKOTAN JUNA CHAPTER 6

MAKOTAN JUNA

CHAPTER 6


Adnan sai da ya fara Ciro kudi a bank kafin ya nufi wajen da ake siyar da kujeru dan so yake yayi furnishing gidan ko gidan ya d’an haska.
+

Masu d’an saukin kudi ya siya ash en red ya siyi labulayen dasuka dace da kalar kujerar.

Daga nan ya wuce inda ake siyar da kayan kallo ya siyi plasma maidaidaiciya da sauran kayan amfani na gida irinsu hearter bokitai kayan abinci gas cooker generator k’arami da sauransu
1

A katon akori kura aka loda masa kayan ya shige motarsa a kori kuran na binsa abaya.

Ita kuwa Zara wahallalen bacci ne yayi awon gaba da ita ak’asan tiles d’in d’akin bata san tsawon lokacin da ta kwasa tana baccin ba har sai dataji muryar Adnan nayiwa mutane umarni dasu shigo da kaya.

Mik’ewa tayi daga kwancen da take da sauri tana yamutsa fuska sakamakon ko’ina na jikinta dake mata ciwo.

Mik’ewa tayi tana cije lebb’e ta nufi k’ofar d’akin ta bud’e dan ta ga mai ake ta shigo dashi.

Had’a ido tayi da Adnan dake tsaye a gefe ana ta shigo da kayayyakin da ya siya

Hararar da ya galla mata ne yasa ta koma ciki da sauri tana rufo k’ofar dan yanzu tana bala’in shak’arsa da tsoronsa

Zub’ewa ta k’arayi a k’asan tiles d’in tana rik’e cikinta dake k’ugin yunwa.

Cikin awa d’aya da rabi Adnan da wayanda suka kawo masa kayan suka shirya palon suka saka komai a muhallinsa tuni gidan ya haska kamar na amarya.

Nan da nan Adnan ya kamo tashan daya saba ji ya ware kid’a a gidan kamar bashi da wani matsala dan shi mutum ne mai san holewa.
1

Sai daya gabji rawa ya gaji ya zub’e akan kujera yana maida numfashi

Mik’ewa ya k’ara yi sakamakon yunwar da yake ji ya nufi d’akin da Zara take.

A kwance ya sameta ta rik’e cikinta sai hawaye take
Wani mugun tsawa ya daka mata yana “ke dalla tashi ki d’orawa mutane abinci dan bani da kudin da zan ringa yin take away kullum ga kayan abinci can na siyo babu abinda babu har tukunya ki tashi ko jollof d’in taliya ne ki d’ora mana zan shiga wanka ki tabbata kafin na fito kin gama”

Zara mik’ewa tayi dak’yar sabida rawan da jikinta yake yi tace “wlh Ad ban iya girki ba sai dai idan indomie zan dafa maka”

Wani mugun harara Adnan ya zabga mata yace “aikuwa yau zaki koya dan bazan yi tolerating nonsense ba ace babu abinda kika iya sai iskanci ke yanzu ahaka Ameer ya zauna dake batare da kin iya girki ba tab ba zai yiwu ba na baki minti goma sha biyar ki tabbata my food is set kafin na fito”

STORY CONTINUES BELOW


Daga haka ya juya ya bar d’akin ya bar Zara da zubar hawaye

Duk da jirin da take ji iska na d’aukar ta ahaka ta mik’e ta nufi tsakar gidan inda kitchen yake

Babu abinda zata nema dan komai Adnan ya siyo har da greter gas d’in ta kunna ta d’ora ruwa ta zabga mishi farin mai maggi tumatir d’in leda curry da gishiri ta rufe.

Ta farka kwallin taliyar ta zaro guda d’aya ta k’ara bud’e tukunyar ta kakarya taliyar aciki ta zuba sardine guda biyu ta rufe ta koma bakin k’ofa ta zauna tana jiran ya dahu ta juye dan ji take kamar taci babu sabida yunwar da take ji.

Taliyar ko nuna baiyi ba ta sauke ta d’auraya plate guda biyu ta zuba mishi nashi itama ta zuba nata ta d’auka ta nufi palon jikinta sai rawa yake

Ajiye mishi tayi a tsakiyar palon ta d’auki nata ta koma d’aki tun kafin ta zauna ta d’iba da hannu Tana kaiwa bakinta sabida tsabar yunwa da takeji.

Aikuwa k’asa had’iyewa tayi sabida gishirin da yayi yawa gashi bai dahu ba ga karnin kifin gwangwanin da ta saka

Rufe ido tayi ta had’iye ta k’ara kai hannu da zumar deb’o wani ta kai bakinta wani irin Amai ya kwace mata amai take bilhakki dan Rabin aman ruwa ne sabida babu abinci a cikinta a cikin wanan halin Adnan ya banko k’ofar da plate d’in abincin a hannunsa yana mata wani irin kallo duk da ba kallonsa take ba amanta kawai take yi.

Adnan shiga d’akin yayi ya dire plate d’in agabanta duk da har lokacin bata d’ago ba kakarin aman kawai take

” Kema kanki kin kasa cin guban da kika dafa da sunan abinci ballantana ni kinsan Allah koda zaki amayo kayan cikinki wanan abincin shine na darenki idan shima bakici ba shi zaki ci da safe dan wlh bazaki ringa janyomin asara ba common taliya jollof kin kasa dafawa”

Zara d’ago da kanta tayi dak’yar Tana kallonsa sai numfashin wahala take saukewa.

Adnan kuwa ya zabga mata harara ya ja tsaki ya bar mata d’akin dan ko kallon minti biyar baya so yayiwa Zara.

Kitchen ya koma ya dafa indomie mai rai da lafiya yaci ya koshi ya koma d’aki ya shirya cikin kananan kaya a lokacin ana kiraye kirayen sallar magriba sai da yayi alwala ya fito ya tsaya a massallacin unguwar yayi sallah ya d’auki hanyar gidan abokinsa Safwan.

1

A zaune suke a palon Safwan Safwan ya zira masa ido bayan Adnan yagama kora masa jawabin abinda ya same shi babu abinda ya b’oye masa dan amininsa ne tun secondary school kuma halinsu yazo d’aya.

“Kayi kuskure Adnan mai ya kai ka huld’a da matar Aure matar Auren ma matar mak’ocinka”

Ajiyar zuciya Adnan ya sauke yace “bazaka gane ba Safwan wlh Zara nan shaidaniya ce ko Kaine nasan u would fall for her ni ba wanan ba Safwan dan Allah kayi min k’ok’ari na samu aiki a companynku dan bansan Yanda zan fara rayuwa idan sauran chanjina suka kare ba”

“Zan maka k’ok’ari insha Allahu tunda ga takardunka nan ka Riga da ka kawo yanzu ya zakayi da cikin dake jikin nata tunda yak’i zub’ewa”

“Ai yanzu ina bar nan wani maganin zan kuma zuwa na siyo na kai mata yarinyar kamar mayya tak’i tafiya gidansu ta mak’ale min da wallahi guduwa nayi niyyar yi”

Safwan mik’ewa yayi yana gyara zaman face cap d’in dake Kansa dan shi bashida aure holewarsa kawai yake cewa yayi

“Ya kamata kam idan bahaka ba abun ne zai maka yawa nifa club zani zan biya na d’auki Sara dan yau chasun mai Zafi ne”

Adnan mik’ewa yayi shima yace “nima bari na biku ko na samu mai deb’e min kewa da banida wani damuwa amma wlh zuwan yarinyar nan rayuwata ya zame min matsala”

STORY CONTINUES BELOW


Safwan kanne masa ido d’aya yayi yana “that’s kwartanci for u baka san Zata zame maka matsala ba a lokacin da kake enjoying d’inta sai yanzu da abubuwa suka kwab’e maka naso ina wajen mijin nata ya kama Ku hhhhhhhh”
1

Adnan duka ya kai masa a kafad’a yayi sauri ya k’auce yana Dariya ahaka suka fice daga gidan suka hau motacinsu suka d’auki hanyar club.

Adnan a ranar ko gida bai koma ba dan tuni zuwansa club ya saka shi nishadi yana tunanin tamkar lokacin da yake saurayine dan ga ‘yan mata iya ‘yan manta sai wacce ya zab’a ya darje.

Zara kuwa tunda tayi amai ta koma gefe ta k’ara kwanciya dan bata da kwarin da zata zauna ko kad’an.

Tana jin lokacin da Adnan ya fice daga gidan ganin bai dawo ba har 8:30 yasa ta rarrafa ta fito dan ta fara ganin bibiyu sabida yunwar dake nukurkusarta.

Indomie da Adnan yaci ya rage tagani a palon tayi sauri ta d’auka tayi mishi kwasa d’aya ta danna a bakinta

Sid’e plate d’in tayi jikinta na rawa dan kamar k’ara ingizo yunwar tayi a hankali ta mik’e tana dafa bango ta nufi kitchen tana zuwa ta d’ora ruwan zafi

Ta zauna a k’asan kitchen d’in ta fara hargitsa kayan abincin tana Neman kayan shayi.

Wani nanauyan ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da tayi tozali da kayan shayin aikuwa jiki na rawa ta had’a shayi mai kauri ta samu slide bread guda goma ta fara kora shayi da bredin kamar wacce bata tab’a cin abinci.

Luckily kuwa har ta sha shayin bataji tana jin amai ba sai dai gyatsa da ta ringa yi kamar aman zai taso mata sai kuma taji ba aman bane.

Sai a lokacin ta dawo dai-dai ta mik’e ta bar kitchen d’in ta koma d’akin Adnan ta shige band’aki tayi wanka tare da d’aura alwala dan rabonta da sallah tun lokacin da take gidan Ameer.

Kayanta ta mayar jikinta dan ta hargitsa kayan Adnan gabad’aya babu kayan ta a ciki sai a lokacin ta fara tunanin inda Adnan ya kai mata kayanta.

Ahaka tayi sallah da k’aramin mayafi sallar ma shap shap tayi ta kwanta a katifar d’akin sabida wani irin bacci da take ji aikuwa tana kwanciya bacci ya d’auketa.

Cizon da Sauraye suka ringa kai wa fatarta ne yasa ta bud’e idonta.

Da sauri ta maida idonta ta rufe sakamakon duhun da ya mamaye d’akin dan 12 aka d’auke wuta kirjinta ne ya hau bugawa da k’arfi data ji haushin karnuka ko ta ina gashi babu waya a hannunta ballantana ta haska ta kuma ga k’arfe nawa duk a tunaninta Adnan ya dawo Ashe bai dawo ba ita kad’ai ya bari a gidan.

Baccin da Zara bata koma kenan ba sabida tsananin tsoro sai da aka fara kiraye Kirayen sallar asuba aka dawo da wuta da sauri ta mik’e daga kwancen da take ta fito daga d’akin ta nufi hanyar waje dan taga ko gidan a bud’e yake.

Aikuwa a bud’e taga gidan tayi sauri ta saka sakata wani tsoron na k’ara rufeta

Aguje ta koma ciki ta kulle k’ofar palon ta shige d’aki tana fashewa da kukan wulakancin da Adnan yayi mata wato idan ma saceta akayi ko kasheta akayi bai damu ba.


Sai da gari ya fara wayewa bacci ya saceta tana sauke ajiyar zuciya.

Adnan kuwa sai k’arfe goma ya farka da shi da Linda d’in data taya shi kwana a gidan Safwan mik’ewa yayi da sauri daya tuna Zara ya fad’a band’aki yayi wanka a hanzarce yayi alwala yafito yana iddar da sallah ya d’auki mukullin motarsa ya fice a hankali dan kar ya tashi lindar dake ta munshari.

Ko kallon d’akin da Safwan da buduruwarsa suke baiyi ba ya fice daga gidan da sauri.


Yafi k’arfin minti goma yana kwankwasa gidan ba’a bud’e ba hakane yasa hankalinsa yayi balain tashi ya fara tunanin ko dai wani abune ya sameta nan kuwa Zara baccinta take bama tasan yana buga gidan ba.

STORY CONTINUES BELOW


Adnan dutse ya d’auko ya cigaba da bugawa dan idan dai yayi amfani da dutse ba’a bud’e ba haurawa kawai zai yi dan duk da baya san zama da Zara bayaso wani Abu ya sameta.

Zara kuwa a firgice ta mik’e da taji Yanda ake buga gidan ta hantsilo daga kan katifar tayi tsakar gidan da gudu.

Wani mugun kallo Adnan ya fara watsa mata dayaga alaman bacci ne ya hana tazo ta bud’e k’ofar.

Zara kuwa juyawa tayi ta nufi palon da ko magana batasan yi sabida yawun data tsinci yana taruwa a bakinta.

Adnan fusgota yayi yana “ke wacce irin dabba ce zan ringa kwankwasa k’ofa ki k’i bud’ewa”?

Zara ido kawai ta zuba masa hawaye na taruwa a idonta Dan ko a mafarki idan akace mata Adnan zai iya wulakanta ta haka karyata wa zatayi Ashe duk kalmomin soyayya nan da yake mata yace zai iya rabuwa da kowa akanta Ashe karya yake abun takaici ma ko halin da take ciki bai gani ba yake mata rashin mutuncin daya ga dama.

Lumshe idonta tayi hawaye suka hau sauko mata a karo na farko data fara tunanin irin kuskuren da ta tafka a karo na farko dataji ta fara Dana sanin abinda tayi a karo na farko data fara jin tsanar Adnan na ratsa ta.

Adnan kuwa tsaki yayi ya saketa tare da nufar palon.

Zara kuwa sai da ta ci kukanta ta koshi itama ta nufi palon.

Ko kallonsa batayi ba ta shige d’akin da babu katifar

Adnan kuwa ya bi bayanta da ya k’ara girma da kallo yana dasa wani Abu a ransa dan d’an rik’e tan da yayi yaga Yanda tayi wani fresh kirjinta ya ciciko sosai ko Dan bata bud’e bakinta bane shiyasa yaga tayi mishi wani irin kyau.

Mik’ewa yayi ya k’unna kayan kallon tare da kamo tashan daya saba ji aikuwa ya fara kad’a kai kamar bashida wani matsala take ya fad’a kogin tunanin abinda ya dace yayi idan bai samu aikin companyn daya sa Safwan ya samo mishi ba, aikuwa tunanin daya fad’o masa na ya zama DJ ne yasa ya mik’e da sauri ya zauna dan yasan ba laifi DJ suna samun kudi indai za’ayi occasion tuni ya fara lissafin kudinsa dake bank zasu ishesa ya siyi manyan speakers da kayan kid’a har kudinsa ma suyi Saura sosai wani irin murmushi ya saki yana jin wani sanyi na ratsa masa zuciya dan gani yake ya samo mafitar Rabin matsalarsa yanzu Saura cikin jikin Zara. 2

Mik’ewa yayi da sauri ya d’auki mukullin motarsa yayi waje.

Bai tsaya ko’ina ba sai wanan pharmacy d’in da ya siyi maganin zubar da ciki.

Sai da ya k’ara bawa nurse d’in kudi bayan ya mishi bayanin cikin bai zub’e ba sabida aman da Zara takeyi allurai ya had’a ya hau motar Adnan suka nufi gidan dan ya mata alluran tunda Adnan ya Riga da ya biya shi.

A lokacin da suka isa gidan a kwance ya tarar da Zara a palon tana ta bacci dan da alama cikin nata bacci yake sata.

Kofin data sha shayin ya fara d’aukewa ya d’aura fuskarsa ya fara tashinta

Nurse d’in na zaune a one seater yana kallon TV dake kunne

Zara bud’e idonta tayi tana kallon Adnan daya d’aura fuska a hankali ta tashi daga kwancen da take ta zauna tana kallon Nurse d’in dake zaune

Adnan cikin d’aurewar fuska yace “ki tashi za’ayi miki allura”

Zara bata ce masa komai ba ta nufi band’aki dan ta zubar da yawun bakinta sai da ta zubar ta dawo ta kau da kanta tace “alluran mai zai min”

“Allurar zubar da ciki zai miki dan na fad’a miki ban shirya haifen d’an shege ba”

“Bismillah” Zara tace tana nufar d’akin daya zame nata dan itama zubar da cikin shi zai sa ta rabu da wanan mugun laulayin datake fama dashi daga nan ta san nayi dan bata jin zata iya cigaba da zama da Adnan yana wulakantata.

STORY CONTINUES BELOW


Adnan mamakine ya rufe shi dayaga ta yarda a zubar da cikin

Da sauri yacewa Nurse d’in yabi bayanta ya mata alluran.


Allura biyu yayiwa Zaran ya bata wani tabs kananu guda biyu yace ta kora

Zara kuwa tun kafin ya bar d’akin ta kora tabs d’in aikuwa ta hau kelaya amai.

Kakarin amanta ne yasa Adnan ya shiga d’akin da sauri ya rik’e ta sai da ta gama aman ya gyara wurin ya goge mata jiki ya d’aga ta ya kaita d’akinsa ya dawo wajen nurse d’in daya Dade da dawowa Palon ya tsaya.

Nurse d’in ce mishi yayi kar ya damu cikin zai zube zuwa anjima da wuya ayiwa mutum allurar ciki bai zub’e ba ko da cikin ya kai wata hud’u.


Adnan sai daya maidashi ya dawo gidan.

Direct d’akinsa ya nufa yana shiga yaga Zara baccinta kawai take hakan ne yasa yafito ya nufi kitchen ya dafa musu jollof din taliya dan yana san taliya jollof.

Sai da yaci ya koshi ya ajiyewa Zara nata ya koma d’akin ya k’ara wanka yayi sallar azahar ya dawo Palo ya zauna ya cigaba da tunanin sana’arsa ta Dj.

Adnan lek’en Zaran ya ringa yi yaga ko ta farka amma har k’arfe uku bata tashi ba har sai da akayi sallar La’asar ta farka sakamakon wani mugun yunwa da take ji.

Adnan kallo ya bita dashi har ta zauna dan duk a tunaninsa zaiga tana kukan ciwon Mara yasan daga nan cikinta zai zube amma ina garau ya ganta

Tambayarta yayi da bata jin ciwon Mara ta gyad’a masa kai

Adnan yace kila anjima zatayi ciwon maran ga abincinta nan ta zauna taci.

Zara tas ta cinye abincin tana gama shan ruwa ta fara kelaye amai.

Wasa wasa sai da aka Samu kwana hud’u Adnan na zuba ido yaga cikin Zara ya zube amma ina ko alama

Ahaka ya cigaba da kwaso mata magungunan zubar da ciki da allurai amma ina ciki bai san suna yi ba.

Dan wani mugun laulayi Zara take yanzu in banda amai Tara yawu da zazzabin da take kwana dashi babu abinda take yi da kanta ta fara rok’on Adnan a zubar mata da cikin dan babu abinda take iya ci sai shayi da bredi.

Hakane yasa Adnan kaita wani k’aramin prvt hospital ya gayawa likita abinda ke tafe dasu Likita sai da yayiwa Zara scanning ya mata gwaje gwaje yace bazai iya zubar da cikin jikin Zara ba
dan zubar da cikin dai-dai yake data rasa ranta.

Zara tana jin ya ambaci mutuwa ta fice waje da sauri akan dole Adnan ya baro asibitin zuciyarsa fal da bak’in ciki dan yasan dolensa ya hakura Zara ta Haifa masa shege.

Ahaka Zara ta ringa laulayi Adnan ya hakura yana kula da ita dan a halin da take ciki sai ana taimaka mata dan wani zubin ma shi zai mata wankan ga bacci da take yawan yi wani irin fari tayi ta cicciko tayi fresh hakane yasa Adnan ya mata developing sabon feelings zaman Nasu ya dai-dai ta duk da Zara ta kanta take bazata iya wani abun ba Tasan dan jikinta Adnan ke kula da ita dan har kayan sawa ya sisiyo mata duk dare sai ya hayeta ko tausayinta bayaji. 1

B’angaren Ameer kuwa hankalinsa a kwance yake bashi da wani matsala daya wuce soyayyar Aliya dake dawainiya dashi dan sau uku kenan yana zuwa gidansu da sunan yaje ne su gaisa amma baya wani samun fuska a wajenta bayan gaisawa da sukeyi sai dai ya gama kame kamensa ya taho hakane yasa masa zullumin Yanda zai tunkari Aliya yace yana santa har ta amince ta aure shi Alhaji Abubakar kuwa yana ganin mutuncinsa sosai gani yake sabida tausayin Aliya yasa Ameer ke zuwa ganin Aliya inda shima yaji inama Ameer d’in ya Auri Aliya dan ya ga dacewarsu sosai dan ya hango nagarta da kyawawan halin Ameer.
1

B’angaren Aliya kuwa tuni ta dage da addu’a ta cire komai aranta ta rok’i mahaifinta akan zata koma makaranta islamiyya akan zaman nan da take yi haka har ta gama iddarta duk da tasan babu wani idda akanta tunda cikin jikinta ya zub’e amma gwara dai tayi iddar.


Mommy Hauwa kuwa tunda ta k’ara kiran Ameer sau biyu yace mata har a lokacin bai ji labarin indai Zara take ba ta hakura ta barwa Allah ta dage ta cigaba da addu’a akan Allah ya kare mata Zara duk a inda take dan ranaku d’ad’ayane bacci zai d’auketa batare da tayi mafarki da Zara ba……………….Kafin mu cigaba da labarin bari muji ma waye Adnan mene asalinsa


Adnan d’a ne ga Margayi Alhaji Sulaiman mai Turare Alhaji Sulaiman mai Turare haifaffen d’an Maiduguri ne tun suna yara mahaifinsu ya rasu Shine babba a gidansu Mahaifiyarsa Hajiya Amasil ta masifar iya had’a turaruka masu kamshi shine sana’ar data rik’a take ciyar da marayun ‘ya’yanta har suka girma

Alhaji Sulaiman shima tun yana yaro yake taya mahaifiyarsa siyar da turaruka har ya girma ya kai ga su bud’e shaguna sabida Yanda Allah yasa musu Albarka a sana’ar tasu da Mahaifiyarsa ta rasu kanensa ne suka cigaba da had’a turarukan har sukayi Aure .

Da wanan sana’ar Alhaji Sulaiman yayi Aure ya Auri wata Asmau customer d’insa dake zuwa tun daga Niger siyan turarruka a wajensa.

Suna da shekara goma da Aure suka haifi Anwar Sai da Anwar ya shekara kusan shidda suka haifi Adnan daga  Adnan sai Aliyu Sai Aminatu da auta Amatullah.

Suna cikin rufin asiri da sutura ta ubangiji dan Alhaji Sulaiman baza’a sa shi sahun masu kudi can ba ba kuma za a sa  shi sahun talaka ba dan yaci k’arfin bukatun gidansa.

Ahaka rayuwa ta ringa tafiya Alhaji Sulaiman na tafiyar da gidansa akan tarbiyya matarsa  na taimaka masa dan duka yaran suna zuwa daga boko har islamiyya Sai dai duk cikin su Adnan ne ya fita Zakka dan baya san makaranta a rayuwarsa baya  ta shi rashin lafiya Sai za shi makaranta  idan kuwa aka tilasta masa yaje sai ya dawo ya shirga wata karyar tun Alhaji Sulaiman na dukansa har ya hakura dan yaga alamar duka bazai sa Adnan ya ringa fashin zuwa makaranta ba  har gwara makarantar boko wani zubin ana samu yaje sau uku a sati islamiyya kuwa idan an samu shine zai je sau biyu awata ahaka  ya  ringa wasa da karatunsa ana zabga masa repeating har kaninsa Aliyu yazo ya Riga shi gama secondary school da yake duk suna da k’ok’ari tuni yayansa  Anwar ya kusa gama degree d’insa 

STORY CONTINUES BELOW


Alhaji Sulaiman ganin irin hazak’ar Anwar yasa ya d’ora shi akan harkar kasuwanci nan da nan shima Allah ya sa mishi Albarka duk da yana karatu hakan bai shafi kasuwancinsa ba

A cikin wanan halin ya had’u da wata yar level 2 Hindatu haruna ya aureta.

Adnan kuwa yana ganin Anwar yayi Aure yace zai koma gidan da zama dan aganinsa acan zai fi sakewa babu mai takurasa akan lailai sai yaje makaranta


Anwar da k’yar ya shawo kan Alhaji Sulaiman ya yarda akan Adnan ya zauna a gidansa dan aganinsa zai iya samu ya shawo kan Adnan ya rage shashanci ya maida hankalinsa yayi karatu.

Tunda Adnan ya koma gidan Anwar ya bud’e sabon iskanci ya fara bin abokanan Banza babu abinda ya sa agaba Sai shashanci daga yaje wancan partyn Sai dai yaje wancan partyn da k’yar Anwar ya samu ya shawo kansa ya cigaba da zuwa wani secondary school dake unguwarsu ya cigaba daga ss 2.

Hindatu kuwa matar Anwar a lokacin da Adnan ya dawo gidansu da zama da farko k’i tayi ta ringa yiwa  Adnan rashin mutunci Tana hanasa abinci Sai da Anwar ya tsawatar mata ta shiga hankalinta.

Adnan kuwa dayake dan duniya ne biyayya ya ringa mata wani zubin har yana wanke mata kayanta na sawa a hankali shak’uwa ta fara shiga tsakaninsu Wanda ya kai ya kawo Hindatu bata da burin daya wuce ta kasance da Adnan suyi hira suna labaran duniya Dan Adnan akwai saurin sabo da farinjini gashi wayaye dan gayu.

Hindatu a hankali ta fara jin kaunar Adnan a ranta inda Adnan kuwa bai ma san halin da take ciki ba dan ko bai shiga b’angarensu  ba ita zata shigo b’angarensa ta kai masa abinci daga nan tace su buga game dan Anwar bai Fiye zama ba sabida tafiye tafiyen da yake yi saro kaya.

A hankali Adnan ya fara wayar gari da matsanacin sha’awar Hindatu sabida irin shigar tsiraicin da takeyi tazo d’akinsa dan ko game d’in sukeyi idan ta cinye shi tayi ta fad’awa jikinsa kenan Wanda hakan ke d’aga masa hankali a karshe Sai yayi masturbating yake samun relief.

Hindatu itama da shaidan ke buga mata ganga Tana sane take irin shigar da take yi dan taja hankalin Adnan dan babu abinda takeso sama da ta kasance da Adnan ganin duk k’ok’arin ta Adnan baya gane wa yasa wataran ta had’a plan Sai da ta shiga wanka ta fara kwalla ihu daga band’akin Adnan da shigowarsa kenan dan ya dau abincinsa aguje ya nufi bandakin yana shiga Hindatu ta rungume shi gam babu komai a jikinta.

Adnan kuwa ko’ina na jikinsa ne yafara rawa sakamakon jin naked skin d’inta ajikinsa.

A gigice ya rungume ta shima Hindatu kuwa ta fara shafa shi inda suka dangana da d’akinta daga nan mai afkuwa ta afku tundaga lokacin Hindatu ta lalata Adnan ya bud’e ido da Neman mata ahaka ya zanna waec ya wuce da pass Anwar ya samo masa Admission da cuwa cuwa ya fara jamia.

Adnan yana shiga level 2 Allah yayiwa Alhaji Sulaiman rasuwa ta hanyar rashin lafiya dayayi ta fama dashi.Bayan shekara biyu da rasuwarsa Mahaifiyarsu ta Auri wani d’an uwanta ta koma Niger da zama bayan anyi Rabon gado yaranta gabad’aya suka koma hannun Anwar da zama da zumar idan anyi hutun makaranta zasu na zuwa Niger hutu.

Anwar babu Yanda baiyi da  Adnan ba  akan ya ringa kasuwanci yana juya kudin da suka Samu na gado Adnan yak’i dan aganinsa shi ba yaro bane yanzu yasan Yanda zaiyi da Kudinsa ahaka ya ringa wulakanta kudinsa ta hanyar Neman mata Banza ya ringa kashe kudi yana hade haden party.

Aliyu kuwa da sauran kanensa Aminatu da Amatullah gadonsu na hannun yayansu Anwar yana juya musu kudinsu  da yake shima Aliyu ya saka kansa a harkar kasuwanci yana bin Anwar yana ganin yanda yake yi.

Adnan tun daga lokacin da aka raba musu gadonsu ya bar gidan yayansa da zama ya koma gidan daya zama rabonsa ne dan Alhaji Sulaiman Sai da ya barwa duka yayansa maza gidaje.

STORY CONTINUES BELOW


A cikin irin abokanan da Adnan yake huld’a dasu ya had’u da wani shu’umi dan 419 yace mishi ya siyar da gidansa ya kawo duka kud’adensa akwai wani hark’a da ake yi aka samun mahaukatan kudi a cikin wata uku ka zama multi millionaire aikuwa Adnan bai yi shawara da kowa ba ya kwashi komai da yake dashi ya damkawa abokin nasa da zumar idan ya dawo daga Dubai ya gama samun kudi aikuwa dawowar da baiyi ba kenan.

Adnan kamar yayi hauka daya gano damfararsa yayi.

Akan dole yaje ya Samu Anwar ya masa bayani halin da yake ciki Anwar kuwa ganin babu Yanda zaiyi dole ya taimakesa tunda basu da sama dashi yasa yayiwa wani amininsa magana akan ya nemawa Adnan aiki a companynsu da ake Siyar da part  d’in motoci inda dak’yar yasamu aka bashi fake result dan Adnan korarsa aka daga makaranta sabida spill ova da ya ringa samu ahaka ya samu aiki a company ya fara aiki dasu.

Shekararsa d’aya da fara aiki Anwar ya kwashi kanensa da sabuwar amaryarsa Amal dan ya rabu da Hindatu sakamakon kamata da yayi da wani akan gadonsu na aure suka koma Maiduguri da zama gabad’aya inda suka bar Adnan shi kad’ai a kano.

Tunda suka koma Maiduguri Adnan bai tab’a waiwaiyarsu ba ballantana akai ga yaje Niger da Anwar da Aliyu ke zuwa duk karshen wata su gaida Mahaifiyarsu Hajiya Asmau.

Anwar ke jigilar kiransa yayi ta masa fad’a akan ya ringa zuwa yana gaida Mahaifiyarsa koda ba zai zo wajensu ba.

Amma ina Adnan kullum cikin karyar aiki ne ya hana shi zuwa yake inda A karshe Anwar ya zuciya yaje kano da kansa dan Mahaifiyarsu ba k’aramin daga hankalinta take ba  Akan Adnan .

Amma abun takaici dayazo baram baram suka rabu da Adnan dan Adnan nuna masa yayi baya san takura idan Mahaifiyarsu Tana kaunarsu haka akan me zataje tayi wani Auren ta rabu dasu shi babu inda zaije zai ringa kiranta awaya suna gaisawa.

Ahaka suka rabu aranar Anwar ko kwana baiyi a gidan ba  ya nufi hotel ya kwana washegari ya koma Maiduguri.

Adnan bai tashi waiwayansu ba sai da Auren sa ya tashi da Aliya.

Sanin Anwar yayi fushi dashi sosai yasa yaje Niger ya samu Mahaifiyarsa ya tsarata akan tayiwa Anwar magana su shige masa gaba wajen Neman  auren Aliya.

A takaice sai da Hajiya Asmau tayiwa Anwar barazanar tsinuwa ya shigewa Adnan gaba wajen Neman Auren Aliya.

Tunda yayi aure bai kuma waiwayarsu ba har yau.wanan kenan.

Cigaban labarin

Adnan tunda abokinsa Safwan yace masa yayi iya bakin k’ok’arinsa dan yasama masa aiki a company su amma abu ya gagara yasa ya fara bin manya manyan DJ idan  zasuje gidan biki suna ko chasu dan yaga yanda harkar take tafiya da irin abubuwan da ya kamata shima ya siya bashida aikin daya wuce siyo sababin wakokin da ake yayi ya ringa ji.

A cikin wata d’aya shima ya had’a nasa kayan kid’an yasawa kansa suna  Dj  AD duk inda yaji zaayi biki ko suna sai yaje koda Ba’a gayyace shi ba dan kawai a San shi inya fita tun safe sai dare yake dawowa wani zubin ma sai dai ya dawo washegari .

Zara kuwa a hankali cikinta ya cigaba da girma Tana shan bak’ar wahalar laulayi yanzu da Adnan ya saka harkar Djnsa agaba kallon inda take bayayi ballantana yasan halin da take ciki dan ba kowane abu take iya ci ba idan kuwa ta tilastawa kanta taci sai tayi amai.

Yau Tana zaune a Palo gidan ta buga tagumi tana jin wani irin yunwa kamar bata tab’a cin abinci ba babu abinda take sha’awan ci sama da meat pie da fanta mai sanyi gashi ko biyar bata dashi.

D’aga kanta tayi ta kalli agogon palon taga k’arfe goma da rabi Na Dare.

A hankali ta maida idonta kan TV ta cigaba da kallon hawaye Na zubo mata dan babu ranar banzan da zai wuce batayi data sanin biyewa san zuciyarta ba addua kawai take yi Allah yasa yau Adnan ya dawo ko fanta kad’ai ya siya mata idan ba haka ba bazata iya bacci ba.

STORY CONTINUES BELOW


Adnan bai dawo cikin gidan ba sai wajen sha biyu da rabi tana jin dirin motarsa ta mik’e da sauri sabida rawar da jikinta ke yi dan kamar ta zub’e dan yunwar da take ji.

Adnan kuwa ko sallama baiyi ba ya shiga gidan yana wak’e wak’e ko kallon Zara bai yi ba ya nufi d’akinsa

Zara kuwa tayi k’arfin Hali ta sha gabansa tana “Sannu da zuwa Adnan”

Adnan amsawa yayi ya kewayeta zai wuce ta e da sauri “Adnan dan Allah ka siyamin fanta na sha wlh rabona da abinci tun Safe gashi yunwa nake ji”

“Iyye jin dadi gaske lailai kice fanta zaki sha to kisha mana wani ya hanaki kisha kuma idan yunwa kike ji ai kinsan hanyar kitchen zaki iya girki kici amma sabida iskanci kamar daga kanki akafara ciki zaki wani cemin fanta zaki sha ni banida kudin da zan siya miki fanta dan yanzu kinsan ba aiki nake ba biyar wahalar kashewa nake”

Adnan yace yana mata mugun kallo

Hawaye ne ya hau zubo mata tace  murya Na rawa “Adnan ai idan inada kudi bazan ce ka siyamin ba kuma ba wai jin dadine yasa nace zan sha fanta ba ji nayi shi nake sha’awa da meat pie idan bansamu meat pie d’in ba ko iya fantan nasamu sai nasha haka”

“To bazaki samu ba kije kisha ruwa idan kuma kin matsu zaki iya tafiya gidanku nasan zasu siya miki har sai kince ya gundureki daga haka ya juya ya shige d’aki yabar Zara a tsaye tana zubar da hawaye ganin tsayuwar ba yi mata zai yi ba yasa ta nufi kitchen ta Dora farin taliya yana dahuwa ta sa manja da maggi ta dawo Palo tafara ci.

Aikuwa ko rabin abincin bata ci ba tafara kwara amai kamar zata amayar da kayan cikinta sai da ta samu minti goma tukuna ta mik’e dak’yar ta gyara wajen da tayi aman ta koma d’akin ta ta kwanta akan bargon da Adnan ya bata Dan ya Dade da korarta daga d’akinsa idan kuwa ya kirata d’akin to nemanta zaiyi 

Ahaka wahalallen bacci yayi awon gaba da ita tana mai jin tsananin yunwa.


Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya Zara na rainon cikinta da wahala Adnan na harkar DJ d’insa duk da baya samun wani kudin arziki sabida ko ya samu a wajen matan Banza zai tafi dan yanzu iskancin nasa ya kai ya kawo har gida yake kawo matan wasu su kwana wasu su tafi.

Zara kuwa ido kawai ta zuba mishi dan ita yanzu tsoron sa ma take dan tana gudun ya saka mata cuta.

Bata tab’a zuwa asibiti awo ba dan ko taje wajen Adnan akan ya bata kudi ce mata yake bashi da ko biyar cikinta na shiga wata shidda ta shirya da kanta ta fara zuwa asibitin gwamnati awo inda Anan ta fara samun saukin laulayin da take yi cikinta ya daina mata tsurfar zaban abincin da zata ci dan kome ta samu yanzu sai taci

B’angaren Ameer kuwa tunda Aliya  ta gama idda ya fara nuna mata yana santa duk da bai fito ya fad’a mata kai tsaye ba amma yana ta nuna mata alamomin  amma ina Aliya ma nuna masa take batasan abinda yake nufi ba dan idan yaje bai fiye samun fuska a gurinta ba Rabin hirar shi yake yi eee da aa kawai ne amsar ta fuskar da bai samu ya sa ya kasa fitowa ya gaya mata abinda ke ransa game da ita ga wani irin kaunarta dake dawainiya dashi dan zai iya cewa tunda yake bai tab’a yiwa mace irin san da yake mata ba haka ya cigaba da zuwa wajenta indai zaije sai ya tafar mata da wani abun.

A yau ya kuduri niyyar gaya mata abinda ke zuciyarsa bayan ya dawo daga office ya shirya cikin wani lallausan yadi coffe color  daga hula har takalminsa duk kalar yadin ne yayi kyau ba karya sai da ya kalli kansa a mudubi ya kara gyara zaman hulansa ya  sakarwa kansa murmushi dan yasan yayi kyau   mukullin sabon motarsa da ya siya kwana uku da suka wuce ya d’auka yayi hanyar waje.

Motar tasa kuwa sai kyalli take sai da yafara shiga main house d’in yacewa Hajiya Ameena zai tafi wajen Aliya tayi mishi addua Allah yasa ta k’arbeshi da hannu biyu Hajiya Ameena murmushi tayi ta mishi adduar Allah yasa su daidaita daga nan ta mik’e ta shiga d’aki ta had’o kayan kwalliya turaruka masu kamshi da  turmin atamfa ta kawo wa Ameer tace ya bawa Aliya tace injita.

Ameer cikin farinciki ya amshi ledar tare da mata godiya.

K’arfe biyar da rabi ya isa gidansu Aliyan ya kirata a waya yace mata gashi nan awaje.
Aliya dake kwance kanta akan cinyar Hajiya Rukayya tsaki tayi tace “gaskiya nikam wlh Ameer ya fara takuramin”


Hajiya Rukayya murmushi tayi tace “Ummm anya nidai zaryar da yaron nan yake yi akanki ba sanki yake yi ba”?

Aliya da sauri ta mik’e tana ” Haba Hajiya  ya zakice sona yake yama zai soma tunanin haka Mak’ocinmu ne fa”

“To haramune kijiki da wani magana Allah ma yasa ma san naki yake ai da kin dace da nagartacen miji kinsan yanda Abbanku yake kaunar yaron nan kuwa yake  yabon kyawawan halinsa”

Aliya tashi tayi daga zaunen da take ta mik’e tana “ni ba abunda zanyi da Ameer wlh ni bana ma san Auren yanzu sai na huta sosai na nutsu fatana dai ki kara rok’ar min Abba ya barni dan Allah in cigaba da degree d’ina”

Hajiya Rukayya murmushi tayi tace “kije ki sameshi kin bar shi waje tundazu zaki cigaba da Degree d’inki a d’akin mijinki insha Allahu”

Aliya d’akinsu ta shige ta sako bakin hijabinta mai hannu ta d’an fesa Turare ko hoda bata shafa ba tayi hanyar waje tana mai d’an daura fuskarta dan tunda Hajiya Rukayya tace kila santa yake yasa ta shirya mishi kora da hali.

Ameer tun daga nesa ya zuba mata ido yana hadiyar yawu sabida mugun kyau Da Aliya tayi mishi dan fatarta wani irin glowing yake duk da babu make up a fuskarta har tunani yake  idan zata yi kyau a cikin hijabi haka ya kyaunta zai zama idan babu Hijabi zai so ya ganta babu Hijabi yasan sai tafi haka kyau a fili.

Har ta k’araso wajensa kanta a sunkuye yake cikin siririn muryar  ta Tayi mishi sallama

Ameer ya amsa jikinsa a sanyaye dayaga yanda ta d’aura fuska.

Bayan sun gaisa shiru sukayi dan Ameer ji yayi gabad’aya ya nemi kuzarinsa ya rasa wani sashe na zuciyarsa na ingiza shi akan ya gaya mata kawai a wuce wajen wani sashe na zuciyarsa na hana shi.

Aliya kuwa kanta a sunkuye yake tana wasa da k’asan Hijabinta sau d’aya ta d’ago ta kalleshi duk da yayi bala’in kyau hakan bai sa ya wani burgeta ba.

Sai da suka samu minti goma sha biyar ahaka Aliya kuwa ganin yak’i magana ya sa ta d’ago tace “ina girki  ne fa zan koma ciki dan  kar girkin nawa ya k’one”

Ameer fitowa yayi daga motar dan tunda tazo yana zaune a ciki k’afafunsa kawai ya zuro waje.


Gyara tsayuwarsa yayi yana kallon Aliya bayan ya tattaro duk wani kwarin gwiwarsa yace

“Aliya akwai wani magana danake so na fad’a miki duk da bansan ya zaki amshi maganar tawa ba barin kashi a ciki baya maganin yunwa so gwara yau dai na fito na gaya miki abinda ke cikin zuciyata game dake Aliya a gaskiya Allah ya jarrabceni da so da kaunar ki na Dade ina Adduar Allah yabani mace mai irin halayenki mace da zata zamo uwar ya’yana da kuma dukan alamun kece macen da Allah ya zaba min lura da kaunar ki da na wayi gari dashi dan Allah Aliya kisa min wuri a zuciyarki dan nasan da wuya ki iya kuma yarda da wani namijin amma inaso kisan ba’a taru an zama d’aya ba insha Allahu bazaki yi nadamar aurena ba”

Tunda ya fara magana gaban Aliya ya fara fad’uwa dan bata tab’a tunanin Ameer zai Ce yana santa ba dan aganinta ma duk da sun rabu da Adnan shima ya rabu da Zara idan yace yana santa tamkar sunci amanarsu ne”

Sai da suka samu minti goma yana jiran yaji mai Aliya zata ce yaji tayi shiru ta k’i magana

Sai da ya k’ara mata magana ta d’ago tace “Ameer a gaskiya kayi hakuri bazan iya auranka ba dan gani nake kamar munci amanar Zara ni yanzu ma ba aurene agabana ba makaranta zan koma dan Allah kayi hakuri Allah ya baka wacce tafini”

Daga haka ta juya da sauri ta nufi cikin gidan.

Ameer binta yayi da kallo har ta shige cikin gidan inda hankalinsa yayi masifar tashi dan duk fitar numfashinsa sai San Aliya ya linku a ransa.

Sai da ya samu minti goma a tsaye yana tunanin abinda ya dace yayi kafin ya shige cikin motarsa ya tafi…..Aliya kuwa tana shiga ciki ta zube akan kujera tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu.
+

Hajiya Rukayya dake zaune mik’ewa tayi tana “ke lafiyarki kuwa mai haka kika shigo kina haki kamar wacce ta sha gudu”?

” Hajiya nida Ameer ne mana wlh ya bani mamaki wai kiji sona yake zai Aureni ko kunya baiji ba salon ace dama can soyayya mukeyi dashi”

“Laillaha illallahu Aliya mai abun kunya aciki dan yace yana sanki mai kika ce masa?

Aliya zumb’ura bakinta tayi tace ” hakuri na basa nace yayi hakuri dan Gaskiya bazan iya aurensa ba”

“Amma ke kuwa anyi sokuwar yarinya wlh Allah ya saka miki abinda Adnan ya miki ta hanyar baki Salihi kamar Ameer kice bakya so anya kina ma da hankali kuwa ke daya kamata ace kinfi kowa murna kinsamu hanyar da zaki cusawa Adnan bak’in ciki dan ni nasan idan yaji labarin Ameer zaki Aura sai yafi kowa shiga tashin hankali da bak’in ciki shine zakice bakya sansa to bari Alhaji ya dawo na fad’a masa zakiga yanda zaki kwashe dashi kullum sai ya min maganar Ameer akan yana San ya mashi maganarki amma yanzu Allah yasa ya kawo kansa kince bakyaso”

“Haba Hajiya ya zaki gayawa Alhaji Dan Allah kiyi hakuri ni idan Auren ne ma kukeso kuyi Min ku  samo min kowaye banda Ameer dan Gaskiya bazan iya aurensa ba”

“Idan na tashi gayawa Alhajin anjima sai kizo ki matse bakina”

Hajiya Rukayya tace tana zabga mata harara tare da nufar d’akin ta.

Ameer kuwa yana isa gida ya zube akan cinyar Hajiya Ameena dake cin abinci 

Hajiya Ameena kuwa ta d’ago shi da sauri da d’aya hannun nata tana tambayarsa mai yafaru.

Ameer a hankali yace “Hajiya tace bata sona wai bazata iya aurena ba inyi hakuri Allah ya bani wacce ta fita”

Yanda yayi maganar kamar Mara lafiya ne yasa Hajiya Ameena sakin murmushi

Wanda hakan yasa Ameer  k’ara daura fuska yace “Haba Hajiya kinji kuwa mai nace kike murmushi cewa nayi miki fa Aliyar tace bata sona”

Murmushi Hajiya Ameena ta k’ara yi tace “najika sarai Ameer ai Dariya kabani ne dan bansan yaushe ka zama ragwon namiji ba da tun ba’aje ko’ina ba za  kabi ka karaya haba dan Allah kamar ba Ameer d’ina ba ai ba’ayi macen da zata ce bata sanka ba”

Ameer shagwabe fuska yayi yace “Hajiya dan Allah kibar batun wasa wlh hankalina ya tashi bana San na rasa Aliya dan wlh Allah ya jarrabceni da santa bazan iya jure rasa ta ba Aliya irin macen dana Dade nake fatan ta zamo uwar ‘ya’yana ce dan wlh halinmu yazo d’aya da ita ina aureta na samu Aljannar duniya”

STORY CONTINUES BELOW


Hajiya Ameena tagumi tayi tace “oooo yanzu Ameer kafisan Aliyar nan akaina kenan”

Tayi maganar tana matse matsen ido aikuwa Ameer Dariya ya  kyalkyale dashi Wanda hakan yasa itama Hajiya Ameena sakin murmushi dan dama abinda take so kenan

“Karka damu Ameer insha Allahu Aliya zata soka za kuma ta aureka karka wani karaya dan dama dole kafin ta aminta da kai sai an kai ruwa rana lura da yanda namiji yaci mata amana kaga kuwa yanzu kafin ta kara yarda da wani namijin  za’a d’an dau lokaci Dan haka karka wani damu kanka
nace mata zaka yi ka cigaba da zuwa ni nasan insha Allahu wataran zata kaunace ka”

“Hajiya anya bake zakije min gidan ba ki roketa  kila taji nauyinki ta yarda ta Aureni”

“Ooo ni Ameena wai gaggawan na menene Ameer kabita a hankali mana ni nasan zata soka wlh”

“Aaa nidai Hajiya ina tsoron wani ya rigani gwara dai kije min dan Allah”

“Ka dai cigaba da zuwa Ameer idan naga alamar bazata saurarekan ba sai naje gidan nasu da kaina kaji babana maza wanke hannunka muci abinci dan dama nasan baka wani ci abincin rana ba sabida dokin zuwa wajen Aliya ooo ni kam zanso naga wanan Aliya data susutar min da d’a”

Ameer murmushi yayi yana wanke hannunsa yace “Hajiya Bazaki gane ba Aliya ta had’u ko ta ina shiyasa nace miki tsohon mijinta bashida rabon duniya Dan Wlh Aliya macece da kowane namiji zaiyi fatan ya sameta a mata shiyasa kika ga na dage dan tana da tarbiyya sosai ga kunya wlh ban tab’a ganinta babu Hijabi ba”

“Allah sarki ai ana samun irinsu wlh idan kaga haka gidansu an Gina shi akan tarbiyya ne ba kamar waccar kwashashiyar da mahaifinta ma tarbiyya tayi mishi karanci ba dan ko a lokacin daka dage sai ka aureta babu yanda zanyi dakai ne dan Sam ba’a fadi kyawawan halin ‘yan gidansu ba daga dan iska sai dan shaye shaye kuma ance Mahaifinsu ne ya lalatasu haka”

Ameer hadiye loman tuwon da ya kai bakinsa yayi yace

“Allah sarki har kin tuna min da Mahaifiyarta wlh Dan shekaranjiya ma ta kirani tana tambayata ko naji labarin inda take nace mata wlh ni ban ma kara zuwa unguwar nan ba ballantana naji labari yarinyar nan sai tayi nadamar abinda tayiwa Mahaifiyarta dan bakiga wulakancin data mata ba Hajiya har zaginta tayi amma ki duba kiga yanda ta damu da ita ko ina ta shiga oho yarinyar nan tayi nisa wlh”

Hajiya Ameena tab’e baki tayi tace “gwara ma ta manta da ita idan ba haka ba bak’in ciki yayi ajalinta dan wanan kam tayi Nisan da bazata ji kira ba sai dai idan duniya ta koya mata hankali”

“Allah ya shiryeta idan tana da Rabon shiryuwa”

“Ameen bari a karo maka tuwon naga ka kusa cinyewa”

Hajiya Ameena tace ta mik’e tare da nufar kitchen.

Aliya a zaune take agaban Alhaji Abubakar tana ta matse hawaye sabida yanda yake zabga mata fad’a kamar zai daketa dan yana gama cin abinci Hajiya Rukayya ta kwashe komai ta gaya masa

“Banda rashin hankali da tunani awane dalili zakice bakya San sa ko har yanzu wanan Dan iskan mijin naki kikeso”

Aliya da sauri ta d’ago ta fashe da kukan bak’inciki dan ko kad’an bata so ma taji sunan Adnan ballantana akai ga ace tana San sa cikin kuka tace “ni wlh bana sansa ko sunansa bana San ji”

“To idan bakya sansa awane dalili zakice bakya San Ameer yaron dan mutunci da yafito daga gidan tarbiyya dan har mahaifinsa ya rasu wajen shekara biyar kenan har yanzu ana yabon kyawawan halinsa idan ba Wanda bashida rabo ba babu Wanda bazai so ya had’a zuria da ‘yan gidan ba yaro nagartace irin Ameer kice bakyaso abinda godewa Allah ya kamata kiyi da ya saka miki da abinda wancan dan iska manemin matan  ya miki ta hanyar baki Wanda ya fishi nesa ba kusa ba yaron da kullum cigaba yake arayuwarsa yana k’ara samun matsayi awajen aikinsa sabida kyawawan dab’iunsa wancan kuwa dan iskan tsohon mijin naki shi k’ara tab’ewa yayi ya lalace dan Yanzu aikin DJ yake yi”

STORY CONTINUES BELOW


Hajiya Rukayya da Aliya a tare suka ce “Djjj”?


Alhaji Abubakar yace “kwarai kuwa DJ fa dan yanzu duk inda ake bad’ala a garin nan shi ake kira yayi DJ shekaranjiya Alhaji Saminu ke bani labari dan a unguwarsu yake ance har mace ya ajiye a gidan mai cikin shege”

Hajiya Rukayya zaro ido tayi tana  
“Subhanallahi kace yaron ya K’ara nisa ooo Allah mungode ma da Aliya bata had’a zuria dashi ba da ya zamuyi”

Aliya kuwa runtse idonta tayi tana mai k’ara jin tsanar Adnan aranta

Alhaji Abubakar kuwa yace “Dan haka ki gayawa ‘yarki Ameer Alherine agareta gwara ta amshe shi hannu bibiyu dan kowane uba zai zo ‘yarsa ta Auri irinsa idan kuma ba San tsohon mijinta take ba”

Aliya kuka ta k’ara  fashewa  dashi tace “ni wlh bana kaunarsa ko sunansa bana San ji”

“To idan hakane ki ringa sauraran Ameer a hankali zaki so shi dan idan zan samu ne ma na had’a aurenki dana kanwarki sumayya nan da sati biyar masu zuwa  kiringa kula shi karki sake ki kara  wulakanta shi kinji mai nace ko”?

Aliya gyad’a kanta tayi a hankali tana share hawayen fuskarta Alhaji Abubakar yace ta tashi ta tafi.

Ta mik’e ta nufi d’akinta tana zuwa ta zub’e akan gado tana tunanin yanda zata soma ma San Ameer ballantana har ya kai da ta aure shi.


Kid’a ne yake ta tashi a wani k’aton hall da ake bikin wasu Amare biyu.

Adnan shine Djn da aka kira awajen bikin yayi shigar bak’akk’en kananan kaya yayi masifar kyau dan tunda ya fara harkar DJ yake wani irin gayu yana ajiye saje

Kai idan ka gansa kaga Wanda yake masifar ji da kansa 

Yana daga zaune agaban manyan speakernsa ya k’afa head phone a kunnensa yana cacanza wakokin da ake yayi acikin system D’in dake gabansa  ‘yan mata nata ihu da  shewa.

Girgiza kansa kawai yake yi yana Dan rawa da jikinsa jefi jefi sai ya d’ago ya kalli yanda ‘yan mata ke dancewa a tsakiyar Fillin.

Wak’ar Kizz Daniel yasa “Baba”

‘Yan matan suka saki shewa da ihu hakane yasa shi d’agowa da murmushi asaman fuskarsa aikuwa idonsa ya sauka akan wata kyakyawar hallitar data kusa sa numfashinsa d’aukewa.

Kyakyawa ce idan aka ce kyakyawa  irin first class d’inan

Adnan hadiye yawu yayi ya k’ara ware idonsa yana kallonta fara ce tas mai d’auke da doguwar fuska da dogon hanci idonta yafi ko’ina kyau dan irin lumsassun idonan ne da ita farare tas gasu manya kallo d’aya zaka mata kasan ta had’a jini da ‘yan shu’uwa.

Adnan wani yawun ya k’ara hadiye ya kai idonsa kirjinta da take girgizawa  a hankali na fulaninta na lek’owa waje sabida girmansu

A hankali ya kai idonsa kan hips d’in ta ya k’ara hadiyar wani yawu sabida makoshinsa dayaji ya bushe dan yanda cikinta yake so flat hips d’in ta kuma mai fad’i ko ba’a fad’a masa ba yasan ba ciko tayi ba dan tsabar sanin matan da yayi da muamalla da yake dasu yanzu yana iya tantance jiki mai acuci.

A hankali ya k’ara maida kallonsa kan fuskarta murmushi take yi ta d’aga hannuwanta sama tana rawa tana juya hips d’in ta dimples d’in ta ya lotsa sosai.

Adnan wani irin harbawa kirjinsa ya fara yi a karo na farko dayaji yaji mace ta kwanta masa da ya aure ta a karo na farko dayaji yana yiwa mace wani irin so daga kallo d’aya.

Mik’ewa yayi yasa yaransa dake taya shi entertaining mutane idan sun fita yace su cigaba da saka wakokin yana zuwa.

Kujera ya samu ya zauna ya cigaba da kallonta.

Ajidde dake ta tikar rawa kiran daya shigo wayarta ne yasa ta tsayar da rawar da take yi  ta daga wayar da hannunta dake sanye da zobunan gwal tayi hanyar waje.


Adnan da sauri ya mik’e yabi bayanta har yana tuntub’e 

Adnan waje ya samu ya tsaya daga d’an nesa da ita ta juya masa baya tana waya haka kawai jikinsa yayi sanyi dan shigar jikinta kawai ya nuna masa babbar yarinya ce dan ko takalmin k’afarta kawai zai yi dubu Ashirin.

Juyowar da tayi ne yasa gabansa wani irin fad’uwa jikinsa ya d’au rawa adai-dai lokacin da ta nufo wajen da yake tsaye dan ta koma cikin hall d’in.

K’afeta yayi da ido jikinsa na cigaba da rawa har tazo zata wuce shi.

Gabanta yasha da sauri Wanda Saura kiris suyi karo.

Ajjidde kuwa tayi sauri ta ja  da baya ta zubawa masa idonta dake   ji kamar ya narke.

Cikin wani irin siririn murya  tace “Lafiya kuwa ya zaka zo kasha gabana”

Adnan tattaro duk wani jarumtarsa yayi ya sakar mata murmushin da yasan yana sace zuciyar ‘yan mata yace “u are very beautiful”

“I know u are not the first person that says so do u  just cross my way to say am beautiful”?

Adnan murmushi ya k’ara sakar mata fararren hakoransa suka bayyana

Ajjidde kuwa itama ta zuba masa ido tana karewa hallitar fuskarsa kallo dan ba karya Adnan din ma ya had’u.

” ko d’aya ban tsayar dake dan nace kinada kyau ba na tsayar dake ne sabida kaunar ki danake”

Ajjidde wal tayi da idanuwanta ta saki murmushin dake Neman kayar da Adnan k’asa tace “OK then try your luck am Ajjidde by name nyc to meet u”

Tace tana mik’a masa hannunta

Adnan shima mik’a mata hannunsa yayi yana mai d’an mamakin yanda tayi saurin sakin jikinta da shi lumshe idonsa yayi da yaji taushi da sanyin hannunta yace  ” Am Adnan nyc to meet u too hope am accepted”?

“Eee to bansani ba tukuna just have my contact and call me tomorrow”

Adnan da sauri ya Ciro Samsung d’insa daga Aljihunsa ta karanto mishi lambarta ya kirata tayi saving daga nan ta shige ciki ta bar shi  a tsaye.

Adnan bayanta yabi da kallo yana hadiyar yawu wani irin santa na ratsa masa zuciya.

Hall d’in ya nufa sukayi kicibis dashi ta kuma fitowa tana amsa waya murmushi kawai ta sakar masa ta wuce shi.

Adnan kuwa ya juya yana kallonta.

Wani katon  bakin jeep daya shigo Harabar wajen yaga ta nufa ta bud’e gaban motar ta shige.

Adnan kirjinsa ne yayi wani irin bugawa hankalinsa yayi bala’in tashi har suka bar wajen yana tsaye kamar Wanda aka dasa shi tunani ya fara  da Allah yasa Ajjidde bata fi k’arfinsa ba dan shi bill haki so yake ya aureta.


Kuyi manage insha Allahu zan ringa kokari ina posting kullum dan yanzu labari zai d’auko dadi dan Adnan ya zai d’ebo ruwan dafa kansa zai haka ramin da zai binne kansa tun lokacin mutuwarsa baiyi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page