EL-MUSTAPHA CHAPTER 3

EL-MUSTAPHA
CHAPTER 3sosai likitan ya karaya, kukan jiddah na tsuma xuciyarsa, yanaji kamar ya gaya mata gaskiya patient din lafiyan ta qalau sakashi tayi.

Bata qara sauraren shi ba ta fito daga office din, inda aka kwantar da uwani ta nufa, tana kwance idanunta a lumshe kamar da gaske barci take.


‘meyasa xaki min haka uwani? Meyasa kike son mijina, meyasa kike son rabani da farin cikina, why can’t you stay alone with Yusuf and free my husband, el’mustapha baya cikin k’addarar rayuwar ki, kece kika ja kuma watarana xakiyi dana sani kasancewar ki mata a gurin sa.

Daga inda uwani take kwance kamar ta tashi ta fara rawa saboda tsananin farin ciki, xata auri el’mustapha? Dana sanin me xatayi, ai baxata taba dana sanin auren sa ba tunda mallakarsa take son yi ya xamto ba wata sauran mace a xuciyarsa sai ni Aisha Uwani koda kuwa ke jiddah ce ko ya’yansa,

Ana maganar maza irin su el’mustapha wake sanyo su Yusuf aciki, idan tana tunanin ni kadai xan xauna a gurin Yusuf haka ma watarana ni kadai ce a xuciyar el’mustapha, sannu sannu ai bata hana xuwa sai dai a dade baa kaiba, muje xuwa.

Xama jiddah tayi tana sharar kwallah, numfashin ta na sauka a hankali saboda yanda xuciyarta ke mata xafi, bata da xabi a rayuwarta na ganin ta ceto rayuwar uwani ba dan komai ba sai dan iyayenta da suka riqe ta amana, baxata so yaranta su salwanta saboda wani dalili na damuwa ba, amma taya xata iya xama da uwani a matsayin kishiya, taya xata jure ganin el’mustapha da wata mace a rayuwarta.

Ya Allah ka kawo sauqi, ka bani haquri da juriya naganin na cinye wannan jarabawa taka.

Bata jima asibitin ba ta fice bayan ta turo wacce xata xauna da uwani,

Su Aryan na dawowa makaranta ta tura su inda mama mahaifiyar el’mustapha, ko kadan bata son hayaniya da yawan surutu, she needs to stay alone har lokacin da el’mustapha ya dawo.

Wayoyin sa ya ajiye yana kallonta,
‘ya jikin Uwani, inaji duk damuwar tane kika xauna anan shiru?

Ta sauke numfashi tana kallonsa batayi mamakin jin ya san uwani bata lfy ba cos duk abinda suke ciki idan dai har sun fita sai an buga an sanar dashi, akwai tsaro sosai tsakanin gidan da yan’sanda.

‘Barka da bawowa,
Ya xauna kusa da ita,
Gobe xanje xamfara, akwai mutanen mu da yawa da aka kashe attack din da aka kai masu acan, am not happy idan kinje harda ASP Mukhtar Takai an kashe,

Subhanallah, Allah ya gafarta masu, ya tsare mana kai a duk inda kake.

Amin jiddana, kibani abinci inci inajin yunwa sosai, sai a lokacin ta tuna duk yinin ranar bata ci komai ba,

Ta tashi ta soma hada masa kayan abincin a inda yake xaune yana latsar wayarsa, duk wani movement din ta akan idonsa tana yin komai ne a sanyaye babu kwarin jiki, haka babu walwala a tare da ita kamar ko yaushe idan ya dawo daga office, ya dauki hakan a matsayin qila saboda yar uwarta bata lafia ne,

Tare suka ci abinci suna fira jefi jefi duk bai wuce al’ummar da ake kashewa bane da kuma mutanen sa yan sanda da aka kashe.

‘Washe gari sai ga uwani ta dawo wai anyi discharging nata, yanda ta shigo gidan sukuku sai ka dauka kamar da gaske bata lfyr ne.

A raunane ta qarasa inda jiddah ta tsugunna da gwiwowinta duka biyu idanunta taf da hawaye,

Halin da take ciki yasanya jiddah rudewa, ta riqa ta da sauri tana kiran banan, uwani ta lafe jikin jiddah tana sauke numfashi da sauri sauri kamar wacce rayuwarta xata bar jikinta.

Kada ki mutu uwani, indai el’mustapha ne xaki aure shi kiyi rayuwa dashi kamar yanda kike buri, ni kaina nasan mutuwa xanyi xuciyata xafi take min.

Ta fashe da kuka sosai, jikin uwani yayi sanyi ta daina abinda take sai dai idanunta a lumshe suke, hawaye ke fitowa a idanuwanta jiddah tayi matuqar bata tausayi tana son farin cikin jiddah amma baxata iya haqura da el’mustapha ba, kuma ta yarda 100% jiddah na qaunarta da xuciya daya dalilin haka take ganin jiddah baxata cutar da ita ba, anty jiddah kiyi haquri baxan iya haqura da el’mustapha ba,

Banan ta shigo falon da sauri tana amsa kiran jiddah, halin da ta same su ciki yayi matuqar rudata, kuka sukeyi musamman jiddah, shekara uku tana xaune a gidan bata taba ganin hawayen jiddah ba sai ranar, bata bi ta kan uwani ba tayi inda uwar dakin ta,

‘Anty jiddah meya faru, wani ya mutu ne.

Jiddah ta bude idanuwanta tana kallon banan, kafin ta dubi inda uwani take kwance tana hawaye sai ta tashi batare da tayi magana ba tabar falon.

Banan kallon uwani tayi kafin ta maida dubanta ga wani photon el’mustapha wanda yake tare da jiddah. 

Jin shiru ya saka uwani bude idanuwanta, wayam babu jiddah a falon ta dubi banan cikin mamaki abinda taga tana kallo, ba zato ba tsammani banan taji saukar Mari a kuncinta wanda ya saka ta xabura hade da dafe kuncinta tana xaton ko jiddah ce. 

Ganin uwani ce ya sakata xare idanuwanta, 
‘meyasa kike kallonsa, ki gayamin ko na illataki a yanxu, 

‘bashi ne nake kallo ba anty jiddah nake kallo, ina tausayinta ne na ganta tana kuka. 

Mtsewwwww good for you, fice daga falon nan munafuka, sum sum ta fice da sauri bako waiwaye.Sum sum uwani tabar falon ta nufi dakin ta.

Daren ranar suna kwance da el’mustapha, 

‘ina so naje birnin kebbi gobe tunda xakaje xamfara, dama ina so na duba hajiya kwana biyu banje ba. 

‘meyasa baxaki bari idan nadawo muje tare ba, nima ina so naje na gaidata. 

‘A’ah, ina son naganta ne baxan iya jiran ka ba, please let me go, 

‘akwai abinda kike boyemin jiddah, my eyes are on you, kina ganin kamar hankalina ba guri daya yake ba, kina cikin damuwa kike boyemin, meyasa kika canxa min jiddah, ashe dama akwai lokacin da damuwar ki baxata xamo tawa ba, why did you change, kigayamin damuwar ki, ina so nasani a yanxu. 

Tayi qoqarin saita numfashinta, jikinta ya dauki rawa, hawayen da take boyewa suka soma xarya, 

‘amma kasan ina son ka ko?

damuwar ki nake son ji, ba son da kike min ba, idan har ban cancanta nasan damuwar ki babu mgnr wata soyayya da kike min, you are deceiving yourself jiddah. 

Ba yanxu take son sanar dashi ba har sai taji raayin iyayen su tukunna, tasan halin el’mustapha sarai xai iya hanata tafiyar idan batayi da gaske ba, hannunsa ta riqo tana kallonsa. 

Uwani ce damuwa ta you know, ban gayama dalilin kwanciyarta asibiti ba, likitoci sunce tana cikin damuwa kuma ta kamu da ciwon xuciya a kowanne lokaci xata iya rasa rayuwarta, nayi juyin duniyar nan ta gayamin damuwar taqi shine nake so naje na sanar da hajiya kada wani abin yaxo ya sameta batare da sanin su ba. 

Yaja numfashi yana kallonta, you are right jiddah na fahimce ki, amma tare da uwani xakije ne?

Aa bana son tasan da tafiyar Ma, 

Allah ya tsare ya kaiki lafia, amma ni bana son kina damar da xuciyarki saboda uwani, kinsan dalili? Ta girgixa kanta tana kallonsa, 

Saboda uwani bata taba damuwa dake hakan ba, akwai wani abu dana ke boye maki game da uwani wanda ke baki sani ba, tun daga lokacin nadaina ganin mutuncin ta. 

Xuciyar jiddah ta tsananta bugawa to kodai el’mustapha ya san uwani na sonsa ne?

Sanda akace xaa yi maki c.s ga haihuwar twins wlhy uwani is happy, ina kallonta babu damuwa a tare da ita kamar iyayenku, hajiyarku harda kuka tayi, did you know that, jiddah ta girgixa kanta. 

Shiru tayi tana saurarensa, maganar sa gaskiya ce, uwani tana son rusa farin cikinta saboda son el’mustapha, no it can be possible, uwani baxata mata haka ba tasan uwani tana son ta kuma tana nuna mata soyayya, gashi sanadiyar el’mustapha tana neman rasa rayuwarta, idan har mgnr el’mustapha gaskiya ce uwani ta cutar da ita Allah baxai barta ba kuma xai saka mata, duk wanda yayi niyar aikata alheri baxai taba tabewa a rayuwa ba, taimakon uwani xatayi saboda iyayenta kada ta rasa rayuwarta dalilinsa. 


‘Wannan tunanin yayi yawa jiddana kixo ki kwanta, el’mustapha need you today komai ina so daga jiddatulmusty, 

Murmushi tayi tana kallonsa cikin so da qaunarsa, tau baban biyu bani minti biyar kacal na shirya, 

Janyota yayi, ya kwantar da ita, a hakan nake son jiddana, bana son wani abu da xatayimin saboda ta birgeni, kome jiddah xatayi ina son ta, tana birgeni, kuma duk wanda baya son jiddah nima bana son shi. 

Hannu tasa ta rungumosa sosai, yayin da ya hada fuskarsa da tata yana shaqar qamshin jikinta. 

*

‘Washe gari el’mustapha ya nufi xamfara, jiddah Ma ta shirya sai da xata tafi ne ta sanar da uwani xataje birnin kebbi kan maganar taji raayin iyayen idan sun amince. 

Abu biyu ne ya hadewa uwani farin ciki jiddah ta amince xata bari ta auri el’mustapha da kuma yanda xata shige mata gaba a auren, sai fargabar abbanta wanda take ganin da kyar ne xai iya amincewa da auren da kuwa ta shiga uku. 

Sai dai abinda jiddah ta jiyo uwani na fada a waya yayi matuqar bata tsoro da tada hankalinta matuqa wanda ya xama dole ta amince da auren el’mustapha da uwani idan ba so take ta ruguza mata farin cikinta ba. 

‘Walllahi baxan haqura da el’mustapha ba surry kidaina min mgnr bana so, da kinsan yanda numfashina ke bugawa tare da qaunarsa da baki nemi in barshi ba, ke idan fa ta kama ko nijar xan iya xuwa inda boka domin farin cikina. 

Hankalin jiddah ba qaramin tashi yayi ba jin uwani ta ambaci boka, abin ya kai har haka, meyasa uwani keson ganin bayanta, bata nunawa uwani taji komai ba sai dai kallon da takewa uwani a yau daban ne da irin wanda ta saba yi mata a matsayinta na yar’uwa. 

Babu kunya ta soma yiwa jiddah godiya ta rakata har harabar gida, inda mota ke jiranta, police biyu ne tare da ita wadanda xasuyi tafiyar, ta bude motar ta shiga tana adduar tsari a xuciyarta. 

Tun da jiddah taje masu da mgnr da abinda ya sami uwani a asibiti iyayen suka soma kumfan baki, basu yarda da maganar ba kuma basu yarda uwani ta auri el’mustapha ba, domin ya xama cin amana garesu, 

Duk iya qoqarin jiddah ta kasa shawo kansu sai Ma sabani da suka samu da hajiya wanda ta dauki fushi da ita mai tsanani, 

Dalilin hakan yasa jiddah ta fasa komawa a ranar dole sai tayi convincing iyayen har su amince da auren bata son abinda xai taba mijinta da lafiyarta dan baxata iya  gayamasu abinda taji uwani ta fada a daxu ba. 


‘Washe garin ranar sama sama suka gaisa da Hajiya, 

‘hajiya kiyi haquri bana son fushin ki ko kadan, tunda na taso ban taba fuskantar wannan canjin daga gare ki ba, ki sassauta min fushin ki agareni ba alkhairi bane. 

‘baxaki taba ganin canjin fuskata har sai kin janye mgnr ki akan uwani ta auri el’mustapha, Sam ban amince ba shiyasa tun farko da ta gayamin daga ni har abbanku ba wanda ya goyi bayanta. 

Kallon mamaki jiddah ke mata, ashe Ma tasan da mgnr kenan, tuntuni uwani keson el’mustapha aka boye mata meyiwuwa wannan dalilin ne ya saka har ta kamu da ciwon xuciya bata sani ba. 

Kuka jiddah keyi sosai mai taba xuciya wanda kukan yayi matuqar daurewa hajiya kai, 

Jiddah saboda na hana uwani ta auri el’mustapha ne kike wannan kukan?

‘bana son na rasa uwani ne hajiya, tare muka taso muke rayuwa tare da ita, baxan so ta rasa rayuwarta saboda abinda take so ina da iko akan sa ba, meyiwuwa el’mustapha yana cikin qaddarar mu shi mijin mu ne. 

Mijinki ne jiddah ke kadai bana son kibiye uwani Sam ban yarda da ita ba, mahaifinta Ma bai amince da auren ba, tunda kinji xaki iya kije gaki ga uwani ki aura mata abinda kike so a rayuwarki amma bada yawun bakin mu ba, ina roqon Allah ya albarkaci rayuwarki jiddah ya kuma kareki ga duk wanda ya nufeki da sharri, ke yar halaq ce. 

Godiya jiddah tayi ita kadai tasan abinda take ji a xuciyarta game da wannan auren, tana tsoron uwani tabi wata hanyar da bata dace ba domin ta mallaki el’mustapha kamar yanda taji tana fada, tana tsoron uwani a yau da komai nata. 


Kusan marece suka iso abuja, uwani taxo yi mata barka da dawowa da son jin bayanin iyayenta daga jiddah amma bataga wannan fuskar ba, babu alamar wasa a tare da jiddah tunda suka gaisa bata qara kallon uwani ba, toilet ta nufa domin ta watsa ruwa. 

Jiddana ta tafi gida ta dawo amma na rasa gane kanta, bai jira cewarta ba ya fara making love da ita, 

Duk abinnan da yake idanun jiddah a lumshe suke tana tunanin watarana fa haka xaiyiwa uwani, 

El’mustapha kuwa sosai ya rungumeta wata qila inda hali da ya tsaga qirjinsa ya sanyata ciki saboda qaunarta, mai yiwuwa sannan ne xai xamo contented. 

Sai da komai ya lafa ya fahimci jiddah kuka take, kukan da nayi matuqar daure masa kai, 

Duk sai ya rikice, kukanta da hawayenta suna matuqar daga hankalinsa

Ya tarairayo ta ya dorata akan qirjinsa, cikin sassanyar murya yake tambayar _did I hurt you jiddah?_, ta girgixa kanta, batasan yanda xatayi masa mgnr ya auri uwani ba domin tana matuqar tsoron abinda xai biyo baya, sai dabara ta fado mata, cikin sheshshekar kuka tace, 

Ni dai ka qara AURE… 
Sai ya janye jikinsa da nata cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwowi, tare da tsananin mamakin jin wannan kalmar daga jiddansa, wani irin kallo yake jifanta dashi, 

Kafin in baki amsa jiddah ko nabi umarnin ki ina so nasan dalilinki na son na qara aure?

Saboda el’mustapha ya cancanta ace yana da mata biyu, matsayinsa ya kai, shekaru kusan nawa rabona da haihuwa ya kamata ace su Aryan suna da qanni yanxu kuma nasan kaima kana buqatar hakan, 

Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken farin wata daya keto shara sharan farin labulen dakin, kafin yayi murmushin takaici ya xauna sosai ya bata baya. 

Hauwa’u haihuwa ce tasa na aure ki ko kuma tun bayan haihuwar twins kin taba ganin wata alama dana nuna maki ta ina son na qara haihuwa?

Ta girgixa kanta, idan Ma haihuwar ce ke kike baiwa kanki ne? Inaji ko haihuwar ce baki taba yi ba baxaki nemi na qara aure ba ballantana Ma kin haihu, 

Ni ina son yarane a ynxu el’mustapha, ina so naga yara sun cika gidannan, shiyasa nake son ka qara aure dan Allah, 

Ki gayamin idan twins ba yara bane, baligai ne, yaran dake nursery 2 yanxu sune ba yara ba, wai me kike nufi ne jiddah?

Xatayi magana ya daga mata hannu a fusacce, ya isa… Ya isa jiddah…. Sai ma ya rasa me xai ce mata saboda takaici, dogon tsaki yaja ya dauki wayoyinsa ya bar mata dakin.
Jiddah ta bisa da idanuwanta karo na farko a rayuwar auren su da el’mustapha yayi irin wannan fushin da ita, amma ya xatayi farin cikin su take so, bata son a sanyasu wata hanya da bata dace ba a ruguza masu farin cikinsu ta lura uwani komai xata iya a ynxu da take ganin take takenta, 

El’mustapha yayi wannan fushin dan tace ya qara aure ina ga idan yaji uwani ce xai aura?

Dole ta dage ta nuna masa fa da gaske take har lokacin da xai sauko ya amince. 

Kwanaki uku suna kan wannan taqaddamar, inyayi fushi sai kuma ya sauko yayi dariya wai jiddah ke son ya qara aure, baisan jiddah ita kanta qarfin hali kawai take ba, tana matuqar axabtuwa da rashinsa kamar yanda shima yake yi. 

A rana ta hudu ya kasa jure wannan tsiri da take masa na shariya, dan bashi da wannan juriya ta wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan, sai ya cafki hannunta ya langabar da kai kamar qaramin yaro, idanuwansa sun juye sun rikide xuwa ja, idan Ma wasa take zai gwada ta shima ya gani ya nuna ko a jikinsa. 

Jiddah na baki wuqa da nama, kece mijin kece matar, ki xabo min duk yarinyar da kike ganin ta dace dani don bani da idon kallon wata d’iya mace tun daga lokacin da Allah ya mallakamin ke…. 

A hankali take dubansa yayin da gabanta ya tsananta bugawa

Ganin yanayin ta, qiris ya rage ya saki dariya amma sai ya cije, 

Yace ki nema min niko acikin manya manya qawayenki ne ko riqaqqun yan boko irin su Nabila Mohd, 

Haushi ya kama jiddah sosai, ga kishi ga kuma ganin ya maida abin xolaya, 

Ya rungumota ta baya ya dora kanshi a kafadunta, a sanyaye yace, 

‘ko kin daina sona ne jiddah kike neman kai dani? A da ko kallona wata tayi wanda bai maki ba sai kin kwana baki min magana, amma yanxu duk kin daga hankalinki wai inyi aure which means kin gaji dani, kin daina sona, kina neman mataimakiya a yanxu don ki huta, meyasa jiddah, me nayi maki, wane canji kika fuskanta daga gareni domin inyi gaggawar gyarawa?

In gayamiki gaskiya baxan iya sharing kaina ba, ina da kyankyami kin sani, ba kowace mace xan iya hada jiki da ita ba, babu, ban taba ba, kuma bana fata, baxan iya adalciba, ance kuma idan baxaku iya adalciba ku xauna da daya. 

Amma inkin gwammace ranar qiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same sai na auri Nabila, kinga daganan sai ku qara danqon xumunci abotarku tayi qarfi ni kuma na sami yara da yawa shikenan?

Ta ture shi da sauri duk da jikinta yayi matuqar sanyi da kalamansa domin gaskiya yake fada mata, don shi baya fadin abinda ba haka bane a xuciyar shi don kaji dadi ko dan ya faranta maka, in hakane kenan el’mustapha da gaske xai iya auren Nabila?

Magana take yi a xucci bata san ta fito ba, ya sauka a gadon ya xauna dabas akan carpet, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi, 

Ni *el’mustapha* na shigesu duk yanda nayi ban yi dai dai ba, to ki fadi yanda kike so ni mijin tace ne. 

Idanunta fal da hawaye wai ana wata ga wata, 

Yanxu el’mustapha son nabila kake?

Yayi murmushi yana lasar labbansa, 

Yaya baxan so taba tunda aminiyar matata ce kuma itace xata riqa bani ya’ya a yanxu. 

‘ni ba wannan nake mgn ba, 

Duk da kuka take batasan sanda tayi dariya ba, ganin ya dawo ya rungumeta yasa ta biye masa. 

She have no choice banda ta rungumi mijinta mai sonta mai qaunarta, ta nuna masa sonsa kadai ne a xuciyarta. Banan yau kinje makaranta kuwa?

‘banje ba anti jiddah, 
‘meyasa baki je ba, 

Ta soma inda inda cikin fargaba, dama.. dama anti uwani ce ta hanamin xuwa yau. 

‘akan wane dalili?
‘ta bani kayanta ne na wanke bayan na shirya xanje makaranta, na roqi ta bari har na dawo na wanke shine taqi, makarantar ma tace baxan je ba. 

‘kira min uwani, banan ta tsorata ta xaro idanu, 

‘Anty jiddah kiyi haquri, xata ce nakawo karar tane gunki dukana xatayi. 

Jiddah bata kula ta ba, ta daga murya tana kiran uwani kusan sau biyu kafin ta amsa, 

Ta fito da sauri harda wani russunawa, 
‘Anty jiddah naji kina kirana, 

‘akan wane dalili xaki hana banan xuwa makaranta?

‘aiki na sakata anty jiddah taqi tayi saboda ta raina ni. 

‘wannan ba hujja bace uwani, ban taba gayamiki kowacece banan bane, marainiya ce bata da iyaye, kakarta ta kawo amanar ta tayi aiki a gidan nan, kuma kina gani lokaci lokaci tana xuwa duba ta, kasancewar ta marainiya yasa na saka ta makaranta domin ta sami ilimi da xatayi alfahari dashi watarana, ina son maraya kuma bana so naga an takura maraya duk mai yin haka baxan xauna inuwa daya da shi ba, ba banan kadai ba duk masu aikin gidannan, babba da yaro har tsofaffin ina lura dake ba wanda kike ragawa, duk cikin su ba wanda ke qarqashinki ko kike ciyarwa game da takurasu da kikeyi kada ki sake, kuma daga yau kada ki sake baiwa banan wankin kayanki, akwai washing machine idan baxakiyi da kanki ba kibari. 

Uwani ta hadiye wasu yawu da kyar yayin da wani qololon baqin ciki ya taso ya tokare xuciyarta, baa taba wulaqanta ta ba kamar yau kuma wai agaban shegiyar nan banan, idan ta xamo matar gidan ta hana mata iko dasu, wlhy ta ja masu, amma tunowa da tayi ita ke nema yasa ta qara russunawa hade da kwantar da muryarta, 

‘Allah ya huci xuciyarki anty jiddah insha Allah xan kiyaye, ta juya tana kallon banan kamar da gaske, banan kiyi haquri nima ina son maraya a xuciya na. 

Jiddah ta dube ta tana fadin, xo ki cigaba da gyaramin salad din kafin abokan wasar naki su dawo, 

Banan ta xauna cikin farin ciki, uwani kuwa ji take kamar ta shaqe ta ta huta, ta qara matsawa kadan yanda banan baxata ji taba. 

‘Anty tunda kika dawo nake xuba kunnuwa naji mesu hajiya suka ce game da mgnr amma kinyi shiru shiyasa har na kasa jurewa nake tambayar ki a yanxu. 

Kallonta jiddah keyi cike da mamaki, 

‘Na tambayeki uwani, ta gyada kai tana kallonta. 

‘ki gayamin tun yaushe kika fara son el’mustapha, 

‘wlhy anty na fara sonsa tun ranar dana fara ganinsa, sonsa nake tsakani da Allah da xuciya daya ba dan na cutar dashi ba ko na cutar dake anty kinsani kuma nasan ke baxaki cutar dani ba kasancewar yar’uwa a gareni dan ‘Allah ki taimakamin anty. 

‘taya xan taimakamiki bayan iyayen mu basu amince ba, Yusuf suke so ki aura ba el’mustapha ba. 

‘ashe har wadanda suka haifeka xasu iya Ma baqinciki a rayuwa? Ta fada a xuciyar ta batare da ta furta a fili ba. 

‘bayan wannan, ashe xaki iya xaman kishi dani, xaki iya auren mijina ina raye bawai mutuwa nayi ba, meyasa kike son mijina uwani, meyasa kike son rusa min farin cikina, kinsani da xuciya daya nake sonki, xaman ki da Yusuf xai fiye maki farin ciki akan auren ki da el’mustapha domin baya sonki kuma baxai taba qaunar kiba. 

Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un, dama likita yace kin kamu da ciwon xuciya, shine har kin fara aman jini, subhanallah meyasa uwani kike son rasa rayuwarki saboda abinda baki da iko akai, idan ni na amince ki auri el’mustapha shi kuna yaqi ya xakayi. 

‘Anty ke xaki sa ya amince, nidai ko shekara daya ne ya aureni dai dai lokacin xuciyata ta sami sauqi sosai akansa, wlhy anti na amince nayi auren shekara daya dashi kice ya sakeni baxan damu ba. 

‘mutumin da kike so kamar ki mutu har kina son a rabaki dashi auren shekara daya kacal uwani ina son da kika ce kina masa. 

Uwani ta daburce ta soma inda.. Inda.. anty ko auren kwana biyu ne ina so ko ba komai burina ya cika na xama matar wanda nake so a rayuwata, wlhy baxan tabbata da mijinki ba kibani shi na shekara guda xan bar mikishi na nesan ta kaina dashi, ina so na sami sauqin ciwon xuciyata na warke daga cutar da ta kamani. 

Jiddah taja numfashi, tana maimaita mgnr auren shekara daya uwani, idan kika aure sa bayan shekara daya mutane sukaji ya sake sa so kike a xargeni? Idan hakane ki haqura dashi…. Kafin ta qarasa uwani ta duqe gurin hade da dafe qirjinta tana Jan numfashi sosai tana daukewa, ta kakkafe idanuwanta kamar da gaske mutuwa xatayi wanda yayi matuqar ruda jiddah harda banan Ma dake saurarensu, 

Jiddah ta soma jijjigata tana kiran sunan ta da qarfi wanda ya janyo hankalin mutanen gidan gare su harda securities din Ma, 

Duk aka kewaye su tuni jikin jiddah ya fara rawa ta soma kuka sosai, banan taxo da ruwa ta kwarara mata, ta sauke wani numfashi da kyar tana fadin, 

Wayyo qirjina, ku taimakeni mutuwa xanyi, anti jiddah xan mutu, wayyo anti jiddah. 

Wani dan sanda a gurin yace, hajiya bari aje da ita asibiti xaifi tunda qirjin nata yana ciwo haka. 

Jiddah ta share hawayen ta tana fadin to shikenan, ku kamata ku saka ta a mota kuje, duk abinda aka nema kai sai kayi ni baxan je ba. 

El’mustapha tare suka dawo da su arham yaje ya daukosu inda mama, rungume ya’yan tayi tana farin ciki, suma haka ne a gurin su sunyi missing mamin tasu sai faman surutu suke xuba mata. 

‘Angon jibi kaxo mu fara tattauna kan maganar mu fa, 

Kallonta yayi yana xare safar qafafunsa, 

‘Uwargidan el’mustapha me kike so mu tattauna akai, idan nabila ta amince nima na amince dama xan dauki Hutu kuwa yanda xan angwance da kyau. 

Murmushi jiddah tayi cikin qarfin hali tare da danne kishinta. 

Tace Uwani bata da lafiya anje da ita asibiti, yanxu ta kai uwani har aman jini take yi, abinda uwani keso ina da iko akansa kuma ina son na inganta rayuwarta, ka taimakeni el’mustapha kada ka bani kunya, 

‘ina jinki jiddatulmusty kome kike so xaayi, me uwani ke so kudi ko me?


Kai… Kai.. take so el’mustapha, auren shekara daya ne, akwai yarjejeniya akai ku…… tayi shiru sakamakon wani kallo da el’mustapha ya jefe ta dashi sai da tayi suman xaune. 

Kallon Aryan da Arham tayi hade da fadin, kuje inda banan yanxu xan fito nima, duk mgnr da takeyi jikinta rawa yakeyi tun daga kallon da el’mustapha yake mata. 

Suna fita ta juya tana kallonsa cikin marairaicewa, 

‘Dan Allah el’mustapha kada kaqi… Shut up pls ya katse ta cikin tsawa, 

‘wai me kike nufi ne, me ya same ki, kinsan me kike fada, na auri uwani, akan wane dalili, ni el’mustapha na auri uwani, lallai yau na saka ki cikin jerin mata marassa hankali da wayo, idan har wasa kike kada ki qara kwatanta min irin wannan wasar domin baxakiji dadina ba, ya tashi a fusacce ya bar falon xuciyarsa na tafarfasa. 

Kuka take yi sosai, kukan da bashi da mafita illah ta cigaba da convincing el’mustapha har lokacin da xai yarda da auren, su taimaka su ceci rayuwar uwani dake kwance a asibiti tana fama da ciwon qirji. 

Binsa tayi dakin, bakin gado ta xauna tana jiransa har lokacin da ya fito wanka, da sauri ta qarasa gabansa kafin yayi wani yunquri ta riqo qafafunsa tana kuka. 

Fincike qafafunsa yayi daga gareta, haushinta yake ji sosai, abinta ya xama rainin wayo, taya xata xo masa da maganar ya auri uwani, wai uwani ya qara nanatawa a xuciyarsa yana mata wani irin duba mai cike da dimbin mamaki, tayi saurin sunkuyar da kanta baxata jure kallon kwayar idanun sa ba a yau. 

Doguwar jallabiya ya xura ya fita daga dakin gabaki daya, sosai jiddah ta shiga damuwa. 

A daren ranar yini tayi sukuku ba walwala a tare da ita, da kyar ta iya yin wanka, binni binni tana kallon agogo dare ya tsala sosai amma el’mustapha bai dawo ba, bai xo yaci abinsa ba ita Ma ta kasa cin abincin, ta kira wayarsa tana ringing bai dauka ba. 

A falonsa ta xauna xaman jiransa, barci ya soma fisgarta, sanda ya dawo kallo daya yayi mata ya dauke dubansa daga gareta, motsin dawowar sa ya farkar da ita, tabi bayansa da sauri lokacin da yake qoqarin cire jallabiyarsa.

‘Dan Allah ko menene ka ajiye shi a gefe kayi haquri kaxo kaci abinci, dan Allah mijina kada kamin wannan horon, lets save a soul, tana buqatar taimakon mu, ya kake so tayi da rayuwarta Allah ne ya dora mata. 

let her die, sai me? Ina ruwan wani, idan ke damuwarta damuwarkice sai akace harda el’mustapha? Duk garinnan ba namiji ne sai ni, ya nuna ta da yatsa cikin matuqar bacin rai, 

Look jiddah, I can’t take it anymore, kada ki qara xomin da magana irin wannan. 

Kwanciya yayi akan gado bayan ya rage hasken dakin, jiki a sanyaye ta hau gadon matsawa tayi sosai xuwa ga jikinsa, dogon tsaki yaja bayan ya janyeta daga jikinsa, juya mata baya yayi hade da Jan blanket ya rufe jikinsa har kansa. 

Bata iya daukar wannan fushin ko kadan, xuciyarta ta karaya, ta soma hawaye sosai hade dasa hannu ta toshe bakinta kada sautin kukan ya fito, 

Kadan kadan yake jin sautin kukanta, yana jinsa har cikin ransa, he can’t take it anymore, ya juyo a fusacce hade da kunna bedside lamb, 

Ban nemeki ba kece kika kawo kanki baxaki xo kidameni da sheshshekar kuka anan ba ki hanamin barci You can leave pls, ya fada lokacin da yake qoqarin hada ido da ita. 

Haduwar idanuwansu ya sanya xukatansu bugawa lokaci daya, akwai soyayya mai tsanani tare da wadannan masoyan, bacin rai ke dawainiya dasu, yanda idanunta sukayi luhu luhu ya sanyashi weakness, bai qara magana ba ya juya ya kwanta abinsa, ganin haka ya sanya ta rungumosa ta baya, daga shi har ita suka sauke numfashi lokaci daya ba kamar ita kamar wacce tayi gudun fanfalaqi. 

*


Kusan sati daya babu canji daga el’mustapha, tun da safe xai fice ya barta baxai dawo gidan ba sai tayi barci, sosai ta shiga damuwa, ga uwani tunda ta fuskanci akwai matsala ta kwanta ciwon qarya bata cin komai sai Lipton, daga ita har jiddah sukayi wata irin rama, 

Ana haka mama taxo gidan, yanda taga jiddah sai da hankalinta ya tashi, 

jiddah ko dai ciki ne dake kikayi wannan ramar?

Ta girgixa kanta cikin jin nauyin ta, 

‘ki gayamin damuwar ki, idan el’mustapha ne inji, kinga yanda kika lalace kuwa?

Shiru kawai jiddah tayi batare da tayi magana ba, sosai mama ta matsa da sai taji damuwar jiddah har lokacin da tagayamata komai tana kuka. 

‘Wannan mgnr babu dadin ji Sam jiddah, el’mustapha baxai auri uwani ba ni kaina bana son yarinyar.

Mama ki duba halin da take ciki, tana axabtuwa da qaunarsa, dalilinsa ta kamu da ciwon xuciya, kije kiga yanda uwani ta koma a yanxu, baxan iya samun nutsuwa a yanxu ba har sai uwani ta sami abinda take so, dan Allah ki saka baki ya amince da mgnr mama, ta soma kuka sosai, 

Mama taji tausayin jiddah, ke kam rayuwarki dabance jiddah, kowace mace tana gudun kishiya ke kina roqo da kukan ki, kuma yar uwarki kike so a aura, ina ma laifin wata qawar kice daban amma Sam rayuwar uwani bata dace da ‘dana ba. 

Uwani ta canxa daga yanda kika Santa mama, xo kiga yanda ta dawo, sukaje dakin uwani na kwance tsakiyar dakin tana jin motsin shigowa dakin ta soma wani irin numfashi gwani ban tausayi. 

Mama ta riqe haba cikin salallami da mamakin yanda uwani ta dawo, 

Yanxu saboda el’mustapha ne yarinyar nan ta dawo haka, lallai abin a duba mata ne. 

Suka koma falo suka bar uwani na murmushi, sosai mama ta tausayawa halin da ta tsinci uwani akai tana tunanin idan yar’ta ce a haka ya xataji. 

Bayan kwana biyu sai ga el’mustapha ya shigo dakin jiddah tana xaune tana tana duba wayarta, yanda ta ganshi sai da ta tsorata. 

Ya watsa mata wata harara yana mata wani duba kafin yaja dogon tsaki ya bar dakin.

Dogon Numfashi taja tana kallon bayansa har lokacin da ya fice, 

Tana ganin Allah baxai kamata da laifin komai ba tunda alheri tayi niyar aikata, bata ga laifinta anan ba illah son xuciyarta da tagani, yes da gaskiyar el’mustapha da yace ta shiga haqqinsa ta tursasa xuciyarsa auren abinda baya so, insha Allah komai xai wuce kamar baa yi wannan rigimar ba, ta cigaba da duba wayar amma hankalinta baya jikinta. 


*

Uwani ki shirya kije gida inda su hajiya ki roqi gafarar su, su sanyawa auren ki albarka domin kina buqatar hakan saboda babu mai goyon wannan auren naki. 

‘ni har sai naje na roqesu gafara sai kace mutuwa anti. 

‘baxakije ba kenan?
‘A’ah ni bance haka ba, 
‘ki shirya yau kitafi, driver xai kaiki ya dawo shi kadai, kwana biyu xakiyi acan har dangi Ma kije, rayuwar aure da kike gani ba abin wasa bane. 

Uwani bata qara mgn ba amma xuciyarta har wani tuqiqi take, haka taje ta hada kayan tana qunquni ko sallama batayi da jiddah ba ta fice, 

‘au inda ban fito ba ashe baxaki sanarda ni kin tafi ba, kina min wannan abin uwani kuma kike son mu xauna lafiya dake uwani? Tana jin haka tayi saurin russunawa, 

Kiyi haquri anty jiddah, yanayin jikina ne kesani kuya akan komai amma xan kiyaye. 

Ga wannan ki baiwa hajiya kuma ina gaida abba, uwani ta karbi saqon hade da jefawa cikin handbag din ta, murmushin yaqe tayi tana kallon jiddah. 

‘Anty jiddah na tafi kimin addua, 

Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya, 

Amin ta juya ta fice.

*

Sanda uwani ta iso gidan taga canji sosai wanda yayi matuqar bata mamaki daga iyayenta, ashe da gaske jiddah take mata basu farinciki da auren ta?

‘Abba har da kai baka son auren ne? Ta tambaya tana kallonsa, 

‘tunda ke kina so kije kiyi, duniya ce uwani kije gaki gata wanda bai xo cikinta ba Ma jiransa take, duk kika cutar da rayuwar jiddah Allah baxai barki ba kuma xaki gani, Allah ya gani bana son auren nan bana farinciki dashi kuma baxan taba xama waliyyin daura shi ba, tunda bamu isa mu hanaki ba kije kiyi duk yanda kike so da rayuwarki, ya tashi ya fice ta bisa da kallon mamaki a xuciyarta tace banda abin abba shi kadai ne datijjo a duniya da xai xama waliyina, ko dashi ko ba dashi ba ai dama auren xanyi, a fili kuwa tabe bakinta tayi ta juya tana kallon hajiya tana cewa, 

Iyayen yanxu idan baka nuna ka isa da kanka ba kwarar ka suke suci amanar rayuwar ka. 

Kika ce me? Hajiya ta tambaya tana kallonta, 

Uwani ta washe baki hade da gyara xamanta, aa hajiya wace ni d’iyar Malam Adamu addua ce kawai nake masa. 

Addua indai daga gare kice bama buqata domin ba karbabbiya bace, 

‘hajiya kinsan gaibu kenan, gayamin dalilin da yasa baxata karbu ba tunda nidai musulmace, sallah biyar kike yi nima ita nake yi. 

Jikin hajiya yayi sanyi, abin uwani ya soma bata tsoro da mamaki, a da uwani xata maida mata magana amma cikin qunquni ynxu kuma abin yayi tsauri ta kai ido da ido uwani xata iya gaya mata magana. 

Ni dai kam uwani lafiya na gama rayuwata da iyayena har suka mutu kuwa, 

‘nima lafiya qalau xan gama daku, Allah ya nuna mana lokacin. 

Story continues below

😳Xuru hajiya tayi tana kallonta, sai kuma taja bakinta tayi shiru, Allah ya gani sun baiwa uwani tarbiya kamar yanda suka baiwa jiddah, itace ta banxar tar da tarbiya insha Allah, Allah baxai kamasu da laifi ba. 

Xuge jakarta tayi ta dauko saqon jiddah ta miqa mata, gashi hajiya abokiyar xamana tace in kawo maki. 

Ki maida mata indai ta hannunki saqon xai xomin wallahi na yafe, 

Qas… Qas.. Qas… Uwani ta tauna cingam din ta tana maida saqon cikin jakarta, 

Hajiya fushi kike dan xan auri mijin jiddah, ai abin farin cikine, kuma ni bana tunanin cin amanar jiddah a rayuwata saboda tamin halaccin auren mijinta na har abada, ashe da gaske ne wadanda suka haifeka suna maka baqin ciki idan sunga cigaba ya same ka. 

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un shine abinda hajiya ta fada lokacin da hawaye ke fitowa a idanuwanta. 

Ni uwani, ni ke maki baqin ciki, ni kike gayawa magana haka?

‘ga wani baqin ciki na biyu nan kina min, saboda kar naji qamshin aljanna kike min hawaye hajiya, to dan Allah kiyi haquri ki gafarceni ki barni na shiga aljanna lafiya qalau tare da el’mustapha, dan Allah ki yafemin. 

Alherin da kike cewa ina maki baqin ciki akansa kije kigani insha Allah baxaki taba ganin alherinnan acikin rayuwar auren ki ba, Allah ya albarkaci jiddah da ya’yan ta, fuuu hajiya ta fice a fusacce. 


Kwanan ta biyu ta tattara inata inata tabar gidan. 

Ana gobe saura kwana biyu auren, suna xaune da uwani a falo suna tattaunawa akan bikin, el’mustapha ya shigo. 

Kallo daya uwani tayi masa ta soma neman nutsuwarta saboda kwarjini da sonsa dake qara linkuwa a xuciyarta ta xuba masa idanu tana kallonsa, 

Idanunsa kyam akan na jiddah yana murmushi cikin boye damuwarsa kada uwani ta gano akwai yar tsama tsakanin sa da jiddah. 

Ya xauna yana fadin jiddatulmusty me akeyi hakane aka manta dani. 

Cikin yanayin ta mai sanyi take kallonsa, 
‘abubuwan biki muke hadawa mijina kai kuma nasan ba abinda xakayi dasu. 

Murmushin dake fuskarsa ya kau har lokacin bai kalli sashen da uwani take xaune ba, ta kuwa tsura masa ido ba kakkautawa kamar ta hadiye sa take ji. 

‘Na manta ban sanar da ke ba, kada naga kowacce mace ta tako gidannan da sunan taxo biki na rigada na gayawa securities kada su bude mini qofar gidana mata su shigomin. 

Sannan baxaa amin taron biki ko a ina bane ke koda walima ce ban amince ba, 

Hankalin uwani ya tashi bata da ikon magana domin bataga fuskar hakan a tare dashi ba tana matuqar tsoronsa. 

Amma meyasa, jiddah ta tambaya cikin damuwa, kasan auren farko ne yana buqatar koda walima ce. 

Kin dai ji abinda na fada an I mean it, a wannan auren banda waliyi sai ibrahim ne xai xama waliyina dan haka kema ki nemo nata waliyin saboda mahaifinta ya rantse, dama ke kikaji xaki iya kuma nagayamaki kome xai biyo baya ki kuka da kanki. 

Sosai jikin jiddah yayi sanyi, meyasa xakamin haka el’mustapha, bar maganar waliyi naji ko acikin securities din nan ne xan samu, banji kana maganar gidan da xata xauna ba. 

Har akwai wani gida da xan bata ta xauna ya wuce wannan da take xaune a yanxu, ai amaryarkice ko kin manta, uwani ce da kika xaba akaina, har akwai wani gata da xan mata da ya wuce ta xauna a gidan kuma a dakin da take xaune anan xata cigaba da xama shine mallakinta.

Ban fahimce ka ba el’mustapha, wannan dakin da take xaune wai xata cigaba da xama?

kwarai da gaske, 

Itama fa matar kace, kabata ko wancan bangare ne idan har baxaka iya bata gida daban ba. 

Nafiso na saka yan haya aciki, bana son musu. 

Haba mijina dan Allah ka sassauta haka kasani kayan dakin tama baxasu ishi wannan dakin ba, yayi qarami. 

‘Wannan kuma ya rage naki, ai nasan kina son ta kuma damuwar uwani damuwar kice, nafi kowa sanin jiddah uwar tausayice da karamci nasan xaki iya bar mata sashenki ta xauna ke sai ki dawo nan dakin saboda tausayawa. 

Jiddah tayi shiru ta juya tana kallon uwani sai ta ganta tana kuka, to ni ya xanyi, wannan karon banda mafita banda kibi umarnin mai gidan. 

Kudi ya ciro daga cikin aljihunsa ya qirga dubu goma cif ya bawa jiddah, ta karba tana kallonsa da son sanin kudin menene. 

Ba jiddah kadai ba wannan karon Ma uwani ta firgita da jin wulaqancin da el’mustapha ke qoqarin yi mata, wannan wane irin toxarci ne haka. 

Dubu goma sadakin budurwa el’mustapha?

Banyi qoqari ba kike nufi, a maimakon ki gode min, kin manta wani nauyi kika doramin, cin ta shan ta da suturar ta duk sun dawo kaina, a da kudi na dagani sai jiddana da twins dina tayi mana karambanin kawo mana bare ta shiga cikin mu, 

Ya soma laluben aljihunsa, dubu biyu ya ciro ya miqawa jiddah, kinsan kowane aure da yanda arxikinsa ke xuwa inaji wannan kam babu kanta dan ba wanda ya bani gudumuwa sai ibrahim shima dubu biyu ne kacal yace a siye goron daurin aure. 

Shiru ya biyo baya tsakanin jiddah da uwani, 

‘nikam uwani da kin haqura da auren el’mustapha kinga tun baki aure sa ba kenan, 

‘Anty jiddah karki damu, abinda kake so shike wahalarda kai, nasan watarana har gida xai bani, kuma na haqura da bikin, ni yanxu damuwata daya ce. 

Mecece kuma uwani. 

Cikin rashin fahimta jiddah ke kallonta, gyaran me uwani?
Tun da kina ganin ban miki gata bane uwani kije ki hada da kanki, ta wannan fannin banda kwari akai, ta fada cikin takaici da kishin uwani, lallai yarinyar nan bata da kunya. 

Uwani ta dafe qirjinta tana fadin ni xuciyata ke min xafi anti jiddah duk na nemi abu ban samu ba sai ta dinga min xafi. 

Ina ji wannan karon kam idan kika fadi anan, nan xaki cigaba da kwanciya ba wanda xan saka ya kaiki asibiti, abin naki ya xama rainin wayo tunda baki da kunya, ta tashi ta fice fuuu, uwani ta bita da kallo to ko anty jiddah ta fara kishine, bari na lallaba matar nan har a daura auren kada ta bore ta fasa. 


El’mustapha yana dakin sa kwance, komai na jiddah mamaki yake basa yanda ta jajirce ga wannan auren, shi kansa yasan qarfin hali take yi amma yasan jiddah sa game dashi bata da haquri akan kowace mace, lallai uwani ta taki sa’an auren el’mustapha sai dai kam xaman ne bamusan yanda xata kaya ba. 

El’mustapha shiru kawai yayi a saman gado idanunsa a lumshe har lokacin da jiddah ta shigo dakin, 

Kallon sa take tana jin wani sonsa da kishinsa, wai yau el’mustapha ta xai xama mijin wata, watan Ma uwani, batare da tayi magana ba ta juya ta nufi kitchen domin hada breakfast, duk abinda take el’mustapha na kallon ta, yasan kishine ke dawainiya da ita, da shine ya bijiro da aure nan da yanxu yasan babu xaman lafia a tare da jiddah sa. 

Dakin dasu banan suke a bayan gidan ta nufa, maaikatan sai gaidata suke cikin girmamawa yara da manya, cikin sakin fuska take amsa masu kamar yanda ta saba, tsofaffin Dany take barkwanci da su kuwa suna tabawa suna dariya kamar wacce bata da damuwa a tare da ita. 

Ni kam tun jiya banga banan ba, lafiya dai ko. 

Ai banan bata lafiya hajiya tun jiya tana fama da xaxxabi. 

Subhanallah amma shine ba wanda ya sanar dani, ta shiga dakin tana fadin tasha magani kuwa. 

Banan na kwance xaxxabi take, tun lokacin da taji ana maganar uwani xata auri el’mustapha, ta riqo hannu jiddah jikinta yayi xafi rau sai makyarkyata take, 

‘Anty jiddah wai da gaske uwani xata auri Alhaji?

Eh mana yau ake daurawa Ma, me akayi. 

Banan ta fara hawaye sosai, anty jiddah kar ki barta ta aure sa dan Allah. 

Meyasa banan
Saboda ita muguwa ce, bata da tausayi bata dace dashi ba. 

Jiddah ta share mata hawaye, ko kadan bata da kyankyami akan masu aikinta, ta riqo banan sosai, tace uwani ta canxa kuma xakiyi mamaki kada kisa damuwa a tare dake, uwani kuma taimakonta xanyi dalilinsa ta kamu da ciwon xuciya. 

Banan tayi shiru kenan itama idan anti jiddah taji dalilin el’mustapha ne bata da lafiya itama xata barta ta aure sa, no baxan iyama anti jiddah haka ba xan cigaba da boye mata koda kuwa sonsa xai xama ajalina cos nasan el’mustapha baxai taba son Irina ba, ina Ma ko sau daya ne na ganshi, tunda nake gidannan ban taba ido da ido dashi ba sai dai kallo daga nesa. 

Tashi ki shirya yanxu xaa kaiki asibiti kinji banan. 

Ba musu kuwa ta tashi ta soma shiryawa, jiddah na fitowa sashen kitchen din ta tanufa, 

Har ta gama shirya masa breakfast wani abu na nan a qirjinta ya tokare mata,wai ita ce da kishiya a yau, anya tayi Saar xuwa duniya kuwa, ko da yake itace ta jawa kanta, amma ita da xuciya daya tayi taimakon kuma tasan baxata taba tabewa ba. 

Story continues below

Dai dai lokacin da suke ganiyar soyayyar su da el’mustapha a lokacin wata xata shigo rayuwar su, su dinga sharing love, anya xata iya? Wata ta dinga yin abinda suke da mijinta, rumtse idonta tayi ta jingina da bangon kitchen din da yaji marbles, hawaye mala mala a fuskarta a hankali ta dinga furta Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un, 

A hankali ta fara samun sa’ida a xuciyarta har ta sami relief, ta kwashi kayan ta soma hadawa a dining, 

Ta qara shiga dakin nasa, yana kwance wannan karon kansa na kallon fankar dakin, ya riqe goshinsa da hannunsa daya, 

Gefen gadon ta xauna hade da Jan yatsar qafarsa, el’mustapha lafia? Ta fada tana murmushin yaqe

Kura mata ido yayi, shi kansa yasan qarfin hali take wai barawo da sallama, 

Your breakfast is ready ta fada cikin sanyin murya uwa tasa ihu take ji, baiyi niyar miqewa ba, hakan yasa ta qara magana, komai bai ce ba ya tashi suka fito tare. 

Breakfast suke daga ita har shi bamai cewa qala kowa da abinda yake tunani har lokacin da suka kammala, kallonsa tayi da murmushi a fuskarta, 

Oya get ready, 
For what ya tambaya yana kallonta, 
For bathing mana ango, shiru yayi baice komai ba har lokacin da tajasa toilet, suna wankan tana adduoi a xuciyarta na Allah ya kawo mata sauqin kishin da ke ranta. 

El’mustapha kuwa kallonta kawai yake, sai yanda tayi dashi binta yake kamar raqumi da akalarsa. 

Da kanta ta shiryasa, yau kam harda babbar riga, ta feshe shi da taurare mai sanyin qamshi, ta tsura masa ido, 

Shikenan yau beautiful man din ta xai dawo nasu ita da yar’uwarta, wasu hawaye suka xo mata da sauri ta rungumesa sosai kyam a jikinta, ya saki ajiyar xuciya, rungumota yayi sosai yana shafar jikinta hade da dora kansa a kafadunta. 

Jiddah ko a fasa auren ne please, nima bana so kinsani. 

Ta girgixa kanta bayan ta dago tana kallonsa, auren shekara daya ne el’mustapha kayi min alqawari da lokacin ya cika xaka sauwaqe Ma uwani. 

Nayi alqawari, 
Kayi min alqawari baxaka juyamin baya saboda ita ba. 

Nayi alqawari, sai me jiddah, tayi shiru tana sharar kwallah, talk jiddatulmusty el’mustapha naki ne, yana matuqar sonki baxai taba iya hada soyayyar ki da wata ba, trust me jiddah, idan na karya daya daga cikin alqawarin ki kibarni har abada, ta kallesa cikin son gasgasta maganar kuma hakanne. 

Yau 25th ne ranar da ta amshi daurin auren El’mustapha Maneer da Aisha Adam (Uwani) miji ga Hauwa Ahmed (Jiddah ). 

Auren da akayi sa acikin masallaci bayan sallah.

Jiddah ta dawo daga duba jikin banan sosai ta warware har Ma taci abinci ta saka ta tayi wanka, tana qoqarin shiga sashen ta sukayi kicibis da uwani na qoqarin fitowa, cikin wani uban lace Blue, baqaramin kyau tayi ba tasha make up wanda ya fito da sirrin kyawunta, idanu jiddah ta xuba mata cikin tsoron irin kyau da uwani tayi. 

Murmushi uwani tayi tasan ko jiddah bata fada ba yanayin ta kawai ya nuna kwalliyar ta ta qawatar, ina ma el’mustapha xai shigo ya ganta shima, russunawa tayi cikin girmamawa, 

‘Anty jiddah tun daxu nake neman ki, yau bamu gaisa ba, kuma gashi yau rananr farin cikina ce burina ya cika na mallakar abinda nake so, qirjina ma ‘ga daina min ciwo a yanxu xuwa shekara daya inaji komai xai dai dai ta na bar miki shi. 

Da kyar jiddah ta iya hadiye wasu yawu da qarfi, ta tattaro nutsuwarta tana kallon uwani. 

Nagani kam kwalliya kika xo ki nuna min kuma kinyi kyau, amma wanda akayi domin sa ba gani xaiyi ba ballantana ya yaba. 

Nikam anty jiddah banxo dan kiji haushi ba idan Ma kika ce inje incire yanxu xanje na cire, idan kuma magana ta ce tabaki haushi kiyi haquri, xama nake so muyi dake na amana ba cutar wa. 

Da xanfi farin cikin haka, ni ban iya cutar da mutum ba ballantana nayi qoqarin cin amanarsa, duk wanda nake xaune dashi da xuciya daya ne, 

Ni xan iya baiwa duniya labarin wannan, kina da hali mai kyau ki godewa Allah. 

Jiddah bata qara mgn ba tana qoqarin ficewa ta tsaidata, 

‘Anty jiddah nace kada ki gaji dani, kima yaya mgn ko ba komai ina da haqqi amin kayan aure, idan suma baida kudin ne ni xan iya rantawa na aramasa kudin yayi min, 

Murmushi jiddah tayi, 
Ai yanxu uwani kin fini kusa dashi, kece yar gaban goshi, ko kin manta yau kece amaryarsa sai yanda kikayi dashi, 

Hakane kinyi gaskiya anti uwani daga nan ma xan masa mgnr honey moon din mu. 

Acan daki kuwa jiddah roqon el’mustapha take yaje ga uwani, qarfin haline kawai take amma kamar ta fashe da kuka takeji, 

Kayi haquri mijina, ina sonka bana son Allah ya kama ka da laifin rashin adalci a tsakanin mu, ka yafemin tirsasawar danayi Ma akan auren uwani dan Allah ka yafemin, ya rungumota sosai hade da sumbatar ta a goshi, 

Bana son wannan damuwar da kukan, I want my jiddah back as before, wannan ba jiddah na bace, jiddah na bata cikin damuwa, she is always happy, bata da lokacin kowa sai na mijinta ya fada yana qoqarin cusa hannuwansa cikin rigarta. 

Ta soma girgixa masa kanta, please el’mustapha kaje tana jiranka, your new bride… Cak ya tsaya yana kallonta, 

Jiddah ta daina sonsa a yanxu, ta daina kishinsa, yau jiddah ita ke roqonsa yaje ga wata macen, shi kam me xai tsinta a jikin uwani, mexai sa ya hada shimfida da uwani, kada Allah ya nuna masa wannan ranar. 

Ya cire hannuwansa daga cikin rigarta jiki a sanyaye ya sauko daga saman gadon, bai qara waiwayen ta ba ya fice, uwani najin alamun takun mutum xai fito daga dakin ta xura da gudu daga laben da takeyi ta nufi dakin ta tana addua Allah yasa yaxo kai gaskiya jiddah mace ce mai gaskiya bata da son xuciya ai na dauka baxata barshi ya xo ba da nayi Allah ya isa domin nike da shi ehe. 

Sanin muhimmanci sallama ya saka shi yinta, yana sanye da kayan barcinsa masu kyau da taushi, qamshin turaren sa ya gauraye dakin uwani wadda tun shigowar sa jikin uwani ke rawa sai take neman abinda xata rufe jikinta dashi, ita kanta batasan tana kunya da tsoron el’mustapha ba sai yau ashe duk cika baki ne takeyi a bayan idonsa, a xahiri kuwa wane ita. 

Wata xungureriyar farar takarda ya miqa mata kansa a sunkuye har lokacin bai kalle ta ba, 

Jikinta ya dauki rawa, ta soma ganin dakin na juyawa da ita, takardar mecece yake bata kada dai el’mustapha ya sake ta ne, a daren ta na farko, daren da kowace mace take alfahari da farin ciki dashi. 

Jikinta yayi sanyi ta kasa miqa hannu ta karbi takardar,  ba dan komai ba sai dan tsoron abinda xata tarar acikinta. 

Ganin haka el’mustapha ya ajiye mata takardar a gefen gadon da take xaune, ya juya ba tare da yayi magana ba ya fice. 


Zuru tayi tana kallon farar takardar, har lokacin jikinta rawa yake, kafin ta fara kuka. 

Shikenan ta faru ta qare dama tasan el’mustapha baxai so ta ba, ya karbi auren ne domin ya wulaqantata, ai kuwa kansa yayi mawa saboda takardar jiddah xata bawa ita acewar ta tace, dan wlhy bai isa ya sakeni a farkon daren aure na ba. 

Ta dauki takardar da sauri ta sakata cikin wardrobe din ta, baxan nuna masa na karanta takardar ba dan Ma karnaga sakin, jiddah xan bamawa ko saki nawa ne ya xamto itace yayi Ma bani ba, sai inga yanda xaiyi Allah yasa saki uku ne aciki ta tafi ta barmin shi har abada inga qarshen soyayya, ingani idan baxasu iya rayuwa ba kamar yanda suke fada. 

Da wannan tunanin uwani ta kwanta barci, mafarkinta a ranar duk cike yake da el’mustapha, gani kawai take suna ta xuba soyayya ita dashi. 

Jiddah kuwa a ranar ta kasa barci, tayi kuka harta gode Allah, once in life el’mustapha din ta kwance da wata macen ba ita ba, tunani iri iri, ganin bata da mafita ya sakata shiga toilet ta dauro alwallah taxo ta fara sallah. 

El’mustapha kuwa bashi da damuwa illah ta kewar jiddah sa, rigar barcinta ya sakawa pillow ya rungume, barcinsa yake hankalinsa a kwance batare da tunanin komai ba. 


‘Washe gari jiddah ce a kitchen tare da banan suna hada breakfast suna hira abinsu. 

‘Anty kinga har yanxu kaka bata xo dubiya ta ba, ta dade sosai wannan karon kuma ina so na ganta. 

‘kibari idan kukayi hutu bata xo ba sai kije, ai ba abin damuwa bane banan, meyiwuwa wasu hidimomi suka yi mata yawa. 

‘hakane anty, amma a makaranta an fara mana maganar kudin waec da neco. 

‘eyyeh ashe Banan an xama yan mata, na manta ai wannan shekarar kike gamawa,  kice su arham sun kai ga babbar anti. 

Murmushi banan tayi tana kallonta, 
‘Anty ai xaki sakani University nima kamar anti uwani. 

Me xai hana banan, inaso kiyi karatu, kinga ni banyi ba iyakar secondary ne kawai dani, kuma bayan nayi aure banyi qoqarin shiga ba kasancewar el’mustapha baya so, Uwani kuma kinga saboda bata da aure ne har kika ga ta cigaba kuma yanxu xata cigaba tunda kinga tana kai ya aure ta, dan haka kema ina so kiyi karatu koda kin sami mijin aure ki cigaba, ilimi yana da matuqar muhimmanci ga ‘ya mace, ina so watarana kaka tayi alfahari da bokon ki. 

Banan tayi dariya tana kallon jiddah cikin tsananin qaunarta, 

‘Anty jiddah rayuwarki daban ce, halinki mai kyau ne kuma kina da kirki, shiyasa nake matuqar sonki, mutanen gidannan Ma basu da magana sai ta alherin ki, baxan iya cutar dake ko cutar da jinin ki ba shiyasa kika ga ina matuqar qaunar yan biyu saboda mamansu bata kyamace ni ta soni da xuciya daya. 

Jiddah ta wanke hannuwanta a sink, kafin ta juyo tana kallon Banan, 

Nagode da kulawar ki sosai akan twins, Allah xai saka miki, taimaka ki kwashe kayan ki jera a dining, ni xanje wanka. 

Cikin shirinsa na uniform ya fito, suna hada ido da jiddah ya sakar mata murmushi, 

‘Uwargidan el’mustapha, amaryar el’mustapha, mata kadai a xuciyar el’mustapha da fatar kin tashi cikin qoshin lafiya, 

Murmushi tayi tana kallonsa, 
‘Good morning my cwt, angon uwani. 

Bai wara mgn ba ya qarasa dining yana duba abubuwan da ta hada masa, 

Xama yayi yana fadin, all dis for me jiddana, gashi kuma am late ina sauri. 

Ta qaraso tana fadin, all for you an your bride, ka jirata ta fito mana. 

Hannu yasa ya mintsineta, ya jawota kacokan ya dorata akan qafafunsa, 

Bari na duba ki matata nagani wai akwai sona kuwa a xuciyarki, jiya kin barni cikin kewa da kyar na sami barci, kafin tayi magana ya hada bakinsa da nata. 

Suna haka uwani ta fito cikin shirinta, ganin su a haka ba qaramin tada hankalinta yayi ba, haka taji falon na juya mata, ga wani uban kishi daya danne mata qirji. 

Ai wallahi sai dai na katse maku abinda kuke amma baxan koma ciki ba, ta qarasa dining da sauri. 

El’mustapha sarai ya ganta amma jiddah bata ganta ba kasancewar bayanta ke fuskantar uwani, 

Tana isa dining ta daga murya sosai yanda xasu ji ta, 

‘Anty jiddah sannu da aiki, 

Sosai jiddah ta jiyo ta sai dai batayi yunqurin barin jikin el’mustapha ba kasancewar bai bata wannan damar ba ya riqeta sosai a jikinsa, 

Uwani ta xauna ji take kamar ta fashe masu kai a yanda suke, da kyar jiddah ta tashi, ta xauna gefensa tana qoqarin hada masa tea, 

‘is ok jiddah, sauri nake kuma tuni na qoshi tunda na sami abinda nake so daga jikinki, taji nauyin maganar sa saboda uwani amma bata nuna ba, 

Tace amma kasan xan shiga damuwa idan har bakaci abinci ba, tukunna Ma idan kaje me xakaci haka xaka xauna a office da yunwa. 

Bani farfesun naje dashi ya isheni, da kanta ta hada masa ta bashi, xata raka sa ya dakatar da ita. 

‘Na hutar dake xauna kiyi breakfast dinki, kafin tayi magana ya juya da sauri ya fice. 

Dogon tsakin da uwani taja ne ya dawo da hankalin jiddah xuwa gare ta, batayi magana ba kuma bata qara kallon uwani ba, 

‘An shiga haqqina Allah ya gani, abinda ke xuciyata kuma na barwa kaina sani, na yafe ko ban yafe ba, ta murguda bakinta tana qoqarin ture kayan dake gabanta. 

Kallonta jiddah tayi cikin son gasgasta abinda taji uwanin na fadi, 

Me kike cewa uwani?

Cewa nayi an min shige, kwana bakwai ne girkina saboda kowa yasan ni budurwace, amma saboda me xaa xauna da mijina ranar girkina ana tsotsar bakinsa, nima sai na rama wlhy. 

Murmushi jiddah tayi cikin mamakin uwani, wai mijinta, a yanda tasan halin uwani iyayenta Ma bata raga masu ba wurin maida masu magana ya saka ta ja bakinta tayi shiru, ta dauki kofin tea ta kai bakinta tana sha. 

‘Wannan halin ko in kula da jiddah tayi akan uwani yayi matuqar bata mata rai da fusatata, 

Ni dama nasani ba saboda tausayina yasa aka aura min shi ba sai dan a qara cusa min baqin cikin da xai sa xuciyataa ta fashe na mutu a huta dani an yarda kwallon mangwaro, to yanxu na fara rayuwa, kuma ba wanda ya isa ya rabani da mijina, ta bigi table din ta tashi a fusacce ta bar gurin. 

Binta da kallo jiddah tayi har ta bacewa ganin ta, batayi mamakin abinda uwani tayi mata ba a yau domin shine karo na biyu, sun taba irin wannan fadan kamar uwani xata dake ta saboda ta gayamata gaskiya akan iyayenta da take Ma rashin kunya, tun daga lokacin bata qara mata magana akan ta daina ba, sai yau da ta qara mata wannan, dama tasan halin uwani idan tana neman abu a gurinka xata riqa baka girma kamar xata hadiye ka amma da xarar buqatarta ta biya to ba shege a gurinta sai kai. 

Allah ya shiryeki uwani shine abinda jiddah ta fada tana qoqarin cusa arish a bakinta.

A gurguje🙄

2 month

‘Surry ke kallon uwani tana yatsina fuskarta, 

Dube ki dallah malama, kin bata wayonki da qurciyarki, dubi yanda kika dawo, son maso wani qoshin wahala, kuma abinda aka gina da cin amana ai baya kyau. 

Ko ma me xakice kice, ban kiraki kixo gidana ba ehe, wanda nake so tunda bake bace akansa ba ruwanki. 

Hakane, ni uwar karambani da cusa kai,  maganar makaranta kindai na xuwa tunda kikayi aure, ko miye dalili. 

‘Na ajiye karatu, bautar aure nake yi. 

‘ni badan na ganki da casbi a hannu kina a ba da na soma xargin kin fara shaye shaye, yaushe Ma kika fara riqa carbi a hannunki ne, ko duk el’mustapha ne ya sauyaki. 

Shiru uwani bata tanka ba, 

Saboda auren kike cewa kin fasa karatu uwani, kima kanki fada uwani ynxu kike da damar karatun kafin ki fara haihuwa, shekarun da kikayi a baya kina nufin sun tafi a banxa?

Karatu dai nikeyi ba wani shege ke min ba, kigayamin tun da nake xama a ajin me nake fahimta ko kin manta irin kwakwalwata ne, dana bata lokacina ina shiga aji bana fahimtar komai gwanda na xauna nayi bautar aure tunda har nayi secondary, kin manta semester can da result ya fito duka c.o ne uku kawai nayi passing na kawo result gidannan matar nan harda dangwara ta tana cemin takkwala ko ban gayamiki haka ba?

Dole xataji haushi saboda kudin da take kashe maki na School uwani wlhy ko nice xan qara da ce maki mai kwakwalwar kifi saboda naki daqiqancin yayi yawa, abinda ke qara bani haushi akanki ayi maki dictation baki iya rubutawa copying Ma da kalma daya daya kikeyi shiyasa nake juya maki baya idan aka shiga jarabawa. 

Yanxu sai dai ki juyawa iska baya, uwani ta daina shiga aji ni bautar aure nake yanxu, wannan casbi da kika ga ina ja kariya ce daga sharrin aljannu ko wani sihiri da kishiya ke aikowa amarya dan ta hana mata xaman gidan miji. 

Lallai uwani, ai kowa yasan xuciyar jiddah abinda kike fada baxata iya aikata maki ba kuma insha Allah xan sanar da ita yanxu cewa kindaina xuwa makaranta. 

Kifi ruwa gudu, kada ta barni da rai tunda tasan gaibu kotasan dalilin qin xuwana. 

‘Surry ta tabe baki, idan kika ce kina bautar aure dariya Ma kike bani, keda miji baya kulawa bai masan da xamanki a gidan ba, is better ki koma makaranta ko kin sami abinda xaki taimaki kanki watarana, kafin uwani tayi magana ta ciro mata katunan auren ta ta miqa mata, 

Ina miki albishir aure na da Yusuf wani sati. 

Wane Yusuf din?uwani ta tambaya tana kallon katuna,

Yusuf dai wanda kika sani….. Ashar din da uwani ta dura ya katse surry, 

‘Dan kaza kaza…… Ni xaki ci amana ki yaudara, saurayina xaki aura. 

Auren soyayya kuwa xamuyi, ba auren ina so baya so ba, saurayine kuma ni kadai a gurin sa mu murji quciyarmu da soyayyar mu son ranmu. 

‘ashe dama ke macuciya ce, ina tare dake kina cin amana ta kina soyayya da saurayina, wlhy sai na rama. 

Da auren naki xaki rama, kinji haushi kenan, ashe ba dadi kika Ma anty jiddah, abinda kika ji a xuciyarki yanxu shi itama taji, abinda kikayi aka maki Allah baxai kamani da laifin cin amanarki ba domin har Yusuf din hana sona. 

Wlhy sai kin san kinyi dani daga ke har shi sai na wulaqantaku a garinnan, sai na nuna maki A. I. G na dan sanda nake aure. 

‘Surry ta dauki jakarta tana fadin, to matar A. I. G idan kin tashi wulaqantamu kisa yasa bindiga ya harbe mu duka, mtsewwwww banxa da bata san ciwon kanta ba ta fice ta bar uwani na kumfar baki sai ashar take durawa. 

Jiddah taje ta gayawa halin da ake ciki tunda tace bata san gaibu ba, kafin ta bar gidan, haka jiddah ta aika aka Kira  mata uwani, sai da taga dama taje kiran da qaton casbin ta a hannu tana ja.

‘Na kiraki ne inji yanda akayi kikasan gaibu tunda ni ban sani ba uwani, 

Tsaki taja a ranta, ta xata wani abin kirkine ashe mgnr da sukayi da surry ce, ta bata fuska, 

Ban gane nasan gaibu ba, a ina nayi mgnr, 

Inaji surry baxata maki qarya ba, haka kika gayamata, uwani ta dube ta, 

Dana gayamata ce mata nayi gobe xaa tashi qiyama ne, karatu ne nace na bari kuma ba shegen da ya isa ya sani?

Nice shegiyar kenan? Jiddah ta tambayeta tana kallonta da mamaki a fuskarta. 

Da munafukar da taxo ta gayamiki nake nace ba wanda ya isa yasani karatu bautar aure nakeyi, 

Oh shiyasa na ganki da carbi a hannu kina neman gafarar ubangiji, 

Takaici ya kama uwani na ganin an canxa mata ma’anar wuridi, 

‘to ni ba istigfari nake yi ba, jiddah tace hailala kikeyi kenan tunda kince gobe tashin qiyama, 

Uwani ta muskuna tana cigaba da Jan carbinta bakinta na mus mus, kafin tace, neman tsari nake daga sharrin mahassada kada a jefeni da wani mugun abin a hanamin xaman aure. 

Sarai jiddah tasan da ita take sai ta maida martani da cewa musamman da maqiya sukayi yawa akan auren gashi kuma har da iyayen tunda suma ance harda su suna baqin ciki, Allah yasa kin saka dasu suma ki nemi tsarin su. 

Uwani ta dan kalleta, tace ni ban cire kowa ba, kowa da kowa nace. 

Shiyasa nima ai nace harda su hajiya ai, kuma miye dalilinki na daina karatu bayan kin fara, ni na dauka ai hutun amarcine kike shiyasa bakya fita. 

Tunda ance ni daqiqiya ce ban iya karatu shiyasa na kalli kwanyata da rayuwata nagane Sam babu amfanin karatun a gurina gwanda na tsaya nayi bautar aure na kula da mijina abin sona. 

Hakane kam kinyi dabara kuma kinyi rashin wayo na karatunki, da nice keda damarki ba abinda xai hanamin karatun, kuma ba gori nake maki ba duk kudin dana kashe akan karatunki yanxu kina nufin sun tafi a banxa. 

Kimin Bill in biyaki in huta da gorin kishiya, kada ya’yana su taso a goranta masu an tallafi mahaifiyarsu, dadin abin nima mijina mai kudi ne xan iya biya. 

Jiddah tace ba sai nayi Bill ba ko nawa ne kinfi kowa sani, sai ki biyani idan mijin kuma bashi da kudi sai ki ranta kibani tunda naga mijin naki kullum a rance yake qarewa. 

Shiru uwani bata qara magana ba, cika baki ne ba kudin tasan baxata iya biyan jiddah ba, sai ta cigaba da Jan carbin. 

Jiddah bata qara bi ta kanta ba ta tashi ta soma gyaran gadon ta, uwani na ganin haka ta marairaice fuska, 

‘Na ce ba anty jiddah…. Sai tayi shiru, jiddah tayi shiru tana kallon ta yanda taga uwani ta marairaice fuska tasan akwai abinda take nema, 

Ina jin ki. 

‘Dan Allah kima mijin ki magana, ki roqeshi koda baxai kwana a saman gado na ba, ya roqa sake min fuska yana min murmushi, wlhy anty jiddah ko dakina bai taba kwana ba, kuma dai kowa yasan nima fa ina da haqqi akan sa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page