GIDAN SARAUTA CHAPTER 7

GIDAN SARAUTA

CHAPTER 7
Ahaka harsuka isa bangaren Magajiya tun daga bakin kofa bayin keyi musu iso har suka shiga dakin da take……….. +

Kwance take kan makeken royal bed dinta yayinda hannunta se sanye da drip wanda yanzu na uku kenan da aka saka mata tsakanin jiya dayau sannan likitan yace ah tsanmaci yau zata iya tashi tunda akadawo da Magajiya bangarenta Talatu ke tareda ita bini bini dukda kuwa matar bata farfado ba……..
Koyanzu ma tanazaune gabanta ne ah kasa tana hawaye sosai take tausayin Uwargijiyartata jin anyi announcing shigowar su Almustapha ne yasata saurin tashi tana hawaye sannan tagaidasu tafice abunta kallo Asma’u tabita dashi na tausayi don daganinta dole kasan sunyi matukar shakuwa da Magajiya din zama sukayi ah kasa kan kaceme ancika su da kayan motsa baki………
Duban daya daga cikin bayin Asma’u tayi tace”yamai jikin?”…..
“Dasauki Gimbiya sede haryanzu bata farfadoba”…..
Allah yabata lafiya cewar Asma’u din kafin tadubi Almustapha dake gefenta yayi shiru hakanan bece komai ba kuma suna cikin haka Magajiya ta bude idanunta ahankali tana karema saman dakin kallo tanason tuno maiya faru hakanan tanason sanin inda take yanzu………..

Lokaci guda kuma kwakwalwarta ketuno mata kalaman Sama’ila”Almustapha yayi aure,ya auri wancan yarinyar”, bugun zuciyarta ne yakaru gawani kaikayi da takejin jikinta nayi sosawa takesonyi amma gabadaya jikinta babu kwari daya daga cikin baiwar ne takarasa gabanta cikeda damuwa tace”sannu,Ina keyi miki ciwo ko inkira likitan ne?”……
Kallonta kawai Magajiya keyi don ita haushin yarinyar ma takeji wai ace yau itane abun ayima sannu ma ganin taki takulata sekawai yarinyar tace kinama da baki takarashe maganar tareda nuna direction din da su Almustapha suke kallon wurin Magajiya tayi jiki ba kwari……
Ware idanu tayi cikin sauri hakanan bakinta na karkarwa tana son yin magana amma yakasa fitowa tsabagen shock Asma’u dake kallonta tadan ji tausayin matar seta sakar mata murmushi tareda tashi zataje wurinta don ganin yanda hankalinta yatashi lokaci guda may be she can compose her……
Jitayi anriko hannunta cikin sauri juyowa tayi tana kallonshi cikeda mamaki tashi yayi tsaye still hannunta na cikin nashi sannan yajuya yafara tafiya……
“Let me go,ba dubata mukazo yiba kabari ingaida ta mana”kin sakinta yayi sema janta dayacigaba dayi…..
Ganin tana shirin janyo mishi jama’a yasashi samun wani lungu yaturata”kabarni nikam inacewa Abba yayi muje mudubata”….
Matseta yayi jikin bango tareda daura hannunshi kan bakinta”kimin shiru!”….
Yayin maganar cikin husky voice dinshi,aikuwa lokaci guda tayi shirun tana kallon yanda idanunshi yasauya kala lokaci guda don kuwa haushinta yakeji miyasa zata damu harta tada hankalinta akan Magajiya ina tasanta,she knows how cruel she’s tunda Dad yabata labari then “why is she doing all this?”…..
Nayi Allah,bazan sake maganaba tayi maganar ahankali……
Sakinta yayi tareda dan ja baya, ajiyar zuciya tasauke tareda barin gurin cikin sauri shima bayanta yabi suka koma bangarensu…..
Magajiya kuwa ganin abunda Almustaphan yayi jitake kamar zuciyar ta tayi boasting “what’s going on in this palace,mezata gani Almustapha nefa well dressed cikin kayan sarauta ga yarinyar da aka Kira da matarshi ma hankalinta kwance”……..
Lumshe idanunta tayi wani irin kututun bakin ciki marar misaltuwa ya ziyarci zuciyar ta. …..
Aranta tadinga fadin’i can’t let this happen,basu isaba wallahi babu wanda ya’isa yaja dani”….
Wayannan wune abubuwan data dinga rayama zuciyarta kenan………..

****
Cikin sati guda jikin Magajiya babu laifi don kuwa tasamu sauki sosai tunda har tanadan samu tafita tayi normal abubuwanta dukda bakaman da ba sede wannan kaikayin jikin bebarta ba haryanzu kuma Mai Martaba ya yafe mata yace takoma normal life dinta sede bayason takuma yimashi mistake din datayi tunda yanzu tabarshi da asara dole shine zai sake neman wani kudin ya bayar ayi aikin dashi……….

STORY CONTINUES BELOW


Cewa tayi to kawai don kuwa cikin ranta Allah kadai yasan abunda take kintsawa………

Mallam Audu kuwa tuni Hajiya Muniba tasake shi ganin yanzu Magajiya ta tsaida maganar nemanshi tunda ma abun gabanta sun isheta, she’s just waiting for the right time to expose Magajiya……..

Bangaren Asma’u kuwa tun ranar takoma asalin dakinta bayan Almustapha yabata keys she’s now living a new life with new people batada wani goal daya wuce ta farantawa Ummi dakuma ahalin Almustapha baki daya,tamayar da cinsu da shansu aikinta don kuwa bata yarda akawo musu abinci daga kitchen din masarautar ita takesa ayimusu under her guidance wanda hakan yasake janyo mata so daga surkanan nata bangaren Ummi kuwa kullum seta fitar da ita dayanma sunje garden kaman da she enjoy spending time with her tana kallonta amatsayin mahaifiyarta hakanan amatsayin companion jiyama Sulaiman kecemata Malamin dazaizo ganin Ummi yace ranar asabar zezo yadawo daga tafiyar dayayi…
Bakaramin dadin wannan labarin tajiba donkuwa tanason sanin matsalar Ummin tanason taga ranarda Ummi zata budi baki tayi magana hakanan tanason ganin ranar da zata tashi da kafafunta tayi tafiya kamar yanda kowa yakeyi………….

****
Wuraren ukun dare tafarka yau jawo wayanta tayi ahankali sannan tashiga kiranshi as usual yanda takeyi kullum……….
Ringing yayita yi bedauka ba massage tayi mashi da ..

_”katashi kayi ibada Yaya_ _Almustapha,kakai kukanka gurin ubangiji”_

Turawa tayi sannan tacigaba da kiiran nashi babu kakkautawa daga karshe ma kashe wayar yayi yar murmushi tasaki don ita daman hakan takeso because dataji ya kashe wayar hakan na tabbatar mata da idanun shi biyu kenan muddin yatashi kuma zuciyarta tariga ta amince dashi tasan zaiyi abunda tace din…….
Tsaki yabuga jin tafara kiran nashi kaman wani kayan maita dakyar ya iya bude idanunshi ya karanta massage din nata besan miyasa tun ranar datafara kwana dakin ta take mishi thesame thing dukda kuwa betaba yimata reply ba kullum sede yagaji da jin kiran nata yakashe wayar inkuma yakoma zeyi bacci seyaji yakasa yin bacci,seya tsinci kanshi da tashi yanayin abunda tafada mishi din……

Hakanan kuma kwanan nan yakejin shi wani daban,hakanan yakejin wani kwanciyar hankali Kuma yakejin kaman anasauke mishi wasu abubuwa masu nauyi ah zuciyarshi tabbas ya yarda babu abunda yafi ibada sa kwanciyar hankali dakuma kwantar da zuciya dakuma saka bawa yarda da cewa babu kaman Allah and he’ll always stand by you no matter what………
Yanzu ma baikoma baccin ba haka yatashi yadauro alwala yatada sallah bashi ya tashiba daga kan sallaya seda yaji ana kiran sallar asubahi nan yafara shirin tafiya masallaci kuma……

Seda yabi ya bubbuga masu Amira kofa as usual sede Afiya ne taiya cewa muntashi Yaya,daganan yawuce masallaci abunshi koda yadawo kofar still arufe take hakanan kuma yanada tabbacin basuyi sallar ba haryanzu bubbugawa yashigayi ranshi bace yafi 3minutes yana buga kofar kafin Amira tazo tabude wani irin harara yabita dashi wanda yasa duk baccin dake idanunta suka wartsake lokaci guda”kunyi sallah?”……..

Cikeda tsoro tace yanzu zamuyi Yaya,tureta yayi tareda karasawa cikin dakin yana kallon Afiya dake kwance tana shatata bacci haryanzu”Afiya!”yakira sunanta cikin wani irin tsawa jikina bari tatashi zaune dabas akan gadon”bakiyi sallah bako?”…..
Kame kame tafarayi…..

Ranshi bace yace”yaushe kuka fara wasa da sallah akan lokaci,when?”,yayi musu tambayar cikin tsawa don kuwa shidai yasani ko ah rayuwar talaucin su suna sallah kan lokaci abu dayane baswayi shine zama suyi addu’a kokuma yin nafifilu amma kwata kwata yanzun sun canza…….

Batambayar ku nakeyi ba?……
Muryar Afiya na stammering batasan sanda tace”bamu kwanta dawuri baneba?”……

Karasawa yayi gaban gadon yayi…
“meya hanaku yin baccin dawuri,danne dannen waya ko, social media ke destracting naku this days ko?”……

STORY CONTINUES BELOW


Girgiza kai Amira tayi alamun a’a,cikeda bacin rai yace where are your phones?…….
Hakuri suka shiga bashi cikin tsawa yace ba magana nake muku ba?….
Haka suka kawo wayoyin suka bashi jiki ah sanyaye duk tsoron shi yagama shigansu karba yayi sannan yace and the laptops?……
Kallonshi Amira tayi don da tayi tunanin laptop dinta will survive inma wayar batanan atleast zatasamu na kallo…
“Kayi hakuri Yaya”,cewar Amira Afiya ne tace”please”………

Batareda ya kalli inda suke ba yakarasa gefen gadon inda yaga laptops din na ajiye daya ansaka shi ah chargi haka yacire ah charging yahada dayan yayi hanyar barin dakin ah bakin kofa yaganta tsaye dauke kanshi yayi yafice daga dakin rabonshi da ita almost three days now dukdama koya gantan ba magana sukeyima junaba daman……..

Shiga dakin tayi tasamu guri tazauna tana ganinsu kowa rai jagule suka shige bandaki sukayo alwala sukazo sukayi sallah………
Seda suka idar sannan tace”I’m sorry on his behalf dukda ma kuma kunada laifi”…….

Dagowa Afiya tayi tana kallonta tace”miye laifin mu Sis,muma bayin kanmu baneba nikaina bansan miyasa nike makara sallar asuba yanzuba”……
Murmushi Asma’u tayi sannan tataso daga inda take tadawo gabansu tazauna”sanda kuke rayuwan da karfe nawa kuke bacci Amira?”…….

Dan shiru Amira tayi tana tunani sannan tace wataran taran dare wataran kuma goma that’s if bamu kwanta dawuri ba……
Yanzufa, Asma’u tasakeyimusu tambayar tana kallonsu…..
Wannan karan Afiya ce tace”inmunyi bacci dawuri 12:00am don wataran nakan Kai 3:00am Ina kallo ah laptop kafin na kwanta” .. ……
“Do you now see the difference”, Asma’u tayi musu tambayar tana Smilling.. ..
Nidai bangane ba Sis Amira tayi maganar tana kallon Yar uwarta kafin Afiyan tace nimadai bangane metake nufiba………….

Kamo hannunsu tayi su duka biyun sannan tace kuyi hakuri in abunda xan fada zai bata muku rai but atleast I feel it’s right to remind you people inajinku kaman yan uwana na jinine wallahi…….
Cikin sauri Amira tace”shhh don Allah kifadi abunda yake ranki we’re now families,in mu ba yan uwa bane ada yanzu Yaya Almustapha yayi strengthening bond dinmu”……….
Nagode da fahimtata dakikayi Amira,ni anawa ganin rashin baccin ku dawuri ne yake hanaku tashi sallar asuba tunda ada kunayi din bawai bakwayiba sannan inaganin yakamata kurage kallon nan sabida bashine gabanku ba you two have alot of things dayafi kallon nan besides what will you gain by doing that?……
Inma chats kukeyi mezakuyi gaining ayin chat din,nibance karkuyi chat ba hakanan bance kada kuyi kallo ba tunda nima inayi sede you people have to use your time wisely abunda nake nufi anan shine indai kallo zaiyi destracting naku daga addinin ku to miye anfaninshi?……
Set your time wisely,kowani aspect na life dinku kubashi time dinshi daban yakamata ace ibadan ku yakaru ne bawai yaraguba dubada halin da kuke ciki dakuma halin da Ummi take ciki, she’s so sick yakamata kunayi mata addu’a ne,yakamata kudinga addu’a Allah yasa hankalinta mahaifin ku yadawo kan mahaifiyarku, Allah kuma yasa asirin wanda yacuce ku yatonu,I think this’s what you people have to focus on sede nalura ku abunda yazama muku dole kukeyi we’ve to change please tayi maganar tana hawaye…….
Cikin sauri Afiya take kuka ta rungumeta tace”mungode da shawarar ki Asma’u in Sha Allah zamu gyara,sede kisani bawai munada ilimin addinin sosai bane muntaso cikin wahala tabbas ansaka mu ah islamiyar sede babu wanda yadamu da munje ne ko bamujeba,inmunje dinma wataran koromu akeyi muzo muyi aiki daga boko har islamiyar sanin damukayi din kadan kadan ne Asma’u sannan munfi bada kwari gurin bokon don ah tunanin mu shine zai taimakemu har muzama wani abu daban ah rayuwa mutaimaki Ummin mu,babu maice mana abunda mukeyidin badaidai bane,babu kuma wanda yadauramu akan hanya besides wama mukedashi? Afiya tayi maganar tana goge kwallart sannan takara da shi wanda mukedashi din shima bawai yanada lokacin mu sosai bane sannan koyi muke dashi don abunda yayi shi mukeyi Kuma shima kada kiga laifinsa yatashi cikin rashin gata,yakuma tashi cikin kuncin rayuwa Wanda yasashi manta menene daidai dakuma wanda badaidaiba,abubuwa sunyima kwakwalwar sa yawa sake damke hannun Asma’u Afiya tayi”Yaya Almustapha yanada sanin addini sabida tunyana karami yayi sauka hakanan yakaranta litattafai dadama at his young age ayanda naji,kawai kuncin rayuwa dakuma rashin sanin yakamata ne yamaida shi haka and he was so young to know what was right and wrong harma yafada ma wasu shiyasa yatashi ahaka,ajiyar zuciya takumayi but now Yaya is getting what he deserve,yadawo cikin daular mulki sede baya cikin farin ciki he need some love,he need to be happy and only you can bring happiness to his life Sis,I trust you”……..

STORY CONTINUES BELOW


Tapping bayan Afiyan Asma’u tashigayi cikeda tausayawa tace”I’ll make him happy Afiya, I’ll make him the happiest man on Earth I promise takarashe maganar Itama tana hawaye me tsuma zuciya,sede inason kuma kuyimin alkawari zaku gyara halayenku sannan zaku nemi ilimin addinin ku sabida shi ilima bakana zaune ne zaisamoka ba kaine zaka fita ka nema….

Insha Allah suka amsa mata atare sannan Amira tace zamuyima Yaya Sulaiman magana yanema mana Malami Yana zuwa gida yana mana karatu kawai,kuma yanema mana Islamiya…….
Murmushi Asma’u tayi”zannema muku Malami wanda xenayi muku karatu agida inyaso Yaya Sulaiman din seya sama muku islamiyan”……
Godiya suka shiga yimata cikeda jin dadi kafin tafita tawuce kitchen don gari yayi haske already tasan su Hindatu sunfara aiki…………
****
Tare suka fito daga bangaren Magajiya babu laifi yaudin tadan sakarmai fuska tunda harta ta’iya ta ansa gaisuwar sa duban Zaliha yayi sannan yace”zanje gun Yaya Almustapha i heard that result dinsu is out inason infada mishi”….
“To Allah yakiyaye”.
Da Amin ya amsa mata haryajuya zaiwuce sekuma yadawo sannan yace
“ke atunanin ki kinkyauta?”……

Cikeda tsiwa tace”danayi meye kuma Yarima”…..
riko hannunta yayi batareda yadamu da mutanen dake kallon su ba yace”fisabilillahi Zaliha tunda aka kawo Asma’u ko inda take baki nema ba bare kiso kuyi zumunci yanzu ke aganin ki yadace”…
Wabce hannunta tayi cikin sauri”aa Mallam dakata kada ma kafara,nida ita waye babba naji dai ance sa’ar su Afiya ne ahakan Kuma kake expecting dina ni innemi inda take……
Kallonta yayi da mamaki “Zaliha you’re too much wallahi kuma ma inkina takama da girma ne to Itama ai mijinta ya girmeki kuma Yayana ne so you’ve to give her that respect”…
Kai tsaye tace”I can’t inbazata iya zuwa inda nakeba kowa yayi takanshi is not as if dole semunyi zumunci tunda daman bada ita aka kawoni ba besides I don’t like her tunda Matar Yayanka ce”,tana karashe maganar tajuya tatafi tabarshi tsaye sororo yana binta da kallo besan yazaiyi da Zaliha tagane cewa he’s not meant to be the king ba yakamata tayi putting this at the back of her mind sede takasa shikuma bayason suna samun matsala………….

Karasawa yayi bangaren su Almustapha din dakin Ummi yafara zuwa yaduba jikinta sannan yadawo parlour yazauna don yanzu ba kasafai yake shiga dakin Almustapha dinba tunda he’s married yana nan zaune harya fito cikin shirin shi na kananan kaya don yau babu inda zaije yasama ranshi ko fada bazai leka ba………
Murmushi Sulaiman yasakar mai sannan yagaida shi”Ina kwana Yaya?”…..
Lafiya Lau and you?….
Alhamdulillah,samun guri Almustaphan yayi yazauna tareda dan lumshe idanunshi tunda ta doso hanyar parlourn yakejin daddadan kamshin turarenta harta karaso sa bayin tayi suka ajiye abincin sannan tagaisa da Sulaiman din……….
Amsawa yayi fuskarshi cikeda annuri yana”Uwargidana na fushi wai kinki zuwa ayi zumunci”….
Murmushi kawai Asma’u tayi “tayi hakuri zanzoni in Allah ya yarda”,cewar Asma’u dukda kuwa tana mamakin wacece haka,ae itane bakuwa kamata yayi ita tafara zuwa gurinta bawae tace ita taje ba sede koma miye ne she’ll go for the sake of Sulaiman…….
Haka takoma dakin don barinsu suyi breakfast donta lura kozata yi yaya Almustapha bazai taba cin abinci ah gabanta ba kam………….

Seda suka gama cin abincin sannan Sulaiman yace”result dinku is out Yaya”….
Yanda Sulaiman yayi masa maganar ah bazata seda yaji kirjinshi ya buga kafin dakyar ya iya cewa Allah yasa muji alkhairi……..
Amin cewar Sulaiman din sannan yace…..

“your ID number zanje induba maka don nasan ba lallai kasamu fita ba”……

Bashi Almustapha yayi ganin yanda jikinshi yayi sanyi yasa Sulaiman din dan tapping shoulder dinshi sannan yace calm down ynzu zan duba maka so far as you wrote the exams nasan you’ll surely pass dayardar Allah……..
Allah yasa cewar Almustapha din sannan yatashi yakoma daki yakwanta gabadaya jiyayi duniyar ta mishi zafi bayason ace abunda yake faruwa dashi every year yafaru dashi yanzuma……..
Daukar wayarshi yayi yakunna data abunda yakwana biyu beyi ba kenan nan yashiga WhatsApp kozai samu wani information daga group massages ne suka shiga shigo mishi ganin number dinta yayi asama alamar yanzu taturo massage din……….

STORY CONTINUES BELOW


Mamaki ne yakama na massage din meyene zata turo mishi yanzu bayan bata dade da barin gurin shiba bude wa yayi picture ne yagani dauke da massage akasa wanda yadauki hankalinshi lokaci guda……..
Karantawa yashiga yi batareda yyi viewing picture dinba dukda kuwa yayi downloading akready…..

_You have not only created a niche for yourself at your young age…._

_But you have also inspired many Young people to dream big,_

_Your achievement will surely be a motivation for all the young people around you So, super congrats “My Doctor” I am so very proud of you_…..

Yakaranta massage din yafi sau hudu kafin ahankali yabude result din clear pass yagani,sosa idanunshi yayi because he really can’t believe it amma still thesame thing yake gani sake duba ID number da sunanshi yayi shima nashi ne lumshe idanunshi yayi tareda fadin”Alhamdulillah fa, Alhamdulillah, Alhamdulillah fa”, Allah ne kadai yasan irin farin cikin dayake ciki……..
Dakyar ya iya sake duban wayan seya tsinci kanshi dasake karanta sakon nata besan sanda murmushi yasubuce maiba tareda yi mata reply azuciyarshi Yana”she’s so cunning,tama rainashi shinema yaro wato”…..
Yaga massage dinta na kwanaki seyayi ignoring tunda ae tasan shine yanzun ba Sulaiman din bane ba …

” _waya yaron?_”

Shine sakon daya tura mata tana zaune ah parlour itadai Sulaiman taga massage din nashi dan bata rai tayi tareda wurgar da wayar wato ma of all this write-up that’s what she’ll get in return”Arrogant Dr taciturn”,shine abunda tafurta tana bata rai…….
Sulaiman ne yadubeta jin kaman tayi magana”lafiya?”…..

Bakomai tayi maganar rai bace,dariya yayi sannan yace “kukuma naku salon soyayyar kenan?”…..
Sarai taji meyace amma setayi kaman batajiba”uhmm mekace?”………

Yasan taji don haka shima seya kawar da maganar tahanyar cewa “yaga massage dinne ko inje infada masa kada yayita tada hankalinsa?”…..

Yagani mana aishiyasa naketa bata rai,waifa ma ko godiya baiyimin ba takarashe maganar tana mikama sulaiman wayar yaga reply din Almustaphan dariya yayi daganin massage din sannan yace”kunfi kusa wallahi nikinga tafiyata zanje infada ma su Dad”……
Seka dawo tabashi amsa tareda tashi tana kunkuni ita kadai harta fice zuwa bangaren Mom………

*Around 9:30pm*…

Seda tagama wankanta tsaf tayi shirinta cikin kayan bacci riga da wando sannan tafeshe jikinta da turare harzata kwanta setaga yakamata tayima Almustapha maganar karatu datayi niyar yi kan yanayimusu atleast it’ll help him retain his memory Kuma shima yasamu lada tunda tanada sani inma yayi mistake seta gyara mishi dawannan tunanin tasaka soft flat shoe dinta datake yawo dashi cikin gida tafice……..
Straight dakinshi tawuce knocking tayi tayi be amasaba dan tabe baki tayi “Yana ma ji ze iya kin ansa mini”,takarashe maganar tareda murda handle din kofar tayi Allah yataimaketa abude kofar take shiga dakin tayi yayinda lallausar kamshin dakinshi yaziyarci hancinta ga sanyin AC ya mamaye koina karema dakin kallo tashigayi ganin baya ciki tarasa Almustapha wani irin namiji ne haka,sabida itadai bata taba ganin namiji mai tsaftarsa ba gashi kominshi anutse yakeyinshi tana cikin wannan tunanin ne taji yabude kofar bandakin don haka tamaida direction dinta gareshi wani irin kara tasaki tareda juyawa lokaci guda zuciyarta na racing shima saurin juyawa yayi sanda yaganta gabanshi sabida tunda yake betaba tsayuwa gaban wata hakaba hartasamu taga jikinshi……….
Bangaren Asma’u ma kasa taka kafanta tayi itadai tana sankare guri guda yayinda yanda taga kyakyawan jikinshi keyi mata yawo ah kwanya gawasu kwantaccen gashi dake shimfide ah kirjinshi wanda suka kasa vanishing ah idanunta……
Sa hannu tayi tarufe fuskarta cikin sauri don gani take kaman zegane abubuwan dake yawo ah kwanyarta da kwakwalwar ta jitake kaman kasa ta tsage ta shige ciki………
Jin bata bude kofar dakin ba seya juyo kawai gani yayi tana tsaye agurin still jijjiga kai yayi cikeda mamaki sannan ya tabe bakinshi yayi wucewarshi jikin wordrop dinshi don yanada tabbacin bazata taba juyowa ba ahaka harya gama shirin shi,harya hau gado zekwanta seya tuna bai kashe wutan dakin ba don haka yaje yakashe yadawo yayi kwanciyar sa tareda lullubuwa cikin blanket batareda yadamu da existence dinta agurin ba……….

STORY CONTINUES BELOW


Tanajin sanda yakashe wutan setayi saurin cire hannunta ah fuskarta amma babu abunda take gani se duhu ah dakin don har bedside lamp dinma yakashe daya koma………
Kici kicin neman kofa tashigayi kuma don tasamu tafita daga dakin amma takasa samun direction dukda kuwa tana mamakin bawai nesa tayi da kofar ba to ya akayi haka batayi giving up ba haka tacigaba da lalume amma setaji ta bugu da wani abu da karfi Yar kara tasaki don ba karamin buguwa tayiba akafarta tareda zamewa tazauna agurin tana taba kafar sekuma tasaki kuka…….
Yana jinta amma seyaki kulata dukda bason jin kukan nata yakeyiba……
Cikin kuka tace…
“Yaya Almustapha bakaji naji ciwo bane?”,yanda tayi maganar harcikin kwakwalwar shi yaji sabida yanda tayi maganar ashagwaba amma seyayi kaman baijiba…….

Sautin kukan takara”naji ciwo fa! gashi gurin duk duhu nikam kazo ka kunna min wuta to……
Yar dariya yayi kasa kasa yanda bazata jiba jin yanda take maganan,kara marairaice murya tayi”don Allah mana nasan kanajina wallahi tayi maganar murya akarye”……..

Gyara kwanciyanshi yayi yanadan smilling dukda tabashi tausayi aranshi yana”yarinya dani kikewasa”,sannan afili yace..
“meya kawoki dakina?”…..
Cikin sauri tace…
“Allah nazo in maka magana ne kanamana karin karatu da asuba,amma nafasa ma nidai ka kunna min wuta intafi dakina”…….

“Bakince ni yaro bane kinemi Babba yataimake ki,har inmiki magana kikimin reply?”yakarashe maganar tareda lumshe idanun shi…..
Turo baki tayi kaman yana kallonta”Ina kaine kakiyimin godiya”…..

Shiru yayi kaman baijitaba itakuwa tacigaba da sharara kuka jin ta dameshine yace in a serious tune”Allah kika sake baremin baki I’ll throw out,I want to sleep for goodness sake besides nibankawo ki dakina ba so,find your way out”……
Tanajin wani sabon kukan nashirin zuwa tayi saurin sa hannu tarufe bakinta tasan Almustapha ze iya abunda yafada din haka tadinga kukan zuci har bacci yayi awun gaba da’ita akan tiles ….
Seda yadaina jin kukan nata sannan yasamu bacci yadaukeshi sede da mamakinshi yau dede time din datasaba tashin shi yatashi shima batareda yaji kirantaba……….

Da hasken wayarshi ya yi using don mugunta yayo alwala yazo ya tada sallah bashi yatashi ba seda yaji ana kiran sallar asuba kunna wutan dakin yayi tareda kallon direction din da take kwance gabadaya ta dukun kune guri daya kamar marainiya ga baccin wahala datakeyi samun kanshi yayi da daukan pillow da blanket yakarasa gabanta tsugunawa yayi yadan daga kanta yasaka pillow din tareda rufa mata blanket din sannan yatashi cikin sauri yafice jin ana shirin shiga sallah……..

Koda yadawo baccinta take peacefully wannan karan lallai ma yarinyar nan shine abunda yafada sannan yakarasa gaban gadonshi yadauko glass cup da ruwa aciki yadawo gabanta diban kadan yayi yadan yayyafa mata motsi tayi kadan ganin tana shirin komawa baccin ne yasashi sake yayyafa mata ruwan wannan karan cikin sauri tatashi tazauna komawa yayi ya ajiye cup din sannan yafice daga dakin zuwa dakin Ummi…..
Binshi tayi da kallo harya fita daga dakin sannan tamaida hankalinta kan wall clock din subhanallahi shine abunda ta furta ganin har 5:40am yayi cikin sauri ta yaye bargon dukda tana mamakin waye ya lulluba mata jinda tayi kafarta tayi wani irin zafi ne yasata saurin komawa tazauna sega hawaye kuma zululu,dakyar ta’iya daurewa tamike tana”itakam Allah yahadata da mutum”……..
Dakinta tawuce tayi sallah abunta sannan takoma takwanta don yaukam bacci be isheta ba koda su Hindatu basu ganta ah kitchen ba sunsan kilan bata tashi baneba don haka sukayi girkin dakansu tunda tayi time table na abinci already daman……….

Su Afiya ma anfara tashi dawuri don kuwa sundauki shawarar Asma’u din sannan tun jiya sukayima Sulaiman maganar Islamiyar su yace in sha inyasamu time zekaisu ayi masu interview awata islamiya dake kusa dasu………..

****
Yau kin gyaramishi daki tayi kwata kwata sabida fushin da takeyi dashi har azahar hakan yasa shima yagyara dakanshi batareda yaneme taba tunda koda dinma bashi yasakata ba ita tasaka kanta daman……
Sosai Dad da Abba sukayi mishi murna na kyaun da result dinshi yayi sannan Abba yac he should expect his gift soon……..
Ranar wuni yayi cikin farin ciki don kowa tayashi murna yakeyi cikin yan uwan nasa dakuma iyaye baki daya har hawaye yayi dayaje gaban Ummi inama inama,inama zata iya magana he know for sure she’ll be more than happy to hear this news, she’ll be the first person to hug him and congratulate him………..

Washegari da asuba Asma’u tasha mamaki dataga Almustapha nayima su Afiya karin karatu sede taji dadi bakadan ba aranta dukda tana mamakin ya akayi ya yarda dabadan fushi take dashiba babu abunda zai hanata jonawa sede dukda haka batabar gurin ba don samun wani spot tayi tazauna tanajin yanda yake karatu cikin kira’arshi me dan karen dadi har yagama sannan ta lallaba tagudu don kada ma yaganta yafada mata ba dadi………

******

Tana sanye cikin wata atamfa hadaddiya data amshi jikinta se katuwar gyale data yafa hnyar bangaren Zaliha tayi don zuwa sugaisa tunda tace setaje mata sannan ita tazo tundaga nesa take hango yanda bayi suka taru guri daya da alama wani abu ke faruwa suka tsaya kallo……….
Duban bayinta biyu dake binta abaya tayi”hafsat meyake faruwa acan?”……..

Sunkuyar dakai yarinyar da aka kirada hafsat tayi sannan tace”bansaniba wallahi Gimbiya amma barina duba”,cikin sauri Asma’u tace no need zanje dakaina takarashe maganar tareda yin gaba wurin suka Isa inda bayin suka shiga bata hanya harta Isa ta gaba gaba…..

Magajiya ce ke dungurin Talatu tana”don ubanki banace kifita harkataba,ko anfada miki ana dolene?”…….

“Nace miki banason kara cudanya dake miyasa bazaki gane hakan ba, you’re a betrayer kin cuceni Kuma kinason in karbe ki don ubanki, Magajiya takarashe maganar tareda kaiwa Talatu Mari wannan Karan”innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma’u ke furtawa don tayi mamakin yanda matar ke bugun mace da tayi kusan sa’arta wannan wane irin wulakanci ne haka besides if she could remember kaman itace ke tareda Magajiyar lokacin da bata da lafiya she was very worried for her and now itakuma tahaka zatayi repaying dinta tana wannan tunanin ne taji Talatun na”Uwargijiyata wallahi babu abunda nayi akomai ina bayanki,bantaba cutarki ba hakanan bantaba yimaki karyaba kiyarda dani please takarashe maganar tana hawaye tareda foldung hannunta alamun roko”.
Takaici ne ya ishi Magajiya azuciye tayi ball da Talatun tana”Zan hallaka ki inbaki bace min da ganiba”,still Talatu bata daddara ba ball da’ita Magajiya tashigayi tana huci cikin sauri Asma’u ta’isa wurin tareda shiga gaban Magajiyar da har take shirin ball da ita Itama cikin kuka tace”kibari don Allah,haba sekace wanda kika samu dabba, she’s busy pleading with you amma ko ajikin ki sekace wanda bakida zuciyar imani Asma’u takarashe maganar tana hawaye………..

Magajiya ta saki baki tana kallonta donkuwa waye ya isa yayi interrupting dinta intana abu lallai Matar Almustapha taga gadon baccinta,lallai taganta amatsayin marar lafiya ne ba a matsayin magajiyarta ba, lallai batasan wacece itaba don taga tayi musu shiru tunda tazo gidan batace komaiba azuciye tace “who do you think you’re dazaki shiga gabana inama slave dina hukunci?”…
Cikin kuka Asma’u tace”kiyi hakuri don Allah kibarta hakanan,she can be your slave but she’s also a human being like you bekamata kina treating dinta kamar dabba ba”…..
Wani irin kukan zaki Magajiya tayi kafin tadaga hannu daniyar kaima Asma’u mari cikin sauri taji anriko hannunta daga ita har Asma’un juyawa sukayi don ganin wanene wannan cikin husky voice dinshi yace…
“Don’t you dare touch my wife!”….
Wani irin huci Magajiya tayi tana shirin kwatar hannunta amma yaki saki wani irin kallo yakeyimata dayasata rikicewa lokaci guda Asma’u kuwa dasauri tayi kan Talatu tana riko hannunta”sannu baiwar Allah”….Dukda kukan da Talatu takeyi behanata dagowa don ganin wanene yazo ceton ta ba arba tayi da kyakyawar fuskar Asma’u mika mata hannu Asma’un tayi tana”kitashi kinji,sannu”…… +

Batasan dalili ba seta kasa rejecting offer din dukda kuwa yanda take tsoron Magajiya din haka Asma’u takama hannunta sukayi bangarensu…………

Bangaren Almustapha kuwa seda yaga Magajiya tarage hucin da take sannan yasaki hannunta yana kara jaddada mata”babuke babu family na stop messing around with us”,yakarashe maganar yana nunata da yatsa cikin sauri tayo gaba tana neman shakareshi amma tuni ya juya yatafi yabarta da takaici jitake kaman tadora hannu aka ta fasa ihu cikin gurnani tace”Don ubanka da ni kake wasa Almustapha, harni zaka fadama magana akan wata filthy Matarka I’ll make sure you regret this”, Almustapha kuwa yiyayi kaman baima jitaba harya Isa bangarensu……

Tana nan tsaye tanata fadan maganganu kamar wata me tabin hankali harta gaji juyawa tayi taga bayin suna kallonta wani irin tsawa tamusu”meyekuke kallo,ni kuke kallo don baku da hankali” takarashe maganar tana nuna kanta da yatsa cikin sauri kowa ta juya takoma bakin aikinta cikeda tsoron Magajiyan Itama bangaren ta takoma tanata huci itakadai…………

Tafi minti talatin ahaka kafin daga karshe takira daya daga cikin bayinta tace anemo mata Laure,cikin sauri yarinyar tafita don zuwa takirata ba ajimaba kuwa segasu sundawo…..
Zubewa Laure tayi gaban Magajiya tareda mika gaisuwa dukda kuwa yanda zuciyarta ke bugu don gani take kaman ankamata da laifine(kunsan mutum marar gaskiyar)…….
Kare mata kallo Magajiya tayi”kedin miyene kike abu kamar wata munafuka?”……
Wallahi babu Uwargijiyata cewar Lauren muryarta na stammering………

Dan sosa jiki Magajiya tayi tareda gyara zama sannan tace”dago ki kalleni daman nakiraki ne infada miki daga yau kezakinamin duk wasu aikace aikacena na kusa dani sabida bayan Talatu babu wanda nayarda da irinki Itama kuma kinga ta yaudareni”…..
Kiyi hakuri cewar Lauren…….
Harara Magajiya takaimata tana”bawai hakuriba kika yarda kika cuceni gunduwa gunduwa zanyi dake infada miki”…….
Gyada kai Laure tayi cikeda tsoro don itakam yanda tasamu Hajiya Muniba batason ace tacuceta, sallamanta Magajiya tayi sannan tatashi cikin sauri tafice bata tsaya koina ba se bangaren Hajiya Muniba zama tayi gabanta tana gaisheta lura da yanayinta Hajiya Muniba tayi sannan tace lafiya laure,meke damunki naganki duk ah birkice?……………
Cikeda tsoro laure tace ranki shi dade inacikin hali mai wuya wallahi….
Fadamin meke damunki yata Hajiya Muniba tayi maganar cikeda damuwa….
Nan Laure takwashe mata yanda sukayi da Magajiya sannan tasaki kuka tana wallahi ni banason inzama baiwar ta ninasan Matar nan nakuma san halinta bakiga abunda tayima Talatu ba yau Rankishi dade kuma wallahi babu wanda ya’isa yaje yafada ma Mai Martaba wannan zancen…………
Cikeda tausayawa Hajiya Muniba tace….
“kiyi hakuri Laure insha Allah babu abunda ta’isa tayimiki I’m with you kuma wannan wani chance ne muka samu na bayyana wannan matar kikwantar da hankalinki kada kibari tama gane you’re not loyal to her”,dagowa Laure tayi tana kallon Hajiya Muniban murmushi tasakar mata tareda kara bata kwarin gwiwa kafin sukayi sallama…………….

*
Adakinta ta taimakama Talatun tazauna batareda taji kyamartaba koda kuwa kadan ne sa Salma tayi takawo ruwa ah kofi kafin tazauna gefenta tana”baiwar Allah ga ruwa Kisha”……

Girgiza kai Talatu tayi alamun takoshi Asma’u bata takura mata ba ta ajiye ruwan gefenta dede lokacin Jamila baiwar Ummi tashigo zare idanu tayi ganin Talatun…….
Asma’u ne tace iya Jamila kikaraso mana…..
Dan jijjiga kai tayi sannan tace…
“bazama nazoyiba Gimbiya daman Yarima ne yace inkiraki”……
Tashi Asma’u tayi tafice don zuwa gun Almustapha din tareda murtuke fuska don haryanzu batasauko daga fushin da takeyiba….

STORY CONTINUES BELOW


Jamila kuwa karasawa tayi cikin dakin tana hararan Talatu”kekuma hatsabibiya dame kikazo kuma yanzun?….

Cikin kuka Talatu tace kiyi hakuri don Allah banina kawo kainaba Gimbiya dakanta takawoni dakinnan batareda Jamila tajira sake jin me Talatun zatace ba tajawo hannunta tana “kizo kibar dakinnnan don inada tabbacin datasan wacece ke ko hanyar bangaren nan bazaki taba ganiba bare harkisamu daman zuwa kizauna mata ah daki”…..
Haka Jamila tadinga jan Talatu hartakaita ta back door tasaketa ah kasa tana wallahi baki isa kizo ki sake taimakawa wurin sake gurbata musu zuria ba don na lura ku anan kuka fi auki daga ke har uwar dakin naki kuka sosai Talatu take tana bahaka bane ita……..
Tsaki Jamila tayi tareda shigowa tarufe backdoor din rukayya da Hindatu ne suka ce kinyi daidai wallahi don wannan zaman ta agidan nan kona minti daya ba alheri bane ah gidan nan……

Bangaren Asma’u kuwa koda ta isa bakin kofar dakin nashi knocking tashigayi amma yaki kulata kuma tasan yanajinta yana expecting tashigo ne as usual komi?toko lallai baidamu da kiran nata ba haka tajuya don komawa setaji yace “come in”……

Itama seda taja mishi aji sannan ta tura kofar dakin tashiga batareda ta gaidashi ba tace…
“ance kana kirana”…….
Yana zaune kan wata sofa dake dakin ya lumshe idanunshi kanshi na kallon sama kin kulata yayi seda tasake maimaita wa akaro na biyu sannan yace”Ina kika kai Matar nan?”……
Wace mata tayi tambayar kamar wanda bata gane inda maganar sa ta dosa ba bude sharp idanunsa yayi yadago tareda dorasu kanta fuskar sa babu alamun wasa”you know who I’m talking about so,stop pretending”……

Turo baki tayi”tana dakina”……
Yasha mamakinta amma seya boye mamakin nashi yace”send her away banason insake ganinta acikin gidana kinajina?”……

Cikin sauri takarasa gabanshi kamar ba itace tayi kicin kicin da fuska ba tace”meyesa zankoreta bakaga yanda matarcan tayi mata bane?”takarashe maganar murya ah karye……..
“Asma’u”,yakira sunanta cikin husky voice dinshi……
“Na’am”ta amsa mishi da muryar tausayi……
Gyara zamanshi yayi batareda yakuma kallonta ba yace”just do as i say”……
Yunkurin yin wani maganan tayi ya daga mata hannu alamar bayason wani zance kuma babu yanda ta’iya haka tatashi tafice cikeda jin haushin shi”waishi bashida tausayine ko bashida idanune sekace bega abunda matarnan tayima Talatun ba”…….
Karasawa tayi dakinta tana ta kunkuni ita kadai sede to her own surprise babu Talatu agurin……

Dasauri tafito cikeda tashin hankali tana kiransu Salma, iya Jamil, rukayya,iya Hindatu kuna inane?….
Dasauri suka karaso gabanta bayan sun amsa kirannata”bakuga bakuga bakuwar dana kawo bane ba?”……..
Jamila dake gefe tafara magana nervously”munganta Gimbiya nice na koreta”…….
“What”,shine abunda Asma’u tace cikin sauri Jamila tace”Gimbiya wallahi bakisan halinta bane shiyasa,munafuka ce wallahi”…….
Ba wannan nikeson jiba tana inayanzu Asma’u tayi maganar ranta bace murya ba dadi Jamila tace”tana ta kofan baya”….

Batareda tabi takansu ba tafice dasauri bin bayanta sukayi Jamila da Hindatu na Gimbiya kitsaya don Allah kada kizo kina nadama daga baya………
Ah waje tasamu Talatun inda Jamila tabarta cikin sauri takarasa gabanta tareda cewa kiyi hakuri kidaina kuka don Allah tashi……
Jijjiga mata kai Talatu tashigayi alamun bazata tashiba……..
Dakyar Asma’u tayi convincing dinta sannan takama hannunta dubansu Jamila dake kallon ikon Allah tayi tace Ina makullin dakin waje?….
Yanda Asma’u tayi maganar rai bace yasa babu musu Jamila takoma cikin gida tadauko makullin takawo karban makullin tayi tabude kofar dakin dakanta sannan takama hannun Talatun suka shige dakin katifa dayane kawai ah dakin babu ko tabarma bare kafet sekuma bandaki ah ciki……
Kizauna ki huta anjima zanzo muyi magana Asma’u takarashe maganar tareda fita,ah bakin kofa tahadu dasu Hindatu kallon rukayya tayi sannan tace”kije kikawo mata abinci sannan banason inji bakin wani ya ambaci nakawota dakin nan”…….
To Gimbiya cewar rukayya sannan tawuce don yin aikin da Asma’un tasakata…
Asma’u kuwa daki takoma Hindatu da Jamila ne suka bita murya can kasa kasa Jamila tashiga bata hakuri kaman zatayi kuka”nasan nayi kuskure Gimbiya nayi aiwatar da abunda nayi niya batareda izinin ki ba kiyi hakuri”………

STORY CONTINUES BELOW


Haka Hindatu tadinga bata hakuri wanda yasa Asma’un jin wani iri tunda Matar ta girmeta bazata iya turning nata down ba dukda kuwa abunda tayin yabata mata rai cikin sauri tace “Iya Hindatu kidaina bani hakuri don Allah haka kinasani jin wani iri”…….
Babu komai Gimbiya nice da laifi kuma nayi hakan ne sabida lafiyar iyalin ki banason susake shiga cikin wani hali kamar da………..
Dan shiru Asma’u tayi tana nazari sannan tace”wai miyasa bakwason yarinyarnan ne ku bakuga abunda akayi mata bane ba, haka shima Yariman cewa yayi once tabarmasa bangarensa what if inta koma matarnan tasake yimata abunda tayi dazu”..
Asma’u takarashe maganar cikeda damuwa wannan karan Hindatu ne tayi magana……
“Bakisan waye Magajiya ba inajidai ko?….
Dan shiru Asma’u tayi sannan tace nataba jin sunan ta amma namanta ah Ina cikin sauri kuma se tace oh natuna Dad yabani labarinta…….
Yauwa cewar Hindatun sannan takara da itace wacce kika gani tana dukan Talatun cikin sauri Asma’u tazare idanu tareda dafe kirji gyada mata Kai Hindatu tayi”itace Gimbiya babu wanda baisatantaba cikin masarautar nan hakanan babu wanda baisan halintaba sede kuma baza’a iya furtawaba afadi laifin nataba kuma yarinyar da take dukan ita tasan duk wani sirri nata sannan tare suka duk wata kullla kullansu shiyasa kikaga Yarima Almustapha yace kikoreta hakanan muma shiyasa muke tsoron zama da’ita sabida wannan zai iya zama cikin hadinsu dakuma munafurcin su”……

Tunda Hindatu ke magana Asma’u ta kasa kunne tanajin metake fada donkuwa bakaramin mamaki tabata ba tabbas tasan Magajiya yaddikon Almustapha ne sede bata taba sama ranta zasu haduba tunda ah iya saninta akan samu sarki yanada Mata sunkai hudu shiyasa ma tadauka daya daga cikin matan ne Mai Martaba yace suje su gaisar yaudin………
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abubuwan datake maimaitawa aranta haba ashe shiyasa taga haka, shiyasa taga anacin zalin yarinya batareda wani yayi magana ba don dama atunaninta mutum me imani bazaiyi abunda taga Magajiya tayi dazunba amma seta daure tace “kuka sani ko itan ta shiryu tunda kunga ai wulakanta ta tayi please kibarni intaimaketa”…..
Jamila na niyan magana Asma’u tace”please Iya Jamila kibarni nayi abunda nayi niya “……
To shikenn cewar Jamilan amma dai kiyi ahankali da’ita sabida ba ayarda da irin mutanen nan karaf daya…
gyada musu Kai Asma’u tayi tareda gode musu don harga Allah batajin zata iya barin Talatu yanzu may be this might be helpful to them wurin exposing evil act na Magajiya dukdama bazata takura mata na saita fada ba ita dakanta intayi niya zata fada mata……….

******
Duban Dad Mai Martaba yayi sannan yace….
“nikam akwai abunda yake damuna Yaya inason innemi shawarar ka”…..

Murmushi Dad yayi tareda gyara zama sannan yadubi kanin nashi”meyafaru Abdulrahman,share you problems with me kaji I’m all ears”……
Numfasawa Mai Martaba yayi sannan yace”akwai bakuwa datazo daga nijar yanzu wurin watan ta biyar ah masarautar nan wai tazo neman dangin iyayenta ne don tun tana yarinya aka kawo musu hari agidan su babu wanda ya rayu se ita don agabanta ma wuta yakama gidansu she’s went through alot of terrible experience kaman yanda tafada harzuwa girmanta yanzu tadawo gidan neman danginta ko Allah zai bayyana su amma shiru babu labarinsu dan numfasawa Mai Martaba yayi…..

Muniba is a very nice person adan zaman damukayi da’ita ah masarautar nan na watanni biyar nagane hakan bata sati biyu batazo tagaisheniba hakanan wataran xata aikomin abinci she’s so free and jovial ina ganinta amatsayin kanwata shiyasa nakejin kaman batajin dadin rayuwa itakadai atleast yakamata tayi aure don tace min bata taba aureba……….
Cikin saurin Dad yace Allah sarki but are you sure she’s a nice person?…..
Cikeda assurance Mai Martaba yace”she’s,nayarda da’ita dari bisa dari”…..
To shikenn daman ni tsorona kada ksyi trusting mutum yazo ya cuceka kasan mutanen yanzu se ahankali……

Hakane Yaya sede Muniba bazan taba shakkuntaba koda na second dayane infact sometimes nakanji kaman munjima da sanin juna, nakanjita kaman yar uwata shiyasa kaji nafadi hakan….

To ae shikenan tunda kace hakan sede Kai”what are your plans?”……
Kai tsaye Mai Martaba yace I want her to settle down and start a family atleast zairage mata kewan yan uwanta kafin ace tasamu labarin danginta and I promise to stand by her kaman dan uwanta gyara zama Mai Martaba yakumayi sannan yakarada daman naso inyi magana da Galadima ko dagaci kokuma wani dai daga cikin masarautar nan ya aureta sede matsalar bansaniba kozasu yarda tunda kaga bawai ansan danginta bane ba…..
Kai tsaye Dad yace”why not Kai ka aureta Abdulrahman?”…
Wani kallo Abban yamasa yana dariya donshi bedauki abun serious ba….

STORY CONTINUES BELOW


“I’m serious Abdul bawasa ba,you need a companion too besides you trust her gakuma maganar ba lallai daya daga cikinsu ya auretaba dukdama nasan indai kanemi alfarmarnan they’ll surely agree kainedai kake tantama sedefa zasuga kaman ka cusa masu itane gwanda ace kaidin ne ka aureta”…..
I’ve a wife Yaya kokamanta Magajiya ne?…

Dan tabe baki Dad yayi jin an ambaci sunan Magajiya kafin yakamo hannun Mai Martaba yace”look at me please?”…..

Kallonshi Mai Martaba yayi cikeda damuwa Dad din yace”nasan bawai kana farin ciki dazaman dakukeyi da’ita bane she never cares batadamu da Al amuranka ba kuma naga dai you’re allowed to marry har four wives ma so why not ka kara yanzun?…
Dan shiru Mai Martaba yayi yana nazari kafin daga baya yace”banason matsala ne Yaya yarana sun girma banason ana samun matsala tsakanin matayena shiyasa nake avoiding sake aure inbahaka ba saunawa ake kawomin offer na aure nake kin karba”…..
Dafa kafadarshi Dad yayi sannan yace Ya’yanka duka sunyi aure baswa gidan nan so,nibana ganin wata matsala daza asamu Sulaiman ma won’t have a problem i know that besides you’ve to think about yourself first kaima yakamata karinka samun kwanciyar hankali so ni inaganin indai har Muniba tayarda just go ahead and marry her…….
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace nagode Yaya I’ll think over it…….
It’s okay Allah yazabi abunda yafi alkhairi ansawa Mai Martaban yayi da amin kafin suka sauya wata hirar kuma………. 1

***
Koda dare yayi Asma’u seda tasaci hanya taje taduba Talatu ta tabbatar taci abinci sannan tace”feel free don Allah kikwantar da hankalinki anan babu mai cutanki in Allah ya yarda”, gyada mata Kai kawai Talatun tayi tana kallon Asma’u din cikeda mamakin how kind hearted she’s batasanta ba,batasan ita wacece ba amma tadauketa tabata gurin zama in her difficult times dukda kuwa tasan ma ita baiwa ce,dama akwai mutane irin haka shine tambayar data shiga yima kanta kenan…….
Sallama Asma’u tayi mata sannan takoma dakinta takwnta bacci…….
*****
Washegari Mai Martaba da Dad dakansu sukaje gidan dasuka sauki Hajiya Muniba tayi mamakin ganinsu kwarai hakanan bata boye mamakinta ba tace”ranka shidade aidaka nemeni zanzo da kaina basai kawahala ba”……
Murmushi Dad yayi sannan yace “zuwa dakanmu yafi tunda kokon barar mu muka kawo”Bata gane inda maganar tadosa ba amma setayi musu iso mekyau sannan takoma takawo musu kayan motsa baki seda suka gaisa sosai sannan Dad yafada mata abunda yakawo su…….
Hakanan setaji takasa rejecting Mai Martaba dukda kuwa bata manta alkawarin data daukar ma kanta nakinyin aureba harsaita yi taking revenge sede itamafa wannan opportunity ne gareta tunda ma aidaman sabida Mai Martaban ne Magajiya tayi wannan aika aikan itakuwa seta nuna mata cewa shidinma bazata zauna dashi lafiya yanzuba”……

Kanta akasa tace”ammadai ranka shidade kasan labarina banida iyaye bani da kowa to tayaya zaka aureni”……
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace”se akacemiki wanda baida iyaye bazai auruba ko cemiki akayi kedin bakida right din zama cikin farin ciki ne?”….
Gyada mishi Kai tayi ahankali yayinda idanunta suka ciko da kwalla atleast he makes her feel she’s special…….

“Nagode”…
shine abunda tafada…..
Dad ne yadanyi dariya yana…

“to ai bakice kinyarda ba”…..
Yar dariya tayi tareda rufe fuskarta da gyalenta..
“Allah yazaba mana abunda yafi alkhairi”….
Amin shine abunda suka amsa baki daya kafin Dad yace”karkidamu nizan zame miki uwa kuma zan zame miki uba Muniba kidauka cewa banida da halaka da Abdul seke”……
Oh hakama abun yakoma cewar Mai Martaba din……
Dariya sukayi dukansu Dad na to daman nasanka ne tunda?……
Itadai Muniba se murmushi donkuwa yanda suke rahan setake tuno rayuwarsu nada yanda suka shaku da juna gashi har girmansuma wannan so da shakuwar nanan dukda jimawan dasukayi baswa tare sunjima ah gidan kafin suka tafi bayan Dad yace bayason ayi prolonging bikin tunda su ba yara bane if possible ko Friday dinnan ma ah daura aure inyaso sanda tashirya seta tare abunta…..
Godiya tayima Dad din kafin suka tafi……..

STORY CONTINUES BELOW


Ranar juma’a kuwa aka daura auren Mai Martaba da Hajiya Muniba bakaramin hauka Magajiya tayiba data ji labarin don kuwa bayinta ma ranar sun ji ajikinsu don babu wanda baisamu rabonshi b ba daga karshe ma zuwa bangaren Mai Martaban tayi ta cakume rigarshi tana”wallahi Abdulrahman baka Isa kacuceniba harni zakayima kishiya?”…
Tureta yayi kadan sannan yace”look at yourself Magajiya,why are you behaving like this?”…..
Hawaye tafara tana dan sosa jikinta cikeda takaici tace”oh hakama zakace bayan ka cuceni?”…..
Zama yayi bakin gadonsa batareda ya kalli inda take ba donshi kwanan nan kyama tafara bashi sabida bata kula da jikinta gashin setazo taita soshe soshen jikin kaman me cutan chicken pox sannan yace”Danna sake auren haramun ne akace miki komi?”……
Kara yin kanshi tayi daniyar cakume rigarshi yace kul Magajiya kada ki kuskura abunda yahanani fada mikin kenan ashe ahakan ma bantsira it’s better you get back to your senses and accept the reality *Muniba* is now my wife and nothing can change that yana gama fadin hakan yatashi yafice yabata guri zama tayi agurin tana hawaye “wai ita zaiyima kishiya don ya raina ta koko danyaga tafara canza kamanni ne?”…..
Itakanta tarasa meyake damun jikinta tunda dai yanzu tana wanka bawai batayiba sannan taje asibiti anbata drugs tanasha amma haryanzu bataga wani sabon changes ba raya wa ranta tashigayi kode taje gurin bokan ta ne may be ya iya taimakonta…..
Dakyar ta’iya controlling kukanta sannan tafice daga bangaren nashi don zuwa tasamu Laure su zanta….. 1

Bangaren Hajiya Muniba kuwa cewa tayi sewani sati zata tare babu yanda suka iya haka suka barta ko Almustapha da Sulaiman basusan da labarin ba seji sukayi an daura auren Mai Martaba da Hajiya Muniba abun baidamu Sulaiman kaman yanda yadamu Almustapha ba sabida haka kawai seyaji yanajin haushin Mai Martaban watoma ko mahaifiyarshi baya iya tunawa tunda har ya sake aure ranar yini yayi rufe ah daki haka kawai seyaji koma wacece Hajiya Muniba to bata kwanta masa araiba donji yake kaman she’ll also be like Magajiya………..
Haka Asma’u tazo tayita knocking kofar dakin amna ko kulata beyiba barema tasan yasan da existence dinta agurin ita daman damuwarta yafito koda abinci ne yaci daga karshe Kiran wayarshi tayitayi amma yanaji yaki picking daga karshe ma kashe wayar yayi baki daya tabe baki tayi takoma daki tana mita”danma yasamu nakulashi dukda ina fushi dashi shine zewani wulakanta ni to yaktyauta”,tana cikin mitar ne wayarta tashiga kara Asiya ce takira wani irin tsalle tadaga tareda daga wayar…
“Aseey nayi kewarki”, Asma’u tayi maganar kaman zatayi kuka…. 1

Daga daya bangaren ma Asiya tace baki kainiba Asma’u gwanda ke agari kike inkinaso zakije kiga su Ummi da Mommy……
Waya fada miki tunda nazo babu inda naje wallahi inanan zaune kamar wata Matar kulle bamuda maraba wallahi….
Dariya Asiya tayi tana to yakike,ya mijinki kuma?…
Uhm duk lafiya kalau Asma’un tabata ansa and you Ina Yaya Aslam kice nayi fushi tunda muka kaimishi Mata yamanta dani………
Dariya Asiya tayi aikuwa gashinan yanajinki sa hannu Asma’u tayi abaki tana yar dariya”haba dai?”….
Wallahi kuwa cewar Asiyan kafin tamika ma Aslam wayar suka gaisa da Asma’u yana tsokanarta da”Gimbiya Gimbiya”,kafin daga karshe yamaida Asiyar suka cigaba da hirarsu na yan uwa……

******
Washegari Mai Martaba ya aika akira masa Almustaphan koda akazo fadan sakon Kin bude kofar yayi se da Asma’un tazo tafada mishi tayi tafiyarta……
Jiki ba kwari yatashi yayi wanka donba karamin yunwa yakejiba seda yashirya tsaf sannan yabude kofar abakin kofa yaganta rikeda tray din abinci harara ya zabga mata sannan ya raba ta gefenta yawuce dukda kuwa yunwar dayake jidin….
“Yaya Almustapha ka tsaya kaci abinci please”………
Kobi takanta baiyiba yayi tafiyarsa fada koda ya’isa Mai Martaba da Dad yasamu gaidasu yayi yanata shan kamshi murmushi Dad yayi don ya ganoshi tsaf amma sebaice komai ba……..

Mai Martaba ne yace”yaushene convocation dinku?”…..
Two weeks from now cewar Almustapha din……
Allah yakaimu cewar Dad din kafin yamika masa files yace gashi tun sanda kadawo gareni naga kayi final exams naka nakesa zumman bude maka asibiti Almustapha sabida taimakon alumman mu baki daya dukda kuwa acikin garin Zaria nayi niya sede naji labarin akwai kauyikan dasuke lacking health attention agurinsu infact sukan sha wuya kafin susamu asibiti in mutum baida lafiya kuma kaga irin wannan for the sake of emergency yakamata ayi wani avu sabida nasan yayi leading to loss of many lives…….
We can’t control everything but atleast we can help tayanda zamu iya iyakacin karfinmu……

Akwai abokina munyi makaranta tare sede shi MBBS yayi haka danshi ma so seya gina hospital ah can cikin kauyen *Gangara* dayake dan Giwa local government ne har ansa kayan aiki dasauransu anyi komai infact yanemi nurses da likitoci dazasu taimaka masa awurin yin aikin sekuma yacanza ra’ayi wai yanason yasayar dukdama bansan dalilinsa ba I know yanada genuine reason it might be family issues of something else dabayason Sharing with outsiders yayimin talle nikuma senace zansayi asibitin In your name….
Yanzu nasaya alhamdulillah yazama naka Almustapha nace danshi should take care of the hospital before kazama settled and atleast yafika experience ma sede inason after the conversation kaje can din kazauna for sometime ka tabbatar ana aiki mekyau anakuma bama mutane treatment yanda yakamata…….

Almustapha wani irin dadine yakeji harcikin ranshi,seyau yaji yasan yanada uba seyau yaji feeling din cewa Mai Martaba yadamu da feature dinshi kobakomai and it’s also a sign that he cares tuni yamanta kishin dayake taya uwarsa yashiga yima mahaifin nasa godiya…………
Rungume shi Mai Martaba yayi yana Allah yayima karatun albarka….
Amin suka amsa duka dede lokacin aka shiga shigowa da abinci harzai tafi Mai Martaba yace yazauna suci abinci daman yunwa yakeji kaman zaiyi yaya don haka yazauna sukaci dasu Dad din seda suka gama sannan Mai Martaba yace”yauwa namanta ma nikam akwai kaya damuka fidda zaku kai wasu kauyuyyuka kaida Sulaiman gobe so kashirya”…..
Gyada kai kawai yayi sannan yayi musu sallama yafice…..

*****
Dakinsu Afiya taje tana ta turo baki….
Lafiya dai sister in-law meya faru haka?……….
Yayankune mana yaki cin abinci tun jiya takarashe maganar yayinda hawaye suka taru ah idanunta……
Cikeda damuwa Afiya da Amiran suka dawo gefenta suna cewa”waya fadamiki wallahi Yaya Almustapha zai iya yaci abinci yanunama baicinba so kidaina tada hankalinki”…..
Ware hannunta yayi”I’m sure baici ba Allah kuyarda ni”……

Nan tabasu labarin yanda akayi Amira ne tafara tunani to “why will he be angry,wani abu yahadaku ne?”..
Jijjiga kai Asma’u tayi alamum aa..
Caraf Afiya tace kodai don auren da Abba yakara ne?… ..
Hararanta Amira tayi sannan tace”I don’t think wannan shine reason din besides irin abunnan becika damun Yaya ba”……. +

Cikeda damuwa Asma’u tace nifa duk wannan bashine matsalataba damuwata shine yanzanyi convincing nashi yaci abinci he can’t stay hungry you know……

Kallonta sukayi cikeda so ganin yanda ta damu da Yayan nasu sannan Amira tace”I’ve an idea”…..
Cikin sauri daga Asma’u har Afiyan sukace miyene fada mana muji,nan Amira tashiga yi masu bayani hartakai karshe………
Kallonta Asma’u tayi tanadan bata rai”waya fada miki don banci abinci ba zaisa yadamu wallahi nasan ko kallon inda nake bazaiyi ba”…….

Sis kede ki gwada mana kigani……
Tashi Asma’u tayi tana impossible nikam bazan jama kaina rashin mutunci ba da safiyar Allahn nan……..
Amira ne tace okay then nidai Afiya inkina da solution kifada mata don nikam iya abunda zan iya kenan Afiya ma cewa tayi batada idea,tashi Amira tayi tana ciro uniform dinsu na islamiya tareda kiran daya daga cikin bayinsu tazo tadiba awanke ayi ironing…….
Yayinda Afiya tace Sister in-law kizo kibimin karatun nan tundazu nakasa kumafa Yaya yabimin yafi sau biyar da asuba………
Sakan baki Asma’u tayi tana”watoma harkokin gabanku kukacigaba dayi ko?”….
Dariya Afiya tayi”toya zamuyi miki Sis besides I’m sure yaci abincifa kene kika damu”…..
Zama tayi tareda turo baki”Allah baici ba”…..
“Okay fine beciba,to kibi shawarar Amira I’m sure it’ll work besides Yaya Almustapha cares for you Allah kuwa”……..
Kallon Afiyan tayi tanadan tunani kafin tace I’ll try amma inwani abu yafaru I’ll blame you two takarashe maganar tana nunasu da yatsa dariya suka mata Amira na”Cabdi aida kinshige kuma se anganki”,haka sukayita zolayarta daga karshe tayi zuciya tafice abunta dakinshi takoma amma baidawo ba haka tazauna ah parlour zaman jiranshi amma shiru hakan yasa tashiga kiran layinshi wayarma ah kashe take tsaki tayi tareda wurgar da wayar tarasa miyasa tadamu ma da mutumin dabai damu da’ita ba kwata kwata ahaka tahakura tatashi sukayi girkin rana koda suka gama kasa cin abincin tayi sabida bata wani jin yunwa………
Wanka takumayi tayi bangaren Gimbiya Zaliha tunda ranar batasamu taje ba due to incident din daya faru………….

Koda ta’isa ah parlour aka sauketa tafi minti talatin zaune Zaliha bata fito ba dukdama an cika gabanta da kayan motsa baki can kuma segata tashigo sewani yauki takeyi zama tayi da murmushi Asma’u tagaidata dakyar ta iya amsawa daganan bata kuma cewa komai ba bayan minti biyar kuma tatashi tayi shigewarta mamakine yakama Asma’u sosai amma sebatace komai ba jiki ah sanyaye tatashi tafice takoma bangaren su tana”Nima maganina,dabanzo inda takeba bazata wulakanta niba but I’ve learnt my lesson now”………..

Dakin da Talatu take tafara shiga murmushi tasakar mata yayinda dakyar Talatun ta’iya mayar mata sabida mutuncin yarinyar is too much tarasa Asma’u wace irin being ce…….
Ina wuni Asma’u tagaidata dasauri Talatu tazube ah kasa tana gaida Asma’un batareda ta amsa tata gaisuwar ba……….
Don Allah kitashi iya,zauna abunki kinji Asma’u takarashe maganar tana murmushi komawa Talatu tayi tazauna ah spot dinta nadazu zama Asma’un ma tayi kafin tace”suna kawo miki abinci koda yaushe ko?”…..

Eh Gimbiya Talatun tayi magana kanta akasa,tambayarta Asma’u takumayi…
“Babu dai wata matsala ko?”….
Gyada mata kai Talatun tayi kafin tace”amma inason inkoma cikin yanuwana Bayi kar ayita nemana kuma nasan haryanzu Magajiya batadaina fushi daniba yana iya zamemin matsala”…….
Dan kallon ta Asma’u tayi cikeda tausayawa sannan tace”basai kin koma ba kiyi zaman ki anan tunda kokin koma bata hakurin ma ba lallai tahakura ba”….
“Ko bazata hakuraba Gimbiya inason tagane cewa nidin ban cuceta ba,bazaki gane irin jimawar damukayi tareda ita ba itane cina hakanan itace shana kuma mu daman bayi koda yaushe muna zaman amana ne tareda shuwagabannin mu batareda munjuya musu baya ba koda kuwa hakan na nufin zamu cutu ne”Talatu takarashe maganar tareda jan kasan zaninta tana goge kwalla …….

STORY CONTINUES BELOW


Dan shiru Asma’u tayi nawasu dakiku kafin tace”koda mutumin ze iya halaka ku iya,donkuwa matarcan bana tunanin zata barki darai dabadan antsaidata ba jiyannan,don kunayi masu aiki bekamata ace suna treating dinku kamar ba Allahn dayayisu shiyayikuba kuma mutane ne kuma kuna bukatan ah kyautata muku,mutumin dazai rike maka amana yayi duk abunda kace aibai kamata ayimishi abunda tayi mikiba besides yakamata ace duk zaman dakukayi tayarda dake dari bisa dari hakanan yakamata ace tasan abunda zaki iya dawanda bazaki iya ba Iya,dan numfasawa Asma’u tayi sannan tace I consider this as cin zali dakuma wulakanci wanda inada tabbacin da Mai Martaba yasan dahaka seya daukar miki fansa sabida Abba mutum ne dabazai taba bari ana wannan badakalar ah masarautar sa ba..”……

Jin Asma’u ta ambaci Mai Martaba Talatu tace don Allah kada kibari yaji wannan zancen don inyaji ze iya zama silar barina duniya kokuma yazamanto hanyar kuntatamin dukda ma basu sukafi damunaba abunda yafi damuna shine hukuncin daza ayima Uwargijiyata……..
Murmushi takaici Asma’u tayi cikeda mamaki azuciyar ta tana anya matarnan bata asirce Talatun bama?……..
Kinji Gimbiya don Allah kada aji maganar nan abakin ki ……..

“Haka zakucigaba da rayuwa kenan,haka zakucigaba da ganin ana cin zalinku batareda kun kwaci yancin kanku ba?”…….
Gyada mata kai Talatu tayi alamar eh sannan takarada”dalilin dayasa mukenan kenan, wannan shine kaddarar mu kuma mundade da yarda da hakan”…

Jijjiga kai Asma’u tayi tana iya”wannan ba destiny dinku baneba,you can change it by doing the right thing and by standing for your right,so dole infada ma Mai Martaba nibazan iya shiru inaganin ana irin wannan abu agaban idanuna ba”……..
Kuka Talatu tafarayi itadai rokon Asmau takeyi karta fada dakyar Asma’u tayarda kafin tace amma nima inada nawa sharadin……….
Folding hannu Talatu tayi alamun roko tana kuka”kifada wallahi kowani irin sharadine zanbi amma nidai karkifada ma Mai Martaba halin da ake ciki”……..
Kai tsaye Asma’u tace”sharadina shine bazaki sakemin maganar komawa cikin bayiba bare har ki kusanci Magajiya”……

Dan shiru Talatu tayi har Asma’u zata tafi cikin sauri tace nayarda….
Murmushi Asma’u tayi sannan tace kikwantar da hankalinki ni taimakon ki zanyi…………
Daganan tafice zuwa dakin Ummi don fitar da ita zuwa lambu as usual…….
Tana addu’ar Allah yasa Malamin nan yasamu zuwa jibi kaman yanda yayi alkawari tunda baisamu zuwa wancan karan ba……
******

Tare suka ci abincin dare dasu Afiya ah parlour se nishi take tana Allah nakoshi yaudinnan harji nake kaman cikina zai fashe……….
Dariya Amira tayi”kema meya kaiki Sis”…….
Turo baki tayi tanadan taba cikinta”miyan ne yamin dadi bakisan yanda nikeson miyar kubewa bane shiyasa kuma abunda yasa naci dayawa don bani nayiba Jamila ce tayi inni nayi abinci bancika ci sosaiba” ……..

Tashi Afiya tayi tana nima cikina yacika sosai aeduk laifin Amira ne tatashi ta lafta mana…..
Itadai Amira se dariya takeyi masu jisukayi Sulaiman na magana da Almustapha da alama shigowa parlourn zasuyi cikin sauri Asma’u taruga da gudu tashige daki tana masu alama da suyi carrying on plan dinsu………
Turo baki Afiya tayi tana to afili kuma tace “nifa nasan Yaya yaci abinci babu yanda za ayi yayini beci komaiba kuma har ya iya yawo”……
Hararanta Amira tayi”kefa kinada mita inzakiyi yanda akace kiyi and this might help us muga ko Yaya nason Sister In-law”…..
Dariya Afiyan takoma tanayi tana”haba aini bangane da biyu kikayi ba”….

Tsaki Amira tayi tana dariya”Ina zaki gane tunda hankalinki baya jikinki”……
Tana shirin ma Amira reply su Sulaiman din suka shigo gaidasu suka shiga yi yayinda Afiya tashiga kiran rukayya ba ajima ba segata tazo”kuzo kukwashe kwanukan nan takarashe maganar tana nuna mata trayn dake ajiye da kuma kuloli”….
Zama Sulaiman yayi yana dan taba cikinshi”nimafa yunwarnan nikeji gwanda inzauna inci”……..
Dariya Amira tayi tana ae abincin ku naciki bari ace akawo muku nan tacema Rukayyan intaje ciki tace akawo abincin su Sulaiman……

STORY CONTINUES BELOW


To ta amsa sannan tayi gaba…..

Ba ajimaba sega Hindatu takawo abinci ta ajiye saukowa Sulaiman yayi daga kan kujerar yazauna kasa tareda janyo warmers na abinci yafara zubawa juyowa yayi yana tambayar Almustaphan…
“Yaya inzuba dakaine ?”…..
Kaman bazaiyi maganaba sekuma yace”I’m not hungry”……
Sakan baki Sulaiman yayi yana”tunfa safe muke tare kuma nidai banga kawani ci abincin kirkiba sannan yanzu kace kakoshi bafa muci komaiba”……..

Ko kallon Sulaiman din beyiba bare yayi tunanin samun ansa daga gareshi tabe baki Sulaiman yayi yamaida hankalinshi kan tuwon dake gabanshi……

Amira ne tace”to meyeke faruwane, Sis Asmeey ma takicin abinci tun safe wai batada appetite gashi naji Aisha tace tanada chronic ulcer inyatashi mata baya mata wasa but she’s being stubborn kode azumi kukeyi ne Yaya?”, takarashe maganar tana kallon Almustaphan dariya Sulaiman yayi yana”Amma babu dan rainin wayau irinki Sis,azumi fa kikace”…
Ware idanu tayi eh mana,to naga Itama bataci komai ba tunsafe cewar Amiran yanzu kuma tashiga ciki wai tana jin hajijiya……..
Tose akace miki azumi sukeyi kobaki ganin har anyi Isha ne dasuna azumi zasu fada ai kawai may be itan batajin dadi ne and shikuma bansan dalilinsa ba Sulaiman din yakarashe maganar yana kai wata lomar sannan yace ba ingama inje induba Sister in-law na……

Almustapha najinsu bece komai ba sema tashi dayayi yayi gaba dakinshi yashige yayi freshen up yayi shirin kwanciya amma gabadaya hankalinshi nakan yarinyar…
“why will she not eat food bayan tasan tanada ulcer,ulcern ma chronic”……..
Zama yayi bakin gadonshi tareda sa hannu yadan hargitsa lallausar gashin kanshi”he really need some rest now tunda zaiyi tafiya early morning gobe yasan definitely it’s going to be a very hectic day”……….

Komawa yayi yakwanta sekuma zuciyar shi tashiga raya mishi”what if ulcer dinta yatashifa,her family will blame them for not taking good care of her and hakan zaisa susake yarda shiba mutumin kirki baneba”……..
Tashi yayi ahankali yayi hanyar kofar dakinshi haryakai bakin kofa sekuma yadawo yana”no,i should just let her be that’s her bussiness not mine”……
Haryaje bakin gado zaizauna sekuma yakasa zaman yasakeyin hanyar kofa nanma zuciyar shi tace yadawo kawai koda yadawo kasa komawa yayi yakwanta,dan tsaki yayi ahankali tareda dafe kanshi sannan yafice adakin……..
Straight parlour yawuce haryanzu su Amira na parlourn se dariya sukeyi da alama wata hirarsu sukeyi sede suna ganinshi kowa tayi shiru har Sulaiman dinma………..
Harara yabisu dashi sannan yace “Afiya”…
Murya narawa tace”na’am Yaya”tareda karasowa gabanshi cikin sauri……….

Tafi minti uku tsaye gabanshi bece mata komaiba kafin ya iyacewa….
“arrange some food and take it to her room”…..
Tagane meyake nufi amma setace”dakin wa Yaya?”…
Wani harara ya daka mata wanda yasata barin parlourn ba shiri shima dakin Asma’un yawuce batareda yabi takansu Sulaiman ba seda suka tabbatar yayi nisa sannan suka kwashe da dariya Sulaiman yatashi yazo yatsaya inda Almustaphan yatsaya dazun yana imitating din Yayan nashi”arrange some food and take it to her room now”,yakarashe maganar yana sake kwashewa da dariya shida Amiran……..

Amirane ta iya rike dariyar tace gashi abayanka cikin sauri yajuya seyaga babu shi agurin kan Amiran yayi yana shirin kaimata maka cikeda wasa….
To yi hakuri Yaya Sulaiman dina,my one and only Yaya tashiga bashi hakuri tana…
“Wasa fa nakeyi Yaya Sulaiman”…..
Murmushi yayi sannan yace
“anaso ana kaiwa kasuwa ba inje gurin tawa Matar nima yakarashe maganar tareda fita”…….
Amira na Yaya inzakaje daukan Sumayyan zamubika karka manta……
To yace mata don gobe Sumayya zatazo gida wai hutu……..

*
Yafi minti biyar abakin kofar dakin kafin ya iya yayi knocking tana waya da Zahra taji anbuga kofar cikin sauri takatse call din tareda tura wayar karkashin pillow don tasan shine because insu Amira ne bazasuyi knocking bama zasu shigo….

Seda ta kimtsa tashige bargo tayi lamo kamar wata marar lafiyar gaske sannan tace”come in”…..
Tura kofar yayi ahankali sannan yashiga dakin wani irin scent medadi ne yaziyarci hancin shi this’s the very first time daya shigo dakinta tunda aka kawota gidan sede koda yashigo din hankalinshi nakanta dukda ranshi nason karema dakin kallo amma ya basar………

STORY CONTINUES BELOW


Cikin takunshi na kasaita yakarasa bakin gadon ya tsaya kanta tareda sa hannunshi cikin aljihun wandonshi……

Idanunta alumshe kamar wata me baccin gaske sede kallo daya yayimata yagane ba baccin takeyiba seda Afiya tashigo da abincin ta ajiye tafice sannan yace….
“open your eyes”….
Sake rumtse idanun tayi wai don karyace ba bacci takeyiba…..
Dan murmushi yayi ganin yanda tayin aranshi yana”so childishi”yayinda afili kuma yace…
“I said open your eyes Asma’u”…….
Aebatasan sanda tabude idanunba sabida yanda muryarshi keda effect akanta shidai ba tsawa zaiyi makaba hakanan ba magana cikin lallashiba magane kawai inyayita seta bita……..
Tsuru tsuru takuma farayi da idanu kamar wanda aka kama tayi satan nama…….

Kare mata kallo yashigayi”zaman ma senace kiyi?”…..
Turo baki tayi kafin tatashi tazauna dabas…….
Zama yayi bakin gadon kallon shi take sosai ganin kallon yayi yawane yasashi directing idanunshi to kan abincin Itama kallon abincin tayi daya kusan cika plate…….
“Mezanyi dashi?”….
Batareda ya kalleta ba yace…
“me akeyi da abinci?”…..
Kaman zatayi kuka tace”ci”…..
Cikin cool voice dinshi yace
“Fine,tunda kinsani ma”….
“To ai banajin yunwa tayi maganar ashagwabe”,wani harara yadaka mata dayasata birkicewa amma dukda haka tadaure tace
“Allah I’m not hungry kainedai zakaci bakaci komaiba tunsafe infact tun jiya”…….
Kallonta yayi cikeda mamaki sannan yace…
“shiyasa kika cin abinci?”…..
Gyada mishi kai tayi ahankali,dan tsaki yayi tareda lumshe idanunshi yama rasa maizaice mata sabida takuremai tunaninshi….

Jiyayi tana”inbakaci abinciba nima bazan ciba”…..
Bude oily eyes dinshi yayi yadaurasu kanta tareda cewa…
“this’s nonsense kinajina?”…..
Gyada mishi kai tayi alamar to yayinda batasan daliliba sega hawaye sunfara zuba…….
Daukar plate din tayi tamika mishi”gashi kaci to”dukda taji haushin abunda yacedin…..

Wani hararan yasake watsa mata”ke kici”…..
Make kafada tayi alamar aa itabazata ciba…..
Ware idanu yayi cikeda mamaki don yalura Asma’u tarainashi dayawa in a serious tune yace”nace kiciko ko sokike inmiki dole?”…
Sake make kafada tayi”nifa bazanciba sekaci”….

Wannan karan ranshi yagama baci hargitsa gashin kanshi yayi sannan cikin tsawa yace”I’m not playing with you nace kici ko!”……
Seda ta tsorata wanda haryasa plate din abincin yakusa subucewa daga hannunta sabida baitaba mata tsawaba seyau kai bama itakadai ba bata tabajin yayima wani tsawan daya mata yaudinba hawayenta karuwa sukayi tana kallon abincin don itakam cikinta cike yake tam azuciyarta tana su Amira sungama da’ita yaudinnan………

Dagowa tayi carab idanunta suka shiga cikin nashi sede daka gansu kasan ranshi bace yake don haka tayi saurin maida kanta kan tuwon babu shiri tafara ci tana hawaye seda tayi wurin loma bakwai taji bazata iyaba ba takuma dagowa tace”nakoshi”…….
“Sekin cinye”yayi maganar calmly……..
Babu shiri tacigaba daci tana hawaye amma koya kyaleta seda tacinye tuwon tas sannan yadauki glass cup din ruwa yamika mata karba tayi tasha yayinda yatashi yafice abunsa batareda yasake cemata komaiba ae tana ajiye cup din ruwan taji wani irin amai yazo mata tsabar overfeeding datayi…..
Dagudu tayi toilet seda ta harar da abincin sannan ta kuskure bakinta tafito tana nishi Amira da Afiya tagani suna dariya…..
Kuka tafashe musu dashi tana kunja min cin abincin dole haka kawae…..
Dariya Amira tayi tana sorry Sis mundauka zecine inkikayi insisting ke bazaki ciba……
Hararanta Asma’u tayi”nidai kunmin mugunta kawai daga ku har Yayan ku”…….

Aa wannan duk acikin so ne wallahi babu wani muguntan da Yaya yamiki Afiya takarashe maganar tana dariya……
Turo baki Asma’u tayi”wani so bayan yayi forcing dina inci abinci bayan cikina a cike yake”…….
Baisani bane Sis wallahi dayasan kinci abinci bazai saki dole kiciba….

Bawani nidai kungoyamai baya dai kawai hankalinku yakwanta takarashe maganar tareda kwanciya tashige blanket abunta tacigaba da sheshekar kukanta haka suka dinga bata hakuri amma taki kulasu daga karshe sukayi ficewarsu sukabarta……

****
Washegari dasafe Almustapha yagama shirinshi cikin kayan Sarauta bakaramin kyau yayiba as usual hakanan kuma betsaya yayi breakfast ba yawuce bangaren mahaifin nashi don yasan yau he has a long way to go inbasu fita dawuriba suna iya bata lokaci……….
Koda yaje yasamu Sulaiman agurin Abban tunkan yashiga kuma yaga anshirya Motoci guda biyar wanda zasuyi masa rakiya yayinda dayan kuma daf ce dauke da kayan abinci makil acikinta……….

Karasawa yayi yazauna tareda gaisar da mahaifin nasa cikeda ladabi, murmushi mai Martaba yayi sannan yace harka shirya Son?……

Gyada ma Mai Martaban kai yayi ahankali sannan Mai Martaba yace kaga kaninka yace bazaiyima rakiyarba kuma wai zeje taro kanwarku Sumayya ah airport yau zata zo gida hutu……..
Murmushi kawai Almustapha yayi batareda yace komaiba, Mai Martaba ne yadubi Sulaiman yace”to dole sekaje ne bagasu Afiya ba sesuje da driver su tarbe ta”……
Cikin sauri Sulaiman yace”Abba Allah nayi mata alkawarine”……
To shikenan Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya yakarashe maganar yana dariyarsu ta manya….
Amin suka amsa baki dayansu kafin Mai Martaban yace anfada maka kauyikan dazakuje ko?…..
Eh Abba yayi maganar kansa akasa,fara irgo kauyikan Mai Martaba yakumayi sabida kar asamu matsala yace”Birnin yaro,turunku,Faro kwai,Gadan gayan,Gangara,Dorayi,Takama,Kugi,Loko,Gelobai,Gwandan,Dogo dawa,Funtuwan badade,kwala kwangi,kutemeshi,kwashi da Tabbani inaganin sune kauyikan da muke kaiwa kayan abinci kowani shekara seka tabbatar kunje kuma kayi supervising properly inma baku gama yauba zaku iya karasawa gobe………..

to cewar Almustaphan……
Allah yayi muku albarka shine abunda Mai Martaban yafada bakaramin dadi wayannan kalaman keyima Almustapha ba haka suka rakashi harjikin mota kafin sukayi convoy suka tafi da fadawa…………Koda Mai Martaba yakoma bangarenshi shirin fita Fada yafarayi ba ajimaba sega Magajiya tashigo fuskarta daukeda murmushi……..
Ina kwana ranka shidade….
Dukda yayi mamakin ganin annuri ah fuskarta hakan behanashi amsa gaisuwarta ba…..
“lafiya Lau alhamdulillah”,and you ya jikin naki kinkoma asibitin ne?….
Dasauki bankoma ba tukun tabashi ansa don tasan intace mishi taje zedameta da tabashi details kokuma me likitan yace bayan itakuma ba zuwa tayiba tagaji dazuwa asibitin shiyasa takoma na bokan ta kawai………
Cikeda damuwa Mai Martaba yace baki koma bakuma ke miyasa kina wasa da lafiyarki ne Magajiya? +

Dan dafe kai tayi aranta tana”nagudu ban tsiraba”,kafin afili kuma tace”zanjeni ae yanzuma wata magana nazo muyi”……..

Zama yayi bakin gadonshi tareda kallonta sannan yace”inajinki”……

Matsowa tadanyi tanason taba jikinshi cikin sauri yajanye tareda cewa Magajiya sauri nakeyi zanshiga fada kifadi matsalarki first………

Dan janyewa tayi ranta badadi sannan tace daman maganar kula da household dinnan ne inaganin yakamata abama daya daga cikin Daughter in-laws namu kaga ni girma yazomin gakuma rashin lafiyar danakeyi shiyasa nakeson insauke wannan nauyin akaina sannan suma befi experience garesu ba tunda wataran sudinne zasuzo sucigaba dayi din………..

Dan shiru yayi yana nazarin maganarta kafin yace zanyi tunani akai…..
Godiya tayi mishi sannan takoma bangarenta……

Bangaren su Afiya kuwa se shiri sukeyi wai za a tafi dauko Sumayya koda sukayima Asma’u magana cewa tayi bata fadawa Yaya Almustapha ba so bayanda za ayi tafita…..

Amira ne tace kikirashi mana, murmushi tayi tareda daukar wayarta don kiranshi don Allah yagani Itama tanason tafiyar tunda tun zuwanta babu inda taje amma koda takira lambarsan akashe take fuskar tausayi tayi sannan tace”wayarshi akashe”……
To muje mana ninasan ko maganarma bazaiyi mikiba cewar Afiya Amira kuwa tsaki tayi tana bazaima san tajeba wallahi Yaya Almustapha harwani damuwa yayi da Al amuran mutane?……..
Dariya Asma’u tayi sannan tazauna”bazaku gane bane ba shi aure is base on sacrifice and yin biyayya ko bai san naje ba Allah yasani tunda shi yana ganina kuma akwai ranar hukunci I need to get his permission first kuje kawai Allah beyi zanjeba ne”………
Shiru sukayi mata don jikinsu yayi sanyi tunda tabbas sunsan gaskiya take fada daga karshene Amira tayi karfin halin cewa hakane kuma Allah baiyi zakijeba kuma ma itanma saukan dare zatayi kilan Yaya Sulaiman yace mubari sai gobe mutaho dasafe don Abba bayason ana tafiyar dare……….
Gyada musu kai kawai tayi tafice tabarsu sunata shirye shiryensu…….

*****
Dayanma wujajen karfe biyar ana yima Magajiya massage din kafa Laure tashigo dakin hannunta daukeda kwandon kayan itatuwa da alama daga lambu take……..

Dubanta Magajiya tayi sannan tace kigyara min fruits dinnan yanzu kikawomin cikin sauri Laure tayi kasa da kanta sannan tace”nawanke Uwargijiyata sauran inyanka ne”……

Zokiyi to Magajiya tayi maganar tana dan sosa jikinta tarasa miyasa maganin da boka yabata befara mata anfaniba haryanzu it seems like worsening kaikayin ma yakeyi…….
Dakyar tace Laure mikomin wayana akan mirror gyada mata kai Lauren tayi kafin tadauka tamika mata duban yarinyar dake mata Massage din Magajiya tayi sannan tace
“tashi kije ya isa hakanan”……….

STORY CONTINUES BELOW


To Uwargijiyata yarinyar tabada ansa sannan tatashi tafice abunta…..
Maida hankalinta kan wayar tayi kafin tayi dialing wani number ta kara akunne dukda kuwa takure volume wanda harna kusa da’ita na iyaji……..

Daukar wayar akayi dafari aka fara mika mata gaisuwa donkuwa Laure dake cire kwallayen cikin kankana tanazaune gaban Magajiyan tanaji……

Lafiya lau Matawalle ya aiki?…
Munata fafatawa ranki shi dade yanzuma munfito daga Funtuwan badede zamu shiga mota mu taho gidane……….

Murmushi Magajiya tayi”to yayi kyau yamaganar mu inadai fatan baka cikin mutane?”…..
Ah haba ranki shi dade na’isa kinsan yan sa Ido Allah yayi yawa dasu komawa nayi gefe koda kika kirani kuma maganarcan nariga na bula tayar motar Yariman yau daga shi har drivern nashi babu wanda zaiyi rai,yau karshen sa yazo ranki shidade ki kwantar da hankali don Yarima Sulaiman seya zama Sarkin Zaria ko anki ko anso,wani irin murmushi Magajiya tasaki don bakaramin dadin maganganun Matawallen tajiba sannan tace ka tabbatar babu wanda yajine?”…….

Na tabbatar rankishidade…..
To sekun iso da gawar sabida wannan shine gudumawar danakeson kukawo wa Mai Martaba nikuma nayimaka alkawarin gagarumi. Kyauta……
Dariya Matawalle yashekeda sannan yace “angama ranki shidade”,nan tayi masa sallama ta katse wayar tunda Magajiya tafara maganganu Laure jikinta ke rawa gawani irin zufa datake keto mata…
Bakaramin tashin hankali tashiga ba aranta tana”nashiga uku na kaddai Yarima zai mutu”…….
Kallonta Magajiya tayi tana dariya kafin tace”anjima zan baki kudi kikaima Matawalle in sun iso”……
Cikin sauri Lauren ta gyada kanta tana..
“to Uwargijiyata”,dukda kuwa hankalinta baya jikinta don babu abunda tafi bege ayanzu daya wuce taganta gaban Hajiya Muniba because only she can help Yarima may be… …….
Kallon Laure Magajiya tashigayi ganin tadai na gyaran kankanan sannan tace”ke lafiyarki?”…..
Lafiyata kalau takarashe maganar tana faking smile dakyar ta’iya gama gyara kankanan sannan tashiga mikama Magajiyan dai dai tanaci hankalinta kwance harta gama ta sallame ta…….
Tana fita ah dakin tashiga sauri kamar kafarta zaiyanke daga karshe ma gudu tafara ganin takusa isa gidan Hajiya Muniba din yau ko sallama batayiba bare Hajiya Muniba tayi tsanmanin zata gaidata….
Haki take sosai sega hawaye kuma “nashiga uku Ranki shi dade Magajiya zata kashe Yarima Almustapha”…..
Cikin sauri Hajiya Muniba tatashi tana”Laure lafiyarki kinsan mekike fada kuwa?”,tayi maganar hankali tashe itadai Laure se aikin kuka takeyi tana kije kitaimakeshi don Allah lokaci yana kurewa…..

Ganin kaman Lauren bata cikin hankalinta yasa Hajiya Muniba tashiga jijjiga ta tana”kimin bayani Laure yanda kikeyi dinnan bashi zaisa ingane mekike nufi ba”……
Goge kwallah Laure tashigayi dukda basu daina zubowa ba sannan tace”dagaske nikeyi jinayi tana waya wai asace tayan motan Yarima kinsan sunyi tafiya dasafe”……
Cikeda tashin hankali Hajiya Muniba tace”tabbas Mai Martaba yacemin yau Almustapha zeje rabon abinci kauyika,tasaka an bula tayar mota kikace kominene?”….
Eh Ranki shi dade harma zasu kamo hanya kuma motar da Yariman ke cikine………
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Hajiya Muniban ke furtawa cikeda tashin hankali “She need to save him but how?”……
Kallon Lauren tayi tana tunanin wani mataki zata dauka jitayi Laure na kozamu fada ma Mai Martaba yakira shi su tsayar da motar……
Hakane kuma cewar Hajiya Muniban kafin tace amma bazaki shiga cikin maganar nanba Laure your life could be in danger kinji…..

To amma..
Daga mata hannu Hajiya Muniba tayi sannan tace ninasan yanda zanyi ke kikoma gurin uwar dakin ki kadama tayi suspecting wani abu Magajiya is so cunning she can go to any length…..
Ina ah daki tayi wayar kikace?…..
Gyada mata kai Lauren tayi kafin Hajiya Muniba tace kijeki ninasan yanda zanyi da maganar nan………
Cikin sauri Hajiya Muniban tafice batareda tasake bi takan Lauren ba koda ta’isa bangaren Mai Martaba bayanan wayarshi tashiga kira bejimaba yadaga cikeda tashin hankali tace “Ina bangarenka kazo don Allah akwai important magana”,bata jira cewarsaba takatse call din bin wayar yayi da kallo yana mamakin wace irin important magana ne haka dukda kuwa daga muryarta zakasan cewa tana cikin tashin hankaline don haka yatashi daga fadar yayi bangaren nasa cikin sauri….
Ah tsaye yasameta tanata safa da marwa acikin dakin….
Muniba lafiya,meya faru kika kirani haka?…

STORY CONTINUES BELOW


Batajira yakaraso cikin dakin ba tayi saurin karasawa gabanshi tareda riko hannunshi cikin nata”kakira Yarima don Allah kace su tsaida motarsu”….
Cikida rashin fahima yace..
“kaman Yaya?”…..
Kaman zata saki kuka tace…
“kafada mishi kaidai it’s really important now,his life is in danger”…….
Ware idanu yayi cikeda tashin hankali”Muniba fadamin meyake faruwa,what do you mean by his life is in danger?”……
Kaidai kakira please yanzu safety din shi shine first takarashe maganar wannan karan hawaye sunfara zuba sabida takasa controlling dinsu…….
Allah yataimakeshi wayarshi na hannunshi cikin sauri yashiga dialing number din Almustapha hannunshi na karkarwa amma not reachable yake cewa yakira yafi sau goma amma thesame thing yake cemasa………
Hankali tashe yace”baya tafiya call din kifada min meya faru please?”……
Tana hawaye tashiga masa bayani”daya daga cikin bayi ne tazo tasameni yanzu hankalinta tashe wai taji wani yana waya kan akashe Yarima infact har ansace tayar motarsu ma………..

Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda mai Martaba yashiga maimaitawa yayinda kafarsa ma takasa daukarsa dakyar ya’iya zamewa yazauna ah tsakiyar dakin cikin sauri Hajiya Muniba tace we’ve to find a way out ranka shidade………
Dagowa yayi yana kallonta da idanu jazir kafin yace”who’s behind this?”…….
Cikeda damuwa Hajiya Muniba tace yanzu bawannan bane damuwar Mai Martaba musan halinda Yarima yake ciki shine the most important…….
“I said who’s behind this Muniba!”,yayi maganar rai bace gakuma tashin hankali duk alokaci guda……
Hajiya Muniba data zabura tace I don’t know yarinyar ma cewa tayi batasaniba sabida bataga fuskar wayeba…….
Lumshe idanu Mai Martaba yayi yayinda Hajiya Muniba tashiga consoling dinshi”don Allah being weak won’t help mutashi musan abunyi”…..

Cikin sanyin murya Mai Martaba yace anfada miki since tayar mota wasa ne Muniba is not as if nayi giving up kawaidai narasa abunyine I’m not my self now yakarashe maganar tareda dora kanshi kan kafafunshi Allah ne kadai yasan halin dayake ciki yanzu, Allah ne kadai yasan irin abubuwan dayajeji aranshi yanzu gawani juyi dayake jin kanshi nayi mishi lokaci guda….
Fuskar Almustapha ne kemishi gezau ah idanu tun yana little boy with that his charming smile……
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine kalmomin da Mai Martaban ke maimaitawa ko Allah zaisa yasamu sauki aranshi ya iyayin wani abun……
Hajiya Muniba ganin Mai Martaba baya cikin his normal self yasata saurin daukar wayar nashi tashiga kiran Dad cikeda damuwa tace”Yaya don Allah kaxo bangaren Mai Martaba”….

Batajira amsar saba tacigaba da kiran layin Almustapha ko Allah zaisa yashiga amma still not recheable gashi ita basanin number wani tayiba dasukayi tafiyar tare bare ta kira anacikin hakane Dad yashigo nan take fada mishi halin da akaciki……

Cikin sauri yace let me call him right now….
Wayarshi bata shiga tabashi amsa,still daukar wayarshi yayi yashiga kiran layin wasu daga cikin fadawan dasuka tafi tare amma duka daga me waya ah kashe se me not recharge…….

Subhanallah cewar Dad hankali tashe kafin yashiga kiran layin Sulaiman ba ajimaba yadauka……
“Kuna inane?”….
Muna kaduna Dad wani abu yafaru ne Sulaiman yayi tambayar cikeda curiosity jin yanayin muryar Dad din…….

Sabida kada ya tada masada hankali yace”kunyi waya da Yayanka recently ne?”……
Eh munyi Dad yacemin zasu fita ah Funtuwan Badede………
Alright shikenan daman nakirashi wayar bata shigane se anjima…….
Shikeda rashin damuwa da zancen Sulaiman yace may be network problem ne Sulaiman din yabama Dad din ansa….
Yea probably cewar Dad din kafin ya katse wayar….

Duban Muniba da Mai Martaba yayi hankali tashe sannan yafice daga dakin atake yasa akamishi arranging mota yace daya fito sallar maghrib zasuje police station sukai report sannan sukama hanyar Funtuwan badede…….
Mai Martaba dakyar ya iya tashi yayi sallar maghrib shima adaki don yakasa fita kwata kwata……

Koda Dad din yatashi tafiya bebi takan Mai Martaban ba don yasan zai iyacewa zai bishi sede he’s not in a state to follow him……..
Kan kaceme labari yagama karada masarautar cewa ga abunda yake faruwa daga bayin har dogaraye dama sauransu kowa yashiga tashin hankali tareda addu’ar Allah yasa kada wani abun yasamu Yariman……..

STORY CONTINUES BELOW


Bangaren Magajiya kuwa dataji labarin bakaramin tashin hankali tashiga ba don haka tayi saurin yin bangaren Mai Martaba don babu abunda yafi damunta kaman taji shin an ambaci sunanta ne ko yaya……..
Koda taje samun Mai Martaba tayi zaune kan sallaya yana addu’o’i yayinda Hajiya Muniba kezaune bakin gado don tana fashin sallah Itakam…….

Dagudu takarasa cikin dakin tareda rungume Mai Martaba tabaya tana kukan munafurci”nashiga uku na wai maiyake faruwa damune acikin Masarautar nan,miyasa za ace Yarima yamutu
“………..

Hajiya Muniba dake gefe tana hararan Magajiya tace”cemiki akayi mutuwa yayi?”, takarashe maganar tana hararta……

Dukda kukan da Magajiya keyi seda ta dago tana karema Matar kallo donkuwa yaune first encounter dinsu koda suka hada Ido seda taji gabanta yafadi donji tayi kaman tasan idanun nan amma seta daure tacigaba da act dinta”nibacewa nayi yamutuba amma dai kinsan in ansace tayar motar babu abunda zai hana accident faruwa kuma irin wayannan hatsarin dakyar mutane ke rayuwa dukdama muna fatan shidin ya rayu sede nasan ba lallai yadawo kalauba”,takarashe maganar tana kukan munafurci..
….
“Mai Martaba tureta yayi ta baya ranshi bace yayinda Hajiya Muniba tace”Amma kinbani mamaki wallahi amatsayinki namai hankali dakuma shekaru irin naki banyi tsanmanin irin wayannan magan ganun daga garekiba, inbazaki fadi alkhairi ba kiyi shiru please”……
Kuma maganar cewa dakikayi babu abunda zai hana accident kuwa akwai tunda Allah nanan kuma shine meyin komai hakanan yana iyacanza al amarinsa aduk lokacin dayaso……..

Wani kallo Magajiya tayi mata tana shirin yin magana Mai Martaba yace dukansu su fita su bashi waje he wants to be alone don shi maganarsuma haushi yake bashi he’s worried about his Son sukuma argument ma sukeyi………..
Koda suka fitan harara Magajiya tabi Muniba dashi tana kifita idanuna banason shishigi bakisan wacece niba ah to……
Murmushin takaici Hajiya Muniba tayi sannan tace”banida lokacin ki yanzu sabida halin da ake ciki”takarashe maganar tareda wucewa bangaren ta……

Koda su Dad sukaje police station sukayi report cemusu akayi zasu kira mutanensu nacan ah bincika ko anyi accident ah hanyarnan so there is no need for them to go there sukoma gida kawai insha Allah zasu bincika musu adaren nan……
Babu yanda Dad ya’iya haka yadawo gida gurin dan uwansa yana keeping nashi company……..

******
Fitowarta daga wanka kenan shiryawa tayi tsaf cikin simple doguwar riga na material kafin tafeshe koina najikinta da turare

shimfida sallaya tayi ta tada sallah haka kawai setakejin gaban ta na wani irin mugun faduwa ahaka dai harta idar da sallah duba time tayi ganin Isha yakusa kawai setace bari tajira tayi sallar Isha din……
Seda tayi Isha sannan taninke sallayar ta maidashi ma ajiyinsa fita tayi ah dakin gabadaya yau setakejin gidan shiru sabida su Amira ma baswa nan daga ita se bayin ne kira tashiga kwalama Salma baiwarta……..

Cikin sauri tazo kanta akasa tace”gani Gimbiya”…..
Ankai abincin su Abba ne dana Mom…..
Jijjiga kai Salma tayi alamun a’a cikeda mamaki Asma’u tace to me ake jira tunkan nashiga wanka nace azuzzuba abincin su iya Hindatu baswa gurin ne?……
Suna gurin yanzu za akai Salma tabata amsa ahankali tabe baki Asma’u tayi sannan tace daukomin na Yarima inkai dakinshi nasan by now ya’iso gida…….
To kawai Salman tace kafin tajuya takoma kitchen din……..

Asma’u nanan tsaye har kusan minti biyar ba akawo abincin ba aranta tana yau meke damun mutanen nan ne gabadaya they’re not active at all…
Gajiya tayi da tsayuwar tawuce kitchen din don daukowa dakanta sede to her own surprise lokacin ne ma rukayya ke kokarin sauko da coolers din daza asa abincin………

Bin su Jamila da Hindatu tayi da kallo ganin duk fuskarsu badadi da alamar suna cikin damuwa…
Cikeda mamaki tace”subhanallah wani abunne yafaru naganku kunyi tsage tsage kaman wasu marayu?”…….
Hindatu ne tayi karfin halin cewa babu komai Gimbiya…..
Dukda bata yarda dame tacedinba setace to meya hanaku zuba abincin tun dazu?……
Kame kame suka farayi batareda tabi takansu ba takarasa cikin kitchen din takarbi ludayin tashiga zuba masa abincin nasa tana…
“ayya yau Yaya Almustapha shikadai zaiyi dinner Yaya Sulaiman bayanan”…….
Jamila kasa controlling tears dinta tayi don hakama tafice ah kitchen din cikin sauri Asma’u kuwa gama zuba abincin tayi tasaka ah tray sannan tafice abunta dakinshi tawuce straight tayita knocking amma shiru turo baki tayi tana”he likes being so arrogant ana zakal kale namishi girkin ma”……..
Tura kofar tayi ahankali sannan tashiga dakin nashi sede to her own surprise wuta akashe Allah yataima keta wayarta na hannunta don haka takunna haske kafin tanemi switch na wutan dakin takunna koina na dakin fes yake agyare kaman yanda yake tunsafe da alama ma babu wanda yashigo……

STORY CONTINUES BELOW


Ajiye tray din tayi kan stool kafin taduba toilet nanma shiru babu kowa fitowa tayi ah dakin tana kiran Hindatu…..
Cikin sauri takaraso tana gaidata…
“Yarima bai shigo bane daman?”….
Gyada mata kai Hindatu tayi jiki ah sanyaye,ikon Allah tokodai yatsaya gurinsu Mai Martaba ne kafin yashigo don anjima da idar da sallar Isha yanzu to 9:00pm fa……..

“Inagani hakan ne Gimbiya Hindatu takarashe maganar idanunta sunciko da kwalla”,cikin sauri Asma’u takaraso gabanta tana meyake faruwa ne naga fuskokin ku duk babu walwala batakai ga rufe bakiba taga hawaye nazuba idanun Hindatu….
Subhanallahi why are you crying Iya Hindatu,wani abunne yafaru?…..

Hindatu kasa holding tears dinta tayi gawani tausayin Asma’u datake ji yasata juyawa zata tafi lokaci daya bugun zuciyar Asma’u yakaru shan gaban Hindatu tayi tana kallon ta”meya faru,kifadamin meya faru please wani abunne yasamu Yaya Almustapha kosu Amira tayi mata tambayar cikeda tuhuma?….
Shiru Hindatu tayi tana hawaye still,wani irin tsawa Asma’u tayi hankali tashe”kifada min mana,meya samesu?……
Murya na stammering Hindatu tace”babu Gimbiya”……

Jijjiga ta Asma’u tashiga yi tana”karyane kifadamin,su Amira ne?”…..
Jijjiga kai Hindatu tayi alamar aa,cikeda tashin hankali murya na karkarwa tace”Ya..ya almus…ta..pha ne?”……
Yanda tayi maganar bakaramin tausayi tabama Hindatun ba hakan yasa kukanta yakaru harta kasa bata ansa…
“kifadamin mana meya sameshi Iya Hindatu?”…….
Takarashe maganar tana hawaye maganan datayi da karfine yajanyo hankalin sauran bayin sukayo parloun dasauri…..

Jamila ne takaraso Itama tana kuka tace”Gimbiya don Allah kikwantar da hankalinki babu abunda zaisameshi”……
Wani irin kallo Asma’u tayi mata sannan tasaki Hindatu tadawo kanta tana kuka me tsuma zuciya”nayarda dake Iya Jamila nasan ke bazakimin karyaba,kifadamin don Allah meyasamu mijina takarashe maganar tana folding hannunta alamar roko”…….
Babu abunda Hindatu da Jamila keyi se hawaye haka wasu daga cikin bayinmma…
“Don Allah kifada min amma karkicemin yamutu please i can’t bear it,zuciyata bazata iya daukaba he can’t just leave me like this we’ve a long way to go,our journey has not been completed yet don Allah kifadamin ina Yaya Almustapha Asma’u takarashe maganar tana damke da rigar Jamila duk ta cukwiwuyeta”………
Kuka Jamilan take Itama tareda rungume Asma’u din janyewa Asma’u tayi daga jikin Jamila tana bazaki fadamin ba?….
Kema dana yarda dakedin yau bakida bakin sa zuciyata tayi sanyi?…..
Yanda Asma’un keyi dukwanda ke gurin seya tausaya mata suna cikin hakane sukaji anbude kofa cikin sauri tace”kingaba nacemiki bazai taba barina ba”, takarashe maganar tareda juyawa tayi hanyar kofar da gudu da zummar ganin Almustapha din sede to her own surprise Dad da Abba dakuma Mom tagani………….
Tsayawa tayi cak kafarta takasa daukarta don ganin yanda fuskokin su yake yasa bugun zuciyarta kara karuwa Mom ne takaraso gabanta cikin sauri tana”Daughter”……

Hawaye Asma’u takeyi tace…
“Mom inayake don Allah?”….
Sun iso ko,hope sun iso lafiya?…..
Cikeda tausaya wa Mom tajata jikinta Itama idanunta sunciko da kwallah tana”kidaina kuka insha Allah Almustapha will be fine”……..
Lamo tayi ajikin Mom din tana…
“yana Ina don Allah kikaini gurinshi Mom”…….
Ganin Asma’un is not in her right senses yasa Mom cikeda rarrashi tace”zankaiki Asma’u, I’ll take you to Almustapha kidaina kukadai yanzun”……..
Dagowa tayi daga jikin Mom din tashiga share kukanta”Allah nadaina Mom kikaina don Allah I want to make sure he’s fine by looking at your faces nasan ba lafiya ba”,kama hannun Mom din tayi tana shirin janta cikin sauri Dad yace compose yourself Asma’u you can’t see Almustapha now……
Muma bamusan halin dayake cikiba bincike akekanyi tukunnan…….

Sakan baki tayi tana kallon Dad din shima kallonta yakeyi cikeda tausaya wa ana cikin haka kuma se wayarshi tashiga kara dagawa yayi dasauri yana officer ansamu wani news ne please?…….

Daga daya bangaren ne officer yace”eh yallabai”….
Yanda yaji muryar officer din ya tabbatar akwai damuwa don haka yace kafadamin meyake faruwa don Allah….
Murya akarye officer din yace…
“I’m sorry ansamu motar kunce marcedese ba?”…..
Cikin sauri ya gyada kai kaman wanda yana gaban officer dinne kafin dakyar ya’iya cewa eh marcedese ce….
“I’m sorry Allah yayiwa mai motar rasuwa it was a very terrible accident sundauki body dinma zasukai hospital gobe dasafe sekuzo kukarba, Allah yajikanshi sede sunce driver din is still alive anyi rushing nashi to the hospital”……..
Cire wayar Dad yayi daga kunnenshi batareda ya katse call dinba yayinda yashiga furta innalillahi wainna ilaihir rajiun…….
Innalillahi wainna ilaihir rajiun…
Cikin sauri Mom tace meya faru,kafada mana mana please…….
Idanun Dad sunyi jazir dakyar ya’iya cewa”babu abunda Almustapha ke bukata irin addu’armu ayanzu”…….
Daganan yakama hannun Mai Martaba dako magana baya iyayi suka fice ah bangaren Asma’u wani irin hajijiya tadinga ji yana dibanta yayinda tafadi ah sume kanta su Jamila sukayi suna kuka mai tsuma zuciya suna kiran sunanta ……
Daukanta sukayi suka kaita daki Mom nabiye dasu abaya cikeda tashin hankali……
Salma ne takawo ruwa cikin sauri aka shiga yayyafama Asma’u din aikuwa tafarfado kuka tashigayi kamar ranta zaifita Mom ne takaraso gabanta tana…
“Compose yourself Asma’u babu abunda Son ke bukata agurinki irin addu’ar ki,stop crying please”……
Murya ah dushe tace”Mom kema kinyarda yamutu?”…..
Ninasan bemutuba,wallahi Yaya Almustapha baimutuba jikina yana bani he can’t just leave me like this………
Kowa saida yatausaya ma Asma’u tsabar yanda taketa sambatu……….
Mom daga karshe kasa controlling tears dinta tayi Itama tashi tayi tafita…..
Asma’u nata ita tasan Almustapha baimutuba sudaina daura mishi mutuwa……
Jamila ne tace kiyi hakuri Gimbiya yakamata kikarbi kaddararki hannu bibbiyu Yarima adduarki yake bukata………….
Sa hannu Asma’u tayi aduka kunnuwanta tana”kudaina fadamin irin wannan maganar please,kufita kubarmin dakina ninasan mijina bai mutuba takarashe maganar tana nuna kanta”mijina bai mutuba we’re still on the journey he can’t just leave me on the way”…..
Tashi tayi ahankali tafice daga dakin straight dakin Almustapha tawuce shiga tayi tana karema dakin kallo komai nasane yashiga dawo mata arai tundaga farkon haduwarsu harzuwa yau……
Karasawa tayi bakin gadon tazauna tareda daukar pillown shi tarungume tana shakar kamshin turarenshi”you can’t just leave me Mr Taciturn,we still have a long way to go”…….
Tana kuka tana maimaita thesame thing tafi awa biyu ahaka lokaci daya tabi takoma kamar wata marainiya kafin tafara jin ana bubbuga kofa Jamila ce”Tana Gimbiya kibude kofar don Allah”……..

Cikin kuka Asma’u tace”bazan budeba inacewa kuke Yaya Almustapha na yamutu,bazan bude ba fushi nike daku duka tayi maganar kamar wata tababbiya hawaye nabin kuncinta”………….Cigaba da bubbuga kofar Jamila tayi tana kibude Gimbiya don Allah zakiga miyasa nace kibude kofar…….. +

Make kafada Asma’u tayi kamar wanda tana gaban Jamilan…
“uhm uhm bazan budeba nikam nasan wayau kukemin kibarni don Allah ninasan mijina bai mutuba Iya Jamila”……

Jamila dake bakin kofa tadubi Dad da Mai Martaba tana”taki budewa rankashidade bansan yazanyi da’ita ba kuma”…..
Dan ajiyar zuciya Mai Martaba yayi dukda dawowan Almustaphan hakan baisa shock din dazu yagama fita daga idanunshi ba dan duban bangaren da Almustaphan yake yayi sannan yace…”
“why don’t you take care of your wife Son,she needs you now only you can calm her down”….
Amma Abba kaifa are you still alright…..
Dan dafa kafadarshi Mai Martaba yayi idanunshi sunciko da kwalla”i thought I loose you for the second time,but alhamdulillah I’m fine now”, Mai Martaba yakarashe maganar yar siririyar hawaye dayajima yana makewa seda ya ziraro cikin sauri Almustaphan ma ya rungumi mahaifinnashi cikeda kaunarshi yanzukam ko duk duniya zasu taru sucemai Abba bayasonshi bazai yarda ba dubada yanda yadamu dashi ada dinma circumstances ne dakuma Allah yakadarta zasu rabu kamar yanda Dad yafada mishi………..
Tapping bayanshi Mai Martaba yadingayi kafin yasake shi yana
“go to your wife I’ll be fine”…..
Gyadawa Mai Martaban kai yayi yayinda suka juya duka suka fice suka barshi shikadai tsaye agurin……….

Karasawa yayi dabda kofar dakin ahankali kafin yashiga knocking cikeda nutsuwa……..
Kin kulashi tayi don duk azatonta su Jamila ne sabida tagaji dayi musu bayanin cewa bazata bude dinba……….
Yafi 5minutes yana buga kofar bata budeba ahankali yakai bakinshi kusa da kofar cikin cool voice dinshi yace…
“Asma’u!”……
Dukda irin kukan datakeyi behanata gane muryarshiba lokaci daya ta tsaida kukan tanajiran jin yasake kiranta shikuwa jin tayi shiru yakuma cewa..
“Asma’u!”…
Aidasauri tatashi daga kan gadon ta ta’isa bakin kofar dakin tana sosa kunnenta sannan takai kunnen jikin kofa still tana sheshekar kuka jin tanakusa ne yasashi cewa..
“Are you there?”….
Gyada mishi kai tayi kamar wanda tana gabanshi sannan tace…
“uhmm, dagaske Kaine Yaya Almustapha ba illusion nakeba?”……

Yanda tayi maganar sedayaji zuciyar shi tayi wani iri gawani tausayinta daya shigeshi lokaci guda da muryar dabaisan yanada itabama yace..
“it’s me,open the door kinji?”……
Kama kofar tayi tashiga budewa ahankali kamar wata mai tsoron kada tabude taga bashidin baneba aikuwa tana budewa figure dinshi yayi appearing agabanta kallonshi ta tsaya tanayi tana kuka mai tsuma zuciya harda rufe baki ko Allah zaisa ta’iya controlling tears din nata da gudu kuma ta’isa gabanshi tashiga bugun kirjinshi”miyasa kaki dawowa dawuri,you don’t even know how worried i was about you harcewa akeyi ka mutu does this make you happy,ana dora maka mutuwa?”…….
Shidai ko gezau beyiba haka taita dukan kirjinshi tana kuka kafin ta riko wuyan riganshi tana karemai kallo ganin ko gezau beyiba cikin damuwa tace…..
Are you not sorry for making me cry?……
Kallon pierced eyes dinta yayi wanda ke dauke da abubuwa kala kala daya kasa gane menenesu sannan yace..
“I’m”…..
Sake bugun kirjinshi tayi da karfi wannan karan…
“Then say sorry”…..
Muryarshi na cracking besan sanda yace”sorry”dinba…
Fadawa tayi jikinshi tareda rungumeshi so tightly as if her life depends on him…..
“I love you Yaya Almustapha,I really do love you bazan iya rayuwa babukai ba hakanan bazan iya barin wani abu ya samekaba and if that happens I’ll be shattered”, takarashe maganar tana kuka ah physique kirjinshi……
Lumshe idanunshi yayi don tunda tafara fadan wayannan kalmomin yakejin zuciyar shi nayi mashi wani,irin feeling din dabai tabajiba ah rayuwarshi because this’s the very first time in his whole life dawata mace tabudi baki tafadi wannan kalmar directly to him so,it really feel some how,a bit weird harma yarasa abunyi because he’s out of words, totally out of words!……….. 1

STORY CONTINUES BELOW


Dagowa tayi tana kallon kyakyawar fuskarshi sannan tace you know sunacemin ka mutu naki yarda because somewhere in my heart I know you’ll never leave me all alone,we still have a long way to go and this is just the beginning of our journey Yaya nasan bazaka taba barina bako?”….
Tayi masa maganar tana kallonsa shima kallon nata yakeyi babu ko kiftawa ga fuskarta duk yayi ja idanunta sun kumbura tsabar kuka lips dintama sunyi swelling dan jijjiga shi tayi wanda yafitar dashi daga trance dinsa……..
“Bazaka barni bako, I’m asking you?”…..
Besan lokacin daya gyada mata kaiba ahankali sake komawa tayi cikin jikinshi tana”thank you”,sannan bata daina kukan ba jin kukan yafara damunshi yasa hannunshi na karkarwa yadan zagaye waist dinta tareda engulfing nata in a very warm hug too…….
Cikin rada yace
“what’s the crying for Asma’u,bagashi nadawo ba I’m save and sound”……
Sake shigewa jikinshi tayi wanda yasashi fara feeling uncomfortable don haka yace…
“it’s very late now kije kikwanta nima zantafi dakina”….

Cikin sauri tamake kafada”aa nikam,I want to stay right here with you” takarashe maganar tana kara shigewa jikinshi kamar wanda za asaceta don gani take intabarshi yatafi washegari dasafe ma cewa za ayi ya mutun dagaske.. …….
Cikeda damuwa yace bazan sake tafiya ba you’ll see me tomorrow……

Sake make kafada tayi dan ciro hannunshi daya yayi daga jikinta tareda dafe kaishi shikanshi yarasa miyasa yake biye mata………
Muje kikwanta to sake girgiza mai kai tayi alamar bata yarda ba, alright I’m not going anywhere muje tare……
Dan dagowa tayi dakanta tana kallon shi”dagaske?”….
Gyada mata kai yayi ahankali rike hannunshi tayi gam cikin nata harsuka isa bakin gadon kafin yace to hau kikwanta I’m right here………
Aa sede mukwanta tare zaka gudu kabarni,ware idanu yayi cikeda mamaki itakuwa babu abunda yaxo ranta haikan manikan take fadar gaskiyar ta……
Batarai yayi tareda juyamata baya saurin janyo hannunshi tayi wanda yasa yayi loosing step suka fada kan gadon dukansu biyu kokarin tashi yakeson yi amma ta rungume shi kamkam……….
Babu yanda ya’iya haka yabarta batareda yakuma cewa komaiba Itama batasake maganaba seji yayi tana sauke numfashi alamun tayi bacci kokarin tashi yakumayi amma taki sakinshi kwata kwata hakan yasa yayi giving up yagyara kwanciyar shi tareda jamusu bargo ya lullubesu Allah ne kadai yasan yanda yakeji donkuwa ko bacci kasa wa yayi tunanine kala kala ke yawo ah kwanyarsa hakanan yake tuna kalamanta na dazun……
So,she love him but how,yaushe daman akwai macen dazata soshi arayuwa bayan duk abubuwan da ake accusing dinshi akai,he really find it very hard to believe sede from all indication Asma’u iya gaskiyarta take fadi he can see the truthfulness through her shiny eyes………..
If she really have feelings for him toshi yasan he can not love her in return sabida he’s not the perfect match for her seyanzu yakejin she’s somehow too good for him,he’ll let her go as soon as yayi proving nasu innocent sabida taje ta auri perfect guy wanda zaikula da’ita yakuma yi reciprocating love dinta sede before that he has to change his ways yakamata yadaina mata wulakanci atleast she cares………
Wayannan sune tunanin dayayitayi ah daren yau harma besan sanda bacci barawo yayi awun gaba dashiba……..

Itace tafara tashi daga daddadan baccin da takeyi jitayi kaman abu mai nauyi ajikinta cikin sauri tadansa hannu don turewa amma setaji jikin mutum bakaramin tsorota tayiba hakan yasa tayi saurin yaye blanket din daga kansu arba tayi da kyakyawa fuskar Almustapha yana baccinshi peacefully ahankali abunda yafaru jiya yafara dawo mata daya bayan daya tashi tayi tazauna jikin sauri bayan tacire hannunshi daga jikinta yau na shiga ukuna menayi nikam,meyakai bakina furta wayannan kalaman jiki ah sanyaye cikeda nadama tadubi wall clock din 6:32am alamar sun makara sallar asuba”innalillahi wainna ilaihir rajiun” shine abunda take fadi kafin tashige bandaki don dauro alwala koda tafito baya dakin yafice hamdala tayi don ayanzu babu abunda tafi jin kunya irinshi sekuma iyayenshi datayita baran barama agabansu itakam tashigesu yanzu dawani idanu zata kallesi fisabilillahi wannan abun kunya dame yayi kama takarashe maganar tareda dan bugun kanta…………

STORY CONTINUES BELOW


Dakyar ta’iya tayi sallar asuba seda tagama addu’o’inta sannan tawuce kitchen already su Jamila se aiki sukeyi,gaishesu tayi kanta akasa……
Sukam se murmushi sukeyimata(kungane irin murmushin nan na gulmakaida kayi abu daka gani zaka gane manufar murmushin)…….

Ya darenki cewar Jamila,murtuke fuska Asma’u tayi lafiya Lau Iya Jamila harkun fara aiki ashe…….
Bakomai aimunsan kina tareda Yarima shiyasama nace karsu tasheki yau din jitayi kaman ta nutse tsabar kunya daga karshema komawa daki tayi abunta tadale gado sekuma tafara jin kamshin turarenshi ahankali taduka tana shinshinar bedsheet din murmushi tasaki tareda lumshe idanunta…
“it smells good”…..
Dakyar ta’iya tashi tayi wanka tasaka atamfa mekyau abunta lokacin har 10 na safe yayima kwankwasa mata kofa Jamila tayi….
kishigo mana iya Jamila,karasowa Jamila tayi tana murmushi sannan tace daman abincin Yarima ne angama hadawa shine nazo infada miki……..
Dan shiru tayi kafin tace kikai mishi iya jamila………
To kawai Jamilan tace sannan tafice ah dakin tawuce kitchen daukar abincin tayi takarasa dakin nashi tareda kwankwasawa………

Dakyar ya’iya cewa”Come in” don duk azatonshi Asma’un ne….
Bude kofar tayi fuskarta daukeda murmushi tana mika mishi gaisuwa……
Dukda ba’ita yayi tsanmanin gani awannan lokacinba behanashi maida mata murmushin ba ajiye abincin tayi sannan tace ga abincinka Yarima…….
Gyada mata kai yayi sannan tace inkagama Mai Martaba ya aiko yana nemanka ah fada………
To Iya thank you……
Ficewa tayi tana hamdala ga ubangiji daya dawo da Almustapha safe and sound………

Koda tafita zama yayi yana karema abincin kallo dakyar ya’iya budewa yayi serving kansa yaci dukda kuwa baida wani appetite shiyasama baici wani dayawa ba………..
Tun adaren jiya bayin sukasan da dawowar Almustapha din dukdama bakowaba shiyasa koda gari yawaye wasunsu basu sha wahalar samun labariba…..

Shadaya dot yafice zuwa fada anan yasamu su Dad, Mai Martaba da manyan manyan yan fada tunda yashigo ake mika masa gaisuwa samun guri yayi yazauna tareda gaida mahaifin nasa sannan yagaida sauran……………
Gyara zama Mai Martaba yayi sannan yace jiya we were all stressed out shiyasa bamu tambayeka maiya faruba tunda kadawo lafiya daman shine damuwarmu and alhamdulillah daya daga cikin fadawan yazo yafada mana yanda akayi sede still inason muji daga bakinka………..
Dan shiru Almustapha yayi kafin ya numfasa kanshi na kasa yafara magana dukda kuwa ranshi bayaso sede babu yanda ya’iya………

“Munfito daga Funtuwan badede dayanma sosai wanda it was third to the last village damukaje,I wanted to finish yesterday shiyasa nace musu muje Dorayi daganan se Loko mugama semu wuce gida I’ve no problem komun kai dare but unfortunately se motar daneke ciki tasamu matsala so driver din da daya daga cikin fadawan sukayi deciding mu mutafi kada muyi dare in an gyara motar they’ll follow us kaji yanda akayi Abba from then bansan meya faruba seda naxo gida nakejin wasu labarai daga bakinku” ………

Kowa shiru yayi ah fadan yana sauraron ikon Allah, Galadima ne yace ikon Allah kenan Allah yayi babu abunda zaisameka Yarima…….
Gyaran murya Mai Martaba yayi sannan yace kana nufin kenan bakuzo kunhadu dashi bafaden da driver ba?…..
Gyada Kai Almustapha yayi sannan yace”eh Abba we thought suntaho gida already”……
Salallami akashiga yi ah fadan yayinda Dad yace kenan motar can din itace and bafaden ne Allah yayimishi rasuwa?……
Gyada kai Abba yayi ahankali sannan yace innalillahi wainna ilaihir rajiun Allah yayimishi rahama…….
Amin ya Allah kowa ya amsa sannan Abba yace daman yasa aje asibitin aga dagaske motar tasu ne so by now yakamata suna hanyar dawowa……

Dad ne yakuma cewa tonaji Almustapha yace zasunemi car mechanic aeyakamata ace angyara motar……

Wannan karan Dagaci ne yace”kasan shi megyara in ankirashi problem din mota za afada mishi kuma da abunda akafadamishi zaiyi anfani so it might be possible basuyi realizing ba kuma koma miyene yanzu abakin driver zamuji inyasamu sauki”….

Almustapha ne cikeda rudani yace”accident sukayine?”…..

Gyada masa kai Abba yayi ahankali sannan yace someone was after your life anje ansace tayar motar dakake ciki muma wata baiwace tafada ma Hajiya Muniba shine tazo take fadamin we were very worried son but alhamdulillah it’s a miracle you’re safe and healthy…….
Shiru Almustapha yayi kafin yace ita yarinyar bataga wayebane ba?…..
I’ll investigate that after asr prayer yanzu we should focus on the janaza na bawan Allahn nan…….
Gyada Kai Almustapha yayi ahankali sannan yace”Allah yajikanshi”….

Amin kowa ya amsa da, bakaramin jijjiga Almustaphan yayi da mutuwarba haka kawai seyake tuna mutumin ah jiya he was so nice and gentle rayuwa kenan da may be shine ze mutu instead of him ashede darabon kwanan shi agaba damuwarshi wayene wannan,waye yakeson karar da rayuwarsa hakanan meyayi mishi sannan meya tare mashi………
Yana cikin wannan tunanin ne akace an iso da gawar jiki ba kwari yatashi suka fice don ayi mashi sutura…………


*Ga masu complain nabama Magajiya power dayawa kokuma asirinta yaki tonuwa I’m really sorry ni inayin littafina gradually ne bana rushing and inaso in isar da sakon danakeson isarwa acikin lumana da kwanciyar hankali if I’m making you wait for long I’m really sorry but believe me you won’t regret reading this book.with this inafatan zakucigaba dabin littafin har mukai karshe Allah yabamu ikon kammalawa baki daya Nagode! nagode! Nagode kwarai da kaunarku bansan Almustapha nada masoyaba se jiya,bansan GS nada fans harhakaba se jiya*…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page