EL-MUSTAPHA CHAPTER 1

EL-MUSTAPHA
CHAPTER 1

Motoci ne keta sharara gudu tsakanin titin kaduna xuwa Abuja,
A qalla motocin xasu kai shidda koma fiye da hakan,

Dare ne mai tsananin sanyi, cikin watan nuwamba, haxo ya lullube duhun daren ta yadda ya fidda launi mai haske kamar hadadden hadari, wanda ya takura da yawan al’ummar birnin tarayya.

Daya daga cikin motocin A.I.G (Assistant inspector General of police) El_mustapha Maneer ne tare da Matar sa.

Kallon ta yake cikin alhini da son sanin asalin damuwar ta, ta yanda har ta takure kanta nesa dashi tana kallon hanya ta glass batare da ta damu da ta kwanta a jikinsa ba kamar ko yaushe idan suna cikin mota xasuyi tafiya.

Yayi tunani ya kasa gano laifinsa gurin uwargidan sa tun bayan barowar su kaduna bikin wani taro da akayi.

Tana sanye da suwaita ta rungume hannayenta duka biyu a qirjinta, alamar tana jin sanyi sosai amma hakan bai hanata takurewa guri daya ba saboda tana fushi dashi.

Murmushi yayi marar fitar da sauti bayan ya dauke dubansa daga gareta, Jiddah rigima, kome xatayi a rayuwa tana burgeshi, yana sonta sosai, so bana wasa ba, komai nashi xai iya salwantar wa saboda ita, yana yi mata son da alqalamin Pherty baxai iya rubutawa a takarda ba, saboda yaransa dake cikin motar suna tsaron lafiyar sa ya hana yaje gareta ya rarrashe ta tare dajin laifinsa har ake wannan fushin dashi.
Jiddah kuwa qara takure jikinta tayi, xuciyarta nayi mata wani xafi ganin halin ko in kula da mijin ta yayi da ita a yau, tasa yatsun ta biyu batare da tabari ya gani ba ta dauke wasu siraran hawaye da suka xubo a idanuwanta tana cigaba da kallon titi xuciyarta a daqushe tare da tunani iri iri duk a kansa.

Wata sassanyar ajiyar xuciya ta saki lokacin da taji saukar hannunsa cikin tafin hannunta, ta juya tana kallonsa ta cikin hasken farin wata da ya haske motar, bata ganinsa sosai ta dai san ba ita yake kallo ba hakan yabata damar janye hannunta a hankali hade da qara matsawa nesa da shi cikin tunxuro baki idanunta taf da hawaye.

Jikinsa ya qara sanyi, meke damun Jiddah, meyasa ta canxa masa haka lokaci daya?

11:30pm

Suka shigo garin abuja, dirar motocin su ya sanya Uwani miqewa da sauri ta gyara powder fuskarta hade da qara feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi.

Ta mirror take kallon kanta tana qara jujjuya jikinta, ita kanta tasani ta ko ina tayi bata da makusa har take ji Ma tafi matar gidan komai amma meyasa El mustapha ke ganin Jiddah tafi mata dubu a duniya, meyasa yake ganin Jiddah ce tauraruwa acikin mata, meyasa ya kasa gane yanda xuciyarta ta mutu da qaunarsa, har take kishin yar’uwar ta duk saboda shi.

Ina son elmustapha da izinin Allah sai na aure shi, sai na sami matsayi a xuciyarsa fiye dana Jiddah.

Jiddah tana fitowa motar bata tsaya wata wata ba tayi shigewarta kai tsaye, a falo taci karo da uwani tana fitowa kallon mamaki ta bita dashi wanda ya sanya uwani daburcewa…

‘Uwani duk wannan kwalliyar ta mecece, ina xakije da wannan daren haka?

‘Anty Jiddah.. Uhm.. dama Yusuf ne yaxo to bai jima da tafiya ba, yanxu dama nake so na cire kayan na kwanta sai naji dawowar ku shiyasa Ma na fito…. ta fada cikin murmushi

Jiddah bata bi ta kan xancen ba ta soma tafiya tana fadin,
‘Naji gidan shiru, ina Arham da Aryan ne.

‘Sun jima da yin barci bayan sun gama rigimar nemanki,

Story continues below

Jiddah ta juya tana fadin
‘Alhamdulillah, domin a yanzu ba abinda taxi muradi,irin taga yaranta cikin koshin lafiya,ta haura steps, Uwani kallo ta bita dashi tana sauke numfashi a hankali ganin asirinta bai tonu ba, juyawa tayi ta fita harabar gidan inda ta tsinkayosa tsaye duk police sun xageya sa, da alama magana yake dasu yanda taga duk sun tattara hankalinsu da nastuwarsu ta reda sunkuyar da kansu suna saurarensa.

Wannan dalilin ya sanyata dawowa Falon xaman jiransa.

Kai tsaye ya shigo falon idanunsa na kan wayar sa da alama akwai abin da yake nema kamar mai son yin waya, ko wanda ze tura saqo,

Qamshin turarensa ya soma fisgarta, jikinta ya dauki rawa, nan da nan wata irin kasala ta rufeta, a yanda takeji kamar ko yatsanta ba zata iya motsawa ba,haka zuciyarta ke ingizata tamkar taje ta rungumeshi, bata san wane irin so take masa ba,

‘Barka da dawo wa yaya, cikin dauriya tayi maganar,da kashe murya irinta mai jan hankali..

Ya dago rinannun idanunsa yana kallonta wadanda ke qara ruruta wutar qaunarsa a xuciyarta, cikin sakin fuska ya soma yi mata mgn,

‘Mun same ku lafia Uwani, ashe bakiyi barci ba,

Murmushinsa kawai tamkar ya barar da Uwani a falon, don haka duk qarfin halinta sai ta kasa tankawa illah girgixa kanta da tayi domin idan ta tilastawa kanta mgn a wannan lokacin tabbas xata iya bayar da mata domin ba abinda xai hana mata fallasa masa sirrin xuciyarta, bugu da qari Ma bata ga fuska a tare dashi ba.

Batare da yabi ta kanta ba, ya nufi sashen sa, kallon sa take harya bacewa ganin ta, ta qara kallon jikinta, sama da qasa,tana girgiza kai tana mai tambayar kanta,

Ko bai lura da kwalliyar da tayi domin sa ba, baiyi mgn ba kamar yanda Jiddah tayi magana, sai ta tuna elmustapha yana da halin ko in kula akan kowa idan ba Jiddah bace, tana gani Jiddah kome xatayi sai ya yaba yayi godiya amma saboda ba itace gabansa ba ya kasa gano abubuwan da takeyi domin sa. 

Jiki a sanyaye ta nufi dakin ta, kuka take na zuci har yafito fili,tayi kukan sosai, Wanda tana ganin yin hakan kadai xaisa ta sami sassauci daga xafin da xuciyarta keyi ma ta, kamin ta samu damar cikar burinta.

Jiddah kuwa sai da ta duba yaranta biyu, twins maxa masu shekaru shidda shidda, tayi masu addua, wadda acikin ranta, tana fatar ta rayu da su har izuwa girmansu,kafin ta numfasa, taja musu kofa, ta nufi sashen ta, 

Tana cikin cire kayan jikinta ya shigo dakin,ko baa fada ba tasan waye sai tayi qoqarin shigewa toilet, yayi saurin riqota yana kallonta, 

‘Haba jiddatulmusty, wannan fushin duk na menene, na kasa gano laifina, ki gayamin. 

Ta dauke kanta gefe tana tunxuro baki, bai yi fushi ba saboda kome Jiddah xatayi masa a rayuwa yana birgesa yana sonta da yawa, 

‘idan kuma baxan sami amsar tambayata bane shikenan, xan barki kiyi ta fushin amma nima xanyi fushi da kowa da komai a gidannan har lokacin da xaki daina fushi dani ciki kuwa har abinci xan daina ci, ya juya kamar da gaske xai bar dakin yasan ba abinda ta tsana kamar xamansa da yunwa, kamar daga sama yaji muryarta, 

‘to ba kai bane…. sai kuma tayi shiru ya juyo yana kallonta, 

‘ya salam…. Ya furta a hankali bayan ya dafe goshinsa da hannunsa na dama, ya dago yana kallonta, 

‘kin san wacece kuwa? Me xanyi da wannan matar jiddah?

Story continues below

‘idan hakane meyasa kaja ta can gefe inda ba kowa kuna magana, kuma naga harda hannunka ta taba baka hana ta ba. 

‘saboda ke ne Jiddah, nasan kishi irin naki bana son bacin ranki ko kadan ya sanya na jata nesa da mutane muyi mgn amma meyasa idan kishinki ya rufe maki ido kina manta ko waye mijinki?,pls Jidda don’t ever doubt ur trust in me, I give you my heart so honestly!,

Tayi shiru bata tanka ba, sai dai ta sami nutsuwa a xuciyarta domin ta yarda da mijinta baxai taba mata qarya ba,

‘Wannan matar is a Christian, matar Captain Johnson ce, tana min mgn akan abubuwan da yake mata ne bayan ya rabota da qasarta yaxo da ita inda bata san kowa ba yana cutar da ita, tana ganin ba wanda xai masa mgn yaji kamar ni wannan dalilin ne yasanya har kika ganni da ita, maganar riqe min hannu da tayi kinsan su a gurin su ba wani abu bane halin da take cikine ya sanya na kyaleta. 

Ta saki ajiyar xuciyata tareda wani zazzafan iska, wanda batasan tariqe shi ba se fitowarshi ta ji, hade da langabe kanta gefe tana kallonsa, se cemata yayi breath my dear….and don’t repeate to act like dat I can take it anymore my dear, I am madly in love wit yhu, habawa da sauri Jidda ta dago kanta suna had’a 2eyes ya ce yes my Jiddah I love u…….pls say something I want to hear ur sweet voice,

‘Cikin tsanaki ta bude bakin tace am sorry…. My dear Ka yafe min, yaja dogon hancinta yana murmushi,kurawa juna idanu sukayi 4 sometimes at d end Elmustapha ya janye Na shi tare da bata peck a forehead da kumatunta,

‘I love you jiddana… ta fada jikinsa tana dariya, ya dauke ta cak suka nufi toilet. 

‘Uwani…. Uwani, take kiranta cikin muryarta mai sanyin gaske, 

Shiru Uwani bata amsa ba kuma bataji motsinta ba hakan ya bata damar isa dakin nata tana kiranta, 

Babu alamar ta a dakin amma ta jiyo motsinta a toilet, ta fita daga dakin, harabar gidan ta nufa sashen masu aiki, 

Bata jima ba ta dawo tare da wata yar budurwa a bayanta, 

‘kinga yanda su Arham suka bata falonnan, kuna cikin gidan amma ba wanda yayi tunanin gyarawa, idan wani baqo yaxo ya same ni a haka fa, ko shi maigidan?

‘Dan Allah kiyi haquri hajiya, ba wanda ya gani acikin mu…. tayi saurin katse ta, 

‘Wannan ba magana bace, aikin kune na gyaran cikin gidannan, akai akai nake gayamaku kuriqa dubawa idan sun bata ku gyara ko dole ne ni xan riqa tashi kullum ina xaryar kiranku akan kuxo an bata ku gyara, idan aikin ne kun gaji dashi kuyi magana akawo wasu abarku ku tafi mana?

‘insha Allah daga wannan baxaa sake ba, kiyi haquri hajiya. 

‘ki kira su jamila kuxo ku hada hannu yanxu ku gyara, kun sani a kowane lokaci baqi xasu iya xuwa gidannan, gidane da baa rabashi da mutane, idan kun gyara nan din ku duba dakin su Arham din kugani ko sun bata, ta juya ta fice,

Story continues below

Uwani ce ta fito da sauri daga dakinta, da kallabi a hannunta, kallon Banan take cike da wulaqanci, 

‘ke idan kin gama da falon nan kije ki wanke min toilet, kwana biyu rabon da ki wanke sa, harda dakin Ma xaki gyaramin kafin na fito, ta fice fuuu da sauri xuwa sashen jidda. 

Kallonta Banan keyi harta bacewa ganinta, yatsina fuska tayi hade da tabe baki bayan ta juya tana kallon jamila dake shigowa. 

‘Yauwa kamar kinsan ke xanje nema, hajiya tayi fada yanxu a gyara falon nan ina indo, 

‘tun daxu ku nake nema, indo ce kawai ban gani ba, ban san inda ta shiga ba, suka soma gyaran falon. 

Da sallama ta shiga dakin, idanunta akan na jidda, 

‘Anty naji kina nemana, ina toilet ne, kallonta jidda keyi, 

‘kaya xaki kaiwa Hajiya Ruhayma ta duba idan akwai wadanda xata siya aciki, tun kafin kayan su iso tayi min mgnr su, ki kula da kyau uwani nasan ki da rikicin kudi 

Murmushi Uwani tayi tana harhada kayan, insha Allah anti wannan karon baxaa sami matsala ba, xanje dasu har gidan qawayena na tallata maki nasan xasu siye. 

Murmushi jidda tayi batare da ta qara magana ba harta gama harhada kayan, kallonta tayi, 

‘Anty jidda waye xai kaini, ibrahim ya tafi ya dauko su Arham makaranta, jidda ta tashi ta qarasa bakin window dakinta tana leqa harabar gidan, 

‘kuma motata ba isashen mai aciki amma bari na baki kudi sai kisa ko a hanya ne kafin ki qarasa. 

Uwani ta washe baki, ba sosai taji dadin mgnr ba, a rayuwarta tana son taga tana hawa manyan motoci, ta ganta da manyan qawaye masu ji da kudi, ta ganta acikin qaton gida na alfarma, ta ganta da santalelen miji wanda ya morewa ilimi sosai kuma yake da kudi, shiyasa take son el_mustapha domin shine irin mijin da take son samu. 

Jidda ta xuge zip din jakarta ta ciro kudi dubu biyar ta bata, 

‘ki lallaba dasu uwani nasan xasu isheki, karki jima sosai pls kinsan bana son yawon nan, 

shikenan anti, ta karbi kudin ta qarasa bakin mirror tana gyara daurin kallabin ta, 

Jidda bata damu ba idan da sabo ta saba da halin uwani na kuri da nuna ita watace, ta rasa wannan hali irin nata Sam bai dace da tarbiyar da aka basu a gida ba. 

Uwani ta jima da fita kafin tajiyo hayaniyar twins nata, 

‘Mami… Mami…, we are back, 
Murmushi tayi bayan ta ware masu hannuwanta biyu sukaje da gudu suka rungumeta, daya bayan daya ta sumbace su a goshi tana kallonsu da murmushi a fuskarta, 

‘da fatan yau bakuyi fada a aji ba? Arham ya dubi Aryan shima kallonsa yake, (kallo daya xaka masu ka gane cewa identical twins ne), 

Aryan ne yayi fada Mami, harda karyawa friend dina pencil dinshi yayi kuka, shine na dauki nawa na bashi. 

Ka kyauta Arham, xan gayawa Abba ya siyama wasu masu kyau, kuma yaje da kai Magic land, shi kuma da bayajin magana kullum yake fada a class ba ruwana dashi, tashi daga saman jikina munyi fada. 

Ba musu kuwa ya tashi, fuskar nan tasa ba yabo ba fallasa ya matsa gefe daga garesu, ta dauki Arham tana fadin, muje Banan tayi maka wanka yaron Mami da Abba, ya qanqameta har suka fita, a tunaninta Aryan din xai biyo sune, har ta kai arham wajen banan bai xo ba, 

Uniform dinsa kawai tagani a qasa ajiye, tana jin motsin ruwa ta nufi da toilet da sauri, xindir ta samesa cikin jacuzzi yana qoqarin hada ruwan wanka, ta daure fuska tamau tana kallonsa, 

Fito tun ban fara dukanka aciki ba, ba musu ya fito, haka ta riqo hannunsa suka fito, fada tayi masa sosai har sai da ya bata haquri kafin ta kaishi inda Banan.

Story continues below

Har suka xo cin abinci bai saki fuska ba, tunda anyi masa fada fushi yakeyi abincin Ma ya gagara ci tun daxu sai juya spoon yake yi, suna haka uwani ta shigo da fara’arta, bakinta dauke da sallama, 

Jidda ta amsa mata tana kallonta, 
‘sai yanxu kike dawowa Uwani, tun daxu is after 10 fa yanxu, kin kyauta kenan?

‘Dan Allah kiyi haquri anty jidda wlhy surry ta tsaidani wai sai nayi isha naci abinci, amma anty jidda kinga nayi maki ciniki sosai, biyu ne kawai aka dauka bashi, sai wadannan dana dawo dasu. 

‘bata kudin nake ba uwani, Allah ya gani bana son kina fita kina dadewa a waje dan Allah ki daina, 

‘xan kiyaye insha Allah, ta miqa mata kudin tanayi mata bayanin komai dalla dalla, 

Kallon twins tayi tana murmushi, My twins are back, shine ba magana, 

Arham yace anty Uwani nayi nemanki ban ganki ba ina kika je, 

Dama nasan xaka nemeni ai, shi wannan meke damun sa ne, 

Jidda ta kwashi kayan ta nufi dakin ta, Aryan yana ganin haka ya tashi shima cikin falon ya koma ya xauna jira yake abbansa yaxo ya gayamasa tunda Mami tayi masa fada, uwani Ma shigewarta tayi, arham kuwa kekensa ya hau ya soma xagaye da ita tsakiyar falon.

Jiniyar motocin da sukaji wanda ke nuni da dawowar mahaifinsu ya sanya arham sakin keken ya nufi harabar gidan da gudu, Aryan kuwa ko motsi bai yi ba a hakan jidda ta sauko ta same sa. 

Uwani kuwa tunda taji alamar dawowarsa ta nufi toilet a gurguje ta watsa ruwa yau duk yanda xaa yi sai tayi hira da elmustapha ko xata sami nutsuwa a xuciyarta. 

Da sallama ya shigo falon dauke da Arham, sannu da xuwa jidda tayi masa, da fara’a ya amsa yana kallonta kafin ya maida kallonsa ga Aryan, ajiye arham yayi ya nufe sa, 

‘nasan ba mai tabamin yaro haka sai Mami right? Ya gyada kai yana kallonsa idanunsa taf da hawaye, kafin yayi mgn arham yayi caraf yace, 

‘Abba fada yayi a class shine Mami tayi masa fada yake fushi. 

Ya dauke sa yana fadin, Mami ta kyauta sosai Aryan, menene amfanin fada a class, idan ka qara dukan ka xanyi sannan babu kyau fushi da Mami, tell her sorry. 

Sai ga hawaye sharrr na bin kumatunsa kamar wanda aka daka, da kyar ya iya furta, sorry Mami… 

Jidda murmushi kawai tayi cikin tunanin hali irin na Aryan, bata san inda ya sami wannan halin ba. 

Elmustapha ya maida kansa kirjinsa yana shafawa a hankali cikin shigar rarrashi, is ok kukan ya isa haka… dai dai lokacin uwani ta fito sanye da hijab har qasa sai qamshi take xubawa idanunta kyam akan sa kamar xata hadiyesa take ji saboda kauna. 

Yaya sannu da xuwa, ya aiki, ta fada cikin muryarta mai Jan hankali, kallonta jidda tayi tana naxarinta, 

Batare da ya kalle taba yace, yauwa uwani ga Aryan a canxa masu kaya xuwa na barci, akwai skul gobe. 

Cikin rawar jiki uwani ta nufesa ta karbi Aryan, ba abinda take so kamar taji jikinta ya hadu danasa koda sau daya ne, kamar jidda tasani tayi qoqarin tsaidata ta amfani da karban Aryan hannunsa ta nufi uwani dashi wanda saura kadan ta kife qasa saboda baqin ciki. 

Karo na farko kenan a xamantakewar su da ta soma jin haushin jidda, batare da ta bari jidda ta gane halin da take ciki ba ta saki murmushi mai cike da baqin ciki da haushi cunkude a xuciyarta kamar xata kifa ihu, haka ta karbi Aryan ta riqa hannu arham ta jasu badan ta so ba ta nufi dakin su jamila, banan ta miqawa su ta nufi dakinta a fusacce. 

Da sassarfa jidda ta nufesa, rungumesa tayi hade da kai masa peck a kumatunsa, kallonsa take da murmushi a fuskarta, 

All I have is you, ina matuqar son ka, bana fatan Allah ya kawo abinda xai rabani da kai koda kuwa mutuwace, nafison ta daukeni kafin kai, 

Mutuwa xata daukeni ne kafin ke jiddana, duniyar nan idan babu ke am useless, ki daina maganar. 

Taja dogon hancinsa tana murmushi, bana son kishiya elmustapha, I hate her, baxan iya rayuwa ina ganin ka da wata mace ba, baxan iya jure ganin ko wacce irin mace a kusa da kai ba koda a mafarki ne, ni dai bana sonta, bana sonta ba…. Yayi saurin rufe mata baki da nasa, sun dauki tsawon mintuna a hakan kafin ya dauke ta cak ya nufi dakin sa da ita. 

Uwani dake bayan curtains tana kallonsu, jikinta ya fara rawa, hawaye take ba kakkautawa tare da ayyanawa a ranta wlhy sai dai jidda ta mutu amma sai ta auri elmustapha kuma sai ta raba sa da ita, sai ya sota fiye da yadda yake son jidda. 

Bayan sun fito wanka wanka sun shirya cikin kayan barci, yaci abinci yayi abubuwansa da ya saba na aikinsa kafin ya kwanta, ya haye gado yayi kwanciya abinsa. 

Hakan ba qaramin sosa xuciyar jidda yayi ba, domin ba abinda take buqata a yau kamar mijinta, tafi kowa sanin elmustapha yana daya daga cikin irin maxan nan da basu cika neman mace akai akai ba, sai sufi sati a haka bai damu ba amma romance tana samu sosai domin yafi sonshi sosai akan wancan, yau kam tana tsananin buqatar shi. 

Gadon ta hau, yanda suka kwanta suna fuskantar juna sai dai shi idanunsa a lumshe suke, qirjinsa take kallo kafin ta dora hannu akai tana shafawa a hankali, bude idanuwansa yayi yana kallonta cikin yanayi na barci, 

jiddana yau ban sami Hutu ba ko kadan, nagaji sosai, ban gayamaki ba har xaria naje yau. 

Tayi shiru batare da tayi magana ba, amma yanda idanunta sukayi jaa kawai xai tabbatar maka na bacin rai ne, ta juya masa baya cikin fushi, hannu yasa ya juyo da ita hade da matse ta ajikinsa, hannunsa na yawo a doron bayanta, 

‘wannan kadai ya isa ki gane, ke kadaice macen dana keso, kin isheni a rayuwata, baxan iya lalurar wata macen ba, baxan iya son wata ‘ya mace bayan jidda ba, bana son kina juyamin baya ko kadan. 

Still bata tanka ba, banda sauke numfashi ba abinda take, 

Ko baya buqata jidda ta nuna masa tata buqatar yana qoqarin sauke wannan nauyin just to make her happy and satisfied, baiga abinda jidda xata nema a gunshi ya hanata ba, ballantana karan kansa kacokan, ya sabule hannun rigar baccinta bayan ya hada bakinsa da nata. 

‘Washe garin ranar ga baki daya yinin ranar uwani bata fito ko falo ba tana can qunshe acikin daki. 

Ganin shirun yayi yawa ne yasanya jidda xuwa ta dubata, 

Kallo daya tayi wa uwani sai da hankalinta ya tashi, jikinta ya dauki rawa ta qarasa kusa da ita fuskarta dauke da mamaki take kallonta. 

‘meke damun ki uwani, meya same ki haka, idanunki sukayi jawur suka kumbura, 

Ganin uwani tayi shiru batayi magana ba ya sanya hankalin jidda qara tashi, ta riqo kafadarta hannunta sai karkarwa yake kamar itama xatayi kukan haka take ji. 

Uwani ki gayamin damuwar ki, a duniyar nan akwai wadda tafini muhimmanci a gurin kine kamar hajiya, ko kin sami matsala da Yusuf ne?

Uwani ta girgixa kanta cike da quncin jin ta ambaci wani Yusuf, 

‘ko matsala kika samu a makaranta? Nan ma ta girgixa kanta, 

‘to menene uwani, kiyi magana, ke ba arham bace da xan xauna rarrashin ki tun daxu jin matsalar ki, atleast ko menene ya kamata ki fara sanar dani kafin kixo kina kuka anan, kinga yanda idanunki sukayi kuwa?

‘ba komai anty jidda, xaxxabi ke damuna kuma bayan wannan sai na tsinci kaina bana jin dadin rayuwata, I just feel like to cry. 

‘shine kuma baxaki gayamin ba, idan wani abu ya same ki am to hold responsible, dan Allah kidaina min haka bana so, idan abu na damunki let me know da wuri, kinsha magani ne?

Asalin labarin…….

Hajiya zubaida aminiya ce ga hajiya maimuna, xama suke na amana irin wanda yayi qaranci a wannan xamanin namu, xama suke batare da hassadar juna ba. 

Suna rayuwa a gida daya ne, kasancewar mijin hajiya maimuna ba wani mai qarfi bane sosai yana xaune a gidan haya, wulaqanci iri iri yake gani sanadiyar hakan hajiya zubaida ta umurci da su dawo a gidan ta su xauna tunda bata da miji kuma gidan yana da girma sosai. 

Yan uwan hajiya xubaida irin mutanen ne masu son cin dukiya hassada da kyashi ba abinda suke so daga gare ta kamar abin hannunta. 

Sanda ta kwanta wani ciwo mai tsanani ta soma ganin take taken su tun tana da rai suke kissafa dukiyarta saboda sun dora mata mutuwa, tana tuna mahaifin Jiddah sanda yana raye shima haka sukayi saboda auren xumunci ne dama a tsakaninsu. 

Dalilin haka hajiya zubaida ta tara su duka, ta basu wani abu cikin dukiyarta kada bayan mutuwarta su tayar da wata fitina, sauran kuwa ta damqawa hajiya maimuna tare da amanar jidda lokacin tana shekara goma a duniya, Uwani tana shekara biyar itace yar’hajiya maimuna. 

Baa dauki wani dogon lokaci ba Allah ya yiwa hajiya xubaida cikawa, tashin hankalinsu a ranar bai misaltuwa, musamman jidda kusan sau biyu tana suma. 

Jidda ta taso cikin maraici ba uwa ba uba, amma ta sami kulawa sosai a gurin hajiya maimuna tamkar yar’ta Uwani babu banbanci ko hantara tsakanin su, ta dauki jidda hannu biyu tana bata tarbiya gwargwadon iyawarta. 

Ta hada kan ya’yanta, abu mai kyau da marar kyau duk tana nuna masu kuma tare da illar sa, duka family suna son junansu musamman jidda da bata da hayaniya, tana da sanyin hali da kauda ido akan komai, gata da girmama iyayenta sabanin uwani da ita a rayuwarta tana son ta ganta da manyan qawaye masu kudi, komai dai ayi qarya, kun dai gane😀

Sannu sannu har jidda ta kammala secondary School din ta, a lokacin ta hadu da elmustapha hajiya ta aike ta banki.

Daga yanayin tafiyarta xaka gane nutsuwarta da kamalarta, kai tsaye ta shiga bankin hannuwanta duka Acikin Jakarta da alama abu take nema tana tafe tana dubawa, 

dai dai lokacin ya fito daga cikin bank din, sanye da baqaqen suit, hannuwansa wayar sa yana tafe shima yana latsa ta cikin sauri da alama wani yake son kira
Qoqarin kunna babbar wayar yake yagani ko xata tashi, cikin sa’a kuwa ta tashi, tunani yayi to kodai screen guard dinne ya tarwatse, da kuwa yayi murna sosai ya cilla wayar cikin mota. 

Yana qoqarin shiga ya ganta ta fito, wannan karon waya take amsawa

Kallo ya bita dashi har sanda tayo gab dashi dai dai lokacin tana qoqarin mai da wayar a jaka, ko kadan batayi tunanin sake kallon sa ba saboda cike take da tsoronsa gani take kamar xai iya dukanta, meyiwuwa tsayuwar sa anan Ma ita yake jira, 

Kamar ance ta dago, suna hada ido yayi mata alama da hannu taxo, sai da hantar cikinta ta motsa, ta juya tana kallon wani security tunani take ko xata hada shi da shine kada yayi mata wani abin, bata qara tsorata ba sai sanda ta gansa yana xuwa da kansa, ta riqe jakarta dam jikinta ya dauki rawa kamar ta xura da gudu take ji, 

‘amma ai nace kayi haquri ko, cikin rashin sani ne dan Allah kada ka cutar dani…. ta rumtse idanunta, 

Idanu ya xura mata kallonta yake sama da qasa har xuwa lokacin da ta bude idanuwanta, irin kallon da yake mata ya qara ruda ta, 

‘your name? Shine abinda taji ya fada, 
Tace ni.. ni… Hauwau Ahmed suna na am.. am.. Sai kuma ta kasa qarasawa, 

‘ki nutsu, ni ba mugu bane da xan cutar dake, ya nuna mata card dinsa, am a police, ko wani naga xai cuta maki xan kare ki. 

Sai ta fara sauke numfashi ahankali ba dan ta nutsu dashi, ita kawai ya barta ta tafi xata fi samun nutsuwa fiye da tsayuwa dashi, ya nemi address nata ba gardama ta bashi, da sauri ta bar gurin yana ganin lokacin da ta shiga napep ta bar gurin. 

Tana xuwa gida ta bawa hajiya labari, sosai sukayi dariyar ta bama kamar uwani, 

‘Anti Jiddah kin fiye tsoro ne meyasa xaki tsaya masa kuka, 

Jidda ta tashi ta nufi dakin ta tana fadin ai kuma tunda ba ke bace ni sai ki barni. 

*

El’Mustapha Maneer (CP) yana dawowa gida ba abinda ya fara sai maganar ya sami matar aure, 

Jin kalmar matar aure a bakin el’mustapha ba qaramin mamaki ya sanya mahaifiyar sa ba, idan ta tuna shekarunsa da muqaminsa amma bashi da aure kuma baya da niyar yin auren sai a yau da taji mgnr a bakinsa. 

‘bana son kina min wannan kallon mama, I mean it nasami matar aure, very young, ina son mace mai nutsuwa da kunya, macen da xataji tsorona at anytime. 

‘kace qaramar yarinya ce, anya batayi Ma qanqanta ba, ba wannan bama ita tace tana son ka ne. 

Ya tashi yana fadin koma menene mama ki shirya, very soon xaki sami in law, sai ki fara shirye shirye. 

Ta bisa da kallo fuskarta dauke da murmushi, Allah ya karbi adduarta mustapha xaiyi aure, oh Allah ni har ina tunani ko aljana ta aure min shi, Allah ka nuna min ranar auren nan ka sanya alheri aciki. 

Bayan kwana biyu…. 

Jiddah na kwance jikin hajiya tana tsifa sai ga Abban su ya shigo, 

‘ina jiddah?
‘gani Abba ta fada bayan ta tashi tana kallon qofar shigowa, 

‘sanyo hijabinki ki sameni falo na yanxu, 

Ta juya xuwa dakin ta, bata jima ba ta fito sanye da hijab din ta. 

Tun da ta tunkari falon take jin bugun xuciyarta na qaruwa, da sallama ta shiga kanta a sunkuye, suka amsa mata sallamar. 

Ta nemi guri ta xauna tana kallon abba, 
‘ga baqon ki, shi keson ganin ki. 
‘wata irin faduwar gaba ta dirar mata lokacin da sukayi four eyes da el’mustapha, jiki na rawa ta gaidashi kana ta juya tana kallon abba idanunta taf da hawaye. 

‘Abba wallahi na bashi haquri dan Allah  kace yayi haquri idan yaqi ka siya masa wata wayar ni ya barni. 

Murmushi ya subulcewa el’mustapha, yana kallonta qasa qasa yana jin wani abu game da ita a xuciyarsa mai girma da nauyi, tabbas yana son jidda yana son kasancewa da jidda tana matuqar birgeshi. 

‘ba maganar waya taxo dashi ba jidda, maganar aure taxo dashi amma xan barki dashi kiji da bakinsa, idan kin amince shikenan dan baxan maki dole ba, bai jira cewar ta ba ya tashi ya bar falon, tsananin mamaki ya sanya jidda binsa da idanuwa har sanda ya bar falon kafin ta juyo tana kallon el’mustapha cikin son gasgasta maganar mahaifinta. 

Da sauri ta maida kanta ta sunkuyar, baxata jure kallon kwayar idanunsa ba, ya tashi ya dawo kujerar da take xaune, da sauri ta matsa cikin jin tsoron sa, bai damu da hakan ba fatan sa ta amince da shi a matsayin mijin aure. 

‘ina son ki jiddah, taji muryarsa tamkar saukar aradu a kunnuwanta, 

‘aure nake so muyi jidda, kamata baxan tsaya ina jeka ka dawo ba kamar yanda samari keyi idan suna neman budurwa, banxo rayuwar ki dan na cutar dake ba, ina son kasancewa dake ne jiddah amma idan kin amince kamar yanda mahaifinki ya fada a yanxu, ya gayamin wacece jiddah tun farkon rayuwarta har xuwa yanxu. 

Jikinta yayi sanyi, qamshin turarensa ke sanyaya xuciyarta, baxata ce bata da samari as her age ba, akwai su kam har masu son auren ta Ma amma batasan meyasa xuciyarta tafi amincewa da el’mustapha ba, bata san meyasa take jin sa axuciyarta a yanxu ba, tunaninta idan matar sa bata son ta fa. 

‘kinyi shiru jiddah, ko nayi maki girma ne? ta girgixa kanta, yace to menene?

‘ina jin tsoron matar ka ta ganni qarama ta riqa dukana, dariya yayi sosai yana kallonta. 

Funny jiddah, saboda me xata dake ki, ballantana banda mata ban taba aure ba jiddah, ta dago tana kallonsa da mamaki, ya gyada kansa cikin tabbatar da xancen sa. 

‘ba wai na rasa matar aure bane, ina dasu har masu roqon mahaifiyata na aure su ko na auri ya’yan su, ban sami wadda nake so ta kwanta min a xuciya ba kamar jiddah, aure lokaci ne, nikam yanxu nawa lokacin yayi Allah yasa jiddah xata soni. 

Kafin kace me jiddah ta saki jiki sosai tana kallon el’mustapha yanda yake bata labarinsa da yan’matansa sai dariya take tana kallonsa musamman da yace itama sai ta bashi labarin samarin ta. 

Ta tambayi kanta shin ko mutane nawa ne a duniyar nan irin El’mustapha? 

yana da wasu ilhamomi na musamman a tare da shi da bata taba ganin su a ďa namiji ba, ko yanda yake duban mutane daban ne da sauran maxa,

Tsarin maganarsa cikin seriousness shine babban abinda ke burgeta dashi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin son wasa ta ko ina, amma yana da fara’a sosai. 

Suna tsaka da firar su sai ga Uwani taxo dauke da qaton tire a hannunta, dawowar ta daga School kenan lokacin tana S.s.2, 

Har qasa ta gaida sa cikin satar kallon sa, tana yaba sa a xuciyarta, cikin sakin fuska yake amsa mata yana kallonta kafin ya maida dubansa ga jiddah, 

Gwiwoyinta sukayi sanyi, xuciyarta ta karaya, duk wata soyayya da Allah ya halitta a xuciyarta ta haďu ta tattare waje ďaya taji ba wani wanda take so a duniyar nan sama dashi batasan dalilin hakan ba amma haduwar idanun su ne sila. 

bayan ta fito ta nufi cikin gida. 

Hajiya kinga mijin anty jiddah kuwa?

‘me akayi? Hajiya ta tambayeta bayan ta tsaida idanunta akanta. 

Babban mutum ne fa, ya hadu amma da ganinsa baxai rasa mata da ya’ya ba. 

Alhaji yace baida mata, police ne ai, nima yanxu yake gayamin. 

Bana son kinibibi da iyayi, d’an sanda ba mutum bane kinsan shi wane irin muqami ne atare dashi? Kar na qara jin wannan mgnr a bakinki. 

Ta tabe bakinta batare da ta qara mgn ba, uniform na jikinta ta soma cirewa amma har lokacin xuciyarta fuskarsa take hasko mata, duk ta tuna dashi sai gabanta ya fadi har lokacin da jiddah ta dawo bayan ya tafi. 

Kallo daya xakayiwa jiddah ka tabbatar tana cikin farin ciki, sai murmushi take, hajiya nayi mata dariya tana tsokanarta, Matar dan sanda. 

Ranar jiddah da el’mustapha baxaa ce komai ba sai faman juye juye suke a gado tare da kewar juna, suna jin wani sabon al’amari a tare dasu. 

A gurguje pls

Ana gab da bikinsu lokacin uwani ta jewa hajiya tana kuka, ita a duniyar ba wanda take so kamar el’mustapha. 

Batare da tunanin komai ba hajiya ta dauke ta da Mari. 

Kina da hankali kuwa Aisha, kinsan me kike mgn akai, mijin yar uwarki kike so, kul na qara jin wannan mgnr ko kika nuna wata alama da jiddah xata gane kina son mijinta wlhy da ni da ke ne a gidannan kuma har abban ku sai na fadawa. 

‘kiyi haquri hajiya, bansan yanda xanyi ba tun farkon ganina dashi na kasa cire sa a xuciyata ki taimaka hajiya kisa baki ya aure ni tare da anty jiddah tun….. Saukar Marin da taji a kuncin tane ya hanata qarasa mgnr ta, kallonsa take cikin mamaki bayan ta dafe kuncinta da tafin hannunta. 

Hajiya ma bata qara magana ba ta barta nan cikin qunci. 

Ranar uwani tayi kuka kamar me, el’mustapha ya riga yayi mata nisa ta riga ta rasa shi a karo na farko amma bata debe tsammani da cewa watarana sai ta xamo matar el’mustapha. 

Jiddah tayi juyin duniya tana tambayar uwani meya kumbura idanunta kukan me take gashi harda bakinta ya kumbura taqi magana, 

Taje ta tambayi hajiya cikin nuna damuwa da halin da take ciki
Me akayiwa uwani ne take kuka tun daxu hajiya, kinga yanda fuskarta ta kumbura kuwa?

Story continues below

‘kyale ta kawai jiddah kada ki matsa da tambayar meke damun uwani kinsan ba hankali ne da ita ba, yanxu haka daga makaranta ne. 

Jiddah bata qara magana ba, ta xauna kusa da hajiya tana fadin. 

‘hajiya ya maganar mu, xaki bani uwani inje da ita, tun ina qarama na taso tare da uwani nayi sabo da ita sosai kibarni naje da ita. 

‘da so samu ne kibar uwani ta xauna anan jiddah, Uwani ta canxa daga yanda kika Santa, bana so taje ta jawo maki wata matsalar da xaa xo ana dana sani. 

Babu wata matsala insha Allah hajiya, kiyi mana addua. 

‘amma ba yanxu xata xo ba har sai ta gama makaranta, idan ya so sai ta cigaba acan tunda kin matsa. 

Murmushi jiddah tayi tana fadin Allah ya kaimu hajiyar mu ya barmu tare da ke.

A gurguje pls😊

Ranar da aka daura aure a ranar ake dinner da dare akai amarya gidanta. 

Ranar dinner sunyi matuqar kyau, murmushin dake dauke a fuskarsu ke qara fito da kyawunsu, 

Sai hasken camera kake gani a ko ina ana daukar su hoto, yayin  da wasu ke qoqarin uploading a status, Facebook da Instagram. 

Duk abin nan da ake uwani na xaune da qawarta surry, idanunta kyam akan el’mustapha, duk wani motion dinsa akan idanunta ne, duk wani motsi da xaiyi tare da xuciyarta ne, kallonsa kawai yana sanyaya xuciyarta, hannunsa dake riqe dana jiddah ji take kamar ta rusa ihu a gurin saboda wani abu daya xo ya tokare a qahon xuciyarta. 

‘ke wai tunanin me kike ina ta magana kina can kina kallon mijin yayarki?

Uwani taja numfashi batare da ta kalle ta ba sai dai ta dauke idanuwanta daga kallon el’mustapha tana kallon wasu yan mata gurin. 

‘Surry son sa nake yi, idan ban same sa ba xuciyata xata iya bugawa na mutu, kowane daqiqa na xuciyata tare da tunanin sa yake tafiya, ki taimakeni ta wace hanya xanbi na mallake sa?

‘ikon Allah, waye wannan kike so haka uwani harda hawaye?

*el’mustapha* mijin anty jiddah….. ta fada idanunta kyam akan na surry xuciyarta na tsananta bugawa. 

Xare idanu surry tayi batayi mgn ba qoqarin Kora Swan water take a maqoshinta da taji alamar ya fara bushewa, kusan rabin robar tayi kafin ta ajiye tana kallon uwani. 

‘Mijin anti jiddah kike so, mijin yayar ku, kinsan me kike magana akai kuwa, kinyi tunani kafin ki furta abinda ke fitowa bakin ki, dan Allah ki daina wannan wasar Sam bata dace ba by mistake anty jiddah taji baxata ji dadi ba.
Kallonta uwani tayi, 

El’mustapha ya shiga cikin rukunni wasu mutane da nake ganin matuqar qima da mutuncinsu sannan kuma yabi ya manne a xuciyata yadda dai dai da minti daya na kasa manta shi, amma mutumin da baya ganin kowace mace a idanuwansa sai matar sa,, taya xan iya janyo hankalinsa gareni yaji ba wata a duniyar nan sai ni?

Cikin bacin rai surry ta tashi tana fadin Allah ya kyauta ya kuma shiryeki, nikam bada ni xaa yi wannan ba kuma tun wuri ki farka daga mummunan barcin da kike yi, mtsewwwww ta fice daga wurin cikin mamakin uwani tsantsa. 

Bayan an tashi dinner, suna tsaye tare da jiddah a gurin motar el’mustapha, yayin da shi kuma yana can yana faman sallamar mutanen sa da suka xo dinner. 

Uwani ta gyara tsayuwar ta tana kallonta, 

‘Anty jiddah yaya fa ya barmu anan tun daxu, sai qoqarin watsewa akeyi abarmu anan fa. 

Murmushi tayi tana kallonta, 

Kinsan mai mutane dole sai ana haquri, yana da jama’a ne sosai baki gani bane, idan yaje ya barsu ai baxasuji dadi ba tunda lalura suka xo masa, haqurin da xamuyi na dan wani lokacine yanxu xaki ganshi ya dawo bai manta damu ba. 

Uwani ta tabe bakinta kawai, ta rungume hannayenta a qirjinta hade da jinginawa da motar. 

Jiddah ta dan dubeta, idan kin matsu ne tunda ga motoci nan ki tafi kafin muxo kada mu tsaidaki an takura maki. 

‘A’ah baa takurani ba xan jira ku ai…. Juyawar da xatayi ta tsinkayosa tsaye tare da wasu yan mata guda biyu, uwani taji dadin wannan abin sanin da tayi jiddah tana da kishi sosai. 

‘Anty jiddah dubi yaya acan tare da wasu matan amma ke ya dirke ki anan ya manta dake. 

Jiddah ta juya tana kallon inda uwani ke nuna mata dai dai lokacin da el’mustapha ke qoqarin daukar yan matan biyu photo, nan take annurin fuskarta ya kau ta tsura masu ido tana kallon yanda suke style yana daukarsu foto. 

Uwani ta saki murmushi ganin yanayin jiddah ya canxa, 

Da alama tun daxu yake tare dasu ya manta dake sai dariya yake masu gashi a idon mutane ya toxartaki sai a dauka baki da wani muhimmanci a tare dashi, banda abin yaya ai ba sai ya fito ya nuna mana shi manemin mata bane. 

Jiddah kam batace komai ba amma xuciyarta xafi take mata sosai, friends dinta dake xuwa gurin suna mata Allah ya sanya alkhairi sama sama take amsa masu, 

Bayan ya gama daukarsu juyowar da xaiyi suka hada ido da jiddah, yanayin fuskarta kawai ya sanyaya jikinsa, ya riga yasan kishin jiddah akansa amma taya xaiyi mata bayanin wadannan cousins nasa yanda xata fahimcesa  batare da xargi ba akan sa. 

Kafin ya qaraso jiddah ta juya tabar gurin da sauri, motar dake qoqarin barin gurin batare da tunanin komai ba ta bude ta shiga, kafin ya qaraso tuni motar ta fice. 

Juyawa yayi yana fadin, nagode kawai ya shiga motar sa ya tayar, uwani ma ta bude ta shiga da sauri suka bar gurin. 

Har suka xo gidan ita kadai ke surutun ko uffan  baice ba, 

Ji take kamar ta fada jikinsa ta rungumesa tana shaqar qamshin jikinsa, 

Uwani ki kira min jiddah pls na kira wayar bata shiga. 

To kawai tace ta fice fuskarta ba walwala, boyewa tayi ta dan jima kadan ta dawo tana fadin

Yaya tace baxata xo ba gsky. 

Yace to shikenan bai saurari komai ba yaja motar da qarfi yabar gurin ko taqi ko taso dole yau xaa kawo masa ita. 

Police fa hajiya? Me anti jiddah xatayi da ‘Dan Sanda, mtsewwwww. 

‘Ashe baki da hankali ban sani ba Uwani? Mijin jiddah kike so yar uwarki? Wallahi na qara jin wannan maganar a bakin ki ban yafe maki ba, ni ba mutumin banxa bane da xanci amanar marainiyar Allah, kin manta dani dake da mahaifiyar ki a inuwar ta muke, dukiyar tace fa, bani da buri a duniyarnan na ganin na aurar da jiddah ga miji nagari kuma alhamdulillah na samu, ke baxaki sani jin kunyar idon duniya ba, kuma ki kiyayeni wlhy, ya juya ya fice da sauri. 

Hajiya ma bata qara magana ba ta barta nan cikin qunci. 

Ranar uwani tayi kuka kamar me, el’mustapha ya riga yayi mata nisa ta riga ta rasa shi a karo na farko amma bata debe tsammani da cewa watarana sai ta xamo matar el’mustapha. 

Jiddah tayi juyin duniya tana tambayar uwani meya kumbura idanunta kukan me take gashi harda bakinta ya kumbura taqi magana, 

Taje ta tambayi hajiya cikin nuna damuwa da halin da take ciki
Me akayiwa uwani ne take kuka tun daxu hajiya, kinga yanda fuskarta ta kumbura kuwa?

Story continues below

‘kyale ta kawai jiddah kada ki matsa da tambayar meke damun uwani kinsan ba hankali ne da ita ba, yanxu haka daga makaranta ne. 

Jiddah bata qara magana ba, ta xauna kusa da hajiya tana fadin. 

‘hajiya ya maganar mu, xaki bani uwani inje da ita, tun ina qarama na taso tare da uwani nayi sabo da ita sosai kibarni naje da ita. 

‘da so samu ne kibar uwani ta xauna anan jiddah, Uwani ta canxa daga yanda kika Santa, bana so taje ta jawo maki wata matsalar da xaa xo ana dana sani. 

Babu wata matsala insha Allah hajiya, kiyi mana addua. 

‘amma ba yanxu xata xo ba har sai ta gama makaranta, idan ya so sai ta cigaba acan tunda kin matsa. 

Murmushi jiddah tayi tana fadin Allah ya kaimu hajiyar mu ya barmu tare da ke.

A gurguje pls😊

Ranar da aka daura aure a ranar ake dinner da dare akai amarya gidanta. 

Ranar dinner sunyi matuqar kyau, murmushin dake dauke a fuskarsu ke qara fito da kyawunsu, 

Sai hasken camera kake gani a ko ina ana daukar su hoto, yayin  da wasu ke qoqarin uploading a status, Facebook da Instagram. 

Duk abin nan da ake uwani na xaune da qawarta surry, idanunta kyam akan el’mustapha, duk wani motion dinsa akan idanunta ne, duk wani motsi da xaiyi tare da xuciyarta ne, kallonsa kawai yana sanyaya xuciyarta, hannunsa dake riqe dana jiddah ji take kamar ta rusa ihu a gurin saboda wani abu daya xo ya tokare a qahon xuciyarta. 

‘ke wai tunanin me kike ina ta magana kina can kina kallon mijin yayarki?

Uwani taja numfashi batare da ta kalle ta ba sai dai ta dauke idanuwanta daga kallon el’mustapha tana kallon wasu yan mata gurin. 

‘Surry son sa nake yi, idan ban same sa ba xuciyata xata iya bugawa na mutu, kowane daqiqa na xuciyata tare da tunanin sa yake tafiya, ki taimakeni ta wace hanya xanbi na mallake sa?

‘ikon Allah, waye wannan kike so haka uwani harda hawaye?

*el’mustapha* mijin anty jiddah….. ta fada idanunta kyam akan na surry xuciyarta na tsananta bugawa. 

Xare idanu surry tayi batayi mgn ba qoqarin Kora Swan water take a maqoshinta da taji alamar ya fara bushewa, kusan rabin robar tayi kafin ta ajiye tana kallon uwani. 

‘Mijin anti jiddah kike so, mijin yayar ku, kinsan me kike magana akai kuwa, kinyi tunani kafin ki furta abinda ke fitowa bakin ki, dan Allah ki daina wannan wasar Sam bata dace ba by mistake anty jiddah taji baxata ji dadi ba.

Kallonta uwani tayi, 

Ko ki yarda ko kada ki yarda, ‘Mijin yar’uwata nake so, farin cikin da yake baiwa matarsa nake son samu fiye da hakan, so nake na rabashi da matar sa da ya’yan sa ya zamto ba kowa a xuciyar sa sai ni. 

El’mustapha ya shiga cikin rukunni wasu mutane da nake ganin matuqar qima da mutuncinsu sannan kuma yabi ya manne a xuciyata yadda dai dai da minti daya na kasa manta shi, amma mutumin da baya ganin kowace mace a idanuwansa sai matar sa,, taya xan iya janyo hankalinsa gareni yaji ba wata a duniyar nan sai ni?

Cikin bacin rai surry ta tashi tana fadin Allah ya kyauta ya kuma shiryeki, nikam bada ni xaa yi wannan ba kuma tun wuri ki farka daga mummunan barcin da kike yi, mtsewwwww ta fice daga wurin cikin mamakin uwani tsantsa. 

Bayan an tashi dinner, suna tsaye tare da jiddah a gurin motar el’mustapha, yayin da shi kuma yana can yana faman sallamar mutanen sa da suka xo dinner. 

Uwani ta gyara tsayuwar ta tana kallonta, 

‘Anty jiddah yaya fa ya barmu anan tun daxu, sai qoqarin watsewa akeyi abarmu anan fa. 

Murmushi tayi tana kallonta, 

Kinsan mai mutane dole sai ana haquri, yana da jama’a ne sosai baki gani bane, idan yaje ya barsu ai baxasuji dadi ba tunda lalura suka xo masa, haqurin da xamuyi na dan wani lokacine yanxu xaki ganshi ya dawo bai manta damu ba. 

Uwani ta tabe bakinta kawai, ta rungume hannayenta a qirjinta hade da jinginawa da motar. 

Jiddah ta dan dubeta, idan kin matsu ne tunda ga motoci nan ki tafi kafin muxo kada mu tsaidaki an takura maki. 

‘A’ah baa takurani ba xan jira ku ai…. Juyawar da xatayi ta tsinkayosa tsaye tare da wasu yan mata guda biyu, uwani taji dadin wannan abin sanin da tayi jiddah tana da kishi sosai. 

‘Anty jiddah dubi yaya acan tare da wasu matan amma ke ya dirke ki anan ya manta dake. 

Jiddah ta juya tana kallon inda uwani ke nuna mata dai dai lokacin da el’mustapha ke qoqarin daukar yan matan biyu photo, nan take annurin fuskarta ya kau ta tsura masu ido tana kallon yanda suke style yana daukarsu foto. 

Uwani ta saki murmushi ganin yanayin jiddah ya canxa, 

Da alama tun daxu yake tare dasu ya manta dake sai dariya yake masu gashi a idon mutane ya toxartaki sai a dauka baki da wani muhimmanci a tare dashi, banda abin yaya ai ba sai ya fito ya nuna mana shi manemin mata bane. 

Jiddah kam batace komai ba amma xuciyarta xafi take mata sosai, friends dinta dake xuwa gurin suna mata Allah ya sanya alkhairi sama sama take amsa masu, 

Bayan ya gama daukarsu juyowar da xaiyi suka hada ido da jiddah, yanayin fuskarta kawai ya sanyaya jikinsa, ya riga yasan kishin jiddah akansa amma taya xaiyi mata bayanin wadannan cousins nasa yanda xata fahimcesa  batare da xargi ba akan sa. 

Kafin ya qaraso jiddah ta juya tabar gurin da sauri, motar dake qoqarin barin gurin batare da tunanin komai ba ta bude ta shiga, kafin ya qaraso tuni motar ta fice. 

Uwani ta qaraso tana fadin, 
‘nayi qoqarin fahimtar da anti jiddah qila yan’uwan kane ko abokai amma taqi ta gane saboda kishi dake cinta kasan halinta. 

Juyawa yayi yana fadin, nagode kawai ya shiga motar sa ya tayar, uwani ma ta bude ta shiga da sauri suka bar gurin. 

Har suka xo gidan ita kadai ke surutun ko uffan  baice ba, 

Ji take kamar ta fada jikinsa ta rungumesa tana shaqar qamshin jikinsa, 

Uwani ki kira min jiddah pls na kira wayar bata shiga. 

To kawai tace ta fice fuskarta ba walwala, boyewa tayi ta dan jima kadan ta dawo tana fadin

Yaya tace baxata xo ba gsky. 

Yace to shikenan bai saurari komai ba yaja motar da qarfi yabar gurin ko taqi ko taso dole yau xaa kawo masa ita. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page