KE NAKESO CHAPTER 2

KE NAKESO
CHAPTER 2

Sai dai a halin yanzu ba yadda ta iya, ya riga ya ganta. Ta karaso cikin taku a tsanake har inda yake tsaye a jikin motarsa. “Yallabai sannu da zuwa”.
“Lafiya kalau, sai godiya. Da fatan dai ban takura ki ba da zuwa na a daidai wannan lokacin?”
“A’a ba komai, ina maraba da kai. Bismillah ka karaso ciki mana”.
Alhaji Yusuf ya bi bayan jagorar da ta yi masa zuwa cikin gidan su, inda ta yi masa masauki a falon mahaifinta da bai faye tarkace ba.
Face kujerun zama da kafet a tsakiyar falon, sai ko T.V da ke ajiye akan teburin ajiye shi, wanda bai cika aiki ba, idan ka dauke kallon labaru da mahaifinsu ya kan yi da shi.
Ta dawo falon da abin jika makoshi, yayin da suka ci-gaba da gaisawa da Alhaji Yusuf. Mai-jidda dai ba abin da take kokarin yi.Irin ta danne balli-ballin da zuciyarta ke mata da kuma zufan da ke yawaita jika mata hannu, ta gyara lullubin gyalenta tana tunanin yaushe Alhaji Yusuf zai gama bayaninsa, ya sallameta.
Gaba daya amsa masa tayin sa babban kuskure ne a gareta, sai yanzu take ganin hakan.
Wanda kuma oganta ne a wurin aiki, tana ganin ya fi fahimtar inda ta dosa, yana kuma daga mata kafa ganin rashin da ta yi.
Yana da saukin magana damutane, ga shi da mu’amala mai kyau, haka duk sanda ya budi baki yayi mata magana, ta kan ji saukin radadin da ke ranta, hakan ya sa ta ba shi damar zuwa a karshen mako, domin su tattauna.
Baya ga haka kwata-kwata shekarunta ashirin da takwas ne, ba za ta watsar da rayuwarta ba ko kuwa ta cure wuri guda.
Tana makokin mijinta har karshen rayuwa ba, haka ba za ta kange rayuwarta ta tsaya kan aikinta ba, da kuma renon Danta mai shekaru biyar a duniya.
“Na ji bayaninka Yallabai, kuma na gode kwarai da ka yi hakuri da ni har ka ba ni lokaci, domin farfadowa daga zafin rashin da na yi.
Na amince da batunka, sai ko mu yi fatan Allah ya yi mana jagora. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ina ga wannan batu zai shiga tsakanina da aikin da na ke yi a kamfaninka”.
Alhaji Yusuf ya gyara hannunsa saman kujerar da yake zaune ya-ce, “Duk wannan ba wani abu bane, kar ki ji komai. Lokacin aiki, ayi aiki, lokaci irin haka kuma sai mu kara fahimtar juna, ko me ki ka ce?” Ya fada yana murmushi.
“To shi kenan, zan duba na gani”. Ta fada yayin da take wasa da yatsun hannunta, ta san kawai tana yaudarar kanta ne, don ba za ta taba son wani Da namiji ba, kamar yadda ta so Daktanta.
“To na gode da lokacin da ki ka ba ni, sai na ji daga gare ki kenan”. Alhaji Yusuf ya fada yayin da ya mike daga kujerar.
Sallamar da suka ji a bakin kofa ne, ya hana Mai-jidda amsa masa maganar sa, turus! Ta yi da ta ga mai shigowan, nan take ta ji wani abu ya yi tsalle a cikinta, amma ta danne, daurewa ta yi ta amsa sallamar mai shi.
Ya sa kai cikin falon tare da kamshin turarensa biye da shi. Sanye yake da jumfa da hular duka launin kasa. Engr. Abdul-Aali Sani kenan, kanin mijinta.
Sannan mutumin da ya dauki fadin rai na duk duniya ya dorawa kansa, ya karaso cikin falon. Murmushi ya yi wanda yake kara bayyana asalin isar sa da halayyarsa, sannan ya-ce, “Jidda kin yi mamakin ganina ne?”
“Tabbas kuwa”. Ta fada muryarta kusan a shake. Rabon da ta gan shi, tunda ya zo ya yi masu sallamar tafiyarsa wani (Course) a kasar waje, wanda yanzu shekara guda kenan. “Na zaci har yanzu ka na UK, ka na karo ilimi”.
“Na dawo yanzu, domin a amfana da ilimin”.
“Oh” Ta furta cikin sanyin jiki. Mai-jidda ta rasa yadda za ayi ta rage gudun zuciyarta ko kuwa tsigar jikinta da ke ta faman tashi tun shigowar Abdul-Aali falon.
Ko kadan bai taimaka ba wajen dada rikita halin da ta shiga da zuwan Alhaji Yusuf, ga shi ya dauko nuna isar sa da tsawon sa da cika wurin sa ya kawo cikin falon.
Musamman yadda ya kara wani annuri cikin shigar da ya yi yanzun, wanda ba haka ya faye shigarsa ba. Ba abinda take gani cikin idanun sa, sai tsantsar tsana da kyara, wanda ta saba gani tun farkon haduwarta da shi kafin auren ta da Rayyaan.
Hakan ya sa karfi da yaji, ya hana matarsa mu’amala da ita, bayan kowa a Dangi yana sonta. Shi me ya sa yake kin ta? Ita ma ta tsane shi. Wannan kallon dake idanunsa ne, ya sa ta shiga taitayinta ta-ce “Sorry! Alhaji Yusuf, wannan shi ne Abdul-Aali kanin marigayi”.
Alhaji Yusuf ya yi saurin mika masa hannu. “An wuni lafiya?”
Abdul-Aali ya karbi hannun, suka yi musabaha “Lafiya Alhamdulillahi”. Yana sake hannun sa, ya dubi gefen da Mai-jidda take tsaye, ya-ce.
 “Na ga alama har kin gama makokin naki.” Ya yiwa Alhaji Yusuf murmushi, sannan ya kara da cewa.  “Ya yi kyau.” 
Ba ga irinta ba, daga zuwan sa ko minti biyu bai yi ba, har ya fara (Judging) dinta, wai ko meye manufarsa, oho? Shi kadai ne yake tunanin yake jin ciwon mutuwar Dan-uwansa ko kuwa don Dan-uwansa ya mutu.
 Sai ta tabbata a bakin ciki? Mugu. Saura kadan ta harare shi, amma ta daure ta hana kanta, suka fita da Alhaji Yusuf zuwa bakin motarsa, inda suka yi sallama. 
A falon ta zo ta same shi, har za ta shige ciki, ta kira Umma ne, don su gaisa, ta ji ya-ce, “Jidda!” Duk duniya shi kadai yake kiranta da wannan sunan. Ko Dokta, Hauwa yake ce mata, wasu ko su ce Mai-jidda.
 Amma don ya gwada mata kin ta da yake yi ma, ba zai kirata da sunanta duka ba, saboda bata lokaci ne a wurin sa. Tana zama ta-ce, “Yaya su Mamin Mimie?”
“Lafiyar su kalau, su Umma duk suna lafiya?” Me ruwansa da lafiyar Ummata?
“Lafiyar su kalau, dama ita zan shiga na kira ku gaisa. Ga shi kuwa ka zo. Muhammad ya tafi gidan Yaya Hamza yau da safe”.
Abdul-Aali ya jinjina zancen, kwarai ya yi kewar yaron, ya so da zuwan sa, ya fara ganin sa. “Ina ruwan Muhammad, sai dai na zo ne, domin mu yi wata magana dake.”
Sai da ta ji gabanta ya fadi, wace magana ce za ta hada su kuma? 
“Abdul-Aali magana kuma?”
“Eh magana a kanmu”. Mai-jidda dai walkiya bai taba buganta ba, amma ta tabbata idan ya bugeta, haka za ta kasance, sai da ta ji wani jiri na neman dibanta, a zaune take, amma sai ta ji kamar za ta zame, saboda rudanin da kalamansa suka haddasa mata. 
Har ma akwai wani ‘Mu’ ne tsakaninta da Abdul-Aali? Dan-uwan mijinta da ya rasu shekaru biyu da suka wuce, mutumin da ya fi kowa tsanarta?
“Ban gane magana a kanmu ba, akwai wani abin da za ka fada mana, bayan wanda ka fada shekara guda da ta wuce?”
“Na kula lokaci ya yi da za ki san me na ke ji game da ke”. Ya fada cikin yanayi na murmushi, wanda ba kasafai ta faye gani a tare da shi ba.
Mai-jidda dai an bar ta da kullewar ciki da kifta idanu, tsabar kidimar da maganganun Abdul-Aali suka jefata. “Har akwai abin da ka ke ji, bayan tsana a tare da matar Dan-uwanka? 
Ko kuwa yanzun ma za ka lissafa min laifuka na ne, akan fara kula wani da na yi, tunda na auri Dan-uwanka, ba ni da damar sake wani auren?”
Abdul-Aali ya runtse idanu, ya bude, ya saki ajiyar zuciya. “Jidda, ke kin dauka na tsane ki ne?”
“Idan ba tsanata ka yi ba, ka fada min dalilin aikata duk abin da ka aikata daga haduwata da kai, zuwa yanzu, musamman bayan aurena da Rayyaan”.
“Wannan wani labari ne na wani lokaci daban, amma zuwa lokacin ina so na ba ki magana guda ki je ki yi tunani a kai. Zan koma Kano yau Insha-Allahu, amma sati na sama zan  dawo.”
Mai-jidda dai baki bude, ta tsaya ganin ikon Allah, idanunta kuwa suna bin shi da kallo a lokacin da ya mike ya-ce. “Ehen, Alhaji Yusuf yake ko waye, ina so ki sallame shi zuwa lokacin da zan dawo.”
Mamaki ne ya hanata iya furta komai a wannan lokacin, sai da dakikai suka shude, ta samu muryarta da kyar ta-ce, “Zan iya sanin dalili?”
Ba tare da ya jira komai ba ya-ce, “Saboda ki na da mijin aure, bata maku lokaci ki ke yi.” Ya kara hada fuska, sannan ya-ce, “Sai wani sati”. Ya fita daga falon.
Lalle jijji da kan wannan mutumin ya kai intaha, me yake daukar kansa ne? oho! Don kawai yana matsayin kanin mijinta, hakan bai ba shi damar ya fadi abin da ya ga dama ba.
 Cikin gida ta shiga. Ummanta na tsakar gida tana aikin yamma. Mai-jidda ta zo ta wuce fuuu! Zuwa dakinta. Wannan ya sa Umman ta san an samu matsala da bakon kenan.
 “Oh, Allah ya kawo wa ‘yar nan mafita, ya ba ta wanda zai kwanta mata a rai, amma mutum ya sa abu guda a ransa, ba sassauci? Allah ya kyauta.”
*******
Washegari da kyar ta samu karfin zuwa wajen aiki, domin kuwa duk wani kuzari na ta, ya fice a jikinta tare da ficewar Abdul-Aali.
 Wai me ma ya sa take kara tuno wannan mai matukar fadin rai da tunanin duk abin da yake so, shi za ayi? Haka dai ta karasa wunin ranar a ofis, hakan ya jawo hankalin Walida kawarta kuma abokiyar aikinta ta-ce, “Mutumiyar yaya dai na gan ki haka? Ba dai Alhaji Yusuf din bane ya maida ke haka ba?”
Mai-jidda ta yi murmushi, sannan ta-ce, “Damuwata har ta kai haka bayyana?”
“Kin ga yadda ki ka koma kuwa? Gaba daya yau ba ki tsinana komai ba, kan files din dake gabanki, ga shi an sake turo mana wasu, domin mu duba, don (Auditors) za su zo bincike karshen wannan satin”.
“Komai tsakanina da Alhaji Yusuf lafiya, duk da dai na kawo masa uzurina na maganar aiki da shi, idan har maganar neman mu zai dore.”
“To menene matsalar?”
“Ke dai ki bari, kin san kanin Rayyan dake Portharcourt ai, Abdul-Aali?” Walida ta gyada mata kai alamar ganewa, “Jiya muna zaune da Alhaji Yusuf har ma yana kokarin tafiya, sai gashi ya iso, kin san yadda yake da daukar kansa, tamkar ya fi kowa, ya gama zafin kansa, amma dai bai tafi ba, sai da ya juya min duniyata gaba daya. Yanzu ba abinda na ke so, illa na samu hanyar raba gari da wannan mutumin.”
Walida ta yi murmushi ta-ce, “Madam kenan, to ke ko ina za ki yakice shi? Ai da ke da ‘yan-uwan Dokta kun riga kun zama daya, tunda haihuwa ta hada, ko da babu haihuwa, na san ke ba mai watsar da Mama da zuri’arta bane, ko dan yadda suka kaunace ki.”
“Tabbas maganarki dutse, amma wani abin da ba ki sani ba, duk iya lokacin da na dauka a wannan gidan, ban taba samun wuri ko yabo a tare da Abdul-Aali ba.
 Duk wani abu, in dai ya shafeni, to ya tsane shi, har katanga ya yi wa matarsa da shiga sabgata, duk sanda suka zo, don me ni zan so na mu’amalance shi?”
“Daga ji dai kun dau zafi ne da junan ku. Yaya labarin Muhammad, kwana biyu ban gan shi ba?”
Mai-jidda ta ji dadi a ranta ta-ce. “Lafiyarsa kalau, yana gidan Yaya Hamza gun Anty Fauziyyar sa”.
“Dan gidan Anty Fauziyya kenan, don Allah ki saki ranki, ki rabu da zancen Abdul-Aali, gobe dai aiki ne tirim! A gaban mu, don haka ki warware”.
Mai-jidda ta yi shiru tana jinta kawai, ita kadai ta san me kalaman Abdul-Aali suka haddasa mata. Tana tuna farkon haduwar ta da shi, lokacin da suka je wurinta da Rayyan, bayan an yi masu baiko…
Ranar dai murna baya misaltuwa a gun Mai-jidda. Allah ya kawo randa Rayyan zai hada ta da kaninshi abokin sa, sannan abokin shawarar sa Abdul-Aali.
Don haka ta gama duk wani shirye-shirye na tarban su, musamman ta tafi gidan Yaya Hamza ta-ce su same ta a can,
 Saboda za ta yi amfani da Oven din Anty Fauziyya wajen yi masu gashe-gashe, dabarata kenan. 
Tana kammalawa, ta yi wanka ta fito cikin shiga mai daukar rai saboda a wannan lokacin duk wani abu in dai ya shafi Rayyan ne, to an gama magana, sai inda karfinta ya kare. 
Suna isowa, ta bude masu falon Yaya Hamza suka shigo. Mai-jidda ta fadada fara’arta, duk irin hirar da Rayyan ke mata na Abdul-Aali, bai taba ce mata ga yadda yake ba, to me zai sa ya fada mata? Don haka ta ji mamakin ganinsa da ta yi, kusan sa’o’i da Rayyan
 A ladabce ta gaishe su, sai dai kallon da Abdul-Aali yake mata ne da murmushi, ya sa ta tunanin ko dai ta labta hodarta ne, ta manta ba ta gyara ba, don sai ta soma tsarguwa, har dai da kansa ya gane kallon ya yi yawa, ya daina. Idan har Abdul-Aali ya sake mata wani murmushi ko dariya daga wannan rana, to ita dai ba ta gan shi ba, kuma ba ta kula ba.
 “kullum Dakta sai ya ba ni labarinka da yadda kusancin ku yake.” Sai dai daga idanunta da ta yi suka hada ido, ta tsinkayi wani duhu a fuskarsa.
Sabanin shigowarsa, amma dai ta ci-gaba. “Sai dai bai fadi rabin komai game da kai ba, sannu da zuwa”…
Walida ta taba kafadunta ta-ce “Don Allah ki dawo hayyacinki, wai yau ba za ki tafi gida bane?”
Nan Mai-jidda ta duba agogo har karfe biyar saura, ta yi maza ta mike, suka fita bakin hanya, domin neman abin hawa. Tana komawa gida, ruwa ta watsa, sannan ta nufi dakin Ummanta.
                                          ***********           
Abin da ya razana Mai-jidda, shi ne bayan rasuwar Rayyan da wata uku, sai ga wayar Dan Kano, ita har ta manta da shi, rabon ta da shi, tun ana gobe daurin auren ta da Rayyan da ya kira.
 Don yayi mata fatan alheri, sai ga shi yanzu ya kira yana mata ta’aziyya. “Na gode sosai, amma don Allah a ina ka samu labarin rasuwar nan?”
 “Na yi tafiya, dawowana na hadu da Auwal abokin karatunki, shi yake fada min.”
Tabbas su Auwal sun zo mata gaisuwa. “Allah Sarki na gode sosai. Allah ya rubuta lada.”
“Ameen. Allah ya kara hakuri da dangana.”
Jif- jifa yana bugowa su gaisa, amma dai ba ta ba shi fuska ba, saboda tana cike da radadin rashin mijinta. 
*********
“Hauwa, har yanzu ina jinki a raina tamkar da, kamar yadda na fada miki, ba zan iya daina sonki ba. Na yi kokarin kau da kaina na rarrashi kaina amma na shiga wani hali saboda rashinki, har yau ba ni da sukuni, saboda rasa ki da na yi.”
“Na gode da kaunarka a gareni, amma don Allah ina so ka min hakuri, ka ba ni lokaci saboda ba na tsammanin zan iya bada gurbi wa wani a zuciyata, saboda halin da na ke ciki.”
“Na gane, kuma ina tayaki alhinin rashin mijin ki, ina kuma miki fatan samun sauyi mafi alkhairi.”
Ta ji dadin maganarsa, tunda kuwa suka yi haka da shi, sai dai ya kira ya ji labarinta da su Umma da kuma danta Muhammad, ta-ce ya gayar da matarsa, shi kuwa ya-ce ta gaida mutanen gida, bai sake mata maganar soyayya ba.
Sai dai su yi shawara ko kuwa idan abin alkhairi ya same shi, ya fada mata, haka ita ma. Ko da kewa ya mata yawa, shi ya ba ta shawarar ta fara aiki tunda ta kammala karatunta.
 Ranar wata Talata. Manajan su ya shigo inda suke aiki su biyar a cikin office dinsu, da yake Economics ta karanta bangaren adana da kidayar kudin kamfanin aka ajiyeta. 
Tare yake da wani mutumi wanda Mai-jidda tana gani, ta san cewa babba ne a wajen, ganin girman da suke ba shi, da kuma yanayin shigarsa, duk da yake a shekaru ba zai wuce shekaru arba’in zuwa da uku ba. Nan ne Manaja ya gabatar da ita ga mutumin a matsayin sabuwar daukar da suka yi a kamfanin. Alhaji Yusuf kenan, shi kuwa yana ganin Mai-jidda wani abu ya darsu a ransa. 
Ba tare da yayi mata magana ba, ya ci-gaba da kula da ita, tana da sabo da mutane, amma ba ta da hayaniya, sannan akwai kwazo kan aikin da take yi, muhimmin abin dai ta iya, shiga rai.
 Kafin ace meye dai Alhaji Yusuf ya fada cikin soyayyar Mai-jidda, hakan ya sa ya nemeta a waya, har ya mika mata bukatarsa, amma fir! Mai-jidda ta nuna ya bata lokaci tukun.
 Shi kuwa Alhaji Yusuf mutum ne mai hakuri kan abin da yake so, wannan ne ma ya taimaka wajen kai matsayin da yake a yanzu, don haka ya saurara mata har sai da wani lokaci da suka yi waya, ta-ce masa. “Yallabai, za ka iya samuna a gida sai mu tattauna.”
Kwarai ya ji dadin zancenta, don kuwa Mai-jidda na dawainiya da shi fiye da zatonta. Tun randa ta yanke wa ranta kula Alhaji Yusuf, abin ya dameta saboda tana ganin kamar ba ta yiwa Dan Kano adalci ba.
 Saboda ya dade yana binta kuma ta yarda da shi, amma ta kasa ba shi dama. Da yamma tana zaune kuwa, sai ga wayarsa, “Kamar ko ka san da magana a baki na”.
Ya yi murmushinsa mai tayar wa Mai-jidda tsikar jiki a ko da yaushe. “Haba, na kira a daidai kenan.”
“Wai me ya sa ka ke boye lambarka ne?”
“Ok, I’m sorry ban san yana boye ba kuwa, zan bude Insha-Allahu. Meye to labarin?”
“Ka san Alhaji Yusuf da na fada maka? Kawai na yanke shawarar ba shi dama mu ga abin da zai faru, amma kuma sai na ke tunanin ban san me ye ra’ayinka ba?”
Zuciyarsa ce ta yi mummunar faduwa da jin kalamanta. “Ra’ayina kuma Hauwa?”
“Ganin ka yi shiru da maganarka, ya sa na ba shi kofa, saboda na bude sabuwar rayuwa, kamar yadda ka ba ni shawara, amma kuma na fi son na ji shin ka yi na’am da hakan?”
Murmushi ya yi ya-ce. “Yaya za ki min wannan tambayar, bayan kin san abin da na ke ji game dake?”
“Na san me ka ke ji, amma ni kuma ka san me na ke ji ne?”
“Idan har Alhaji Yusuf zai saki farin-ciki, ki ba shi dama, ni ba zan hanaki ba, amma kuma meye manufar alaqar mu?”
Mai-jidda ta rude, ita kanta ba ta san meye matsayin Dan Kano a rayuwarta ba, su ba soyayya suke yi ba, rudin kanta kawai take yi da cewa ita kanwarsa, shi kuma Yayanta mai ba ta shawara.
“Na dauke ka a matsayin Yayana mai bani shawara.”
“Yanzu, Hauwa baza ki ba ni wuri ba, ko kankani a zuciyarki?”
“Na yi kokarin haka, na ba ka wuri sosai, sai dai kuma…” Ta yi ajiyar zuciya. 
“Right, ba za ki iya son wanin Dokta ba. Amsar kenan kamar kullum, to Allah ya bawa Alhaji Yusuf sa’a, ko shi zai yi nasara.”
“Don Allah Yayana ka yi hakuri.”
Cikin zafin rai ya-ce. “Ki daina kirana Yayanki, ki na rudin kanki, bayan ke kanki kin san abin ya wuce nan. Tunda kin yi zabin ki a yau, shi kenan sai dai nace Allah ya ba ki sa’a. A karo na biyu Hauwa.”
Jikinta ne ya mutu. Yaya za ta yi ne wai? Da kunya ta amince cewa ta kamu da son mutumin da ba ta taba ganin sa ba, sannan ba ta san ma ko da gaske yake ba. Abubuwan da ya ce mata. 
Zuciyarta ta kasu kashi biyu, amma dole ta sallami Dan Kano ‘Yayanta’ kamar yadda take kiransa. Saboda tana ga tamkar ta ha’inci Rayyan ne, idan ta bari zuciyarta ta so wanin sa. Wanda kuma zuciyarta na barazanar so mata Dan Kano.
Tunda ya kashe waya, ranar ba ta sake ji daga gare shi ba, ga shi daya lambarsa ba ta shiga wanda yake kiranta da shi daga baya kuma, a boye take bare ta neme shi. 
                                          ********** 
“Sweety, yaushe zamu koma ne?” 
“Ke kam ba gida ki ke son zuwa ba, kuma kin zo, sai ki mora, son ranki kafin ki koma, don idan mun koma za mu dade ba mu zo ba.”
Hamamatu ta Dan bata rai cikin ‘yar shagwaba ta-ce. “Bayan tun da muka zo ma ba ka ba mu lokaci ba, kullum ba ka zama.”
“Abubuwa ne suka min yawa, ki dauki yaran ku je, duk inda ku ke son zuwa ba damuwa, sai ki yi amfani da motar wurina zan nemi Mukhtaar ya ban tasa motar.”
Cikin farin ciki ta-ce. “To shi kenan mun gode, zan je yau na gaida su Mama Insha-Allahu. Sai na bar masu yaran su wuni a can.”
“To ba damuwa, ni zan tafi Dutse Insha-Allahu, zuwa yamma ina ga zan dawo”.
Hamamatu ta juyo tare da tsayawa daga saka abin hannunta da take yi “Sweety last week ba ka ce min ka je Dutse ba, yau ma za ka koma?”
“Eh, ban samu ganin Muhammad ba, ya kamata na gan shi kafin mu tafi”.
Ta dan yi shiru daga bisani ta-ce. “To ko na shirya na maka rakiya? Ka ga sai na gaisa da Anty Hauwa, tun kafin tafiyarmu UK rabona da ita”.
Abdul-Aali ya dauki hularsa, ya sa hade da daura agogonsa sannan, ya-ce “Kar ki damu, zan kai ku daga baya da yara, yanzu yau din ku je gidan Abban.”
Ya kula ba haka ta so ba, amma zuwan da zai yi yau ba ya bukatar tafiya da ita, don haka ya shafi fuskarta, sannan ya ja ta jikinsa. 
******
Yana karbar motar Mukhtaar, ya kama hanya, gidan Yaya Hamza ya fara zuwa ya same shi kuwa a gida suka gaisa. 
“Abdul-Aali, ai ba ni da labarin ka dawo kuwa.” Abdul-Aali ya yi murmushi.
“Jidda ba ta fada maka ba kenan, na zo (Last Week), ai ta-ce Muhammad yana gidanka,  nace to sai wannan satin zan dawo”.
“Lallai ta manta ba ta fada ba, ah sannu da dawowa.” Yaya Hamza ya sa baki ya-ce. “Fauziyya!” Tana zuwa ta ga bakon nasu, nan da nan ta gaishe shi, ta shiga hidima. 
Abdul-Aali ya-ce. “To Hamza, na gode, we’ll be in touch Insha-Allahu. Ni zan karasa wurin su Umma mu gaisa.” Nan ya dauki kudi ya bawa Fauziyya, cikin jin nauyi dai ta karba da ya matsa. 
******
Mai-jidda ta gama gugan kayan Muhammad kenan, sannan ta shiga wanka, wannan satin ta gaji da yawa a ofis, hakan ya sa take son ta huta sosai, a karshen makon kafin litinin kuma ya yi. 
Ta gama shirinta cikin wata doguwar riga mai kalar makuba, ta sa hular da ta shiga da rigar, sannan ta ja hannun Muhammad. Ta-ce.
 “Yau kam dai ka kwanta ka huta wa ranka, amma kullum banda wasa, ba abin da ka ke so, ga shi an taso makarantar an gaji, amma wai kai sai ka ce wasa za ka yi.”
Umma ta-ce “hmm in dai Muhammad ne kam ba gajiya yake yi ba”.
“Yau kam barci zai yi.” Nan ta tisa keyarsa ta sa shi kwanciya. Kwanciyarsa ko barcin bai yi ba, sai ga Abdulmajid ya shigo cikin gidan, yana fadawa Umma.
 “Umma fa Injiniya Abdul din su Yaya Mai-jidda ya zo, yanzu isowar sa, amma na bude masa falo.”
“To, lalle maraba da zuwan sa.” Nan Umma ta mike, ta nemi luffaya, sannan ta isa falon. 
Mai-jidda tana jin sakon Abdulmajid hankalinta ya dunguma ya tashi, ashe daman da gaske yake yi zai dawo? Ita ta rasa wai me Abdul-Aali yake so da ita ne, dole ta san abin yi, dole ta yi masa iyaka, don me zai takurawa rayuwarta? Kafin ta gama lissafin abin yi. Ta nemi Muhammad ta rasa, tuni ya ruga da gudu wajen Baffansa.
 Tana zaune a wurin kamar an kafata har Umma ta dawo dakin, ta same ta. “Yaya na gan ki haka a zaune, yana kan hanya ne, ko ba za ki je ku gaisa ba?”
“A’a Umma ai mun gaisa, satin da ya wuce.”  
Umma Laraba ta sa hannu a habarta, ta tallafe shi cikin mamaki. “Ashe mutumin nan ba don ke da Danki yake dawainiya ba, sai a ce ya zo har ya koma bai ci albarkacin gaisuwarki ba? 
Ko ke kadai ne mijinki ya mutu? Shi ma Dan-uwansa ne ai ya rasu. Amma hakan ya daure yake zuwa duba ku, don me ya sa ba za  ki saurare shi ba. 
Ni ban ga me ‘yan-uwan marigayi suka yi miki ba, banda alkhairi, me zai sa za ki guji haduwa da su. Ki tashi ki je ku gaisa”.
Ta mike cikin kunar rai, ta sa mayafinta, sannan ta nufi falon Baba. Yana zaune a kan kujerar da take kusa da kofa. Muhammad ne a kan kafafunsa, suna ta zuba labari, ta ji mamaki ma yadda tsawon shekara guda kenan, amma yaron bai manta shi ba. 
“Sannu da zuwa.” Ta fada wanda a zahiri, ya fi kama da ‘ka tashi ka tafi ba a marabceka ba’. Tsabar yadda ta fade shi cikin daci.
“Muhammad, wai me ya samu Mamanka ne? Ko ba ta da lafiya ne?”
“Uncle Abdul lafiyarta kalau, dazu ta gama min fada, wai na faye wasa”.
“Haba? Da fatan dai kana karatu sosai, ba wasa kawai ba?”
“Ina yi sosai, ni ma Dokta zan dawo irin Babana”. Yaron ya fada a daukance, yayin da Abdul-Aali ya dago suka hada idanu da Mai-jidda na tsawon lokaci kafin ta kawar. 
“To ya yi kyau. Je ka dauko min littafinka na gani”. Da sauri Muhammad ya fita Mai-jidda ta mike za ta bi bayansa ne, ya-ce mata. “Ban sallameki ba.”
Ita har mamaki karfin halin Abdul-Aali yake ba ta, gaba daya bai dauketa a bakin komai ba, ya dauka zai juyata son ransa ne.
Ta koma ta zauna ba tare da ta-ce masa komai ba, “Ke na ke saurare, me ki ka ce game da maganar mu ta Last week?”
Kamar ta yi shiru, ta yi ta jinsa, amma ya ci albarkacin Dokta, don haka kanta a kasa ta-ce.
 “Abdul-Aali, tsakanina da kai ba maganar wasa ko kuwa raini, don haka ina ganin mutumcinka, ko don saboda Muhammad dake tsakani, ina ga rike wannan girman yana da matukar muhimmanci, don haka kar wata magana ta rashin tunani ta shiga tsakanin mu.”
Abdul-Aali ya nisa sannan, ya-ce. “Ban ji hujjarki ba ko daya a wannan maganar, idan akwai inda addini yayi min hani da manufata, ina saurarenki ki fada min.”
Tabbas da wata kullaliya a zuciyar Abdul-Aali, ya zo ne ya tarwatsa mata duniya, ya sa wadanda suke kaunarta a danginsu su ma su tsaneta tamkar yadda ya tsaneta.
“Ko kuwa ni Abdul-Aali, ni kadai ne ba ni da wannan kofar? A tunanina yanzu kin shirya fara sabuwar rayuwa. Hakan ne ma ya ba ki damar kula manema aurenki. 
Akan me ya sa za ki saurari mutanen da ba auren su za ki yi ba? What’s the point, ko so ki ke yi ki ce min har cikin ranki za ki iya auren wani a cikin su? Har shi Alhaji Yusuf din.”
“Ni zan shiga gida, randa ka tashi zuwa ganin Danka, kofa a bude take, amma ba za ka zauna ka na ci min zarafi ba, ko zan sake aure, ko ba zan sake ba da wanda zan aura duk ba damuwarka bane.
 So, I suggest you mind your own business.” (Ina ba ka shawarar ka yi abin da ya shafe ka).
 Mai-jidda ta ajiye numfashi, ta kasa yarda wai Abdul-Aali take mayarwa amsa, kuma yana zaune yana saurarenta ba tare da ya yayyankata ba, don ta san tsanarsa ta kai haka.
“Ni zan koma nan da Three weeks Insha-Allahu, idan har kin canza ra’ayinki, ki na son ki saurareni, sai na zo mu yi magana a tsanake kafin nan.”
*******
Mai-jidda ta ajiye numfashi, ta kasa yarda wai Abdul-Aali take mayarwa amsa, kuma yana zaune yana saurarenta ba tare da ya yayyankata ba, don ta san tsanarsa ta kai haka.
“Ni zan koma nan da Three weeks Insha-Allahu, idan har kin canza ra’ayinki, ki na son ki saurareni, sai na zo mu yi magana a tsanake kafin nan.”
*****
Ba ta san lokacin da hawaye ya zubo mata ba, nan take wani bakin ciki ya damketa, yau Dokta baya nan, wai har shi ne zai sa mutumin da ya fi kowa tsanarta a duniya ya zo ya-ce zai aureta, sannan ma kanin Dokta? Bayan ma haka yana mata tamkar dole ne ta amince.
“Yanzu har za ka iya daga idanu ka dubi kanka a madubi, bayan abinda ka furta?”
 Bayan a lokacin da yake da rai ba ka da makiyar da ta fita? Don me ya sa zan saurare ka, don me ya sa zan yi tunanin akan wannan gurbataccen al’amarin? Duk yadda Dokta ya so mu daina kyarar juna, na san ba zai amince ka auri matarsa ba, koda kuwa bayan ransa ne.”
“Muna matsayin amana a gareka ka, iya tafiya har na shekara guda ba tare da sanin halin da muke ciki ba, mun mutu ko mun rayu? Rashin ka bai rage mu da komai ba, saboda haka idan amana ka ke son rikewa.
 Ka rike na wanda ya zamo maka lallai, shine Muhammad, shi ne maraya, shine mai bukatar kula, amma ni kam, ina tsammanin na wuce nan.” Ta fada tare da goge hawayen ta, sannan ta-ce “Allah ya kiyaye hanya.”
Muhammad ne ya koma cikin gida da gudu ya-ce. “Umma Mamana tana kuka”. Daidai lokacin ta fito daga falon ta samu Umma akan baranda tana zaune kan tabarma.
 Amma yanzu kwata-kwata ma ji ta yi auren ya fita a ranta. Umma ta-ce “Mai-jidda, lafiya ki ke kuwa, me ya faru haka?” Ba tare da ta bawa Umma amsa ba, ta tuna ranar da ta san cewa lokaci kawai suke jira…
Idanunsa a rufe suke, amma ba barci yake yi ba, yayin da numfashinsa yake fita da kyar, nan ma da taimakon roba mai bada iskar Oxygen.
Bakin sa ya bushe, ba abin da za ka ji a dakin, sai karar na’ura kawai, a cikin shekaru biyu da suka shude, anyi masa aiki sun yi uku.
 Sannan kusan gabaki daya shekarun a asibiti suka shudesu, randa ya yi lafiya a sallame su. Amma a wannan lokacin an daina maida shi gida ma, saboda wahalar da yake samu a dalilin hakan. 
Tun aikin da akai masa na karshe. Dokta ya bukaci a maida shi Najeriya ya yi jinyarsa a can, ko ya raka ganin ‘yan-uwansa duka da Dansa kullum a gefensa. “Hauwa na fi son idan lokaci ya yi, na kasance cikin ‘yan uwana, cikin gatana.” 
Hannu ta sa ta toshe bakin sa. “Muna nan a tare da kai har zuwa lokacin da za ka warke, kowa yana jiranka, kar ka cire rai, do not lose hope.”
Murmushi ya yi cikin rashin karfin jiki da sarkafewar murya ya-ce. “Hauwa, kin tuna lokacin da ki ka ce kar na sake boye miki komai ko?” 
Ta gyada masa kai. “To wannan karon ba zan boye miki ba, amma ni na san lokacina ya kusa, gaskiyar maganar, ita-ce ba zan…” 
Tari ne ya sarke shi kafin nan ya ci-gaba “…Tashi ba. Na gode sosai da juriyarki da kokarin da ki ka yi a kai na. Allah ya saka miki da aljannar firdausi…”
Story continues below
Cikin kuka ta fada jikinsa, rigar sa a cikin hannunta take wasu maganganun da ita kanta ba ta san meye take fadi ba.  Abdul-Aali ne ya shigo dakin ya tarar da su a haka, ya sa kai zai juya ne. Rayyan ya yunkura ya kira shi da hannunsa. 
Mai-jidda ta tashi ta zauna, idanunta sun yi luhu-luhu da kuka. “Abdul-Aali, Hauwa da Muhammad amanata ce a wurinka, koda wani zai tozarta su, kar ka bari su wulaqanta. Allah shi ne gatansu, na bar maka su amana.”
Abdul-Aali ya kawar da kansa gefe, yana share kwalla, daga bisani ya rungumi Dan -uwansa “Insha-Allahu ba abin da zai faru.”
Rayyan ya kada kai ya-ce. “Da ni da kai mun sani…” Numfashin sa ne ya soma yin sama-sama, cikin sauri Abdul-Aali ya kai hannu kan robar hancin sa da ya cire na Oxygen, daidai lokacin Mai-jidda ta kai hanunta, don ita ma ta mayar masa. Da sauri ta cire hannunta ta matsa da baya. 
“Yana bukatar hutu, ki daina zuwa ki na tayar masa da hankali da koke- koke.” Ba ta yi mamakin kalamansa ba. Mamakin da ta ji shi ne na inda ya furta kalaman nasa.  Dokta Allah ne kadai gatan mu, amma wanda ka barwa amanarmu, tunda ranka ma yana kyarar mu. 
Bayan Umma ta gama sauraren Mai-jidda ne ta-ce. “Lallai wannan abu da daure kai, ke dai ki yi ta addu’a. Allah ya yi miki zabi na-gari”.
“Umma ba ma yadda zan sa Abdul-Aali a addu’ata, saboda ba mai yiwuwa bane ma, ba na fatan ko a mafarki ne hakan ta faru bare a zahiri. 
Don haka zan rabu da shi ne har ya gaji ya bari.” Umma ta jinjina kai, don ita ma kanta tana tunanin yiwuwar wannan al’amari. 
Ransa na kuna ya bar Dutse, ba haka ya so ya baro can ba, ya so ya kawar da wani tunani a tare da Jidda. Amma kuma ya kula da abu guda, har yanzu ba ta manta da mijinta ba. 
Lokaci take bukata, wanda shi kuma bayida shi. Yana isa gidan Abba ya wuce, ya san a can zai samu su Hamama, sai da ya ci abinci.
Sannan ya bada motar Mukhtar wa kaninsa Kasim ya-ce ya kai masa ita. Nan ya biyewa su Mimie, don su kawar masa da damuwar da ke ransa, har bayan issha, sannan ya-cewa Mama. “Yau kam mun gaisheki, sai an kwana biyu kuma”.
“Wannan wace irin gaisuwa ce? Ni ku bar min Ramlatu anan za ta kwana”.
Mimie ta juya ta-ce. “Daddy ka yarda mu kwana?”
Abdul-Aali ya yi dariya ya-ce. “Idan ku na da kaya anan, ba sai ku kwana ba.” Mimie ta juya ta dubi Mamin ta. “Mami mu kwana?”
Dole dai haka suka baro yaran a gidan Abba, sannan suka kama hanyar gida, ta kula da yadda ya yi shiru da yawa, saboda haka da farko ta yi tunanin ta rabu da shi, don ba yau ya fara ba. Amma daga baya ta canza ra’ayinta.
 “Sweety, yau kam zan iya sanin dalilin da ya sa ka ke janyewa walwala a wasu lokuta?” Sai da ya yi firgigit! Ya gane magana take masa. 
“Great! Ina maka magana ma ba ka san ina yi ba, wane irin abu ne yake dauke maka hankali haka?”
 “Wani abu ne na ke matukar so, kuma yana ba ni wahalar samuwa. Don haka ki tayani addu’a. Allah ya zabar min da abin da ya fi alkhairi. Idan kuma alkharin ne, Allah ya ba ni ikon cimma sa cikin gaggawa.”
                             *************
Cikin dare ta samu kanta da gwada wayar Dan Kano da zummar ba shi labarin abin da take ciki, ta san zai ba ta shawara, sai dai kash! 
Story continues below
Shi ma ta tuna rabuwar da suka yi ta baram-baram! 
Mai-jidda na zaune a ofis dinsu, banda damuwa ba abin da take ciki. Walida ta shigo ta dubeta, sannan ta-ce. “Alhaji Yusuf ya zo yana ofis din Manaja.”
Mai-jidda ta sauke taguminta ta-ce. “Yau na ga ikon Allah, wasa ki ke yi dai ko? Mutumin da muka yi da shi sai a Weekend zai zo gida, ba ranar aiki ba ma, shi ne zai ce na same shi a ofis din Manaja?”
“To ni dai sako aka ba ni, idan ba ki je ba, ki na ji, ki na gani zai shigo har nan ya same ki,  don kin san zai iya aikatawa, in dai a kanki ne.”
Mai-jidda ta ja tsaki hade da buga wani sabon tagumi. Tana zaune har sai da Walida ta sake mata magana tukun, sannan ta mike zuwa ofis din Manajan.
 Ga mamakinta shi kadai ne a ofis din, da alama ya yi aron ofis din ne, don su gana, to meye ne mai muhimmanci da ba zai jira sai ya zo gida ba, ko kuwa ya fada mata a waya, har sai ya sameta a wurin aiki? 
A tsume ta zauna, wanda aka yi fushin domin sa kuwa ya kula da hakan. murmushi ya yi ya-ce. “Haba Hauwa Kulun Majada, duk wannan fushin wa Yusuf shi kadai ake yiwa?”
Dole ta sa ta dan saki fuska kadan. “Yallabai, a tunanina mun gama magana kan cewa koda maganar mu za ta dore ba za mu hadu a ofis ba”.
“Na ji, ina kuma neman afuwa, saboda saba yarjejeniyarmu, amma wani albishir na zo miki da shi, wanda ba zai iya jira har karshen mako ba.” Ya fada yana kallonta. A hankali ta-ce. “Albishir kuma?”
“Eh, na gama shawara kuma ina son bada dadewa ba na tura gidanku, domin ayi min tambayar aurenki.”
Wani sauti Mai-jidda ta saki, shi ba dariya ba, shi ba kuka ba, har ma sai an yi wata shawara a kanta.
 A bangare guda an maida ita abin gado a wani bangaren kuma ana shawara kafin a mallaketa, tamkar kaya. Wayyo duniyar maza! Ita Hauwa’u ko yaushe za su gama dawainiya da ita a cikin ta oho.
“To, lalle magana ta girmama, amma dai ina tsammanin wannan shawara ba da Yayata aka yi ta ba ko?”
Alhaji Yusuf ya yi murmushi, yana sosa habarsa ya-ce. “Yayarki kam ai sai lallaba, ke dai mu yi fatan samun alkhairi cikin wannan al’amari”.
Ta auna amsar ta sa, sannan ta-ce “Ameen.”
“Wannan ya sa na kira ki, don na ji wani lokaci ki ka ga ya fi dacewa su je?”
“To ba damuwa, zan dan bukaci lokaci, domin na isar da maganar ga Baba duk lokacin da ya bayar, za ka ji daga gareni Insha-Allahu”.
“To, Allah dai ya sa bada jimawa ba, don ba ni da burin ya wuce na gan ki a gidana.”
Murmushi Mai-jidda ta yi. Duk da ba wani dadewa ta yi da Alhaji Yusuf ba, amma ko wani lokaci sai ya nuna mata tana da muhimmanci. Har tana shirin mikewa ne, ta zauna ta-ce.
“Ka san sha’anin aiki, kar su dauka ina samun wata kulawa ta musamman daga kamfanin, tunda ina samun bakunta daga mai shi.”
“Hauwa kar ki damu. Insha-Allah, na gane na yi kuskure, nan gaba idan na tashi zan yi amfani da waya shi kenan?”
“Za ta ji.”
Ita ta fara fita zuwa ofis din su, nan ta samu Walida na jiran kwakkwafi. “Ke da ki ke cewa ba za  ki je ba, shi ne daga zuwa har da shan zaman ki ko?”
Story continues below
“Hmm! Ke dai bar ni da Alhaji Yusuf, wai nan zuwa ya yi ya fada min zai tura ayi tambaya, yana bukatar na ba shi lokaci.”
“Ke da zafi-zafin sa ashe, to me ki ka ce masa?”
Nan ta fada mata yadda suka yi. Walida ta-ce. “Ke sha’aninki sai ke Mai-jidda, me ki ke jira kuma? Alhaji Yusuf mutumin kwarai ne, kowa ya san halayensa, sannan ya gwada miki so a zahiri, ya nuna kaunarsa gareki da Danki, me kuma ki ke nema?”
“Hmm! Walida ba na miki fata, amma ki na fadan haka ne kawai, don ba ki san mutuwar miji ba. Har yanzu Dokta na raina.”
Walida ta zauna a kujerar dake fuskantar ta Mai-jidda.
 “Duk da ban san mutuwar miji ba, amma na san abu guda, shin rashin mancewa da shi zai dawo da shi, ko kuwa haka za ki rayu cikin tunaninsa iya ranakun rayuwarki, dole ki ci-gaba da rayuwa. You have to move on. 
Ko shi ba zai so ya gan ki cikin kunci ba. Rayyan wani bangare ne na rayuwarki da ya wuce addu’a ce tsakanin ki da shi, ki kuma tarbiyyantar da Dansa zuwa hanya na kwarai, ki gwada masa son mahaifinsa. Amma ke kuma fa, za ki kasa rayuwa ne saboda rashinsa?”
Mai-jidda ta nisa tare da jinjina zancen Walida. Tabbas! Gaskiya ta fada mata, kuma ita ma tunanin da ta yi kenan, wanda har ya sa ta samu karfin gwiwar bawa Alhaji Yusuf dama. 
Amma tambayar aure yanzu, kamar ya yi sauri, ta fi son ta san mu’amalarsa da matarsa kafin ta shiga, don zai iya yiwuwa yadda yake a waje, gidan sa ba haka yake ciki ba, shi ya sa za ta bi a hankali tukun, kafin abubuwa su yi nisa. Kada ta dau kara da kiyashi….!
*****
“Mabruka kenan, ni dai nace masa zuwa karshen wata mai kamawa, kafin nan mun kara fahimtar juna”.
“To Allah ya tabbatar da alheri, na yi murna kwarai, lallai Alhaji Yusuf ya taka rawar gani, tunda ya rusa wannan katangar. Allah ya nuna mana lafiya”.
“Hmm! Ina Farida da Babanta?”
“Lafiyarsu kalau! Farida ta kusa shiga makaranta”.
“Wai sai yaushe za ku zo mana ne, kun je kun makale a Ibadan, kamar an shuka ku”.
“Ke dai zolayarki ta yi yawa, ki gayar min da ‘yata sai kun zo.” Kamar ta ba ta labarin wainar da Abdul-Aali yake toyawa, amma ta yi shiru, saboda ko maganar ba ta son tunawa, bare maimaitawa.
Suna gama waya da Mabruka, ta shiga taya Umma ayyukan gidan, suna cikin aiki ne, sai ga Anty Fauziyya ta shigo.
 Nan Mai-jidda ta mai da hankalinta kanta, suka koma dakin Umma. “Kawai ranar sai ga Abdul-Aali har gida, har da shiga dawainiya. Don Allah ki min godiya idan kun yi waya”.
Mai-jidda ta zaro idanu, yanzu kuma Abdul-Aali sayan danginta yake tunanin yi ko meye “Yaushe ya je gidanki?”
“Last week, ke kuma ashe ya dade da dawowa, shi ne ko ki fada, sai da ya zo yake fadawa Yayanki”.
“Hmm! Ki rabu da shi kawai, duk wani dadin bakin da zai maku, kar ku ma saurare shi.”
Fauziyya tayi mata kallon mamaki, “Abdul-Aali fa nace, ko kin dauka wani na fada?”
“Shi din na ke nufi. Anty Fauziyya ke ba ki san me ya zo min da shi ba, yana neman rikito min wani rikincin da ya fi karfina ne, na daukar dala ba gammo.”
Nan Mai-jidda ta fadawa Anty Fauziyya duk yadda suka yi da Abdul-Aali. 
“To, ni ban ga laifi ba anan, don ya-ce yana son auren ki, meye laifinsa? Ai ni ina ga ya kyauta ne ma da yake so ya rike ki da Danki”.
Story continues below
“Idan ya yi niyyar kyautatawa, ai hanyoyin yinsu da yawa, me ya sa zai ce zai aureni? Ni fa na san shi, baya kaunata ko ta kwayar zarra.”
“Ke ki na kaunar Alhaji Yusuf ne, da ki ke shirin auren sa?”
Mai-jidda ta dubi Anty Fauziyya, sannan ta-ce. “Ba anan maganar take ba, ni na san tafiyar mu za ta zo daidai da Alhaji Yusuf, kuma baida wani hali da ya yi kama da na Abdul-Aali. Sannan ina son yanayin komai nasa, domin mutum ne mai kamala.”
“To ashe za ki iya auren wanda ba kya kauna kenan, shin da bakinsa ya shaida miki baya kaunarki, ko ya tsaneki? Kai idan baya sonki, me zai sa ya-ce zai aureki? Bayan ba iyali ya rasa ba, ba komai ba, sannan shi ba karamin yaro bane, bare ya yi maku wasa da hankali.”
Ajiyar zuciya Mai-jidda ta sake kawai, ta san Anty Fauziyya ba za ta fahimci daga inda take tunani ba, don haka ta-ce.
 “Shi kenan, tunda sun yi haka, amma ai ni ban ce ina kaunarsa ba, kuma nace ya kyale ni, ashe ba sai ya kyaleni ba? Ko an taba auren dole?”
“Ba a taba ba, amma dai ni shawarata shi ne ki ba shi dama, ki gane hakikanin manufarsa, ya fi ai, kin san sai an gwada, akan san na kwarai. Kuma magani sai da gwaji”
Mai-jidda ta yi kwafa. Allah ya sawwaka ta neme shi, tana da zuwa Kano. Kai Muhammad ganin su Mama, amma haka ta hakura har zuwa lokacin da ya dace Abdul-Aali ya tafi, kamar yadda ya fada mata, sannan za ta tafi. Ai sai dai ya samu labarin aurenta, amma ba dai da shi ba kam. Bindin rakumi ta yi nesa da kasa. 
*******
Hankalinta a kwance, ta manta da wata sabga ta Abdul-Aali. Ranar Juma’a ta shirya Muhammad don ta kai shi wurin su Mama a Kano. Yaya Abbakar ne zai kai su. 
“Ki gaishe da su Hajiya Zainab din”.
“To Umma za su ji Insha-Allahu, gidan Yaya Maryam zan kwana, ina ga sai lahadi Insha-Allahu zan juyo”.
“To ba damuwa, kin yi sallama da Baban ku ne?”
“Eh, tun kafin ya fita ma.”
Umma ta jawo Muhammad jikinta ta-ce. “To, banda kiriniya Babana. Yaushe za ka dawo?”
“Ni kam a can zan zauna.”
Umma ta yi dariya ta-ce. “Shi kenan, idan ka zauna a can, na fasa auren.”
“Shi kenan Mama za ta aure ni ai.”
Suka yi dariya, sannan suka fita, inda Yaya Abbakar ke jiran su. Mama ta yi murnar ganinsu sosai, da gudu Muhammad ya shiga falon Abba, yana cewa yau kam ya dawo kuma sai an masa aure da Mama ya koma. 
Mai-jidda na zaune a dakin Mama, ta shigo dakin, haka kawai ta samu kanta da faduwar gaba da kuma jin wani iri, musamman da ta gan shi ya shigo rike da Ramla a hannunsa, tana murmushi ta-ce. “Mamin Mimie, ku na nan ashe ba ku koma ba.”
“Kai Anty Hauwa, har na ji kunya, ba ki ganmu ba, duk ga shi nan Sweety ne ya yi ta wasa da hankalinmu”.
“Ba komai ai, komai lokaci ne, shi kam ai muna ganin shi ko bai fada miki ba?”
Nan take hankalin Abdul-Aali ya tashi, ya dubi Mai-jidda da sauri ya kada mata kai hade da cewa. “Rabu da ita Jidda, tun zuwansu in banda yawo, ba abinda suke yi”.
Mai-jidda ta yi murmushi ta san Hamama ba ta da labarin abin da yake da shirin yi, don haka ta san maganin sa.
“Mamin Mimie ku wane irin aiki ku ke yi ne? Kun kwashe wata guda ba ku wurin aikin ku.”
“Ai sai wata mai kamawa ne zai koma bakin aikin na sa.”
Mai-jidda ta karbi Ramla, tana mata wasa. “Ina Muhammad din yake?”
“Muna shigowa, ya yi falon Abba yana can yanzu haka ya cika shi da surutu.”
Tana sane da Abdul-Aali dake zaune kan kujera bai fita ba, don haka gaba daya ta kasa sakewa. Hamamatu ta-ce. “Ki na nan ne ko kuwa yau za ki koma?”
“Zuwa Sunday dai Insha-Allahu, zan duba su Yaya Maryam”.
“Allah Sarki, ya kwana biyu ba mu hadu da ita ba Sweety, yaushe za mu je na gaishe ta?”
Abdul-Aali ya kalli yadda Mai-jidda ta hada rai, sai ya-ce. “Tunda ita ma za ta je, ba sai ki jira, idan ta zo tafiya, sai na kai ku ba?”
“A’a kar mu bata maka lokaci, ka bar ta kawai, za mu yi tafiyar mu.” Mai-jidda ta fada da sauri.
“Ke ma dai kya fada masa Anty Hauwa, bini-bini ko ina, sai ya-ce shi zai kai mutum, ba dama nace ya ba mu, ko danin motarsa mu zagaya son ran mu, sai ranar ne ya ba mu sau daya.”
Mai jiddah dai babu abinda yake damunta irin yaddah Abdull_aali yake mata wani irin kallo a gaban matarsa duk sai wani iri take ji gashi ya samu wuri ya zauna baida niyyar fita sai canja tasha yakeyi a TV 
Amma tana sane don sau biyu suna hada idanu idan takai masa harara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page