GIDAN SARAUTA CHAPTER 3

GIDAN SARAUTA

CHAPTER 3


Acan gidan yari kuwa su Sulaiman na fita daya daga cikin dogareyen yayi saurin zuwa yasamu Sarkin gidan yari yake fada masa sannan yake tambayar shi yaje yafada ma Magajiya ne!….
Cikeda tashin hankali Sarkin gidan yari yace babu ruwanka kakoma bakin aikinka harsai inta zo dakanta ko ta tambaya se ace mundauka ita taturo Sulaiman din don kuwa banshirya fita yawon banza da daren nan ba kasan muddin akafada mata zatace se annemosu kuma dai ninasan ba samunsu zamuyiba tayuyuma shi Yariman barin garin zeyi da’ita……
Gyada Kai dogarin yayi yakoma bakin aikinsa dukda kuwa zuciyarshi bugu takeyi don yasan daga karshe shine ah ruwa kuma dai bai isa yayima Sarkin gidan yari musuba…….
*****
Kanada tabbacin kana ganinshi da mace kwanan nan Magajiya tayi tambayar cikeda mamaki…….
Cikeda assurance mutumin yace tabbas Uwargijiyata don sau biyu inaganin su tare sede kaman ita yarinyar ne kebinshi don ranar har tureta yayi tafadi sekuma akwai ranarda nagansu harda kanwarshima dakuma yarinyar,gyada kai Magajiya tayi sannan tace kayimin bincike akan ita yarinyar kaji?…
kanshi na ah kasa cikeda biyayya yace to uwargijiyata, murmushi tayi sannan tace ina nufin komai game da yarinyar tundaga gidansu har zuwa rayuwarta na makaranta zuwa jibi ka tabbatar kazomin da komai,gyada mata Kai yayi sannan yayi godiya yatafi…..
Talatu dake gefen Magajiya ta washare baki cikeda gulma tace “Uwargijiyata kinji yaro yagirma har budurwa yayi,ai dama mun tambaya ko kyakyawa ce mai aji don kuwa irin matan dasuka dace hadadden yaron can kenan” …..
Cikeda takaici Magajiya takai hannu zata maki Talatu,cikin sauri Talatu ta gauce sannan tashiga neman gafara”wallahi tallahi Uwargijiyata subutar bakine, Allah kuwa”…..
Harara Magajiyan takai mata”inbaki iya bakinki ba I can’t help it wataran senayi rugu rugu dake wallahi”….
Za agyara Uwargijiyata tayi maganar kaman zatayi kuka,tsaki Magajiya tayi don bakaramin bata mata rai Talatun tayiba sannan tawuce tabarta agurin…….
***
Kusan 12:00am ya Isa cikin garin kaduna straight gidansu abokinshi yawuce wanda already daman yakirashi yafada mishi yana hanya da kanwarsa………
Bayan sun gaisa da Matar Idriss dinne wanda itama batakai gayin bacci ba yayi musu sallama yawuce hotel abunsa dukda kuwa sunyi sunyi yakwana tunda sunada extra room amma yaki, washegari wuraren goma yazo yadauki Afiya yakaita shopping don kuwa batazo da kaya ko dayaba dadai sauransu se kusan azahar suka dawo gida inda yake cemata da la’asar zasu wuce Abuja….
Itadai mamakine yakamata don tayi tunanin ah kaduna ze barta tazaune tareda Matar Idriss din don harta fara jin dadin zama da’ita sabida Matar akwai kirki kuma koda zata girmeta ma to befi da irin shekaru biyu ko daya ba,amma se bata tambayeshi ba tunda yace mata she should trust him to tayarda dashidin tabbas…..

****
Tunda Asma’u tagama shirin makaranta setasamu guri tazauna kamar yanda tasaba ada intana jiran Asiya,setakejin kaman zata aiko akirata tazo su tafi seda Ummi tayi mata magana sannan ta tashi tatafi hannunta rikeda car keys…….
Tana zaune cikin motar takira wayan Zahra seda suka gaisa sannan take tambayar Zahra din kota shigo school nan Zahra kecemata a’a bata shigo ba tukunnan ai Antynta ma tahaihu adaren jiya dakyar inzata samu shigowa,cikeda farin ciki Asma’u tataya Zahra murna sannan tace tagaida Antyn inta tashi ah school may be tabiyo tayi musu barka…
Ah dayan bangaren ne Zahra tace to senaganki Asmeey,nan sukayi sallama…..
Tunda Zahra tace mata bazata shigoba setakejin batama jin shiga school library yau don dama itane me sata zuwa din, starting motar ta tayi sannan takoma hanyar gun data saba ganinshi parking motar tayi ahankali sannan tafito hannunta rikeda litattafanta tayi lungun gurin seda ta lelleka tako ina amma bayanan juyowan dazatayi kuma setayi arba dashi daga can gefe yana karatunshi hankali kwance, murmushi tadan yi sannan takarasa inda yake harta samu guri tazauna bece mata komaiba hakanan bedago yakalletaba amma bata damuba setace…
“Ina kwana Yaya Almustapha?”…..
Dukda yayi mamakin ya akayi tasan sunanshi seya kyaleta be kulataba yiyayima kaman bejitaba,dan tabe baki tayi sannan tace insabida abunda nace ranar ne kake kin kulani I’m really sorry,I was just hurt by your attitude bawai yakai har zuci bane ba.tayi maganar kaman me shirin yin kuka. …
Still bekulataba sema bude next page na takardar dake gabanshi yayi,sa hannu tayi tadauke littafin gabanshi yayinda cikin sauri yadago kanshi yadaura idanunshi kan nata seda ta tsorata amma seta dake”tunda bazaka kulaniba nima bazan barka kayi karatunba”,wannan karan ah shagwabe tayi magana…..
Dauke kanshi yayi daga kallon oily eyes dinta ya kawar gefe sabida wani irin yanayi dayake ji wanda betaba jiba a rayuwarshi kafin yatashi ahankali zebar gurin don ya lura yarinyar neman fitina take dashi shikuma bashida lokacinta Itama cikin sauri tatashi tareda shan gabanshi sannan tamika mishi littafinshi”indai don nabaka hakuri ne zaka tafi, I’m sorry just stay back bazan sake damunka ba”….
Yanda tayi maganar seyaji jikinshi yayi sanyi, atleast she’s being nice and hakurine yakamata yahakura tunda ko Allah ma muna mishi laifi ya yafemana ballantana mukuma bayinshi,karban littafin yayi kaman bazaiyi magana ba sekuma yace”It’s okay”…..
Kallonshi tayi sannan tace”hakan na nufin ka hakura?”….
Jijjiga mata kai yayi sannan yajuya zai tafi cikin sauri tace indai ka hakura basai katafiba please kazauna kayi karatunka nima zanje can inyi….
Bayason musu da takura don haka yakoma yazauna Itama godiya tayi mishi sannan ta tafi can dan nesa dashi tabude littafin ta tashiga karatu batareda wani damuwa ba setakejin yau karatun nawani shiga sosaima…..
Can tana cikin karatun ne seta iso inda takasa ganewa, don haka takarasa gurin shi hoping that he might help ……
Yanajin sanda ta taso jiyayi kaman yatashi ya gudu don da alama zatazo tadameshine Kuma, yana cikin wannan tunanin ne tayi mishi sallama ansawa yayi azuciya kafin tace don Allah I’ve a question if you don’t mind,I mean muna yin course daya and you’re ahead of me may be ka iyamin bayani…..
Gyada mata Kai yayi alamar to batareda yadago yakalletaba,nan tashiga yimishi tambayar hartakai karshe,dan shiru yayi nadan dakiku yana tunani,he can explain it but shidai he cannot talk for that long bakinshi seyayi ciwo ai don haka seyadubeta yace”zanmiki bayani in written”….
Damamaki ta kalleshi sannan tace ta ina zangane suma ai in written dinne shiyasa banganeba kamun explaining don Allah tayi maganar tana dan make kafada,daukan littafinta dake kasa yayi yamika mata alamun tatashi tatafi inbata yardaba kenan,cikin sauri tace nayarda karubuta din,yiyayi kaman baijitaba seda yaja mata aji kafin yakarbi littafin yashiga rubutu cikin nutsuwa seda yacika paper biyu na long note duka dauke da bayanin sannan yamika mata yacigaba da karatunshi,kallon rubutun nashi takeyi gwanin ban sha’awa tunda take bata taba ganin handwriting din daya tafi da imanintaba irin wannan ba sannan cikin nutsuwa tamaida hankalinta kan rubutun tashiga karantawa aikuwa segashi tagane don bayani yayi mata sosai kaman yanda zaiyi mata bayani in magana zaiyi….

Story continues below

Seda takai karshe sannan tadauki pen dinta Itama tafara mishi rubutu…

” _Thank you *Mr Taciturn* ,nagane sosai fiyeda yanda inwani mai bayani da baki zaiyimini bayani.i must say you’re very talented_”…

Mika mishi littafin tayi tana dan murmushi,littafin yafi minti uku agabanshi beko kalla ba seda tace”Yaya Almustapha!”…
Dagowa yayi yadubeta,nuna mishi littafin tayi da hannu sannan yamaida hankalinshi kan littafin yashiga karantawa sannan yadawo mata da littafin batareda yayi reply ba,murmushi kawai tayi tana dan satan kallonshi sannan ah ahankali ta furta”Mr Taciturn, tareda yin ‘Yar dariya sannan tace and the name really suits him”…..
Tana cikin wannan tunanin ne taji kaman abu ah gefenta cikin sauri ta kalli gefen nata kadangare tagani yayo kanta aikuwa datawani fasa ihu se kan Almustapha faduwa sukayi dukansu biyun yayinda tana kanshi ta kankameshi sosai ga hawaye nata shatata, lizard! Yaya Almustapha help me!….
Shikuwa tunda tafada jikinshi wani yar yaji kaman electric shock don haka yashiga kokarin tabuketa daga jikinshi amma ina tabi ta kankameshi shi da abun ya isheshine yace”get back to your senses, yatafi lizard din” ….
Dago kanta daga kirjinshi tayi cikeda tsoro sannan tasaukesu kanshi “are you serious yatafi”,kasa karasa maganar tayi because she get lost in his dashing eyes gakuma heart dinta daya shiga beating so fast at thesame time,batasan metake ciki ba she just know that she’s in another world,the world of Almustapha may be! wanda awannan lokacin zuciyarta takasa cemata takoma nata duniyar,duniyar da kowa ke cikinta sannan inda take din bai dace da’ita ba ah bangaren Almustapha ma hakane tunda yake kallon cikin idanunta yakejin wasu irin feelings dabai taba jiba ah rayuwarshi,a new feeling dabaisan ana jinshiba, feelings din daya kasa defining nashi duk kuwa da irin basira da kwakwalwar da Allah yabashi.shine yafara dawowa cikin trance dinshi har ya farga da condition din da suke ciki cikin sauri ya tureta tafadi gefe don tariga ta sassauta rikon datayi mishi already,tashi yayi cikin sauri kaman wani marar gaskiya sannan yadibi litattafan shi yabar gurin……
Itakuwa tunda yayi gefe da ita takasa tashi donkuwa wani irin kunya ne yakamata gakuma haushin kanta datakeji seda ta tabbatar yabar gurin sannan ta tashi tana salati da dafe kanta, sega hawaye kuma”meya kaiki Asma’u,kinason jama kanki bala’i ne komi,what were you thinking, why were you lost in his eyes wannan abun kunya damai yayi kama”,sune abubuwan data shiga nanata ma kanta tafi awa tana zaune ah gurin takasa tashi kuma takasa cigaba da karatun she is just regretting what has just happened,what if he yayi taking advantage of her weakness yamata wani abun yazatayi,mezatacema iyayenta kuka tadingayi sosai kafin daga karshe tayanke ma kanta hukuncin fita harkar Almustapha dukda wata zuciyar na hanata yin haka sede this’s the best solution,diban takardunta tayi tawuce gida batareda taje gidansu Zahra dinba because she’s not in the mood kuma…..

****
Sanda su Sulaiman suka isa Abuja hotel yaje yakama mata daki sannan yace tahuta anan zeje yadawo,kallon shi tayi sannan tace Yaya Sulaiman anan zamuyita zama?….
Murmushi yayi sannan yadan jaa hancinta”little Angel na isa inbarki ah hotel,sokike Yaya Almustapha yayi raga raga dani kenan?”….
‘Dan turo baki tayi sannan tace tonikam inazamuje,yar dariya yayi sannan yace you’ll see kamun yaduba wristwatch din hannunshi”I’ve to go somewhere now innadawo zamuyi magana,in anyi knocking kitambaya waye kafin kibude kinji?”….
To kawai tace mishi kafin yafice yabar ta zaune tana karema dakin kallo,ko ina ah dakin yayi kyau very perfect! ‘dan jan soft pillow din tayi takwanta tareda sakin murmushi dukda kuwa tana tsoron ranar komawan ta masarautar dakuma ranar gamuwanta da Magajiya,she never thought for once in her life zatabar cikin masarautar Zaria har ta fita wani gari talk more of ace hartazo Abuja,garin masu kudi dakuma masu kasar baki dayanta bata tashi mamaki bama seda Sulaiman din yadawo yadauketa suka tafi airport don jirginsu da dare zaitashi zuwa Indonesia dukda kuwa da private plane zasu tafi wanda yakasance na Mai Martaba ne kukan murna tashiga yi tareda rungume Yayan nata,I love you so much Yaya Sulaiman.yar dariya yayi and I hate you more little Angel,turo baki tayi sannan tace “hate Kuma?”,dariya yakuma yi more than love kenan Sisto,to naji amma tonikam kafada ma su Amira ne, I’m getting worried about them ….
Jan hancinta yayi sannan yace “I told them kada kidamu”….
nanfa tashiga murna sanda suka shiga jirgin kuma tajuyo ta kalle shi with questioning look “mezamuje yi ah Indonesia?”…..
Ah takaice yace”to meet a family”….
Gyada mai Kai tayi kawai batareda takuma cewa komaiba,shikuma jingina kanshi yayi dajikin kujera yana tunanin yasu Almustapha zasu Kare ah masarautar dukda kuwa yayita kiranshi ta numbern daya saya mishi tareda wayar amma akashe which means Almustaphan be kunna wayar bama kwata kwata numbern Mallam Hudu kuwa tunsafe yake Kira ah kashe don haka ya hakura besides indai Magajiya tasamu labarin yatafi da Afiya to tabbas su Almustaphan ma zasuji labari shiyasa bai wani damuba……
Afiya kuwa da jirgi yatashi lulawa sararin samaniya seda tayi kauyanci with the help of her Brother tasamu tazama stable
haka jirginsu yadaga zuwa Indonesia (su Afieeya mutan Indonesia)………
****
Koda Asma’u takoma gida setayi kokarin cooling kanta sabida batason Ummi tashiga yimata tambayoyi,seda tayi wanka sannan tawuce bangaren Mommy kaman yanda suka saba zama ah parlourn haka tasamesu anata hira sede babu Asiya cikinsu, gaida Mommy tayi sannan tashiga gaida yayun nata kowa ya ansa amma banda Mubaraq idanunta suka ciko da kwallah tace Yaya Mubaraq don Allah kadaina fushi dani…..
Dubanta yayi ganin hawayen sunfara zuba kaman famfo yace zonan….
Karasawa tayi gabanshi tareda samun guri tazauna,riko hannunta yayi “kekam bakya gajiya da kuka ne?”…..
Sa hannu tayi tana goge kwallar dukda kuwa kara zuba suke non stop tace”to ai kaine kake fushi dani”,wannan karan dariya duka yan parlourn sukayi ga yanda tayi maganar kafin Mommy tace”to Yaya Mubaraq yakamata adaina fushi da Ma’u hakanan”…..
Dubanta yayi tareda dan Kai mata rankwashi”To kinci sa’a Mommy tashigan miki sabida haka nahakura”,godiya tashigayi mashi yayinda yace “aini akan godiyar nan dama noodles kika shiga kika dafa mini don nayi kewan dafuwan indomie dinki”…
Cikin sauri tatashi tana “right away,yanzu zan dafa maka Yaya Mubaraq” su Sadiq, Musa da Aliyu ne suka ce muma zamuci Mata ah gidan Doctor Mukhtar….
Yar dariya tayi tareda jijjiga Kai, Hajja dake gefe tanajinsu tayi tsaki sannan ta tashi tashige ciki don aganinta bazata iya ganin kayan takaicin nan ba…..
Hadaddiyar indomie tadafa musu sannan tabaje musu shi ah parlour nanne takejin wai iyayen Mukhtar zasuzo cikin weekend neman aurenta na Aslam kuwa gobe ma zasuzo neman auren Asiya,haka kawai setaji gabanta nawani mugun faduwa yayinda duk wani walwalarta ta gushe don haka bata jima ah gurinsu bama tayi musu sallama takoma bangarensu….. .

Story continues below

****
Magajiya ganin Sulaiman tunsafe be ziyarcetaba ta aika akira mata shi amma se akace mata bayanan yayi tafiyi, hankali tashe tace akira mata isah….
Jikina bari Isah yazo bangaren Magajiya,zubewa yayi gabanta tareda mika gaisuwa irinta sarauta,cikeda zafin rai tace dago ka kalleni!….
Dagowa yayi sannan tace meyene Talatu tazo tana fadamin bangane ba?…..
Cikin in Ina Isah yace “tazo duba Yarima dazu kan kina kiranshi shine nace mata yayi tafiya tun jiya da daddare”…..
Kan uba shine abunda Magajiyan tafada sannan tace”kanason kacemin Yarima yayi kusan awa ashirin da hudu da barin masarautar nan amma nibanida labari?”….
Jijjiga Kai yayi alamar eh kafin yace ranki shi dade tafiyar gaggawa ne takamashi,tsaki tayi sannan tace au kamasan da hakan shine bakazo ka fadaba,shiru Isah yayi don ya lura ah garin kare Yariman yajaza ma kanshi,hakuri yashiga bata yayinda tace yatafi yabata guri zata dawo kanshi sanda takeda lokacinshi kafin tawuce bangaren Mai Martaba direct harya kwanta yana shirin bacci tashiga dakin,dubanta yayi ganin ranta ah bace yatashi yazauna…
“Magajiya lafiya?”….
Zama tayi bakin gadon kafin tace “yanzu fisabilillahi har Sulaiman yayi tafiya bawanda yayi tunanin ya fadamin?”….
Kallonta yayi cikeda mamaki sannan yace shidin bai fada miki bane?…..
Kai tsaye tace befadaminba nikam….
Tabe baki Mai Martaba yayi sannan yace to bansan dalilinsa nayin haka ba sede niyacemin ana nemanshi ah makaranta Kuma nabarshi yatafi zedawo ai kafin bikinsu,zare idanu Magajiya tayi sannan tace Mai Martaba kana nufin Sulaiman London yatafi?…..
Jijjiga mata kai yayi kafin tashiga salati,tsaki Mai Martaba yayi sannan yakoma yakwanta don yasan halin Magajiya da exaggerating akan abunda baikai yakawoba,yana kwancen yace inzaki kwantar da hankalinki gwanda kikwantar da hankalinki yafi bawai kitsaya kina tada zaune tsayeba kifita kibarmin daki bacci zanyi”…
Rai bace tatashi tafita tana masifa,haka adaren bayin ta dazasu tayata canza kaya zuwa na bacci seda sukasha fada da mazga don kuwa akansu tashiga huce haushi haka tadinga Kiran layin Sulaiman na London amma baya tafiya dakyar tasamu ta kwanta bacci…….
…..
Wuraren karfe biyun dare kowa yayi bacci ah masarautar se dogaraye dasuke gadi ne kawai,wata mata ce sanye da bakin kaya from head to toe tashigo dakin Magajiyan tawani hanya hannunta rikeda wuka cikin sanda tadingayin kusa da gadon Magajiyan, Magajiya dake shatata bacci tayi juyi kaman zata tashi yayinda matar dake lullube cikin bakin kayan tayi saurin buya kusa da gadon wanda karan saukanta kasa yasa Magajiya tashi,dube dube tashigayi ah dakinnata sede bataga kowaba don hasken harabar masarautar na dan hasko cikin dakin,komawa tayi ganin ba kowa tacigaba da baccinta seda matar ta tabbatar takoma takwanta sannan ta tashi takaraso jikin gadon wuka tadago tana niyar kaima Magajiyan dede lokacin Magajiya tabude idanunta sekuma ga Talatu ma tashigo don Itama daga dakinsu dake dab dana Magajiya su masu kula da ita taji kaman motsin mutum,wani irin ihu daga Magajiya har Talatun suka saki wanda yajanyo hankalin guards din, dasauri Matar kuma tabi ta hanyar data shigo dagudu sanda guards din suka shigo Talatu tanuna musu hanyar da Matar tabi kafin takaraso gurin Magajiya dake haki tana sharban hawaye shikenan dayanzu an harba da ita lahirafa……..

Talatun ne tace”Uwargijiyata sannu?”…
Tureta Magajiya tayi tana goge kwallarta kafin tace kinga fuskarta ne?……
Jijjiga kai Talatu tayi kafin tace aa banganiba fuskarta ah rufe take,tsaki Magajiyan tayi sannan tace aida kinbita kin kamota yanzu ba lallai su sugantaba,Talatu datayi tsumu tsumu Kai akasa tace kiyi hakuri yayinda ah zuciyarta kuwa cewa take”aiko ciwon haukane yakamata batabi mace irin wannan da wuka sh hannunta ba”,ana cikin hakane sega guards din sundawo Magajiya already ta lullube jikinta tana tsaye tace baku sameta ba?…..
Babban cikinsu ne yace ranki shi dade bamu gantaba wallahi sede munga kaman anbude wata tsohuwar kofa tacan baya inatunanin tanan tashigo, cikeda tashin hankali Magajiya tace to wacece haka take niyar hallakani ni Magajiya….
Shiru kowa yayi agurin,yayinda cikin sauri kuma Afiya tafado ma Magajiya ah rai,duban daya daga cikin guards din tayi sannan tace kaje kasa ah sanar da Mai Martaba abunda yake faruwa kukuma ku buyoni tayi gaba suka bi bayanta har zuwa gidan yari, Sarkin gidan yari daganin Magajiya nan take cikin shi yashiga dura ruwa,dubanshi tayi rai bace sannan tace kafito min da tsinannan yarinyarnan I know she’s behind all this…..
Zare idanu Sarkin gidan yari yayi sannan yashiga kiran daya daga cikin dogarayen dake gadin cell din da akasa Afiya,cikin sauri dogarin yakaraso yana mika gaisuwa,Sarkin gidan yari yayi kaman baisan komai da al amarin barin Afiya gidan yari ba yace “Kai Habu kafito da yarinyar can”,cikeda tashin hankali Habu yasauke kai kasa ranka shi dade ai Yarima yazo yatafi da ita tun jiya da dare mu munyi tunanin Hajiya ce tasakashi bekai ga rufe bakiba Magajiya takai mishi wani wawan mari”ninasaka shi kakeson kacemin komi,kokataba ganin inzanyi abu inasakashi?”….
Iye,shidai kanshi na kasa bece komaiba dukda kuwa yaji zafin abunda tayi mishi aikoba komai taduba girman shekarunshi tayi mishi afuwa sede ashe yamanta wacece Magajiyan,Matar da batasan mutunci dan Adam ba domin batadaukesu abakin komaiba…. suna cikin hakanne akashiga announcing Mai Martaba ya iso,sa hannu tayi kan lips dinta tana ma Sarkin gidan Yari nuni dayayi shiru kada yace komai sannan tayima Habun ma haka gyada mata Kai yayi……
Alokacin Kuma Mai Martaba yakaraso,meyake faruwa tambayar dayayi kenan…
Kicin kicin Magajiya tayi da fuska sannan tashiga bashi labari tun abunda yafaru na sa abinci ah guba dakuma nayau din sannan takarada”tunda akaso kaimin wukar yarinyar tayi nasarar guduwa shine nace barinazo gurin wannan din ko itace aikuwa inazuwa suka cemin tagudu daga gidan yari suma neman ta sukeyi”……
Sarkin gida da Habu speecchless suka zama donkuwa sune sukasan komai tunda sauran lokacin da ake bayani duk attention dinsu yakoma ga tarban Mai Martaba da aka fadi isowanshi……
Mai Martaba ne yace ma guards din duk yanda akayi batabar masarautar ba may be tanacikin harabar gidan su rabu tako Ina ah nemeta,dogarin daya ga hanyar data fitan ne yazo gaba yayima Mai Martaba bayani…..
Cikeda mamaki Mai Martaba yace ikon Allah,to duk yanda akayi wacce tasan kan masarautar nan ne domin kofarcan bakowa yasan da’ita ba,anjima da daina anfani da ita tun kakanni…..
Magajiya ne tace”shekarunsu nawa acikin Masarautar nan ai babu inda basu saniba”…..
Kallonta Mai Martaba yayi sannan yace kinada tabbacin ita dinne?…..
Ahankali tace “Mai Martaba inba itabane wanene zeyi yunkurin kasheni tunda ba ataba irin abunnan ba acikin Masarautar nan,babu wanda yataba kaimin hari se ita,to inko ba itan bace to wanda tasakata ne,cikeda takaici tace Kai itannema tunda dai gashi tayi escaping”……..
Gyada kai Mai Martaba yayi sannan yace wannan binciken zamuyita gobe yanzu dare yayi,sannan yadubi Sarkin gidan yari yace yakira masa Sarkin sojoji babu bata lokaci segasu sundawo, Mai Martaba ne yace masa a sake tightening securities more especially ta bangaren Magajiya ……
Cikin sauri Magajiya tace itafa bazata koma dakintaba bin Mai Martaba zatayi inyaso ah sa securities din ah nashi bangaren…….
cewa yayi to kafin suka tafi,duk wannan abunda yake faruwa su Almustapha basu da labari tunda cikin darene abun yafaru abu dayane yabashi mamaki yau dayaje duba Afiya kwata kwata Sarkin gidan Yari yahanashi shiga…..
Washegari dasafe tafiyar gaggawa takama Mai Martaba zuwa sokkoto wanda hakan yabama Magajiya daman yin abunda tayi niyar aikatawa tun jiya don ita bazata tsaya har ah aikata lahira batareda tadauki matakiba kuma bazata tsaya jiran Mai Martaba ba…..
don haka shida waziri suna tafiya da tawagarsa zuwa sokkoto itama tasa aka kiramata wasu daga cikin dogarayen gidan sannan tace suje su tabbatar yau su Almustapha sunbar masarautar nan sannan kuma batason taji labarin yakoma kunnen waziri don kuwa zatayi musu abunda basu taba tsanmani ba,jikina bari duwawu na zikiri dogarayen sukayi gidan su Almustapha….
Amira na sharar tsakar gida taji anbangazo kofa,cikin sauri tadaga kai nan taga dogaraye sunkai goma batareda sun mata magana ba suka shiga dakin da Ummi ke kwance sannan suka fara diban kaya suna fita dashi waje,Kuka Amira tashigayi tana basu hakuri”wai miye hakan kukeyine?”…
me muka Kuma, hakanan me muka tare muku acikin gidan nan,daya daga cikin dogarayen ne yakai mata maka sannan yace yauko kubar gidan ko muyi waje daku bayan mungama fidda tsunmokaranku,cika umarnin Magajiya mukeyi…….
Almustapha dake daki yanajinsu,amma ko gezau beyiba Amira data gama yimusu magiya ne taga basuma kulataba yasata yin dakin Almustapha tana kuka,Yaya Almustapha don Allah kafito kaga abunda sukeyi ah waje……
“Ahankali yace let them do their work,ihunki bazaisa subari ba”…..
Sakan baki tayi tana kallon shi da mamaki don kuwa ranta yabaci,bedamuda tsayuwar datayi akanshiba sema tashi dayayi yafita ah dakin ah lokacin sukuma sungama tattare kayan se Ummi dake kwance kan katifa ne suna shirin shiga dakin yayi saurin shiga tareda rufo kofar yasa sakata zuciyarshi nayi mishi wani irin Kuna,he can let them do anything but bazai bari suyi disgracing mahaifiyarsa ba, ahankali yadinga takawa har ya Isa gabanta sannan ya tsuguna cikin sanya hawaye yagani ah idanunta yana zuba non stop,rimtse idanunshi yayi shima ahankali besan sanda shima hawayen yafara bin nashi kuncin ba he can be strong agaban kowa,he can hide his tears from anyone amma bazai iya taba boyema Ummi ba dukda kuwa halin datake ciki because the situation is so tough daya rasa inazaisa ransa……
Ahankali yadaura kanshi ah jikinta tareda rike hannunshi cikin nata,yanajin dogarayen na buga kofa kaman zasu ballah amma bai damu ba sema cikin kuka yace “Ummi get well soon,kitashi don Allah as you can see irin injustice da ake mana ah gidan mahaifin mu,Kara kankameta yayi yana kuka me tsuma zuciya”we really need you Ummi!we need your support”…
Sunfi 30 minutes ahaka yayinda dakyar ya iya sassauta kukan nashi don ayanzu kuwa har dogarayen sungaji da bugawa se Amira dake faman Kiran sunanshi tana cewa yabude kofar don Allah……
Jiki ah sanyaye yatashi yabude kofar cikin sauri Amira dake kuka tashigo cikin dakin tana Yaya Almustapha inata buga kofa muyi mubar gurin don Allah nan suntafi fadama Magajiya abunda kayi kada tazo tasameka….
Kallonta kawai yayi don shi tunaninshi daya,inda zasuje tunda dai su ba kudiba bare wani gidan bare ace sukoma can…….
Duban Amira yayi sannan yace kishiga ciki and kirufe kofar taciki I’m coming, juyawa yayi zai tafi yayinda tana binshi da kallo,harya fita ah kofar seya dawo kuma yadubeta”karki bude kofar harsaina dawo”…
Gyada mishi kai tayi yayinda yawuce yatafi straight kasuwa gurin Mallam Hudu bayan sun gaisa ne Almustapha yace”zamu samu gida please?”…..
Cikeda mamaki Mallam Hudun yace gida kuma,meya faru dan dafe kai Almustapha yayi yakumacewa”gidan haya nike nufi”….
Jijjiga kai Mallam Hudu yayi sannan yace ni Almustapha bangane inda ka dosaba,kana nufin gida zaku canza hakanan?…..
Jijjiga kai Almustapha yayi alamun aa, ahankali Mallam Hudu yace koranku akayi acan din?…..
Gyada Kai wannan karan Almustapha yayi,ikon Allah shine abunda Mallam Hudu yace sannan yace mutanen nan basuda imani narasa yaushene karshen wannan abun kafin Kuma yadanyi shiru yana tunanin inda zesama musu gida ah yaudin don bayason ah wulakanta su……
Tunowa dawani abokin dillali yayi,nan yashiga
kiranshi bejima yana ringing ba yadaga kiran,tambayarsa yayi koza asamu karamar gida haka bayan sun gaisa,cemishi yayi eh za a samu…..
Ayau fa muke bukatar gidan cewan Mallam Hudun…
Daga daya bangaren dillalin yace za asamu kaikam koyanzuma, godiya Mallam Hudu yayi sannan yace barinazo insameka semuje muga gidan……
Haka suka dunguma shida Almustapha don zuwa su samu mutumin yana cema Almustapha din ai gwanda ma kubar wannan masarautar don sharrin yau daban nagobe ma daban,shidai Almustapha bece komaiba harsuka isa gun mutumin yaje yanuna musu gidan,babu laifi gidane medan kyau compared to wanda suke ciki ah masarautar don kuwa wannan akwae daki da parlour gakuma kitchen sannan akwae daki ah gefe wanda zekasance na Almustapha,anguwan talakawa ne sosai don haka kudin hayan baiyi wani tsadaba,mota Mallam Hudu yasamu akaje har masarautar aka tattare kayansu da akayi watsi dasu aka kai can gidan dazasu koma din sannan sukadawo suka dauki Ummi don Amira tajima dazuwa can tana gyare gyare,dukda kuwa sanda suke duba gidan bayan tafiyar Almustapha Magajiya tazo takarashi haukanta amma taki bude kofar kamar yanda Yayanta ya umarceta….

Bayan sunkoma gidan ne Amira tagama putting komai into its right place sannan ne Mallam Hudu yace yau da dare zedawo don akwai important magana dayakeson suyi, Amira ne tace Allah yakaimu da daren …..
Amin ya amsa kafin tamasa godiya yafita,kallon Almustapha dake gefe tayi sannan tace yazamuyi da batun Afiya,yazamuyi Yaya Almustapha?…
I’ll think about it shine kawai abunda Almustapha din yafada sannan yatashi yafita shima….
***
Magajiya kuwa tunda takoma bangarenta taketa banbami su Humaira ne suka shiga bata hakuri dukda haka kasa kwantar da hankalinta tayi seda daya daga cikin dogarayen yazo yace mata ai sunzo sun tattare kayansu kafin hankalinta yadan kwanta, atleast she’ll now be able to sleep peacefully……

****

*INDONESIA*

Tunda jirginsu yasauka ah city na Jakarta taketa kallon kauyanci sanda sukabar harabar airport din taxxi ya tarar musu sannan yacema mai taxxi din yakaisu any suitable hotel wanda they’ll be comfortable….
To mai taxi din yace kafin yakaisu hotel din wani hadadden hotel,booking two rooms yayi musu sannan aka rakasu, har daki ya rakata sannan yace tayi wanka kafin akawo abinci tomorrow morning he’ll start his work,haka tayi wanka sannan tarama sallolinta kafin aka kawo abinci taci,tanaci tabi lafiyar gado dama isowan dare sukayi and she’s very exhausted…..
Washegari tunda Sulaiman yatashi yayi sallar asuba bekoma bacciba kiran numbern Mallam Hudu yashigayi tasabon number din dayasaya dasuka iso amma still baya shigo don haka seyashiga wanka abunsa yashirya tsaf kafin yashiga gurin Afiya still tana bacci written note yabar mata kafin yawuce…….

Story continues below

Yana fita yatari taxxi yace yakaishi CIM bank,aikuwa hargaban bank din me taxxi din yakaishi biyanshi yayi sannan yawuce bank din yana duba agogon hannunshi 8:30am yawuce he hope that Uncle Almustapha yafito dukda kuwa yasan nan kam suna valueing time sosai bakamar mu Africans ba,shiga cikin bank din yayi yana kare ma gurin kallo bakidayanta, babban bank ne sosai kuma yahadu babu karya, Kai tsaye yayi ciki receptionist din yasamu bayan sun gaisa yake tambayar ta tasan wani Almustapha Sulaiman please…
Murmushi tadanyi sannan tace mai batasanshiba gaskiya,dan bubbuga hannunshi yashigayi tareda sa dayan yatsanshi abaki because he’s fully sure bank dinnan yagani ah jikin paper din,tunawa yayi da yaxo ma dashi don haka yayi saurin ciro envelope din yaciro paper din dake dauke da information din Uncle Almustapha sannan yamika mata yana nuna mata passport din jiki…
Karba tayi sannan takalla,dan sakan baki tayi sannan tace”oh,you mean this Man?”….
Cikin sauri Sulaiman yagyada mata kai,dan kallonshi tayi with questioning look na miyasa yake nemanshi sekuma taga suna matukar kama don haka tamaida makaman tambayoyinta”are you his son?”….
Gyada mata kai yayi sannan yace

” _please i need to see him,can you help me?_”….

Yar dariya tayi sannan tamika mai paper din

” _I’m sorry, actually he doesn’t work here anymore_”…

Dafe kai Sulaiman yayi cikeda damuwa yace” but,how could that be possible?”….
Kai tsaye tabashi amsa

” _He resigned since last year,I was his secretary_”……

Da Sulaiman haryayi losing hope amma jin tace “she was his secretary” seyaji dan relief,may be tasan wani abu gamedashi.cikeda hope yace…

” _Do you know his house please,I really need your help in this,as you can see we’ve been separated for years now and I want to meet him that was why i came all the way from my country”_ ….

Cikeda tausayawa tace

” _I’m sorry Young Man,I don’t know his current address but I know the name of the university his Daughter is studying in_”….

Cikin sauri Sulaiman yace”please tell me”
dauko pen cikin drawer tayi sannan tamika mishi karba yayi kafin tace *Bhayangkara University of Jakarta* ….
Rubutawa yayi sannan yace her name please?…
*Sumayya*,maimaita sunan yayi ahankali sannan yadan yi dariya jin yanda matar tayi pronouncing….
kallonta yayi sannan yace”thank you,but one last question please?”…
“Go ahead Young Man”, murmushi yayi sannan yace “do you know what she’s studying over there,I mean her department may be it could help”…..
Directly tacemishi *Industrial design*……
Godiya yayi mata sosai, cewa tayi “never mind just send my regards to them”,god’s willing yabata amsa kafin yatafi……

Wani taxxi din yatara sannan yace akaishi address din university din da Matar tafada mishi,sanda yashiga school din kallo yashiga karema makarantar, makaranta ce mekyau dukda kuwa shi kyaunta bata razanashiba tunda yaga wayanda suka fita ah komima,taku yashigayi kafin yasamu wasu students yamusu tambaya kan inane department na industriy design,kwatance sukayi mishi kafin yatafi wurin department din,tsayawa yayi yana karema gurin kallo tareda tunanin ta ina zaifara nemanta ma tukunnan,yana nan tsaye yahango wasu yanmata biyu sunfito daga department din, daya tayi dressing cikin doguwar riga yayinda tayi rolling gyale akanta sekuma dayar tana sanye da riga da wando jeans,jeans dinma tayi folding dinshi daga kasa kadan sekanta sanye yake da hula mekyau hannunta daukeda books, ahankali yakarasa gabansu tareda yimusu sallama tunda yaga dayan tayi kama da musulma dayar kuma se yayi stretening hannun shi yana mika mata alamun sugaisa sede da mamakinshi seyaji ta amsa sallamar kuma bata mika mishi hannunba, murmushi yayi tareda maida hannun nashi cikeda kunya sannan yace”please I want to ask you something, that’s if you don’t mind”…..
Yarinyar dake sanye da English wears dinne tace “go ahead”…..
Dan sosai Kai yayi sannan yace”please do you girls possibly know Sumayya Almustapha?”..
Zare idanu tayi sannan tace, are you looking for me?…..
Dariya kawartata tayi,dan duka takai mata yayinda Sulaiman yashiga sake kare mata kallo because yakasa yarda itace…..
Uhm,you said?,takuma tambayarshi…..
Cikin sauri yace,yes,yes kenake nema…..
Yar dariya tayi sannan tace danayi laifin me kuma yau takarashe maganar tanasa hannunta ah cheeks dinta alamar tana tunani,shiko cikin sauri jin tayi hausa yasake kallonta dukda kuwa shiyafara mata hausan batareda yamasan yayiba….
Composing kanshi yayi sannan yasa hannunshi cikin aljihun wandonshi yana dan murmushi,kinason sanin mekikayi?…..
Jijjiga mai kai tayi tana dan murkuda mai baki,ciro hannunshi yayi ah aljihun wandonshi sannan yasa akan bakin nata yadan murkuda shi,ihu take shirin saki yayi saurin sa hannunshi ah bakinta,be quiet now….
Ture hannunshi tayi tana haki”who the hell are you, I’ll call my father right away and he won’t spare you a promise”…
Dariya Sulaiman yayi sannan yace,Daddy’s favourite right?…..
Kawarta dake gefentane tashiga tsakaninsu,”Sumayya why are you always looking for trouble for goodness sake,kafin tace mata go ahead, I’ll apologise to him and follow you”….
Don duk ah tunanin kawar wani Sumayya ta tsokano don halinta kenan akullum neman tsokanan jamaa don taga ana shigar mata, kallon Sulaiman kawar tayi”I apologise to you on her behalf please”…..
Dariya Sulaiman yayi sannan yawuce kawar yakamo hannun Sumayyan yajuyo da’ita”so my little Sister is so stubborn like this?”…..
Turo baki tayi,don ita tarasa meyesa take biyemishi da bata cimishi mutunci har yanzuba………
Shiru tayi tana Kare ma fuskarshi kallo, ahankali tace”nasanka ne?”,tayi mishi tambayar cikin hausarta dabawai tazauna sosai bane….
Riko hannunta yayi sekuma taji takasa kwatan hannun,”kindai san Mai kama dani?”……
Tunani tashiga yi dawama yake kama,cikin sauri tace afili”My Dad”…..
Kafin ta kalli Sulaiman din,are you by any chance from Nigeria,inanufin Kai ‘Dan uwana ne?,gyada mata Kai yayi ai wani irin dalewa jikinshi tayi cikeda murna”are you really saying the truth?”…..
Shafa bayanta yashigayi ahankali”I’m telling the truth Sumayya, I’m your cousin Brother Sulaiman,nidan Uncle dinki Abdulrahman ne I know you must have heard about him from your Dad”…..
Kara kankameshi tayi cikeda jin dadi akullum burinta taga yan uwanta, yan uwan babannta and finally yau gata ga daya daga cikinsu…..
Sulaiman dinne yadan dago da fuskarta,take me home Sumayya I want to meet Uncle, jijjiga mishi Kai tayi tana goge yar kwallarta murna kawarta tayi mata sannan sukayi sallama….
Ah motarta suka tafi inda yace mata zebi ta hotel sister dinshi nacan……
You mean my cousin Sister?, gyada mata kai kawai yayi haka tadinga damunshi da tambayoyi duk akan yan gidansu harsuka Isa hotel din cewa yayi tajira shi amota yana zuwa,haka yashiga yasamu Afiya nakwance tana kallo da alama tamayi wanka abunta don cikin shirinta take…..
Gaishe shi tayi kamin yace mata tatashi zasuje wani gu,cikeda zumudi tatashi ta zari gyalen abayan daya sayamata ah kaduna tayafa daman ta gaji da zaman daki……..
Sanda suka isa jikin motar Sumayya, dasauri Sumayyan tafito daga motar tana murmushi,kallonta Afiya tashiga yi kafin tamaida kanta wurin Sulaiman din with questioning look..
Sumayya ne tadan bugi hannun Sulaiman din sannan tace “bazakayi introducing dinaba?”,kafin tasake maida kanta gun Afiya tareda mika mata hannu”I’m Sumayya budurwar Yayanki”,takarashe maganar tana kanne masa ido…
Sakan baki Sulaiman yayi,yar dariya tayi tana kallon Sulaiman din”Toya zanyi I know this must be what she’s thinking,Kuma kaki kamata bayani”…..
Slight hug takaima Afiyan, I’m glad to meet you little Sis, I’m Sumayya your cousin sister…..
Sulaiman ne yakarada little Angel kafin mutaho banacemiki we’re going to meet a family ba?..
Gyada masa kai tayi kafin yakarada “to family din Uncle Almustapha ne Yayan Abba, I mean Mai Martaba and she’s his Daughter”…
Hugging nata Afiya takuma yi sannan tace sunana Afiya I’m happy to meet you as well…..dukda kuwa bawai tasansu sosai bane tunda labarinsu kawai takeji sede taji dadin haduwa da Afiya din,haka suka dunguma suka tafi gidan su Sumayya din tunda suka shigo Unguwar zaka gane cewa unguwa ce tamasu kudi Sulaiman baitashi mamaki ba seda Sumayya tayi parking ah makeken mansion din…
Fita tayi sannan tace suma sufito,dagudu tayi cikin gidan kamar wata yar yarinya tana Kiran Mum,Dad where are you……
Kallo Sulaiman din yabita dashi yana”she’s unbelievable”……
Dariya Afiyan ma tayi,atarekuma suka bi bayan Sumayya sanda suka iso bakin makeken kofan already abude yake,katafaren parlour ne wanda ke dauke da furnitures masu kyau tundaga bakin kofar Sulaiman yake hango wani babban mutum zaune kan seater yayinda Sumayya din nazaune gefen shi da alaman tana fadamishi zuwansu ne sekuma can gefe wata mata Itama dabazata fi shekaru arba’in da biyarba yar kyakyawa da’ita tana shan fruits hankali kwance……

Story continues below

Tunda Sumayya takiran sunan tilon kanin nashi yaji wani irin feelings na taba zuciyarshi bama kaman sanda tace danshi yazo, ahankali yadaga kanshi yana kallon bakin kofar datake mishi pointing…..
Tashi yayi cikin sauri yayi gurinsu Sulaiman din idanunshi sun ciko da kwallah,ko shakka babu wa’yannan jinin Abdulrahman ne barinma Sulaiman dayake matukar kama dashi…..
Janyo Sulaiman da Afiyan yayi ah tare sannan yahada ah jikinshi yarungume”ashedai darabon zai sake ganin wani nasa,ashedai da rabon zai sake gamo da dan uwansa after so many years”…..
Dagowa yayi yana kallonsu sannan yace”Ina mahaifinku,babu shakka ku jinin Dan Uwana ne”…..
Murmushi Sulaiman yayi sannan yace mukadai mukazo Uncle, Sumayya dake gefenshine tadan harari Sulaiman din”Dad akecewa ba uncle ba”….
Dariya dukansu sukayi yayinda Uncle Almustapha din yakama hannun both Afiya da Sulaiman yakarasa dasu cikin parlour Mum din Sumayya dinne ta taresu da murmushi ah fuskarta………..
Yayinda Dad din yace”yau Allah yayi Hadiza Kinga ‘ya’ya na sunbiyoni har inda nike”..
Gaisar da Mum din sukayi se alokacin Sulaiman yaga ashe Sumayya kamar uwarta tadauko,Mum dinne tace sutashi su shiga suyi wanka se suci abinci….
Haka aka sa masu aiki suka tafi da Sulaiman din yayinda Sumayya takama hannun Afiya sukayi sama, murmushi uncle Almustapha yabisu dashi yanaji wani irin dadi aranshi…….
Seda suka ci abinci suka huta sannan Dad din yanemesu,tambayarsu yasakeyi ya hanya dakuma tambayar mutanen gida….
Nan Sulaiman yace duk lafiyansu kalau,kafin Dad din yace Abdulrahman yasamu address dina kenan?…..
Murmushi kawai Sulaiman yayi sannan yace tun tafiyarka yake nemanka Dad,for all this year babu ranar da Abba baya tunaka hakanan babu irin effort din dabaiyi wajen neman ka ba sede makiya sukan shiga tsakani su hana yin hakan,cikeda mamaki Dad din yace banganeba ….

Dan numfasawa Sulaiman yayi sannan yashiga bama Dad labarin abubuwan dasukai ta faruwa bayan tafiyar shi ah masarautar,daga wanda labari aka bashi harzuwa wanda yayi witnessing da idanunshi harzuwa yanzu daga karshe yace”Dad Masarautar mu yanzu ta lalace ba kaman yanda kasanta ah da ba, it’s surrounded by people who are so selfish,many things are going on over there that nikaina nakasa fahimtar komai besides i don’t want to be the crown prince,inason insama ma yan uwana yanci, Almustapha deserves to be the next king that’s if bakada ‘da namiji Uncle,duban Afiya Sulaiman yayi sannan yace yan uwana suna going through injustice amma banida halin taimakonsu,Uncle yan uwana acikin Masarautar nan ko bawa yafisu daraja nikuma nakasayin komai akai shiyasa nataso all the way from Nigeria nazo insameka sannan abu nakarshe inason Abba yahadu da Dan uwanshi daya dade yana burin haduwa dashi,I want to be the reason for his happiness don ina iya cemaka tun rabuwar Daddy da Kai dakuma Ummi yadaina walwala ah rayuwarsa daman ita tadawo masa da hope din sake ganinka bayan kunrabu……….
Daga karshe Sulaiman yayi folding hannunshi”don Allah Dad kataimaka mukoma gida,meet everyone and then we can work as a team sabida mugyara ahalinmu dama komai”…
Dad,Mum, Sumayya da Afiya duk sukayi shiru suna sauraren Sulaiman yana bayani har yakai karshe,Afiya da Sumayya kuwa kankame juna sukayi suna kuka,Dad kuwa da Sulaiman yakai karshe seyadan sa hannu tacikin eye glasses dinsa yagoge kwallarsa sannan yace “Son nikaina nayi mamakin rashin samuna da Abdulrahman baiyi ba sabida irin naci irin nashi inyasa abu agaba to seya cinma shi dukda kuwa inajin labarin komai dayake wakana ah gida daga kan mutuwar mahaifinmu,auren mahaifinka to Magajiya dama sake aure dayayi sede bansan meyake faruwa acikin gidan ba all I thought was that my brother is now happy and Kuma mutanensa ma suna farin ciki dashi don yana musu aiki mekyau da kwatanta adalci shiyasa nadaina bincike gamedasu da jimawa,wallahi bansan abu kamar haka yafaru ba da tun da jimawa nakoma gida don ceton dan uwana, amma tunda yanzu kafada min I’ll do whatever it takes to put things into places…..
Murmushi Sulaiman yayi tareda tashi ya rungume Uncle Almustapha din,thank you Uncle…
Shafa kanshi Uncle din yayi sannan yace kadaina min godiya, Sumayya dake gefe tana goge kwalla tace”didn’t I tell you to stop calling him uncle”….
Dariya Dad din yayi sannan yace “Sweetheart miyena bata rai Kuma,talk to him politely”….
Yar Turo baki tayi”Dad I’m jeolous of him Kanata embracing dinshi after all I’m the only one da ake pampering agidan nan amma yanzu naga kaman kafi sonshi”…..
Dariya duka sukayi yayinda Mum tace to Babana kashirya shan mita gurin Sumayya….
Kanne mata ido daya Sulaiman yayi sannan yadubi Mum din”inadaidai da ita ai Mum karki damu”…..
Bubbuga kafa tashigayi akasa yayinda Afiya tace”don’t mind them Sis I’m with you tashi mutafi ciki”….
Nan suka fice dariya Dad din yayi sannan yacema Sulaiman”she’s my only Daughter,itakadai Allah yabani kaga dole in shagwabata”….
Murmushi Sulaiman yayi”she’s so lovely Dad”…….
Dariya kawai uncle Almustaphan yayi sannan yace I’ll plan on when we’re leaving for Nigeria…..
Okay,cewar Sulaiman din yayinda yashiga yima Dad din massage akafa sunadan hira abunsu….

Story continues below

*****
Koda dare yayi Mallam Hudu bemanta da alkawarin dayama su Almustapha ba hargida yazo yaduba jikin Ummi din sannan yatara Almustapha da Amiran yace suzauna akwai maganar dazaiyi agaban Ummi din…
Shiru sukayi duka kafin yafara magana”naso ace Afiya nanan sede Allah baiyi ba najima ina rikeda nauyin nan akaina Allah bai bani ikon saukeshiba sabida mahaifiyarku batason kusani sede nagaji da ajiyeshi araina kuma ayanzu danaga rashin lafiyarta yaki ci yaki cinyewa naji inason fadamuku gashi nima tsufa yazo baasan sanda rai zaiyi halinsaba…
Amira ne tace kadaina irin maganar nan Mallam Hudu don Allah,dubanta yayi ahankali sannan yace Amira indaina zancen mutuwa kikeson cewa?…..
Gyada mishi Kai tayi ahankali, murmushi yayi sannan yace kona fada koban fada ba mutuwa tazama dole don tana kan kowa don haka kikwantar da hankalinki sannan muzamanto muna cikin shirin tarbarta akowani lokaci don bata sallama bare ankarar da mutum,inlokacin mutum yayi daukan ran kawai takeyi batareda tayi la akari da shekaru,hali,kudi kowani abu nakaba…
Almustapha da jikinshi yayi sanyi ya gyada Kai, Mallam Hudu ne yamika masa wata takarda sannan yace “hungo wannan rike kagani”….
Karba Almustaphan yayi yayinda Mallam Hudu yacigaba da magana”wannan bayanai ne aciki na duk wani kaya damuka saya dakuma wanda muka sayar ma mutane ah shagon ku,daga Almustapha har Amira dagowa sukayi suna kallon Mallam Hudu din don basu gane inda yadosa ba….
Murmushi yayi sannan yace”shagon dakaga ina kasuwanci aciki banawa bane Almustapha nakune kaida kannenka wanda mahaifiyarka ne tasani nabude mata shi da kudinta tun lokacin da tarabu da mahaifinku,alokacin duk wasu kadaranta aka sayar aka bude wannan shagon sannan cangin muka sayi fili wanda filin sanda tayi rashin lafiya ne nasayar dashi mukayi harkan asibitin ta dukda kuwa Sulaiman ma yaturomin kudi awancan lokacin batareda saninkuba sabida shiyabukaci hakan …

Dan numfasawa yakuma yi sannan yace abunda yasa banfada muku ba sabida irin tsanar da mutane sukayi muku ne nasan muddin akasan shagon ku ne ze durkushene cikin kankanin lokaci amma ah yanzu kam nafison infidda abun araina infada muku kusani Kuma tunda yanzu kunbar masarautar inaganin kunada right din sani din kilan kunason ku bukaci kudi mai yawa sabida samun cigaban rayuwa….

Tunda yake maganar Almustapha da Amira shiru sukayi suna mamaki don basu taba ganin mutum me amana irin Mallam Hudu ba Amira ne takasa hakuri tace lallai Mallam Hudu kafita daban cikin Al umma Allah yasaka makada alkhairi..
Mallam Hudu ya amsa sannan yace bazan taba iya cutan mahaifiyarkuba sabida irin halaccin datamin ah rayuwa bakowa zeyimakaba…
Nidai ga komai na shagon nan sannan akwai ATM aciki wanda nike tara muku duk ribar da aka samu aciki sannan pin din na ciki…
Murmushi Almustapha yayi sannan yamaida ma Mallam Hudu takardar yace”kacigaba da ajiyewa agurinka Mallam Hudu,Kai ubane garemu it should be with you”…
Maida mishi Mallam Hudu yakuyi yana baza ayi hakaba, Amira ne tace gaskiyarshine Mallam Hudu komun rikedin aiba iya cigaba da rike shagon zamuyiba tunda kasan yanda aka tsanemu kilan shagon ta durkushe inaganin kai kacigaba da tafiyar da al amarin inbadai takuraka zamuyiba…
Gyada Kai Mallam Hudu yayi sannan yace to amma ATM Kam ku ajiye agurinku don babu abunda zanyi dashi, murmushi sukayi sannan sukayi mishi godiya yajima yana musu bayanin komai kafin yatafi gida……
Amira ne tace inama Afiya nanan datayi mamakin wannan abun Al ajabin yau……
Almustapha dake gefenta ne yace shiyafita, Mallam Hudu kuwa tun fitar shi ah gidan sega international number takirashi cikeda mamaki yadauka ashe Sulaiman ne bayansun gaisane yake fada mishi yana tareda Afiya yayita neman number dinshi bayasamu……
Cikeda farin ciki Mallam Hudu yace zefadama su Almustapha din donkuwa hankalinsu kwata kwata ba akwanceba daman, juyawa yayi yakoma gidan ah bakin kofa suka hadu da Almustapha din nan yake labarta masa wani irin ajiyar zuciya yayi don daman yanzu ma yana niyan zuwa masarautar ne batun Afiya din…

****

Talatu ne tazo tasamu Magajiya kan bakonta yazo,kallonta Magajiya tayi sannan tace yana Ina?……
Kan Talatu ah kasa tace yana inda kukasaba haduwa,tashi Magajiya tayi sannan tace sutafi haka suka tafi bayan sun tabbatar babu wanda yasa musu ido sanda suka isa har kasa mutumin ya tsuguna yana mika gaisuwa,batareda Magajiya ta ansaba tace kayi aikin danasaka kane?…..
Eh Uwargijiyata yayi maganan cikin sauri,nayi bincike akan gidan su yarinyar yar gidan Alhaji Muhammad ne yanada mata biyu sannan dan kasuwa ne sosai kafin yakarada itada yar uwarta suke karatu acikin makarantar ABU sede kaman yar uwar tasamu matsala da ita Asma’u din sabida Asma’u taje gida tafadi abubuwan datakeyi…..
Yatsina fuska Magajiya tayi sannan tace me Yar uwar takeyi?…..
Nan mutumin yakwashe labarin komai yabata nan yace yanzu haka anamaganar ma kaman aurar da Yar uwar za ayi Kuma tanajin haushin Asma’u don gani take ita taja mata…..
Yar dariya Magajiya tayi sannan tace”anzo gurin,fadamin yarinyar tadaina ganin Almustapha dinne itada take pretending to be pious?”…
Dan sosa Kai mutumin yayi yana washare baki, Uwargijiyata inafa ae duk kanwar ja ce don ranar dare dare naganta jikinshi,ciro waya yayi ah aljihunshi yakai kan hotuna sannan yanunama Magajiya din yasake shiga video yanunamata,shekewa da dariya Magajiya tayi sannan tace “kayi aiki mekyau yau dole inyimaka kyauta me tsoka sede bakayimin abu dayaba”…..
Cikin sauri yace Uwargijiyata nasan menene zaki bukata Kuma nariga danayi miki shi kallonshi Magajiya tayi sannan yamika mata wata number,number din Asiya yar uwartata….
Murmushi Magajiya tayi sannan tace “ashedai kwakwalwarka naja”…..
Washare baki yashigayi yana”awurinki na koya Uwargijiyata”…..
Ganin number din tayi sannan tasake mika mishi”sauran aikin kai zaka karasa,nan tashiga yimishi bayanin yanda zaiyi”..
Daga karshe tace inafatan kagane?….

Gyada mata kai yayi  cikeda gamsuwa kafin tasa Talatu ta sallameshi nan suka juya cikin masarautar,suna cikin tafiya Magajiya tace”Talatu nayi tunanin mutum irin Almustapha mace bazata taba tafiya da imaninshiba,ashedai shima yanada feelings!ikon Allah kitsaya kiga yanda zanyi raga raga da rayuwarsu wannan kadai zaisa insamu kwanciyar hankali……
Talatu ne tace Uwargijiyata dukda sunbar masarautar bazakibarsuba,tsaki Magajiya tayi sannan tace inason inbatashi ah idon Mai Martaba ne tukunnan yanda koda ansamu akasi bazai taba koda iya kallonshiba….
Murmushi Talatu tayi sannan tace mezakiyi to,mekuma yasako yarinyarnan cikin al amarinki……
Dariya kawai Magajiya tayi tayi gaba tabar Talatu da jimami…..
***
Auren Asma’u da Asiya duka ansaka shi lokaci daya dana Yayansu Mubaraq,don haka bangaren Ummi da Mommy tuni suka fara shirye shirye abunsu,Asiya kuwa tana nan kullum ah kunshe ah daki tana kuka wai ita yanzu batason Aslam, Mommy kuwa cewa tayi ko mutuwa zakiyi se ankaiki gidan Aslam inma zaki dawo cikin hankalinki gwanda kidawo babu abunda za acanza …

Hajja ne kadai ke lallashin Asiya,tanabata hakuri don kuwa itamafa bata goyi bayan Asiyan nakin Aslam din da takeyiba…..Kafin tace”indai Asma’u na abunda idanunta suka gane mata to tabbas itan silent killer ce, ahankali tafita daga hoton sannan tashiga video din shima thesame thing ne da hoton sede wannan din video aka musu, murmushi takuma saki sannan tadaura yatsanta daya kan lips dinta tana tunanin taya zata nuna ma ‘yan gidan su abunnan”will they believe her?”,shine tambayar datayima kanta sabida tasan halinsu suna iya ganin abunnan suce editing akayi because they trust Asma’u so much,dan tsaki tayi kuma”she’s a bitch! atleast ni ah fili nakeyi banji tsoro ba amma itakuma ah boye,she’s busy pretending to be pious all this time Allah dai ya sauwaka to amma abu daya ne nasani tunda har tatonamin asiri to nima I’ll make her life miserable…………
Tana wannan tunanin ne seta rasa tawani hanya zatasamu tarama abunda Asma’u tayi mata sabida ita ba burinta tayi exposing dinta sabida tagyara halintaba aa sedan daukan revenge,yar dariya tayi sanda taji wani idea yafado mata lokaci daya, ahankali tafurta”Mukhtar”,yes “Mukhtar” I’ll send him the video and nasan for sure ze nuna ah gida wata zuciyar kuma tace mata “Amma dai bazaki tura masa ta number dinkiba ko,what will he think of you inkika tura abunda kanwarki takeyi”….
Dawannan tunanin tayi deciding sayan sabuwar Sim don aiwatar da abunda tayi niya sede inazata samu Sim din tunda ba bari ake tafita ah gidan ba kuma ko tace yayunta su suyo mata bazasu suyoba,idea ne yafado mata kan tabama mai gadi yasiyo mata dawannan tunanin tazari hijab da kudi ah hannunta tafita…..

****
Mukhtar! Mukhtar ! Mukhtar abokin nashi yakira sunanshi yafi sau uku amma bemasan yanayiba sabida irin duniyar tunanin daya shiga seda Sagir yakai hannu yatabashi sannan yayi saurin juyowa gareshi……
What,mekace Sagir?….
Jijjiga kai Sagir din yayi sannan yace”ikon Allah, Mukhtar wani irin tunani kakeyi haka kwanan nan se ayita yimaka magana bakaji”…..
Hmmmm shine kawai abunda Mukhtar din yafada kafin yatashi yana shirin tafiya,riko hannunshi Sagir yayi kafin yadawo dashi yazauna”inamaka magana zaka tafi,don Allah kafadamin matsalar ka meyake damunka kwana biyun nan?”….
Kallon abokin nashi Mukhtar yayi sannan yace”Asma’u ce Sagir,itakebani tough time dinnan bansan mena mata ba tunda akasaka bikinmu take behaving strangely, she no longer give me her time and attention”…..
Gyada Kai Sagir din yayi kafin yace”ka tambayeta ne, you should have asked her mekayimata”….
Wallahi na tambayeta yafi ah kirga Sagir kullum setace min babu abunda nayimata,nikuma senake ganin kaman bataso aka sa auren kwana kusa bane tunda bawai munjima da haduwa bane…..
kamo hannun Mukhtar Sagir yayi kafin yace”I don’t think wannan zaisa tacanza maka indai har tana sonka may be kawai stress din exams ne kabata time zuwa lokacinda za agama may be she’ll come back to her normal self”,don Sagir duk ah tunaninshi hakane tunda yasan Mukhtar dason sama ranshi damuwa akan abunda baikai yakawoba dakyar yayi convincing dinshi ya yarda da hakan ne kafin yace mishi”kadaina sama ranka irin abubuwan nan please it might affect your studies”..
Murmushi Mukhtar yayi sannan yace”thank you Sagir,zankiyaye in Sha Allah”….
Dahaka suka tashi suka fita….

****
Tunda tafita da mayafinta abakin gate tasamu Baba mai gadi nan tagaida shi tareda rokonshi tanason yasiyo mata sabon sim card ne babu gardama yakarbi kudi tareda tambayar ta wani layi sabida shima adan waye yake”MTN” tabashi amsa harzai tafi tace yauwa Baba Adamu layin yazamanto anyi registernta….
To ‘yata nan tajuya takoma gida bayan tacemishi inya dawo ya ajiye agurinshi kawai anjima zatazo takarba dakanta basai yashigo ciki ba…….
Bayan kaman awa daya taje takarbi sim din komawa daki tayi tareda sa key akofar dakin, murmushi tayi sannan ta ‘dale kan gado abunta,saka Sim din tayi ah wayarta kafin tasayi recharge card from her account through mobile banking,unisntalling WhatsApp dinta tayi kafin tasake installing wani tashiga yin register da sabuwar number din……
Batasamu wahalar ganin numbern Mukhtar ah whatsapp dinba don already number nakan phone dinta,nanfa tatura mishi hoto da video din tareda yin yar massage akasa…..

Story continues below

” _Assalamu alaikum Mukhtar inafatan kana lafiya,yakuma karatu da alamura, Allah yabamu sa’a baki daya.nasan kana da tambayoyi aranka nakan cewa ni wanene sede abinda nakeson kasani shine ni masoyinka ne mesonka da alkhairi shiyasa naturo maka wannan sakon sabida nasamu labari kan kana neman auren yarinyar nan Asma’u yar gidan Alhaji Muhammad,inason kasani cewa ba yarinya ce data dace da nagartaccen namiji irinka ba bata kuma dace dazama uwar yayankaba tunda dai ga abunda takeyi ah zahiri,basai kanemeni ba nina maka taimakone inkuma baka yarda daniba kana iyayin bincike dakanka_”

Takaranta massage din yafi sau uku kafin ta tura mishi dukda kuwa baya online amma yatafi, murmushi tayi sannan tacire simcard din tamaida nata because batason asamu matsala yace zeyi tracing haka WhatsApp dinma tamaida ainahin number dinta because the important thing is for him to get the massage tunda yatafi to ai shikenan sauran game din Kuma zatagani ah zahiri in Mukhtar yazo gida….
****
Tafiya takeyi cikin sauri daka ganta kasan ah tsorace take,tana tafiya tana dan juye juye sabida batasan kowa yaganta seda ta tabbatar babu mai ganinta sannan tashige gidan. makeken gidane acikin Masarautar wanda ina iyacewa yana daya daga cikin tsararrun gidaje dake cikin masarautar……..
Bayan tashiga ne tayi sallama awata kofa,matar dake cikin dakin ne dabana ganin fuskarta sabida yarinyar ta tareta tamata nuni data shigo da hannu……
Karasawa yarinyar tayi yayinda ta tsuguna har kasa tana mika gaisuwa”in wuni ranki shi dade?”….
Lafiya Lau Matar ta amsa ah yatsine kafin tace babu dai wanda yaganki ko?…..
Babu tabama Matar amsa, murmushi tayi sannan tace “Kinga tun ranar ban nemekiba ko seyau”….
Eh wallahi ranki shidade senayi tunanin kintsorata da abunda yafaru ne kika fasa cinma burinki,wani irin dariya Matar tayi kafin tace”haba Laure sede wata badai niba,babu abunda zaihana ni kawar da Magajiya ah doran kasan nan najima ina shirin yin haka Kuma yanzu ne lokacin da zan aiwatar da niyana(Niko dake bakin kofa inadaukan rahoto nadafe kirjina tareda fadin innalillahi wainna ilaihir rajiun, Laure,so Laure is behind all this,kafin ahankali nayi karfin halin lekawa Inga ko wacece Matar sede bani iya ganinta se shadow dinsu sabida dakin akwai duhu don haka nahakura nacigaba dajin zantukan dasukeyi)….
Laurene tace hakane Ranki shi dade nima inabayanki Kuma zangoya miki baya akoda yaushe tahanyar jiyo mana dukwani sirri nasu kuma zanyi iya kokarina gurin ganin ba akama muba har mu kai ga cinma burinmu……..
Dan shafa kanta Matar tayi kafin tace yauwa Laure nagode sosai kema tahakan ne zaki cinma naki burin nazama ta hannun damar Matar sarki….
Washare baki Laure tayi sannan tace,nagode Ranki shi dade nagaji da bautawa Magajiya da ‘ya’yanta kullum sede zagi da tsangwama sannan bata daukeni abakin komai ba kamar yanda tadauki Talatu,nima inason wannan matsayin…..
Indai wannan ne kinsamu Laure,yanzu yanda zamu hada next move dinne matsala banason asake samun matsala kamar nada kinga nafarkon Allah yataimakemu akayi tunanin wancan yarinyar Afiyace,nabiyun kuma da ankamani ah dalilin Talatun nan amma Allah yataimakeni nasan wata kofa shiyasa nabi tanan nafita…….
Gyada kai Laure tayi kafin tace hakane Ranki shidade in Sha Allah zamu kiyayena gaba…..
Cikin sauri Matar tashiga yimata bayanin abunda zatayi,gyada Kai tayi cikeda gamsuwa kafin Matar ta sallameta tatafi…….

****

*INDONESIA*

Zaune suke dukansu kan dinning table sunacin abinci banda Afiyya datake bin abinci daya bayan daya da kallo don ita gani take bazata iya cibama tarasa dalilin dayasa kullum different girki sukeyi gashi ita ah Nigerian ma bakomai tasamu takeciba bare ace wasu Indonesian foods nan,kallon Sulaiman tayi yawani dage seci yakeyi hankalinshi kwance yamutsa fuska tayi tana tunanin ina ya iya cin irin wannan abincin…
Sumayya ne data lurada abunda Afiyan keyi tashiga kwalama me musu abinci kira, ” *Kiara* come here”…
Cikin saurin wanda aka Kira da Kiara tazo tana…..”Yes Ma’am”….
Hararanta Sumayya tayi sannan tace”didn’t i ask you to go and learn about Nigerian recipes on net?”…
Cikeda tsoron kada ah koreta Kiara tace”you told me Ma’am”…..
Tsaki Sumayya tayi kafin tace then what’s all this?…..
I’m sorry Ma’am Kiara tashiga bada hakuri, get lost Sumayya tabata amsa kafin tadubi Dad sannan tace….
“Dad duk masu aikin nan nalura basu san aikinsuba akoresu kawai kaga Afiya cannot eat any of this”…..
Murmushi Sulaiman yayi yana kallon Sumayya din kafin yace “I  was the one that asked her not to cook any Nigerian food Sis,sabida inason Afiya takoyi ci,inbata koya yanzuba when is she going to learn what if wataran tazauna da irin su kowani abu yataso that she need to eat their food,besides tunda tazo batayi tasting abincinsu  kodayaba inalura daku ke kenema mata abunda zataci daga baya”……
Harara Sumayya takai mishi kafin tace, to ai batason cine dazataci,dariya kawai yayi kafin yatashi daga inda yake yakoma kujerar dake kusa dana Afiya din kafin yadauko bowl din *Nasi Goreng* dana *Ayam rica-rica* sannan yadauki plate yadubeta “Little Angel wanne zakici?”….
Yamutsa fuska tayi, murmushi yayi sannan yace”trust me Sis you will like them,da dadi fa sosai”…..
Allah Yaya Sulaiman, Afiya bta tambayeshi tana fuskar tausayi..
Gyada mata Kai yayi alamar eh kafin yace barina zubamiki wannan kamar shinkafa shinkafan yana da dadi sosai,gyadamai kai tayi kawai yayinda yazuba mata sannan yamika mata plate din”try one spoon sekin gode min”….
Badan ranta nasoba ta zari spoon din tadiba tana yamutsa fuska sannan takai baki take kuma se expression na fuskarta tacanza sabida dadin abinci, nan danan tashiga ci,dariya dukansu sukayi yayinda Sumayya ta tsaya tana kallon Sulaiman din aranta tafurta”he’s so caring”…..
Dad ne yace, Daughter kikara da *Gado Gado* sekince bazaki sake cin abincin Nigeria ba,dariya tayi tana cin fried rice dinnasu wanda suke kiranta da Nasi Goreng tace a’a Dad se dare kuma cikina yacika yanzu sosai takarashe maganar tana taba cikinta……
murmushi Mom da Dad din sukayi kafin Dad yace Sulaiman I’ve arranged everything ranar Thursday zamu tafi in sha Allah, Allah yakaimu cewar Sulaiman din yayinda Sumayya tace 6 days from now kenan, can’t wait namatsu inganni ah Nigeria….
Harara Sulaiman yamata cikeda wasa yace amma dai tundaga nan zaki sayi atamfofi ko don akasar mu ba abari ayi yawo da irin wayannan kayan……
Sakan baki tayi cikeda damuwa tace”dagaske?”…..
Eh kawai yace mata kafin yatashi yace zeje yayi freshen up sesutafi yawo………

Story continues below

****
Munira ne tashigo dakin tana Yaya Asma’u wai inji Yaya Aliyu kikai mishi ruwansha,harara ta doka mata sannan tace “can’t you see I’m studying,common ruwa dinma harsai kinzo kinfadamin instead of kikai mishi direct”…..
Sorry shine abunda Muniran tafada tareda fita daga dakin tana yamutsa fuska,tarasa meyake damun Yayarta kwana biyun nan she’s becoming rude abu kadan setafara ma mutum fada…..
Asma’u cigaba da karatunta tayi hankali kwance,wayarta dake gefenta ne tashiga kara dan tsaki tayi don duk ah tunaninta Mukhtar ne seda takai dubanta kan screen din sannan taga ashe bashi baneba kawartane Aisha,jiki ah sanyaye tadaga call din,daga daya bangaren Aisha tace”guess what Asma’u?”….
Sekin fada Aisha inajinki,cikeda damuwa jin muryar kawartata Aisha tace “Asma’u bakida lafiya ne?”….
“Kibari kawai Aisha bansan meyake damunaba nima”,tayi maganar kamar zata fashe da kuka Aishan ne tace daman zance miki ina Zaria ne nazo gidan Aunty suwaiba hutu…..
Cikeda jin dadi Asma’u tace dagaske,yaushe zakizo gida?….
Yar dariya Aisha tayi sannan tace”atleast i brightened your mood, probably inshigo gobe”….
Tabe baki Asma’u tayi kamar wanda tanagaban Aisha din kafin tace “ou ouuu gobe zanshiga school za ayi mana tutorials against exams na Monday”….
Kada kidamu Asma’u basai inzo Sunday ba duk dayane ai, a’a Aisha ba ayi hakaba kawai innataso ah school zanzo gidan Anty suwaiba din intayarda indauke ki muzo gida mukwana ……
To shikenan senaga zuwanki, Kuma kikwantar da hankalinki kidaina damuwa Kinga dai kina exams ne dukdama ina fushi dake baki fadamin aurenki ba sede inji abakin wasu….
Hakuri Asma’u tashiga bata tanacewa itafa babu wanda ma tafadawa so batasan ya akayi wanda sukafada matan suka saniba…..
Kekikasani dai cewar Aisha din kafin tace sekinzo goben kawai…..
Okay Asma’u tabata ansa tareda yimata sallama,ajiye wayar tayi jiki ah sanyaye”why is she not happy about the wedding tunda tanason Yaya Mukhtar,miyasa akoda yaushe tashiga duniyar tunani se Almustapha yafado mata rai,tanajin tausayin Mukhtar ba ason ranta takemishi wasu abubuwan ba she’s just following her heart without a reason,lumshe idanunta tayi kafin tafurta”Ya Allah gani gareka,help through and chose the best for me”……
Because tunda akasa ranar aurenta bata wasa da neman zabi gurin ubangiji sabida tasan bata da kamarshi…….
kasa cigaba da karatun ma tayi don haka tadibi takardunta tadorasu kan bedside drawer sannan takoma takwanta tuni bacci yayi awun gaba da’ita…..

****
Yau so late Mukhtar yadawo gida sabida yini yayi ah school,daman haka yakeyi duk lokacin exams sedare yake komawa gida tunda yashigo yajefar da jakanshi ah tsakiyar parlour tareda samun daya daga cikin seaters din dake parlour din yakwanta……
Ciro wayarshi yayi daga aljihunshi rabonshi dajin muryarta tun jiya dasafe don haka yashiga kiran layinta amma yayi ta ringing batadauka ba seda yakira sau uku duk bata dauka ba, lumshe idanunshi yayi ahankali kafin yakuma budusu sekuma yayi tunanin kunna data dinshi she might be online dukda kuwa 90% na zuciyarshi naraya mishi bata online din donkuwa Asma’u ba mutum bace meyawan chat……….
Bayan ya kunna data dinne massages suka shiga shigowa sede shi baya begen ganin kowani massage inba nata ba scrolling yashiga yi kozaiga nata amma bata turomai komaiba, inbox dinta yashiga tareda turamata sallama kafin yafita yana replying massages har ya iso kan wata sabuwar number budewa yayi inda yaga picture da video already sunfara downloading ma donkuwa wayarshi na automatic download,karanta massages din yashigayi yayinda zuciyarshi tashiga bugawa kasa karasa karantawan ma yayi don yafi damuwa yaga hoton budewa yayi yagani tabbas Asma’u ce dakuma Almustapha dan iskan yaron da kusan kowa yasanshi cikin ABU Zaria, innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda yashiga maimaitawa,he really can’t believe his eyes atake Kuma yaji kanshi nawani irin sarawa,Kiran number din yashigayi amma akashe yakira yafi akirga amma duka switch off ake cemishi…..
Yazaiyi yanzu,wazai tunkara dawannan maganar wata zuciyar Kuma tace babu kyau daga ganin abu kayanke hukunci yakamata ka tsawalla bincike besides Asma’u is a good girl Kuma gidansu gidan tarbiya ne dawannan tunanin ne yadanji zuciyarshi tarage zafi dukda kuwa inya tuno hoto seyaji kaman yafasa ihu, yanda Mukhtar yaga rana haka yaga dare don ko runtsawa beyiba daga karshe yayo alwala yazo yatada Sallah ko Allah zaisa yaji sauki ah zuciyarshi……….
Washegari dasafe kuwa ciwon kaine yadinga damunshi haryakejin kaman bazai iya shiga school ba sede kuma yana da important abunyi don haka yadaure yatashi yashirya cikin kananan kaya sannan yafita ….

Story continues below

****
Asiya kuwa tunda taturama Mukhtar sakon video da hoto ta WhatsApp ta tsiri zuwa side dinsu Asma’u don jin mezai faru amma haryau shiru,tsaki tayi tana addu’ar Allah yasa Mukhtar din yaga hoton……

***
Asma’u kuwa seda safe data tashi taga missed calls din Mukhtar sede tana sauri tashiga school wannan dalilin yahanata sake kiranshi………

Tun 8:00am akafara yimusu tutorials se 11:00am aka gama, itada Zahra suka fito suna yar hirarsu, Zahra ne tace nikam kinga ran Monday zamuyi exams na practical aspect din chemistry sede ban iya wanda akayi last day ba kinsan ranar banshigo school ba……
Murmushi Asma’u tayi sannan tace nikam nagane sosai basai muje mugwada ba ah lab tunda bamuda abunyi kinga nima befi inkara koyaba,thank you Asma’u,muje don Allah muyi dannaji ance yana fitowa ah exams sosai……
Ware idanu Asma’u tayi tana”Allah?”…
Kinga past questions ne?….
Aa banganiba Basma kefadamin cewar Zahra din haka suka rankaya zuwa college din sannan suka shiga lab din dasuke chemistry practicals….
Babu kowa aciki sewani dasuka hango daga can gefe yana karatu abunshi,kasancewar lokacin exams ne ba ayin lecture sede dalibai su shigo suyi karatu kuma lab bawai ancika zuwa karatu gurin baneba,Zahra ne tayi gaba kafin tashiga duba musu instrument din wanda zaiyi misu anfani gurin gudanar da experiment dinsu….

Kusa da saurayin tasamu abubuwan don haka seta zauna,karasowa Asma’u tayi sannan tace bazamuyima lab attendant maganaba?…..
Hararanta Zahra tayi”Kai Ma’u akwaiki da tsoro wallahi,babu abunda zaice mana ai munzo yin abu mai amfanine”….
Asma’u da tunda tashigo takejin gabanta na fadi tace,toshikenan semuyin ai haka suka shiga setting abubuwansu seda suka gama setawa sannan Asma’u tace to ai babu sample anan fa………
Nuni Zahra tayi mata da hannu inda aka ajiye samples din tashi tayi taje gurin suna jere acikin wani glass kowanne an ajiyeshi daban cikin conical flask,can ciki tahango wanda take nema din don haka tashiga kokarin ciroshi Zahra dake zaune tace wai Asmeey baki gani bane haryanzu?…..
Nagani ynzu zan dauko,karasawa gurin ta Zahra tayi sannan  cikin rada tace nikam fitsari nikeji wallahi nayi tunanin bazai matsamin ba har intafi gida amma yanzukam I can’t hold it anymore jinake kaman zai zubo,dariya Asma’u tayi sannan tace kije kidawo inajiranki ko in raka kine?……
Dagudu Zahra tafice tana aa nima yanzu zandawo fa mosque zani ba hostel ba…..
To sekin dawo Asma’un tabata ansa still tana kokarin ciro conical flask din seda ta ciroshi successfully harta juya zata tafi kafanta yabugu dawani kujera yayinda flask din yayi slipping ah hannunta yafadi ya fashe kafin ta ankara ta taka wani katon glass din conical flask daya fashedin wani irin Kara tasaki”wayyo Allah na” Almustapha dake gefe yana karatu yanajinsu tundazu sede yajuya musu bayane,yayi saurin juyowa jin Asma’u tayi ihu……
Babu shiri kafanta yafara bleeding dasauri yakaraso gurinta itakuwa se aikin kuka takeyi kallon kafar yayi haryanzu glass din najikinta sa hannu yayi yacire glass din tsabar zafi wani Karan takuma saki tsaki yayi tareda toshe kunnenshi,don yatsani hayaniya ah rayuwarshi,jin anyi tsaki ne yasata maida hankalinta kanshi tana shirin yin masifa ganin shine tayi saurin dauke kanta don bata manta abunda yafaru ranar ba,tashi tayi tafara tafiya nan tasake taka wata kwalbar wani karan tasake saki tana shirin taka wani kwalban ne yayi saurin janyota tadawo kusa dashi daukan seat yayi yazaunar da’ita kai sannan yace cikin kakkausar muryarshi”don’t move,I’m coming”……
Yanda yayi mata maganar da command taji haushi amma se zuciyarta takasa sabama abunda yace din tana nan zaune tana ta raki yafito daga office din lab attendant din  hannunshi rikeda first aid box wanda yabarmishi abude sanda zai fita saboda sunbasa……
Tsugunawa yayi gabanta bayan yabude box din….
yadauko spirit da cotton wool kafin yakamo kafar wani yar sukaji daga ita har shidin,shirin kwace kafar takeyi amma yaki saki nan yashiga yimata treatment tana kuka tsakaninta da Allah haryagama ma bata saniba don rimtse idanunta tayi,kallon fuskarta yayi tareda jijjiga kai aziciyarshi kuwa cewa yakeyi”Allah yasauwaka,wannan raki haka”…..
Jisukayi an rufe kofar da karfi daga ita harshidin attention dinsu yakoma gurin sede meshi yariga yatafi,ta window ne tahango Mukhtar yana tafiya da alama ranshi abace yake cikin sauri ta tashi zatabi bayanshi don tana da tabbacin tunda yatafi ba magana yaga Almustapha ne……
Cikin sauri yakuma rikota yamaida ta tazauna kafin yace”wait for your friend”,yana kaiwanan yajuya yatafi yabarta agurin kaman gunki daukan takardunshi yayi yafita bakin lab din yazauna aikuwa sega lab attendant din sallama yayi mishi yatafi……….
Tunda yafita yabarta takasa tashi ah gurin don gani take inta tashi kaman bata kyautamai ba,he cares shiyasa yace tazauna gashi tanason Kiran Mukhtar she don’t know what he must be thinking,batasan miyasa mutane ke judging Almustapha ba,tarasa dalilin dayasa suka kasa ganewa shi mutumin kirki ne,yanzu miye abun bacin rai anan don Mukhtar yaga yana taimakonta,tana cikin wannan tunanin ne Zahra tashigo tana mekikeyi agurin har yanzu?….
Nuna mata kafarta tayi da hannun dayasha bandage,cikin sauri Zahra tace subhanallah ya akayi haka?….
kekam tsautsayi cewar Asma’u din kafin tace come and help me kada infame ciwon……..
Cikeda damuwa Zahra tazo tadagata,tana wayamiki treating gurin?…

Murmushi Asma’u tayi sannan tace “Mr Taciturn”,dasauri Zahra tadago tadubeta wayeshi Kuma?….
Dan bugun kafadanta Asma’u tayi cikeda wayincewa”just someone”,kidaukomin bag dina acan mutafi i need to call Yaya Mukhtar……
Cikeda damuwa Zahra tace shikenan nibazan koyi abunnan ba?…..
Kiyi hakuri Zahra Monday din ai se 2:00pm zamushiga so zanshigo dawuri semuzo muyi Kinga da inason bin gidan Antyn Aisha ma amma yanzu bazai yuyu ba,toshikenan Allah yakaimu cewar Zahra din kafin tadaukoma Asma’u jakanta har mota tarakata sannan tatafi,Kiran Mukhtar Asma’u tashigayi amma yaki dagawa kwata kwata daga karshema kashe wayar yayi…..
*****
Mukhtar kuwa duk abunda yafaru yagani,zafin da kirjinshi keyi mishine yasashi kasa tsayuwa ah gurin yatafi abunshi,seda ya isa gida sannan tadinga kiranshi,tsaki yayi tareda wurgi da wayar”what is she going to tell me now that she’s calling,so take tacemin it was a mistake ne ko wasu karyayyaki zata hadamin”….
Innalilahi wainna ilaihir rajiun,shine abunda yake maimaitawa jin tadameshi da Kiran ne non stop yasashi kashe wayarma baki dayanta……Tirkashi!
Mekuke tunanin zai faru da Asma’u,shin  wani mataki Mukhtar zai dauka yanzu,sannan wanene ke son ganin bayan Magajiya?..

Jin yakashe wayar jiki ah sanyaye taja motarta zuwa gida da dingishi tashiga bangarensu Sadiq ne yafara ganinta cikin sauri yakaraso inda take kamin yakama hannunta  yana “Adda Asmeey ciwo kikaji?”….
Gyadamishi kai kawai tayi,garin yaya hakan tafaru cewar Ummi dake fitowa daga kitchen……
Nan Asma’u tabasu labari,sannu Ummi tashiga yi mata kafin tace you should be more careful next time kinji……
To tacewa Ummi kafin tace Sadiq kaimin jakana ciki,dauka yayi yatafi mata dashi…..
Haka ranar takwana tana tunanin yaushe Mukhtar ze bude wayanshi don takira shi times without number amma koyaushe takira kuma se acemata switchoff dakyar tasamu bacci yayi awun gaba da’ita…….

Tun cikin dare Mukhtar yasaka ma ranshi cewa yakamata ya rabu da Asma’u,he has to free himself from this relationship tunda ita ga wanda takeso da Sagir ma yazo mishi dasafe yatambayeshi meyafaru nan yafadamishi, shiru Sagir din yayi nadan dakiku kafin yace”I’m sorry Man,but tunda daman naso infada maka abunda yafaru da sister dinta sede alokacin banason inyi discouraging dinka daga neman aurenta and besides nayi laakari da kowa daban yake hakana
kowa da irin halinsa sabida zaka samu ah gida iyaye sunyima ‘ya’yansu tarbiya mekyau amma sekaga daya daga cikin ya’yan bayajin magana kuma bawai iyayen basuyi kokaribane akanshi aa kowa da irin nashi kaddarar dakuma halin shiyasa wallahi banfada maka ba nabar maganar araina…….
Murmushin dayafi kuka ciwo Mukhtar yayi kafin yace now”it’s over Sagir,da ace tanasona I won’t mind amma duka behaviors dinta yanuna clearly cewa basona takeyiba, it’s better i just free her from this relationship shine mafita kawai because ko anyi auren we might not be happy”, gyadamai kai Sagir yayi kafin yace Allah yasa hakan shiyafi alkhairi amma mezaka cema iyayenta?…..
Dafe kai Mukhtar yayi cikeda damuwa kafin yace”Nima shine bansaniba because banason nuna ma iyayenta abunda tayi sede wata zuciyar nacemin kuma innayi shiru nabarta kaman na cucesu ne gwanda sudauki mataki akanta”……….
Jijjiga Kai Sagir yayi kafin yace keep it to yourself kada kanuna musu,besides kaima bakasan waya tura makaba,with time indai dagaskene zasu sani,gyadama abokin nashi kai yayi tareda yimashi godiya kafin yatashi yashiga bandaki yin wanka because bayason yabata lokaci gurin zuwa ganin Daddy……..

Around 10:30am ya isa gidan tarba akayi mishi sosai kafin Sadiq yace bari yaje yayima Asma’u magana, jijjiga Kai Mukhtar yayi kafin yace kyaleta inason ganin Daddy tukunnan inna fito zamu hadu, murmushi kawai Sadiq din yayi don bedauka abakin komai ba sannan yace bari yaje yafada ma Daddy din dama Sunday ne weekend,ba ajimaba kuwa Daddyn yace ashigo da Mukhtar ahankali yakarasa cikin katafaren parlourn don bakaramin nauyin Daddyn yakejiba…..

Gaisawa sukayi kan Mukhtar din akasa, Daddy yatambayeshi ya exams yace masa alhamdulillah,nan kowa yayi shiru cikinsu babu mai magana don shikanshi Daddyn bejima da recieving shocking news of his life ba sannan daganin Mukhtar din seyakejin 90% na zuciyarshi naraya mishi abunda yakawo Mukhtar din kenan……….

Daddy ne yayi karfin halin cewa Mukhtar lafiya,akwai wata damuwa ne??…
Jiki ah sanyaye Mukhtar yace eh Daddy yayinda take idanunshi suka kada sukayi jazur,to Mukhtar fadamin mana inafatan dai lafiya?…..
Jijjiga kai Mukhtar yayi kafin yayi karfin halin cewa Daddy maganar auren mu da Asma’u ne yakawo ni, I’m sorry to say this ina inaganin afasa shi kawai sabida ko anyi ba lallai muji dadin zaman ba……
Murmushin dayafi kuka ciwo Daddy yayi kafin yace da akayi yaya, Asma’un ne tace maka tafasa?…..
Cikin sauri Mukhtar yajjijiga kai alamun a’a yayinda yakarada batafada min ba amma inaganin tanada wanda takesone bayan ni nikuma banason in tauye mata hakkinta,kafin yayi folding hannunshi alamar roko yace Daddy don Allah ku tuntunbe ta kuyimata abunda ranta keso kada tafada wani hali……
Gyada kai Daddyn yayi kafin yace,I regret the fact that you cannot be my son in law sabida kai yaro ne me hankali da sanin yakamata,ko gobe katashi neman aure indai ah gidan nan ne inkuma inada halin baka zanbaka Mukhtar Kuma inason kasani rabuwarku da Asma’u bawai yananufin kayanke zumunta damu bane please…….

Story continues below

To Daddy insha Allah, murmushi Daddyn yayi sannan yace bazan takuraka ba,may be your decision is the best sede inason kafada ma iyayenka tun wuri kada sunacan basu saniba,gyada Kai yayi sannan yace zanfada musu dayardar ubangiji nagode Daddy,nan yayima Daddy sallama yatashi yatafi batareda yanemi Asma’u dinba don Allah kadai yasan yanda yakeji ah yanzun…
….

Daddy kuwa tun fitan Mukhtar yadafe kanshi cikeda damuwa,yarasa meke damun ‘ya’yanshi mata,yayi musu tarbiya maikyau,yasosu iyaso amma abunda zasu sakamishi dashi kenan,isa daki yayi yadauki wayanshi yakira Ummi yace tazo itada Asma’u,kafin yakira su Mommy da Asiya dakuma yayunta…….
In no time suka hallara ah parlourn, Asma’u kuwa tunda Sadiq yazo yacemata Mukhtar yazo yashiga gurin Daddy hankalinta yatashi zuciyarta tashiga bugu …….

Kowa yayi shiru ah parlourn kamar babu mai rai ahankali Daddy yaciro wayarshi yamikama Ummi,jiki ah sanyaye Ummi tabi hoton da kallo wanda tun ranarda Asma’u tafada jikin Almustapha dakuma na jiya ah lab,sa hannu tayi ah bakinta tana kokarin rike kukanta maida ma Daddy wayar tayi kafin ta tashi tadauke Asma’u da wani irin wawan mari”Tarbiyar danayi miki kenan Asma’u?”……
Asma’u dake zaune batasan me Ummi tagani ba tace menayi Ummi,wani makan Ummi tasake kai mata tana innalillahi wainna ilaihir rajiun kukam wani irin yarane,miyene yashigeku iye,dan ubanki tambayana ma kikeyi Ummi takarashe maganar tana hawaye……..
Mommy ne tace haba Maryam miyena dukanta Kuma,ko dukanne zeyi solving problems don already Daddy yabama Mommy hoton takalla….
Cikeda takaici Ummi tace Anty Zainab bakiga metayibane fisabilillahi,inban duketaba mezan mata yarinya tana neman bata rayuwarta……
Daddy ne yayi gyaran murya tareda cewa ya Isa haka dukkanku kuzauna,dakyar Ummi tabar Asma’u kafin takoma tazauna zuciyarta na tafarfasa miko wayar ma Daddy Mubaraq yayi jikinshi yayi sanyi because yakasa yarda da abunda yagani…….

Gyaran murya Daddy yayi kafin yace”tunranar dana taraku kan maganar
Asiya danaji Asiya tayi maganar Asma’u da yaroncan hankalina yatashi don haka nasa jibril yayi min bincike akan abun batareda kowa yasaniba,and here it’s jiya da dare yakawomin hotunan nan nakan cewa yagansu tare sau biyu and dasafen nan Mukhtar yazo yace min yafasa auren Asma’u shi dukda yakifadamin directly abunda yasa ninasan wannan dalilin ne yasashi janyewa…….
Jiki ah sanyaye Daddy yace my girls are trying to ruin their lives I don’t know why,yanda yayi maganar zakasan cewa akwai bitterness sosai acikinta,kallon Asma’u yayi sannan yace I thought you’re more sensible than your sister ashe duk daya kuke, Asma’u mezakiyi da yaron can,yaron da bashida tarbiya yaron da ubanshima yakishi?….
Cikin kuka tace believe me Daddy there is nothing between us wallahi sharri akayimin, cikeda bacin rai Daddy yace I don’t care abunda nagani shizanyi anfani dashi ko anfada miki mudin mahaukatane”this’s not the first evidence Asma’u”……
Nunata da yatsa Daddy yayi,daga yau  babu ke babu zuwa makaranta kuma kishirya nanda sati biyu zanyi miki aure dakoma waye naga dama Itama Asiya zan tuntubi iyayen Aslam din inbasuda matsala da hakan zanhadaku duka ko hankalina yakwanta kafin yadubi Mubaraq yace”kamin siezing wayoyinsu kakawomin yanzunnan”,tashi Daddy yayi yafita yabarsu dukansu se kuka……
Karban wayoyin Mubaraq yayi kafin yakaima Daddy din yafice abunshi Mommy da Ummi ma fita sukayi haka Asiya,kuka takeyi kaman ranta zai fita yautashiga uku meyake shirin faruwa da’ita ne wai,jiki ah sanyaye tatashi tana dingishi takoma side dinsu tundaga bakin kofa Ummi tadinga janta kafin tashigar da’ita daki tashiga Kai mata duka,ihu Asma’u tadingayi amma babu mai taimakonta se kannen ta dake bakinn kofa suma suna kukan seda Ummi tadaketa son ranta kafin tafito tarufe dakin…….
Hararan Munir,ikram da Munira tayi dake tsaye bakin kofa suna kuka sannan tace”inbaku bacemin dagani ba senayi muku dukan tsiya Kuma”….
Jiki na bari suka koma parlour, Ummi kuwa daki takoma takwanta kanta nasarawa, Asma’u kuka takeyi harda shikewa gabadaya jikinta yayi rada rada,inazata saka kanta taji dadin rayuwarta gashi Daddy yakwace wayarta bare takira Mukhtar taji dalilinsa nayi mata haka don ita tsabar rikidama bataji bayanin Daddyn dakyau ba don duk ah tunaninta Mukhtar ne yanunama Daddy din………
 Bangaren Asiya kuwa tunda takoma bangarensu tashige dakinta tana hawaye don ita damuwarta Simcard dinta don tanada wani waya da Ahmad DJ yabata taboyeshi sabida kada agani ah gida ah tambayeta inatasamu,ah take kuma tatuna cewa ashe tacire Sim card dinnata dasafe tasa wanda Baba maigadi yasiyo mata don duba ko Mukhtar yaga massage dinta tunda tajishi shiru…..
Dan murmushi tayi atleast she’ll now get to chat with her friends babu boring life,tunowa da halin da kanwarta tashiga tayi setaji kuma she’s not happy da abunda tayi din,tsaki tayi afili tafurta”Asiya kindauki revenge amma miyasa bakyajin dadi harcikin ranki,miyasa bakyajin dadin ganin Asma’u acikin wannan halin”……
Tashi tayi cikeda damuwa tabude wardrobe dinta tadauko wayar tasaka simcard din sannan tajonata ah charging bayan tasa key akofar dakinta……
Komawa tayi takwanta tana tunanin abubuwan dasuka faru,she just want to be happy about it sede she couldn’t zuciyarta takasa aminta da hakan,dakyar tasamu ta kauda tunanin aranta…….


Story continues below

*****

Magajiya kuwa ana Masarauta anata shirye shiryen biki sabida yau sauran kwana shida auren ‘ya’yan nata dukda kuwa gabadaya tadamu da rashin dawowar Sulaiman din gashi Mai Martaba ma na complain tunda Sulaiman yatafi baikirashiba…..

Itadai addu’ar ta daya Allah yasa Sulaiman ba guduwa yayiba don kuwa daba karamin rusa mata plan yayi ba,layinshi na London kuwa kullum cikin kira takeyi amma amsar dayace kullum  akashe ……
Yanzuma tana zaune tanata gwada layinshine amma yaki shiga,gabadaya tadamu gashi tasan daga gobe Monday baki zasu fara hallara agidan kuma za afara tambayar inayake,Talatu ne tashigo cikin kuskus tacema Magajiya tayi bako,tsaki Magajiya tayi kafin tace inazuwa seda Talatun tafita sannan Magajiya tabi bayanta ah inda suka saba haduwa tasamesu,rai bace tace lafiya?……
Kai kasa yace kiyi hakuri Uwargijiyata Inna bata mikirai…..
Kai tsaye tacemishi me ake ciki da batun yarinyar?……

Nan yashigayimata bayani, Uwargijiyata naturamata amma inaganin itan batadau matakiba, Allah yataimakeni yaron da mahaifin yarinyar yasa yayi bincike akan Asma’u din seya sa anemo mishi wani yayi aikin donshi bazai iyabin ta makaranta kullum ba yanada abubuwan yi to wanda yasa yanemo mishi meyin aikin abokina ne shine yake fadamin don yasanni da neman kudi shine nace  mishi zanyi nanna gudanar dakomai nahada dawancan video da hoton farkon dana jiya natura masa shine yakai ma mahaifin yarinyar to yanzu dai bamusan matakin dazai daukaba se anshiga sati zankoma cikin makarantar in bincika, toshikenan kasan adireshin da Almustapha yakoma ko?…..
Gyada mata Kai yayi kafin tashiga yimishi bayanin aikin datakeso yayimata ….
Cikeda ladabi yace anyi angama ranki shi dade,sa Talatu tayi ta sallameshi kafin yatafi,duban Talatu tayi sannan tace Ina bayin da Yarima yayi anfani dasu?…..
Kan Talatu akasa tace sunanan Uwargijiyata akirasune?…..
Eh kice suzo su sameni yanzu,gyada mata kai sannan suka koma cikin masarautar ita Talatu tayi hanyar zuwa kiran bayin…..

Ba ajimaba segasu sunzo tareda Talatu din gaisuwa suka shiga yima Magajiya kafin tace kwanaki nace muku zakumin aiki ko,innatashi zan neme ku….. 
Atare sutayika amsa da eh Uwargijiyata …
Murmushi tayi sannan tace lokacin yayi to,gobe zaku gudanar min da aikina ah fadar yanke hukunci……
To uwargijiyaa sukayi maganar cikeda ladabi,bayani tashiga yimasu kafin daga karshe tace sutafi in aiki yayi kyau zasuji kyautarsu,jikina bari duwawu nazikiri suka fice ah dakin nata……

*****
Asma’u yini tayi tana sharbar kuka,yayinda lokaci daya wani irin ciwon kai yashigeta batayi sallar azahar ba bare laasar gashi har maghrib tagabato kai,duban agogo tayi nan taga biyar da rabi cikin sauri tatashi tashige bandaki tadauro alwala tazo tatada sallah tana sallah tana hawaye non stop seda ta rama sallolinta sannan takwanta kan darduman tana jiran akira sallar maghrib,ba ita tatashi daga kan sallaryar ba se washegari bayan tayi sallar asuba don akanta tayi bacci koda su Munira suka kawo mata abincin dare ma kinci tayi yananan ajiye inda suka barshi……..
Seda tagama azkar dinta sannan tatashi tafita ah dakin don shirya kannenta makaranta sede to her own surprise already Ummi nayi musu wanka,Ina kwana Ummi tagaida Ummin,ko kallon inda take Ummi batayiba sema daukan ikram datayi ah hannunta cikin towel tana goge mata jiki tafice ah bandakin Munir  da Munira kuwa harsunyi wanka suna kan shiryawa duban Munira Ummi tayi kafintace inkingama shiryawa kishafama auta mai kishiryata zandora muku abinci yanzunnan……

To Ummi cewar Munira din, Asma’u dake gefe hawaye nabin kuncinta tace Ummi zanyi musu girkin……
Ko kallonta batayi ba sema ficewa datayi ah dakin,zubewa kasa Asma’u tayi ah gurin don jitayi kafafunta bazasu iya daukartaba wani irin zafi takeji aranta,her very own Mother is angry with her,her very own Mother takasa yarda da’ita bayan tasan halinta,waye zeyi supporting dinta awannan al amarin,inama tanada number Almustaphan ko satan wayar Ummin zatayi takirashi kilan shidin inyazo yamusu bayanin babu komai ah tsakaninsu kilan suyarda…….
Tana cikin kukan ne Munira tazo tatsuguna gabanta tareda mika mata tissue…”Adda Asma’u kidaina kuka don Allah kanki zeyi ciwo”,dagowa tayi da idanunta dasukayi jage jage da hawaye tana kallon kannen nata dasuke tsugune gabanta wani sabon kukan ne taji yazo kuma,Munir ne yace”Adda Asma’u kece fa kikace mana duk bawan dayake cikin damuwa inya dogara ga Allah yacigaba da addu’a Allah zai kawomai sauki cikin lamuranshi”,wani tissue Munira taciro tashiga goge ma yayartata hawaye tana kina karanta addu’ar dakika koyamana”Allahumma rahamni birahmatika ya arhamar rahimin,you will surely get peace of mind”…….
Cikeda son su tajanyosu tarungume su,tana nagode kanne na Munira harda dan bubbuga bayan Asma’u wai ita tana lallashi……
Ummi ne tashigo tagansu cikin tsawa tace Munira abunda nasaka ki kenan?…..
Cikin sauri Muniran tatashi takama hannun ikram,harara Ummi takaima Asma’u din”kitashi kifitar min ah daki”……
Jikinta na rawa takaraso gurin Ummin,don Allah Ummi kiyi hakuri kiyarda dani babu abunda nayi wallahi sharri akayimani,tunkudeta Ummin tayi kafintace cikin bacin rai”nace kifitar min ah daki ko,koso kike inmiki najakin dana miki jiya”…..
Juyawa Asma’u tayi tafita tana hawaye,tsaki Ummi tayi takoma kitchen abunta……

Story continues below

****
Tunda Almustapha yafito ah masallacin sallar asuba yakejin kamar anabinshi ah baya,dukda haka baifasa daina tafiyarba don duk ah tunaninshi illusion nashine,yanacikin tafiyarne be ankaraba yaji an shaqo wuyanshi tareda shafamai abu ah hanci in no time yasulale yafadi batareda yasan meyake cikiba,daya daga cikin samarin ne yace kudaukeshi kusashi ah mota kafin wani yaganmu,cikin sauri suka dagashi suka sa ah mota suka tafi dashi……
*****
Mai Martaba nazaune akan kujerarsa na sarauta ah fadar yanke hukunci,gabadaya manya manyan fada sunzauna suna  jiran afara gabatar da matsaloli kamar yanda aka saba kullum,mutane da dama sunkawo matsalolinsu ana taimaka musu yayinda wanda za ayanke ma hukunci aka yanke musu har aka iso kan bayi daya daga cikinsu ne tafito tana kuka kamar ranta zai fita tace “Ranka yadade mundade muna wahala hakana mundade ana cutarmu acikin Masarautar nan batareda munkawo karaba sabida bamu da shaida sede yanzu munsamu shaidar dazata sa abi mana hakkin mu…..
Mai Martaba ne yace”rashin adalcin me akayi muku?”…
kanta akasa tana kuka tace wani ne yakebin bayi yanmata yanayimasu fyade wanda nima anyimini sede wajen wata uku dasuka wuce harzuwa yau abunna wakana…..
Sallallami yan gurin suka shiga yi,yayinda Mai Martaba yace”wayeshi,kuma shaidar me kuka samu?”……
Baiwar ne tadubi kattin dogaraye biyu tayi musu nuni dasu zo,cikin sauri suka juya can segasu sunzo dukansu sunriko Almustapha jikinshi ko riga babu dagashi se wando wurgar dashi sukayi ah kasa yayinda daya daga cikin dogarin yamikama Mai Martaba waya,kallon hoton Mai Martaba yayi zuciyarshi na wani irin bugu Almustapha ne kwance jikin wata baiwa,baiwar dake kawo karan ne tace Mai Martaba wannan shine ke keta mana hakkinmu dakuma mutunci mu duk wannan lokacin,hoton dakake gani da asuban nan aka dauka wanda har Magajiya tagani sannan idanunta sungane mata komai……
Jikin ah sanyaye Mai Martaba yamikama dogarin wayar Magajiya sannan yadubi Magajiya dake zaune gefen Mata  alamar yana neman karin bayani…….
Cikeda ladabi ta taso tana sake mika mishi gaisuwa kafin tace tabbas Mai Martaba abunda lantana tafada daidaine,sundade suna fuskantar irin wannan rashin adalcin acikin Masarautar nan sede tunda suke kawomin kara sainake ganin laifinsune kuma bazai wuce ah tsakaninsu su bayi sukeyin hakan ba,seyau da asuba sukazo suka same ni kan yaron nan yashigo yayi attacking Hindatu yanason keta mata hakkinta, kaman ma abuge yashigo shine naje nagane ma idanuna sannan nasa aka tafi dashi gidan yari sabida kar yagudu kafin azo kotu don yanke mishi hukunci…….
Jiki ah sanyaye Mai Martaba yacema Magajiya takoma tazauna yayinda yadubi Almustapha ranshi ah matukar bace ada yayi tunanin yaron is innocent sede ashe besani ba shidin mutumin banza ne,babu abunda Mai Martaban yatsana irin ah wulakanta ‘ya’ya mata,babu abunda yatsana irin namiji ya keta hakkin mace don aganinshi rashin imani ne da rashin tsoron Allah tunda kowane namiji ubane,yayane,mijine   Kuma,in akayima ‘ya’yansu zasuji dadi koko in akayima kannensu,yayunsu da matayensu zasuji dadi?….
Yasan bazasu taba jin dadi ba sannan they can even fight to get revenge for their loved once,they always protect them sabida su basuson ah wulakanta nasu amma su sukeyima ya’yan wasu dakuma kannen wasu batareda suntuna ranar haduwarsu da ubangijiba………
Lokaci daya Mai Martaba yaji yatsani yaron sabida tunda yahau karagar mulki ba ataba kawo mishi irin wannan kararba na zancen anyima bayi fyade ko anketa musu hakkinsu……
Shiru yayi nawajen mintuna biyar kafin yace akira mishi Sarkin yanke hukunci,dasauri yakaraso gaban Mai Martaba yana mika gaisuwa,batareda Mai Martaba ya ansaba yace “kaji laifin dayayi?”….yakarase maganar yana nuna Almustapha…
Eh ranka yadade,to kaje kayanke mishi hukunci dede da laifinshi yanda addini ya fada…..
Godiya Sarkin yanke hukunci yayi kafin yajuya yace ma dogarayen sudauki Almustapha subiyoshi…….

Haka aka karasa zaman fadan sannan aka tashi kowadai yau da maganar Almustapha yabar gurin ana Allah yawadarai da irin wannan hali nashi, murmushi Magajiya tayi da Sarkin yanke hukunci yazo yasameta yana cewa wani hukunci kikeso ayanke mishi Hajiya?……
Gyara zama tayi kan kujerarta kafin tace Ina tsohon gidan galadima daya kone ata can baya,dan shiru yayi yana tunani kafin yace”kina nufin gidan marigayi galadima?”…..
Gyada maikai tayi kafin tace nan zaka kaishi,amishi bulala dari sannan adaureshi acikin gidan abinci da ruwa saudaya za ana bashi ah rana har seyayi tsawon wata biyu agurin sannan kullum za anamishi bulala goma masu shiga jiki sannan abi jikinshi da gishiri,kada kamanta bulalan yau dari za ayi mishi…………
Cikeda gamsuwa Sarkin yanke hukunci yace toshikenan Hajiya amma dai shiwancan gidan anyi wurin shekara baa hukunta wani acikiba,don dama inmutum yayi laifi me tsauri yawanci nan ake kaishi ah daureshi,anayi mishin hukunci wanda wannan din tsarin Magajiya ne…
Harara ta zabga mishi ina ruwana,kayi abunda nasaka ka naceba…
Jiki na bari yace to uwargijiyata,nan yatashi yatafi bayan Talatu ta sallameshi,duban Magajiya tayi tace Uwargijiyata”wata biyu beyi yawaba?”…..
Tunkudeta Magajiya tayi kafin tace”kezaki fadamin abunda zanyi?”…..
Hakuri Talatu tashiga bata kai ah kasa, murmushin mugunta Magajiya tayi sannan tace”banama bazai rubuta jarabawan ba,ahaka zaikare bazai taba cinma burinshi ba”..
Talatu dakusan sati tana tunanin miyasa Magajiya tadamu da sa Almustapha cikin wani hali fiyeda bikin dake gabanta tayi saurin kallon Magajiya don seyanzu tagane dalilin uwardakin nata nayin hakan,dariya tayi sannan tace se yanzu nagane Uwargijiyata……
Tsaki Magajiya tayi”aikekam kwakwalwar kifi gareki wanda basu kaiki kusanci danibama sunfiki sanin abubuwan danikeso dawanda banaso”……
Kiyi hakuri zanna haddacewa nan gaba,tsaki Magajiya tayi yayinda wata baiwa tazo cikin sauri tace Uwargijiyata nazo inmiki albishir……
Inajinki Magajiya tayi maganar ah yatsine,”baki ne daga masarautar Daura Allah yayi musu isowa don halarta bikin Yarima da Gimbiya Hamida”……
Murmushi Magajiya tayi sannan tatashi tafita bayinta nabinta don zuwa tarban bakin,dede lokacin kuma laure tasamu tashiga dakin Magajiya hannunta daukeda wani katon kwarya da abu aciki kuma anrufeshi kamkam,seda ta duba taga babu kowa sannan tatura kwaryar karkashin gadon sannan tasince daurin da akayima marfin kwaryan tabarshi ah ajiye batareda ta budeba,fita tayi ah dakin cikin sanda….

Story continues below

******

Almustapha kuwa har wannan gidan suka kaishi akamishi bulala dari  duk kuwada radadin dayakeji ajikinshi besashi yin koda hawayeba,jikinshi duk ya faffashe sannan aka debo gishiri aka dunga shafa mishi,rumtse idanunsa yayi in pain don bakaramin zafi yakejiba kafin daga karshe suka samu jikin karfe suka daureshi,zama yayi ah kasa tareda jingina kanshi da karfen,lumshe idanunshi yayi yana tunanin Amira da Ummi yasan by now they must be worried about him ace tun sallar asuba baidawoba har laasar tayi……….
Besan me Magajiya kesoba,after ta koresunma bazata barsuba………

*****

Amira nazaune tana kallon hotuna ah wayar Aisha,tace nikam nadamu Yaya Almustapha tunsafe bedawoba…..
Murmushi Aisha tayi kafin tace kai Amira kincika damuwa da Yayankin nan he’s not a kid kilan yatsaya wani gurin ne…..
Dagowa Amiran tayi tadubeta kafin tace,bazaki ganeba Aisha…..
To nayi shiru Amira amma kikwantar da hankalinshi inada tabbacin zedawo cikin koshin lafiya, Allah yasa cewar Amira din isowa kan hoton Asma’u tayi takura ma hoton Ido tanason tuna inatasanta,cikin sauri kuma tace laaa wannan yarinyar tanada kirki ina kikasanta Aisha?…..
Amira tayi mata tambayar tana daga mata wayar, murmushi Aisha tayi kafin tace she’s  my bestfriend Asma’u,ke kinsanta ne?…..
Nasanta tanada kirki sosai ranar ita takaini gurin Yaya Almustapha acikin makarantarsu danaje ina nemanshi,ayya cewar Aisha din kafin tace nikingama inason zuwa gidansu gobe don tun ranar tace zatazo ta daukeni mutafi tare bataxo ba kuma nayita Kiran layinta akashe shiyasa gwanda inje Inga ko lafiya…..
Nima kuwa zanbiki don ranar bansamu nayi mata godiyaba,inason ta kawai senaji yarinyar takwantamin arai cewar Amira,to ai shikenan innatashi tafiya zanfada miki Amira……
Cikeda jin dadi Amira zata yawo tace in Yaya Almustapha yazo zan tambayeshi tunda bazai shiga school gobeba jarabawanshi se wani sati……
To shikenn,haka suka cigaba da hirarsu can sukaji ana sallama jin Mallam Hudu ne yasa Amira ansawa tareda yi mashi iso……
Yanda taganshi ta tabbatar ba lafiya ba bayan sun gaisane yace yajikin Ummi?…..
Dasauki Mallam Hudu amma lafiya naganka wani iri haka?…..
Cire hular kanshi yayi yana share gumin kanshi sannan cikeda damuwa yace ba lafiya ba Amira,ankama Almustapha yanacan gidan horo…
Zabura Amira tayi wanda yasa Aisha tsorata,dafe kirji tayi”Gidan horo kuma Mallam Hudu,me Yaya Almustapha yayi musu kuma”…
Cikeda damuwa Mallam Hudu yace kinsan halinta makirci kam tariga tahada mishi shikuma bazaiyi magana ba,kuka Amira tashigayi tana tashiga uku ita yazatayi, Mallam Hudu da Aisha ne suka shiga rarrashinta nan yafada mata abunda yafaru,amma yadinga bata hakuri kan zekira Sulaiman yafada mishi shikadai ne zai iya yin wani abu akai tunda shikanshi Mallam Hudu ba abakin komai yakeba ah masarautar bare ya iyayin komai….
Daga baya yatafi yabarta da Aisha, Aisha harda kukan tausayi dukda kuwa tana mamakin wannan wace irin matace,wani irin makirci ne wannan din,daman su Amira makotan su Aunty suwaiba ne yayar Aisha,tunda tazo hutu suka sabada Amira shiyasa kullum take shigowa da yanma ta tayata hira don Anty suwaiba bawai tasan wanenesuba kawai dai makotaka batasan asalinsuba,ranar cewa Anty suwaiba tayi zata kwana gurin Amira don batada lafiya hakana Umminsu ma Anty suwaiba sanin condition din Ummi din tace bakomai takwanan……….
Haka suka kwana hankali tashe don ko runtsawa Amira batayiba daga karshene ita Aishan bacci barawo yayi awun gaba da ita dukda kuwa tana mamakin yanda ace Amira na cikin irin wannan halin amma batayi koda sallar dareba bare ta nemi mafita gurin ubangijinta………
Washegari ita tayi musu breakfast yayinda Amira nazaune se hawaye, dakyar ta rarrrasheta taci abincin safe sannan suka bama Ummin ma,se wuraren shabiyu tace zataje gida tayi wanka tatafi gidansu Asma’u…..
Murmushin dayafi kuka ciwo Amira tayi kafin tace nikam kinga Allah beyi zuwanaba,kigaidamin ita don Allah…….
Cikeda tausayawa Aisha tace zataji sannan tace kema kikwantar da hankalinki tunda Mallam Hudu yace zekira dayan Yayan naku in Sha Allah za asamu mafita…..
Kallon Aisha Amira tayi kamar wata zararra kamin tace nagode,sallama Aisha tayi mata tatafi gida don shiryawa se wurin karfe biyu kafin tatafi gidansu Asma’u din…..
Sanda tashiga suka gaisa da Ummi normal Ummi ta amsa mata harda tambayarta ya Antynta tace lafiyarta kalau…..
Nan tace Ummi Asma’u nanan,eh kawai Ummi tace mata kafin tace kishiga daki tanaciki….
Jiki ah sanyaye Aisha tatashi tashiga dakin hade dayin sallama, Asma’u dake kwance kan gado tajuyama kofar baya ta amsa mata sallamar tana dan goge kwallarta….

Aisha ne takaraso tana Asma’u miye duniya haka alkawari yace fisabilillah,kasa karasawa tayi sakamakon ganin fuskar Asma’un datayi duk idanunta sun kumbura alamun tasha kuka harta godema Allah……..
Subhanallahi shine abunda Aisha tafada kafin takarasa jikin gadon cikin sauri, Asma’u! Asma’u what’s wrong with you,miyasa kike kuka takarashe maganar muryarta ah karye don ta tsorata da ganin kawartata duk tarame kamar ba itaba…….
Goge kwallah Asma’u tashigayi tana faking smile, Aisha yanzu kikazo tayi mata tambayar cikin dashashiyar muryarta…….
Kamo hannunta Aisha tayi”are you trying to hide you pain from me komi kikeson nunamin Asma’u?”….
Cikin sauri Asma’u tadaura hannunta kan bakin Aishan tana jijjiga mata kai kafin tafada jikinta tana kuka me tsuma zuciya…..
Babu wanda yakeson ya yarda dani Aisha, everyone hates me now even my family……
Cikin sauri Aisha tace wani irin magana kikeyine how can your family hate you Asma’u,don Allah kibar wannan maganar kanada wanda yafi danginka ne, they’ll never do that Ma’u kafin Aisha tariko hannunta tace kidaina kuka kifadamin mekedamunki only then i can help you….
Dakyar Asma’u ta iya tsaida kuka,tayarda da Aisha sosai fiyeda yanda mai karatu zaiyi zato tare suka taso and they always share their problems shiyasa takeji zata iya fadamata komaima, ahankali tashiga bata labari tun farkon haduwarta da Almustapha dakuma yanda Mukhtar yanuna yanasonta dakuma feelings datakeji dakomai harzuwa hukuncin da Daddy ya yanke akanta dakuma fushin da Ummi takeyi yanzu dama kowa na gidan except her little siblings wanda suma basusan meyafaruba………
Cikeda tausayawa Aisha tace”What a test! you’re going through Besty”,sa hannu tayi tagoge nata kwallar kafin tace,you never realize that you’re in love Asma’u,baki taba ganewa son Almustapha kikeba kosau daya?……
Jijjiga mata kai Asma’u tashigayi,basonshi nikeyiba tausayinshi nikeji, murmushi Aisha tayi sannan tace what if nace miki Almustapha anakan horonshi yanzu,what if nacemiki yanacan yanasha wahala hannun makirai mezakiyi?…….
Cikin sauri Asma’u tace”mekike nufi ah Ina kika sanshi?”…..
Neighbors dinmune ah gidan Anty suwaiba kanwarshi Amira munsaba har cemin tayi tasanki she wanted to come unfortunately due to abunda yafaru da Almustapha din batazoba …
Cikin sauri Asma’u tace meyafaru dashi please?……
Kallon yanda Asma’u tadamu yasata cewa miyena damuwar keda bason shi kikeba,don Allah kiyi hakuri kifadamin Aisha yanda take rokonta ne yasa jikin Aisha yin sanyi hartayi regretting dauko maganar kafin tashiga bata labarin yanda Mallam Hudu yazo yana fada,sa hannu abaki Asma’u tayi tana kuka me tsuma zuciya….
“What must he be going through over there Aisha?”..
People are so heartless wallahi…….

Asiya dake bakin kofa tanajinsu duk maganar dasukeyi taji idanunta sunciko da kwallah,itakam da akasamata aure bata shiga damuwar da Asma’u tashiga yanzuba,ashema duk abubuwan dasuka farun coincidence ne,jiki ah sanyaye takaraso cikin dakin  tazauna gefen Asma’u……..
Kallonta Aisha tayi batareda tace komaiba don tasan halin Asiya tun suna yara bawai tanason Asma’u kaman yanda ita Asma’un kesontabane ba……

Cikin kuka Asma’u tariko hannun Asiyaa tace kinji abunda Aisha tace Aseeey,how could people be so heartless like this,Mr Ta…citur..n they want to kill him tayi maganar tana shikewa, Asiya dawannan Karan takasa holding tears dinta tajanyo Asma’u zuwa jikinta tace”tayaya zakice bason bawan Allahnan kikeba,we agreed it was merely a coincidence duk abunda yafaru but no matter what there is something between you two”…….
Rungume Asma’un takumayi kafin tace”it’s all my fault, I’m so selfish, I’m so stupid,bansan darajar yan uwantakaba,bansan darajar masu sona ba shiyasa nayi abunda nayi kiyi hakuri Asma’u nice silar bakin cikin ki don daban turama Yaya Mukhtar video din da aka turomin ba dabazai taba fasa aurenkiba har akai ga wannan gandun, I’m really sorry Sis kiyafemin don Allah tun ranarnan dana ga hukuncin da Daddy yadauka akanki hankalina yakasa kwanciya,nasan ni mutum ne meson kaina dayawa sede believe me bantaba jin dadin ganin wani dan uwana na jini cikin damuwa naji dadi ba, I’m really sorry”……
Kara rungumeta Asma’u tayi don ita ah yanzu bawannan bane damuwarta,damuwarta halin da Almustapha ke ciki………
Tapping bayanta Asiya tadingayi cikeda tausayawa seda ta tabbatar tadaina kukan sannan tace Asma’u dago kiji…….
Dagowa tayi tana kallon Asiya din ahankali Asiya tafara magana”Asmeey i don’t know what exactly is the truth about this guy tunda nidai ah iya sanina Almustapha ba mutumin kirki bane tunda kowa yasan da hakan sannan directly bazan musakiba ince Almustapha ba mutumin kirki baneba saboda yawanci ah *GIDAN SARAUTA* akwai sarkakkiyar al amari da bakowa yasan dashiba,ah *GIDAN SARAUTA* naka ma yana iya cutarka ya juya maka baya,ah gidan sarauta Ma’u wanda baka taba tunanin ze cucekaba shizai cuceka and do you know why they are doing all this?……
Jijjiga kai Asma’u tayi alamar aa batasaniba,riko habarta Asiya tayi sannan tace dukansu they’re fighting for the throne,wani kuma damuwarsa ya zamanto shine ah kusa da mai throne din,wata Kuma damuwarta ta auri me throne din,haka zalika wasu burinsu su sa bakin ciki ah rayuwar masu kusanci damai karagar mulkin tunda su basu samuba,gaskiya ah iya sanina dakuma yanda nakaranta littatafai dakuma yanda nike kallon films na sarauta This’s what always happens Asma’u,dan numfasawa tayi sannan tace so,in the case of your Almustapha I can’t say anything about him besides there is no smoke without fire shine abunda nayi believing shiyasa iya shawarar dazan baki ah matsayina na Yayarki shine kicire Almustapha aranki besides he does not reciprocate for your love Asma’u kodama yana sonki kina sonshi rayuwarku tare abune me kamar wuya sabida kinsan Daddy bazai taba yarda ba na daya,na biyu mutanen gari da wani ido zaki kallesu,na uku bakya tunanin future din ‘ya’yanki?….
What will people say,wahala zaki sakasu ciki because he’s the illigitimate Son which means your children will be humiliated bazasu taba jindadin hulda da jama’a ba kada ma mukai ga wannan maganar yanzu Daddy ranshi ah bace yake damu kamata yayi munemi hanyar faranta mishi,and the only way to make him forgive us shine muyi abunda yasakamu muyi………
Shiyasa ni aganina yanzu kiyi hakuri kikwantar da hankalinki may be Daddy yafasa aura miki wanda yayi niyarma,tunda Asiya take magana takure mata idanu,so Asiya have some sense,so Asiya can talk like a sensible person tabbas taji dadin canjin datagani ah tattareda Yayar tata sede she don’t think shawararta ko daya tayi tasiri ah zuciyar ta, Aisha dake gefene tace Asiya maganarki gaskiyar ne nima shawarar danaso bata kenan and kicigaba da addu’a, Allah yazaba muku abunda yafi alkhairi shine kawai,don Allah kikwantar da hankalinki Almustapha kuwa abu daya zakimishi “pray for him and not crying”…..
Gyada musu kai kawai tayi yayinda suka cigaba da bata shawarwari daga karshe sukayi forcing nata taci abinci bawai don tanada appetite ba…….
Aisha se yanma lilis tabar gidansu Asma’u takoma gida daniyar inta huta seta shiga gidansu Amira din…..

****
Tunda Mallam Hudu yakirashi yafada mishi halin da ‘Dan uwanshi yake ciki bakaramin tashin hankali yashiga ba nan yafadama Dad, Dad din yashiga tashin hankali sosai kafin yadubeshi that means yakamata mutafi before Thursday cewar Dad din, Sulaiman ne yace no Dad indai bakagama shirin tafiyaba i can go inyaso kusai kutaho ranar Thursday din……
Dad ne yace gobe Wednesday right,why not mutafi goben gabadaya girgiza kai Sulaiman yayi kafin yace Yaya Almustapha needs me now bansan me Amira take cikiba she must be worried  zanbi commercial flight dayanman nan inyaso ku sai kutaho ta private plane din Abba sabida Afiya……..
Dafashi Dad yayi kafin yace bazan hanaka ba, Allah yakaika lafiya muma gobe zamuhau hanya in sha Allah……
Gyadama Daddyn Kai yayi jiki ba karfi kafin yatashi yatafi dakinshi cikeda damuwa,he can go to any length in order to save his Brother,so Mamanshi tayi using abunda shi yakeyi against his Brother innalillahi wainna ilaihir rajiun,betaba regretting yin zina ba sai yau….
lumshe idanunshi yayi jiyayi anyi knocking kofar dakinshi,cikin kakkausar muryarsa yace “come in”, Sumayya da Afiya ne suka shigo……
Afiya ne tace nikam zanbika Yaya Sulaiman please,sauke idanunsa yayi akanta kafin yace kiyi hakuri gobe kuma zaku taho I’ve to go there and handle things kafin ku iso,trust me Sis…
Goge yar kwallarta tayi kafin tace nayarda dakai dari bisa dari Yaya Sulaiman,Sumayya ne tace “nika tafi ma daman ka takuramin dayawa,hardawani cewa wai ba ashiga Nigeria da English wears”…..
Murmushi yayi yana kallon yanda take magana kafin yace”oh haka ma kikace,I know you’ll be the first one to miss me”…..
Harara takai mai kafin ta tashi ninama fasa taya Yayanki shirya kayan nashi yabata min rai,dariya Afiya tayi kafin tace nidai baruwana dakankima zaki dawo……
Fita tayi tana bubbuga kafa,binta yayi da kallo yana murmushi…..
Kafin Afiya tashiga hada mishi kayanshi,har airport suka rakashi seda jirginsu yatashi sannan suka dawo gida suma don karasa nasu shirin zuwa Nigeria washegari…..
*****
Magajiya na zaune acikin bahon wankanta tana dan shan dumi kafin bayinta suzo su yi mata massage,bandaki ne babba wanda yake daukeda swimming pool dede gwargwado wanda Magajiyan ke wanka cikinta sewani lum lumshe idanu takeyi hankali kwance kaman ance tabude idanunta tayi arba da wata katuwar maciji daga can gefe tanata jujjuya kai,take jikin Magajiya yashiga bari kafin tasaki wani irin ihu batama san sanda tafito acikin swimming pool dinba tana ihun maciji!maciji bayinta dake daki suna hada turarrukan da ake mata wanka dashi suka shigo bandakin aguje dalewa jikin Hindatu Magajiya tayi tana ihu harda hawaye”wallahi maciji tashiga nuna musu da hannu”……
 Karasawa daya daga cikinsu tayi cikeda tsoro amma itabataga komaiba,hango wata baiwar sukayi cikin bandakin tana haki cikin sauri suka karasa gurinta suna lafiya….
Cikeda rudani tace nashiga na dauko kasko acikin wancan dakin nafito kenan nahango maciji yanashirin kai ma Uwargijiya hari shine nayi kokarin jefa mishi kasko kawai senaga ya bace……
Magajiya dake jikin Hindatu daga ita sedan karamin rigar wanka ajikinta tace nidai ince naga maciji sannan cikin rudani tashiga kalle kallen gefenta tareda taba jikinta don ji takeyi kaman macijin ze bullo ajikinta tunda ance bacewa yayi,mehakan ke nufi?…..
Macijin daga inayake tayi maganar cikeda rudani,bayin kuwa ganin yanda Magajiya ta rude sunason yin dariya amma babu halinyi don suma sunsan sauran……
Hindatu ne tayi karfin halin cewa Uwargijiyata mukoma daki inyaso se akira azo ah duba ko Ina,cikeda tsoro Magajiya tace hakan za ayi nan suka fice tanemi kaya tasaka kafin akaje aka kira dogaraye,zuwa sukayi suka duba koina amma basu ga komai ba….
Cikeda tashin hankali da al ajabi tasamu gefen gado tazauna Allah yataimaketa babu baki ah dakin, Talatu ne takaraso kusa da ita tana Uwargijiyata kinfasa yin wankan ne?…
Wani irin harara takaima Talatun kafin tace wankan yaci ubanshi dan uwarki,Kai ah kasa Talatu tashiga bada hakuri Magajiya ko kallon inda take batayiba ita tunanin ta daya waye zaikawo mata macijin cikin daki don takowani fanni na daki babu tainda maciji ze iya shigowa, tabbas wani ne yashigo dashi,to wanene shine tunaninta tunda wanda take zargin ma baswa cikin masarautar tariga da ta koresu,cikin sauri tazabura ta tsaya zuciyarta nawani irin bugawa”badai wani na shirin illata ta bane acikin masarautar?”………
Talatu ne tace waye zeyi miki haka Uwargijiyata?….
Bansaniba Talatu, Talatu ne takuma cewa nagadai baki da makiyane,cikeda bacin rai Magajiya ta nuna kanta kafin tace ina Matar sarki zakice banida makiya tsabar kwakwalwar taki yanzu juyewa tayi komi?……
Yi hakuri Uwargijiyata cewar Talatu kafin tafice tabar dakin don talura ran Magajiyan ah bace yake sosai……..

Story continues below

****

Tunda ta idar da sallar isha’i takwanta kan sallayar tana juye juye hartasamu bacci yadauketa sede abun mamaki mafarkin Almustapha tayi ansaka shi cikin wani kogo anata bugunshi yana ihu asking for help gashi kogon duhu ne dashi baka iya ganin komai,ah zabure tatashi tana furta innalillahi wainna ilaihir rajiun taba fuskarta tayi taji wani irin gumi na keto mata gabadaya jikinta yajike da gumi,dakyar ta iya tashi ta kunna wutan dakin agogon jikin bango takalla karfe uku da mintuna shida bandaki tashige tadauro alwala tadawo ta tada sallah tana kai ma Allah kukan ta har lokacin sallar asubahi tayi seda tayi sallar asuba sannan ta nade sallayar komawa bakin gado tayi tazauna tana tuno mafarkin datayi, what if it’s true,what if mafarkinta gaskiya ne,what if Almustapha nashan wahala kamar yanda tagani jin hawaye tayi sunabin kuncinta she need to save him tunda babu mai taimakonshi,she need to protect him and take him far away from them may be yasamu sauki acikin al amurarshi wata zuciyar ne tace tayaya Asma’u,tayaya zaki taimakeshi bayan bakimasan inasuka kaishiba yayinda afili tafurta”why am i even afraid to lose you when you’re not even mine Mr Taciturn?”,wata zuciyar ne kuma tadinga cemata because you’re in love Asma’u, because kinason shi and duk wanda kakeso bazaka tabason ganinshi cikin damuwaba dawannan tunanin ne zuciyar ta tadinga ingizata ga tadau mataki duban wall clock din tayi still karfe biyar da minti sha biyar,tashi tayi taleka window still gari da duhu kuma daman su Daddy insun fita masallaci baswa dawowa se gari ya waye in rana tadan fara fitowa bude kofan dakinta tayi bayan tadauki kudi acikin drawer dinta cikin sanda tafita har parlour duk wuta ah kashe kuma babu motsin kowa don daman Ummi keda girki probably tana bangaren Daddy,koda ta isa bakin gate din Allah yataimaketa Baba mai gadi bedawo daga masallaciba don haka tafice daga gidan tafiya tadungayi cikin sauri seda tayima unguwarsu nisa sannan ta tsaya tana dube dube ko Allah zaisa tasamu abun hawa dukda kuwa tasan bawai ancika samu bane ah irin wannan lokacin cigaba da tafiya tayi can Allah yataimaketa tasamu, tsayar dashi tayi sannan tafada masa unguwarsu Anty suwaiba har kofar gidan tayi mishi kwatance yakaita bashi kudi tayi yatafi bata tunanin zata iya zuwa gidansu Aisha ah yanzu tunda tace mata gidansu Amira   nagefen nasu ta hannun dama kawai seta shiga kwakwansa kofar batareda tayi wani tunaniba Amira dayanzu ta idar da sallah taji ana buga kofa tataho tabude dukda kuwa tana mamakin wanene ze buga musu kofa da asubar Allahn nan…….
Arba tayi da fuskar Asma’u dukda kuwa gari begama haskeba tagane ta, Asma’u kece agidanmu yanzu…
Cikeda damuwa tace nazo gurin kine muje muyi saving Yayanki yanzu ne opportunity dinmu kafin gari yagama wayewa nibansan kan masarautar ba,cikeda mamaki Amira tace kaman yaya bangane ba taina kike tunanin zamu iya taimakonshi so kike ah kashemu Asma’u?……
Kiyi hakuri gaskiya zan iya Laying life dina for him but you bazan goya miki baya muje tareba inaganin sabida bakisan Magajiya bane shiyasa kike neman kisa rayuwarki acikin hadari…….
Cikeda damuwa Asma’u tariko hannun Amira tace in Sha Allah babu mai ganin mu kekam kizo muje jijjiga kai Amira tayi sannan tace”Asma’u bakisan mekike fada bane shiyasa,inbamu sa kan mu ah wahalaba muna iya kara sa Yaya Almustapha acikin wani wahalar gwanda kikoma gida kada anemeki,idon Asma’u yaciko da kwallah sannan tace wallahi bazan koma gidaba harsai kinzo munje abinda yasa nake binki sabida bansan kan gidan baneba bansan inda akasakashiba”…..
Jiki ah sanyaye Amira badan ranta yasoba tace muje don ah ganinta in bare zata iya wannan jarumtakar ma Dan uwanta why not she,Ina zuwa barina fada ma Aisha tana bacci ah daki dan zare idanu Asma’u tayi kafin tace karkicemata muna tare please!kuma kema karkice mata ga inda zakije kawai kice mata yanzu zaki dawo kinji…
To kawai Amiran tace mata kafin tadauko hijab dinta tafito bayan tayima Aishan magana don yauma agidansu takwana……
Machine suka tara aka kaisu har masarautar basu samu wahalar shigaba kasancewar anfara taron biki sosai,itadai Amira secewa take itafa tsoro takeji bazata iyaba tana tsoron Magajiya….
Kwarin gwiwa Asma’u tadinga bata har suka fara doson gurin lokacin gari yayi haske sosai hango dogare uku sukayi sunzagaye gurin amma dukansu akwance suke sunata shatata bacci,cikeda hope Asma’u tace kinga bacci ma sukeyi dukansu babu mai noticing dinmu cikin sanda suka cigaba da tafiya har suka shiga gurin, Asma’u hawayene sukacigaba da bin kuncinta ganin gurin  wazece mutum nazaune cikin gurinnan fisabilillahi aiko dabba ba abarshi yayi rayuwa cikin gurin nanba bare mutum,rushashen gurine koina very scattered gawasu ciyayi ah gurin da sun tsiro har sun bushe guridai kaman bola and somehow Amira ne tagoge nata kwallar kafin tace muyi sauri muje gurinshi kada ah kamamu gyada mata kai Asma’u tayi kafin suka shiga wani daki ah gurin daman gidan ko roof babu,can suka hangoshi zaune fuskarshi tayi jina jina jikinshi ko riga babu yajingina kanshi guri daya idanunshi suna rufe wanda zakayi tunanin bacci yakeyi amma ba baccin yakeyiba dagudu Amira tayi gurinshi tana kuka tareda fadawa jikinshi fama mai tabobin jikinshi tayi wanda yasashi yin saurin bude idanunshi amma se baiyi magana ba Asma’u data lura da hakan ne tana hawaye takaraso kusa da ita kafin tace Amira you’re hurting him …..
Cikin sauri Amira tatashi daga jikinshi kafin tashiga yimishi sannu tanabin jikin nashi da kallo,sannu Yaya Almustapha…….
Asma’u kuwa zuwa tayi ta bayanshi tashiga since igiyar hannunshi tana we need to get out of here kafin sutashi……..
Amiran ne tazo ta taimaka mata suka sunce hannunshi daya kumbura tsabar irin daurin da sukayimai juya baya tayi kafin tace help him yatashi Amira……
Lumshe idanunshi yayi ahankali don bayajin ze iya tashin, ahankali Amira tace katashi mutafi Yaya Almustapha,kallonta yayi kafin yace “kubar nan gurin banason suganku”….
Cikin sauri Asma’u tace”tare zamu tafi kuma bazasu ganmuba da yardar Allah”…..
Batareda ya kalletaba yace”I’m not going anywhere”…..
Sakan baki tayi tana kallonshi,meyake nufi duka hardwrk dinsu abanza zai tafi….
Zuwa tayi cikin sauri ta tsuguna gabanshi”don Allah katashi baka ganin irin illar dasukayi maka ne,kumafa basuda niyar barinka you don’t know when they are going to release you”,takarashe maganar tana goge kwallarta kallonta ya tsaya yanayi tareda mamakin ya akayi tasan halin dayake ciki kuma mai yakawota, batareda yasan yayi magana ba yace”what are the tears for,besides why do you care?”,yanda yayi maganar seda yasa tsikar jikinta yatashi  don ko Amira dake tsaye bataji meyace ba,kallon cikin idanunshi tayi batareda tasan ansar dazata bashiba dakyar ta iya dauke fuskarta kafin tace”I don’t know and yanzu ba lokacin argument baneba please”..
Lumshe idanunshi yayi batareda yace musu komaiba,Amira ne tace nidaman nasani bazai taba bamu hadin kaiba he don’t want to be a coward bakisan Yaya Almustapha baneba damuka samu yadubemuma muji dadi,kallon Amira Asma’u tayi batareda tasan abunyiba,can kuma tasamu guri tazauna gefenshi sannan cikin kuka tace “if he’s trying to be stubborn then, I’m stubborn as well idan be tashiba babu inda zanje nima”…..
Bude idanunshi yayi yadaurasu akanta saurin dauke kanta tayi don batason su sake hada idanu……….
Maida kanshi yayi kan Amira,kibarnan gurin yanzunnan and keda kika kawota kidauke ta kutafi….
Cikeda damuwa tace sorry Yaya Almustapha amma bazamu iya barinka cikin wannan condition dinba,wani harara daya dakamata ne yasata saurin juyawa tana cema Asma’u ta tashi su tafi suna cikin hakane suka ji anbude kofa bakaramin rudani suka shiga ba dukansu Amira tafara salati tana shikenan nasu yakare……..

Story continues below

Almustapha dukda zafin dayakeji ajikinshi bazai iya bari agansu ba cikin sauri yatashi yakama hannayensu sukayi cikin wani daki dake dauke da katakai ah jubge,bayan katakan suka shiga suka buya kafin yamusu alama da hannunshi kan suyi shiru Asma’u dake gefenshi ne taga kafarshi na bleeding yataka kusa,hawaye ne suka zubo mata harara yadaka mata wanda yasata hadiye kukanta,sunajinsu sunata nemansu babu inda basu shigaba ah building din kafin daya daga cikinsu yace kilan baya cikin nan yagudu don haka suka fita cikin sauri don dubawa,seda suka tabbatar dogarayen sun fita kafin yace sufita su tafi make kafada Asma’u tayi wani harara ya sake daka mata wanda yasata saurin bin bayan Amiran batareda ta shiryaba………
Komawa yayi yazauna ah inda suka daureshi din tareda jingine kanshi jikin karfen…..
Asma’u da Amira na fita basuyi nisaba sukayi kicibis dawani dogari,ihu yayi yana calling attention nasauran yan uwansa kafin yabisu abaya ah guje suma gudun sukeyi sosai sede basu da sa’a don wasu dogarayen gabansu suka sha,ihu Amira tashigayi dasauri  daya daga cikin dogarayen ya maketa,Ina munafikin Yayan naki?….
Shiru tayi batareda tace komaiba,daya daga cikin dogarayen ne yace daga gurin suka fito duk yanda akayi sunbaro shi acan cikin sauri suka kama Asma’u da Amiran suka maidasu gidan,tunda Almustapha yaji anbude kofa yaji hankalinshi yatashi ga kukan su Amira dayakeji wurgi akayi dasu kafin wani ya make Almustaphan yana tsabar kai rayuwarka ah son Mata yakare sunema zasu zo taimakonka?…..
Dariya suka kwashe dashi dukansu yayinda daya daga cikinsu yace”yarasa masu tsirar dashine ko kamanta bashida kowa?”…….
Kama Asma’u da Amira sukayi suka dauresu suna ku kuka kawo kanku sannan suka daure Almustaphan wasu daga cikinsu suka tafi sanar da Magajiya abunda yafaru…..


****

Munira ne tashiga dakin Asma’u don dubata taga wayam babu ita hakanan taleka bandakin ma babu kowa cikeda tashin hankali tashigo parlour tana Kiran Ummi, cikeda bacin rai Ummi tace miyene kike kirana kamar wanda zaki tashi sama, karasowa tayi tana haki tace Ummi Adda Asma’u bata daki,cikeda  damuwa da maganar Ummi tace shine kikazo kinamin wannan kiran,kinduba bandaki batanan ne?……
Batanan wallahi Ummi,hararanta Ummi tayi kafin tace kizo kici abinci kada kuyi latti banason shirme ko in zata fita daman seta sanar dakene…..
Jiki ah sanyaye Munira tanemi guri tazauna tafara cin abinci ba ajima ba sega Munir da Ummi ta aikeshi yakarbo mata abu cikin agurin Mommy yashigo yanacewa Asiya tace yakawoma Asma’u littafinta data samu cikin Jakarta…..

Ummi ne tace itan bata canne?….
Batacan Ummi,atake se Ummi taji hankalinta yatashi dakanta taje duba Asma’un batanan ta aika bangarensu Mubaraq ma batanan,dafe kanta tayi cikeda damuwa tana tunanin ina Asma’u tashiga,bangaren Daddy tawuce don fada mishi amma koda tayi mishi bayani cewa yayi bayason damuwa Asma’u is getting out of hand and she’ll surely come back ko Ina ma tajeta shikuma zai dauki mataki lokacin,jiki ah sanyaye Ummi tafita…..
*****…
Saukar dare yayi don wuraren karfe shadayan dare jirginsu yasauka ah Abuja straight yawuce yadauki motar sa yakamo hanyar Zaria dukda kuwa yasan irin risk din dake hanyar na yan fashi dadai sauransu……
Sanda ya iso masarautar tayi shiru duk kowa yakwanta bacci se guards wanda suma bakowane yasan da isowarsa ba, straight bangarenshi yawuce yasamu guri yazauna yana tunanin matakin dazai dauka don saving dan uwan nashi daga wannan masifar………
Aikuwa garina wayewa yayi wanka yayi shirinshi cikin kayan sarauta,he knows what he’s going to do is very risky sede bashida wani option ah yanzu daya wuce yayi hakan only then his Mother will stop all the accusations……
Straight bangaren Mai Martaba yawuce batareda ko breakfast yayiba,tundaga hanya da bayi suka ganshi suka shiga rige rigen zuwa fadama Magajiya donkuwa kowa burinta ta isarma Magajiya sakon isowar ‘Danta don su samu kyauta…..
Aikuwa lantana ne tayi sa’ar zuwa sanar da Magajiya, murmushi Magajiya tayi dukda kuwa irin damuwar datake ciki na ganin maciji jiya ah dakinta seda taji zuciyarta tayi wasai atleast Sulaiman is back koba komai zecika mata daddaden burinta……
Kyautan zoben gwal akabama lantana tana godiya cikedajin dadi tafice yayinda Magajiya tafice don zuwa bangaren Mai Martaba taga ‘Dan nata don bazata iya jiran har yazoba…..
Sulaiman kuwa tunda ya’isa bangaren Mai Martaba aka shiga yimashi iso ah parlour yasamu mahaifin nashi cikeda jin dadi sede bangaren Mai Martaban bahaka baneba……..
Tsugunawa yayi yana mika gaisuwa kin amsawa Mai Martaban yayi sannan yace Baba na kasan irin tashin hankalin dakasani aciki kuwa?…
Cikeda damuwa Sulaiman yace kayi hakuri Abba,i wanted to surprise you shiyasa naki communication dakowa agida….
Bata rai Mai Martaba yayi yana”wane irin surprise ne haka dahar zaisa kasaka family dinka cikin damuwa,munata nemanka bamwa samunka…..
Murmushi yayi tareda karasawa kusada mahaifin nashi sannan yakama both kunnuwanshi…
“I’m really sorry Abba,bazan sakeba”….
Murmushi Abban yayi kafin yace nayafemaka tunda kadawo gida safe and sound…
Cire hannunshi yayi ah kunnuwanshi kafin yace”nagode Abbana”..
Gyada Kai Mai Martaba yayi kafin yace isowar dare kayi kenan?…
Eh Abba Sulaiman din yabashi ansa kafin Mai Martaba yace to Ina surprise din…..
Cikeda damuwa Sulaiman yace bansamu nazo dashi ba amma insha Allah yau zaka ga surprise din Abba zuwa anjima da dare, dukda kuwa bahaka nasoba tahowar dole ne takamani Abba……
Ganin yanda fuskar Sulaiman din tacanza lokaci guda yasa shi cewa,lafiya Sulaiman,meke damunka?..
Dago idanunshi dasukayi jazur yayi yace,Abba naji labarin kana hukunta wani ah dalilina shiyasa hankalina yatashi nadawo gida,naji labarin kana hukunta wani akan laifin dabashi yayiba bayan nine nayi laifin wannan karan hawayene suka zubo ah fuskar tashi,cikeda damuwa Mai Martaba yadubi Sulaiman din yace bangane inda ka dosaba……
Goge yar kwallarshi yayi kafin yace Abba inamagana ne akan Almustapha, yaron dakasa amishi hukunci ranar Monday sabida ankamashi da laifin yima bayi fyade ah masarautar nan, folding hannu Sulaiman yayi kafin yace believe me Abba he did nothing duk abunda yafaru ninayi bashiba bansan ya akayi akayi turning abun kanshi ba bansan miyasa bayin suka ce shineba,tunda yafara magana Mai Martaba kallon shi yatsaya yi cikeda mamaki don shi yarasa gane me Dan nashi yake ciki Magajiya kuwa da dede shigowarta parlourn taji abunda Sulaiman din yake fada tayi saurin karasowa cikeda bacin rai tana”baka da hankaline Sulaiman”, Mai Martaba ne yayi saurin daga mata hannu fuskarshi babu ko annuri yayinda Sulaiman kanshi nakasa kokadan beyi regretting abunda yayiba yagaji da abunda mahaifiyarsa takeyi,yagaji da zuba mata idanu hakanan yagaji daganin itace take winning all the time,he will do all that it takes to save Almustapha koda kuwa hakan yana nufin ruining image nashi ne,shine keda laifi miyasa Dan uwansa zaiyi suffering for his deeds…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page