HUTU CHAPTER 10

HUTU

CHAPTER 10
Wuyan abu a farashi, wasa wasa su Zeena sunyi nisa a waec dinsu sun kusa gamawa inda en js3 su Binta kenan ke shirin fara nasu wanda Binta tafara karatu sosai ga kuma couching teacher da Kausar tasa aka sama mata dan kawai taci jarabarwar waec dinta koda da pass ne, Kausar kuwa har yanzu morning sickness be barta ba, amma a haka take daurewa koh kadan bata langwabewa wai dan bata da lfy, sosai Hydar ke kula da ita yanzu da yake zaman gida dan hutu sosai aka bashi saboda ya warke da kyau, soyayyan Khaleel da Zeena kuwa se abinda yayi gaba dan a halin yanzu har an fara maganan aurensu wanda za’ayishi bayan su Binta sun gama waec da sati biyu saboda haka saura wata daya da en kwanaki aurensu. Zinaru, Hajiya da Antyn birni kuwa rayuwa sabowa suka fara a prison cell, sosai suke shan wahala ba kaman Zinaru da roommates dinta suka bala’in rainata, duka, zagi, tsangwama babu wanda basa mata amma har yanzu babu digon nadama a tattare da ita, babu abinda take buri kaman taga an sallameta ta koma kauyensu wurin malaminta dan kawai a mata maganin Hydar da Binta dan har yau har gobe gani take kaman ta dalilinsu ta tsinci kanta a wannan halin da wannan yanayin, kaman yadda court ta bukaci da gwamnan kasa yasa a maida karuwan dake gidan Hajiya kauyukansu tareda basu jari da kuma yi musu kashedin karsu kara dawowa cikin gari da sunan sunzo karuwanci haka gwamna ya aikata amma abin takaicin maimakon a maidasu cikin mutunci se aka musu koran wulakanci wanda wannan yasa suka bazama cikin gari sukaci gaba da karuwancinsu ba kaman Asabsy da ta samu ta damke wani senator banda kudinshi ba abinda takeci. (wannan kenan) .

Binta ce kwance kan gado ta zurfafa cikin tunani Zeena na school yau suke rubuta final paper dinsu mathematics, Kausar na zaune a parlor tana kallo wani program, Hydar ya fita jin shiru shiru Binta bata fito ba yasa ta tashi da kanta ta shiga dakin, kwance ta ganta dan da alama ma bataji shigowar Kausar din ba, zama Kausar tayi kan gado sannan tasa hannu tayi tapping din bayan Binta da sauri ta juyo dan bataji shigowarta ba ganin Kausar ce yasa ta mike zaune tareda cewa “aunty ashe kin shigo banji ba”, Kausar tace “eh na shigo, najiki shiru shine nazo na duba ki, amma da alama akwai abinda ke damunki”, shiru Binta tayi tana wasa da yatsun hannunta Kausar ta dafata tace “u knw u can confide in me”, murmushi Binta tayi dukda bawai ta gane me confide din ke nufi ba amma dai ta fahaimci Kausar, kara tabata Kausar tayi ga mamakinta sega hawaye na sintiri a fuskar Binta, sosai Kausar tasha mamaki, cikin damuwa tace “Binta lfy, koh an miki wani abu ne?”, girgiza kai Binta tayi tareda kwanciya kan kafadar Kausar tace “Antyna har yanzu na kasa mantashi, yaki barin zuciyata ta hutu, kullum da tunaninshi nake kwana nake tashi, basan me zanyi na samawa zuciyata sauki da farin cikinta ba”, ta karashe tareda fashewa da kuka me cin rai, Kausar cikin rashin sanin inda Binta ta dosa ta dagota tareda cewa “wayeshi?”, cikin shessheka Binta tace “An.. Anwar”, dam gaban Kausar ya buga ta juyo da Binta sosai suna kallon juna ido cikin ido tace “Binta karkice min har yanzu baki manta da wannan yaron ba?”, shiru Binta tayi Kausar tace “Binta u need to forget him, dole ki manta dashi dan ba yaron arziki bane, u have a bright future ahead of you, dole ki san yadda zakiyi ki yakiceshi daga cikin ranki, u have to face reality, kisan abinda kikayi for goodness sake karkisa duka abinda nakeyi akanki na ganin kin samu rayuwa me inganci da amfani ya tashi a banza, dan Allah Binta kiyi kokari ki mantashi pls”, girgiza kai Binta keyi cikin kuka me tsanani tace “wlh anty nayi kokarin mantashi amma na kasa”, “ki kara kokari, kuma ki dinga addu’a nima zan tayaki da addu’a kinji”, gyad’a kai tayi alamar toh sannan Kausar tasa hannu ta share mata hawaye tareda cewa “jeki wanke fuskarki kar a gane kinyi kuka”, da haka ta tashi ta shiga bathroom Kausar kuma ta bita da kallon tausayi dan a ganinta Anwar ya cuceta ne kawai ta tusawa karamar yarinya soyayyarshi ya barta nan kuwa batasan shi yamafi Binta shiga damuwa da tashin hankali ba.
Alhmdlh su Zeena an rubuta last paper daga yau sun gama sa uniform, dadin da sukeji baya fasaltuwa, gabadaya sun bata school uniform dinsu da permanent marker daga mazan har matan gashi duk sun jika kansu da ruwa banda murna ba abinda sukeyi, tana cikin wasanta da classmates dinta taji wayarta na ringing, dauka tayi cikin farin cikin ta matsa gefe tareda cewa “hello Ya Khaleel”, yayi murmushi ta dayan bangaren yace “congratulations dear, hope nine first person danayi congratulating dinki”, tayi murmushi tace “yes, kaine first person and I appreciate it”, murmushin ya kara saki dan idan yana tareda Zeena koh suna waya wani farin cikin yakeji yana lullube shi, “inzo in daukeki in kaiki gida?”, ya tambaya hoping she will say yes, ai kuwa without thinking twice tace “I would love that”, yace “ok expect me in less than 30mins”, da haka sukayi sallama tareda kashe wayan, friend dinta Rahma dake gefenta tace “hmm, nidai soyayyarku da wannan yayan naki yana burgeni, ke gentle shi gentle”, murmushi Zeena tayi tace “Allah koh”, kawar ta kada kai tace “Allah kuwa, Allah ya barku tare musha biki”, Zeena ta amsa da “Ameen” tana murmushi.

Kaman yadda Khaleel ya mata alkawari cikin minti talatin se gashi nan a kofar school dinsu, wayanta ya kira yace mata gashi yazo tace ya bata minti biyar, seda ta rungume duka classmates dinta mata ta musu sallama tareda cewa “se mun hado ran graduation”, duk suka amsa da “sure”, sannan ta musu sallama ta fito da kayan jikinta hakanan wanda suka riga suka bata da permanent marker, a mota ta sameshi zaune ya bude mata ta ciki ta shiga ta zauna tareda cewa “Ya Khaleel ina wuni”, “lfy lau my angel, shikenan alhmdllh kin gama secondary school”, tayi murmushi tace “u don’t know how happy I am da na gama”, fara jan motan ya farayi idonshi na kan titi yace “this calls for celebration”, a haka sukata hira amma sedai taga ba hanyar gida ya dauka ba, batace dashi komai ba dan tasan Ya Khaleel baze cutar da ita ba tinda ba yau ya saba fita da ita ba.

A gaban wani fancy restaurant yayi parking sannan ya kalleta yace “let’s eat here, yunwa nakeji”, shagwabe mishi fuska tayi tace “Kalli fah kayan dake jikina duk ya baci”, murmushi yayi ya kalleta yace “toh ai ke kika bata, kuma kowa ya ganki haka yasan kinyi hakan ne saboda murnan gaba paper dinki”, kara shagwabe mishi fuska tayi tace “nidai bazan iya shiga haka ba”, cike da adoration yake kallonta dan komai tayi burgeta yake, hannu yasa a back sit ya dauko wani leda yace “change into this”, dubawa tayi taga straight gown ne na material ta kalleshi tace “ina ka samo wannan?”, kallonta yayi yace “na meenah ne, Mom ta siya mata amma ya mata tsayi akace na canzo,toh ni nama manta dashi se yanzu na tuna, change bari na baki privacy”, kai ta kad’a mai ya fita tareda kulle kofan dan ta samu ta canza. cikin kankanin lokaci ta canza sannan tasa veil dinshi ta fito, kiris ya rage bata saki dariya ba ganin trekkers din school dinta ne a kafarta, yana ganinta yayi murmushi yace “u look beautiful”, kanta kasa tace “thank you”, da haka suka jira cikin restaurant din kowa ya kallesu tunanin su ya da kanwa ne not knowing aurensu ma is in less than 1mnth.

Ciki suka shiga ya musu ordering din lafiyayyan abinci sukaci suka cika ciki sannan suka fito, daga nan mall ya kaita wanda duk a wuri daya suke da restur din, suna shiga ya kalleta yace “ki dau duk abinda kikeso as a congratulatory gift”, bata musa ba saboda akwai wani perfume da takeso ta siya kuma batada kudin perf din, layin da kayan perfs suke tayi ta fara dubawa cikin ikon Allah kuwa taga perf din ta dauka, yana kallonta yace “is that all”, ta kad’a mishi kai juyawa yayi ya koma ya siya kayan chocolates da ice cream sannan suka biya kudi suka fito ya dauki hanyar gida. Be shiga ba a waje yayi parking saboda an kirashi a hospital emergency saboda haka sama sama sukayi sallama ta shiga gida shikuma yaja mota da mugun sauri saboda yayi meet up. Da Kausar ta fara cin karo Kausar dake zaune tace “se yanzu, na tura driver wai bakya school”, zama Zeena tayi ta zayyane mata inda sukaje da Khalil harda nuna mata abubuwan da ya siya mata, “lallai ya kyauta”, cewar Kausar sannan taci gaba da cewa “go and freshen up Binta na ciki wai kanta na ciwo”, dakin ta shiga taga Binta na bacci saboda haka ta shiga bathroom bayan ta rage kayan jikinta.


BAYAN SATI BIYU

Yau ya kama Monday kuma a yau ne su Binta zasu fara JSCE dinsu wato junior waec wanda kuma yayi daidai da yau Zeena zata koma gida saboda bin umarnin Ummi dan tanaso ta fara gyara ‘yarta kar lokaci ya kure mata, Hydar da kanshi ze saukesu, seda sukayi breakfast sannan suka fito gabadayansu harda Kausar da alhmdllh yanzu jikinta yayi sauki dan aiki ma takeso taje ta dan duba wasu abubuwan ta dawo, Binta aka fara saukewa a school sannan ya sauke Kausar a gaban workshop dinta ya karasa da Zeena gida, yana parking ta fito tayi cikin gida da gudu, a parlor taga Ummi tana zaune tana kallon news at 8 da sauri taje ta rungumeta tareda kankameta Ummi tace “kunga zata karyani”, Hydar da shigowanshi kenan yayi murmushi ya samu wuri ya zauna Zeena tace “Ummi nayi missing dinki sosai”, hararta Ummi tayi tace “keda koh kirana bakya yi”, dariya tayi ta mike tana cewa “bari naje naga dakina”, da haka ta wuce Ummi da Hydar suka gaisa ta kalleshi tace “yaushe zaka koma bakin aikinka?”, “bayan bikin da sati daya Insha Allah”, “Allah ya kaimu”, cewar Ummi ya amsa da Ameen daga nan kuma suka shiga hiran bikin Zeena da Khalil. Sosai Kausar taje ta tarar da aiki na jiranta, da taimakon secretary dinta ta samu tayi abubuwan da ya dace, ba ita ta kira Hydar ba se biyar na yamma dan se lokacin ta gama, koda suka koma gida Binta ta dade da komawa suna zaune parlor ita da Hajara, sanda zuwa suka musu sannan suka haura sama saboda su huce gajiya.

Wasa wasa cikin two weeks su Binta suka gama waec se jiran result, shirye shiryen biki ake sosai daga gidan amarya har gidan angon, Binta ma tana gama waec ta koma gidan Ummi wai harse bayan biki, Zeena kuwa gyara takesha ciki da waje ko kadan Ummi bata wasa wurin gyara autarta, haka zalika ba’a bar Anty Maryam a baya ba ita duk wani abu datasan ze amfani Zeena kawo mata takeyi, Zeena tin bataso har tazo ta hakura, Anty Maryam taso a siyawa Zeena kayan daki daga Italy amma Ummi tace a’a tinda Kausar na siyarwa kuma nata nada kyau a siya biyu a hannunta in yaso se a siya biyu a Italy tinda ance four bedrooms ne, haka ma kayan parlor za’a siya daya wurin Kausar a siya daya daga waje, haka suka tsara abun Abba da Hydar kuwa jira kawai suke ace su kawo suke bayarwa, ko kadan basa kyashin cirar kudi ko nawa ne kuwa.
A bangaren Khalil kuwa sosai Mom ke nuna bajinta wurin ganin ta hada lefe na gani na fada saboda haka ma ta yanke a dubai zataje ta hado lefen kudi kawai Khalil da Dad suka dire mata, tareda Meenah da wata sister dinta zasu inda sati daya kawai zasuyi su dawo dan abinda ya kaisu shi zasuyi su dawo, Mom ta kira Anwar ta shaida mishi maganan bikin inda ya fada mata ze kokarta yazo koda daurin aure kawai ya samu, sosai taji dadi dan tinda ya tafi wurin wata bakwai kenan going to 8mnths be waiwayo gida ba waya ma se yaga dama suke waya, dan dadi seda ta shaidawa kowa Anwar zezo daurin aure dukda batada tabbaci amma she hopes ya samu zuwa koh ba komai sunyi missing dinshi. An buga IV inda aka ta rabawa ba kaman Abba,Dad,Khalil da Hydar, dan sunfi kowa mutane, Mom ta riga da ta tafi Dubai inda itama Anty Maryam ta tafi Italy da wata Anty dinta, Kausar kuwa sosai take aiki kan kayan Zeena wanda ze fito daga side dinta cus she wants what’s best for her, dukda kudin kaya bibbiyu aka bata na daya kawai ta karba inda dayan set din zatayi shi a matsayin gudunmawan ta. Amarya Zeena da Binta kuwa ba aikin fari balle baki, kullum suna gida dan dikinsu ma har gida akazo aka karba Binta ta nuna style dinda takeso.


A WEEK LATER

A WEEK LATER

Sosai shirye shiryen biki ya kankama ba kama hannun yaro, Zeena tasha kyau kaman a saceta a gudu tsabar kyau, an gama mata kayan daki inda akaje aka mata jere a gidanta dake maitama, yau ya kama Thursday kuma yaune za’a kawo lefen amarya, karfe hudu amarya da kawayenta suka bar gidan zuwa gidan anty Maryam saboda wani event da suka tsara na bridal shower, ko kafin su je an musu decorating din wurin inda duk suka shirya cikin blue nd pink amarya kuma tasa white gown, sosai sukayi kyau kaman basuba musamman ma Binta da tafi sauran kawayen haduwa. Sosai event din ya kayatar wanda daga ita se kawayenta da cousin sisters dinta wa’anda sukazo daga adamawa musamman saboda bikin, anci ansha anyi rawa sannan aka watse aka fara komawa gida.


Koda suka kai gida har an kawo lefenta akwaiti goma cif da kaya sheke a ciki na gani na fada dan kuwa bana banza a ciki, ita abinma mamaki ya dinga bata wai itace zatayi auren, gidan cike yake da en uwa da abokan ariziki shiyasa ko ina hayaniya ne, Binta kam tasha introduction dan Anty Maryam janta tayi tana nunawa en uwa da dangi Binta sannan ta fada mata yadda suke da ita, sosai tayi murnan ganin en uwanta na dayawa, ashe dai dama chan da gatanta Zinaru ke wulakanta ta. Zeena, Binta da cousin sisters dinsu gabadaya a daki daya suka kwana wanda seda suka raba dare suna hira sannan suka samu bacci. Washegari ya kama Friday da safe akasa amarya lalle, da rana sukayi fulani day da yamma akayi kamu a wani arnen hall dasuka kama, basu suka dawo daga wurin kamu ba se kusan sha daya na dare, bayan duk sunyi wanka sun kwanta dansu huta Ummi ta tura Kausar data kira mata Zeena, har dakin taje ta kirata sannan ita ta wuce wurin mijinta dan be yarda ta kwana a gidan ba, acewarshi su tafi gobe da safe seta dawo, be yadda ta iya da Hydar haka ta hakura ta mishi.

Zaune kan gado ta tarar da Ummi a hankali ta karasa ta zauna tareda cewa “Ummi kin kirani”, murmushi Ummi ta mata sannan ta mika mata wani box tareda cewa “bude ki gani”, budewa tayi inda taci karo da family album dan karami, kallon Ummi tayi Ummi tace “bude ki kalla”, budewa tayi ta dinga kallo inda yawanci daga Ummi se Abba da mahaifiyar Anty Maryam acewarta, dan ita a iya zamanta a gidan tasan cewar mahaifinta matanshi biyu kuma daya ta rasu wacce itace mahaifiyar Anty Maryam dan bata taba sanin ita da anty Maryam ciki daya suka fito ba, duk a tunaninta ita da Hydar ne suka fito ciki daya, “kinsan ko wacece wannan?”, Ummi ta tambayeta tana nuna mata Hajiya Hindu, murmushi tayi tace “maman Anty Maryam ce”, kallonta Ummi tayi cike da tausayawa kafin tace “haka zalika kima mahaifiyarki ce, wacce ta dau cikinki har na tsawon wata tara, a wurin haihuwarki ita kuma Allah ya karbi abarsa”, baki sake take kallon Ummi kaman wani yaren da bata taba jinshi ba Ummi ta mata, tafi minti uku batayi magana ba kafin daga baya murya na rawa tace “Ummi yanzu kina nufin bake kika haifeni ba, all this while nida Anty Maryam ne muka fito ciki daya bada Ya Hydar ba?”, ta karashe a daidai lokacin da hawaye suka wanke mata fuska, hannu Ummi tasa tana share mata hawayenta tace “kiyi hakuri bamu fada miki ba tin farko, ba komai ya hanamu fada miki ba se tausayinki da yayi mana yawa a zukatanmu”, kara kallon hoton tayi tareda fashewa da wani irin kuka wanda da batasan da irin wannan kukan ba, kuka biyu takeyi a lokaci daya, daya na rasuwar mahaifiyarta wacce bata taba gani ba balle taji dumin jikinta, na biyu kuwa kuka takeyi saboda so da hallaci da Ummi ta mata, ko sau daya Ummi bata taba nuna mata banbanci ba dan zata ma iya cewa Ummi tafi sonta akan Hydar dan bata neman abu sau biyu a wurin Ummi, da tace ga abinda takeso toh Insha Allah abinda zata tarar kenan, sannan koda wasa Ummi bata taba dukanta ba, kuka take sosai Ummi ta rungumeta ba tareda ta lallashe ta ba dan tasan cewar kukan take bukata a wannan lokacin.Seda tayi kukan sosai sannan ta dago ta kalle Ummi sosai tareda cewa “ngd Ummi da hallacin da kikamin, Ummi bani da abinda zan saka miki dashi se addu’a dan kin rikeni sosai kaman ‘yarki ta cikinki”, rufe mata baki Ummi tayi tace “banaso ki godemun sannan inaso ki sani ke ‘yatace dukda ban haifeki ba amma ban taba miki kallon ‘yar kishiyata ba sedai ‘yata ta cikina, dan na fada miki asalinki baya nufin komai ya canza kenan, a’a har yanzu ina nan a matsayina na Umminki kuma kina nan a matsayinki ta autata”, murmushi Zeena tayi tareda kara rungume Ummi tana sauke ajiyar zuciya, ranan a dakin Ummi Zeena ta kwana su Binta sun jirata har suka gaji suka kwanta.

WASHEGARI (RANAR DAURIN AURE)

8:00am na safen ranar asabar wanda ya kasance ranar daurin auren Khalil da Zeena, Nnamdi Azikwe International Airport Abuja, wasu samaruna uku na gani, kyawawa, matasa, masu jini a jiki suke saukowa daga mattatakalar jirgin da ya taso daga Delhi India, na gaban nake karewa kallo dan ganin he looks familiar, sanye yake da black jeans white top, white shoe da black wrist watch, ya taje gashin kanshi ya kwanta luf luf dashi, seda suka karasa saukowa sannan na ganesu, ashe Anwar ne da Jamil da MK, wayyo Allah na readers zanso kuga yadda Anwar ya canza ya kara haske kyanshi ya kara fitowa sedan rama kadan da yayi, da murmushi ya karasa wurin Khalil da Mom ta matsa mai akan lallai lallai seyaje ya dauko kaninshi, rungumeshi yayi tareda cewa “congrats bro, ashe dai zakayi auren, nida nake tunanin zan rigaka”, dariya Khalil yayi tareda kai mishi duka yace “toh gashi dai nan da awanni kadan zan zama ango”, murmushi Anwar yayi yace “meet my friends, Jamil da Mukthar amma MK ake kiranshi”, gaisawa sukayi sannan suka shiga mota zuwa gida inda Khalil keta bashi lbrn yadda Mom ke murnar zuwanshi duk ya cika musu gida dan surutu yau danta ze dawo, murmushi kawai Anwar yayi dan shi kanshi yasan Mom na bala’in sonshi kaman yadda shima yake sonta.


A waje Khalil yayi parking saboda gidan a cike yake, yana ajiyesu ya juya kan motanshi zuwa hotel inda ya ajiye bakinshi, abokanshi da sukayi karatu tare da kuma en uwanshi, shiga gida Anwar yayi yana kallon yadda aka canzama gidan paint sannan ba baba mai gadin da ya sani a bakin gate bane, an canza, parking lot ya kalla yaga motocinshi suna nan yadda ya barsu da alama ma ko tabawa ba’ayi ba. Da sallama ya shiga parlor su Jamil na biye dashi a baya, parlorn cike yake da mata, se yanzu ya fara dana sanin biyowa ta wannan kofan, daya sani ta kofar baya yabi, shiga yayi suka fara gaisawa da en uwa da dangi ana tambayanshi ya karatu, Meenah ce tazo da gudu jin muryanshi ta rungumeshi tana cewa “Ya Anwar oyoyo”, shima rungumeta yayi yana murnar ganin ‘yar tilon kanwarshi, Mom dake guest room da sauri ta fito da aka shaida mata Anwar ya dawo, “son”, ta kirashi cike da kin yarda, kallonta yayi sonta na kara shigarshi da sauri ya saki meenah ya karasa wurin Mom tareda rungumeta yana cewa “I miss u Mom”, “miss u more my son”, dagawa yayi daga jikinta yayi introducing dinsu Jamil as friends dinshi suka gaisa da Mom sannan tace suje su huta kafin a kawo musu breakfast, fita sukayi zuwa bq dan yasan Dad baya gida balle yace suje su gaisheshi, Meenah bin bayansu tayi tanata zuba musu dan bazan surutu kaman yadda ta saba Anwar se murmushi yake yana bata amsa inda Jamil da MK ke kallonsu cike da birgewa da sha’awa, dan kuwa Jamil shi kadaine a gidansu, MK kuwa beda baby sister sedai baby brother.

Da misalin karfe goma aka fara shirin tafiya daurin aure, Khalil ya fito cikin shadda dikin babban riga er ciki da er waje fari sannan ya dora hula baki kirar zanna bukar da agogon hannu baki da takalmi cover shoe shima baki inda ya feshe jikinshi da turare kala kala da za’a kasa tantance irin tureren da yasa, murmushi yakeyi bakin yaki rufuwa abokanshi se tsokanarshi sukeyi da cewa “ango ango”, a yayinda suke shiryawa suna. Hydar yana gidanshi inda Kausar ke shiryashi cikin blue din shadda shima dikin babbar riga kala ne kawai ya banbanta shigarshi da ta ango amma kowa ya ganshi yaga abokin ango na kut da kut, tareda Kausar suka fito inda ya ajiyeta a gidansu sannan ya wuce hotel dinda su Khalil suke, be shiga ciki ba kiransu a waya yayi tareda cewa suyi suyi su fito lokaci na kurewa kar a daura aure ba ango.

A chan gida kuwa Anwar shima ya shirya shi da abokanshi bayan yace a wanke mishi motarshi sannan a mishi warming dinshi dan dashi zasu tafi, gabadayansu sunyi kyau cikin dikin ash yadi da sukasa, seda ya shiga gida yawa Mom sallama sannan ya fito suka shiga motan suka bar harabar gidan zuwa gidansu Hydar dan a masallacin unguwar za’a daura aure, hira sukeyi a motan har suka doso unguwar inda tindaga nisa ake hango cunkoson da wurin ya dauka, Anwar ya rasa dalilin da yakejin faduwar gaba tinda ya shigo unguwar, a dan nisa da masallacin sukayi parking saboda ba hanya, da kafa suka karasa a wajen masallacin sukama kansu masauki dan kuwa ciki ba matsaka tsinke tsabar cika da yayi.

Auren Khalil da Zeena aure ne daya tara dumbin jama’a, malamai, shuwagabanin kasa, ma’aikata, en uwa da abokan ariziki, an cika sosai wurin daurin auren, seda liman yayi en nasihohinshi akan aure da zaman takewar aure sannan aka daura auren Khalil da Zeena akan sadaki naira dubu hamsin, ana daura aure Khalil dake cikin masallaci shida Hydar ya kai kanshi kasa tareda yin sujjadal shukur, ana daura auren aka fara congratulating dinshi ana watsewa har dai ya rage daga shi se friends nd family dinshi. Cikin gida kuwa wanka akasa Zeena yi ta turara jikinta sannan akasata shiryawa cikin white shadda yasha aiki da multicolor din zare, makeup aka mata dan dai dai ba kaman su Binta dasuka sha makeup sosai ba, sosai taji gabanta na faduwa dan duk abinda akeyi sunaji saboda ya speaker liman ke magana, ana daura aure gabanta yayi wani mugun faduwa na shikenan yanzu ta zama matar aure se yadda Khalil yayi da ita, Anty Maryam ce ta shigo ta ganta zaune kawaye sun sata gaba suna mata tsiya ita kuma tana kuka murmushi Anty Maryam tayi dan tasan duk maccen da aka daurawa aure dole ta feel hakanan, karasawa ciki tayi ta kalli Zeena tareda cewa “matar Khalil yada kuka”, cigaba da kukan nata tayi Anty Maryam tace “tashi kiyi alwallah kiyi sallan godiya ga Allah kafin angon naki ya shigo”, ba musu ta tashi tayi abinda aka sata, tana idarwa aka gyara mata makeup dinta tareda daura mata dankwali sannan ta zauna zaman jiran angwanen su shigo. 

Binta na nan kwance kan gado ta dunkule gefe daya hannunta kan kirjinta daidai saitin zuciyarta dan wani harbawa dataji zuciyar nayi, sanye take da bakin shadda wanda ya karbi fatar jikinta sosai kaman ba ita ba, ga wani makeup da aka mata gabadaya seta canza, Kausar ce ta shigo dakin da sallama tareda cewa “amarya ta fito, ga angwanai sunso”, da taimakon Anty Maryam ta yafa mayafin sannan duk suka fita dakin ya saura daga Binta se Kausar, sosai hankalin Kausar ya tashi ganin Binta haka dan tayi tunanin koh rashin lfyrta ne ya tashi, zama tayi kan gado tareda cewa “Binta jikin ne?”, tashi zaune Binta tayi tace “a’a Anty, nan ne ke bugawa da sauri da sauri”, ta fada tana nuna saitin zuciyarta, kallonta Kausar tayi cike da mamaki tareda kai nata hannun inda Binta ta nuna mata ai kuwa ba shakka bugawa yakeyi da sauri da sauri, maida kallonta kan Binta tayi sannan tace “yi hakuri, daure muje ayi hotunan dake daga baya mayi magana”, kad’a kai tayi sannan ta tashi suka fita. 

A harabar gidan ake hotunan suna fitowa idanun mutane biyu na sauka kanta, Hydar da Anwar, Hydar kallonta yakeyi yana yaba yadda tayi kyau cikin shigar da tayi yayinda Anwar ke kallonta ganin ta mishi kama da Binta sosai amma sedai yana wasiwasi itace ko ba ita bace yayinda zuciyarshi ya tsananta bugawa har besan sanda yasa hannu ya dafe wurin ba, binta da kallo yakeyi har suka karasa inda Hydar ke tsaye yana sakar musu murmushi, duk hotunan da akeyi hankali Anwar na kan Binta yayinda hannunshi ke dafe da zuciyarshi, Binta naji ajikinta ana kallonta amma idanuwanta sun gaza dagowa dan ganin ko waye wannan yake kare mata kallo haka, har aka gama abinda za’ayi Anwar be dena kallon Binta ba, so yake ta dago dan ya tabbatar ba abinda zuciyarshi ke raya mishi, so yake ta kalleshi dan yasan kwayar idonta baze mishi karya ba, amma ina Binta taki dagowa ta kalleshi, su Jamil sun lura abokinsu ya shiga halara shiyasa suka dafashi amma yaki ya dauke idonshi, yana kallon Hydar ya rungumo Kausar da Binta jikinshi aka musu hoto wanda nan take wani kishi ya taso mishi wanda ya rasa dalili, juyawa yayi yana cewa “let’s go guys”, da sauri Binta ta dago jin muryan da tasan bazata bata mantawa dashi ba ko a cikin bacci taji muryan tasan meshi, amma sedai kash ya riga ya bata baya dan haushin rungumarta da Hydar yayi ne yasa yaji bazema iya tsayuwar wurin ba dukda koh be gama tabbatar da ko hasashen shi gaskiya take fada mishi ba. 

Story continues below


MK ya mikewa key saboda baya ganin ze iya driving, Jamil daya kasa hakuri yace “guy are u ok, naga lokaci daya gabadaya mood dinka ya canza”, he needs to pour it out koh ya samu sassauci a zuciyarshi saboda haka yace “I’m not alright, naga yarinyar da nake muradin ganinta wata da watanni but I’m not sure if she’s really the one, and to make it worst sega wani kato yana rungumeta a gabana, duk da I respect him since he’s my brother’s best friend but a gaskiya ya bata mun rai, gabadaya se naji ya bani haushi”, ba Jamil ba hatta MK seda yayi dariya, seda suka tsagaita sannan MK yace “toh kai Anwar in banda abinka ka sani koh yayanta ne, ko kumama matarsa ce, kuma kai kanka kace u ar not sure if she’s really the one, ka tsaya ka tantance before concluding mana”, tsaki Anwar yaja tareda kwantar da kanshi kan kujera ya lumshe ido yana tunani Binta amma yarinyar da ya gani ke fado mishi arai, “what if Binta ce? What if bayan tayi escape wasu sun taimake ta? What if Hydar ne wanda ya taimaketa daga baya kuma ya aureta”, ai da sauri yace “Noo”, yana girgiza kai, sudai su Jamil kallonshi kawai suke dan kuwa soyayya tama Anwar kamun kazar kuku. 

Har sukaje gida Anwar be daina tunanin Binta ba inda ita kuma Binta sosai ta shiga tashin hankali dan ba makawa muryar Anwar taji in kuma bashi bane toh ta tabbata sun hada dangantaka da Anwar din(😂😂Binta u sick, kina bukatar likitan zuciya dan a duba miki zuciyarki tareda gyara tunaninki). Har waje ta bisu da sauri amma ina ai har sun tada mota haka ta hakura ta koma gida zuciyata ba dadi. Haka ta wuni suku suku da tunanin mutum daya a ranta wato Anwar. Da yamma suka fara shirin zuwa dinner inda amarya ta fito cikin shirinta na gown yellow and black, head dinta ma black an jera mishi yellow stones, 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


angwanai ne sukazo suka kwashesu zuwa wurin dinner din inda Hydar yasa matarsa Kausar da Binta a mota ya kaisu da kanshi dan wai be yarda su shiga motan wani ba, sosai hall din ya kayatu da gani ansan wannan ba bikin kananan mutane bane, sosai dinner ya kayatar inda Binta keta zuba ido koh zataga Anwar dan ta tabbata muryanshi taji kuma indai har yaje daurin aure toh ba mamaki yazo dinner amma babu shi babu alamarshi, Anwar kuwa yanacan mota ta musu tsiya a hanya dan basuyi wani nisa ba suka samu flat tire, gashi sun samu mechanic yana gyara musu amma Anwar se azalzalarshi yakeyi akan yayi sauri dan jikinshi na bashi ze kuma ganin yarinyar nan wurin dinner, ana gamawa ya biya mechanic kudinshi suka harba kan titi se uban gudu yake zubawa dan in be ganta ba zuciyarshi bazata taba samon nutsuwarta ba, a harabar hall din sukayi parking tin daga waje yakejin waka na tashi har suka karasa ciki, zama sukayi Anwar se harba ido yakeyi ya kalli nan ya kalli chan, a lokacin da akace amarya da ango su fito hall su taka a lokacin idon Anwar ya kyallara mishi Binta dan itama ta mike dan tama amarya da ango liki, binta da ido Anwar yayi zuciyarshi na bugawa har ta karasa floor din inda ta fara musu liki da kudin da Kausar da Hydar suka bata sukace na liki ne. 

Sanye take da material dinkin gown sosai yabi jikinta saboda haka gabadaya shape dinta ya fito waje, Hydar na ganin Binta da Kausar sun karaso ya koma musu liki wanda wannan ya bakanta ran Anwar, saboda haka shima ya tashi ya shiga floor ya fara ma Binta barin kudi wanda seda Kausar da Hydar suka kalleshi shi kuwa ko a jikinshi, Binta ganin abin ba sauki yasa ta dago ai carab idonta se cikin na Anwar wanda yasasu jin wani shock da bugun zuciya a tare, Binta ta kasa dauke idonta daga kanshi dan ba shakka wannan Anwar ne shima kuma ya kasa dauke idonshi a kanta dan ko ba’a fada mishi ba yasan Binta ce, murmushi ya sakar mata yana meci gaba da mata liki har kudin hannunshi suka kare sannan ya koma mazauninshi inda ya ciro 1k da pen ya rubuta number dinshi akai tareda rubuta “pls call me”, sannan ya shiga neman meenah, yana hangota ya bata kudin tareda nuna mata Binta data riga ta koma wurin zamanta jiki a sanyaye yace ta kai mata, zuwa tayi taba Binta tareda cewa “gashi inji ya Anwar”, kallon inda yarinyar ke nuna mata tayi aikuwa ta ganshi zaune yana mata murmushi, karba tayi ta bude taga number ne a ciki se ta mayar a jaka ta ajiye, a haka aka tashi dinner lfy inda daga nan aka waste wuraren sha biyu amma sam Khalil yaki yarda ya bari gobe akai mishi amarya, dole su Anty Maryam suka kaita gida tayi wanka ta canza kaya aka mata nasiha angonta da kanshi yazo ya dauki abarshi ba en rakiya amma fah yasha tsiya wurin iyaye da kakanni da abokai. (toh Zeena se muce Allah ya bada zaman lfy). 

Anwar cike da kewa da mamakin Binta ya koma gida, “yaushe ta girma harta waye haka?”, ya tambayi kanshi, all his life be taba kawowa akai cewar ze sake ganinta ba, wani nazari yayi ai da sauri ya mike zaune daga kwancen da yake ya kalli su Jamil tareda cewa “anya banyi wauta ba dana bata number na ban karba nata ba, idan bata kira bafa?”, kallon bakada hankali suka mai sannan duk suka maida hankalinsu kan laptop sukaci gabada kallonsu, a takaice dai a daren ranan Anwar be rintsa ba dan kuwa tsohuwar zumace ta tashi, wani sabon son Binta yakeji daga kashi har ‘bargon jikinshi, ji yake idan ba ita ba baze iya rayuwa ba, Hydar ne ya fado mishi a rai nan ya shiga tunanin dangantakar ta da Hydar amma he couldn’t figure anything out.

Washegari tin safe yake jira ya gani koh zata kira amma shiru babu kira, sosai ya shiga tashin hankali na rashin kiranshi da batayi ba, safa da marwa kawai yakeyi dan hatta abincin kirki ma ya kasaci, su Jamil ba yadda basuyi dashi akan ya kwantar da hankalinshi ba amma ya kasa, hatta Mom seda ta fahimci danta na cikin wani hali, Dad kam be gama sallaman baki ba shiyasa bema da lokacin gida balle yasan halin da Anwar ke ciki. Kafin yamma zazzafan zazzabi ya kama Anwar duk saboda rashin kiranshi da Binta batayi ba, sosai hankalin Mom ya tashi, tambayan duniyar nan gabadaya seda ta mishi amma yaki bata amsa dan ya tabbata idan tasan saboda Binta ya shiga wannan halin maidashi India zatayi da gaggawa shikuma be tashi tafiya ba batare da ya sake ganin Binta ba. 


Binta kuwa daga wurin dinner din Hydar gida ya kaisu ita da Kausar dan be yarda sun kwana gidan Ummi ba, bayan tayi wanka tasa nightee dinta ta kwanta tareda fadawa tunanin Anwar wanda tinda ta ganshi be bar zuciyarta ba, se yanzu ta tabbatar son Anwar takeyi dan tinda take bata taba jin makamancin abinda taji akan Anwar yau ba, amma sedai kash, she’s not ready for it now, ta riga tayiwa Antynta alkawarin bazata bari soyayyar Anwar ya shiga karatunta ba, bataso taba Antynta kunya saboda haka tasa a ranta bazata bata kiranshi ba dukda tasan ba karamin yaki zatayi da zuciyarta ba kafin tace iya aikata hakan. Haka ta kwana cike da tunanin Anwar har gari ya waye, seda tayi sallahn asuba sannan ta samu bacci ya dauketa cike da mafalkan Anwar dinta.Yau dai Kausar da kanta ta tashi dan tayi alkawarin da kanta zata shiga ta hadawa mijinta breakfast saboda taga yanda en mata ke kalle mata miji a wurin biki wanda tasan cewar idan tayi wasa se sun kwace mata miji dan Miemie ta kira ta fada mata Miemie tace gwara ta tashi ta rike mijinta tin gari be waye mata ba tazo ta rasashi, koda ya shiga kitchen Hajara na kokarin hada breakfast, bayan ta amsa gaisuwarta ta kalli Hajara tace “Hajara kije ki gyaramin daki yau ni zanyi girki”, “toh”, tace sannan tayi waje Kausar ta juna ruwan zafi a electric kettle sannan ta kwaso potatoes ta fara ferewa, a hankali take peeling dinshi wai saboda karta yanke, ba karamin lokaci ta bata ba kafin ta gama hada breakfast wanda seda ta kone da mangyada wurin soya, seda ta gama jerawa a dinning sannan tace Hajara ta mata wanke wanke sannan ta haura sama dan ta tashi mijinta amma ga mamakinta har yayi wanka yanasa kaya ta karasa gabanshi tace “yaushe ka tashi”, murmushi yayi tareda rungumota yace “time dinda kike girki”, kallonshi tayi tace “ya akayi kasan nayi girki”, yace “ga kamshin abinci a jikinki”, sosai taji kunya shiyasa ta janye jikinta daga nashi tace “bari naje nayi wanka”, yayi murmushi yace “do u need my help”, harta kai kofa tace “no thanks”, tareda fita daga dakin zuwa nata.

Agogo zesa amma ya nema sama da kasa ya rasa kuma ya tabbata ya shigo da agogon nan gidan shekaran jiya, mamaki ne ya kamashi nan take ya fara duba kayanshi ai kuwa ya nema agogo sama da uku ya rasa, links dinshi ma babu su haka ma bracelet dinshi, “tirkashi!!”, ya fada rai bace, abu daya yazo mishi a rai lokacin shine sata aka mishi kuma ya tabbata Kausar koh Zeena koh Binta bazasu mishi sata ba haka zalika masu tsoron gidanshi be basu daman shiga mishi gida ba, duk tsiyarsu iyakacinsu compound, saboda haka mutum daya ce ta fado mishi arai wato Hajara, rai bace ya bar dakinshi zuwa dakin Kausar wacce fitowanta kenan daga wanka ya kalleta yace “duba kayan jewelries dinki if anything is missing”, da mamaki ta kalleshi tace “mine hope all is well”, furzar da iskar bakinshi yayi yace “kedai yi abinda na saki”, ba tareda ta mishi musu ba ta shiga closet dinta yabi bayanta ai kuwa  sunsha mamaki dan amma fi sace mata kaya akan na Hydar, da sauri ta bude akwatin lefenta dan tayi ajiyar tsarkar daham wanda Mom ta bata bayan bikinta ai kuwa ta nemeshi sama da kasa ta rasa, Hydar duk yana kallonta ta juyo ta kalleshi zatayi magana ya rigata da cewa “kinga illar masu aiki koh”, magana takeso tayi amma be jira me zatace ba ya fice tin daga sama ya soma kwalawa Hajara kira da kakkausar murya wanda Binta ma dake bacci seda ta jiyoshi.


Kausar hijabin sallarta kawai tasa kan towel dinda ke jikinta ta biyo bayanshi, Binta ma fitowa tayi, Hajara kuwa ta gama tsurewa yana kaiwa gabanta ya wanketa da wani wawan mari wanda seda taga taurari ta kuma kurmance na hucin gadi, Hydar babu abinda ya tsana kaman ka mishi karya ka kuma mishi sata uwa uba ka munafunceshi, “ni zaki cuta, duk biyanki da akayi a gidan nan be miki ba sekin dan gana da sata dan kin daukemu kaman bamusan abinda mukeyi ba koh?”, arikice ta dago dan tasan yau kashinta ya gama bushewa, wani mugun harara ya watsa mata wanda seda ta saukar da idanunta kasa yace “fadamin me kika rasa a gidan nan da har ya kaiki dayi mana sata?”, kasa ta duka cikin borin kunya ta fara bashi hakuri tana kuka, Kausar ta matso kusa dashi ta kama hannunshi tace “haba mijina ka kwantar da hankalinka mana, idan kuma ba ita ce tamana satan bafa”, kallonta yayi yace “naga ai bata karyata ba”, numfashi Kausar ta sauke tace “mubarta da Allah tinda munsan munfi karfin abinda ta dauka, ita taci kadan bamu ba”, yasan matarshi ba cikakken lfy ne da ita ba, karfin hali kawai takeyi saboda haka ya rungumota jikinshi tareda sassauta murya yace “ta barmin gida kafin raina ya kara baci”, dama ance sojoji akan matansu kadai suke sauke wannan mugun zuciyar tasu, murmushi Kausar tayi tace “ur wish is my command”, kallon Binta yayi yaga duk a tsorace take kaman ita yakewa fadan yayi murmushi yace “je kiyi wanka kizo muci abincin antynki dan yau ita da kanta tayi girki”, kad’a mishi kai Binta tayi tareda shigewa dakinta da sauri har taso ta basu dariya, shima Hydar juyawa yayi ya haura sama koh sake kallon Hajara beyi ba, Kausar ce ta kalli Hajara tace “kinji abinda yace, ki tashi ki wuce zan turo miki albashinki na wannan watan Insha Allah”, Hajara cikin borin kunya ta tashi ta harhada kayanta ta fita dan tama kasa yiwa Kausar din godiyan hallacin da tayi mata. Gabadayansu zaune suke kan dinning harda Binta, Kausar na serving dinsu duk sun kagu suci suji koda dadi, tea ne da potato da kwai, spoon daya sukasa baki amma da kyar suka hadiye saboda yawan gishirin da tasa, Binta dai ci gaba daci tayi saboda Antynta ce ta dafa saboda haka zataci koh ba dadi, shima Hydar haka ya ringa turawa ita kuwa Kausar kallonsu kawai takeyi dan ita data soya ta kasaci amma gashi su ko a jikinsu, ganin idan bata hanasu ba zasu illata kansu saboda gishirin kadai ya isa ya illata mutum yasa ta janye plates din daga gabansu idonta cike da kwalla, at that moment Mom dinta kawai take blame tinda itace bata tsaya ta koya mata ba, tabbas mahaifiyarta ta cuceta, murmushi Hydar yayi yace “don’t worry, this was ur first, da haka zaki kware, yake tamai, ya dauki wayanshi ya musu order din breakfast sannan ya kalli Binta yace “tinda an bada hutun school me zakiyi for the main time”, kallon Kausar tayi sannan ta kalli Hydar tace “catering school nakeson shiga”, murmushi Kausar tayi tace “kin shiga kin gama dan ko bakice ba zan saki dan se a yanzu nasan muhimmancin iya girki”, “nagode anty”, murmushi kawai Kausar tayi ita dai tanason Binta saboda kunya irin nata, Binta bata taba kallon idon mutum ta mishi magana, bayan an kawo musu breakfast sunci Binta ta koma dakinta tareda dauko one thousand naira note dinda Anwar ya bata tana kallon handwriting dinshi, wani abin na cewa ta karashi amma kuma taki kira, sosai takeso taji muryanshi amma da alama bazatajishi ba, wayarta ta dauko ta zuba number Anwar ciki tayi save da MY SOULMATE💕💘💋 sannan ta ajiye wayan tareda kwanciya dan ta biya bashin baccin da batayi ba a daren jiya not knowing Anwar na chan yana jinyar zuciyarshi saboda rashin kiranta.Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page