GIDAN SARAUTA CHAPTER 9

GIDAN SARAUTA

CHAPTER 9


Babban guri ne wanda ke dauke da dumbin bayi da kowanne suna da fannin aikinsu wasu suna wanke wanke,wasu yankan albasa wasu gyaran kayan miya,wasu tankade gari wasu su kuma suna fannin girki………… +

Binsu take da kallo abun tausayi don abunda ta lura dashi kusan gabadayansu agajiye suke ga duk kayan jikinsu sun kode sunyi dikin dikin dashi mostly jitayi Hindatu nacewa”Gimbiya ga Jakadiya itake kula da duk wani harkokina abinci”……
Murmushi Asma’u tayi tareda kallon dattijuwar da Hindatu takira da Jakadiya kafin tagaida ta gaida ta Itama jadiyar gaisheda Asma’un tayi cikeda ladabi kafin takara da sannun ki dazuwa Gimbiya……

Yauwa sannu jakadiya ya ayyuka?….
Alhamdulillah tabata ansa kafin tace zamu zaga dake ne kiga kitchen din?…
Gyada kai tayi ahankali kafin suka fara tafiya tana binsu yawanci guraren yanmatan daketa aiki suka kaita suna nuna mata ayyukan dasukeyi kafin suka karasa wurin rabon abincin bayi donkuwa yanzuma aka sauke abincin daren……
Layin kwanuka ne ah ajiye sunfi ah irga yayinda masu raba abincin inkaga yanda suke difana shi kaman wanda za abaiba kaji suci ko kulwa don inzata iya rantsewa duk abincin da ake sawa mutum befi ya’iya loma ukuba inyayi tsawoma to loma biyar cikeda mamaki tace wannan ne abincin da ake basu?……

Gyada Kai Jakadiya tayi sannan tace sau uku ah rana ake basu ai Gimbiya………
Shiru kawae tayi batace komai ba kafin jakadiyan tarakata bangaren abincin manyan masarautar inda taga bama mutane dayawa ke girkataba gakuma abinci da akeyi kala kala agurin haka tana ganin wayanda aka fara zubawa ma ancika kuloli makil bakaman na bayin data gani ana difana musuba seda jakadiya tagama mata bayani tareda zagata koina kafin tarakasu bakin kofa tadawo kitchen din tafiya suka cigaba dayi don zasu kaita wani bangaren kuma itadai cike take da curiosity don haka takasa shiru tabudi baki tace”nikam Iya Hindatu iya Quantityn abincin da ake baiwa bayi kenan sau biyu ah rana?……
Gyada kai Hindatu tayi kafin tace”eh Gimbiya wani ahakan ma bazai samuba don inbaka kawo kwanonka dawuri ba aka gama rabo babukai babu samu kwata kwata sede ka kwana da yunwa don ba kowani bangaren da kake aiki bane za abaka abinci kaci don baka isama kace zakaci abincin da manyan masarauta keci ba cewama akeyi raini ne………
Cikeda damuwa Asma’u tace”to ba akawo kayan abincin ishasshene komi?”…….
Hummm shine abunda Jamila tace kafin tadubi Asma’u tana”Gimbiya abun masarautar nan se ahankali nibansan ranar da bayi zasu samu yancin kansu ba”,Yar dariya Hindatu tayi kafin tace”kilan se randa Magajiya tabar duniya”…….
Mehakan ke nufi Iya Hindatu dasa hannunta ah rashin bada abinci ishasshe komi kikeson fadi?….
Aikomai ma dasa hannunta Gimbiya, Magajiya babba ce ah masarautar nan da babu wanda yakejadaita duk abunda tace ayi shi akeyi ko anaso ko ba aso, tsarin abincin dakikaga anabama bayima ita ta gindaya shi don kayan abinci ishasshe anakawo amma setace baza’a dafa iya yawan dazai isaba kadan za adafa sabida in bayi suka ci abinci dayawa bazasu iya aiki mekyau ba yandama naji anacewa raba sauran kudin sukeyi da wanda keda dawainiyar kawo kayan abinci haka na sutura ma Gimbiya ance ana raba mana kaya set bibbiyu bayan shekara shekara Kuma ana bada kudi amma baswa bamu sesucinye kudin ah tsakaninsu wani sa’in bayan shekara uku abamu inmunyi sa’a kenan inko bamuyiba yana iyakaiwa tsawo shekaru biyar ma ba abamu wasu kayan ba shiyasa inkika lura zakiga duk kayan bayi wasu sun barke wasu sunyi baci wasu kuma kodewa yayi………
Shiru Asma’u tayi tana Al ajabin wannan wulakancin wato Magajiya bata tsaya akan mutanen marasautar bama harda bayi takeyi ma mugunta lallai she’s so cruel and tasamu dama dayawa ah masarautar nan donkuwa talura anbata power mai karfi jin kaman ana dukan mutum d bulala ne yasata dagowa cikin sauri daga tunanin datakeyi……..
Fili ne gurin babba sede an siminte koina da cement yayinda gurin ke dauke da taps ta bangare bangare gakuma thanks takoina wanda inada tabbacin suke supplying ruwa to d tap bayan anyi pumping ruwa gakuma kayan wanki zube takowani direction bayi se zuba wanki sukeyi……….
Idanunta ne suka sauka kan wanda taji anata duka dan sakannin da suka wuce jitayi yarinyar na kuka helplessely tana”Yaya Hafsatu banida lafiya wallahi hajijiya nikeji bazan iya wankinnan ba”……..
Wani irin katon bulala wanda aka Kira da hafsatun takuma yarfa mata tana zare idanu”don ubanki kitashi bawani lafiyar ki kallo zakizo kina karya tosekin yi wankinnan kokin ki kokin so”……..
Hindatu ne tadubi Asma’u tana”Gimbiya nanne fannin da bayi ke wanke kayayyakin manyan masarauta kusan koyaushe kikazo wanki akeyi harta tsakiyan dare sabida kowa da lokacin dayakezuwa yayi wasu sanda yan uwansu keyi su suna wani aikin haka sauranma kuma indai kazonan dole kayi abunda yakawoka babu zama batun hutawa Kinga wancan Hafsatun?…..
Gyada Kai Asma’u tayi ahankali Hindatu tace….

STORY CONTINUES BELOW


“itace shugabansu,inmutum yayi kuskure itake hukuntasu kafin akai gaban Magajiya”…….

Cikin sauri Asma’u tace to Amma yarinyar can da alama ba karya takeyiba miyasa za ayita bugunta?….
Murmushin takaici Jamila tayi kafin tace”Babu wanda yake yarda in bawa yace baida lafiya daukan hakan sukeyi amatsayin karya dakuma neman hanyar dojema aiki shiyasa bayi da dama suke rasa rayukansu sabida wannan muguntan,babu wanda yadamu da al amarinsu barekuma lafiyar su”…….
Mai Martaba fa?, Asma’u tayi tambayar cikeda curiosity……..
Kallonta Jamila tayi kafin tace”baisan komai dake faruwa ba don daga bangarenshi yana iya kokarinshi ae yadankama Magajiya kula da bangaren nan shiyasa kikaga hakan na faruwa shikuma duk ah tunaninshi tana akwatar da abunda yadace ko ankira mutum bada shaidama bazai iya budan baki yafadi gaskiya ba sabida tsoron abunda zai biyo ba……….

Hmmm shine abunda Asma’u tace kafin tayi hanyar inda taga yarinyar da tace bata lafiya take tana tsugune gaban kayan tacigaba da wankin kaman yanda akasakata tayi amma se hawaye takeyi ga jikinta na wani irin karkarwa don kallo daya zakamata kagane batada ishashen lafiya…………..

Ahankali Asma’u ta dan duka takamo hannunta tareda cewa tashi kinji……
Tashi baiwar tayi jikina karkarwa ga jikinta wani irin zafi kaman ruwan zafi kallon Asma’un tayi hawaye nabin kuncinta tareda cewa”wallahi banida lafiya”….
Bakaramin tausayin ta Asma’u tajiba ahankali ta janyota zuwa jikinta tana dan taba temperature din jikinta”sannu kinji?”……
Duban bangaren dasu Jamila suke tayi sannan tace ta inane clinic din masarautar yake cikeda girmamawa Hindatu da Jamila sukazo suka rike yarinyar suna……
“zamu kaita Gimbiya basai munje dukan mu ba”……
Kallonsu tayi sannan tace aa muje dai duka inyaso makwarasa daga baya haka kuwa akayi sukakai yarinyar clinic akayimata treatment tareda bata drugs kafin sukace gobe tadawo takarbi maganin again taimaka mata sukayi harzuwa bangaren bayi tareda Asma’u din dakuna da dama suka wuce amma babu katifa ko daya abun yabama Asma’u mamaki amma sebatayi maganaba harsuka Isa dakin da yarinyar take zama karema dakin kallo Asma’u tashigayi kafin tace anan kuke kwana ne?…………..
Gyadamata kai yarinyar tayi kafin Asma’u tace to ai babu katifa badai kasa kuke kwanciya ba,sake jijjiga matakai yarinyar tayi alamar eh kafin Hindatu ta taimaka ma yarinyar takwanta kan wani tsumma datagani ah shimfide sannan tace Allah yakara sauki dukwanda yaxo yaganki kwance kice Gimbiya Asma’u ne tace kizo ki kwanta bakida lafiya kinji?…..

Cewa tayi to kafin tasake yima Asma’u din godiya kafin suka fice kasa boye mamakinta tayi tadubi su Jamila sannan tace”wai nikam baswa kwana kan katifa ne ko ince Ina katifun suke?”………
Hmmmm Gimbiya basudashi don tunwanda aka bayar wajen shekaru ashirin dasuka wuce ba asake bada katifa ba kuma dama can katifun bawani karfine dasuba ahaka harsuka lallace toma wai Gimbiya inama sukesamu suyi wani baccin kirki koyaushe bayin nan cikin aiki suke kaman jakai haka babu ilimin addini don bazan hada da boko ba tunda wannan bezame musu doleba anbude islamiya sabida su amma tunda jimawa suka daina zuwa sabida basuma da wannan lokacin sunriga sun sadaukar da rayuwarsu akan bauta ne kawai mudakike gani muke taredaku mune kadai kesamun sauki..
Hindatu tadan numfasa tana inama zanga ranar da Yan uwana bayi zasu samu yancin kansu,inama zanga ranar da za ace suma zasuyi rayuwa kaman Yan uwansu Mata har suyi sure su hayayyafa ta hanyar sunna na ma aiki ba ta hanyar zina ba….
Asma’u ne tace bangane ba Hindatu kimin bayani kina nufin bayin baswa aurene?……
Sunayi ada Gimbiya tun zamanin sarki Sulaiman dama kuma farkon da sarki Abdulrahman yahau mulki amma daga bayannan ba ayi gaskiya sabida Magajiya takan nuna rashin goyon bayanta kuma takan muzguna ma dukwanda sukazo mata da maganar sunason junansu Kuma daman ta hannunta akebi itane yakamata tana kaiwa sarki labari dadai sauransu shiyasa ma yanzu lalata yafara yawa don kuwa mata bayi sukanyi hulda da dogaraye ah boye batareda ansaniba………

Cikeda damuwa Asma’u takefa furta innalillahi wainna ilaihir rajiun don abun sunyi yawa,so many things are not in control ahaka harsuka iso bangarensu batareda ta iya cewa komai ba because she’s really out of words batamasan mezata yiba tasan dai Ummi tace taje ta ga ya suke rayuwa and tabbas taje tagani kuma taji tausayinsu hakanan taga kuma suna bukatan taimako sede how will she help them?….
Ta’ina ma zatafara taimakonsu,ita awa,nawama take she’s just too young to think of anything that can help to meyesa Ummi zatace taje taga rayuwarsu tabbas there must be a reason behind it amma koma miyene zataje tasamu Ummin su tattauna bayan sallar isha don ko yanzu dasuka dawo anata kiraye kirayen sallar maghrib don haka tawuce dakinta direct son yin sallah…………

STORY CONTINUES BELOW


**★**
Bayan taidar da sallar Isha tashiga tayi wanka kafin tasauya kayanta zuwa kayan bacci hijab dinta tasaka se wani asirtaccen kamshi takeyi ita kadai kafin tawuce dakin Ummi dukda kuwa batada walwala don abubuwan data gani yaudin sungama tada mata hankali tareda sata tunani kala kala samun Ummi tayi zaune tana kan gado tana dama fura hankali kwance yayinda kyakyawar fuskarta ke daukeda annuri wanda yasa Asma’un ma smilling Allah yagani matar kyau takeyi mata bana Wasa ba gawani haiba da kwarjini datake dashi wanda tanada tabbacin hakan yasamu asali ne daga addininta dakuma hali nagari irin nata karasawa tayi cikin dakin tana”Ummi Ina wuni”…..
Aaa Habibty kene nadaukama kin kwantafa har inacewa wa zaikaima maigidan naki furar tasa Ummi tayi maganar still fuskar ta dauke da murmushi,cikeda kunya Asma’u tace kawo intayaki damawa Ummi……..

Murmushi Ummi tayi sannan tace kibarshi kawae Dear inason inyi masa yaune amma I promise I’ll teach you yanda ake dama mishi fura nangaba kezakina mishi tunda yayi mata nima na huta…….
Murmushi Asma’u tayi kafin tasamu guri tazauna Ummi na dama fura at thesame time tana examining fuskar Asma’un kafin tace…
“Habibty kunje side din Bayin ne?”…..
gyada ma Ummin kai tayi kafin tace eh Ummi munje…..
Murmushi Ummi tayi kafin tace”and what’s your decision,do you still want to quit?”…..
Take idanun Asma’u suka ciko da kwalla don hakanan abubuwan data gani yaudin sukeyi mata gezau ah idanuwanta………
Cikin muryar tausayi tace”Ummi dukyanda kikace inyi znyi don nikam narasa wani mataki zan daukaba but I definitely want help them,sede tayaya Ummi,who am I to do that?”……
Ummi ajiye bowl din fura da Nono tayi gefe sannan tadubi Asma’u dakyau cikin sigar lallashi tace zo Habibty……
Jiki ah sanyaye takarasa gefen Ummin tazauna riko hannunta Ummi tayi sannan tace”Baki yarda da kanki bane Daughter?”….
Jijjiga kai tayi alamar Itama batasaniba murmushi Ummi tayi kafin tace”you’re the perfect person for this position tunda kika ga har Mai Martaba yazabe ki and believe me it’s going to be tough ride but when you trust the almighty and in zuciyar ki daya Allah zaitaimakeki insha Allah kinji,this people really need help Asma’u and babu wanda yasamu opportunity din taimakon nasu inba keba so,use it please Ummi takarashe maganar ahankali …
Cikin sauri Asma’u tace
“Ummi kidaina rokona please I’ll do it but still I need your guidance and advice”…….
Murmushi Ummi tayi sannan tadan kama chin din Asma’u tace”you’ve the best advicer with you, your Husband “……
Dan shiru Asma’u tayi yayinda Ummi tagyada mata kai don bata courage kafin takara”he’ll always guide you indai kina kaimasa matsalolin ki and he’s a good advicer bawai don ‘Dana bane Dear that’s just the fact inbaki shiga jikin mijinki ba you’ll never know who he’s try and be free with him only then you’ll know his problems,try and bring him close to you only then ze shaku dake Asma’u kidaina nisanta kanki daga Imam shi namiji inkasan halinshi kaida kanshi zaka maida shi tafin hannunka kirage kunya please Dear i want to see some change ah relationship dinku kinji Ummi tayi mata maganar tana murmushi Asma’u kuwa jitake kaman ta nutse kasa tsabar kunya sewani sunne kai takeyi………
Dariya Ummi tayi kafin tace”oh ni yazanyi da kunyar nan ne, I’m your Mother for goodness sake Asma’u kidauka Almustapha ba Dana bane you’re my Daughter may be inkinyi tunanin haka zaki rage kunyar”……
Itadai Asma’u se blushing takeyi tarasa nayi ba abun tatashi tagudu ba ace tayi rashin kunya sakin chin dinta Ummi tayi sannan tadauko furar data gama damawa sannan tamika mata sannan tace gashi kikaimishi ……
Karban Bowl din tayi wanda yake rufe yanzu da ludayi akai tafice cikeda kunyar Ummi tana mamakin wace irin surukace wannan din……….

Straight dakinshi tayi abakin kofa ta tsaya tareda knocking yana zaune kan sofa yayinda system ke gabanshi yanata lissafe lissafe shikadai gabadaya kanshi ah daure yake gameda al amarin boreholes dinnan Galadima yafada mishi total amount daban and the geologist too……
Wutan dakin akashe yake se dim light dake kunne sedan hasken screen din laptop din dake haske kyakyawar fuskarshi gabadaya yayi wani fresh don kwanannan wani irin kyau yake karawa tareda wata irin haiba tsabar hutu dayake samu ga comfortable gurin zama kaci mai kyau sannan ka kwanta ah maikyau shima wani abune bakaman da ba……..
Jiyayi ansake knocking kofar akaro na hudu kenan shidai Allah yagani bayason damuwa ayanzu sede me buga kofar taki hakura hakan yasa cikin cool voice dinshi yace”Come in”……

STORY CONTINUES BELOW


Shigowa tayi dakin ahankali hannunta rikeda bowl ko kallonta baiyi ba amma tunda tasako kanta cikin dakin yagane itane da kamshin turarenta karasowa tayi cikin dakin tana mamakin shi bayajin sanyine don ga sanyin Ac yakaure koina gakuma natural one daya kaure gari sabida lokacin hunturu ne……..
Samun kanta tayi da zama gefenshi kan sofa din bayan ta ajiye bowl din furar sannan tace “Ina wuni Yaya Imam”…….
Seda yadago yakalli fuskarta tsabar jin sunan data kirashi dashi yaudin kafin yadauke kanshi kuma yamaida kan laptop kaman harda bazai ansaba sekuma yace…
“lafiya Lau”……..
Murmushi tayi sannan tace ga furarka nan Ummi tace inkawo maka…….
Kaitsaye yace “thank you”,sunfi minti goma babu wanda yasake magana gashi talura kaman yana cikin damuwa don ya tsura ma screen din laptop Ido ne batare da yanayin wani abu baneba sa hannu tayi ahankali tadauke laptop din agabanshi but still gurin yake kallo dan murmushi tasaki tunowa datayi da ranar data fara ganin ah kasuwa gaban shagon Mallam Hudu he was doing thesame thing tashi tayi daga gefenshi tadawo gabanshi tareda sa hannu tana girgizawa ah gabanshi kaman yanda tayi ah da amma still be kulata seta saki dariya wanda hakan yasashi dawowa daga trance dinshi yadubeta ahankali yana”miye abun dariyan?”……
Dan turo baki tayi sannan tace…
“friends bwasama abokanan su dariya ne insunyi abun dariya?”…….
Kin kulata yayi yayinda tadauki furarshi dake bowl din tana”in fushi kayi sena shanye furar kawae may be only then zaka kulani tunda Ummi tadama”…..
Ganin still bekulataba yasata bude bowl din fura da nonon tareda diba ah ludayin takai baki tana lumshe idanu seda tayi sha uku sannan tace”hmmmmmm Kai gaskiya Ummi har ta’iya damu haka bansani ba, I’ve missed alot and wanima zaiyi missing yau”……
Wannan Karan dukda bayason murmusawan seda yayi aranshi yana she’s so childish tayi tunanin ze damu don ta shanye furar ne komai abubuwa nawa yarasa aduniyar nan dayake matukar so kuma har yau baisamesuba ……
Haka tacigaba dasha ganin baida niyan kulata yasata ajiye sauran furar don akwai dayawa har yanzu sannan tabata fuska yayinda idanunta suka ciko da kwalla “towaima tukunnan ma Ummi tasan halin Yaya Almustapha amma take cemata she can handle him after all tunyaushe take trying amma takasa batasan sanda hawayen suka fara zuba ba hakanan tafara kuka kamar wanda akayima wani abu cikeda damuwa ya jijjiga kai aranshi yana”she’s too much”,don bakaramin damunshi kukan nata yayiba ahankali yadubeta kafin yace..
“to kukan na menene bayan nabar miki furar kishanye duka?”…………
Yanda yayi maganar seda yasa tsikar jikinta yatashi amma hakan behanata dagowa tadube shiba sannan ta turo baki gaba”ninace maka Furar ka nikeson shanyewa”……
Murmushi yasaki sannan yace…
“mekikeso to?”…..
So nake kasha furar tunda sanyin ta ne yafi dadi and after that you should tell me your problem naga kaman kana da damuwa…….
Wannan Karan sake kasa yayi da muryar shi don yarinyar na matukar bashi mamaki”sometimes she behaved like a child and intayi wani maganar kuma sekace ko Yar shekaru samada arba’in ne”….
“Bazansha yanzu ba and cemiki nayi inada problem ne?”……
Tashi tayi daga zaunen da take ah gabanshi sannan tadawo gefenshi inda take dazun tazauna tana”Yaya Imam what are Friends for?”….
Dubanta yayi sannan yace”I’m Almustapha not Iman?”…..
Turo baki tayi tana”to I’ll call you Mr Taciturn”…..
Wani harara yayi mata wanda yasata cewa”to sorry Yaya Almustapha nikeson cewa” kafin tace friends are to support each other right kodai bakayi accepting dina as your friend baneba?,takarashe maganar tana dan langabar dakanta kan kafadunta…….
Kai tsaye yace”i do”….
Cikeda Jin dadi tace”Then,you can share your problems with me ko?”…….
“Why should I do that Kuma?”….
Dan bubbuga kafa tayi cikin sigar shagwaba tace”because we’re friends mana”…..
Kallonta yayi with so much adoration kafin ya’iya cewa “banyi niyaba to”,tunkan yarufe bakinshi tayi saurin daura soft hand dinta kan lips dinshi tana dan girgiza mishi kai itakanta bakaramin kokari tasan tayiba don yanzu Almustapha nayimata kwarjini bakaman farkon ganinta dashi ba sede she need to be her old seld on order for him to open up kaman yanda yace ko ita mayya ce ada to tabbas tayarda tanaso tazama mayyar itama donta lura zamansu bawani progress and everything need to be done in time sabida kowa yasan matsayinshi tsura mata idanu yayi wanda idanunshi kedauke da mamakinta dakuma wani irin feeling da shikanshi besan na menene ba itace tayi karfin halin cire hannunta kan lips dinnashi sannan tace”I’ll like to know your problem as a friend inkuma bakason hakan shikenan”,takarashe maganar tareda tashi don barmishi dakin cikin sauri yariko hannunta juyowa tayi ahankali sauri dauke kanshi yayi daga kanta kafin yace nervously”zauna to mana”, because this’s the very dazai fara fadama wani matsalan shi bayan mahaifiyarsa……
Yafi minti uku shiru yakasa magana murmushi tayi kafin tasa hannunta takamo nashi tasaka cikin nata tace”look at me Yaya Imam”………
Dubanta yayi nervously dukda Itama zuciyar ta beating yake so very fast behanata sakar mai smile ba dukdama dakin ba haske sosai kafin tace…
“feel free with me and trust me please”…….
Hakanan seyaji dukwani fear dakuma rashin yarda dayakeyimata lokaci guda yatafi ahankali yace…
“it’s the work da Abba yabani Asma’u”……
Encouragingly tace”meya faru da aikin Yaya Imam?”………
Ahankali yafara magana kaman bayaso hakan kuma besa tagaji ba ta tsaya tana saurarensa daki daki……
“Abba yabani responsibility na aikin boreholes and he told insamu Galadima muyi lissafe lissafe na kudi dadai sauransu so I met him munyi magana dashi and he told me that kudin aikin kowani borehole dakayaan aiki each is 400hundred thausand but becemin yasamu masuyi ba nikawai yafada min kudin ne dakuma site din da za ayi so,I thought nizan nemo shiyasa nayima Sulaiman magana so sehadani da wani gaye this evening muka hadu dashi he explained everything that kayan aikin kala kala ne akwai local akwae Kuma second hand gakuma sabbi akwae and from the way he’s very honest nasan sun iya aiki sosae and yacemin aikin hawa hawa ne it depends on my money dayanda nakeso but inzai bani shawara adaure ayi me kyaun sabida zejima baisamu matsala ba and suma talakawan zasu farin ciki da haka because Asma’u I went to the places if you see how they’re suffering from scarcity na ruwa sekinji tausayinsu yakarashe maganar yana kallonta kafin yakara cewa shiyasa nayi deciding ayi musu mekyau din wanda zasu Jima suna anfani dashi tunda mutumin told me that in anyi mararkyau din baya wuce one year zakiji anfara samun matsaloli and nama bincika anjima anabada projects na boreholes dinnan amma bayajimawa zakiji ana sake complaint……..

Dan shiru yayi don ji yayi kanshi nadan sarawa kadan kadan cikeda kulawa tace “inajinka Yaya imam”…
Hararanta yayi sannan yace”Almustapha not Imam”…..
Murmushi tayi sannan tace..
“to Yaya Almustapha inajinka”……..
Cigaba da magana yayi “dazun naje nasamu Galadima and I told him everything amma yace a’a aiba kudin da aka bayar ba kenan yanda yafadamin haka akabashi so senace masa muyima Mai Martaba magana musake demanding kudin for the betterment of the poor dasuke fama da rashin ruwa dakuma muma tunda ko gaba akazo bbu ruwan dole zamuso mu taimakesu so why not ayi me gabadaya yanzu?……….
Amma yace a’a i even told him zanyima Mai Martaba magana dakaina but still yahana ni I don’t know why Asma’u,he was behaving kamar marar gaskiya,so very weird yayi maganar ahankali yakai three minutes bekuma yin magana ba itakuwa kallonshi take cikeda burgewa don bataki yacigaba da magana ba he looks so very cute yanda yake fidda kowasu harrufa dakumaa yanda yake nuna concern dinshi and the most amazing thing is ah ita yake fadamata it feels so genuine and amaizing takasa dauke kanta gareshi jin shiruntan ne yayi yawa yasashi sake dubanta”kinyi shiru?”……
“I’m just so happy Yaya,anya kataba magana mai tsayi irin nayau kuwa?”…….
Tashi yayi yana”abunda ma zakice kenan?”…..
Cikin sauri tace yi hakuri barimuyi magana mana……

Zama yayi kafin tace”this’s a big issue but why not kasamu Abba din privately kayi masa bayani Yaya?”..
Cikin sauri yace”banason fada masa kada akwae matsala inzo inbata zumuncin su da Galadima,so I don’t know what to do actually”,yayi maganar make kafada ….
Still hannunta nacikin nashi tace”zumuncin dake tsakanin Abba da Galadima zaka duba kokuma dubbannin mutane dasuke fama da rashin ruwa wanda kai da idanunka kaje kagani kuma kaga wahalar dasuke sha besides wanda yayi nagari dan kansa Yaya inma dagaske akwae wani abu ah kasane shi baiji kunyar cutar wanda ya yarda dashi ba sekai you’re just trying to do what’s right….dan numfasawa tayi kuma kafin tace muma ajiye wannan agefe Inkuma we’re wrong ba haka abun yakeba Kaine kawae kake zargin Galadima may be he has a genuine reason kaga munshiga alhakinshi and zakana kallonshi da laifin sa baiyi ba so, it’s better you clear everything now and hakan zai farune inkaje kasamu Mai Martaba bayani cikin dabara daganan ne zamusan me ake ciki amma koya kagani takarashe maganar tanadan wasa da hannunshi zubama hannayen nasu idanu yayi kafin yace”thank you”because he’s out of words yama rasa mezece mata inba thank you dinba…….
You’re welcome shine abunda tafada sannan tadauki laptop dinnashi tanacewa”kasha furar kada yayi sanyi”……

Budan baki yayi zaiyi magana tayi saurin cewa…
“ba kallonka zanyi ba Allah”…
Hararanta yayi sannan yatashi yadauki furar yasaka ah fridge kafin yakoma bed yakwanta ganin dagaske baccin zaiyi harda kashe dim light din yasata cewa “Abba yabani responsibility”…

Jitayi yace”I know yafada min”….
Cikin Yar karamar muryarta tace “sede bansani ba kozan iya, I’m very scared”…………
Shiru yayi bai kulataba nasukan two minutes kafin yace”I know you can do it,so,I trust you”…….Tasha mamaki kwarai najin abunda yafada din amma hakan baihanata ta’iya cewa “Thank you” ba baima answerta ba bare tayi tsanmanin yajita ma dube dube tayitayi ah laptop sede babu komai cikinta inba wedding pictures dinsu da aka musu Itama tanadasu Sulaiman yatura mata amma bata taba tsanmanin Almustapha will keep it with him ba abunda bata sani ba shine shima wanda yatura mata din shiya tura mashi zaban daya daga cikin wanda sukayin tayi kafin tasaka as wallpaper dinshi ganin babu wasu abubuwa kai yasata kashe laptop din tareda ajiyewa gefe takunna hasken wayarta ahankali takarasa bakin gado tadan haska fuskarshi dagaske kuwa yayi baccin don hartana iyajin saukan numfashi yawani dukun kune guri guda kaman maraya da alama sanyi yakeji aranta take fadi”yanajin sanyi amma bazai rabu da kunna AC ba on top of that ko rufuwa baiyi ba”,daga katon blanket din tayi tareda lulluba jikinshi sannan ta kashe Ac din tafice Itama dakinta tawuce takwanta cikeda Jin wani irin nishadi haka kawai setana tuna conversation dinsu na dazun jitake kaman takoma tatasheshi sucigaba da surutun da sukeyi din ahaka har bacci barawo yayi awun gaba da’ita batareda ma ta ankara ba……

Koda tatashi tsakiyan dare as usual takirashi da mamakinta yau be kashe wayar ba harma reply yayi mata daya tashi bakaramin dadin hakan tajiba aranta……..
★***

Washegari around 9:30am takai mishi breakfast dinshi don already tashigo ta gyara mai dakin daya shiga wanka
ajiyewa tayi tareda gaisheshi amsawa yayi cikin cool voice dinshi yahade cikin sky blue shadda abinci wanda bakaramin karbanshi tayiba sewani glowing yake shikadai zata zubamai abincin yace…
“karki zuba fura zansha”……
Batareda taki daina kokarin zubawan ba tace….
“to ai fura ba abinci bane Yaya Imam you can still take it after eating your breakfast”………
“Kisamin kadanto shine abunda taji yafada din”,aikuwa kadan din tazuba mishi don kada tayi laifi tashi tayi tadauko mai furar ah fridge ta ajiye kafin tafice don bashi guri yaci abinci comfortably……..
Itama wankan taje tayi tasaka sabuwar hadaddiyar lace ganin yau juma’a haji babbar rana ce sannan tazauna bakin gadonta tana tunanin maganarsu da Talatu she really need someone to help her out wurin ciro layoyin nan sede wazata nema taimakonshi shine tambayar datayima kanta…….
Cnkuma se Sulaiman yafado mata arai “Yes he’s the perfect choice sede fa batamanta aikin akan mahaifiyar baneba toma ta’ina ne zata fara neman irin wannan alfarmar daga gurinshi sekuma datayi laakari da waye Sulaiman din setayi deciding zasuyi magana daga baya daga karshe tashi tayi taje tadebo abinci tazo tana ci she’s hope that Talatu tatafi lafiya batareda wani matsala ba hakanan kuma tanajin kewar Yan gidansu dukdama sukan kirata akai akai barinma yayunta maza da su Munnira haka Ummi ma baswa sati basuyi wayaba Abba nedai kawai tana iyacewa baifi sau uku suka gaisa ba tunda aka kawota gidan ………..
Seda tagama cin abincin sannan tadauki wayarta tashiga kiran kawarta Zahra aikuwa baajima ba tace…
“Nayi fushi Zahra sekace wanda kuka kawoni gidan horo ko waiwaye babu?”……
Cikeda damuwa Zahra tace”I’m really sorry My Best wallahi bazaki gane ba I’m so busy with school shiyasa amma kullum kina raina bakiga ko chat banayi yanzu ba?”……
Nagani amma dai no matter how busy you’re you should always try as possible as you can to remember you loved ones you don’t know how much it means …….
Dan murmushi Zahra tayi kafin tace”I’m at fault to kiyi hakuri”….
Turo baki Asma’u tayi kaman wanda tana gabanta ne kafin tace “nibazan hakura ba harsai kinzo min ziyara”,bata jira jin me Zahran tace ba ta katse call din tana yar dariya mugunta haka takira number Aisha don su gaisa dukda itakam suna chat sosai tama koma kaduna amma batayi picking call dinba don haka setayi tunanin ko bata kusa da wayar ne don haka seta fice da plate din dataci abincin takai kitchen dedenan Salma tazota tareda cewa”Gimbiya Mai Martaba ya aiko ah kiraki”…….
“To shine”abunda tace din kafin takoma daki tadauko hadaddiyar gyalenta da flat shoe,ah parlour tasamu Almustapha din ya dan lumshe idanunshi ahankali tace”zanje fada Yaya Imam”…….
Bude lumsassun idanunshi yayi tareda daurasu akanta yanamata kallon “bana hanaki kiran sunan nan ba”,amma setayi dariya kawai tayi gaba abunta jitayi yace”wait for me”,babu musu ta tsaya har ya’iso inda take din kafin suka jera suna tafiya harzuwa fadan sede haryanzu Mai Martaban befito ba dukda sun lura dimbin bayi tuntaru ah wajen……..
Wucewa sukayi cikin fadan Mai Martaban, Magajiya, Hajiya Muniba,Mom da Dad se Sulaiman ne ke gurin sekuma Zaliha dakecan gefe kamar wata mutumiyar arziki……..
Tundaga bakin kofa Magajiya tazuba musu idanu bakaramin jitayi gabanta yafadi ba ganinsu su biyu they just make a perfect couple, looking good together dukwanda yagansu seyaji sun burgeshi ammafa banda su Magajiya yan bakinciki…….
Harara tadinga binsu dashi harsuka karaso cikin parlourn suka tsugunawa tareda gaisheda iyayen nasu amsawa sukayi cikeda jin dadi kafin Sulaiman yashiga yimasu hoto yana mischievous smile”Allah kunyimin kyau yaudinnan I can’t stop myself from snapping you two”…….
Itadai Asma’u kanta na kasa haka se Almustapha ne dake kallon kanin nashi yana Smilling”Sulaiman is just so different and special to him”……..

STORY CONTINUES BELOW


Ganin yaki barin daukan hotunan ne Magajiya da takaici yaishe tace”Nan ba studio din daukar hoto bane indagaske sunyi maka kyau sekadaukesu kakaisu we’re here to do something important kazo kana mana shirme”, murmushi Sulaiman yayi tareda maida wayarshi ah aljihu Yana”perfect idea Mama kinga atleast za a ajiye for tarihi bari agama zaman nan then I’ll take them”……..
Wani harara tabishi dashi wanda yasashi yin shiru lokaci guda shidai Mai Martaba murmushi yayi kafin yace”Magajiya ke kika taramu kinada magana kikace?”……….
Gyada Kai tayi ahankali dukda haryanzu zuciyarta nayi mata wani irin kuna dubansu tayi gabadaya kafin dakyar ta’iya composing kanta tace”Daman maganar danayimaka ne nakan nagaji da aikin household sabida rashin lafiyata nazo incemaka nafasa zancigaba kawai don na lura sudin sunyi kankanta ma wannan responsibility din kuma maga kamar ranka baiso abunda nayi din ba”,takakarashe maganar cikeda tsoron kada Mai Martaba yayi turning nata down……
Kowa shiri yana kallonta da mamaki yayinda suke jiran jin reply daga Mai Martaba din ahankali yadubeta cikin snyin mury yace”sun nuna miki basu so ne?,don nikam banida matsala da shawarar dakika kawo infact it was a very good idea Magajiya”…….
Cikeda damuwa tace”Suma sun nuna baswa so ne kaman”…….
Murmushi yayi sannan yace if baswaso dinkam bazan takurasu daga haka dubi Asma’u yace”Daughter bazaki iya aikin danasaki bane,feel free and tell me what’s on your mind kinji”…….
Dan sunkuyar dakanta kasa tayi kafin jin idon kowa nakanta harda na Almustapha kuwa……..
Wasa da fingers dinta tashigayi kafin tace”Zan iya Abba”……
“Are sure?”…..
Kai tsaye tace”I’m very sure Abba,duk abunda kasani yi nasan kayarda dani ne shiyasa and I know you’ll always guide me when I’m wrong”……..
Murmushin jin dadi yayi sannan yadubi Zaliha dakejin kamar zuciyar ta tashe yace”Daughter kefa,do you have any problem?”…..
Cikin sauri ta girgiza kai don Allah yagani bazata iya bari tayi loosing gabadaya ba gashi Magajiya ta kwafsa musu she’s just blaming her for everything…
Mai Martaba ne yace to alhamdulillahi kinji dukansu basuda matsala zasuyi dukyanda akace and I’ve full faith in them kaman yanda kikace they should practice to hakan za ayi,duban surukan nashi yayi akaro na biyu kafin yace”Allah yayi muku albarka yanzu muje inyi introducing dinku to them dakaina”…….
Haka suka tashi bakidayansu suka fice Magajiya jitake kaman tasa hannu aka ta fasa ihu haka tanaji tana gani aka danka musu wannan responsibility din gashi bayin se murna sukeyi abunsu atleast they’ll have some change………..

Ahaka taro ya watse Almustapha yabi bayan mahaifin nashi don fada mishi halin da ake ciki……….

Mai Martaba na sane da Almustaphan na biye dashi amma baice komai ba harsuka isa karamar parlourn shi zama yayi tareda duban dan nashi kafin yace…
“Son any problem?”……
Zama yayi kafin yace Abba daman akwae maganar danakeson muyi ne…….
Mai Martaba maida attention dinshi yayi kan Dan nashi sosai kafin yace….
“to Son inajinka”….. 
Cikeda ladabi yashiga masa bayanin yanda sukayi da Galadima kafin yace Abba ninasan may be has a genuine reason shiyasa bebarni nayi maka magana ba amma ninaga I’ve to ask you if possible ayi mekyau din sabida tahakan ne zasu samu availability of water all the time batareda ansamu matsala ba hakanan muma wani karin saukine agaremu shiyasa nace ba inzo inrokeka if possible akara amount din kudin……..

Tunda yake magana Mai Martaba kebinshi da kallo don bakaramin mamakin zancen Almustapha din yayiba shidai yasan duksanda za ayi aikin boreholes kudin da Galadima ke karba sunada yawa and sunyi akan amount din da Almustapha din kefada yanzu shine mekyau to all this time kenan ba ayin aiki mekyau komi?………
Wannan shine tambayar dayayima kanshi dukda kuwa shikanshi baida ansar tambayar because he truly trust Galadima like his very own flesh blood Brother so he can’t just take action without any investigation don haka seyace ma Almustapha din kan yaje zaikirashi gobe inyayi tunani dukda seda yatambayeshi “Are you sure Son?”
Gyada kai Almustapha yayi sannan yayi godiya yafice don samun Sulaiman because yadameshi sujesu gidansu Asma’u sugaida surkanan shi dukda ma yau bashine first time dazasu je ba yau na uku kenan da Sulaiman din ke kanshi suna zuwa………
Bangaren Asma’u kuwa tunda takoma bangarensu gurin Ummi tawuce tana fada mata yanda akayi ah fada murmushi Ummi tayi mata sannan tace”Congratulations Dear Allah yabaki ikon yin abunda yadace”…..
Amin Ummi shine abunda Asma’u tace kafin tace Ummi i need to go and see Jakadiya maganan abincin bayi……..
Murmushi Ummi tayi kafin tace Allah yashige miki gaba Habibty amin ta amsa da kafin tayi mata sallama tafita zuwa kitchen din masarautar anan tasamu jakadiya tanata aikin supervising masu girki tunda tashigo kuwa bayin se wani zubewa sukeyi suna mika mata gaisuwa Rukayya baiwarta data rakota ne taje tayima Jakadiya maganar isowan Gimbiya Asma’un cikeda ladabi takaraso inda Asma’un take kafin tagaida ta Asma’un ma gaisheta tayi kafin jakadiyar yace muje daga ciki muzauna mana Gimbiya………
Babu musu Asma’u tabi bayanta harsuka shiga wani daki fes fes yake harda table da kujeru da alama office din jakadiyan ne zama sukayi kafin Asma’u tace daman nazo muyi magana ne akan abincin bayi…

STORY CONTINUES BELOW


Dubanta Jakadiya tayi kafin tace”To Gimbiya Kinga ni banyi miki murna bama haryanzu, Allah ubangiji yataya riko”cewar jakadiyan…..
Murmushi Asma’u tayi kafin tace”nagode Jakadiya daman inason inji quantity na abincin da ake basu kullum safe rana da dare kuma sannan ke aganinki iya yaya za akara yanda zaizama sunaci su koshi daidai misali?”….
Dan numfasawa jakadiya tayi kafin tafara lissafo mata yanayin amount na kayan abinci da suke diba kullum suyi anfani dashi kafin tace inaganin in aka ninka kayan abinci to kowa zaici ya koshi batareda anyi almobaranci ba………..

Dan jinjina kai Asma’u tayi kafin tace nagode indai akwae ishasshen kayan abinci da za’a iya yimasu anfani dashi na daren yau?….
Gyada Kai jakadiya tafi kafin takarada”akan sayi kayan abinci na wata guda ne wanda zai isa sabida haka zai isa aninka nayau harma na kwanakin gaba”…….
Alhamdulillah cewar Asma’u kafin tace to ayi masu abincin yau ishasshe please Jakadiyar kafin insamu inyi magana da Mai Martaba godiya sosai Jakadiya tayi mata kafin Asma’u tayi mata sallama tafice zuwa bangarensu dukda taso zuwa gun Mai Martaba suyi magana sede balallai tasameshi ah bangarensa ba don yawanci ah irin wannan lokacin ah fada yake zama sede zuwa yanma taje gurinsa…..

Bangaren Zaliha kuwa da Magajiya tunda sukabar fada kowannensu ranshi bace yake ga abunda yafarun yayinda Zaliha ke blaming Magajiya for everything daya faru shiyasama suna zuwa bangaren Magajiya tasaki kuka tana Mama dabakiyi hakan ba gashi kingadai babu abunda yacanza…

Cikeda takaici Magajiya tace” au laifina kike gani Kuma bakene kikace yarinyar tace bataso ba,I should be the one to blame you for everything badai ke kiyi blaming dinaba”,takarashe maganar tana nuna Zaliha da yatsa itadai Zaliha tsabar takaici ma kasa cewa komai tayi sema ficewa datayi takoma bangarenta because she’s not in the mood in Magajiya tayi wasa tana iya fada mata maganganu ma……….
Laure dake gyara wordrobe din Magajiya tanajin yanda sukayi da Zaliha amma batace komaiba har Zalihan tafice Magajiyan masifa takeyi taredayin mita wanda daga karshema aka huce kan Lauren don hanata tafiya tayi wae saitayi mata massage sannan ta tsefe mata kitson kanta haka tashigayin abunda tasata din badon ranta yaso ba itakam tafara gajiya da ayyukan Magajiya dinnan gashi dai bawani evidence take samuba yanzu because it seems like idea sunfara karema Magajiya dinnan sabida bataga tana yunkurin yin wani abuba ayanzu kam shiyasa tayi deciding intasamu fitama kawai zataje tacema Hajiya Muniba itakam tagaji da aikin nan tanason takoma gunta……
Dayanma Asma’u taje gurin Mai Martaba Allah yataimaketa yana parlourn shi gaidashi tayi sannan yace
“Zauna mana Daughter”…..
Murmushi tayi kafin tazauna can nesa dashi tana wasa da hannunta cikeda kulawa yace…
“any problem Daughter?”
Sunkuyar da kanta kasa tayi kafin tace”Daman Abba tunjiya daka bani wannan nauyin na zagaya cikin bayi don gano matsalolinsu dakuma wanda ake bukatan agyara and alhamdulillah nagano abubuwa da dama dayake faruwa cikeda lumana tashiga yimasa bayanin komai daga wanda tagani da idanunta harzuwa wanda su Hindatu suka fada mata sede bata fadi wanda baishafi aikinta ba dakuma wayanda take ganin ita yakamata tadauki mataki bashiba shima bata fadaba jinjina kai Martaba yayi cikeda gamsuwa sannan tace”Abba inbabu damuwa inason akara quantity na abincin da ake basu sabida only insun ci abinci mekyau dakuma wanda zai rikesu ne shine zaisa susamu strength din yin aiki,sannan rashin abun kwanciya ma wani abune barinma lokacin sanyin nan yana iya kawo musu cuta batareda an ankareba sekuma batun sutura amma shima suna fama da rashin sutura mai kyau wani ma sekaga kayan shi duk ya babbarke amma ahaka suke shiga mutane dasu batareda sun damuba tunda basuda halin dinka wanin ne”………
Seda takai aya kafin Abba yace kin tabbatar da abubuwan dakikayi discovering kenan Daughter?….
Eh Abba tabashi answer cikeda confidence mamakine sosai yakeyi donshidai from his side yana iya bakin kokarin shi wurin ganin ya biya ma bayin nan bukatunsu hakanan yana bada ishsshen kudi yanda yakamata to amma miyasa hakan tafaru,kenan duk wannan tsawom shekarun abunda ke faruwa da masarautar tasa kenan batareda yasani ba and who’s responsible for this?ko yanzun ma so ake acemishi Galadima is at fault tunda shine ke rike da responsible na kudi ah masarautar nan because duk wata harka ta kudi ake bama takuma hannunshi kudin ke shiga yake kuma fita…..
He really can’t believe this sede ance there is no smoke without fire shiyasa yakira daya daga cikin dogarayen shi atake cikeda ladabi saurayin yashigo dubanshi Mai Martaba yayi kafin yace kaje kakiramin Jakadiya………
Cikeda ladabi yace to….
Ko minti goma ba ayiba sega Jakadiya da dogarin sundawo zubewa tayi kasa tana gaida Mai Martaba din kafin yace kimin bayanin ya quantity din abinci dakuke bama bayi yake babu bata lokaci Jakadiya tashiga yimasa bayani kaman yanda Asma’u tafada masa……
Jiki ah sanyaye yace tun yaushe hakan yake faruwa acikin Masarautar nan?….
Kan Jakadiya ah kasa tace”ranka shidade yanzu yakai kimanin shekaru goma sha uku ko fiye da hakan ma……
Mai Martaba dayaji ranshi nayi mashi wani irin kuna yace”waye yace kiyi hakan kodai tsarinki ne ki bar mutanena sa yunwa”….
Cikin sauri da rudani Jakadiya tace”wallahi bahaka bane Rankashidade nibazan taba yanke hukunci akan abunda ba asakaniba Magajiya ce tabada wannan tsarin tunda jimawa nikuma amatsayina na wanda take kasa da’ita yasa nabi hukuncinta tunda itace babba awurin sannan kabar komai ah hannunta……..
Tunda jakadiya ke magana yake kallonta he can clearly see that she’s telling the truth gabadaya kanshi ah daure yace kitashi kitafi shikenan….
Tashi tayi jikinta na bari tabar fadan don bakaramin kidumuwa tayiba tadauka ita za adaurama laifin ma bakidaya.Mai Martaba dake zaune yasake duban Asma’u sannan yace tashi kije insha Allah zandauki mataki Daughter and thank you for calling my attention……..
Jiki ah sanyaye tatashi tafice zuwa bangarensu Mai Martaba kuwa yanzu target dinshi mutane biyu ne Magajiya and Galadima ne tunda dukwani list na abinci daza asaya magajiya ce zata rubuta ta aika ma Galadima shikuma zesa asayo ah kawo gida gakuma maganar Almustapha na building dinnan gabadaya yadaure masa kai don haka yakuma sakawa akira masa Galadima dakuma Magajiya at thesame time ba ajimaba segasu sunzo dukdama ba atare suka shigo parlourn nashi ba…..

STORY CONTINUES BELOW


Duban Galadiman yayi kafin yace…
“yakukayi da Yarima batun boreholes?”….
Dariya Galadima yayi kaman wani mutumin kirki kafin yace..
“aimun gama magana dashi yallabai”……..
Cikin dakewa Mai Martaba yace “I know still kafada min yanda kukayi nace”,atake Galadima yashiga fadamishi karya da gaskiya kafin daga karshe yace harmun samo mesuyin aikin ma nace mishi cikin sati zasuje su fara……

Bakaramin mamakin karyar da Galadiman ke shararawa Mai Martaba yayiba don haka seya daga wayarsa yakira Yarima Almustapha yana”kana inane Son?”……
Cikeda ladabi Almustapha yace yanzu shigowa na Abba,anutse Mai Martaba yace kazo kasameni ah parlour na yanzunnan……..
To kawai Almustapha din yace yayinda Mai Martaba yakatse call din Almustapha kuwa yanzu shigowansu daga gidansu Asma’u harda Munira da Ikram suka taho wai sunzo zasuyima Asma’u weekend……

Duban Sulaiman din yayi kafin yace”Abba nakirana kukarasa cikin gida dasu”….
Gyada masa kai Sulaiman yayi yayinda Almustapha yayi bangaren Mai Martaba din gaishesu yayi kafin yasamu guri yazauna dubanshi Mai Martaba yayi ahankali kafin yace ka maimaita min yanda kukayi da Galadima batun aikin boreholes……
Cikin nutsuwa Almustapha yashiga bayanin yanda sukayi har karshe duban su duka biyu Mai Martaba yayi sannan yace”I don’t know who to believe between you two dukanku Kuna bani different story I don’t know why?”……..
Galadima dayayi tsuru tsuru kasa cewa komaima yayi because betaba tunanin Almustapha zezo yasamu Mai Martaba ba……..
Mai Martaba ne yafito dashi daga trance dinshi tahanyar cewa…
“Galadima kace kungama magana da Son shikuma yace baku gama ba?”…….
Cikin in inaaa Galadima yace”to ni madai bansan meyesa yace hakaba?”…..
Almustapha dai mamakin mutumin yakeyi haka Mai Martaba ma daga ganin fuskar Galadima zaka gane karya yakeyi don gabadaya reactions dinsa yanuna………
Dan ajiyar zuciya Mai Martaba yayi kafin yace i gave you enough Money for this work miyasa zaka yimin haka Galadima?……
I trust you for years now Ashe you’ve been betraying me and all the time cewa kakeyi aiki mekyau akeyi ba marar kyau dinba but I never intend to investigate sabida nayarda dakai you’re one of my close friends atunanina you’ll never do something like that but you prove me wrong today because daga reaction dinka nariga nasan komai Galadima…

Galadima da gabadaya yagama rikicewa yace”yanzu yarda da Danka da kasameshi ah sama saman nan kayi fiye da ni damukayi shekaru dadama tare?”…….
Murmushin takaici Mai Martaba yayi kafin yadubi Almustapha yace jeka kiramin Jakadiya kace tataho da record book nata yanzun nan …
To shine abunda Almustapha yafadi kafin yafice zuwa yin abunda akasakashi aikuwa tunda sukaji haka daga Magajiya har Galadima suka rude donsunsan yau asirinsu yakusa tonuwa amma mi se Magajiya tadaure ahaka har Almustapha da Jakadiya suka dawo mikama Mai Martaba katoton littatafai guda biyu tayi wanda ke daukeda duk wasu lissafe lissafe na kayan abinci daya ke shigowa hannunta na shekaru da dama yanzun………
Dubawa Mai Martaba yashigayi yanda Asma’u da’ita sukayi mishi bayani dazu haka abun yake arubuce mikama Galadiman yayi sannan yace”kagani da idanunka dukda nasan kana sane da abunda kukayi kaida Magajiya don bazance babu hadin bakinta ba”…..
Cikin sauri Magajiya tace nifa bansankomai ba wallahi ni kawo kayan abinci yakesawa ayi kawai nikuma nawa in sa ah ajiye ah store….
Murmushin takaici Mai Martaba yayi kafin yace”you can’t lie to me Magajiya,miyasa baki taba zuwa kinsameni kinfada min ba inbabu saka hannunki aciki?”……
Cikin rashin gaskiya tace”nadauka iya kacin abunda zaka iya bayarwa kenan”……
Galadima dayaga Magajiya nashirin barinshi aciki yasashi saurin cewa…
“Karya kikeyi wallahi mutumiyar banza,sokike kibar ni aciki wato ko,to indai haka zakiyimin gwanda intona mana asiri baki dayan mu because yanda kikeson kanki haka Nima nake son kaina batareda Galadima yayi wata wata ba yace duk kudin da kake bayarwa Mai Martaba nida ita muke rabawa kama daga kan na abinci dama na suturun bayi dakuma katifu dama na aikin boreholes duk tsakanin mu muke raba canjin daya rage sannan Almustapha gaskiya yafada maganar damukayi dashi kenan Kuma babu algungumin daya kawo wannan shawaran inba itaba and yanzu tanason tabarni aciki dongata shedaniya to baki isaba yakarashe maganar ranshi bace sannan yakarada ninasan I’m selfish, nayi betraying dinka sabida abun duniya kudi sunrufe min iso har hakan yasa namanta irin yardar dakayi dani kakuma dankamin amana amma dukda haka inafatan zaka yafemin abunda nayi I know I’m very selfish bankyauta makaba yakarashe maganar muryar ah karye………

Magajiya dai dagewa tayi tana kuka tanacewa karya yake mata,hmmm shine abunda Mai Martaba yayi kafin yace”tun bangama Samo evidence ba kafadi gaskiyar kenan”….
Kan Galadima ah kasa yace”nariga nasan kasan gaskiya so babu anfanin boye boye asirina yariga yatonu and nothing can change that but believe me I’m always your person dukda banida idanun kallonka ayanzu sabida abubuwan dana aikata”,murya akarye Mai Martaba yace”it’s not your fault laifina ne danayarda dakai dayawa, it’s my fault dabana shiga cikin mutane na dakaina inaduba matsalolinsu sabida ahtunanina kudin kunayin abunda yakamata ashe bahaka bane,ashe my people have been suffering,ashe suna rayuwa da yunwa batareda nasani ba amma bakomai Allah zai sakamin dagani harsu tunda yaga zuciyata………
Cikeda damuwa Galadima yace kayafe min don Allah…..
Mai Martaba ne yace”bani zakanemi yafiya aguna ba kaje kanemi yafiya gurin wayanda kacutar daganan yatashi yafice batareda yasake dubansu ba dagashi har Magajiya din don zuciyarsa takasa daukar abunda yafaru din hakanan yarasa wani irin mataki zai dauka akansu……..
Galadima ma tashi yayi yafice jiki ah sanyaye Almustapha kuwa kallon Magajiya yadinga yi cikeda tsana yana mamakin yanda tadage tanata kukan munafurci kamar wata mutumiyar kirki…
Ganin bazai iya juran tsayuwa kusada itabama yasashi fita don komawa bangarensu……… +

Magajiya kuwa takaici ne yaisheta nafita da kowa yayi yabarta agurin batasan sanda tayi wani irin karaba kafin tayi ball da wani table dake tsakiyar dakin mai Martaban tana huci kamar wata mahaukaciya hararan dakin tashigayi sannan tafice cikin sauri tana huci…..
Dogarayen dake bakin kofar dakin sunajin ball datayi da table din amma hakan baisa sunyi gigin leka dakin ba donsunriga sunsan hali suna iya jama kansu abunda yafi karfinsu don koda tazo fitama yi sukayi kaman basu ganta ba tsabar tsoron Matar haka tawuce bangarenta tanata huci ita kadai tarasa meke mata dadi hakanan tarasa wani mataki zata dauka gashidai komai tabar baremata yakeyi ahankali and she’s not getting any new clue……..

★*★
Asma’u tunda tabar parlourn takejin wani irin dadi na musamman atleast tasani Abba zedau mataki tunda yace yasan yanda zaiyi batada wani damuwa daya wuce
taga bayin nan suna rayuwa maikyau tana wannan tunane tunanen ne setaga kaman Laure nayin hanyar bangaren Hajiya Muniba bayan kuma tasan Laure baiwar Magajiya ce and it seems like yarinyar nata dube dube kamar wata marar gaskiya wanda hakan yasa Asma’u tabi bayanta cikin sauri harta isa sashin tasan babukyau lekan sirrin wasu sede yazatayi?…….
She needs to know if they’re behind something kokuma kansu hade yake ah bakin kofar tasamu dogaraye gaisheta sukayi kafin tashiga ahankali sede koda tashiga parlourn samun guri tayi ta rabe don ta hango Lauren cikin parlour zaune gaban Hajiya Muniba kasa kunne tayi donjin mezasu ce……..
Laure ne ke kuka kamar ranta zaifita tana”nikam Rankishi dade don Allah kitaimaka ki dawo dani amatsayin maiyi miki aiki don wallahi yanzu Magajiya batadauke ni ah bakin komaiba batama fadamin dukwani abu dazatayi”……
Hajiya Muniba da takejin tausayin Laure tace”kiyi hakuri Laure ninasan kina hakuri da matarnan amma inason kisani bazai yuyu murabaki da itaba batareda asirinta yatonu ba don inmukayi haka kaman ma muntona ma kanmu asiri ne kafin mu cika burinmu kicigaba da hakuri komai yakusa zuwa karshe in Allah ya yarda”……….
Dakyar Laure ta’iya daina kukan don tasan gaskiya Hajiya Muniba ke fadi kafin tace”tonikam abun yakici yaki cinyewa ranki shidade kodai zakiyi anfani da Mallam Audu ne dakuma ke karan kanki kitona mata asiri kawai sabida Magajiya tacuci mutane da dama wallahi kuma tana kan cutansu don banga alama tanada niyar saukar da kanta tayi abunda yadace ba”……
Murmushin takaici Hajiya Muniba tayi kafin tace”nikaina inason hakan but I want her to confess all her crimes inason tayi mugun muzanta agaban idanun mutane banason ace wannan laifin guda biyu shine kadai laifin daza a kamata dashi batareda sauran abubuwan datayi sun bayyana ba,inason Magajiya tasha wahalar da babu wani mahaluki daya taba sha ah duniyarnan yanda Hajiya Muniba ke maganar zaka gane akwai bitterness sosai acikinta har jijiyoyin jikinta tashi yakeyi ita kadai tasan irin tsanarda takema Magajiya hakanan itakadai tasan irin dauriyar datake yi har tabarta take numfashi ah doron kasa bayan ga abubuwan da tayi mata wanda bazasu taba iya yafuwa ba.
Asma’u dake boye ta yi saurin fitowa tana”I’m with you Aunty nima banida wata buri dayawuce ta tona ma kanta asiri dakanta, Magajiya tacuceku takuma cuci mutane da dama she has to pay for all that she has done”……..
Hajiya Muniba dake mamakin ganin Asma’u kai tsaye tace…
“yaushe kika shigo?”……
Murmushi Asma’u tayi kafin tace”nadan jima danaga Laure tayonan nabiyo nan i thought kanki hade yakeda Magajiya, I’m really sorry nayi zarginki kiyafe min don Allah”lokacin Asma’u harta karaso kusa da Hajiya Muniba din saurin kamo hannunta Hajiya Muniba tayi kafin tace”laa bakomai Dear nasan aikin ki kikeyi as a Daughter of this family ina matukar alfahari dake sannan ae ah irin gidan nan no one is to be trusted”…..

Zaunawa sukayi yayinda Laure tagaishe da Asma’u din ansawa tayi tana murmushi kafin tadubi Hajiya Muniba tace”what are your plans Aunty?”……
I’ve no plans as of now Asma’u sede da ganin ki anan senaji kema zaki iya taimaka mana cewar Hajiya Muniba din……
Cikin sauri Asma’u tace tayaaya zantaimaka nikuma?…….
Kikwantar da hankalinki anbaki position dinnan I’m sure Magajiya is not happy with it and she’ll surely confront you kotace zatayi miki wani abu kekuma kada kiyarda kiji tsoronta just keep provoking her i think that way we’ll achieve our goal……….
Gyada kai Asma’u tayi dukda kuwa tana kokwanton ko idea din will work out haka sukacigaba da tattauna wa kafin tace nikam tataba yimaki wani abune Aunty kokuma kawai kina taimakon Mai Martaba ne?……..

STORY CONTINUES BELOW


Jin Asma’u tafadi haka take idanun Hajiya Muniba yayi jazir kafin tace ni abunda Magajiya tayi min bazan taba iya kwatanta pain dinshi dana wani ba because I’m still suffering from it Allah kadai yasan irin dauriyar danakeyi wallahi…….
Subhanallahi shine abunda Asma’u tafada kafin Hajiya Muniba tashiga bata labari tundaga farko har karshe innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma’u tadinga maimaitawa dole seda ta zubda ma Hajiya Muniba hawaye itakam tagaji dajin munanan ayyukan Magajiya don tunda tashigo masarautar nan bata taba jin anfadi alkhairi akantaba hakuri tashiga bama Hajiya Muniba tareda bata baki Kan Allah natareda su dukda kuwa Itama dauriyan kawai takeyi kafin daga karshe tayi masu sallama tatafi abunta zuwa bangarensu ahanya tahadu da Almustapha sede shi yana gabanta bema ganta ba cikin sauri ta iso inda yake wanda har hakan yasashi firgita kadan…………
Batasan sanda tasaki dariya ba sabida abunda yayin dukda kuwa halin datake ciki tana…
“Kai Yaya Imam daman haka kake da tsoro?”…..
Hararanta yayi kafin yace”ba tsoro bane bansan dazuwanki bane shiyasa”…….
Murmushi kawai tayi sannan tace”How was you Day?”……
Dan tabe baki yayi kaman bazaiyi maganaba sekuma yace”as usual”……
Ahaka har suka isa bangaren nasu ah parlour taga wasu kaman su Ikram da Munira ware idanunta tayi ahankali kafin tashiga sosasu don duk ah tunaninta imagination ne don kwanan nan bakaramin kewan gida takeyi ba…..
Almustapha dake gefenta ne yadubeta yana kallon expression na fuskarta Ikram ne tafara ganin Asma’un dagudu tayo gunta tana Adda Ashmau oyoyo yarinyar takarashe maganar tareda rungume Asma’un………….
Dagata sama Asma’u tayi tana juyi da’ita don ikram bawani nauyine da’ita ba tananan agurin kaman ka hure tafadi tsabar farin ciki Asma’u batasan sanda hawaye yafara zuba ba”I missed you so much Darling autar Ummi”takarashe maganar tana kara kankameta ajikinta yayinda takarasa parlourn ganin Munira batazo garetaba don tasan Munira da kunya dukyanda akayi ganin Almustapha ne yahanata zuwa ta rungumeta cikeda zolaya tace”ke wato bakiyi kewa na bako?”……..
Turo baki Munira tayi kafin ta ce “Babu wanda yakaini kewarki Adda kema kinsani”……
Murmushi Asma’u tayi tareda zama gefen Muniran tahada su duka cikin jikinta tana”Ya Ummi,ya Daddy,inasu Mommy dasu Yaya Aliyu don Allah?”…

Duk kalau suke suna gaidaki cewar Munira, murmushi Asma’u tayi kafin tace Ina amsawa shine dasuka kawoku kosu jira mugaisa takarashe maganar kaman zatayi kuka Almustapha dake gefe yayi folding hannunsa guri daya yana kallonta cikeda sha’awa betaba tunanin she’ll be this happy ba don taga kannenta…….
Munira ne tace su Yaya Almustapha ne suka kawo mu Asma’u dake share kwallar farin ciki tadubi inda yake cikeda Jin dadi shikuwa yayi saurin dauke kanshi sannan yawuce daki batareda yasake kallonta ba murmushi tayi sannann tace kungaisa da Ummi?……

Munira ne tace wace Ummin?….
Ta gidan nan mana Munira dariya Munira tayi”au daman Itama Ummi akecemata mungaisa da’ita hardasu Anty Amira ma sede sunwuce islamiya shiyasa ma wai basu zauna damuba’…..
Kamo hannunsu tayi kafin tace”kwana zamuyi dai ko?”…..
Gyada mata kai Ikram tayi cikin maganarta dabai gama nunaba tace”hutu zamu miki don anbamu hutun new year shine Yaya Mushty yace muzo mu kina kewanmu kekikace akawo mu”…….
Dariya Asma’u tayi cikeda Jin dadi kafin takama hannayensu sannan sukayi daki tana”Daddy bai hanaba!”…
Wannan karan Munira ne tace”behanaba wallahi amma cewa yayi sati daya kawai zamuyi miki mutafi”……..
Allah sarki Daddyna ashe haka yake sona takarashe maganar yayinda suka shiga dakin nata ganin kayansu tayi already har anshigo dasu acikin karamar akwati dauka tayi ta ajiye wani gefe kafin tace zakuyi wanka ne?…….
Cikin sauri Munira tace”eh daman tunsafe bansake wanka ba”…….
Shiga bandaki Asma’u tayi tahada ruwan wanka tafarayima Ikram kafin tanadota cikin towel tafito sannan tace to Munira shiga kiyi dawuri kinga ankusa kiran sallar maghrib to kawai Munira tace kafin tashige bandakin abunta…

Asma’u kuwa shafama Munira mai tayi kafin tasa mata kayan sanyi dubada yanayin garin don sanyi yashigo sosai ahaka har Munira tafito kafin akashiga kiraye kirayen sallar maghrib haka sukayi sallah abunsu Asma’u ko kitchen bataje ba se tambayar su labarin gida takeyi cikeda Jin dadin zuwan kannen nata har bayan Isha kafin ta’iya tashi tafita don zuwa kai abincin Almustapha ah parlour taga Amira….
Amira ne tace”shine kika boyemana kanne ah daki”,dariya Asma’u tayi kafin tace”na’isa sunce kunje islamiya and dakuka dawokuma nasan agajiye kuke Kuma shiyasa bankawosuba”……..
Bawani mudai kinyi mana rowa kawai sister in-law kafin Amira tayi hanyar dakin Asma’un don samunsu Munira din……..

STORY CONTINUES BELOW


Asma’u murmushi tayi tareda daukan abincin Almustapha da Sulaiman takai musu parlour ganin nanbada jimawa ba zasu shigo tare……..

ahaka takoma daki sede to her own surprise Amira tadebe yaran tayi tafiyar ta dasu murmushi kawai tayi kafin tazari towel tashige wanka abunta batajima ba tafito tayi shirinta cikin kayan bacci hadadde riga da wando har kasa gabadaya sewani kamshi nadaban takeyi itakadai…….

Fita tayi donzuwa tasamo su Amira din amma seta samu haryanzu su Almustapha na parlour dukdama sungama cin abinci yar hira sukeyi jefi jefi Sulaiman ne yafara ganinta yana murmushi yace”Our sister in-law daga ke babu wata inshallah”…….
Dariya tayi tana Yaya Sulaiman bakada dama wallahi……
Murmushi yayi shima yana”kema bakida dama ae tunda kinkasa daina lakabamin Yayan dole bayan nine yakamata ince miki Yaya”,dariya kawai tayi tana jijjiga kai kafin tasamu guri tazauna ah parlourn Almustapha kuwa rasa abunyi yayi don haka yadauki wayarshi yashiga danne danne abunshi duban Sulaiman din tayi kafin tace daman nikam akwai maganar danikeson muyi dakai…….
Murmushi yayi”To sister in-law gani ae I’m available duksanda ake nemana”….
Almustapha jin Asma’u tace zasuyi magana tsulum yatashi yawuce dakinshi don baisaniba ko privately ne takeson yin maganar….. Asma’u tayi mamaki don bataso yatafin ba because she can say it in front of him amma saita dubi Sulaiman din kafin tace”I’m sorry in abunda zanfada ze bata maka rai Yaya sede narasa gurin wa zannemi taimako inba gurinka ba, you’re the only person I can count on.”……..
Sulaiman maida attention dinshi yayi kanta baki daya kafin yace”I’m all ears Asma’u just feel free kinji?”yayi maganar cikeda bata courage din yes tayarda dashidin aikuwa cikin sanyi tashiga yimasa bayanin yanda sukayi da Talatu har karshe kafin tace I’m very sorry Yaya Sulaiman nasan dole ranka ya sosu sede i can’t help it you’re the only one that can help me out….
Sulaiman murmushin karfin hali yayi kafin yace”karki damu Asma’u I’ve experienced more than this indai akan mahaifiyatane so I’m already use to it and insha Allah zanyi kokarin gani ancire layoyin nan tunda ana renovation na gida after two two years I’ll use that opportunity aciresu tunda cikin watannan za afara gyaran na shekarar nan….
Asma’u datasan Sulaiman is just trying to be okay tace thank you jiki ah sanyaye because she can see that that he’s in pain through his eyes………..
Karki damu yacemata kafin yayi mata saida safe yafice dakyar ta’iya tashi tayi dakin Almustapha cikeda tausayin Sulaiman din harmatake danasanin fada mishi dama Almustapha tasamu sede yanzukam it’s too late……..
Bangaren Sulaiman daya fita kasa komawa bangarensa yayi sema samun kujera dayayi ah wani bangare na masarautar dake daukeda fancy chairs ga grass carpets daya kawata gun da flowers masu sassanyar kamshi yazauna tareda jinginar da kanshi kadan ya lumshe su Allah ne kadai yasan abunda yakeji yawanci nan yake zuwa duksanda yaji duniyar tayi masa zafi…………
Jiyayi wayarsa tanata ringing amma yaki dauka bakidaya don yasan wacece mai kiran and muddin taji muryarshi she’ll get to know that he’s in pain shikuma bayason abunda zai tadama Sumayya hankali ah daren Allahn nan abunda yamanta shine ayanzu Sumayya tasan komai nashi kuma bata manta inda yake zamaba when he’s feeling so lonely kawai seji yayi mutum yazauna gefenshi……
Juyowa yayi ya kalleta ahankali kafin takamo hannunshi cikin nata”Yaya Sulaiman dina shine kazo kazauna awajen nan bayan kasn ana sanyi and mura zai iya kamaka” takarashe maganar muryarta daukeda tsantsan damuwa…….
Murmushin karfin hali yayi kafin yace”I’m sorry Sumyna”…….
Cikeda damuwa tace”if you’re really sorry mushiga cikin gida semuyi magana to”……
Girgiza mata kai yayi alamar aa kafin yace”I want to stay here, with you”yakarashe maganar muryarshi nadan cracking …..
Daga cardigan din dake hannunta tayi tareda mika mashi sannan tace kasaka to I know you’ll be stubborn daman shiyasa nafito da wannan murmushi yamata kafin yakarba yasaka komawa yayi position dinshi nada Itama thesame thing tayi kafin tace….
“Kanason damuwana ne Yaya na?”
Cikin sauri yataso yana dubanta”subhanallah banaso wallahi Sumyna”ganin yanda ya rude lokaci guda yasata dagowa tadubeshi Itama fuska ba murmushi tace”then smile for me sweetheart, don’t strees yourself kadaina damun kanka akan abunda bakai kaja ba just keep praying and everything will be alright kaji?”……
Kallon hannunsu dake sarke dana juna yayi kafin yace”okay Sumyna kema kinasakani ah addu’a,it just hurt,so much”, yakarashe maganar yana dan taba kirjinshi murya ah karye cikeda tausayinshi ta kwantar da kanta ah gefen kafadanshi”I’ll pray for you but just keep smiling always i don’t like seeing you like this”…….
Ganin yanda tadamun ne yasashi dan sakin murmushi tareda cewa kimin love peom to,tell me how much you love me Sumyna hakan nasani cikin farin hakan kuma nasani Jin atleast I’ve someone with me no matter what moreover it’ll ease my pain……..
Dan dagowa tayi daga jikinshi sannan tadube shi shima itan yake kallo kamar wani karamin yaro yace…
“ki min mana”……
Make kafada tayi Itama cikeda shagwaba’bazan yiba sekayi the best smile ever”…..
Yar dariya yayi yana gashi har dariya nakeyi……
Jijjiga mai kai tayi tana”from the bottom of your heart nikeso”…….
Wani irin lallausar murmushi yasakar mata wanda yakusan melting heart dinta hakanan batasan sanda tafara jero mai kalaman so ba….

STORY CONTINUES BELOW


_You Have No Clue, How Much I Love You Yaya Sulaiman Because_
_To the rest of the world you must be just another man,_
_But to me you’re the one who makes me smile, ‘coz only you can._

_You give me friendship, you give me support, you_ _give me confidence,_
_Meeting you in life, was definitely no coincidence_

_You are the one who is made for me on earth,and I was made for you, right from birth._

_I can imagine myself with no other but you,I love you so much so much & you actually have no clue Yayana_

Takarashe maganar cikin yar siririyar muryarta tabbas yaji dadin kalamanta donba karamin farin ciki yasashi ba ayanzu kam yasan Sumayya nasonshi dukda yana ganin bazai kai wanda shi yakeyi mataba cikeda kaunarta yana kallon cikin kwayar idanunta yace”I love you more Sumyna and I’ll always be with you sannan inason kisani cewa sonda nike miki bekai wanda kikemin ba, because sonki ah jinina yake with every breath I think of you Dear…..
Frowning fuskarta tayi tareda dan turo baki still suna kallon juna”nidai sonda nake maka bekai wanda kakemin ba”…..
Yar dariya yayi tareda jan kumatun ta yana”lallai yarinyar nan bakisan how much my heart beats for you bane shiyasa,to let me tell you something you do know”……..

Gyara zama tayi tareda sa both hands dinta ah chin dinta tazuba masa oily eyes dinta tana jiran jin mezai fada ba……
Murmushi yayi shima yana kallonta kafin yafara magana cikin nutsuwa……

“Sumayya!”yakira sunanta so calmly wanda har saida tsakar jikinta yatashi sabida tsabar batasaba jin irin wannan muryar ba hakanan batasaba jin yana kiranta da wannan sunanba dakyar ta’iya cewa”Na’am” sede dukda hakan besa yadaina maganar dayafara ba itamakuma saurarenshi takeyi…….

_I love you when you smile at me,_
_I love it when you frown,_
_I love you when you say the sweetest things, that makes my heart go up and down,the you just did now_

_I love you when you make me angry Sumayya_
_I love you the way to come to say sorry._
_i love you the way you make those stupid faces that makes me laugh away to glory._

_I love you when you make me laugh,_
_And even when you make me cry,_
_i love you ‘coz I_ _know you’ll be right there with me and help me make my tears dry_

_I love it when you look at me while I’m looking away,_
_I love you so much ‘coz I will never ever love anyone this much ever again._

Murmushi yadanyi tareda sa hannunshi dede saitin zuciyar shi still yana kallon cikin idanunta”ke kadaice anan Sumayya and no one can take your place believe me everything you do makes me love you more so,kidaina comparing son da nake miki da komai please”……
Sumayya dake zaune takasa cewa komai se hawayen farin ciki she never know she’ll be this lucky dakyar ta’iya cewa”nagode Yaya Sulaiman”,don harga Allah tayarda Sulaiman is the best Man for her………
Murmushi kawai yasakar mata yana kallon kyakyawar fuskarta da akullum kyau yake karawa ah idanunshi bashida wani buri dayawuce yaga Sumayya amatsayin Matarsa na sunna,his very own sweetest wife gaskiya he can’t wait for that day(Nima zeenatu nace I can’t wait)
haka sukacigaba da hira abunsu cikeda so da kaunar juna wanda hakan haryasa Sulaiman manta halin dayake ciki ma………..

Asma’u kuwa koda tashiga dakin Almustapha yana kwance se danne dannen waya yakeyi mamaki takeyi yaushe ma yafara harka da waya har haka badai chat yakeyiba?……
Wata zuciyar ne tacemata”kekuma dawaye zaiyi chat din”,dawannan tunanin ne takarasa gefen gadon tazauna sannan tace”ina wuni Yaya Imam?’….
Ajiye wayar yayi kan bedside tareda tashi yazauna yana dubanta”sau nawa zaki gaishe ni ne yau?”
Turo baki tayi gaba…
“to ai yanzu darene shiyasa”……
Saukar da kafansa yayi daga kan gadon batareda yace da’ita komai ba ahankali tace”thank you”……
“For what”, yayimata tambayar tareda daura lumsassun idanunsa kanta wanda hakan kesata jin wani iri dakyar ta’iya cewa”for bringing my Sisters home”……
“Oh” shine abunda yace,kafin yakara da gobe zan maidasu ma tunda mantawa kike da mutane insuna nan……
Cikin sauri tace…
“nashigesu wana manta Yaya?”……
Yanda tayi maganar seda yasashi sakin murmushi kafin yace..
“kinfini sani ai”……
Hakuri tashiga bashi harda dan guntun hawayenta seda ya wainata sannan yace “naji karki baremin baki kice zakimin kuka don wulli zanyi dake waje”……..
Dukda taji haushin cewa dayayi zaiyi wulli da’ita waje sekace wata kayan wanki behanata cewa “thank you ba”,don duk ah tunaninta dagaske yakeyi zai maidasu din tashi tayi tana”Daman nazo inmaka godiya ne saida safe” juyawa tayi hartakai bakin kofa taji yace”baki tambayeni yamukayi da Abba ba”…….
Murmushi tayi tareda juyowa sannan tadan bata rai cikin sigar shagwaba kuma tace”Nima baka tambayeni ba ai”…….
Murmushi yayi kawai batareda yace mata komai ba still yana zaune bakin gadon ganin becekomai ba yasata sake hasala”tonima bazan fada maka ba tunda kaima kaki fadamin kaga tafiyata ma”……
Yar dariya yayi”Asma’u!”,yakira sunan ta cikin cool voice dinshi wanda yasata tsayawa cak hakanan seda tsikar jikinta yatashi……..
Dubanta yakumayi dukda tajuya mai baya cikin sigar zolaya dabaisan yanada itaba yace”najanye magana na na barinsuma tunda haka kikace”……
Aibatasan sanda ta’iso gabanshi ba cikin shigar lallashi tace kayi hakuri don Allah don batama gane wasa yakemata ba tsabar rikida tukunnan ma yaushe Almustapha ke yima mutum wasa dahar zata tsanmanci hakan daga gareshi……
Rike dariyarshi yayi yaci mur kamar bashiba babu shiri tashiga fada mishi yanda sukayi da Abban ma batareda ya tambaya dinva akaro na biyu……
Kallon yar karamin bakinta yakeyi harta gama masa bayani ga kananun faararen hakwaranta masu ban sha’awa da burgewa dakyar ya’iya cewa”naji to jeki”……
Sakan baki tayi aranta tana”abunda zai fada kadai kenan ma lallai mutumin nan”, cikeda shagwaba tace”to bakace komaiba”……..
Dauke kanshi yayi daga kallonta kafin yace”it’s late kije kikwanta”……..
Make kafada tayi”aa nikam sekace bazaka maidasuba to”……
Batareda ya kalletaba yace”wasa nake miki daman”……
Cikeda Jin dadi tace to good night Yaya Imam tana fadin haka tafice dukda taso yayi comment akan maganar datayi din amma batasan meya hanashi ba itadai tunda bazai maidasu ba ai shikenan kuma koma miyene Abba yace he’ll look into it so she’s okay now………….Dakinsu Afiya tawuce gabadayansu sunyi bacci harma dasu Munira din dake kwance tsakiyansu yar murmushi tasaki tareda kashe musu wutan daki don da alama bacci ne yadaukesu batareda sun ankara ba haka tajuya don komawa dakinta talura tunda Almustapha yayi siezing wayoyinsu da laptop baswa jimawa basu kwanta bacci ba……….. +

Karkuso kuga irin farin cikin da bayi suka shiga ah daren ranar sakamakon sauyin yanayi da akasamu ta bangaren abinci tundaga ranar farin aikin Asma’u hakanan hakan bakaramin daraja ya karamata ah idanunsu ba tareda yima Allah godiya don sukansu sunsan Asma’u will be the best leader, koda gari ya waye taje kitchen don ganin ya quantity din abincin da ake basu yake shin zekai kobazai kai ba sede koda tagani alhamdulillah don dede gwargwado dae abincin nan inmutum zaici kamanshi sau uku arana to he’ll be satisfied haka sukadinga zuwa sunayimata godiya tareda yi mata fatan alkhairi itadai babu abunda takeyi sai murmushi……….
Mai Martaba nazaune ah parlourn shi har wuraren sha daya da rabi don yau kwata kwata yakasa fita fada abun duniya yadameshi he still can’t believe what this people sukayi mashi gashi yama rasa wani irin mataki zaidauka akansu Dad dake gefenshi ne yace”you shouldn’t think that much suda suka cuce ka sune yakamata su shiga damuwa bakaiba”…..
Dago idanu Mai Martaba yayi ahankali tareda kallon dan uwannashi kafin yace…
“Nima da nawa laifin Yaya,inada nauyi me yawa akaina amma bantaba tunanin cewa they might need me ba bntaba tunanin inje dakaina inji matsalolinsu ba sannan bantaba zuwa don ganin aikin danasa ayi masu yanakyau ko baya kyau ba I trusted the people I shouldn’t have”…….
Dan dafa shoulder dinshi Dad yayi in a comforting manner yace”abunda yasa baka dubawan sabida kayarda dasu kayi tunanin they’re doing the right thing”,su kuma sun yaudareka they’re the one to be punished Abdul yanzu mutanenka na bukatar ka you need to put things in their right places……..
Gyada kai Mai Martaba yayi kafin yace Galadima will be under house arrest for three months and Magajiya for two 2 month sabida ita nata laifin baikai nashi ba dukda yana ikirarin itata saka shi amma I consider him to be a Coward ya zaayi mace tace kayi abu sannan kayi fisabilillahi so, that’s his punshment and dole yafi nata……..
Gyada kai Dad kawai yayi kafin yace..
“hakan ma yayi atleast they will learn their lessons”……
Haka kuwa akayi Mai Martaba yafita fada sannan yasa aka kira masa Galadima da Magajiya inda yafadi laiffuffukansu gaban kowa wanda sukansu sun kasa denying sannan yabasu punishment dinsu kaman yanda yafada ma Dad……….

Magajiya kaman tayi hauka takeji tsabar bakin ciki wato yanzu dai she has to go back to that place datayi tunanin bata kara komawa ah rayuwarta babu abunda yafi damunta irin yanda Mai Martaba ya dizgata gaban kowa Galadima kuwa kowa yayi mamakin abunda yayi dubada yanda suke kusanci da Mai Martaba gakuma yarda dayayi mashi wanda ko Waziri mahaifin Magajiya baisamu wannan matsayinba haka ranar masarautar ta kaure da gulmace gulmace da kuma maganganu duk na abunda yafaru yaudin hakanan bangaren Dogaraye da bayi babu mai jajantama Magajiya sema masuyi mata Allah ya kara tareda wish din Allah yasama dagacan ah aikata babban gidan yari kota girbi abubuwan data shuka wanda are not yet revealed Laure kuwa babu wanda yakaita farin ciki donkuwa kobakomai zatasamu ta yi yanda takeso na wata biyun………..
Asma’u ma farin ciki kaman tayi yaya itada Hajiya Muniba dubada yanda abun yawakana batareda sunyi tsanmani ba atleast they’ll not see her cruel face for good two months now koda Ummi taji labari murmushi kawai tayi dukda bekai har zuciba don tasan Mai Martaba must be having a very hard time right now sabida ah iya saninta babu abunda ya tsana irin betrayal babu kaman daga loved ones dinshi wanda ya yarda dasu sosai bata manta how he suffered ba sanda wannan kaddara tafada musu ah baya to tabbas tasan he’ll went through thesame thing yanzuma sabida tunda jimawa tasan matsayin Galadima ah idanun Mai Martaba shiyasa bata cikin wani farin ciki sosai because batason abunda zai tada mishi hankali hakanan kuma kwanan nan time to time takan tuna da danginta wanda har takejin she wants to meet them as soon as possible ko ya suke? Allah ne kadai masani,ko zasu yafe mata abubuwan dayafaru abaya wayasani?…………
Washegari Mai Martaba yakira Sulaiman da Almustapha yadubesu cikeda son ya’yan nashi sannan yace….

STORY CONTINUES BELOW


“nakiraku ne sabida muyi magana akan ayyukan dayakamata ayi yakamata mugyara abubuwan da mutanen da muka yarda dasu suka bata and as of now i trust no one but you two sekuma Yaya daga abunda yafaru jiya it’s really going to be hard for me to trust any one anymore”……..
Gyada kai sukayi duka cikeda tausayin mahaifin nasu don daga yanda yake maganar ma zaka gane akwai bitterness sosai acikinta cikin nutsuwa yace”Almustapha”….
Dagowa Almustapha yayi tareda kallon mahaifinnashi ahankali…..
“na’am Abba”….
nadanka maka project ah hannunka na boreholes i want you to go ahead with it and kudi da komai zan baka sekuma you need to go to that hospital after that kaga ya ayyukan ke ciki…………..
Gyada Kai Almustapha yayi kafin Mai Martaba yadubi bangaren da Sulaiman yake sannan yace”about maganan renovation na bangaren bayi dakuma katifu da pillows and everything they’ll need zanbari ah hannunka Babana because aikin zaiyima Imam yawa”……
Cikeda ladabi Sulaiman yace to Abba ammadai I’ve something to say…..
“Go ahead Son inajinka” mai Martaba yayi maganar yana kallon Sulaiman din sunkuyar dakai Sulaiman yayi kafin yace”ni anawa ganin Abba,Yaya should be the one to take over komai daza ayi sabida karka manta anbashi nanda wata biyar yayi proving kanshi as the best person to be the crown prince Abba and only tawannan hanyoyin ne zai cinma burinsa kuma tawannan hanyar ne mutanen gari zasu yarda dashi sukuma san shine yacancanta ba wani ba,agreed I’ll help him out amma aboye something like zuwa sayan katifu da pillows dakuma nemo masuyin aiki sede he’ll be the to supervise all the time daman boreholes kam aikinshi ne shi kadai but wannan dinma shi ne za ace yayi”…..

Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace “thank you Son, Allah yayimuku albarka hakan ma yayi, Allah yacigaba da hada kayukanku kuma, Almustapha shidai se kallon Sulaiman yakeyi cikeda sonshi he don’t know how to pay him,he’s indeed the best Brother he could ever ask for………..
Sulaiman ganin yanda Almustapha ke kallonshi ne yasashi yin murmushi tareda cewa”you’ve to work hard for your people Bro they really need you,make us proud please I can’t wait to see your turbaning ceremony”……
Almustapha besan sanda yaja Sulaiman yarungumeshi cikin jikinshi ba cikeda son shi…..
Mai Martaba da Dad ne suka kalli juna tareda sakin murmushi because seeing both the two sons together hakan yatuna musu da sanda suke samari kaman su yayinda kowannensu yake fatan Allah yasa zumuncin dake tsakanin su ya dore harzuwa karshen rayuwarsu ……..

bangaren Zaliha kuwa bakaramin tashin hankali tashiga ba jin abunda yafaru da Magajiya din because koda tayi fushi da’ita she really need her sabida itakadai tasan bazata taba executing plan dinsu ba don hakane ma bayan kwana biyu da faruwar abun taje tasamu Magajiya din ah house arrest din don ba ahanata ganinta ba because wannan din bekai nada tsanani ba………..
Allah yataimaketa Magajiya ta sauko daga gandun fushin da takeyi zama tayi gefenta tareda cewa “Mama I’m really sorry”takarashe maganar murya akarye kallonta Magajiya tayi wanda cikin kwana biyu harta sake ramewa ga duhu data karayi sannan tace…
“we’re still together karki damu because komiye zasuyi I can never let them win!”……
Cikedajin dadi Zaliha tace…
“me too Mama sedai yanzu yazamuyi sun rufeki tayaya zamu cika burinmu?”…..
Murmushin mugunta Magajiya tayi kafin tace Almustapha yanada sauran wata uku kafin yacika burinshi nikuma wata biyu zanyi anan suyi duk abunda zasuyi when I’m out I promise you acikin wata dayan nan zan ruguza komai karki damu banason nayi wani abu yafaru inacikin nan sabida kada hakan yajaza mana karaya sedai inason kinemi wata baiwa Salma she’s one of my people tana bangarensu Almustaphan I asked her to keep an eye on them and last week tafada min babu abunda yataba shiga tsakanin Almustapha da Asma’u infact baswa kwana daki daya and it seems that they’re not on good terms kawai duniya ne take ganin suna tare kamar masu son juna but in reality that’s not the truth kiinga wannan wata hanya ce dazai taimakemu but still kinemeta tacigaba dasaka musu ido tana kawo miki information nikuma duk yanda ake ciki just let me know in akwai abunda zamuyi semuyi kafin nafito din dukda I hope nothing works out between the two of them………
Jinjina kai Zaliha tayi kafin Magajiya tace and yes kiyi aiki akan position din da Mai Martaba yabaki just act like nothing happens and you’re okay with it….
Gyada kai Zaliha tayi ahankali sannan tayima Magajiya godiya tafice babu abunda yafi damunta ayanzu ma dayawuce yanda Sulaiman yarage mata maitan son su shirya and baicika shigowa bama se tayi bacci wataran she really don’t know what’s going on with him amma koma miyene bazata biyeshiba she’s sure in the future zegane sonshi takeyi shiyasa takeyin hakan…………….

STORY CONTINUES BELOW


Satinsu Munira daya Sulaiman yamaidasu gida Asma’u harda hawayenta don bakaramin jin dadin zuwansu tayiba sabida suna debe mata kewan gida bakadan ba…….

*TWO MONTHS LATER*……

Around 9:20pm 
Zaune take ah parlour tana kallon ZeeTV taji wayarta tayi kara dubawa tayi Sulaiman ne batareda tayi wata wataba tadaga……
“Sister in-law”shine abunda yace…
Yar dariya tayi sannan Itama tace”Brother in-law”don kwanan nan tagama gane Sulaiman akwae son tsokana shiyasa Itama karfi da yaji ta koya inyace Sister Inlaw tace brother in-law inko yace Aunty Asma’u Itama Uncle Sulaiman inma Yaya Asma’u yace Itama Yaya Sulaiman haka suketa fama dai……

“Lol kindai dage sekin rama duk tsokanar danayi miki”, murmushi tayi to yazanyi dakai Yaya Sulaiman….
“Hhhh toshikenan tunda haka kikace daman nakiraki ne incemiki ki kunna TV za’afara network news akwai abunda nikeson ki kalla”…
“To shikenan”,tabashi amsa kafin tamaida Chanel din zuwa netwrk news din gani tayi ana nuna abubuwan da Almustapha yayi cikin watanni hudun da aka bashi acting crown prince,acewar me bada labaran he has achieved many things wanda yataimaki talakawa dadama kama daga kan availability of wata acikin garin Zaria wanda yaduba areas dasuka fi tsananin wahalar ruwa yakuma taimaka musu wurin dauke wannan wahalar hakan kuma bakaramin taimaka musu yayiba Mai bada labarin yafadi yayinda aka shiga hasko unguwannnin acikin talabijin tareda nuna yanda akayi musu boreholes da panpuna gakuma jama’ar unguwar na ta diban ruwa cikeda farin ciki ah fuskokin su….
Samun wasu daga cikin mutanen unguwar akayi yayinda medauko rahoto yashiga yi ma daya daga cikinsu interview….
Yaya sunanka?…..
Dattijon da aka tambaya yasa bakinshi ah mike din tareda cewa…
“Sunana Hashimu Ibrahim”…..
To barka da rana Mallam Hashimu Ibrahim meye zakece gameda wannan cigaba dakukasamu ah unguwannin talakawa da dama?……..
Dan murmushi dattijon yayi kafin yace”Babu abunda zanfara yi se godema Allah daya aikomana da mutumin kirki kaman Yarima Almustapha sabida mu mungani munkuma yarda without him duk wayannan abubuwan will never be possible tunda kusan shekara na ishirin cikin garin Zaria bantaba ganin anyi mana aikin da shi yayi mana ba kama daga kan gwamnati har ma sauran shuwagabannin dasukayi mulki abaya,shiyaduba matsalolin damuke ciki yamangance mana ita ah matsayin mu na talakawa babu abunda zamu ce masa sede Allah ubangiji yasaka mishi da alkhairi kuma Allah yakuma sake bashi hakurin duk wasu accusations dayayi tasha abaya dukdama haryanzu wasu akwai tambayoyi da dama ah zukatansu gameda shidin nidai yasani ina alfahari dashi nagode kwarai haka talakawan garin Zaria infact bama su kadai ba na yankin kaduna state baki daya”…..
Murmushi mekawo rahoton yayi sannan yace muma mungode da bamu lokacinka dakayi sede inada tambayar karshe inbazaka damuba?…
Yar dariya Mallam Hashimu yayi sannan yace”feel free kayimin duk tambayar daka ga dama tunda ninayi representing duka talakawan garin nan ne don nuna appreciation dinmu ga Yarima Almustapha”…….
“Ah to to ai shikenan tunda abun hakane”,cewar mai kawo rahoton kafin yace”daman naji kayi maganar accusations da ake ma Yarima ada kuma kayi maganar haryanzu dadaman ku kunada tambayoyi dadama aranku shine nikeson inji wasu irin tambayoyine may be kaga hakan ya’iya kaiwa kunnen Yariman shikuma inyaga dama zai iya zai ansa muku ita daidai gwargwado”……..

Gyara tsayuwa Mallam Hashimu yayi kafin yace”wannan ma wani dabara ne da tunani kuma sannan tambayoyine da basu wuce akan tasowarsa ba dakuma rayuwarsa nada sabida mudai ah iya jinmu da saninmu Yarima Almustapha mutumin banza ne wanda baisan darajar dan Adam ba,a’iya labaran damukeji shi mutum ne da ya dauki lalata ya’yan mutane ba abakin komai ba hakanan shi mutum ne daya dauki shan kayan maye amatsayin abincin cinshi da shan shi duban me kawo rahoton Mallam Hashimu yayi sannan yace agaskiya bantaba ganin Almustapha ba awannan lokacin labarinshi kawai nikeji sede tunda yahau mulki yafara yimana aiki sannan nakuma ganshi ah unguwanmu har muka gaisa tun ranar nafara kokwanton abunda mutane ke fada akanshi sabida nidai babu abunda idanuna suka gane min game dashi inbanda nutsuwa dakuma hankali ga sanin yakamata sannan zuciyata tana fadamin mutum mai irin wannan halayen bazai taba ma tunanin sanin halin da talakawa ke cikiba bare yamayi tunanin taimaka musu shiyasa farkon da akace anbashi acting Yarima hankalinmu yatashi gabadaya don atunanin mu daga ranar to kasar mu ta gama lalacewa ne sede ashe abunda bamusani ba shidin alkhairi ne garemu”,daga yatsa daya mutumin yayi sannan yace” kaga yataimaka mana wurin samun ruwa in a very easy way tayarda kowa zaisamu batareda ya wahala ba sannan ga uwa uba lafiyar talakawa daya duba tahanyar bude asibiti for free ah local government din daya lura suna fama da rashin asibiti sannan neighboring villages ma suna samu suje su aduba lafiyar su kuma abasu magani kyauta cikeda girmamawa batareda an wulakanta suba kuma naji anacewa ma yana gina wani asibitin ah garin nan gakuma masarautar su daya duba halin da Bayi da dogaraye suke ciki ya taimaka musu wannan kadaima bakaramin cigaba bane ba sannan bakaramin kokari yayiba don bakowa bane za iya wannan ayyukan acikin wata hudu Kuma mu munyarda dashi amatsayin wanda zai mulke mu bayan Mai Martaba sarki Abdulrahman muna bayanshi dari bisa dari don kamar yanda nafada maka ina representing gabadaya talakawan mu ne because this’s the way they feel about him kuma munfara doubting abubuwan da mutane sukaita fada akanshi harma muke tunanin ko munyi misunderstanding dinshi ne muna fatan zamu samu ansa daga gareshi kwana kusa Inna neman yafiyarshi ne munema don intakasance ba gaskiya bane abunda aka fada to tabbas mutane da dama sundauki alhakin mutum kamili irin Yarima Almustapha………

STORY CONTINUES BELOW


Godiya Mai kawo rahoton yayima Mallam Hashimu kafin yajuya yana kallon Tvn “to masu kallonmu kundai ji hirardamukayi da Mallam Hashimu wanda ya jagoranci talakawan garin Zaria yakuma fadi abubuwan dasukeji gameda Yarima Almustapha wanda yayi fice cikin watanni kalilan sabida halinsa nagari dakuma nagartarsa gakuma tausayin talakawa da yasa agaba tahanyar taimakonsu dukdama sunce sunada tambayoyi zuwaga gwarzon namu kuma inshallah zamu gwada yi muku alkawarin gwada tuntunban shi gwarzon namu inzai yarda yayi hira damu kozamu samu muji ainahin gaskiyar al amari”
Ahaka akakoma nuna asibitin da Abba yasiyama Almustapha ah kauyen *Gangara* under *Giwa Local government*……. Dakuma yanda talakawa daga kauyika ke karban magunguna kuma akebasu treatment cikin kulawa harma akayi hira da wasu ma aikatan gurin dama wasu daga cikin patients dasuke gun wanda duk hirar bewuce appreciation dasuke nunawa bane ga Almustapha din tareda son jin asalin labarinshi suma……

Asma’u dake zaune tana kallon TVn cikeda amazement haka batamasan tana hawayen farin cikiba ashedai rayuwarnan Inka barma Allah komai he’ll never let you down koita datake tareda Almustapha bata taba tunanin things will turn out this way ba she’s really very proud of him hakanan akullum sonshi kara ruruwa yakeyi azuciyarta sede ganin yanda abubuwa ke tafiya gani take rabuwarsu takusa zuwa tunda shidakanshi yace”when everything comes to an end and when everything is back to normal hakanan in iyayenta suka cire zargin da suke mata akanshi to tabbas he’ll free her from this relationship”,and ko kafin yatafi Gangara seda yasake fada Mata,the time has come may be because tanada tabbacin da Almustapha yayi hira da gidan talabijin yafada musu gaskiyar al amari to tabbas komai yazo karshe don ko ayanzu tasani Almustapha da’ita sunfara 
fita ah zargin da akayi musu abaya daga idanun yan gidansu,to mema yarage indai batun masarauta ne everything is back to normal because angama renovation na bangaren bayi hakanan ansaka musu katifu da pillows,fans da duk wasu facilities dazasu bukata hakanan kuma tayi make sure yanzu basuda wata damuwa regarding wahala kamar jakkai don Almustapha dakanshi yayi setting rules as the acting crown prince after 11:00pm bayason yaga kowacce baiwa awaje dasunan tana aiki she should be in their hostel resting sekuma biyar din asuba wanda Asma’u ce tabashi wannan shawarar dubada yanda problems na raping bayi dakuma lalata da ake dasu yayi yawa wanda tanada tabbacin fitan daren nan ne kesawa hakan yafaru kuma yasa ana rufe bangaren nasu 11:00pm dot sekuma biyar na asuba za’a bude wanda Sulaiman ne yadauki nauyinyin patrol akan batun har abun yadaure sannan Almustapha yayi setting rules akan batun karatunsu na addini every Saturdays and Sundays 8:00~10:00am time na islamiya dinsu ne kuma babu wanda ya’isa ya hanasu zuwa don Mai Martaba kanshi yayimagana akan hakan very strictly insunada aikin dazasuyi ma mutum suyi before that time or after sannan sunbama dukwani dogari da bayin daman insuna son auren junan su su fito su fada sukuma zasu goya masu baya dari bisa dari kada su boye sede bazasu bar masarautar ba they’ll remain over there as slaves but zasu samu nasu gidan cikin masarautar hakan kuma bazai hanasu yin aikinsu ba they’re humans too suma sunada needs din dakowacce mace da namiji sukedashi so,bazasu tauye musu wannan hakkin ba haka batun kayama cikin satinnan aka gama dinka musu aka raba musu set bibbiyu abinci kuwa tuni suka fara samun mekyau kuma ishashe sannan hakan bakaramin taimaka musu yayiba gurin samun karfin yin ayyukansu mekyau batareda gajiyawa ba kumadai haryau ba asake samun wani problem ba kuma anabin doka alhamdulillah gawani respect da akebama Asma’u dakuma Almustapha din because sukansu sunsani without them all this will not be possible hakanan baswa gajiya daba Almustapha hakurin abubuwan dasukayi mashi abaya barinma wanda sukasan suntaba fada mishi maganar banza dadai sauransu…….
Asma’u kuwa rashin dawowar Talatu haryanzu damunta yakeyi gashi ita ba wayaba bare ta kirata fatanta daya Allah ubangiji yasa ba guduwa tayi ba dukda 89% na zuciyar ta nafada mata ba guduwan tayiba tunda alokacin she can see that Talatu is telling the truth and she was willing to help adduarta daya Allah yasa she’s fine dai ga haryanzu ba afara renovation na gida baki daya ba bare Sulaiman yasamu yacire wayannan layoyin don Abba cewa yayi abar renovation din tukunnan se angama dawanda is important tunda su nasun kowani two two years akeyi na mutane masu bukata yafi mahimmanci yanzu daga baya ayi nasun tundama it’s not that necessary…………..
Goge yar kwallarta tayi tareda canza Chanel don dama abunda tazauna kallo kenan kuma angama don ita ba gwanar kallon news bace daman….
Kallon screen din wayarta tayi”she’s badly missing him yau kwananshi goma kenan da tafiya kauyen *Gangara* kuma ko kiranta baiyiba itakuma duksanda tadaga waya zata kirashi seta kasa sabida gani take he should be the first to call dukdama cikijn watanni biyun relationship dinnasi yadanyi improving tunda sukan zauna suji matsalolin juna and subama juna shawara hakanan sometimes sukandanyi hirar da baza arasaba dukdama itace mesurutun yawanci …….
Tananan zaune tahango Ummi tafito daga dakinta jikinta sanye da wani tsadadden lace golden colour wanda bakaramin karbanta yayiba nikaina nayi mamakin yanda take takunta majestically kaman ba’ita ce kezaune kan wheel chair two months back ba,karasawo parlourn tayi tana Habibty ke kadai ah parlour?………..

STORY CONTINUES BELOW


Cikin sauri tadan ja numfashi tareda gyara fuskarta don batason ma Ummi tagane tayi kuka don seta tada hankalinta yanzu murmushi tasaki kafin takalli Ummin data karaso cikin parlourn yanzu…
“Eh Ummi su Amira harsun wuce bangaren Mom”,dake yanzu can suke kwana Sumayya takoma makaranta Itama tana final year yanzun basu cikason barin Mom din itakadai ba………
zama Ummi tayi kafin tace”to shine kikayi zaman ki ke kadai dakin sameni ah daki ai musha hirar mu”,yar dariya Asma’u tayi tana kallon Ummin akullum matar kara kyau da fresh takeyi gawani hutu datasamu ya’yanta kuwa kula suke da’ita kamar wata kwai komai takeso shi sukeyi mata bata manta ranar da Ummi tafara tafiya yanzu kusan three weeks kenan Almustapha da Sulaiman baswa gari sunje Giwa ganin ya ayyukan asibiti ke wakana amma data kira tafada mishi wuraren karfe goman dare ah take suka kamo hanya yana isowa gida yazo yarungume Ummin yana…
“I’m so very happy Ummi kiyi tafiya ingani please!”……
Murmushi Ummin tayi cikeda Son Dan nata itakanta tasan she’s so blessed to have all her children dama Sulaiman datake ganinshi kamar Dan cikinta kafin tataka kafar normal…….
Sakan baki Almustapha yayi he really can’t believe it Ummi can walk like before cikeda excitement yadinga Ummi”ya akayi hakan tafaru,how did this happen?”…..
Jan cheeks dinshi tayi tana smilling sannan tace”ikon Allah Imam,I don’t know either kawai yau jinayi inason ingwada tashi senaga natashi cikin ikon Allah without witnessing any sought of pain haka na taka kafarma normally, it’s Allah’s miracle Imam and that happens only because of all your prayers and care”tayi maganar tana nuna dukansu dake daki da hannunta fuskarta daukeda annuri don Allah kadai yasan how much her children means to her which includes Sulaiman and Asma’u aganinta batada wani family daya wuce su they’re all she needs now…….
Dan numfasawa Asma’u tayi tana tuna duk abubuwan dasuka faru aranan itakanta she was very happy because duksanda taga Almustapha ciki farin ciki jinta take kaman tafishi farin cikin ma because her happiness lies in his happiness…….

Ganin tanata murmushi ne yasa Ummi cewa”to Habibty memuka samu ne kike ta murmushi ke kadai”……
Yar dariya Asma’u tayi tareda sa hannu ta boye fuskarta alamun kunya..
“Babu komai Ummi”….
Dariya Ummi tayi kafin tace”sirri ne kenan komi?”….
Itadai Asma’u se dariya takeyi kawai murmushi Ummi tayi sannan tace….
“ko duk murnan Mijinki zai dawo gobe kikeyine gashi keko kwalliya bakiyi mashi ba babu lalle babu kitso Ma’un Imam?”, Ummi tayi maganar cikeda zolaya……
Asma’u da mamaki yacikata tace…..
“Ummi dagaske gobe zaidawo?”,don harga Allah batada labarin….

Ummin ma damamaki ah fuskarta tace befada miki bane ba?….
Dan sunkuyar dakai Asma’u tayi don batason tace mata tunda yatafi basuyi waya ba tana iya yima Almustapha fada shiyasama kawai tace”may be yanason yayi surprising dina ne to”…
Murmushi Ummin ma tayi tana”to nikam nayi baran barama kenan to muma zamuyi surprising dinshi gobe dasafe zansa akawo me kitso da lalli tazo tayi maki har gida”….
Cikeda kunya Asma’u tace…
“thank you Ummi”
Dukdama bawai ranta naso bane ba suna cikin hakan ne wayarta tashiga ringing kallon screen din wayar tayi”Mr Taciturn” ah rubuce wani irin farin ciki da nervousness taji yaziyarce ta lokaci guda sede bazata iya daukan call din ah gaban Ummi ba Ummi dake gefe tanaji har wayar ta tsinke aka kuma shiga sake kira bayan wasu mintuna tuni tagane wayene don haka tace”tashi kije ciki ki answer call din Mijinki”……
Asma’u kaman wanda jiratake tatashi sumui sumui tawuce dakinta sede kafin ma tashiga dakin call din ya katse turo baki tayi tareda shiga dakin tarufe kofar kafin takoma bakin gado tazauna tafi minti biyar bekira ba kuma tasan dakyar yasake kira tama gode Allah dahar yakira sau biyun don haka seta dauki wayar tayi dialling number shi haka yashiga ringing har ya tsinke be dauka ba cikeda kewanshi tashiga sake kira se ana ukun ne yadaga shima har yakusa tsinkewa……….. 1

Kasa magana tayi shima shiru yayi dukda yanason jin muryarta amma ganin yau itakeji da mulkin yasashi cewa…
“inbazakiyi magana ba zan katse I’ve alot of things to do”……
Kawai saita sakinmai kuka ta wayar Allah kadai yasan yatake ji gakuma kewarshi datayi amma don wulakanci abunda zaice mata kenan after good 10days da rabuwansu bekirataba seyau and this’s all she get from him……..
Almustapha dake kwance kan gado ya lumshe idanunshi ahankali harcikin zuciyar shi yakejin kukan nata shikanshi yarasa miyasa kwanan nan yafara damuwa da al amurar yarinyar sosai yau kwananshi goma ah garin nan akullum bashida tunani inya zauna shikadai senason jin muryarta medan karen amo dakuma wannan shegen shagwabar datake mishi aduk sanda suke tare,he just missed everything about her wanda tun yana daure zuciyarshi wurin ganin bai kirataba har yakasa yaudin seda yakira dukdama gobe zai dawo……..
Ahasale yace”miyena kukan to?”…..
Batabar kukan ba hakan bata kulashi ba tashi yayi yazauna akan gadon tareda jingunuwa da gadon sannan yadauki pillow ya rungume akirjinshi in a very calm voice yace”Asma’u ba tambayarki nakeyi ba,miyene abun kuka ah abunda nace din?”,don yalura inmasifa zaiyimata bazata dena kukan ba…….
Yanda yayi maganar seda tsikar jikinta yatashi hakanan batasan sanda tatsai da kukan ba tana jan numfashi kafin ta’iya cewa “bakaine ba daga kirana seka fara min masifa”,sekuma taci gaba da kukan don data tuno abunda yafada din setaji ranta yasake baci……….
Cire hannunshi yayi daga jikin pillown tareda hargitsa gashin kanshi aranshi yana”ya ilahi!”……
Kafin dakyar ya’iya cewa”is this the reason you’re crying?”…
Gyada Kai tayi kaman wanda tana gabanshi cikin sigar lallashi yace…
“to I’m sorry shikenan?”……
Nanma gyada kan takumayi kaman tana gabanshi…..
Jin batayi magana ba yasake kasa da murya kafin yace”to baki hakura bane komi?”……
Jin yanda muryarshi tayi batasan sanda tace nahakura ba yar murmushi yayi aranshi yana”so childish” sannan afili yace…
“to seda safe”……
Ware idanu tayi batasan sanda tace….
“Daman kirana kayi kasani kuka?”….
Rasa dalilin dayasa yakirata yayi shima shidai yasan he just want to hear her voice and nothing else amma seya bingire da 
“daman nakira inason magana da Ummi ne nayi ta kiran layinta bata dauka ba shiyasa amma bartama kawai nasan tayi bacci yanzun”, bejira cewarta ba ya katse call din……
Takaici ne ya’isheta watoma yakirata ne badan yanason magana da’ita ba don wulakanci Ummi yakeson magana da,wulli tayi da wayar yayinda batasan sanda taji hawaye sunfara bin kuncinta ba it’s all her fault data saka ma ranta son the wrong person dakyar tasamu bacci yayi awun gaba da’ita..
Washegari karfe tara yayima mai lalle da kitso ah masarautar haka Ummi tasa aka gyara surukarta tsaf se wuraren shabiyun rana suka gama kafin Matar tatafi karkuso kuga hadaddiyar lallen da akayima Asma’u hakama kitson bakaramin kyau yayiba se sheki yakeyi murmushi Ummi tayi tareda cewa”yanzu naga kinfito ah Matar aurenki”……
Dariya Asma’u tayi yayinda tace barinaje na dora abinci to don daman se yanma zasu iso………….
Ummi ne tace to yayinda Asma’u tawuce kitchen don tace ita dakanta zatayima Almustapha abinci yau fried rice tayi wanda yaji naman kaza gaja gaja se coslow da zobo drink because tasanshi sarai baicika son atara mishi abinci kala kala ba haka tadama mai fura da Nono tasa ah fridge dinshi tasan definitely ze iya sha da dare kafin yakwanta kokuma gobe dasafe,seda ta tabbatar komai yazama set kafin tawuce dakinta donyin wanka……. +

Around 4:00pm haka tahade cikin wata hadaddiyar blue shadda datasha aiki bakaramin kyau Asma’u tayiba sewani sheki takeyi ita kadai haka tayi sallar laasar tunda ta’idar takejin surutu yakaru acikin gidan ga bayin sekai kawo sukeyi akai akai can kuma setaji muryar Sulaiman yanayima Almustapha sannu da zuwa wani irin dadi ne yaziyarce ta jin ya’iso lafiya seda tagama addu’o’inta sannan ta ninke sallaya tadauki hadaddiyar gyalenta tayafa tafice ah dakin baya parlour yanzu hakanan babu kowa da alama sunbarshi yashiga ya huta kenan dakinshi tayi tareda knocking kofar………
Almustapha dake zaune bakin gado gabadaya yadamu yaganta don shi soma yayi yayi arba da’ita first days shigo haka tun yana parlour yadinga leke leke kozega inda zata fito amma babu ita har yakai ga shigowa dakin don haka koda yaji anbuga kofar se yasama ransa may be itane cikin muryar shi me amo yace”Come in”…….
Turo baki tayi kafin tashiga dakin tana….
“he’ll always be the Taciturn as he’s”…….
Tunda tashigo yakafeta da lumsassun idanunshi wanda har hakan yasata jin wani irin uneasiness murmushi tasaki wanda yafidda kyawawan hakwaranta tareda tareda bayyana dimples nata sannan tace…
“sannu da zuwa”…
Seda yadanyi shiru na sakanni kafin yace “yauwa sannu”……
Zama tayi gefenshi tareda dubanshi cikeda kulawa”kagaji sosai ko Yaya imam?”…..
Murmushi yasaki tareda jan karan hancinta dadan karfi…
“kedai adole kinmaida sunana Yaya Imam”……
Cikeda shagwaba ta taba hancinta tana “auch!dazafi fa”….
Yar dariya yayi”serves you right”…..
Batarai tayi da turo baki ahankali tace “yadawo kuma ze isheni da mugunta”……
Sarai yajita haryana shirin tashi seyayi saurin dawowa yazauna tareda matsowa dab da’ita”mekika ce?”….
Cikin sauri tadan jada baya ganin closeness din yayi yawa kafin tace…
“nifa bance komai ba”…..
Tashi yayi tareda shigewa bathroom yana”matsoraciya kawai”…..
Itama harara tabishi dashi kaman wanda yana kallonta aranta tana”nidai ba matsoraciya baceba karfina akafi”,gashi ita koma yaba lallenta baiyi ba bare akai ga batun kitso dake bayan dankwalinta……….

Haka tatashi tafice don hada masa abincinsa tasan wanka zaiyi shima koda tashiga kitchen daukar abincin ji tayi su Talatu na zancen an yi releasing Magajiya da yanman nan daga under house arrest”Hindatu ne tace kinga yanda tayi baki kuwa gashi susan da takeyima ya karu minti minti gawasu kuraje sun fiffito ah jikinta babu kyaun gani”…….
“Hmmmm Allah ba azzalimin bawan sa bane ae”,cewar Hindatu……

Itadai Asma’u karasawa tayi cikin kitchen din tadauki abunda zata dauka tanajin sunata zancen Magajiya da alama ma basusan da shigowarta ba kokuma sunji motsin nata amma basu gane itan bane itadai damuwarta Allah yasa kada matar tazo musu da wani problem kuma they live in peace for the past two months batason wani damuwan kuma………..
Ajiye abincin tayi kan dinning table jin wayarta tayi ringing kafin tawuce dakinta cikin sauri don recieving call din……..
Aisha ce cikeda murna tadaga call din tana”badai har kinshigo gariba?”…..
Dariya Aisha tayi daga daya bangaren tana”yanzunnan naiso gidan Aunty Suwaiba”,ayya ya hanya Aisha?….
Alhamdulillah Ma’un Musty naga news all over mijinki na wuta fa…….
Itadai Asma’u dariya tayi tana “Zaki fara ko kedai yanzu bar maganarnan yaushe zakizo min?”…..
Dan shiru Aisha tayi tana tunani kafin tace”cikin weekend in Allah ya yarda”…….
“Kai Aisha har weekend,nikam gaskiya yayi nisa yaufa wednesday” Asma’u tayi maganar kamar zatayi kuka……….
Ke wasa nakeyi miiki amma gaskiya se Friday zanzo inada abunyi gobe badon Asma’u tasoba tace to shikenan Allah yakaimu Friday din kada kuma ki manta tsarabana na kaduna………
To naji cewar Aisha tana dan dariya, murmushi Asma’u tayi”ba’in barki kihuta kin kwaso gajiya kigaida min Auntyn please”…….
Daganan sukayi sallama Asma’u ta katse call din…….
Jijjiga wayar tashigayi yayinda take fatan Allah yasa Asiya ma cikin watan nan zatazo Zaria don tace mata takusa zuwa gari itada Yaya Aslam……..
Ajiye wayar tayi kafin tatashi tafice tadauki abincin Almustapha tawuce dakinshi koda tashiga haryayi wanka yasauya kaya zuwa kananan kaya white T-shirt sekuma jeans black sewani yalki yakeyi shi kadai ajiye abincin tayi kan stool kafin tace….
“ga abinci Yaya imam”
Dan yatsina fuska yayi don Allah yagani bayajin yunwa kwata kwata ahankali yace”I’m not hungry kibari se anjima”…..
Cikeda damuwa tace”kanasamun kaci abinci mekyau acan ma kuwa?, gashi harkayi baki ka rame please eat something”tayi maganar cikin sigar lallashi…..
Kai tsaye yace”Allah banajin yunwa ne”……
Gyada masa kai tayi sannan tace to
“Inkawo maka ko fura mana kasha”…
Gyada mata kai kawai yayi alamar to don yasanta invai yardaba tadinga yimasa jaraba kenan……..
Cikeda Jin dadi tadauko furar ah firijin dakinshi ta ajiye mishi babu bata lokaci yashiga sha don yanzu yakan ci abinci ah gabanta,seda yagama shan furar tas sannan ya ajiye bowl din itakuma tana zaune gefenshi tana karema features dinshi kallo batareda ta ankara ba taji yana gyaran murya furgigit tayi yayinda lokaci guda kuma wani irin kunya ya lullubeta batareda ta kalleshi ba tace”Harka gama Sha”………
Almustapha da idanunshi kekanta haryanzu yace”kallon na menene kuma?”……
“Ni na kalleka?”,tayi masa tambayar tareda tashi ta kai hannunta don daukar bowl din furan don taganta empty……..
Bata ankara ba taji yakamo hannunta ahankali yana karema lallin kallo jin tana jin wani iri yasata kokarin janye hannun amma seya sake ja cikin sauri wanda hakan yasa suka fada kan gadon baki dayansu yayinda take samanshi harsuna iya jin numfashin 
juna rumtse idanunta tayi ahankali gawani electric shock dataji ya mamaye duka illahirin jikinta bangaren Almustapha ma hakan ne,besaki hannu ba hakanan bedena kallon lallen ba cikin rada yace”miye wannan ahannun ki?”…………..
Asma’u da idanunta ke rumtse takasa kallonshi jin yayi magana batasan lokacinda tabude oily eyes dinta tadaura cikin nashi ba,shima kallon ta yakeyi yayinda dukansu kamshin turaren jikinsu ya gaurayu ya bada wani irin special scent….
Wannan karan bin zanen lallen yakeyi da fingers dinsa yana tracing kafin yakuma yin kasa da murya”what’s the name of this Asma’u?”……
Batasan sanda tasauke numfashi ba tsabar yanda muryarshi keda effect akanta cikin tsoro tsoro da muryarda take cracking tace
“it’s henna design”……
Wannan karan murmushi yayi tareda cewa..
“wayace kiyi to?”……
Jin tambayar shi tafara yawa gashi yaki sakinta yasata cewa cikeda shagwaba…..
“Yaya imam mana”takarashe maganar tareda kokarin tashi daga kwancen don ta lura baida niyar barinta and it’s an opportunity tunda berike waist dinta ba aikuwa tana kokarin tashi ya birkito ta tadawo kasanshi wannan karan shine ah sama………
Batasan sanda tafara hawayeba muryarta na rawa tace”kabarni intafi please”…….
Shima cikin rada yakumacewa…
“sekin fada min wayasaki kiyi wannan abun”….
Wannan karan harda dan bubbuga kafarta cikeda shagwaba tana…
“bakaine kace inyimaka ba har ah kafa ma nayi dakuma kitso”……
Yar murmushi yayi ganin yanda ta daddage shi yace tayi sa hannu yayi yaja yar karamar pink lips dinta yana…
“bazaki daina min karyaba?”…..
Ganin kamar goshinsu nason hadewa dana juna ga kamshin dake fita ah bakinshima yanason rikitata yasata saurin sunne kanta cikin kirjinshi nanma bata tsira ba………..
Jin tayi lamo ah kirjinshi yasashi cewa”silly girl”,tareda tashi daga jikinta yazauna dukda kuwa baiso ba don yanda suke dazun bakaramin comfortability yajiba dawani irin al amari dashi kanshi bazai iya fassara shi yanzu ba…………
Itakam kasa tashi tayi tananan kwance hakanan idanunta ah rufe dariya yakesonyi amma ya gimtseta yanabin duka jikinta da kallo har idanunshi yakai kan lallen na kafanta bakaramin kyau abun yamishi ba ga lallen yakarbi fatar jikinta dubada ita fara ce……..
Jitayi ah jikinta yana kallonta hakan yasa tayi saurin tashi tana neman hanyar guduwa janyota yayi kiiiiii tadawo ta baya cikin sigar zolaya yace”Baki nunamin kitson ba?”……..

STORY CONTINUES BELOW


Turo baki tayi kaman tana kallonshi”banaso bakace bakai kace inyi ba”…….
Yar dariya yayi yana…
“baza dai kidaina min sharri bako?”yakarashe maganar tareda cire dankwalin kanta daman gyale kam tundazu yayi hanyar garinsu……..
Zubama kanta kallo yayi donba karamin kyau kitson yayiba gasu kanana gashi abunka da farar fata se hakan yakara fidda kyaun kitson ga Asma’u akwai gashi masha Allah…………
Sa hannu yayi akan nata yana”yanzu wannan dukdan ni akayi?”…..
Itadai kin kulashi tayi dukda tajishi murmushi yayi sannan yace..
“tonidai baiyimin kyau ba daga kitson har lallen”…….
Tsabar takaici jitayi kaman ya soka mata allura ah zuciya cikin sauri tatashi ko zarar dankwalinta batayi ba tace”nidama badon kai nayiba nayi niya ne”,takarashe maganar kamar mai shirin yin kuka don bakaramin daurewa tayi ba don ganin hawayen basu zuba……..
Lumshe idanunshi yayi don shi kokadan maganar ta bata bashi haushiba don yasani donshi din tayi she’s just trying to deny it sabida abunda yace din shikuma bawai abun be burgeshi bane he just don’t want her to start thinking that she’s special to him………..
Haka takarashi mitarta tafice harda harara baikulata ba bare tasan ma yanajinta ficewa tayi ah dakin zuwa nata rai bace harma takejin kaman ta tsefe kan yanzu shikuwa dan murmushi yayi tareda tashi don zuwa gun Ummi ………

****
Zaliha cikeda farin ciki tace I’m so happy that you’re free now Mama……
Magajiyan da duk ta rame tace”me too Zaliha and now will’ll accomplish our goal together”……

Gyada Kai Zaliha tayi kafin tadubi bayin dake tsaye tace “kuzo kuyimata serving abincin don already hartayi wanka”……..
Cikin sauri guda biyu daga cikinsu sukazo suka shiga serving Magajiya cikeda tsoro don yau gabaki dayansu babu mai farin ciki don gani sukeyi za akoma square one ne kawai………
Seda suka gama serving dinta kafin wanda zata bata abincin ta karaso fita Zaliha tayi bayan tacema Magajiya zataje tadawo, gabadaya tarasa ta’ina ma zata fara yima Magajiya bayanin abubuwan dasuka faru ah masarautar donkuwa for the past one month akadaina barinta zuwa ganin Magajiya sabida zuwan da takeyi yayi yawa awannan lokacin tagaji da ganin abubuwa suna tabarbare musu and she’s happy that Magajiya is back finally may be she’ll take an action itan tana cikin wannan tunane tunanen ne yayinda take tafiya wata baiwa tazo da gudu tazube gabanta tana haki….
“Ina wuni Gimbiya”……
Tsayawa Zaliha tayi tana hararan baiwar don bakaramin tsoratar da’ita tayiba…
“meyene yafaru kikazo aguje kamar wanda akayi maki mutuwa?”………..
Cikeda ladabi yarinyar tace”Gimbiya Safara’u da Halima ke dambe munyi munyi murabasu sunki rabuwa harma suna faman Jima juna ciwo”……..
Hararanta Zaliha tayi kafin tace kije kikiramin sarkin Gidan Yari jiki na bari yarinyar tawuce don aiwatar da abunda aka sakatan yayinda Zaliha tawuce bangaren bayin don ganin meyake wakana tunda ta’isa gurin duk bayin dake kewaye suna kallon dambe sukayi saurin watsewa yayinda kowa takoma bakin aikinta sabida mugun tsoronta sukeyi su Safara’u kuwa se damben sukeyi suna yakusar juna batareda sunsan da zuwan Zalihan ba har Sarkin gidan yari yaxo shine yadaka musu tsawa wanda hakan yasasu rabuwa cikin sauri……
Bakuda hankali ne?…
Ko kunason kumaida mana masarautar filin dambe ne Sarkin gidan yarin yayi magana rai bace yayinda Safara’u batadaina hararar Halima ba tana”nikam cin ubanki zanyi inni zakiyima sharrin sata”…..
Halima kuwa hawaye takeyi tana”wallahi ke kikadauka naganki miyasa kike musawa bayan kinsan kinyi abunda nake tuhumarki dashi!”…..
Sarkin gidan yari ne yace”ahhhhh bazakuyi shiru ba?”…..
Wani harara Zaliha tasakar musu kafin tace da Sarkin gidan yari aje ah kullesu zuwa gobe da yanma don ita yanzu tanada abunyi when she’s free zatazo taji me yahadasu aikuwa hakan akayi se hakuri suke bata amma ko kallon inda suke batayiba tayi wucewarta zuwa bangaren ta tafison se Magajiya ta huta zuwa gobe ko jibi seta sanarda ita halin da ake ciki……..
***
Da dare Asma’u dasu Afiya nazaune ah parlour Amira tace nikam Masa nike kwadayi wallahi……
Dariya Asma’u tayi kafin tace”to basai ayiba nima nakwana biyu banci ba gashi baya time table dinmu na abinci”…….
Turo baki Afiya tayi don ita masa baidametaba kafin tace…
“ba anayi ah can cikin gida ba kusa akawo muku mana?”….
Cikin sauri Asma’u tace a’a muma zamuyi anan barima infada masu iya Jamila ko za ajika shinkafar yanzu gyadamata kai Afiya tayi yayinda Amira cikeda murna tace”you’re the best Sister In-law wallahi”……
Murmushi kawae Asma’u tayi yayinda Afiya tace Sis kije kidawo kiji favour din da zakiyimin nikam don Allah…..
To kawai Asma’u tace mata kafin tawuce dakin su Jamila harsun fara shirin kwanciya da dan damuwa tace zantakura ku ko?…
Cikin sauri Jamila, Salma,Hindatu da rukayya suka tashi cikeda ladabi suna”habadai Gimbiya wani irin takurane wai?”…
“Wani abun za ayine?”wannan karan Jamila ne tayi magana……
Asma’u bakaramin jin dadin respect dinda suke bata takejiba tasan dae she’s far young and she’s also free with them har wasa da dariya sunayi amma hakan baihanasu bata girma amatsayin ta na Matar Almustapha ba, murmushi tasaki sannan tace…
“Daman Masa nikeson muyi na karin kumallo ze yuyu kuwa?”…..
Zeyi mana Gimbiya indae kince ayi se ayi din yanzuma semu wanke shikafar mujikata cewar Rukayya……….
Tashi Jamila da Hindatu sukayi yayinda sukace ku yarannan kuyi kwanciyar ku zamu wanke mudawo……
Rukayya ne tace
“a’a iya Jamila muyakamata muyi ae bakuba”…..
Salma dataji haushin Rukayya na iyayin da takeyi masu tace”eh wallahi kuzauna kawai zamuyi”,dukda maganar tata batakai har zuci ba,cewa sukayi karku damu munyi niyane haka sukafice sukabarsu Salma na hamdala da ba’a bi zancen Rukayya ba don Allah yagani tagaji bacci takeson yi kuma…….
Haka sukayi kitchen harda Asma’u nanne Jamila kecewa dakikayi maganar masa senatuna masar Aunty, ta’iya masa kamar mi inba Masartaba mai Martaba bayacin nakowa……
Cikin sauri Asma’u tace”dagaske Iya Jamila?”….
Gyada mata kai tayi sannan tace haka Yariman ma yanason na Aunty sosai dukda shi yanacin nawasun ma kinga gobe dole muyima mai Martaba abincin shi daban sabida kada asamu matsala……….
Murmushi Asma’u tayi kafin tace…
“Mai Martaba zaici Masa gobe iya Jamila and that too na wanda Ummi tayi da hannunta”…..
Cikeda damuwa Iya Jamila tace…
“Anya zata yarda tayi?” ….
Murmushi Asma’u tayi kafin tace kuwanke shinkafar kawae kujika zanje inyi mata magana she’ll do it I’m sure,gyada kai kawai sukayi sannan sukacigaba da aiyukansu Asma’u kuwa ficewa tayi tayi hanyar dakin Ummi tana sake sake aranta tasan tabbas Ummi will be hurt intayi mata maganar yin masa sede yazatayi?….
She want to help her out,Itama tanason ganin matar tanacikin farin ciki da jin dadi like she always want her to be happy as well,tunda haryau Talatu bata dawo ba atleast she should try her luck also wurin ganin tayi reuniting dinsu though she knows it’ll be difficult bare anhada abu da asiri ahaka harta karasa dakin Ummin…..
Ummi nazaune kan gado idanunta dauke da eye glasses tana karanta news paper tajuyo takalli Asma’un tareda sakar mata wani kayataccen murmushi…….

STORY CONTINUES BELOW


Itama maida mata da murmushin tayi kafin tace…
“Ina wuni Ummi na”…..
Murmushi Ummi tayi kafin tace “lafiya Lau Habibty na se yanzu kika tuna dani,wato miji yadawo ko”,tayi maganar cikeda zolaya……
Murmushi Asma’u tayi tareda dan lullube fuskarta,dariya Ummi tayi tana cire eye glasses din…
“shy shy kawai,nadauka harkun kwanta fa don banji motsin su Afiya bama”…..
Muna kuma parlour fa Ummi bamukai ga kwantawa ba,”sunacan sunata asararren kallon ko bayan ga karatu ah gabansu WAEC and NECO is approaching ga uwa uba jamb ma”……
“Ummi suna karatu fa”……
Yar hararanta Ummi tayi tana”to tare musu ke me kawaye ko kanne nema zance”……
Dariya kawai Asma’u tayi kafin tace”Ummi Yaya wai zaici Masa dasafe nikuma ban iyaba”,tayi maganar murya ah karye sanda ta ambaci masa seda kirjin Ummi yashiga dukan uku uku hakanan rayuwarta da Mai Martaba yashiga dawo mata lokaci guda Asma’u nalura da expression dinta amma batace komai ba…….
Dakyar Ummi ta’iya faking smile tace”kamar kinkoyi yin masa daga yau zuwa gobe, I’ll help you out Dear”……
Cikeda Jin dadin maganarta tace…
“thank you Ummi”…..
Dan shafan cheeks dinta Ummin tayi kafin tace kicema su Jamila sujika kaman yanda nasaba yi inkuma sun manta ne se inzo inyi”gyada ma Ummin kai tayi kafin tasake yimata godiya tafice tasamo su Jamila tafadamusu aikuwa sunyi mamaki kafin sukayi yanda tacedin don basu mantaba koda su suke wankewa su jika daman itakuma inta tashi setayi miya da hadin bayan an niko”……..

Haka takoma gun Afiya fuskarta daukeda murmushi tana”maganar me zamuyi Afiya?”…..
Afiya cikin sauri tataso daga kwancen da take tareda yin kasa da murya alamar roko”don Allah Aunty Asma’u taimako zakiyi mana”…..
Dariya sosai Asma’u tayi don this’s the first time da Afiya takirata da Aunty”lallai wannan taimakon dazanyi gagarumi ne na lura harda Aunty”. …….
Amira ne tace…
“kina wasa da Afiya kenan indai gurin kalaman yaudara ne nabata award”……
“Lol”,cewar Asma’un kafin tace”fadamin miye damuwarki Sis”…..
Kara maraicewa Afiya tayi tana”karki biyema Amira batasan abunda nakeyi harda itabane ba shiyasa take neman hure miki kunne”…………

Dariya Asma’u tayi…
“kekam fadi abunda ke ranka kawai”……
Cikeda Jin dadi Afiya tace…

“Daman inason kitaimaka mana kiyima Yaya Almustapha magana yadawo mana da system da phones dinmu kinga munshiga ss3 yanzu we really need it for assignment and other purposes dai”……

Dariya Asma’u tayi don gani take Afiya magana takeson fada mata,ganin tana dariyar ne yasa Afiya cewa…
“dariyama nabaki Sis?”….
Asma’u daharyanzu takasa daina dariyar tace”yo ba doleba of all people kice nizanyima Yaya Imam magana yadawo muku da laptop dinku ba gwanda kice Ummin bama”……
Cikeda damuwa Afiya tace”Ummi takiyi masa magana fa wai inyabamu zena distracting namu shikuma munmushi maganar yafi ah irga amma yaki dawomana dashi”………
Tashi Asma’u tayi tana”tonidai badaniba kuma kunyi trying luck dinku bebayar ba seni?”…

Wannan karan Amira ce tace”kikasani kozaiji maganar ki,just try your luck for us please”……
Yanda Amiran ta marairaice fuska yasa Asma’u cewa……

“I’ll try but in ya dizga ni akanku zanrama kuma ma kawai dai zanyine sabida karkuce naki”……..
Cikin sauri Afiya tace”eh munji try your luck for us”…….
Gyada musu kai tayi kafin tace”yashigo ne!”…..
Gyada mata kai sukayi duka suna baijima da shigowa bama,to kawai tace musu kafin tawuce dakinshi samunshi tayi zaune kan sofa yanata aiki cikin laptop…….
Turo baki tayi kaman wanda yana ganinta kafin takarasa tazauna gefenshi yanajinta amma yaki kulata because he’s so busy tafi minti talatin agurin har bacci yadauketa kawai seji yayi kan mutum ya kwanto kan kafadunshi cikeda hafula yace”Asma’u aiki nikeyi please!”, yakarashe maganar tareda juyowa don kallonta sede da mamakinshi yaga ashema bacci tafarayi murmushi yasaki yana kallon kyakyawar smooth face dinta ga eye lashes dinta dake kwance zara zara dasu baitaba tunanin karema fuskarta kallo ba seyau fuskarta is so round yayinda gashin giranta ah kwance lub lub dasu gwanin ban sha’awa kaman ita tabama kanta idanunta kuwa dara dara dasu babu laifi ga kwancecciyar eye lashes dinta daya kara musu kyau bangaren hanci kuwa sede ince Masha Allah donkuwa Asma’u akwae hanci tayi gado daga Umminsu se yar karamar pink lips that is well shaped gashi da daukar hankalin jamaa ayanzu ma lips din sanye yace da wet lips wanda yakara haskaka shi don Asma’u bata taba rabuwa da shafa man baki…….
Almustapha kanshi yarasa dame zai fassarata she’s just so perfect kamar yanda takeda sanyayyar hali,Masha Allah dakyar ya’iya kauda tunanin dake ranshi kafin ahankali don kar ya tasheta yadaga kan nata yamatsa sannan yakwantar da’ita kan sofa din daukar laptop din yayi yakai kan bedside drawer dinshi kafin yadauko katuwar blanket din dake kan gadonshi yazo ya lulluba mata ah jikinta yajuya zai tafine yaji anriko hannunshi juyowa yayi ahankali gani yayi idanunta ah bude tana sakar mai lallausar murmushinta…
“Thank you kuma na yafe maka kin yaba lallena dakayi”,don tunsanda yadaga ta daga jikinshi tafarka kawai lamo tayi sekuma ga mamakinta taga ya lulluba mata blanket dukda batayi tsanmani ba,kallon hannunshi data rike yayi sannan yace”kitashi kije ki kwanta to”……
make mai kafada tayi…
“ni ba yanzu ba banajin bacci”…..
Janye nashi yayi cikin nata”to aini inajin baccin ko?”……
Turo baki tayi ah shagwabe”Kai Yaya Imam bazai wuce 5minutes ba, please”,tayi maganar tana karya wuya zama yayi ah gabanta batareda yace komai ba…….
Cikeda Jin dadi tace…
“Daman maganar laptop da phones dinsu Afiya ne please kamayar musu kaga yanzu sunshiga ss3 kuma anabasu assignments gakuma karatu dayakamata sunayi dashi”……..
Kallon ta yayi yana..
“sune sukace kizo ki tambayeni”…..
Cikin sauri tace…
“aa nifa banceba Yaya Imam”…..
Murmushi yayi sannan yace…
“komadai miyene kije kice musu inma suna tunanin kinkai wannan matsayin dahar zaki fadi abu inyine to baki kai ba,when I decide no one can change my mind”,yakarashe maganar tareda tashi daga zaunen dayake ah gabanta yanadan murmusawa kasa kasa yasan tana iya barkemai da kuka don ya lura shine abunda tafi kwarewa akai, sannan yakarasa bakin gado yazauna yana”and yes,kije dakinki kikwanta Asma’u bacci nikeji banason any disturbance please nace bazan basu ba and no one can change my mind”yakarashe maganar tareda kwanciya…..
Asma’u daranta yabaci takasayin shiru cikin karyayyar murya tace”basai ka nunamin I’m not that important to you ba nikaina najima da sanin hakan Yaya,tunda jimawa nasan I’m just an option,tunda jimawa nariga nasan relationship dinmu is just for a time being tunda you said it not even once but twice Yaya Imam,I know it already so,basai kafadamin ka sosa min zuciyata ba, basai ka fadamin ka tozartani ba,I already know that takarashe maganar tana kuka wannan karan don ta ma kasa holding tears nata………..
Goge kwallarta tashigayi because she really want to be strong sede takasa gani takeyima kaman yanzune ma aka bude ma hawayen pampo sudinga zubowa dakyar ta’iya tashi kafin takarada….
“nasan lokaci yayi dazamu rabu,may be ma in the next one week or two haka,i’m very sure za azoyimaka maganar anason hira dakai akan past dinka which is the only thing I’ve been waiting for Yaya Imam”,dan numfasawa tayi cikeda karfin hali kafin tacigaba da magana”please kayarda this’s one of the requests danake nema agurinka”,tayi maganar yayinda tayi folding hands dinta kafin takarada
“They’ll ask you about your past don’t hide anything,tell them about everything, infact we’ve concrete evidences that will help us expose that woman, Mallam Audu yasan maganar kaji sharri akayi maka lokacin hakanan maganar kudin me chemist Mallam Hudu yayi min magana kwanaki sede Aunty Muniba tace mubari tukunnan shiyasa ban tunkareka ba sekuma itakanta Aunty Muniba din zata bada shaida akan abunda yafaru da Galadima da jimawa sekuma Talatu uwa uba wanda banacire ran zata dawo kwana kusa inshallah wanda inada tabbacin itakadai zata warwaremana komai wanda zaisa asirin Magajiya yatonu harma da abunda tayima su Ummi abaya kaga by doing all that Magajiya will be behind boss and zargin mutane zai tafi,she’ll be punished for all her deeds you’ll be free Yaya Imam tayi maganar cikeda excitement a muryarta dukda idanunta nadauke da hawaye jage jage sa hijab dinta tayi tagoge hawayen dukda basu daina zuba ba sannan tacigaba”Ummi ma will be free,she’ll reunite with Abba and you all will live like a happy family”, lokaci daya kuma muryartata tacanza launi daga na excitement zuwana bakin ciki tana”and i….i will also be free from this relationship”,tunda I’m sure iyayena koyanzu sunfara gane gaskiya and they’ll accept me wholeheartedly without any suspicious kuma zansamu incigaba da karatuna wanda yana daya daga cikin manyan burikana arayuwa”,tsugunawa tayi daga tsayen datake sannan tace nasan duka kalaman da nafada will look like imagination to you but believe me it’ll surely come true when you cooperate nasan bantaba neman alfarma agurinka ba anma yanzu ganinan gwiwowina ah kasa inarokon ka kayarda ayi abunnan kowa ya huta,komi yawuce because this’s the best solution, I’m tired of staying in a place where I does not belong too and my second wish is dan zaman daya rage mana Yaya always smile for me because it gives me happiness ko ranka bayaso try and do that please! na lokaci kalilan ne and inkayi min wannan alfarmar i assure you my last days with you will be one of the best days of my life try and make it special please!karka fadamin maganar dazata sa zuciyana tayi kuna sabida ni mutum ce mai rauni zuciyata bazata iya kuma dauka ba”,takarashe maganar tana kuka mai tsuma zuciya sannan tafice zuwa dakinta Allah yagani yanzukam tagaji gwanda data fadamishi kawai ayita takare shine the best,yaushe zasu tsaya jiran Magajiya tatona ma kanta asiri bayan suna da evidence dazazu bayar,Itama tanason takoma gidansu,tanason cirema ranta son Almustapha hakanan tanason tacirema ranta yaudarar datajima tanayima kanta nacewa shidin zai iya zama nata watarana,yanda Asma’u taga dare haka taga rana don kusan kwana tayi tana kuka se wuraren ukun darene ma ta’iya yima kanta fada tayi alwala tatada sallah tana kaima Allah kukanta na ya cire mata son Almustapha aranta sede kamar ma abun karuwa yakeyi…………. 1

Bangaren Almustapha tunda take magana he was just so stunned,he regret his words betaba tunanin it’ll hurt her this way ba tunda shi harga Allah abunda ke ranshi yafada mata bayason a situation whereby nan gaba insunyi laifi ya hukunta su subiyo ta hannunta,she’s just so fragile tanada tausayi da sanyi bazaiso yafara biyemata ba yazo yana ‘bata kannenshi batareda ya ankara ba sede to his own surprise tajuye masa wayannan magan ganun dabaiyi tunanin jinsu awannan lokacinba,shima juye juyen yadingayi don gabadaya yakasa yin bacci daya rufe idanunsa crying face dinta yake kallo haka yakejin muryarta na kuka nayi masa yawo ah kwanyarsa wata zuciyar nason yaje yace mata he’s sorry sede egoistic one din yahana don gani yake yafadi inyaje yabata hakuri,gani yakeyi shibaiyi laifin komai ba abunda ke zuciyarshi yafada,then meyasa zaibada hakuri?………
Asma’u akan sallaya bayan tayi sallar asuba bacci yadauketa ba’ita tatashi ba se wuraren 8:30am haka,subhanallahi shine abunda tace ganin yanda hasken rana ya bullo tacikin dakin ta don labulayen ah bude suke……..
Kokarin tashi tayi dukda ciwon da kanta yakeyi mata sannnan tashige bandaki takalli mirror Allah yataimaketa fuskarta bata nuna alamun tayi kuka sosai ba wanke fuskar tayi kafin tawuce kitchen tundaga parlour takeji kamshi hadaddiyar miyan ganye…….
Murmushi tasaki kafin takarasa cikin kitchen din tana”Ummi sannu da aiki”…..
Ummi dake nan Helter skelter tana hada miya already harta gama toya masan tace”harkin tashi Habibty!”……
Cikeda kunya tace…
“Sorry Ummi bansamu nayi bacci dawuri ba shiyasa na makara” …
Dariya Ummi tayi tana”koma kiyi kwanciyar ki nama gama nikam,jeki huta abinki kinji Habibty”(niko nace su Ummi iyayen fassaara)………
Asma’u kuwa batagane abunda Ummi ke tunani ba don haka tace”Babu abunda zanyi ai Ummi,miyarki se kamshi takeyi tundaga daki nike juyowa”….
Dariya Ummi tayi”kice nacancanci aban tukwici”……
“Kwarai kuwa Ummi ae dukwanda yaci masar nan seyabaki inbahaka ba in ansake babu mai kaimasa”….
Lol lallai Habibty wannan kasawa da tsarewa haka amma dai ba’in fara dake,ke tukwicin mezaki bani Daughter”, Ummi tayi maganar tareda sauke tukunyar miyar don already yagamu…….

Asma’u tace..
“kifadi mekikeso Ummi”….
Lol anya zakiyi Habibty keda kikemin rowar ganin Umminki ma….
Cikeda damuwa Asma’u tace…
“kiyi hakuri Ummi bazanmiki rowartaba dadinma don kafarki begama warkewa bane shiyasa bamujeba”…….
Juyowa Ummi tayi tana sakar mata murmushi ganin yanda tadamu lokaci guda sannan tace…
“I’m just kidding, though daman zanyima Imam magana kan zamuje gida dake kema yakamata kije gida kigasu Ummi nasan kina kewarsu”……
Cikeda Jin dadi Asma’u tace”thank you Ummi”….

Murmushi Ummi tayi kafin tace gashi seku zuzzuba abincin ko nidai nagama nawa dukdama bakiga yanda nayiba but I’ll teach you next time …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page