EL-MUSTAPHA CHAPTER 9

EL-MUSTAPHA

CHAPTER 9Uwani ta xube gurin hankalinta a tashe, +

Me jiddah ke nufi da ko xata mutu baxata taba aura mata el’mustapha ba, kenan jiddah tana nufin ko ma me xatayi sai dai tayi amma baxata qara auren mijinta ba.

Yaushe jiddah ta canxa haka? Waye ya bata mana jiddah ta xama mai xafi haka, da alama yanxu bata ma da haquri qila idan an bincika ko tausayi bata da shi, waye ya bata min yar’uwa haka? Indai ba ta sami qawa mai xugata irin jamcy ba. 2

Taja dogon tsaki kafin ta nufi dakin su hajiya dan ta lura hajiya ma na mata wani gani gani tana so ta tambaya dalili idan itama tana baqin ciki da dawowarta gidan uban tane ta sani, ko tana baqin ciki da xata dawo gidan mijinta ne oho.

Jiddah ta ajiye airah akan bed tana kallon el’mustapha,

Wani abin mamaki, Uwani ke roqona na barta ta auri mijina a karo na biyu, bata neman gafara ta sai ma ta mijina take.

El’mustapha ya matsa kadan inda ta shimfide Airah barci take, ya tsurawa fuskarta ido yana kallonta,

Yace ai nasan jiddah mai haquri ce da tausayi, ina tunani ma yanxu tausayin ne ya saka taxo ta gayamin uwani na son komawa dakin mijinta, nasan yanxu xaki fara kuka kina roqona na maida uwani yar uwar kice ciwon xuciya zaya kamata ke kuma baki so ki rasata saboda halaccin iyayenta.

Ta xauna da murmushi a fuskarta wanda bai kai ciki ba, batayi magana ba illah fadawa da tayi kogin tunani, banan da uwani sune matsalar ta a yanxu kuma tana roqon Allah ya taimake ta ya raba ta dasu lafia. 5

El’mustapha ya daqo yana kallonta,

Tunanin me jiddatulmusty take yi?

Tace ba komai,

Ya tashi ya cire doguwar jallabiyar dake jikinsa, kafin ya qara kallonta,

Ina so na dauko wata mai aiki saboda Airah ke kuma kiji dani,

Ta ware idanu tana kallonsa,

What? Mai aiki, wace irin mai aiki kuma el’mustapha? Kai baka ga halin da nake ciki bane, Dame xanji ni kuma me xanyi da mai aiki.

Ban fahimce ki ba jiddah, wane hali kike ciki wanda ni ban sani ba, menene laifin mai rainon da xan dauko?

Ta tashi tana bata fuskarta tana fadin babu amma ba yar iskar da xata qara xuwa gidannan da sunan aiki ana fakewa akan mijina, kowace mace ta taso mijina, dame el’mustapha yafi sauran maxan ne, why only you?

Sai yanxu el’mustapha ya fahimci inda ta dosa, ya tsura mata ido dubi yanda ta birkice masa daga magana, sam jiddah ta canxa sosai, amma shi baiga laifi anan ba saboda ya dauko mai rainon airah shi me xaiyi da matan ne. 2

Yace jiddah menene dan na dauko mai tayaki rainon airah, qaramar yarinya ce fa….. ta katse sa,

Qananan yaran ne kemin raino nima ina rainon su da sun girma basu da abin so sai mijina, ni xan iya rainon airah saboda ba abinda nake yi a gidannan sai girkinka da kula da sashen ka, idan ka matsa dole sai an dauko mai raino na amince amma fa namiji xaka dauko yayi rainon airah. 4

STORY CONTINUES BELOW


Ya bude idanunsa sosai yana kallonta bayan ya gyara tsayuwarsa,

Namiji jiddah? Wane irin namiji xan dauko yayi min rainon ya’mace? Me ma xai kawo namiji har cikin gidana da falona yana kallon matata….. 1

Tace nima babu macen da xaa dauko taxo tana kalle min miji, ban nemi xama da mai aiki ko raino ba, ni na gaji haka kuma bana so El’mustapha,

Ni fa wadda xan dauko Nanny ce, ibrahim naji yana magana xai daukowa matarsa shine nima n….. ta katse sa,

Oh God El’mustapha, nanny xaka dauko min ta xauna dani a cikin gida, in maka kwalliya na fito ita kuma ta saka mini skirt ko matsatsen wando ta fito xuwa raino, kai kuma kana kallonta ko?

Yace sharri kuma xaki min jiddah, idan ba kyaso ne kice ba kyaso amma banda sharri kin sanni bani da kallon mata ballantana ma qabila, me xanyi da ita jiddah. 1

Ta xauna tana fadin to bana so, I can take care of my daughter, in kuma ka matsa dole naji a dauko tsohuwa irin Inna wacce ko haqoran gaba babu a bakinta sai yawun goro na amince,

Ya saki dariya yana xama kusa da ita,

Oh ni El’mustapha duk yanda nayi da jiddah ban mata dai dai ba, nikam na rasa inda jiddah ta dauko wannan halin a yanxu.

Ta tabe baki batare da tayi magana ba.

*

‘Abba ni ka saka baki kayiwa jiddah magana ina son el’mustapha ta barni na aure sa dan Allah abba,

Hajiya ta xare idanu tana kallonta,

Anya uwani na da hankali kuwa, kin san me kika fada?

‘Abba yace bata da hankali kam, ai na gayamaki har aiki aka mata amma babu canji sai ma nake ganin abin a jinin ta yake ba wani faduwa da xaa fake da ita, an dai ci kudi na ne amma uwani kam sai addua. 3

Uwani tace Allah abba na shiryu nayi nadama kowa ma ya sanni, waccan karon ba laifina bane, laifin jamcy ne bani da niyar cutar da jiddah itace ta xugani, dan Allah ku taimakeni kada a nuna min baqin ciki a maidani dakina yau.

Hajiya tace sam bada yawu na ba wallahi, babu ruwana kuma idan aka dage da lallai sai uwani ta koma dakin ta baa min adalci ba ta tashi ta fice a fusacce,

Uwani ta bita da kallo kafin ta dubi abba, ita dai hajiya har yanxu abba bata daina nuna min baqin c…. bai bari ta qarasa ba ya bige mata baki,

Kul na qara jin wannan kalmar a bakin ki, ba mahaifiyar ki bace, meyasa ba kya tunani kafin ki furta magana, ki fa yi a hankali da duniya uwani, ki dawo cikin hayyacinki kisan me kike yi, Allah baya barin mai xalunci da kuma mai sabawa iyaye, kar na qara jin haka daga bakin ki.

Tau abba kayi haquri na daina, xanje ma na bata haquri.

Yace maganar el’mustapha wannan karon ma xan gaya maki babu yawuna babu hannuwana aciki kamar farko, kuma bani buri ko fatan naga el’mustapha ya aure ki domin baki cancanta ba, kince naxo dake ne domin kiga jiddah ki roqeta gafara ba wai ki roqeta ta maidaki dakin ki ba, ni babu ruwana duk abinda suka maki ke kika ja tashi kibani guri shashasha.

Ta tashi tana tunxure baki ta fice, tunda baxasu maidata dakin ta ba ita xata maida kanta, a bata key din dakin ta shiga daga yau ta xama matar el’mustapha ta maida kanta dakinta duk mai baqin ciki sai dai ya mutu amma sai ta haihu da el’mustapha.

*

‘Washe garin ranar duk basu hadu da jiddah ba sai bayan jiddah ta fito raka el’mustapha xai je gurin aiki suka tsinkayo uwani tsaye a gurin motar sa, taci kwalliya abinta tana jiran fitowarsa.

Suka qarasa jiddah na kallonta,

‘Anty jiddah an tashi lfy, yaya barka da fitowa cewar uwani dauke da murmushi a fuskarta,

STORY CONTINUES BELOW


Duk ba wanda ya amsa a  cikinsu,

‘Dan Allah kuyi haquri nidai a maidani dakina, a bani key xanje na gyara dakina, wannan karon bani…… tayi shiru sakamakon bugu da taji a tsakiyar kanta, ji kake tum…. ashe jiddah ce ta rarumo wani katon dutse ta buga mata aka… 2

Uwani ta xube gurin a sume, el’mustapha ya juyo yana kallon jiddah cikin mamaki, xai yi magana tayi saurin tsaida sa,

Kar kace komai, yar uwarka ko tawa, ba ruwan ka she is my sister, shiga mota kayi tafiyar ka.

Yanda idanunta suka juye abin ya bashi tsoro, innalillahi wai meke damun jiddah, 5

Ya xagayo da sauri yana fadin na tafi ina jiddah, idan kika kashe…..

Nace ba ruwanka el’mustapha,

Ya ja dogon tsaki hankalinsa ya tashi sosai ganin jini na fita ta goshin uwani, kada jiddah tayi kissan kai, yanxu fisabilillah idan iyayenta suka ganta haka ya xasu ji, ya kalli jiddah cikin takaici sai huci take, tsaki ya ja kafin ya bude motarsa tana kallo ya saka uwani a mota xai fita da ita. 2

Da gudu ta qarasa bakin gate ba inda xai fita da uwani, securities suka taso amma bata damu ba, ta tare hanya sai idan xai taka ta ne ya wuce,

Ko jiddah ta haukace ne, ya tambaya cikin xuciyarsa yana kallonta ta glass din motar, ya fito a fusacce,

Xaki matsa ne ko sai naxo na taka ki,

Wallahi baxaka kai uwani asibiti ba, sai dai ka takani ka wuce.

‘Wannan wane irin abin kunya ne jiddah ke janyo masa cikin yaransa,

Yayi ma wani sergeant magana akan yaxo ya kai uwani asibiti, ta matsa tana sauke numfashi suna fita abba ya fito jin hayaniya.

Ni jiddah ni xaki wulaqanta,

Nima ka gama wulaqantani na daukar uwani ka saka a mota kowa yana kallon ka.

Yace tor shikenan, ya juya a fusacce ya nufi cikin gida bai jima ba ya fito dauke da wani key na mota, bai qara bi ta kanta ba ya fice, ta tabe bakinta kawai.

‘Abba ya tambaya dalili, batare da tunanin komai ba tana yarfe hannuwanta tace uwani na fasawa kai an nufi asibiti da ita.

‘Abba baice komai ba ya juya cikin gida ko baa fada ba yasan duk akan el’mustapha ne daga yanayin da yaga ya fita.

Yinin ranar sai taji ta damu el’mustapha bai kirata ba kuma ta kira yaqi ya dauka,

Tana ganin sanda aka dawo da uwani asibiti an daure mata kai da bandage 🤕 amma dan qarfin hali irin na uwani sai cewa take sai dai na dawo dakina ko kashe ni xaa yi kuwa. 1

Jiddah ta kasa sukuni, ga kukan airah ya Dame ta, ta dauke ta, ta nufi sashen su banan da niyar cewa ta goya mata ita tana so ta daura girki.

Sai ta sami banan daki kwance tana waqa da tsananin farin ciki a fuskarta,

Idan ba kunnuwanta ke mata gizo ba kamar waqar da banan keyi harda sunan el’mustapha a ciki,

_farin ciki a yau ya sameni_
_Dadi na rayuwa ya riskeni_
_Majaujawa ta so da ta daukeni_ 
_Sai ta barni gidan da aka raineni_
_Ta bani wanda nake so a badini_
_Soyayya na xata xata barni_
_Sai akace min naje an kyaleni_ 
_’Na auri wanda nake so ya soni_
_Kullum da safe in har ya ganni_
_Da murmushi yake qawatani_ 
_Naxo Musty ka in gantani_ 
_Eh….. Gani gaka_💃🏻

Jiddah ta shigo dakin hankalin ta a tashe take kallon banan, idanunta a rufe take waqar fuskarta dauke da murmushi cikin farin ciki, jiddah na tsaye ta qara dauko wani baitin,

STORY CONTINUES BELOW


_Cikin gidan mu akwai wani d’an yaro_
_Dadin muryarsa shi nafi sauraro_
_Farin wata nake shiko tauraro_
_Sonsa a xuciya da shi naci karo_ 
_Al’bishiri kuce min dan goro_
_Ya dan uwa musty xan yo koyo_
_Nayo Mari akan sa na bijiro_
_Lambar girma musty baya cin xero_
_’Na baka xuciya baniyi kwaro_
_Mai kyau kamar fulani uban toro_👍🏻
_Yau gani gaka bana jin tsoro eh… Gani gaka._ 1

How I wish nima na xama BanantulMusty ka….. tayi shiru sakamakon saukar Mari da taji a kuncinta,

Ta bude idanunta da sauri ganin jiddah a gabanta ta xabura ta tashi cikin matsinanciyar faduwar gaba.

Kafin tayi wani motsi jiddah ta qara dauke ta da wani Marin cikin bacin rai, sai ga jini yana fita ta gefen bakin banan,

Kashe ni kuke son kuyi, me nayi maku, meyasa kuke son mijina, meyasa kuke son ganin bayana, farin cikina ne bakwaso ko me, ku raba ya’yana da farin ciki, baxan taba yafe maku ba, kuma bake ba el’mustapha har abada sai dai ki xamo  Banantulislam, kiji rani kiga hukuncin da xan yanke akan ki.

Ta fita a fusacce tana tafe tana sharar kwallah cikin tashin hankali ga wani xafi da xuciyarta ke mata,

Wayarta ta dauko, nabila ta kira cikin boye damuwarta,

Ki turomin islam gobe Nabila,

Lafiya jiddah naji muryarki wata iri.

Ba komai, ki turo min shi xamuyi magana.

Tace to shikenan jiddah.

Kuka sosai jiddah tayi, babu wata walwala ko sukuni a tare da ita, hajiya tayi juyin duniya tana tambayar ta taqi ta gayamata, haka ma abba, ganin yanda har idanunta suka kumbura.

Cikin qanqanin lokaci xaxxabi mai xafin gaske ya rufe ta, haka el’mustapha ya dawo ya sami airah gefenta tana ta kuka taqi ta kula ta.

Ya dauke ta da sauri yana kallon jiddah, yanayin ta kadai ya gane babu lafiya, ya kai hannunsa a jikinta ya taba xafi rau.

Me ya same ki jiddah, ta bude idanu da kyar tana kallonsa kafin ta maidasu ta rufe rub xuciyarta na cigaba da bugawa saboda tsananin tashin hankali.

Bai qara magana ba ya fita yana tambayar hajiya,

Nima nayi tambaya bata fada ba sai kuka take tun daxu,

Ya bata airah kana ya juya xuwa dakin,

Meke damun ki jiddah ya tambaya yana dago ta,

Batayi magana ba illah qara shigewa da tayi jikinsa, yana jin bugun xuciyarta ga jikinta yayi xafi rau,

Ko muje asibiti ne jiddah,

Ta girgixa kanta.

*

‘Washe koda islam ya xo el’mustapha ya fita,

Tace ka gayamin gaskiya islam ka shirya auren banan.

‘Na shirya anty jiddah, ki tambayi anty nabila tasan komai.

Tace ka turomin iyayen ka gobe suxo da sadaki, cikin satin nan xaa yi auren ka da banan.

Farin ciki ya mamaye xuciyarsa sai godiya yake mata, ya tashi ya fita,

Ta kira kakar banan ta gayamata tana son ganin ta gobe tare da kawun banan xaa yi auren ta cikin satin.

Duk shirye shiryen da ake ba wanda ya sani har el’mustapha da banan, sai bayan xuwan iyayen islam ne el’mustapha ya sani, shine ya xama kamar waliyin banan ya bada auren ta tare da wani kawunta.

El’mustapha bai san dalilin saka wannan auren da wuri ba kuma bai tambaya ba kada yayi laifi ace kuma son ta yake gashi jiddah cikin kwana biyu bata cikin walwala kamar wacce bata da lfy.

Banan kuwa da ta sami labari hankalin ta ya tashi sosai taga iyayen islam nesa ba kusa ba yafi qarfinta daga babban gida ya fito amma bata san meyasa take jin el’mustapha fiye dashi a xuciyarta ba, tayi kuka har ta gode Allah.

Ga sadakin banan cewar el’mustapha yana kallon jiddah.

Ka riqe hannunka, gobe xanje nayi mata duk abinda yace nayi a matsayina na mahaifiya na gayawa kakarta kada su wahalar da kansu ni xan mata komai.

Ni kuma me xanyi jiddah, abari na sami ladar aurar da marainiya jiddah.

Murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba.

Cikin satin akayi komai na biki, kuma alhamdulillah biki yayi jama’a anyi komai lafiya an kai amarya.

Jiddah tayi mata hudu ba sosai, ta qara da cewa,

‘Na xauna dake da xuciya daya banan bani da niyar cutar dake, tun kina qarama na dauki amanarki a wurin kakar ki, alhamdulillah na aurar dake ga mijin da nake ganin ya dace da rayuwarki, idan kika ci amanar sa Allah baxai barki ba, idan kika ci gaba da son el’mustapha a xuciyarki keda Allah kuma baxan taba yafe maki ba, ki rungumi mijinki da hannu biyu kuma ki so shi, mata da yawa a waje suna neman irin islam basu samu ba kada kiyi sake da damar ki, ko kashe auren kika yi kika fito baxaki taba auren El’mustapha ba hassalima baxaki xauna gidana ba sai dai kije qauyen ku kiyi zawarci.

Ta tashi ta fice, banan sai kuka take, ta dauki islam a matsayin qaddararta kuma xatayi masa biyayya ta xauna dashi da xuciya daya tasan jiddah baxata taba cutar da ita ba, el’mustapha ya riga yayi mata nisa har abada. 1

Jiddah na dawowa gida wanka tayi ganin dare yayi sosai, ta nufi dakin el’mustapha suna hada ido ta saki ajiyar xuciya tana kallon sa.Kallon ta El’mustapha yayi, kafin +

Yace uwar amarya an dawo kenan.

Ta qarasa cikin dakin, shimfidar da airah tayi tana kallonsa,

Me ya hana ka barci tuntuni el’mustapha? 1

Rashin barci nawa kuma ya xama abin tuhuma yanxu jiddah, lallai

Sai ya gyara kwanciyarsa hade da lumshe idanunsa,

Ta tabe baki ta xauna tana fadi a ranta in ma banan ce ta riga ta xamo matar wani a yanxu.

Pampers ta soma sakawa airah, tayi feeding din ta kafin ta kai ta saman bed din ta, ta kwantar da ita, ta rage hasken fitilar dakin ta dawo bayan el’mustapha ta kwanta.

Haka take ji cikin kashi 70 na damuwar ta 30 ya kau, uwani ce babbar matsalarta a yanxu kuma bata san yanda xata bullowa al’amarin na ta ba.

Ta sauke numfashi a hankali tana kallon el’mustapha tuni ya jima da yin barcinsa, ta lumshe idanuwanta tana karanto addu’ar barci a xuciyarta.

*

Kuka take tana qarawa, lallai sai an maidata dakin ta.

Saboda baa sona ba wanda ke maganar yayi min aure a maidani dakin mijina abin sona, banan ma da take mai aiki anyi mata aure, ta auri miji mai kyau da kudi sai dan ni da ake ma baqin ciki anqi a maidani dakin mijina.

Sam hajiya bata kula ta ba, ta cigaba da hada kayanta saboda gobe xasu bar garin

Uwani ta tashi ta fito daga dakin taci sa’a kuwa el’mustapha ya fito xai je aiki,

Ta sunkuya tana fadin yaya an tashi lfy, yaya kayi haquri ka yafe min kuskuren da nayi a baya dan Allah ba danni ba ka yafe min, ka roqa min anti jiddah ta yafe min mu dawo tamkar da, dan Allah yaya ka taimakeni nima qanwar kace kuskuren da nayi a baya jarabawa ce da qaddara da bata wuce bawa.

Shikenan ki tashi komai ya wuce… yana maganar ne fuskarsa a daure,

Yaya a bani key din daki na xanje na gyara, yaushe xan fara karban girki. 1

Kafin yayi magana sai ga jiddah ta fito duk da bata ji me uwanin ke fada ba amma tayi mamakin samun uwani da el’mustapha a falon ta, gabanta ya tsananta bugawa.

Idan hauka ke damun ki uwani, na fiki hauka a yanxu indai akan el’mustapha ne, wallahi in baki barshi ba xan iya halaka ki ban damu ba.

Uwani ta tashi tana fadin haquri naxo na baki anty jiddah ki yafemin kuskuren da nayi a baya wallahi sharrin qawa ne, ni yanxu xuciyata a wanke take da alkhairi baxan cutar dake ba, ki qara roqon yaya ya aure ni ko baya da kudin sadaki ni xan iya ara masa, idan key din dakina yana hannunki ki bani naje na gyara. 2

Jiddah tace tau shikenan bari na baki, ta juya da sauri kamar mai neman wani abu

Ta rasa me xata dauka, kujerar dinning ta dauka tayi kan uwani a fusacce,

Uwani na ganin haka tayi bayan el’mustapha da gudu tana fadin,

Aa yaushe anti jiddah ta fara hauka kuma shine abba bai kaita itama a duba ta ayi mata aiki ba,

El’mustapha ya tare jiddah da sauri,

Me kike yi haka jiddah, kashe ta xakiyi?

Ko sauraren sa batayi ba tayi bayansa suka soma xagayen sa yana tsaye a tsakiyarsu, ya kalli wannan ya kalli waccan,

Lallai basu da hankali, wani abu ya taba kan jiddah indai ba gurin aikin bane aka taba kwakwalwarta, 1

Ya tsaida uwani cikin bacin rai yana kallon jiddah,

STORY CONTINUES BELOW


Yace xo gata ki dake ta jiddah, ga mamakinsa kuwa tayi kan uwani da gaske xata iya rotsa mata kujerar a kai,

Cikin fusata el’mustapha yasa hannu ya tare dukan da ta kaiwa uwani sai a hannunsa, yana juyowa ya dauke fuskarta da Mari karo na farko a xamantakewar auren su. 1

Falon ya dauki shiru na wani lokaci kafin jiddah ta saki abinda ke hannunta tana kallon el’mustapha.

Ita kanta uwani ta tsorata bata taba tunanin akwai ranar da el’mustapha xai iya dukan jiddah ba,

Ya yarfe hannunsa cikin jin ciwon dukan da jiddah ta kai masa, har lokacin fuskarsa ba walwala,

Yace na rasa gane meke damunki jiddah, yarinyar nan abba da kansa jiya yake gayamin hankali bai ishe ta ba, har aiki akayi mata amma babu wani cigaba, mutane nawa ne masu matsala irin ta uwani a duniya kuma aka xauna da su, saboda me xaki biye mata, shekaranjiya kin rotsa mata kai yau ma so kike ki rotsa mata kai ta qara samun wata matsalar akan wannan da take da, dan me baxaki kyaleta da haukanta ba is she not your sister?

Kallon uwani jiddah tayi kafin ta maida kallon ta ga el’mustapha,

Saboda uwani yau kake Mari na, saboda ina nemawa kaina yanci a yanxu shine nayi kuskure har ake kirana banda hankali, menene uwani batayi min ba nayi haquri, wace wahala ce ban sha akan uwani ba duk nayi haquri tun kafin na aure ka, wace yarda ce banyi wa uwani ba ta cuceni, na aura mata mijina tana son fiddani a gidana ta rabani da ya’ya na, tana son rabani da duniyar gabaki daya, wanda bashi da hankali yasan ya cutar da dan uwansa, bata da hankali tasan ta biya saboda a sace ni, a gabanta aka nakasa qafafuna, a gabanta aka dauke ni aka tafi dani duk cikin bata da hankali ne, ita uwani wace irin mutum ce, wace xuciya ce da ita marar tausayi da imani, taya xata xauna da mijina ni ta barni xaune a daji qarti suna gadina batare da tayi laakari da cikin dake jikina ba, a gabana uwani tasa a harbe min yarona, kishi ne ko hauka?

Wata na nawa kwance bana tafiya duk ta dalilin ta, bata xo neman gafara na tana nadama ba sai dan na qara aura mata mijina tun da na xama sakarai, amma yau jiddah ake ganin laifinta akan uwani, uwani ce mai gaskiya saboda bata da hankali, uwani ce yau ake tausayi saboda bata da hankali, duk haqurin da nayi yau baa ganin sa saboda uwani bata da hankali, duk jajircewata da tausayina akan ta a lokacin da kowa ya juya mata baya, yau kuma kowa uwani saboda ni bani da kowa da xai yi siding dina, iyayena basu da rai da xa suce suma yar’su tayi gaskiya, gaka ga uwani el’mustapha, ta juya da sauri tana goge hawaye da tafin hannunta.

El’mustapha yabi bayan ta a sanyaye, sai jin muryar uwani yayi tana fadin,

Ai da ka kyaleta tayi fushi ta tafi, ba gani ba, tunda kana dani ba damuwa, amma dai kaje ka rarrashe ta kaine baka kyauta ba da ka dake ta.

Ko kallonta bai yi ba yayi shigewar sa,

Uwani ta xauna tana fadin ta bani tausayi tana da gaskiyar ta wlhy, kuma ita taqi yarda na shiryu ba cutar da ita xanyi ba, gashi yau har tana tunanin ita marainiya ce amma ko jiddan bata ma abba da hajiya adalci ba su da suka raineta, bari ma nagayamasu butulcin da tayi masu, ta tashi ta nufi inda hajiya.

Hajiya kinji me jiddah ke fada,

‘Naji komai uwani, xo ki hada kayanki ki bar gidannan, duk abinda jiddah ta fada gaskiya ne banga laifin ta ba, kece kika ja komai kuma jiddah tayi haquri dake.

Uwani ta tunxure baki, ni wlhy ba inda xanje, ba wanda ya isa ya rabani da gidan mijina, haka kawai ita anti jiddah ba tana da tausayi ba saboda me yanxu bata tausaya min ta aura min shi.

Uwani ki nutsu kisan me kike, ba kowace mace irin jiddah xata maki abinda ta maki a baya ba, ki tuna yarinyar nan fa dukiyar ta dake hannun mu ko sau daya bata taba mgn akai k…

STORY CONTINUES BELOW


Ke hajiya sai anyi magana kice dukiyarta, ai ba dukiyarta muke ci ba, abba yace ya ajiye mata komai nata yana juya mata dukiyarta idan an fitar da riba yana boye mata, ba ciki muke ci da sha ba, abbana yana da kudi kowa ya sani, idan dukiya kike so in kinyi haquri nima fa karatun nan xanyi nayi kudi kiyi alfahari dani ya’yana suyi alfahari dake kuma wlhy duk me min baqin ciki a rayuwa ko kwandala baxai ci ba.

Hajiya ta girgixa kanta, Allah ya shirye ki uwani, Allah ya shiryeki, Allah ya shiryeki.

Uwani ta muskuta tana fadin amin, addua ce kowa yana so, ni yanxu so nake ki saka baki a wannan maganar saboda da kinyi magana wallahi jiddah xata ji, na lura tana maki biyayya tana son ki kuma tana jin maganar ki, kice ta bari a maidani dakin mijina indai ba baqin ciki xaa min ba, kowace mace na gidan aure sai ni, wai ace harda mai aikin da nafi matsayi da gata tayi aure ta barni.

Nan ma hajiya batayi magana ba, so take taje ta rarrashi jiddah kuma kada ta qara jin ta kira kanta da marainiya.

Yana shiga ya sameta tana hada kayanta cikin jaka kuka take sosai airah na kuka,

Hankalinsa in yayi dubu ya tashi, me jiddah ke nufi xata tafi ta barshi ne ko me.

Sai ya nufi airah dake kuka sosai amma uwar taqi ta kulata, ya rasa yanda xaiyi da ita sai ya dauki sucker ya saka mata a baki ta fara tsotsa.

Ya juya yana kallon yanda jiddah ke ta xuba kayan ta a jaka tana kuka, ya qarasa gurin ta a hankali jikinsa na rawa gashi yayi latti sosai gurin aiki,

Am so sorry jiddah, idan Marin da na miki ne yayi maki xafi xo ki rama, 3

Ko kallonsa bata yi ba, ta rufe jakar, ta dauki hijab ta saka, hankalinsa ya qara tashi,

Ina xaki je jiddah? taqi sauraronsa, tana qoqarin ficewa ya riqota, cikin daga murya yace ina xaki je nake tambayarki,

‘Wannan ba damuwar ka bane ta fada cikin muryar kuka,

Ya gane Marin da yayi mata sam bai kyauta ba kuma yasan ba yanda xaa yi ta fahimce sa duk da yana ji kamar ta ji masa ciwo a hannu sai yaje an duba,

Sai ya tsinci kansa da janyota xuwa jikinsa ya rungumeta sosai, duk da suna cikin bacin rai sai da suka ji wani irin yanayi,

Cikin sanyin murya yace, yaji xakiyi jiddah, dan Allah karki fara wannan, kada kiyi yaji pls jiddah, kiyi min duk hukuncin da kike ganin ya dace amma banda yaji,

Ya sake kwantar da murya yana rarrashin ta, yasan halin ta sarai baxata saurare sa ba in ma ta sauraresa xatayi ta qalubantar shine, shi baiga laifinsa anan ba laifinsa daya na daga hannu ya mare ta, 1

Sai ya fita daga dakin hajiya yaje ya kira ya gayamata yana ganin ta nufi dakin jiddah sai ya dauki wayarsa ya fice,

Jiddah fushin ma har da yar ki!kina ji tana kuka ki rasa kama ta, waya ce maki laifin wani yana shafar d’a ko kin manta wahalar da kika yi akan ta.

Shiru jiddah bata yi magana ba, hajiya ta dauki airah ta kawo mata,

Karbe ta ki bata tasha kada fushina ya sauka akan ki yanxu,

Ba musu jiddah ta karbe ta, hajiya ta xauna tana fadin duk wannan matsalar duk akan uwani ne jiddah, ki kwantar da hankali uwani baxata taba auren el’mustapha ba, idan mukayi haka ai mun so kanmu da yawa.

Kuma da kike hada kaya kibar gidan kije ina jiddah?akwai inda yafi maki gidan mijinki kuma da ya’yan ki.

Cikin kuka jiddah tace da ace ina da iyaye a yanxu babu gidan da xai fiye min gidan uba na, gidan miji ai ba gidana bane,

Me kike nufi jiddah, mu ba iyayen ki bane, su waye iyayen ki bayan mu, kada bacin ran uwani ya fitar dake daga hayyacinki, idan abban ku yaji kina wannan maganar a tunaninki xaiji dadi jiddah?

STORY CONTINUES BELOW


Ni kaina banji dadin wannan maganar ba jiddah,

Jiddah bata yi magana ba, ta cigaba da shayar da airah tana kuka sosai, hajiya tasa hannu tana share mata hawayen, kafin ta janyota xuwa kafadarta,

Kowa yasan jiddah mai kirkice da haquri amma bansan me ya canxa jiddah yanxu ba, ki cire mgnr uwani a ranki, qanwar ki ce laifin da tayi maki a baya ki yafe mata kiyi haquri ki daina tunawa, maganar komawarta dakin ta babu ta ba wanda ya isa ya maidata, ki kwantar da hankalinki, kiyi rayuwa mai kyau da mijinki, el’mustapha yana son ki jiddah kidaina masa duk wani abu da xai daga hankalinsa, kukan nan kibarshi haka babu mgnr fushi dashi kin ji ko?

Jiddah ta gyada kai a hankali,

Maxa tashi ki maida kayanki yanda suke, bari naje da airah, ko da kike maganar baki son mai raino dole xaa dauko maki ita, ai ba duka aka taru aka xama daya ba, ZUCIYA kowa da irin tasa.

*

El’mustapha kuwa ya rasa sukuni ranar ko aiki da yaje ya kasa aiwatar da komai, tunanin sa kada ya dawo ya sami jiddah ta bar gidan, ya tashi aiki ya nufi gidan anty ikram ya gayamata komai.

Ita may tayi masa fada sosai na ganin laifinsa akan hukuncin da ya yankewa jiddah gaban uwani, wannan yarinyar ma har kuke barin ta xauna a gidanku, banda darajar iyayen ta da tuni banyi maganin ta ba.

Tare suka xo gidan shi da anti ikram.

Dai dai wannan lokacin hajiya ta tursasawa jiddah yiwa el’mustapha girki, ta gama hada komai ta fito ta sami uwani xaune a falon ta taci uban kwalliya tana xaune jiran el’mustapha ya dawo shi aka yiwa kwalliyar.

Ko kallonta jiddah batayi ba ta shigewar ta, toilet ta nufa wanka tayi ta fito daure da towel dai dai lokacin da taji muryar anti ikram a falonta tana sallama.

El’mustapha na bayan ta suka shigo, lokaci daya suka kalli uwani, el’mustapha ya nufi dakin sa batare da yayi magana ba,

‘Anty ikram tace, ke xaman me kike anan?

Uwani ta tashi tana inda inda dama tana tsoron anty ikram sosai bata taba sake mata fuska ba,

Anti ikram tace karna qara xuwa na same ki xaune a falon nan dai dai lokacin da mai gidan xai dawo, idan inda jiddah kika xo ki same ta a ciki kiyi abinda xakiyi ki fice bawai ki xauna mata ba,

Uwani ta gyada kai tana kallonta, ita kadai ce xata iya gayawa uwani magana ta kyale ta batare da ta maida martani ba, ita kanta uwani ta rasa meyasa take tsoron matar nan haka, shiyasa anti ikram ke daukar duk abinda uwani keyi iskanci ne ba wani hauka dake damun ta.

Fita daga falon nan kuma karna qara jin kin tsaya da el’mustapha idan bada amincewar jiddah ba, maganar a baki key kidawo dakin ki babu ta, jiddah bata so kuma el’mustapha ma baya so to xaman me xaki xo ki masu, idan aure kike so kije ki sami naki mijin a waje ko dole sai el’mustapha ne?

Uwani batayi magana ba ta juya tana kuka, ikram taja tsaki ta nufi dakin jiddah ta same ta xaune akan stool tana shafa mai.

Ta cikin madubi jiddah ke kallonta kafin ta gaida ta,

Ikram ta xauna dai dai lokacin el’mustapha ya shigo idanun sa akan jiddah.

Jiddah xo xauna nan magana xamuyi cewar ikram,

Ba musu jiddah ta tashi ta nufi inda take nuna mata ta xauna, idanunta na kallon kasa.

El’mustapha ya gayamin abinda ya faru tsakanin ku, duk irin mgnr da mukayi dake kin manta kenan, me na gayamaki idan el’mustapha ya bata maki.

Jiddah ta daqo tana kallonta idanunta taf da hawaye, ta kasa magana sai motsa bakin take,

Kiyi magana jiddah,

Da kyar cikin rawar murya tace, cewa ki.. kayi na kira ki na fada maki.

To meyasa baki kirani ba jiddah, amma shi gashi kinga ya kirani, ko dan ni ba yayar ki bace yayar el’mustapha ce kawai.

Jiddah ta girgixa kanta tana share hawaye,

Me yayi xafi haka har kike neman yaji, menene amfanin yaji ga mace, idan kika je kika barshi farin cikin yaran ki fa, sannan shi bakya tunanin halin da xaki saka shi, kenan el’mustapha idan ya maki magana ba kya bi, ba kya bin umarnin sa?

Jiddah ta girgixa kanta batare da tayi magana ba,

Ikram tace to meyasa idan ya maki magana bakya ji, yayi ta baki haquri kinqi.

A sanyaye tace ina bin maganar sa…. yimin shiru ikram ta katse ta cikin daure fuska,

Magana xan gayamaki kada ki koyawa mijinki qin jin rarrashi, ina nufin idan ya rarrashe ki to ki haqura,

Idan kika bari ya saba da idan ya rarrasheki kinka qi ji kika kangare wai ke Jan aji ko taurin kai daina rarrashinki xai yi yana tunanin ko yayi baxaki ji ba, kinga daga nan kin dauko hanyar da xai daina jin tausayin ki, ina gayamaki ne ba dan yana qanina bane kema qanwatace shiyasa na fada maki duk abinda yayi maki na bacin rai just take your phone and call me kigani idan ban xo na kwatar maki yancin ki ba.

Amma anty ikram meyasa xai nuna yafi tausayin uwani akaina, meyasa xai tsawa tamin akan ta har yana kirana marar hankali dalilin ta, kenan uwani ta fini a gurinsa.

Sosai anty ikram ta hau sa da fada da nuna masa rashin kyautawarsa, jiddah matar sace saboda me xai fifita uwani akanta, meyasa xaifi tausayawa uwani akan halin da ta saka jiddah a baya.

Ya sosa kansa, ya lura fushin na jiddah ba akan Marin da yayi mata bane tunda har batayi magana ba,

Yace sister ayi haquri

Kuma maganar duka kada ka qara El’mustapha sam banji dadi ba, ka hukuntata dai dai laifinta amma banda maganar duka, ko kadan bana son namiji mai dukan mace ko yane…

Yace kuskure ne na karbi laifina,

Jiddah bata ce komai ba, el’mustapha ya tashi ya fita,

Ikram ta soma bata baki tana rarrashin ta banda wauta irin ta jiddah saboda me xata damar da kanta akan uwani, ko mutuwa xatayi baxata auri Musty ba, ki kwantar da hankalin ki, mijinki shine farincikin ki, ki bi duk abinda yake so ki gujewa wanda baya so xakiji dadi, yanxu idan kina haka amira tayi kice mata me? Da yayi maki wani misbehaving da bakya so dauki waya kirani kigani, idan naxo idan ban mashi hukunci ba,.

Bata bar gidan ba har sai da ta saka jiddah dariya, ikram na barin dakin ya dawo kusa da ita ya xauna, tafin hannunta ya riqo ya hada da nashi yana murxawa a hankali.

Wani irin yanayi da take ji ne ya tilasta mata lumshe idanuwanta,

Kin yafe min dukan da na maki jiddah.

Ta daga kanta a hankali batare da ta kalle sa ba, ya jawota sosai ya rungumeta, lokaci daya suka sauke numfashi.

Al’amarin daya biyo baya baxai fadu ba🤧 da kyar ta janye bakinta daga nasa,

Yana kallonta yace bani abinci naci jiddah, yau komai ban ci ba tun safe.

Ta tashi a sanyaye ta fita batare da tayi magana ba, yabi bayanta da kallo kawai.’Ko da ya gama cin abincin jiddah bata dakin tana falon ta, da alama har yanxu bata sauko daga fushin ba.

Shi yanxu damuwar sa hannunsa dake masa zugi tun daxu. +

Da dare sai juyi yake akan gado ya kasa barci saboda xafin ciwon hannun, gashi ya kumbura, kallon jiddah yake barcin ta take cikin kwanciyar hankali.

Time ya duba, biyu na dare ya gota, ya sauko daga saman gadon ya fita daga dakin.

Sai safa da marwa yake tsakanin falon sa dana jiddah, yanda yake ji a hannunsa ya tilasta masa xuwa dakin da abba yake ba shiri.

A hankali yake buga qofar dakin,

‘Abba ya tashi yana tambayar waye? Jin muryar el’mustapha ya taso da sauri ya bude dakin yana tambayar lafiya?

‘Na kasa barci, hannuna ke ciwo sosai… El’mustapha ya fada yana nunawa abba hannun.

‘Abba ya duba hannun yana fadin ai gocewar qashi ne el’mustapha me ya jima ka ciwo haka.

Ya yatsina fuska kafin yace na dan xame ne daxu a toilet na fadi, yanxu ya xanyi abba.

Daurewa xaka yi kayi haquri har xuwa gobe sai kaje asibiti ko kuma ayi maka aikin gida duk wanda kake so amma ni bani da sani akan irin wannan matsalar.

Shiru el’mustapha yayi kafin ya juya yana fadin Allah ya kaimu goben.

Xama yayi bakin gadon ya dafe kansa da hannunsa daya, dole ya sami gocewar hannu saboda girma da nauyin kujerar, inda ta sami uwani a kai kenan xaa sami matsala ba babba dan ya tabbata kwakwalwar ta gabaki daya xata juye.

Jiddah ta bude ido tana kallonsa, kallon agogon tayi kafin ta maida kallonta garesa cikin mamaki, meke damun el’mustapha, me ya hana masa barci a wannan lokacin yake xaune?

Ta matso a hankali xuwa inda yake, hannunta ta kai wuyansa ta taba tunanin ta ko xaxxabi ne,

Ya dago yana kallonta, ita ma shi take kallo 
Tace meke damun ka?

Da kyar yace ba komai. 
‘amma naji jikinka da xafi ko baka da lafiya ne?

Ya girgixa kansa kafin yace ki kwanta jiddah ba abinda ke damuna.

Ta gyara xamanta sosai tana kallonsa,

‘Na kwanta nayi barci kai kuma kana xaune, idan lafiyar ka qalau tunanin me kake yi el’mustapha?

Yayi shiru baiyi magana ba, ganin ta matsa da tambaya ya nuna mata hannun.

Tayi shiru gabanta na faduwa tana kallon yanda hannun ya kumbura, ta kasa daqowa ta kalle sa harda wani nauyin sa take ji.

Yaja numfashi kadan yana fadin kije ki kwanta tun kafin airah ta tashi gobe kixo kina complaining baki sami barci ba,

Ta girgixa kanta kafin tace kayi haquri n….. Shishsssss ya katseta ta hanyar dora yatsanta akan labbanta yana kallonta.

Kije ki kwanta bana son gardama,

Ta matsa kadan daga garesa amma taqi kwanciya, bata da wannan nutsuwar bata san yanda yake ji ba ta tabbata duk abinda xai hanawa el’mustapha barci ba qaramin abu bane.

Ganin taqi ta kwanta ya saka shi kwanciya yana fadin xo mu kwanta jiddah nima barci nake ji.

Ta matsa ta shiga cikin jikinsa, ya rungumeta yana lumshe idanuwansa ba dan ya daina jin xafin hannun ba.

‘Washe gari ko da jiddah ta tashi el’mustapha baya gidan, tayi mamakin ina xaije da sassafe haka kuma tana da tabbacin ko wanka bai yi ba ya fita.

STORY CONTINUES BELOW


Ta shiga kitchen ta sami hajiya tana hada breakfast, gaidata tayi kafin ta soma taya ta suna yi suna fira jefi jefi cikin nishadi har suka kammala.

Goma na safiyar ranar el’mustapha ya shigo da alama gurin gyara ya tafi ganin yanda aka daure masa hannu.

Kai tsaye dakin sa ya nufa, jiddah tabi bayansa kallonsa take a sanyaye,

Sorry el’mustapha kayi haquri dan Allah,

Yace bani ruwa na sha magani, da sauri ta fita bata jima ba sai gata dauke da Swan da cup, da kanta take balla mashi maganin yana sha.

Ganin yana qoqarin cire rigar jikinsa ta taimaka mashi ta cire masa, ya kwanta yana fadin,

Kada ki tada ni jiddah, duk wanda yaxo bana nan,  na kashe wayar ma har yaranki kada ki bari su xo su dame ni.

Ta tashi tana fadin asha barci lafia, ya dan kalle ta yace lullubamin blanket sai ki kunna min AC.

‘Ko da su abba suka gama shirin tafiya jiddah har tayi wanka, ta shirya twins ta bawa driver ya kaisu inda anty yusrah har anjima kada rigimarsu ta tada mahaifinsu daga barci.

‘Abba yace ina el’mustapha da hannu, jiya bai sami barci ba ashe ya xame ya fadi ne yaji ciwo.

Jiddah tace bai jima da dawowa gurin gyara ba, ya sami barci yanxu.

Hajiya tace Allah ya bashi lfy idan ya tashi ina mishi ya jiki.

‘Abba yace mu xamu tafi idan ya tashi ki gaidasa.

Suka firfito harabar gidan, jiddah dauke da airah sai wasa take mata tana dariya,

‘Abba ya dubi uwani yana fadin ke kuma fa ina kayanki?

Uwani ta tunxure baki tana fadin ni xan raka ku ne ku tafi ba inda xanje ni.

Hajiya ta fito mota tana fadin baki isa ba, dole sai kin bar gidannan xaman me xaki masu.

Uwani ta juya tana fadin ance mijina bashi da lafiya sai naje na barshi saboda na xama sokuwa, idan ba baqin ciki ake min da ladar jinya da xan samu ba saboda me xaa tafi dani, ni ba inda xanje wallahi jinyar mijina xanyi.

‘Abba xaiyi magana jiddah ta katse shi, shiga mota ku tafi abba Allah ya kiyaye ya kaiku lafia, cikin murmushi ta dubi driver da xai kaisu wani dan sanda ne, tace sai kayi a hankali da tsofaffin nan basu saba da gudun mota ba kamar el’mustapha,

Babu matsala madam, su abba suka shiga cikin motar, jiddah ta matsa lokacin da aka tayar da motar, tana tsaye gurin suka fice kafin ta koma cikin gida.

Tana tafe tana cira airah sama cikin mata wasa yarinyar sai dariya take, ta sami uwani xaune a falon ta kunna TV tana kallo, inda take Ma jiddah bata kalla ba tayi shigewarta dakin ta.

Da sauri ta qarasa gurin wayarta dake qara, New number ta gani hakan bai hanata daga wayar ba.

‘Anty jiddah an tashi lafiya… taji muryar banan a daya bangaren.

Cikin murmushi jiddah tace amarya ce ke kira haka da sassafe,

Tace tun daxu nake kiraki baki daga ba,

Jiddah tace bana kusa ne, ya kwanan amarci.

Murmushi kawai banan tayi batace komai ba, dama jiddah tasan baxata amsa ta ba tasan banan da kunya jiddah ta cigaba da fadin, babu dai wata matsala ko banan?

Babu anti jiddah, na kira ne na gaidaki na qara maki godia akan hidimar da kika min, kin min gata inaji ko iyaye na keda rai iyakar abinda xasu min kenan, nayi kukan farin ciki anty jiddah idan na dubi irin kayan da kika min, ban san da wane baki xan gode maki ba illah nace Allah ya saka da alkhairi ya kuma kare ki daga sharrin maqiya, sannan anty jiddah nayi kukan baqin ciki idan na tuna na so mijinki kuma kinsan da haka, ina jin kunya da nauyin ki anti jiddah dan Allah ki yafe min.

STORY CONTINUES BELOW


Babu komai banan cewar jiddah, kidaina tuna duk abinda ya wuce, kuma duk abinda kike so ko akwai wata matsala duk ki gayamin.

Tau shikenan anty jiddah su kaka ma sunce xasu xo yi maki godia sannan anti jiddah wannan gas din bansan yanda ake amfani dashi ba, akwai abubuwa da yawa wadanda bansan kan su ba.

Oh oh… yanxu dai baxan sami xuwa ba sai an kwana biyu haka amma xan kira nabila na gayamata sai taje ta nuna maki komai ai baki fara girki ba ko.

Tace aa a gidansu aka aiko mana sai nan da sati daya yace kafin na fara girki.

Tau shikenan babu damuwa, ina gaida islam din.

Murmushi kawai banan tayi bata amsa ba kafin tace ina airah anty jiddah.

Gata nan tana ta missing din ki banan, nima kaina nayi kewarki abubuwa sun min yawa a yanxu dole dai sai na dauki wata mai aiki ko na dawo da Inna cikin gida tunda su suna da yawa acan.

Hakan yayi amma Inna xata bata maki falo da yawun goro kin santa fa yanda ake rigima da ita ko ina xubar da yawun goro take yi.

Jiddah tace sam na manta hakane fa, dole wata xan dauka.

‘Anty jiddah ki kawomin twins na gansu…

Xasu xo banan idan xan xo, ki kula da kanki.

Nagode anti jiddah, ta tsinke wayar.

Jiddah ta xauna tana dialing number anty ikram, bata jima da ringing ba ta dauka, suna gama gaisawa jiddah ta soma yi mata bayanin komai akan rashin komawar uwani, anty ikram ta tsinke wayar tana fadin gani dama ina hanyar xuwa gidan el’mustapha ya fadamin bashi da lafia.

Batare da damuwa ba jiddah ta tashi ta goya airah, ta sami uwani ta qure volume tana kallo ta tuna el’mustapha barci yake, sai taje ta dauki remote ta rage volume din, tana ajiye remote din uwani ta dauka tana qara volume.

Gabaki daya jiddah ta kashe kallon tace kada ki qara kunna min komai anan.

Meyasa anti jiddah, inba neman fitina da baqin ciki ba saboda me ina kallo xaa xo a kashe min.

Saboda gida na ne kuma komai nawa ne kuma wallahi idan kika qara kunna min kaya sai kinyi mamakin abinda xan maki, tayi shigewar ta kitchen

Uwani ta tabe baki tana binta da kallo,

Kunji  wai gidanta dadin abin nima gidan mijina ne… bata gama maganar ba taji muryar ikram na sallama xumbur uwani ta tashi cikin rawar jiki ba shiri ta soma gyaran falon kamar wacce aka sata.

Gaisuwar da uwani tayi mata bata amsa ba, jiddah ta fito kitchen da wuqa a hannunta, cikin murmushi take gaidata.

‘Anty ikram tace ina su hajiya ne naji gidan tsit.

Jiddah tace ai suna hanyar komawa,

Ikram ta dubi uwani fuska a daure tace to ke kuma xaman me kike da baki bisu kuka tafi ba.

Jiddah tayi caraf tace ta xauna tayi jinyar mijin tane wai a bata key na dakin ta.

Uwani tayi narai narai da ido tana fadin yaushe nace haka, kada kimin sharri.

‘Anty ikram ta dubi jiddah tana fadin bani makullin dakin nata jiddah,

Jiddah ta maida wuqar ta ajiye kafin ta nufi dakin ta da sauri tana gyara goyon dake bayanta.

Uwani taja numfashi a hankali tana jin wani sanyi lallai matar nan tana sonta bata da baqin ciki tunda har xata maidata dakin ta.

Jiddah ta dawo ta miqawa ikram key din dakin, ta karba tana kallon uwani.

STORY CONTINUES BELOW


Ina kayan da kika xo dasu,

Cikin rawar jiki uwani tace suna wancan dakin bari na dauko, da sauri taje tana kwaso kayanta duka ta ajiye a tsakiyar falon,

Ikram ta soma tafiya tana fadin biyo ni a baya, uwani ta bita sai murmushi take harda kallon jiddah tana mata gwalo a fakaice tace yar baqin ciki sai dai ki mutu.

Murmushi kawai jiddah tayi batare da tayi magana ba tamkar bata ji me uwanin ke cewa ba.

Ikram ta bude dakin tana kallon uwani shiga ciki ki fito da duk kayanki da kike so aciki ki hada su cikin wadancan dake tsakiyar falon kana ki gyaran dakin tsab kafin naxo.

Farin ciki ya qara mamaye xuciyar uwani, ta juya dauko tsintsiya ta shiga dakin tana fito da kayanta, ba laifi dakin yayi qura amma haka uwani ta soma gyara batare da damuwa ba tunda dai xaa maidata dakin ta ko menene xatayi.

Jiddah taja tsaki tana sauke airah ta rasa dalilin da yasa yarinyar bata son goyo ko yaya ne xata fara mutsuniya har a sauke ta,

Ikram tace ina el’mustapha din,

Yana daki barci yake yi, ikram ta nufi dakin sa, jiddah tayi saurin kallonta tana fadin anty ikram yace kada a tashe sa fa.

Baxan tashe sa ba jiddah ai ya gayamin jiya bai sami barci ba hannun nasa kawai Zan duba.

Jiddah ta dauke kanta daga kallonta, ikram ta nufi dakin el’mustapha, bata jima ba ta fito tana fadin ya kanainaye cikin bargo haka taya xan iya ganin hannu, sai ya tashi tukunna.

Ta sami guri ta xauna nan falon tana kallon jiddah,

Gashi nan sai fama kike da yarinya babu mai riqa maki, gata da shegiyar fitina wannan da alama sai tayi quya.

Jiddah tayi murmushi tana kallonta,

Ke dai na gane kina son yarinyar nan sosai kike nuna mata halin ko in kula, kin ganta kyakkyawa da ita ba kamar twins din ki ba.

Me xanyi da wannan ajebo cewar ikram…. Uwani ta fito tana ajiyar xuciya da alama ta gaji sosai, 1

Tace na gama anty ikram cikin washe baki😁

Kallonta suka yi a tare sai xufa take kamar wacce tayi wani aikin axo a gani.

Ikram ta tashi tana fadin yauwa uwani, taje ta rufe dakin da key ta bawa jiddah.

Annurin dake fuskar uwani ya soma gushewa,

Tace saka hijab din ki ko gyale ki fito, yanxu xan saka a fito da kayan naki.

Jiddah da ikram suka fito, a sanyaye uwani ta yada gyale a kafadarta tana fadin to ko wancan part dinne xata kaini, ta fito tana kallo aka soma fito da kayanta ana sakawa a booth din anty ikram.

Uwani ta qara tsuke fuska, ni me xanyi a gidanta inba baqin ciki ba me xai sa ta rabani da gidan mijina.

Ana gama saka kayan a mota ikram ta dubi uwani tana fadin bismillah shiga mota,

A sanyaye uwani ta bude motar ta shiga, ikram ta dubi jiddah tana fadin je ki kula da mijinki idan ya tashi ki gayamasa na shigo.

Cikin farin ciki jiddah ta juya bayan ta fakaici idon ikram suna hada ido da uwani tayi mata gwalo irin mai cin rannan, ta juya cikin gida tana murmushi.

Uwani ta soma hawaye, anty ikram ko kallonta batayi ba taja motar suka bar gidan.

Kai tsaye tasha ta nufa da ita, sai da ta tabbatar uwani ta shiga mota har kayanta an gama sakawa, ta biya kudin motar kana ta sunkuya tana kallon uwani.

Idan kinje ina gaida hajiya da abba, naxo na masu bankwana ashe sun tafi, ke kuma kinxo ki xauna ki hana mata sakewa da mijinta, bayan ga gidan uban ki, ban gaya maki el’mustapha yafi qarfin ki ba kuma baxai taba maidaki ba, ki fitar da naki mijin mana idan babu ni baxan rasa wanda xan hadaki aure da shi ba amma a sakarwa baiwar Allah nan mijinta abarta haka taji dadin abinta yanda hankalin qanena xai sami kwanciya ya more tasa rayuwar.

Uwani ta hadiye wani qololon baqin ciki ta dauke kanta gefe tana hawaye,

A ranta tace idiot yar baqin ciki sai nadawo ba wanda xai rabani dashi kowa baqin ciki yake min da gidan mijina baa so na xauna.

Ikram bata bar tashar ba sai da motar su uwani na daga kana ta shiga ta ta motar tabar gurin.

(karki damu uwani qawarki Batul Mamman xata maidaki tunda ta xama UwanitulBatul tana maki Son So💖) 4

Bata jima da shiga gidan ba taji sallamar ibrahim, amsa sallamar tayi ta nufi dakin ta, hijab ta saka ta fito suka gaisa,

Tun safe nake kiran wayar Musty a kashe, office sai neman sa ake bai fita aiki ba shine naxo na duba ko lfy?

Bashi da lafiya ne ibrahim, kuma yana barci a yanxu.

Ibrahim ya xauna yana fadin Allah mai iko, naga lafiya lau muka rabu dashi jiya, meke damun sa.

Jiddah ta xauna tana kallonsa, yaji ciwo a hannunsa,

Oh yes nagani jiya sanda yace hannun na masa ciwo, na gayamasa lokacin yaji sosai yanda naga baya son riqa hannun ayi yace aa kumburi ne yayi da ya sha magani shikenan.

Tace ni bansan yaji ciwon ba sai da dare da ya kasa barci,

Kuma ke kika ji masa ciwon nan fa duk wajen rigimar kishi banda abin ki ina musty xai iya maida uwani a yanxu,

Ta tabe bakinta kafin tace ni baxan gane hakan ba,

Ya juya yana kallon dinning, dole Musty yaji ciwo waccan heavy chair, gsky yaji maxa tunda ba jikin qarfe ne da shi ba dole xai ji ciwo,  kuma da gaske xaki iya rotsa mata ita banda el’mustapha ya hana?

Wallahi kuwa, fashe mata kai duk mai sauqi ne  akan ni da taso kashewa, ta iya nakasa ni ballantana ni?

Yace haka ne, uwani ta bata mana jiddah,

Murmushi kawai tayi, ya soma qoqarin tashi yana fadin idan ya tashi ki fada masa naxo ina je office xan sanar dasu.

Taimako nake so ka min ibrahim…. ta katse, ya juya yana kallonta bayan ya xauna.

Taimakon me jiddah.

Ka taimakeni, bansan yanda xanyi ba, bani da wata mafita a yanxu bayan wannan dan Allah ka auri uwani… 4

Ya saki baki ya xuba mata idanu yana kallonta,

Ni na auri uwani, Allah ya sauwaqe min, matana biyu suna xaune lafiya shigar uwani a gidana tamkar tashin bomb ne a Maiduguri.

Believe me ibrahim, ina so ka auri uwani saboda kasan halinta kasan wacece ita xaka iya xama da ita, ina so ka aure tane saboda nasan baxaka cutar da ita ba, ba kowane namiji ne a duniyar nan xai iya xama da uwani a hakan ba, dan Allah ka aure ta ka koya mata sonka wallahi xata so ka xata nutsu, ina sa rai uwani xata gyaru amma ni baxan taba iya gyara ta ba saboda ta rainani. 4

Ya tashi yana fadin matar abokina kike so na aura, yarinyar da bata da tarbiya ba wanda ya isa ya fada mata ta ji, so kike nima ta saka matana acikin wani hali ta tarwatsa xaman su.

Jiddah ta tashi tana kallonsa El’mustapha bashi da matsala ibrahim, shima xaiyi farin ciki da hakan, iyayen mu xasu ji dadi ace yau uwani tayi aure ta nutsu ka taimakeni ka taimaki soyayyata da el’mustapha.

Ibrahim ya tabe bakin sa ya juya yana fadin we talk later jiddah idan nayi tunani. 1

Tace tau shikenan, ta nufi cikin gida, tayi mamakin sunyi saurin gama abincin rana haka har suna rabawa maaikatan gida, gashi ita yanxu take shirin dorawa, sha biyu har ta gota.

Hadixa ga airah ayi mata wasa, idan tayi kuka ki goyata in taqi sai ki kawo min ita.

Ta dawo cikin gidan a hanxarce, dakin el’mustapha ta fara nufa ta duba shi kafin ta dora girkin.

Xaune ta same sa bakin gado ya dafe kansa da hannunsa daya, ta qarasa gurin sa da sauri ta dafa sa tana fadin,

Ya jikin, har yanxu hannun yana ciwo ne?

Ya girgixa kansa a hankali,

Get me something to eat,

Sai a lokacin ta tuna ko breakfast bai yi ba, ya tashi ya nufi toilet, ta fita……..

Su abba sun tafi ne, ya fada yana kallonta bayan ya xauna a dining,

Sun jima da tafiya sunce a gaida ka da jiki.

Ya gyada kansa kawai batare da yayi magana ba.

Ta cigaba da ciyar dashi……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page