KAWUNA CHAPTER 7

KAWUNA


CHAPTER 7
“Abeedah!” Da sauri ta ɗago jikinta babu inda baya shirin soma rawa, ganin mai kiran na ta ya sanƴata daɗa firgita. shikenan fa ita yau tata tazo daf da qarshe! a iya kacin tunaninta Hajia Nenne Jia ta ankara da rashinta a cikin gidan shi ya saka yanzun ta ma ta iriyar kiran nan, babu haufi muddin Hajia Nenne ta tambayeta Ina taje jia a ka nemeta a ka rasa toh kuwa babu shakka Hammad zai kamata hannu dumu dumu. kallonta sosai Hajia Nenne ta shiga yi kafin ta maida hankalinta kan Hammad wanda a wannan lokacin ya maida kallonsa kacokan bisa ga wayar hannunsa tamkar ba shi bane ya kira Abeedar ɗazun da ta tsaresa da idanuwanta har ya kasa haƙurin shareta har ta sanƴasa daka ma ta tsawa! ilai kuma tamkar ba shi bane yayi ma ta tsuri yana nazartar hannunta ba, hankalinsa ya mayar kawai bisa ga wayarsa. guntun tsaki Hajia Nenne tayi don iriyar baƙin cikin ganin Hammad zaune a yau ma da ransa, ganin bata ishesa kallo ba ya sanƴata maida hankalinta kan Abee ta ce ” mai ya sami hannunki?” daram Abee taji zuciyarta ya bugu sosai ta seta kanta sa’anan taqi kallon gefen Hammad gudun kar shima yayi wani zargin, ɗan guntun murmushi ta yafawa fuskarta kafin ta ce ” Hajia……..” “Alhaji barka da safiya” ta tsinkayo muryar Hajia Nenne, da sauri ta matsa da baya tana ajiyar dogon lumfashi a hankali don ba ƙaramin cetonta Allah ya yi ba, tabbas ita kanta a lokacin bata san mai harshenta ke shirin faɗawa Hajiar ba gami da abin da zata ce mata ya sami hannun na ta ba. Daddy da ida sa saukowar sa kenan daga stairs ya murmusa ya na amsa gaisuwar Hajiar kafin yayi wa kansa mazauni a ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin fuskarsa a koda yaushe a sake ɗauke da annuri, Abeedah ta gaida sa ya amsa yana tambayarta shirin fara zuwa office Yau ta ce masa a shirye take ya ce Allah taimaka ya bada sa’a ta amsa da Ameen kana ta wuce sama don gyara ɗakin Daddyn, a hankali Hammad ya dubi Daddy ya ce ” Daddy barka be fajiri (Daddy barka da Safia),murmushi Daddyn yayi ya amsa ma sa “Barka en dai Moallahidi (barkan mu dai Moallahidi)” daga nan Hajia Nenne tayi serving ɗin Alhaji suka soma yin kalaci ba tare da kowa yayi magana ba har suka ƙare ci, dede nan kuma Abee ta fito hannunta riƙe da briefcase ta kawowa Daddy murmushi yayi ya ce “Af! Kinga na manta da shi abunki da tsoffi mun fiye mantuwa” dariya maganarsa ta baiwa Abee har sai da ta murmusa sosai, Alhaji ya ce “Hammad ka taimaka ka a jiye Abeedah a office all wasu bayanai will be sent to her through system, Sai kiyi going through kigani Allah taimaka ya bada sa’a” Abee ta amsa da “Ameen” daga haka Daddy ya miƙe don Yau 8:30am zai shiga meeting, Hajia Nenne ta miƙe don yi masa rakiya. Dining area ɗin ya rage daga Hammad Sai Abee, ita kuwa ta kasa koda ƙwaƙwarar motsi a wajen tsayawa kawai tayi kanta a ƙasa tana jiran jin amsar da zai ba ta amma shiru kake ji kamar an shuka dusa! tafi ƙarfin mintuna 4 a haka bai ce da ita uffan ba haka zalika bai motsa a inda yake ba hankalinsa na a kan wayarsa kawai yana chatting, ran Abee ne ya soma ɓaci (kunsan halin mutuniyar taku da saurin zuciya 😂don ma anjima ba’a dawo asalin Abeen ba yau oga Hammad na shirin taro Mach!😂) mai yake nufi? ko zai ce bai ji sa’adda Daddy Ke cewa shi zai ijiyeta a office ɗin bane? ita fa a kafatarin rayuwarta bata taɓa haɗuwa da mutum kamar wannan Hammad ɗin ba, mutum sam baka gane masa baka taɓa sanin gabansa balle bayansa, a duniyarta ta ɗauka babu wanda ya kai Salman miskilanci, ji dakai, rashin magana, iya ɗaukar wanka, a na ta tunanin samsam babu namijin da zai iya kamo ƙafar Salman a duk iriyar abin da ta lissafo sai dai kash a se tunaninta ba haka bane don tazo ta taras da wanda yaci tutar tsere sa a kota wani fanni, a iya nazartar Hammad da ta yi shi mutum ne murɗaɗe, miskilalle,mai kuma wuyar sha’ani zata iya rantsuwa da dukkanin sunayen Allah tsaf zata iya lissafa adadin maganganun da Hammad yayi a cikin gidan nan tun dawowarsa har kawo yau ita har mamaki take yi baya zazzaɓin rashin magana? Itakam bata tunanin zata iya awanni ba tare da ta motsa bakinta yayi magana ba koda ko a ce ciwo take yi. Tunanin ko ta yi masa magana tayi amma taga babu fuskar yin hakan don haka taja bakinta tayi shiru ta kuma zuba masa na mujiya! “go dress up properly (jeki saka kaya madaidaita)” shine kawai abin da kunnuwanta suka iya jiyo mata, bin kayan jikinta tayi da kallo tana nazartar mainene laifinsu? wani zuciyar ne ta raya mata ” da uniform ɗin aiki zaki je masu office?” Hakan ya sanƴata saurin juyawa tabar part ɗin Daddy ta wuce nasu part ɗin don canza kayan jikin na ta.

Story continues below


“Abeedah! Ke kuwa ina kika shiga jia muna ta naimanki ?” Taji muryar Faɗimec wacce harga Allah tama manta yaushe rabon da su zauna suyi maganar tsawon mintuna 3, cak ta tsaya kafin ta juya a hankali tana ƙare wa Faɗime kallo wacce itanma Abeedar take nazarta, ganin kamar kallon tuhuma Faɗime ke yi ma ta ya sanƴata saurin cewa ” Hajia ta aikeni, kinsan yau ce ranar fara aikin nawa a Company ɗin Alhaji” tayi mata ƙarya gyaɗa kai Faɗime tayi cike da gamsuwa kafin ta ce ” da kuwa har zamu cigiyar ki wajen Hajia muka taras ta kori kowa a part ɗin ta sa’annan ta jaddada ma na a kan kar wanda yayi yunƙurin shiga part ɗin ta a jiyan har sai safiyar yau” mamaki Abee ta shiga yi gaskia Allah yayi matuƙar cetonta tabbas ta sani da anci galaba a kisan Hammad da babu abin da zai hana Hajia Nenne sanin bata a cikin gidan amma dukkanin godia na ga Allah don shi ya tsara komai a yadda ya so imani sosai Abee taji yana shigarta don Ubangijnta ya kasance mai taimakonta a duk sa’adda ta durƙusa ta naimi taimakonsa kuma taƙara jaddada wa kanta Allah maji roƙon bayinsa ne.
Tafin da taji Faɗime tayi mata a fuskarta ne ya sanƴata dawowa daga duniyar tunanin da ta afka “Abeedah wooo, lafiyarki? tunanin mai kike yi?” da sauri Abeedar ta kallota sa’annan ta ce “am….am…. Kika ce mai? oh a’a ba tunani na ke ba oh Allah kinga bari nayi maza na canza shiga ana jirana a waje” daga haka tayi saurin juyawa ta nufi closet don sauya kayan jikin na ta. Da idanuwa kawai Faɗime ta bita da shi tana mamakin sauyin Abeedar a cikin kwanakin nan, juyawa tayi tabar ɗakin tabar Abeedar na canza kaya.
Sanƴe take cikin wani doguwar riga Black colour tayi nodding da milk gele sa’anan ta sanƴa wani koren rigar sanƴi mara nauyi kasantuwar sanƴin da’ake yi a cikin garin ta Adamawa. ƙare wa kanta kallo ta shiga yi a cikin mirror tana yaba iriyar kyawun da rigar yayi wa jikinta, sosai kayan suka amsheta murmushi saɓe a samar fuskarta ta ɗauki turare ta fesa kaɗan ta ɗauki handbag ɗin ta ta rataya ta fito oh Allah ta furta ganin Hammad na shirin shiga cikin motarsa, kyau iya kyau yayi mata sanƴe yake cikin ƙananun kaya wanda ta lura sam baya shiri da manƴan kaya shikam, da sauri ta ƙara so wajen motar ja tayi ta tsaya tana tantance inda ya ka mata ta wa kanta mazauni, ganin shiru ba ta da niyyar shigowa ya sanƴasa soma tayar da motar don bai da lokacin shirmenta da sauri ta ɓalla murfin motar baya zata shiga taji ya daka ma ta tsawa wanda yaso tsorata haiƙun, “my friend are you stupid?ni direbanki ne?” Da sauri cikin daburcewa ta koma gaba ta zauna Amma stupid da ya kirata Yayi matuƙar tsaya mata a rai tunda take a rayuwarta babu wanda ya taɓa danganta ta da kalmar stupid hakan yaso ɓata ranta sosai har tayi niyyar mayar masa da martani sai kuma ta fasa tuno dalilin zuwanta garin nan da kuma alkawarin da ta ɗaukar wa Mancy na ƙin faɗa da kowa, wannan shine kawai dalilin da ya sanƴata kame bakinta ba tare da ta ce da Hammad ɗin ƙala ba har suka bar harabar gidan, tafiyar kurame ce ke gudana a tsakaninsu babu mai ce da ɗan uwansa ci kanka, Abee kuwa gefen window take dubanta shi kuwa Hammad hankalinsa kacokan na kan tuƙinsa da yake yi da kuma tunanin inda yarinƴar nan take, taci abinci? ta sha magani? ya jikinta? Babu zazzaɓi? wannan sune tambayoyin da yake yi wa zuciyarsa har suka isa WASACO, parking yayi haɗeda da kashe motarsa yayi unlucking motar da hanzarinta ta sanƴa hannunta zata buɗe ƙofar motar don a matuƙar takure take zugin daya ratsa ilahirin jikinta shi yayi azamar sanƴata janƴe hannunta daga maɓallin murfin motar da sauri tana furta awwwsh, waigowa Hammad yayi yana kallonta wanda ita ɗin ma shi take kallo sunfi mintuna uku a haka suna kallon juna kafin ƙwanƙwasa ƙofar motar da a ka yi ya maida su duniyar mutane, zuge glass ɗin motar Hammad Yayi don ganin waye PA ɗin sa ne da murmushi ɗauke a samar fuskarsa ya ce ” good morning sir” gyaɗa kai kurum Hammad yayi kafin ya buɗe ƙofar ya fito itama Abee ta fito jikinta duk yayi la’asar don tana shakkun iriyar kallon da Hammad yayi mata ɗazun anƴa be gano ta ba kuwa? ” Muje ko?” Taji PA ɗin sa yana faɗa gyaɗa kai tayi kurum tabi bayansu sumi-sumi. Tafiya mai ɗan nisa kaɗan sukayi ita da PA ɗin Hammad don shi suna shiga ya haura stairs ɗin farko don tanan hanƴar na sa offishin yake, ita kuma PA ɗin ya ce ta biyosa ya nuna mata nata offishin a haka suna tafe tana mitar halayyar Hammad in Kuma ta tuna dama tun fil’azal ba son aikin nata yake a cikin Company ɗin ba sai ta kame bakinta tana turo baki waje. “Ma sha Allah ” shine abin da bakin Abee ke furtawa sosai office ɗin yayi matuƙar yi mata kyau komai da akwai a ciki komai kuma nazaune a mazauninsa very neat. PA ya ce ” nan shine office ɗin ki Madam, In kina da buƙatar wani abu ki kira ta landline in sha Allah we will be at your service Welcome to WASACO Company ma’am!” Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi itama Abeen murmushi ne saɓe a saman fuskarta ” thanks You soo much” ta faɗa a lokaci guda tana juyawa tana ƙare wa ofishin kallo cike da jin daɗi wanda har ta kasa ɓoye hakan take nuna sa a fili, girgiza kai kurum PA yayi kafin yayi mata sallama ya tafi, ita kuwa Abee bama tasan da ficewarsa ba don ta lula duniyar yabon office ɗinta. Hannu ta sanƴa zata ƙwame gilashin fuskarta da hanzari ta mayar tana tunanin ƙilan akwai CCTV Camera a cikin office ɗin sam zuwanta na farko bazai zamto silar tunuwar asirinta ba ta raya hakan a cikin zuciyarta.

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

3days later
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar wa Abee da daɗi ba daɗi, a kullum tana zuwa office tayi aikinta in lokacin tashi yayi direba yazo ɗaukar ta, a cikin kwanakin ne kuma Alhaji yayi tafiya zuwa china dan shigo da wasu kayayyakin Company zuwa Nigeria, tare da Hammad suka tafi inda zasuyi sati ɗaya kafin su dawo, nan fa gidan ya koma gidan jia duk da yanzun Abee ta lura abokanayen Asma’u da Faruk ba kasafai suke zuwa ba kuma da zarar sun kunna waqa Hajia Nenne ke shigowa ta musu rashin mutunci ta korasu don ba sosai take ɗasawa da kannen na ta ba a yanzun tun faruwar lamarin kisan Hammad. Mamakin Abee ɗaya har yau Hajia Nenne bata taɓa yi ma ta magana a kan aikinta ba tun ranar da a kayi maganar a falon Dady bata sake jin Hajia Nenne ta tunkareta da wani batu dangane da aikin ba, abin sai yake matuƙar bata mamaki dalili kuwa Alhaji da bakinsa yace Hajiar ce ta buƙaci da a bata aikin toh mainene manufarta na hakan? Allahu a’alam shine Amsar da a kullum Abeen ke baiwa kanta. Zaune take a kan kujerar office ɗin ta sanƴa system ɗin ta a gaba tana daddanawa daga ganinta kasan tana abu mai matuƙar muhimmanci ne a kan system ɗin, ƙwanƙwasa ƙofar dataji anayi ne ya sanƴata ɓata rai kaɗan don bata so abin da zai ƙaseta a kan abin da take yi a ayanzun da kyar ta bada izinin shigowa ba tare da ta ɗago don ganin waye ba, ci gaba da ayyukanta kawai tayi, gani tayi an ajiye mata wani farin takadda don haka ta kallo takaddar sa’annan ta kallo wanda ya ajiye mata shi Faruk tagani tsaye a kanta yana ƙare ma ta kallo, da sauri ta shiga gaisar da shi tana mamakin mai ya kawo sa office ɗinta sa’annan mainene a cikin farar takaddar daya bata? taɓe baki yayi ya amsa gaisuwarta a daƙile kafin ya ɗaura da faɗin ” if you done reading muna jiranki” daga haka ya sanƴa kansa yayi ficewarsa a office ɗin ya bar Abee a daskare a zaune tana mamakinsa da kuma mamakin kalamansa “if you are done reading muna jiranki” suna jiranta? Na mai kenan? Saurin ɗaukar takaddar tayi ta warware ta soma karantawa kamar haka………
Ɗaukar takaddar tayi ta warware ta soma karantawa kamar haka ” Secret meeting at stair 3 office 109 holding up now!” Shine abin da ta gani rubuce a cikin takaddar, mamakine yayi azamar dabaibaye saman fuskarta”Secret meeting?” Na mai kenan? Wani meeting ne kuma secret meeting? don a iya saninta dai ba’a holding kowani meeting sai ƙarshen wata yau kuma ko tsakiyar wata ba’a shiga ba, Kuma iya saninta komai da komai da ya danganci Company ɗin nan an tura mata ta System Kuma ta nutsu sosai ta karanta komai da komai sa’annan kuma ta fahimci komi dangane da abin da ta karanta amma samsam koda wasa bata ci karo da wani abu wai Secret meeting ba! Tasss taji ƙirjinta ya buga tunawa da tayi Hajia Nenne tana haɗa taron meeting a kowacce sati su tattauna ita da mutanenta da suke haɗa kai wajen cutar da kakanta”innaalilahi wa’inna ilaihir rajiun kar dai wannan mata abin da take son jefani ciki dama kenan ta sanƴa Alhaji bani aiki a cikin Company ɗin nan?” Tunani sosai Abee ta shiga yi tabbas sai tayi dagaske, yanzun ne ya kamata ta ɗaura ɗammarar aikin da ya kawo ta cikin garin Adamawa. Amma taya kenan zata fara? Mai Hajiar ke shirin tsomata a ciki? duk wa’innan tambayoyin bata da amsarsu har sai taje wajen meeting ɗin sa’anan zata sama amsoshin tambayoyin ta. Da sauri ta miƙe tana gyara mayafin kanta kafin ta ɗauki wayarta dake kan table ta fito cikin offishin jikinta duk a mace. A haka ta idasa haurawa saman benen da sai sadata da Offishin da ake gudanar da meeting ɗin, tsayawa tayi cak a bakin ƙofar tana ayyana abubuwa dayawa a cikin ƙwanƴarta, addu’oi kawai ta shiga yi a cikin zuciyarta kafin ta sanƴa hannu zata ƙwanƙwasa ƙofar offishin kenan taji anbuɗe ma ta da sauri taja hannunta da baya tana kai dubanta ga mabuɗin ƙofar, PA ɗin Hammad ta gani hakan ya sanƴata ɗan tsorata, toh kodai meeting ɗin na duka mutanen Company ɗin ne? Shiyasaka ma taga PA ɗin Hammad a cikin su? “Mu shiga ko?” Taji ya faɗa ma ta, da idanuwa kawai ta iya binsa tana kuma mamakin ganin iriyar murmushin da yake sakar mata, a haka suka shiga cikin offishin sanƴin AC da ƙamshin mabanbantar turaruka suka yi azamar dabaibaye ƙofofin hancinta, da idanuwa ta shiga bin dukkanin mutanen dake a zaune a cikin offishin babu ko shakka dukkanin jinsin da take gani a zaune a wannan wajen suna ɗaya daga cikin manƴa-manƴan accountants da directocin Company ɗin Alhaji, kai dubanta tayi wajen mutanen dake a zaunen tana ƙare masu kallo wanda su ɗin ma ita suke kallo fuskokinsu ɗauke da ma’anoni daban daban wanda Abee ta gaza fahimtar ma’anar hakan, hango wani kujera da tayi taga a juye ya sanƴata ƙurewa wajen kallo don ta tabbata wanda ke a zaune a kan wannan kujerar shine ko ita ce oga kwata-kwata na wannan taro da’aka haɗa. A hankali ta ga Faruk ya miƙe daga inda yake zaune ya doshi inda wanda ke zaune a kan wannan kujerar dake a juye da baya, ɗan durƙusa wa yayi kaɗan bakinsa ya soma motsa wa da dukkanin alamu dai magana yake yiwa wanda ke zaunen, ɗago da hannunta na hagu tayi wanda yake ɗauke da warwaron gwal wanda hakan ya sanƴa Abee gasgata cewa mace ce zaune a wannan kujerar, alama tayi wa Faruk da hannun wanda yake nuni da yaje ya zauna hakan ya sanƴasa risina wa kafin ya juya ya koma mazauninsa. “Zauna!” Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Hajiar tana bata umarnin zama, a daburce Abee ta soma neman wajen zama har tana harɗewa, dede da zamanta yayi dede da soma juyar da kujerar da take zaune a kai, a hankali ta idasa juyar da kujerar har ta kammala inda fuskarta da jikinta suka bayyana, ras Abee taji gabanta ya Faɗi “Hajia Nenne!” Ta furta a cikin zuciyarta, murmushi Hajiar ta shiga sakarwa Abeen wanda yake ɗauke da ma’anoni daban daban wanda Abeen ta gaza fahimtar ma’anar hakan, bata kaiga yin wani tunanin ba ta tsinkayo muryar Hajiar na ma ta maraba da zuwa ” Welcome to Secret Folks LTD Abeedah Usman!” Rufruf taji mutanen cikin offishin sun fara yin tafi har sai da Hajiar ta dakatar da su kana suka tsagaita, ita dai Abeedah da idanuwa kawai take iya bin su don a zahirin gaskia in ta ce bata tsorata da wannan al’amarin ba tayi babban ƙarya, mai Hajia Ke son jefar da rayuwarta a cikine ita kuwa? So take itama ta shiga cikin jinsin muggan mutane masu fuska biyu ga Alhaji? mai ya saka take son jefa rayuwarta cikin hatsari?” Wannan sune tambayoyin da take yiwa kanta da kanta kuma ta gaza samun amsar su. ” Nasan zakiyi mamakin ko na ce kin ma riga kinyi mamakin ganina anan ko?” Taji Hajia Nenne ta watsa ma ta tambayar, shiru Abee tayi bata tanka ma ta ba don in dai mamakin ganinta anan ne sam bata yi ba don dama ta riga ta san ita ɗin mai ha’intar kakanta ne. “Ba abin mamaki bane Abeedah!” Hajiar ta kuma katse ta daga tunanin data afka, ta ci gaba da cewa ” a tunaninki Abeedah hakanan kina zaman zaman ki zan sanƴa mijina ya baki wannan babbar muƙamin a cikin wannan Company ba tare da kinyi tunanin cewa nayi hakan bane don zaki iya min amfani ba?” Murmushi ta ɗan yi kafin ta ci gaba da cewa ” Toh in har kinyi wannan tunanin Toh fa kinyi matuƙar yin kuskure, dalili kuwa shine ni Hajia Khadija ban saka an ɗaukeki aiki a cikin Company ɗin nan abati siddan ba har sai da nayi nazarin iriyar alfanun da zaki min inkin kasance cikin masu yimin aiki, Hammad yana ɗaya daga cikin mutanen dake tsaremin iska wajen aikata abin da na saka a kan gaba hakan ce ta kasance lokacin da sukayi asarar maƙudan kuɗaɗe Hammad ya sanƴawa accountant ɗin da yanzun kike riƙe da muƙaminsa ido, ganin muddin na bar Hammad haka ya ci gaba da bincikensa zai ɗano jirginmu ya sanƴani saka a maida accountant can wani branch ɗin daban, a farko nayi tunanin baiwa Asma’u wannan muƙamin amma sai nayi tunanin Hammad Zai yi saurin ɗago ni don haka ne nayi nazarin baki wannan muƙamin don naga iriyar yabonki da kuma yarda da Alhaji yayi maki, wannan shine dalilin da ya saka na tunkari Alhaji da maganar baki aiki a cikin wannan Company ɗin don ko ba komai ya yarda dake kuma zaiyi tunanin zaki kawo masa sauyi in kika fara aikin lura da sam kuɗi ba sa gabanki” tana kai wa nan ta tsagaita da maganarta ta, ruwa ta tsiyaya a cup ta sha kafin ta ɗora daga In da ta tsaya ” duk mainene ma amfanin yi miki wa’innan bayanan?” ta faɗi hakan lokaci guda tana mai kai dubanta ga fuskar Abeedar tana mai nazartar yanayin fuskar Abeen, wacce a wannan lokacin babu abin da ke yi ma ta yawo a cikin ƙwanƴarta face irin muggan halin Hajia Nenne “Anƴa matar nan zata ji ƙamshin aljanna kuwa? muguntarta yafi ƙarfin ƙwaƙwalwar mutum, amma da ni take zancen jin Abeedah kawai kike baki san wacece Abeedah ba, sannu a hankali zakiga yadda zan mayar da rayuwarki abar tausayi da allah wadai wanda ko en bayanki bazasu taɓa marmarin sake son ɗaurawa kansu burin cutar wani ba, wait and see how I will tarnish your image and reputation” Abee ta raya hakan a cikin zuciyarta, yanayin fuskarta kuma na nuni da tsoron Hajiar amma a baɗini ita kawai ta san abin da take shiryawa Hajiar a cikin zuciyarta. ” Ina ganin baki da wannan matsayin da zan zauna ma ina miki bayani tiryen-tiryen tamkar wacce nake son ta fahimci karatu, let me go straight to the point. Abeedah kin shigo cikin ƙungiyar Secret Folks LTD wanda baki da ranar fitansa har ƙarshen rayuwarki! Kin shigo kenan babu fita wanda muddin kikayi yunƙurin fita ko tona asirin ƙungiyar nan toh ko tabbas karki ƙara tunani na biyu ki faɗiwa kanki sunanki gawa! Yes gawa Ina nufin ranar da kika yi yunƙurin aikata ɗaya daga cikin abubuwan da na lissafo miki ranar zaki yi sanadin mutuwarki, bari na maimaita miki a karo na ƙarshe, kin shigo group (ƙungiyar) da ba’a fitan sa!” daga haka Hajiar ta kallo PA ɗin Hammad ta ce ” Hamisu zan bar Abeedah a ƙarƙashin kulawarka har sai ranar data fahimci komai dangane da ƙungiyar nan, any mistake that she makes it will definitely be divided with you so u have to be very careful!( Ko wani kuskure ta aikata ka sani za’a rabashi da kai kanka don haka kayi mugun taka tsantsan!).” “In sha Allah ma’am” Hamis (PA) ya bata amsa daga haka Hajia Nenne ta shiga yi ma sauran almunafukan masu fuska biyu (cewar Abeedah😂) bayanin aikinsu na gaba, wanda ya sanƴa Abee daskarewa tare da shiga cikin ruɗani ” kayan da Alhaji yaje exporting zuwa Nigeria na sanƴa an musanƴa ma sa da fake once don haka asarar da zaiyi ba ƴar kaɗan ba ce, Faruk gobe zai je can China inda zai amso mana asalin kayayyakin mukuma sai mu siyar mu adana kuɗin cikin asusun Secret Folks, a iya tunani na Hamis ka ce yanzun kuɗin first asusun Secret Folks yakai kimanin miliyan ɗari uku right?” “Eh Hajia hakan ne” “good so ina ganin wa’annan kayayyakin in mun siyar a ƙalla zamu sama sama da miliyan ɗari biyar ribar kuma zata haura miliyan 3 right” nan ma duka mazauna gurin suka amsa da “Yes” In ka cire Abee da ke faman binsu da idanuwa kawai, tana raya abubuwa mabanbanta dayawa a cikin zuciyarta. “Fine and good, 500k (dubu dari biyar) will be transferred to each and everyone of you at night!( Dukkanin ku za’a aika muku Naira dubu dari biyar yau da dare) zaku iya tafiya sai kuma haɗuwa na gaba” daga haka Abee ta ga sun minmiƙe suna ma Hajia Nenne kirari ko wannen su fuskarsa ɗauke da murmushi da jin daɗin kyautar da ta yi masu, haka take masu iriyar kyautar duk sa’adda ta bushi iska sukuma hakan ne ke sake basu azamar yi ma ta aiki a duk sa’adda ta umarce su kuma suke taka tsantsan wajen bijirewa umarninta. Kafin Abeedah ta sake wani tunanin taga kowa ya watse a cikin offishin, ya rage da ga ita sai Hamis wanda a yanzun Abee tsananin tsanarshi ke ɗawainiya da shi a hakansa tamkar bazai aikata ba zaka rantse shi mutumin Allah da annabi ne kai mutum mugun ice ne, mutanen zamanin nan samsam babu tsoron Allah da Manzonsa a cikin ƙwanƴarsu, yanzun babu abin da ɗan Adam ba zai aikata ba a kan kuɗi komaine kuwa indai zai sama kuɗi ko iyayensa ne zai iya bayarwa a kashe a sha jininsu yayi kuɗi abin da sai du’ai kawai. ” Kin shirya jin bayani?” Hamis ya katse ma ta tunaninta ballo ma sa harara tayi kafin ta ce cikin yaren turanci don tabbas ta sani inta fara yi ma sa balbali da indabur ɗin hausarta tsaf zata koma yi ma sa asalin hausa wanda zai iya saka ya gano ta ya san ita ɗin ba inƴamura ba ce hakan ya sanƴa ta soma yi ma sa magana da turanci ” wallahi kaji kunƴa, ji beka a haka kamar na Allah da annabi amma samsam babu ɗigon tsoronsu a cikin zuciyarka, kaji tsoron ranar da uban gidan naka zai lura da cin amanarsa da kake…..” Bai bari ta ƙarasa maganarta ba ya tuntsure da dariya har da riƙe ciki wanda hakan ya sanƴa Abee dakatar da maganarta, sai da yayi dariyarsa ma’ishi kafin ya tsagaita ya ce ” Hmmm ki kama bakinki In kina son tsira da rayuwarki, ni kaina i was Black Mailed exactly the way they black mailed u here today ( ni kaina Haka suka rinjaye ni da kalaman da suka miki a yau) har na bada haɗin kai karki ga laifina dole a kamin, kin kuwa san hatsarin bijirewa Mutanen Hajia Kuwa? zasu kasheki su kashe wanda ya sanki su kashe kowa naki duk ba abu bane mai wuya a hannunsu, kin kuwa san lokacin dana so bijirewa Mutanen nan sunyi yunƙurin kashe mahaifiyata da shi kansa oga Hammad? I was left with no option than to join them, so Koda wasa karkiyi tunanin ina cutar Hammad ne no! taimakonsa nake yes Ina taimakonsa ta hanƴar tseratar da rayuwarsa wannan shine dalilin da ya saka nake aiki a ƙarƙashin Hajia amma ki sani bani da ranar fita a cikin su haka zalika ba Ni da ikon sanarwa Hammad halin da na ke ciki don duk wani motsinki a ko ‘ina wallahi a tafin hannunsu kike yi, kin san mutane uku sun rasa rayukansu a dalilin son fita a wannan mahajar? Ki rufa wa kanki asiri kiba da kai da wuya kawai tamkar yadda kowa ya bayar, kuma karki yarda da kowa a cikin wannan Company ɗin don kowa da akwai wanda yake wa aiki kuma a ƙarshe kunnen mai kankat ɗin zai koma (Hajia Nenne) don haka kiyi yadda suka ce da ke kawai if kina da burin yin rayuwa mai tsayi , na barki lafiya!” Daga haka Hamis ya sanƴa kansa yayi ficewarsa a cikin offishin ya bar Abee zaune a daskare tana mamakin wannan abu, ita mai ya kamata tayi yanzun? na shiga uku ni Abeedah yanzun dole sai na shiga wannan ƙungiyar? Ya zanyi da rayuwata nikam? Ni da nazo ƙwatarwa mahaifiyata ƴancinta yau ni ce kuma zan bada haɗin kai wajen durƙushe war mahaifinta? anƴa In Mancy taji wannan labarin zata iya yafe min kuwa? Mai zan yi ni Abeedah? Allah ka kawo min mafita” shine abin da kawai Abee ke mitar nanatawa zuciyarta. Ranar kasa taɓuka komai Abee tayi har lokacin tashinta yayi ta koma gida duk jikinta a mace, wanka tayi kafin tayi sallan la’asar taci abinci ta koma ta kwanta tana tunanin abin da ya kamata tayi don kanta duk sai taji ma tamkar an kulle ma ta shi gamgam ba ta iya tunanin komai.
************************************************
Tunda yayi mafarkinta da ya buɗe idanu ya kasa komawa bacci ya kuma kasa runtsawa, a yanzun kam ya soma gasgata wa kansa cewa gamo yayi gamon ma da sarauniyar aljanu, don bayi da haufi in har mutum ce ita yaci a ce yanzun ta bayyanar ma sa da kanta, duba da tun sa’adda ya fara ganinta a Company da DAddy ya umarce sa da ya ba ta compliment card ɗin su a kan ta kira wani lokacin don sanin ko an fara ɗaukan ma’aikata, amma shiru babu kiranta babu alamar zata kiran tun yana tsumayin ganin kiran na ta har ya daina, a daa baya ɗaukar sabuwar lamba amma tun sa’adda ya baiwa Fareedah (Senorita) lambar card ɗin sa ya soma ɗaukar sabuwar lamba amma daidai da rana ɗaya bai taɓa jin mai muryarta ba ya kira wayar ta sa. Shiru yayi yana nazari, nazarin fuskarta, nazarin muryarta, nazarin yadda ta yunƙuro ta taimaka ma sa “Hammaaaaaad!” ya tsinkayo muryarta a Lokacin da tayi yunƙurin taimakonsa “wacece ke? who are you?” Hammad ya furta a hankali, yanzun kam ya gama tabbatar wa kansa ya faɗa tarƙon ƙaunar wannan baiwar Allan.
#wannan kenan!
*************************************************
2weeks later 3

STORY CONTINUES BELOW


Abubuwa dayawa sun faru a cikin satattakin da suka shuɗe, Abee ta gama yankewa kanta hukuncin amince wa da shiga ƙungiyar Secret Folks LTD inda tayi tunanin muddin ta shiga zata fara kamaa zaren sanin hanƴar da zata tona asirin Hajia Nenne, Kuma zata shiga jikin Hajiar sosai har sai ta sama ɗuwawun zama haiƙam a cikin zuciyar Hajiar yanda zata iya yi ma ta shige na fito ba tare da sanin Hajiar ba, zata bi komai sannu a hankali ta yadda mai karatu baya zato yanzun ne zata fara cikawa mahaifiyarta burinta In sha Allah jalla-jalalu zai dafa ma ta har ƙarshen lamarin nan. A cikin kwanakin da suka shuɗe abubuwa dayawa sun faru ciki ko harda asarar kuɗin da Alhaji yayi na shigowar Fake kayayyakin daya exporting daga China zuwa Nigeria hakan kuwa ba ƙaramin tayar ma sa da hankali yayi ma wanda har sai da hawan jininsa ya tashi har ƙarin ruwa sai da a ka ma sa, ranar Abee tayi kuka harta gode wa Allah. Ga shi dai tana da damar exposing (tona asiri)wanda yake aikatawa kankan na ta dukkanin al’amuran dake faruwa da shi amma sai dai kassh rayuwarta na a cikin kwale-kwale ne muddin ta aikata hakan a yanzun, ba mutuwarta take tsoro ba a’a abin da zaije ya dawo shine abin da yake matuƙar tsorata ta, shiyasa ka zata yi shiru ta kame bakinta na wasu ɗan lokaci kafin ta fasa kwai kowa ya huta ciki ko harda bayyana ma su asalinta, asalin wacece ita da kuma dawo da mahaifiyarta cikin ahalinta, tabbas Lokaci ƙanƙani kawai take jira wanda kuma a yanzun tana shaƙar ƙamshin zuwan ranar. Sosai Hajia Nenne kejin daɗin aiki da Abee don yanzun duk wasu shige da fice na cikin ƙungiyarsu sai Hajiar ta fara sanarwa Abee kafin ta sanar da kowa, hakan kuwa yana da nasaba da iriyar ƙwaƙwalwar da ta ga Abeedar na da shi muddin abu ya shige ma ta duhu tana sanarwa Abee zata kawo ma ta haske a ciki hakan ya sanƴata soma janƴo Abee sosai a jikinta, don har ɗaki sukutum ta sanƴa a ka baiwa Abeen a cikin part ɗin ta, Faruk da Asma’u kuwa yanzun ɗasawar ta su da Hajia ba kamar daa ba gwamma-gwamma ma Faruk duk wulaƙancin da take yi ma sa yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen shanƴewa ya mayar da komai ba komai ba, Asma’u kuwa barin ƙasar ma tayi gaba ɗaya a jiya ta koma Cyprus da zama zatayi wata uku kafin ta dawo, wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Hajia Nenne ba at least yanzun zata huta da banbamin Ma’uu a kan Hammad.
*************************************************
Agurguje plss🙄 (1month later, just azumi (kawai kuyi tunanin abubuwa dayawa sun faru a cikin watan, muyi muyi mugama labarin).

Sosai Hammad ya sanƴawa Abee ido a kan aikinta, dalilin hakan da ya soma yi kuwa shine lura da yayi abubuwan Company ɗin ma daɗa lalacewa yake yi, abubuwan da yayi tunanin zasu yi sauƙi ya ga sam babu abin da ke sauƙi a cikin lamuran sai ma daɗa asarar da suke yi a koda yaushe, a zamanta a Company ɗin yanzun kimanin wata ɗaya kenan sunyi asarar kuɗi yafi gabanin miliyan 30 zuwa 50, Daddy yanzun haka yana India ya miƙawa Hammad komai a hannunsa don a cewarsa ya gaji da wannan ɗin bin asarar da yake yi muddin ya cigaba da ganin haka toh tabbas hawan jininsa zaiyi mummunar hawa shiyasa kawai ya yanke hukuncin barin ƙasar ya koma India don hutawa. Hajia Nenne ranar harda haɗa ƙaramin walima ita da gayyanta (Secret Folks) suka ci suka sha, a cewarsu suna nasara kuma nasara a hannunsu yake, ranar Abee har zazzaɓi sai da ya so rufeta amma ya zatayi? Kullum cikin sallolinta babu ranar da zata sallame bata roƙi Allah ya kawo ma ta ɗauki cikin gaggawa ba, gashi yanzun ta lura da yadda Hammad ya sanƴata a gaba kullum sai ya saka ta tura masa komai data aikata a Company through system yayi nazarin su, duk da bai taɓa kiranta yayi ma ta magana a kan asarar kuɗaɗen da take gani Company nayi amma bata ɗaukan mataki a kai.

Yana zaune a kan kujerar offishinsa yana nazarin wasu abubuwa dayawa a cikin ransa, ciki ko harda tunanin yadda zai ɓullowa wannan al’amarin dake faruwa a cikin Company ɗin Alhaji, ya kasa sanin ko hasashen da yake yi gaskia ce ko a kasin hakan baya tunanin in bincikensa ya gano ma sa da sanƴa hannunwanta a cikin wannan lamarin zai iya yafe ma ta ba, yana ji a jikinsa yau ko mahaifiyarsa ce a ka samu dumu dumu da sanƴa hannunwanta cikin daƙulewar Company ɗin Daddy toh tabbas zai bada goyon bayan wajen hukuntata, amma ko waye da wannan ɗanƴen aikin yana gab da kama sa. Kamar wanda a ka mintsila ya miƙe da sauri yabar cikin office ɗin, da fitarsa yayi hanyar office ɗin Faruk komai ya tuna Kuma? Allahu a’alam sai ya juya da baya da zummar komawa offishinsa.
*****
” kada ki damu Mancy, In sha Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe!, Yanzun haka na faɗa miki Hajia Nenne ta matuƙar sakin jikinta dani, duk abin da take yi ko take shirin yi duk sai da sanina take aikata su,” ɗan shiru tayi tana jin abin da Mancyn ke faɗa mata daga na ta ɓangaren dariya ta kuma yi jin abin da Mancyn ke cewa “hhh Mancy ai dama hausawa sunce, ƙarshen alewa ƙasa! Ki saurara kawai yadda zanyi wa gidan nan rata-rata zasu gane shayi ruwa ne, baki da damuwa Mancy komai is going according to plan! Albarkanki Kawai nake buƙa………..” Maganarta ce ta sarƙe a maƙoshinta sakamakon jin muryarsa a dodon kunnenta. “munafuka!” da sauri ta waigo tana kallonsa a tsorace ta ce “Hammad!” da hanzari ta juya baya ta maida wayarta ga kunnenta ta ce “Mancy ina zuwa” daga haka ta katse kiran ta juyo tana kallon Hammad in Wanda zata iya rantsewa da Allah tunda take da shi bata taɓa ganinsa a iriyar wannan yanayin ba sai yau Lokaci guda ya riƙiɗe ya dawo ma ta wani daban, da kyar ta iya haɗiyar miyau muƙut don ta san yau kam ya gama ganota dalili kuwa hausar da yaji tanayi ɓaro ɓaro babu gaurancin da take sanƴawa a ciki yau. ” Ni ba munafuka ba ce” ta tsinta kanta da basa amsa kamar haka, haushinta, taƙaici, sune suka sama damar mamaye Hammad a wannan lokacin don haka cikin ɗaga murya ya ce ” da uban wa kike waya har kike basa sirrin gidanmu? har kike da bakin faɗin duk abubuwan da na ji kina faɗa, dama hausar ki zamzam kin iya kike indaburbur a ciki inkina wa mutane magana?!” Runtsa idanuwanta Abee tayi tana tunanin amsar da ya da ce ta ba sa, ” ba ki ji mai ma ce miki bane da uban wa kike waya?!” Ya faɗa da ƙarfi wanda har ya so firgita Abeen, amma sai ta dake haushin kalamansa yahau kanta, dan rashin mutuncinsa ma Mancy yake zagi saurin runtsa ido tayi kafin cikin zafin rai ta ce ” da ƴar gidan nake waya” kallonta yayi cike da mamaki ya ce “ban gane da ƴar gidan ba” dogon lumfashi Abee ta sauke kana ta kai dubanta ga Hammad ɗin wanda ke yi ma ta kallon data gaza fassara ta mainene tsana? Kyara? Oho Shi kaɗai ya sanin ma kansa, ” Tabbas da ƴar gidan ƴar Alhajin da ita nake waya!” Ji yayi maganarta ta, ta banza da wofi ce don haka ya hayayyaƙo ma ta ransa a matuƙar ɓace ya shaƙo kwalar rigarta, daidai kuma nan gefen hannunsa yayi mistake ɗin shafe kwalen fuskarta da ta yi tabo da shi gani yayi kwalen fuskarta ta ya mauɗe, tsayawa cak yayi yana kallonta itama Abeen shi take kallo amma ga mamakinsa samsam babu alamar tsorata a tattare da ita don haka yayi azamar sake sanƴa hannunsa yana taɓa kwalen tabon fuskar na ta yaga abu dai mauɗewa yake, cike da mamaki ya ɗago ya na kallon ta ya ce ” dama ƙarya kikeyi? dama ke ba yare ba ce kamar yadda kowa ke tunani?dama uban me ya kawo ki cikin gidan Alhaji?” Taɓe baki Abee tayi don yanzun kam ta soma ƙulewa da shi don haka ne ma ta ce ma sa ” Ni ba ƙarya nake yi ba, hasali ma aiki ne ya kawo ni cikin gidan Alhaji Abubakar Dala!, Amma ina zuwa” ta faɗi ma sa hakan daidai da barinta wajensa ta wuce cikin toilet, Shi kuwa Hammad ya tsaya katsaƙe yana ganin ikon Allah tamkar wanda a ka cirewa lakka a jiki haka ya tsinci kansa “aiki take yi?” Shine abin da ya ke tambayar kansa, fitowa tayi daga cikin toilet ɗin hannunta riƙe da towel tana goge ragowar ruwan fuskarta, tsayawa tayi ɗan nesa da Hammad ɗin kafin ta soma cire towel ɗin a samar fuskarta ta ce ” Baffah Hammad!” daidai nan shima ya ɗago ya sauke kekkyawar fuskarsa a saman na ta fuskar, rasrasssssss ƙirjin Hammad ya shiga buguwa cikin karkarwa ya ɗaga yatsan hannunsa yana nunata cikin rawar murya ya ce “…………
Baffah Hammad!” daidai nan shima ya ɗago ya sauke kekkyawar fuskarsa a saman na ta fuskar, rasrasssssss ƙirjin Hammad ya shiga buguwa cikin karkarwa ya ɗaga yatsan hannunsa yana nunata cikin rawar murya ya ce “Senorita?!” Babu abin da Abee ke iya karanto wa a samar fuskarsa face ruɗu, mamaki, jin daɗi da kuma wani abu da taga kwayar idanuwansa na jifar ta da shi wanda kuma ƙwaƙwalwarta ya gaza fahimtar ko fassara mai saƙon ke nufi, kallon kallo kawai suka tsaya yi a tsakaninsu har tsawon mintuna da mutum baya tsammani, ko wannensu da abin da zuciyarsa ke ƙissa ma sa dan gane da ɗan uwansa, a gefen Hammad kuwa kasa tunanin komai yayi na wasu mintuna kafin a hankali ƙwaƙwalwarsa ta soma labarta ma sa komai da komai tamkar a Film, tabbas yanzun ya yarda ya kuma gasgatawa kansa cewa Senorita mutum ce ba aljan ba, sa’annan kuma ita ɗin ce dai yau a gabansa. Abubuwa dayawa Hammad ya shiga nazari akai ciki ko harda lokutan da yake ganin Abee ɗin a matsayin ƴar aikin gidansu sa’adda ya hango shatin jini shimfiɗe ɓaro ɓaro a samar hannunta buguwar da zuciyarsa ke yi ma sa a duk lokutan da ya ji kusancinta a waje, fama ciwon hannunta da tayi lokacin da ya fara kaita aiki, kenan wannan inƴamurar dai ta gidansu itace yarinƴar da ke shawagi da zuciyarsa? itace dai wacce ke adabbarsa a yanzun? Ita ce ɗin dai wacce ya baiwa jininsa, yanzun haka akwai jininsa dake tafiya a cikin jikinta? kuma ita ce tayi azamar taimaka ma sa a lokacin da rayuwarsa take daf da tafiya? Wannan na nuni da cewa kenan ita ɗin ta san wa’inda ke farautar rayuwarsa? but how could she? wacece ita? wa take yi wa aiki? Kuma mainene dalilinta na ɓidda kamanninta?, Aikin mai ya kawo ta gidan Daddy? Shin dama duk zamanta a cikin gidan Daddy dama da fuska biyu ta zo? Hajia Nenne ta san da hakan? koma dai ita ce ta sanƴata aikata hakan? Toh ta ce ma sa da ƴar gidan Alhaji take waya? Wa take nufi kenan? Bayan tun tasowarsa a cikin gidan Alhaji a ke shaida ma sa da cewa ƴar uwarsa ta rasu!. Shiru yayi yana jin abin da zuciyarsa ke kuma ayyana ma sa, dole ya san wacece ita sa’anan dole ya kawar da duk wani sonta a zuciyarsa a yanzun don sanin ainihin abin da ya sanƴata kasance wa mutum mai fuska biyu!. Ita kuwa Abee ɗan mamakin sunan da ya kirata da shi ta shiga yi yau dai ta sani ya riga ya gane ita ɗin ce ta taimakesa a watannin da suka wuce sa’annan ita ɗin ce dai tazo naiman aiki a lokutan baya wajensu, ta sani dole yayi zaton ita ɗin mai fuska biyu ce amma ya ta iya?kar yaga laifinta samsam, sa’annan muddin yayi saurin yanke ma ta hukunci ba tare da ya saurareta ba toh harga Allah bai yi ma ta adalci ba, sake ɗagowa tayi tana kallonsa a hankali kuma ta shiga faɗin ” Senorita?” Jin sunan da ta kira ya sanƴasa saurin dawowa cikin hayyacinsa, kallonta yayi yaga mamaki shimfiɗe a samar kekkyawar fuskarta wanda a kullum duniyar Allah yake muradin sake sanƴata a idanuwansa yau kuma gata a gabansa har sun ɗauki kimanin mintuna 30-40 a tare, amma dai ita ɗin mai fuska biyu ce , tuno da hakan da yayi ya sanƴasa haɗiyan ransa ya dawo aynihin Hammad ɗin sa, annurin fuskarsa ya ɗauke ɓat ya dawo tamkar namijin zaki, wanda hakan yaso baiwa Abeee tsoro amma sai ta dake tana binsa kawai da kallo cikin kakkausar muryarsa ya ce ” kin shirya gayamin gaskia ko sai anjimu da ke, uban wa kike ma aiki a cikin gidanmu?” Ya ida maganarsa cike da gadara, Abee kuwa ɗan taɓe baki tayi kafin ta ce ” tabbas ni ɗin mai laifice don na kasan ce mutum mai fuska biyu, amma hakan bazai baka damar gayamin maganganu son ranka ba, ina da tabbacin cewa muddin kasan koni wacece da kuma dalilina na zuwa nan garin har rana irin tayau da Allah yayi zaka gane ni ɗin ba aikatau ya kawoni gidan mahaifinka ba hasalima aiki nazo yi a kan shi mahaifin na ka, ina ganin ba zaka zauna kana cimin fuska har haka ba!” ta ida maganarta rai Kwance, kasaƙe Hammad ya tsaya yana kallonta kawai, confidence ɗin ta shi yafi ɗaure ma sa kai, ita ɗin wacece? zai iya rantse wa da Allah tunda yake a rayuwarsa babu macen data taɓa gaya ma sa maganganu har haka sai ita zai kuma iya cewa bai taɓa ganin mace mai confidence Kamar ta ba, ko Asma’u dai da ta girmema sa tana matuƙar shakkar yi ma sa magana amma wannan ƴar yarinƴar da yake tunanin zai iya yin ƙanwa ta kusan 4 da ita, ita ce tsaye tana faɗi masa magana ranta kwance babu shakkar komai a ranta. “Am asking you for the very last time, who are you?and wat are you doing here?!(zan tambayeki na ƙarshe wacece ke? Mai kike yi anan?)” Ya faɗa wannan karon har tana iya hango yadda jijiyoyin kansa suka ɗaga tsabagen bai son magana mai tsawo ko ta ce bai saba ɗaga murya wajen magana ba, murmusawa kawai Abee tayi kafin ta ja dogon lumfashi sa’annan ta a jiye towel ɗin hannunta a kan stool, tattaki ta soma yi a hankali har ta isa kan kujera da yake ɗan nesa da Hammad tayiwa kanta mazauni, kana a hankali ta ɗago manƴan idanuwanta ta sauke su a kan fuskarsa, kaɗa idanuwanta tayi wanda harga Allah sai da Hammad ya so tsintar kansa a wani hali na daban, hakan ya sanƴasa saurin ɗauke idanuwansa a kanta ya mayar gefe, a lokaci guda kuma yana daɗa haɗe ransa tamau tamkar wanda aka aiko wa mutuwa, maganarta ce ta maido hankalinsa gareta yana mai sauraron daddaɗar muryarta a karo na biyu. ” kamar yadda ka sani Baffah Hammad, ni dai sunana Abeedah Usman Ɗambatta ko a gaske, ban canza sunana ba sai dai yare kawai da na canza, da kuma kamannin fuskata da na ɓidda, hakan kuma yana da nasaba ne da hatsarin da nayi tunanin zan shiga ciki matuƙar ban ɓidda kamannina ba, wannan shine dalilin da ya saka na ɓidda kamannin fuskata nayi kwalen tabon inƴamurai a fuskar tawa dalili kuwa, Hajiar gidan Alhajinka ta ce bata buƙatar hausa Fulani sunai ma ta aiki sai dai yare, hakan ba ƙaramin daɗi yamin ba dalili kuwa shine muddin na sake na shiga cikin gidan Alhaji Abubakar a haka na” 2

STORY CONTINUES BELOW


ta ɗan tsagaita da maganarta tana masa nuni da fuskarta kafin ta ci gaba da cewa

” toh kuwa tabbas watarana Alhaji, ko hajia,ko Asma’u ko Faruk, zasu sanƴa a yarin tambaya a kan fuskar tawa hakan kuma ya na da na sa ba ne da iriyar kamannin da nake yi da mahaifiyata, zasu iya hango tsantsan kamanni mahaifiyata a nawa fuskar wanda In har ba zaka manta ba ranar dana soma tunkararku kai da Alhaji a nan Company ɗin da ainihin fuskata sai da Alhajin ya ce inai ma sa kama da wata wanda har ya koma ga Allah baya burin sake sanƴata a cikin idaninsa, ka tuna ba?” Ba ta jira amsarsa ba ta cigaba da maganarta ” mai kake tunanin zai faru kenan In har na shigo cikin gidan a haka na? baka tunanin za’ayi saurin harbo jirgina? Hajia ƙilan ma ta saka a binciko ma ta diddigina har ta san cewa iyayena da tayi tunanin sun mutu da daɗewa ta iske su a raye, baka tunanin cewa zata saka a kashe su sa’anan nima ta saka a kashe ni? Don ita kam kisa ba abu bane mai wuya a wajenta ba, a mintuna da basu wuci tunaninka ba Hajia Nenne Zata iya saka wa a raba jikin mutum da lumfashinsa kuma tsaf zata kwana lafiya ba tare da shakkar komi a cikin ranta ba!.”  Zuwa yanzun kam Hammad ya soma gajia da dukkanin wa’innan dogon sharhin nata, a ganinsa samsam baida buƙatar sanin dalilinta na ɓidda kamanninta, shi kawai burinsa bai wuci ta faɗi ma sa dalilin zuwanta gidansu da fuska biyu ba kuma aikin mai ya kawo ta cikin gidan ba, hakan ya sanƴasa saurin katse ma ta maganarta In da ya ke cewa “go straight to the point malama! Aikin mai ya kawo ki gidan Alhaji and who are you working for?” Iya kufluwa Abee ta soma ƙulewa, inhar banda yana a matsayin Baffanta har yana da matsayin da zai zauna yana nuna ma ta attitudes? (Hali) Bata wankesa daga samar sa ba har ƙasa? girgiza kai tayi don bata ga laifinsa ba dama duk wani ɗan Yola akwai sa da matuƙar girman kai (cewar Abee ba Ni Ayshkhair ba!🙄😂) sabida haka ba zata ga aibun sa ba. ” Working for my mom!(Aiki wa mahaifiyata)” sake ɓata rai Hammad Yayi kafin ya ce ” and whose your mom?(waye mahaifiyarki?)” Lumshe idanuwanta tayi kana cikin sassauta murya ta ce ” Haleematu Abubakar Giɗadɗo Dala!” Jaa da baya kaɗan Hammad yayi fuskarsa sam ba zaka iya tantance halin da yake ciki ba, amma Abee na iya cewa tana iya karanto tsantsar firgita, mamaki, farin ciki shimfiɗe a reaction ɗin sa (yanayin da ya shiga), a hankali kuma taga ya soma takowa inda take har ya kusantota sosai, dum-dum dukkaninsu biyu suka tsinci zuciyarsu na bugawa da sauri da sauri, hakan sai ya soma tunawa Abee Sir Salman wanda harga Allah ta manta yaushe rabon da ta tuna sa a cikin lamuranta, tamkar kiran sallan assalatu haka taji son da take yiwa Salman ya ɓace ɓat a cikin zuciyarta, abin har mamaki ya ba ta a wannan lokacin don a iya tunaninta ta za ta ba za ta taɓa iya daina son Salman ba, kuma ba zata taɓa son wani ba takwankwacin yadda ta so Salman ba, a yanzun kuma wannan buguwar da taji zuciyarta nayi sai ya tuna ma ta lokutan da zuciyar na ta ke bugawa a duk sa’adda ta kasance waje ɗaya tare da Salman, mai hakan ke nufi kenan? Ta tsinci kanta da tambayar zuciyarta amma kafin tagaiga samun amsar tambayarta ta, Hammad Yayi azamar daƙile tattaunawarta da zuciyarta. ” Now tell me, Mai kikace? How do you knw Adda Halee? Ina take yanzun? Are You really her daughter? Wow! Ya a kayi nagaza ganin kamannin fuskar Addana a naki fuskar? kai no wonder kike matuƙar yimin kama da wata wanda nasani shekaru masu yawa da suka shuɗe, tabbas i couldn’t recognise you that much don tarayyata da Adda Halee ba mai yawa bane i was 5yrs when she live and ance mana ta rasu, but mahaifiyata always do tell me harta koma ga mahaliccinta cewa Haleematu bata mutu ba tana raye na naimeta a duk inda take wata rana zamu sameta zata dawo garemu, ashe my mom was absolutely right Adda Halee is alive harma tana da ƴa mai matukar kama da ita, tell me ASAP (ki faɗa min da sauri) ina Adda Halee ta shiga for almost pass this year’s now? Ina take yanzun ? Ina take aure? Maisa tun farko baki zo kin sanarmin ke ɗin jinin Yar uwata ba ce? Why Senori….” Komai ya tuna Kuma? oho Sai yayi saurin sauya sunan na ta da “why Abeedah?!” Wani irin lumshe idanuwanta Abee tayi don irin wani daɗi data ji ya ziyarci gaɓɓan jikinta dalili kuwa sai taji duk duniya babu wanda ya iya kiran sunanta kamar Hammad yanayin yadda ya kirata da sunan na ta sai taji dama shi kaɗai ne zai riƙa kiranta da sunanta  Abeedah, gefe guda kuwa tana ƙare wa ƙaramin bakinsa dake ta faman fidda zance tiryen-tiryen tamkar wanda dama yayi haddar su tun da jimawa, mamaki take yi dama yana magana har haka? dama yana magana mai tsayi? sa’anan yana magana dama fuska a sake? Wow she can’t imagine this yau itace zaune gaban Baffanta ɗan uwan mahaifiyarta suna magana, ma sha Allah Rabbi Kaine abin godia, hakan Abee ke rayawa a cikin zuciyarta. “Hey daughter are you lost?” Ta tsinkayo muryarsa na watsa mata tambayar, saurin dawowa tayi daga tunanin da ta afka ta kallesa taga ya tsareta da sexy oily eyes ɗin sa wanda ba kasa fai mutum zai iya jure haɗa idanuwansa cikin nasa ba, saurin kauda idanuwanta gefe tayi don ji tayi bazata juri ganin cikin idanuwansa ba for the first time da tayi hakan a tattare da ita don a iya saninta ita kam tsaf take kalle mutum har cikin idanuwansa ta shuka ma sa rashin mutunci muddin ya shigo cikin gonanta kai ko baka shiga sabgarta bama baka isheta kallo ba bare ka shigan, but here everything changes ji tayi wani kalan baƙon abu wanda bata taɓa experience irinsa ba na ziyartar ilahirin gaɓɓan jikinta, wani abu daban data gaza fassara mainene take ji yana mamaye cikin zuciyarta, whats happening to her? Shine Tambayar data yiwa kanta, nan ma bata kaiga samin amsar ta ba Hammad ya daɗa katseta ” look at me Senorita!” Ya faɗa wannan karon da alaman seriousness a tattare da maganarsa, ita dai mamakin wannan sunan da a yanzun yakai karo na wajen uku kenan data ji yana kiranta da shi zuciyarta ta shiga yi mai ma’anar sunan kuma? what’s Senorita again? shine abin da take tambayar kanta, daidai nan kuma ta ɗago takai dubanta garesa wanda shi ɗin ma ita ɗin yake kallo, a lokaci ɗaya suka lumshe idanuwansu a tare, a kuma mintuna biyu da secons uku suka buɗe a tare, sauke idanuwansu sukayi a samar fuskar junansu, lokaci guda kuma suna sakar wa junansu murmushi, wanda yau itace rana ta farko da Abeedah zata iya cewa ta ga murmushin Baffanta saɓe a samar kekkyawar fuskarsa, sai taji ma dama su dawwama a haka yata murmushi don ba ƙaramin kyau da haiba hakan ya ƙarawa fuskarsa ba. A hankali cikin muryarsa mai dadɗar amo ko muce mai kama da algaita (cewar Abee😂) ya soma cewa ” ki fadamin Pls, ki sanar dani komai da komai karki boƴe min, niɗinnan zan taimaka miki da iya ƙarfina In sha Allah, kicire duk wani tunani da tsoro a tattare dake duk da naga dotar tawa bamai tsoro mace my dota issa hero” ya faɗa hakan yana mai sakin lallausar murmushi wanda har Dimples ɗin sa suka lotse can ciki, Abee kuwa sosai ta sake tana kwasar dariya harda riƙe ciki, don maganar ta sa tay matuƙar bata dariya wai bata tsoro shida a yau ma ya santa taya har zai ce ita ɗin ba mai tsoro ba ce? Shagala sosai Hammad yayi wajen kallon Abee yanayin yadda take dariyarta ba ƙaramin tafiyar da imanin mutum mai lafiya zai yi ba, sosai ya lula wata duniyar ta daban, duniyar da masoya kaɗai masu matuƙar ƙaunar junansu sabida Allah ke shiga. “Baffa’am!” Ya tsinkayo muryarta kamar daga sama, sunan kuma data kirasa da shi yake muradin ta sake kiransa da hakan, kallonta yayi idanuwansa ɗauke da saƙonni daban daban wanda Abee ta gaza fahimtar su, sai dai wani irin feelings dake shigarta a tattare da kallon dayake yi ma ta, shine kawai zata iya cewa ta gane kallon na sa wani irin yanayi yake jefata a ciki don haka tayi saurin kauda kanta gefe kafin ta ce ” Baffah” “no! ɗayan da kika kirani da shi ɗazun da shi nake son ki sake kirana da shi” far tayi da idanuwanta kafin ta ce ” wanne kenan?” Tayi jim ta saka hannunta akan fuskarta alamar tana nazarin sunan. 2

STORY CONTINUES BELOW
Can ta ɗago da sauri ta kai dubanta garesa ta ce “Baffa’am?” Jin-jina ma ta kai ya shiga yi lokaci guda kuma yana sakar ma ta murmushi alamun jin daɗin sunan kafin ya ce “Yes Baffa’am, is so sweet dama kin iya Fulatanci?” Rufe fuskarta tayi da tafukan hannayenta alamar taji kunƴa kafin kuma ta ce ” miɗon na na seɗa-seɗa(inaji kaɗan kaɗan), murmushi yayi kafin ya ce “milari kam, ase Adda Haleema sakkinai volde mako? (Ashe Adda Haleema Bata yaddar da yarenta ba)” dariya Abee tayi kafin tace ” tana yi mana kam lokutan da muke yara amma da muka girma sai kawai muka watsar muka koma yin Hausa amma inajin Fulatanci mayarwa ne dai wasu lokutan bana iyawa,” Abee ta faɗi kai tsaye, murmushi yayi kafin cikin yaren Fulatanci ya ce ” karki damu aikin dawo Adamawa da zama kenan, so zaki iya fulani sosai” shiru tayi kamar mai nazari can kuma ta ce ” hakane, amma sai nagani nan ɗin ma kamar suna sake da yaren na su mafi yawanci hausa kawai naga ana yi jefi jefi suke sanƴa Fulatanci a ciki” murmushi Hammad Yayi ya ce “smart girl, ashe banda aikin da Adda Halee ta aiko kiyi harda spying kika koma yi kenan?” Yayi maganar cikin sigar zolaya, narai-narai Abee tayi da idanuwanta kamar wacce ke shirin kuka ta ce “no Allah aa Kawai nagani a gidan Daddy ba’ayi Sai hausa Kawai da English” murmushi kawai yayi yana kallon tsantsar yarinta a tattare da Abeen kafin ya ce ” hakane, kinsan babu wanda yakai bafillatani yadda Yaren sa ba, da sun shiga birni sun waye shikenan suke ajiye Yaren a gefe su kama yin sauran, toh ina jinki ina Adda Haleema take yanzun?” Murmushi Abee tayi tana hango tsantsar ƙaunar da Hammad Ke yiwa mahaifiyarta a ƙwayar idaninsa, hakan kuwa yayi matuƙar yi ma ta daɗi don haka ta shiga basa labarin su tiryen-tiryen har ƙarshe.

*************************************************

“Nenne, Nenne, Nenne!” a hankali ta soma buɗe idanuwanta tana kuma sauke su a kan fuskar wacce ke tsaye a gefen inda take a kwance tana mitan Kiran sunanta, buɗe idanuwanta tayi fes ta sauke su a samar kekkyawar fuskarta wanda ko a mafarki ta ganta bazata taɓa mantata ba, ita ɗin wata gaɓa ce a cikin rayuwarta da in har ta mance da ita bata yiwa kanta da zuri’arta adalci ba, ita ɗin dai bata isa tace zata manta ta kwata-kwata a cikin rayuwarta ba, domin ita ɗin, itace silar komai nata da take taƙama da shi a yanzun a rayuwarta, ta silarta ta sami hakan ta sami damar cin dukiya babu kama hannun yaro, ita ce silar zamewarta cikin talauci ta shiga cikin daula dake ratsata a yanzun, a daa a kace mata zatayi dukiya har haka toh tabbas zata mu sa amma silar rainonta ta zama hamshaƙiya mai ji da kuɗi da Naira wanda a yanzun da za’a sanƴa ma ta wuƙa a ce ta faɗi a dadin kuɗaɗen da ta mallaka a duniya toh kam tabbas ba zata iya ba, domin ita kanta ba ta san nawa ta mallaka a rabi-rabin dukiyar da ta tara. ”  Haleematu Diddi! Kece? dagaske ke ce tsaye a gabana ? baki mutu ba dama? dama ƙarya suka min ba su kashe ki ba? suka saka na ba su kuɗi? Kee Haleematu faɗamin kodai fatalwarki ce ta bayyana? Ko dai tsorata ni kike son yi? Yoo to shekara da shekaru baki bayyana ba sai yau tsakiyar rana kizo min har cikin ɗaki kina ƙwala min kira? Ina matsiyacin mijinki?” Ita dai Haleematu (Mancy) da idanuwa kawai take bin Hajia Nenne da shi a hankali kuma take matsowa gaf da Hajiar, zama tayi kusa da Hajia Nenne wacce ke ƙare ma ta kallo kawai ” Nenne dama kece kika saka a kashe Ni?” Taji Haleematun ta jefo ma ta tambayar, tana kuma tsareta da idanuwa alamar tana jiran jin amsar tambayarta kenan ” ban gane tambayar taki ba, kinga banson sakar ci Haleematu ki faɗamin ke ɗin fatalwace ko mutum?” Haleematu zata buɗi baki tayi magana kenan Abee da Farhana da Haris, da Abbi suka bayyana a cikin ɗakin, Hajia Nenne daskarewa Kawai tayi a zaune don ba zata iya cewa daga ƙofa taga sun shigo ba kawai dai taga sun bayyana a cikin ɗakin daga sama ko ƙasa Allah kaɗai ya sani dan dai tabbas zata iya bada shaidan cewa ba ta ƙofa ko window suka shigo ba! ” Ga ƴaƴana, sunan Abe……..” Razananniyar ihun da Hajia Nenne ta saki Shi Yayi azamar dabaibaye ilahirin part ɗin ta, babu inda muryarta bai amsa kowa a cikin sashen na ta ba, a firgice ta miƙe daga kwance da take tana faman nuna Haleematu da ƴaƴanta da yatsan hannunta bakinta na karkarwa ta na cewa……
Razananniyar ihun da Hajia Nenne ta saki shi Yayi azamar dabaibaye ilahirin part ɗin ta, babu inda muryarta bai amsa kowa a cikin sashen na ta ba, a firgice ta miƙe daga kwance da take tana faman nuna Haleematu da ƴaƴanta da yatsan hannunta bakinta na karkarwa ta na cewa ” ke Haleematu, ƙarya kike wallahi kin mutu!, Ƙaryane! Ƙaryane!, wallahi Kin mutu! Kin mutuuuuu!” Firgigit ta miƙe a tsorace daga baccin da ta rasa dalilinta nayin sa, a firgice ta soma ƙarewa ɗakin na ta kallo daga sama har ƙasa amma babu wani alamun Haleematu da iyalanta a cikin ɗakin, fiffita fuskarta da yayi matuƙar jiƙewa da zufa ta shiga yi da hannunwanta, duk da sanƴin ACn dake kaɗawa a cikin ɗakin bai haneta fidda zufa ba a dukkanin ilahirin jikinta. Miƙewa tayi tsaye ta soma tattaki har wajen window tana leƙe ko akwai wani a waje amma shiru bata ji alamun kowa ba, hakan ya sanƴata dawo wa ta zauna a kan gado jikinta duk a mace, kallon agogo tayi taga “karfe 2:30am na dare” nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali kuma take faɗin”kenan mafarki nayi ? Haleematu bata raye kenan ? ƙaryar mafarki ne ko?” Ta tsinta kanta da yiwa kanta wannan tambayar a lokaci guda kuma tana baiwa kanta amsa ” tabbas mafarki ne, toh ta Allah ba taki ba Haleematu ni ɗin nan dai da kike ganina, nan gani nan bari ce inji hausawa. Gwara ko cikin mafarki kada ki ƙara zuwa min don rijiya ba gurin wasan makaho bane!”  Hajia Nenne ta furta hakan ranta a matuƙar ɓace, daga nan kuma ta miƙe ta sauya ɗakin kwana ta koma ɗakinta dake downstairs tayi kwanciyarta. #Asubah ta gari Nenne🙄.
***********************************************
<<>>> +

Shiru Hammad yayi, a lokaci guda kuma ƙwaƙwalwarsa na tattauna zantukan da Abee ta gama faɗi ma sa a yanzun, tabbas sun sha wahalan mutane sa’anan Abee tayi matuƙar ganin ƙalubale kala-kala a cikin rayuwarta, sosai yarinƴar ta sake shigar ransa rashin tsoranta, zafin ranta, rashin ɗaukar raini, confidence ɗin ta su suka fi burgesa, babu kuma abin da yafi baƙanta ma sa rai kamar abin da Sir Salman ya aikata a gareta, sosai yaji tsanar Salman har cikin ransa, ɓangare guda kuma yana mai murnar faruwar lamarin dalili kuwa ta sanadin fasa auren Abee da yayi ne Allah yayi silar zuwanta Adamawa, har ya ganta ya kuma ji labarin ƴar uwarsa. “Baffah Hammad!” Abee ta katse ma sa tunanin da ya lula duniyar yin ta, ɗago da dara-daran sexy eyes ɗin sa yayi ya ɗaura a samar fuskarta, saurin kawar da idanuwanta tayi daga na sa don Allah na gani bata iya juran ganin cikin idanuwansa, sosai yake ma ta kwarjini. Murmushi Hammad Yayi kafin ya ce “Do you still love Salman?” Jin tambayar tayi yazo ma ta a bazata, don hakane ma ta ɗago ta kallesa tana nazartar expression ɗin fuskarsa, shiru tayi ta kasa cewa komai, toh mai yake so ta ce ma sa? Bayan ya sani sarai ba ta son Salman ɗin, dalili kuwa babu wanda zai zagar ma ta iyaye har ya iya danganta iyayenta da zaman dadiro suke sa’anan kuma mutum yayi tunanin ita Abeedah zata sake son wannan mutumin, koda ko a ce lumfashi yake hura mata ƙarshe kenan ko? toh babu ita babu shi har abada! don ba’ayi ɗan iskan da zai zagar ma ta iyaye ba ko shi waye kuwa, komin son da take ma ka kuwa muddin ka taɓa mata uwa ko uba ko ɗan uwa toh duk wani alaqa dake a tsakaninku babu haufi babu wani dogon tunani zata yanke shi ɓat tamkar bata taɓa sanin mai fuskarka ba a duniyarta! ” Uhumm, ina tambayarki?” ɗan guntun murmushi tayi kafin ta ce ” Capital letter NO, natsani Salman da duk wani wanda ya san shi, bana ma fata Allah ya sake haɗa fuskana da shi.” Ga mamakinta sai taga Hammad na sakin murmushi mai tsuma ran duk wanda aka ma wa, farin ciki fal fuskarsa ya ce ” good girl, so ki fadamin are we now a team?” Ya ida maganar yana mai ƙura ma ta idanuwansa dake jefata can wani duniyar na daban, murmushi tayi tana gyaɗa ma sa kai alamun eh ” Yes yes! we are team!”  Murmushi Kawai yayi kafin ya miƙe tsaye ya ce ” ki kula da kanki, anjima za muyi magana a gida!” Murmushi tayi itama kafin ta ce ” Allah kaimu, ngde Baffah Hammad” murmushi Kawai yayi kafin ya sanƴa kai ya fita a office ɗin Abeedar. “Awwwn, wow Yau itace ranar farin cikina, oh Allah ngde maka, ƙarshenki ya kunno kai Hajia Khadeejah (Nenne)”! Daga haka Abee ta shiga yin tsallen murna tamkar wacce a ka wa albishir da gidan aljanna. Sosai Hammad ya zurfafa tunaninsa a kan Hajia Nenne, dama ya jima yana zarginta ya jima yana zargin da sanƴa hannunwanta cikin daƙulewar Company ɗin Alhaji, ashe itace babbar annobar dake wawurar dukiyar Daddy, ita ko tausayinsa bata yi? Mutumin nan bai rage ta da ci da sha ba, babu abin da ta naima a duniyarta ta rasa, Daddy yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen sauke dukkanin wasu Hakkokinta da suka rataya a samar wuyarsa, mai ya saka Hajia Nenne Bata da godiar Allah? Bawan Allan nan yayi mata inuwa ita kuma tana naiman kai sa rana?. Kai wai mai ya saka wasu mutane baka taɓa iya masu a rayuwa ? Shi ya saka yanzun jama’un Allah ke tsoron taimako fa, saboda yanzun wanda ka cire a cikin rana ka mayar da shi inuwa a gobe fa shine mai iya wargaza rayuwarka, mai ya saka mutane suke hakane wai? Hajia Nenne wani kalan rufin asiri ne Alhaji bai yi ma ta ba? Tana ƴar aikin ƴarsa fa ya aureta? Amma a Yau itace kecin duduniyarsa da haɗin bakinta a ke tauye ma sa dukiyarsa, da saka hannunta wajen rabashi da ƴarsa, ta raba shi da ƴan uwansa ta raba shi da kowa sai dai ita kawai da a halinta su kawai ta bari yana bautawa. Shima Allah ne ya tseratar da shi daga kaidinta, bata ƙaunarsa sam shiyasaka a kullum bata maraba da shi in ya dawo Nigeria, sosai take sanƴa Daddy ya hana sa dawowa Nigeria, In da yake ɗiban kusan shekaru biyu uku kafin yazo, duk dama tana hakan ne don kar ya ganeta Ko? Shi yasaka watannin baya da taga yayi azamar soma bin cike ta saka a kashe sa kenan? Ya godewa Abeedah da ta sanar ma sa da komai ba tare da ta ɓoye ma sa komai ba, In sha Allahu ƙarshen Hajia Nenne yazo gangare zai mai da ta abar tausayi abar kwatance ga ƴan bayanta, babu wanda zai sake marmarin samun halayya irin na Hajia Nenne, wannan alkawari ne sai ya rusa dukkanin farin ciki a cikin rayuwarta kamar yadda ta rusa na su. Daga haka Hammad ya tattara inasa-inasa ya koma gida jikinsa duk a mace.

STORY CONTINUES BELOW


*************************************************
Da kyar ta iya yiwa kanta mazauni a kan 3cta, sai faman cije ƙasan bakinta take, sosai cikinta ya girma har yana haninta aikata abubuwa dayawa, cike da tausayinta Mommy wacce shigowarta kenan cikin falon tayi saurin ƙara so wa wajenta, kallonta Mommy tayi kafin ta ce ” yi haƙuri Suhailat, sannu kinji mai kike son ci yanzun? ko mu fita ki motsa jikinki ne?” Lumshe idanuwanta tayi kafin ta ce ” Mommy babu abin da nake son ci wlh, kin ga ƙafar nan tawa sai kumburi take” ta ida maganarta lokaci guda kuma tanay wa Mommy nuni da ƙafarta wanda tsananin kumburinsa sai ya baiwa mai karatu mamaki, shiru kawai mommy tayi tana mai nazartar ƙafar ƴarta ta, lokaci guda kuma tanay ma ta addu’an samin sauƙin haihuwa wajen Ubangiji, don iriyar cikin Suhailat da laulayin da cikin ya ke sa ta Mommy za ta iya cewa ta jima bata ga wanda yayi hakan ba, sosai yarinƴar ke shan wahala babu dama taci abu komai ne shi kuwa sai ta amayar da shi, maltina da madara shine kawai abincinta safe rana dare shine kawai zata iya sha ba tare da tayi amai ba, sunje asibitin har sun gaji kullum aikinsu ɗaya ɗirka ma ta uban magunguna, Suhailat wani zubin zama take tayi ta kuka tana faɗin sakayyar Abee ne ke bibiyarta a yanzun, ita kanta yanzun sai take jin dama tun farko ta amince an zubda cikin jikinta da ta sani ta biyewa Salman kawai, In har haka mutum ke muguwar shan wahalar ciki bata sake marmarin haihuwa ita kam yanzun a rayuwarta. ” Nagani Suhailat, bari Abbanki ya dawo sai ya mai damu asibitin. Amma bari na ɗau ointment na shafa miki zakiji relief (sauqin) wajen In sha Allah” Mommy ta ida maganarta lokaci guda kuma tana miƙewa don zuwa ɗauko maganin, ji tayi Suhailat ɗin ta riƙe ma ta hannu don haka ta tsaya kafin ta juyo tana kallon Suhailat in wacce ita ɗin ma Mommyn take kallo, idanuwanta taf da hawaye kaɗan take jira ta zubda su. Muryarta a karye ta ce “Mommy nikam ina ganin mutuwa zanyi wallahi!, Mom….” a ɗan tsorace Mommyn ke kallon Suhailat ɗin ba tare da kuma ta barta ta ƙarasa maganarta ba ta yi saurin katseta kafin tayiwa kanta mazauni a kusa da Suhailat ɗin. “Me kike faɗa haka Suhailat? Waya ce miki kuma don kana da ciki mutuwa zakayi? kin kuwa san mata nawa ke fama da laulayin cikin fin naki sau dubu kuma suke haihuwarsu lami lafiya sa’anan su rayu rayuwa mai tsayi a duniya? Haba Suhailat ina ilimin addininki ya shiga? Sai kace ke ba musulma ba ce, ba zaki  ɗau ƙaddara ba? Karki manta fa kowani bawa a rayuwa da na shi iriyar jarabawar da Allanmu ke jarabtar mafi sauyin bayinsa da yake so!, don kuwa Allah baya jarabtar bayinsa da abin da ya san bazasu iya ɗauka ba, kisani inkika ci sa’an cin wannan jarabawar taki Allah zai tanadar miki da abin da bakya taɓa tsammani anan gaba, saboda haka a kul na kwaɓeki kada na ƙara jin kinyi maganar mutuwa Suhailat!” Mommyn ta ida maganarta a hankali kuma ta shiga sharewa Suhailat ɗin hawayen da ke famar zirya a samar fuskarta, “shhhh kiyi shiru hakanan, In ban da abinki yanzun fa saura wata ɗaya tal ki haihu, yi shiru kinji mamana? In sha Allahu zaki sauka lafiya muraina babies ɗin dota tare! Kaikai waya ga Suhailat da raino oh ni jikar mutum huɗu anƴa mamana zata iya goyo kuwa?” Mommyn ta ida maganar cikin sigar zolaya lokaci guda kuwa ita da Suhailat suka saki dariya, wanda ganin dariyar fuskarta (Suhailat)yayi matuƙar yiwa Mommy daɗi don rabon da ta ga dariyar shimfiɗe a samar fuskarta ya jima sosai, “Mommy inna haifa baby girl sunan Abeedah zan saka kinji ba?” Ta faɗa murmushi saɓe a saman fuskarta, murmushi itama Mommyn tayi kafin ta ce ” toh toh shikenan, Allah Ubangijin ya kawo mana l2l Abee duniyar lafiya” murmushi tayi kafin ta ce ” Ameen momy kin ga sai mu riƙa kiranta ma kawai da l2l Abee-Abee” dariya Mommy tayi ta ce ” l2l Abee-Abee kuma? Mudai bar ma ta l2l Abee” dariya sukai duk a tare, haka dai Mommy ta riƙa tarairayar ƴarta har ta samu ta saki jiki yau da kowa a cikin gidan, ciki ko harda Hafiz(causin ɗin ta da ya so aurenta in baku manta ba?) Wanda har kawo rana irin tayau yana matuƙar son Suhailat Amma ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa a kanta. 
*************************************************

“Hello Hammad?!” Ta faɗa a mamakince, don tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin Hammad ya kirata a waya ba tunda suke sai yau, hakan ba ƙaramin bata mamaki yayi ba tunani iri-iri ta shiga yi na kiran na ta da yayi, har wayar ta kusa tsinkewa kenan tayi saurin ɗaga wa don ba za ta iya barin wannan damar ya wuce ta ba. “Umm Anty Asma’u” taji ya faɗa daga na shi ɓangaren, duk da taji haushin kiran na ta da yayi da Anty, bai haneta jin daɗin jin muryarsa ba, a hankali ta lumshe idanuwanta kafin ta ce “fatan kowa da komai lafiya?” Gyaɗa kai yayi a hankali tamkar yana gabanta kafin ya kai dubansa ga Abee wacce ke a zaune a gefensa tana jin wayar ta su, lallausar murmushi ta sakin ma sa shima ya maida ma ta kafin ya mayar da hankalinsa kan wayar  da yake yi.

STORY CONTINUES BELOW


“Alhamdulullah, ya kike kema?” Taji ya watsa ma ta tambayar, jim tayi na wasu sakanni don ba ƙaramin mamakinsa take ba, ita kawai burinta a yanzun bai wuci taji dalilin kiran na ta da yayi ba, za tayi magana kenan taji ya ce ” yaushe zaki dawo? akwai tattaunawar da nake so muyi” cire wayar tayi daga kan Kunnenta, a hankali kuma take bin wayar da kallo fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki, mai ya saka yake tambayarta lokacin dawowarta? ganin ba ta da amsar tambayar na ta, ya sanƴata maida wayar samar kunnenta kafin ta ce ” nan da kamar sati biyu” ta basa amsa, shiru taji yayi na wasu mintuna don har ta fidda ran zai amsa ma ta, In har kuma da sabo yaci a ce ta saba da iriyar halayen Hammad, ta sani sarai shi mutum ne wanda magana a wajensa babban aiki ne, gani yake yi tamkar in yana dogon magana ko yawan magana zai yi ciwon baki (lol😂💔) tsinkayo muryarsa tayi yana cewa ” Ok!, can u make it ASAP and be back in the next 5days? (Zaki iya dawowa nanda kwanaki biyar?)” Shiru Asma’u tayi kafin ta ce ” fatan dai lafiya? wanine ya mutu?” ga mamakinta dariya  taji yana yi wanda yayi matuƙar ɗaure ma ta kai! ” A’a babu wanda ya rasu Madam, Please ki dawo akwai Maganar da nake son muyi ne and yes please make it snappy nan da 5days ki dawo, thank you na barki lafiya” ya idasa maganarsa yana mai katse kiran, bin wayar da idanuwa kawai tayi tama rasa tunanin da ya kamata tayi, abu ɗaya kawai ta san ta yanke shine zata koma Nigeria nan da kwanaki biyar.

*************************************************
“Yauwa Baffa, yanzun In muka samu ta dawo komai zai zo mana cikin sauƙi In sha Allah” murmushi kawai Hammad Yayi kafin ya ce “karki damu daughter, in sha Allah za muyi nasara a little bit patience and success will befall us kinji?” Jin-jina kai tayi cike da gamsuwa, ita dai fa Allah na kallo Baffanta na matuƙar burgeta sosai take jinsa a cikin zuciyarta, yanzun kam tana jin wani abu daban dangane da shi wanda ta rasa mainene ma’anar abin da ke ɗawainiya da itan a kan Hammad, tafi ɗaukar feelings ɗin da take ji a tattare da shi feelings ne kawai na ƴan uwantaka, amma mai ya saka zuciyarta ke azalzala ma ta shi a kullum safe, rana, dare bata da aiki sai na tunanin Baffah Hammad?. Bata kai ga bawa kanta amsa ba taji yana cewa ” Daughter kafin na manta ban sanar miki ba, gobe in Allah ya kaimu zani Kano!” Ji tayi ya faɗa sunan garin Kano Bambamrakwai, da sauri ta ɗago ta kallesa shi kuwa tuni ya maida hankalinsa kan wayar hannunsa yana daddanawa kai kace ba shi bane yayi magana a yanzun ba, ” Kano kuma Baffa?” gyaɗa kai kurum yayi bai ce komai ba, ” toh zamuje tare ne?” Murmushi yayi kafin ya ce ” kinyi missing su Mancy ne? Yanzun watannin ki nawa a Adamawa?” Ɗan murmushi tayi ta ce ” wata shida ina cikin na bakwai yanzun” murmushi nan ma yayi ya ce ” lalle, ki ce kin kusa shekara, amma fa bana tunanin zaki sake komawa kano fa, shikenan kin dawo ƴar asalin mayo belwa” ya faɗa hakan cike da zolaya, shagwaɓe fuskarta tayi ta ce ” haba haba dai Baffah Hammy (sunan da Abeen ta soma kiran Hammad din Kenan) ai koma wa na Kano dole” ta ida maganarta tana dariya shi ɗin ma dariya yayi, nan dai  suka shiga tattaunawa a kan yadda zasu ɓullowa lamarin Hajia Nenne, yanzun target ɗin su na kan Asma’u don ita kaɗe ce kawai zata iya basu haɗin kai Faruk Kuwa ko giyan wake ya sha, sun san bazai basu haɗin kai ko ficikila ba, hakan ne ma ya sanƴa basa bin ta kansa ko kaɗan.
************************************************
Washe garin ranar Hammad ya je garin Kano, da taimakon Address da Abee ta ba sa na gidan na su, ya samu ya iso har unguwar ta su. Sam Hammad ya haneta sanarwa Mancy da zuwansa don yafi son yayi mata zuwan bazata, sa’anan ya sauke dukkanin wasu hakkokinta daya rataya a wuyarsa, tun mallakan hankalinsa da yayi ya soma aiki a ƙarƙashin Company ɗin Alhaji, Hammad ya soma tarawa Mancy dukiyoyi a jikinsa yana jin tana raye dalili kuwa mahaifiyarsa da mahaifinsa tun suna a waye suke sanar ma sa Haleematu tana raye bata mutu ba, muddin ya girma ya nai meta a duk inda take watarana zata bayyana, da wannan huɗubar na iyayensa ya zauna a kai shiya saka ba dare ba rana yake naimanta amma babu ita babu labarinta har ya gaji ya daina nemanta, amma hakan bai sanƴasa fasa tara mata kaso mafi yawa a cikin dukiyoyin mahaifinta ba, a duk sa’adda kuɗinsa ya shigo hannusa 70% yake ɗauka ya sanƴawa Mancy a bank shi kuma yayi amfani da sauran 40% ɗin, addu’an sa a kullum shine Allah ya sanƴa ranar haɗuwar su, wanda a yau ita ce ranar, ranar da ya jima yana tsumayin zuwanta yau Allah ya cika ma sa wannan burin bai da wani bakin godewa mahaliccinsa don ya gama cika ma sa burinsa na ganin Haleematu. Da idanuwa ya soma bin gidan da a yanzun wani ya nuna masa kuma ya tabbatar ma sa da nan ɗin shine gidansu Abeedah Usman, a cikin labarinsu da Abeen ta basa tabbas bata ɓoye ma sa komai ba ta sanar da shi su ɗin ba ma su ƙarfi bane, rufin asiri kawai gare su tunda basu rasa ci da sha ba. Jinjina kai kurum Hammad yayi yana kuma girmama lamarin Allah, gaskia ne babu yadda Allah baya jarabtar bayinsa, Haleematu ta kasance cikin ƴaƴan masu fitinannen kuɗi ta fito cikin zuri’ar masu arziki, amma a lokacin da bata taɓa zato bata taɓa tsammani ba Allah ya fiddata a cikin wannan daular, Ubangiji ya ɗauke ta daga wannan arziki ya maidata cikin low class (masu rufin asiri)  nan Allah ya nufa zatayi mafi sauyuwar rayuwarta, a ganinsa Jarabawar ta kenan da Ubangiji ya tsara ma ta ne, sa’anan a yau da tayi nasarar haƙurin cinƴe jarabawarta gashin nan Allah cikin ikonsa da rahamarsa ya na gab da maidata cikin ƴan uwanta, Allah ƙara ma na imani Ameen.

STORY CONTINUES BELOW


  “Mancy, khaleefa ya ce wani Balarabe  na sallama dake a ƙofar gida” Harees wanda shigowarsa kenan cikin falon ya sanar wa Mancy, wacce ke zaune tana yiwa Farhana tsifan kai. Kallon Harees ɗin ta yi kafin ta ce ” kaga Harees ban son sakarci fa, kasan halin Khalifa sarari taya balarabe zai zo yayi sallama dani?” Dariya Haris da Farhana sukayi ganin yadda Mancyn tayi maganarta ta cike da tsoro-tsoro, ” kai Mancyn mu, Allah ba ƙarya bane ai nima sai da naje na gansa takunan na yarda” kallon sa Mancy tayi tana karantar fuskarsa kuma babu abin da take hange face tsantsar gaskiya da yake sanar da ita. ” Toh daka je kaima sai ya ce da kai yana naiman Mancy?” Gyaɗa kai yayi ya ce ” eh haka ma yace inje ince Mancy tayi baƙo!” Shiru Mancy tayi tana tunanin waye haka ? Sallamar Abbi da suka tsinkayo shi yayi nasarar daƙile tunanin Mancy, amsa wa sukayi lokaci guda, shigowa yayi fuskarsa ɗauke da tsananin farin ciki, ganin yanayin mijinta ya sanƴa Mancy soma tunanin mai ya jefa sa cikin wanan farin cikin haka? bata kai ga samin amsar tambayarta ba taji yana yiwa baƙo iso cikin falon. “Marhaban lale, da mutan Adamawa, shigo mana daga ciki, Haleematun na ciki”. “Mutan Adamawa Abee kenan?” Mancy ta faɗa daidai nan kuma Hammad ya sanƴo kai ya shigo cikin falon, fuskarsa ɗauke da murmushi mai sanƴaƴa rai, da idanuwa kawai Mancy ta shiga bin Hammad da shi, kallon sani ta shiga yi ma sa, amma ta manta inda ta san wannan sananniyar fuskar. ” Adda Halee, inawuni ya gida na same ku lafiya?” Taji ya watsa ma ta tambayar a lokaci guda, kallonsa tayi kafin ta ɗan saki murmushi ta ce ” lafiya ƙalau Alhamdulullah”  Farhana da Haris ne suka shiga gaida Hammad, lokaci guda yana amsa musu fuskarsa a sake yana sakar musu murmushi, yana mai kuma ƙare wa tsananin kamanninsu da Abee amma sai yake ganin duk ta fisu Haske don ita hasken Mancy ta ɗauka, Farhana da Haris kuwa suma farare ne amma ba cancan ba, dukkanin su dai ma sha Allah,” Hammad ya raya a cikin zuciyarsa, komai Abee keyi yanzun ? ya dai bari a yau zata shiga ɗakin Hajia Nenne don binciko wasu muhimman takaddu a cikin ɗakin na ta, Allah dai ya bata nasara shine abin da Hammad ya faɗa a cikin zuciyarsa. Abbi ne ya katse ma sa tunaninsa In da yake cewa “Haleematu kin kuwa gane Hammad kuwa?” shiru Mancy tayi tana mai tunanin sunan, Hammad? in ba zata manta ba kwanakin baya can lokacin farko farkon Abee zuwa Adamawa ta taɓa tambayarta ko ta san wani mai suna Hammad? A wancan lokacin tayi iya nazarin ta amma ta gaza gane Hammad ɗin, kenan wannan dake zaune a cikin falonta shine Hammad ɗin ? Aikuwa sai yanzun take hango tsantsar kamanninsa da Mahaifinta, da sauri ta kallosa wanda shi ɗin ma ita yake kallo can ta ce ” Moallahidi? Muhammad? Kaine?!” Mancy ta faɗa cike da ruɗu, murmushi Hammad yayi ya ce ” nine Adda Halee baki gane ni ba ko?” Wani irin farin ciki ne Mancy taji yana ratsa ilahirin jikinta, tabbas wannan ɗan uwanta ne yau Allah ya cika mata burinta ya haɗata da danginta koba dukansu ba amma ta ga wani a cikin su, cikin muryar karaya ta ce ” Muhammad, ka girma a mauni masin (ka girma sosai) hattoi Baffa Mahmud be innaah? (Ina kawu Mahmud da innaa?)” Ta ida maganar cike da jin daɗin ganin Hammad ɗin, murmushi kawai yayi kafin yace ” Allah yayi masu rasuwa dukan su Adda!” Ya faɗa a raunane, wani abu Mancy taji ya tokare ƙirjinta hawaye taji yana ƙoƙarin taruwa a cikin idanuwanta, Baffah Mahmud da innaa sun rasu? ba ta mantawa sune suka tsaya ma ta tsayin daka a lokacin da Mahaifinta ya juya ma ta baya, shi Baffah Mahmud da sauran Baffan nin ta sune suka haɗa ƙarfi suka aura ma ta mijinta, shiru tayi tana nazarin abubuwa dayawa ciki ko harda yanke mu’amala da Mahaifinta ya yanke tsakaninsa da ƙannensa duk a dalilinta, share Hawayenta tayi kafin ta ce ” Moallahidi, dagaske Baffah ya rasu? Inna ma ta rasu? Ina Baffah Rufa’i da Baffah Yusuf?” Ta jero ma sa tambayar a jere, murmushi Yayi Ya ce ” duk suna Yola” Mancy ta ce ” Yola kuma? ina a Mubi suke?” Murmushi Hammad Yayi kafin ya ce ” Adda Halee hami jula useni sai mi hokke habaru koɗu me( Adda Halee dan Allah bari nayi salla sai na baki labarin komai)” murmushi Mancy tayi kafin ta ce ” bismillah” daga nan su Farhana suka miƙe ita da Mancy suka shiga ciki, Haris ya kawo ma sa ruwan buta yayi alwala a barandar waje, a tare sukayi sallan la’asar da Abbi da Haris da Hammad, Bayan sun idar Mancy ta kawo wa Hammad abinci, kaɗan ya tsakura yaci yana mai yabon abincin Mancy kuma yana jinjina ma ta don a wajenta Abeensa ta gado iya abinci kenan? Bayan ya ci ya ɗan hutane su Mancy suka dawo cikin falon, babu ɓata lokaci Hammad ya soma basu labarin komai da komai kamar haka:

STORY CONTINUES BELOW


” Lokacin da kika bar Adamawa ina da shekaru 5 ne kawai a duniya, hakan ya sanƴa bani da masaniyar abubuwan da suka faru dake. Tun daga haihuwata Allah bai sake baiwa Inna wani haihuwar ba har na kai kimanin shekaru 12 a duniya sa’annan Allah ya bata ciki, sosai tayi murna ita da Mahaifina da su Baffah Rufa’i, Baffah Abubakar kuwa tun yanke mu’amala da yayi da ƙannensa bai sake bi ta kansu ba, hasali ma In sun zo gidansa sanƴawa yake yi a yi masu korar kare, Hajia Nenne Babu irin wulaqancin da bata sanƴawa Daddy yayi wa su Baffah, ganin Daddy yayi nisan tafiya baya jin kira ya sanƴa su Baffah fita a harkarsa gaba ɗaya, suka daina zuwa inda yake nan zumuncin su yayi balaguro, tun ina yaro na san iriyar ƙaunar da Daddy keyi min hakan ne ma yasanƴasa saka min suna Moallahidi tun ina jariri in Baki manta ba Adda Halee. Mahaifina yayi tafiya zuwa garin Lagos shigo da wasu kayyaki a hanƴarsa ta dawowa yayi hatsari, sai gawarsa kawai aka kawo mana, nida mahaifiyata munyi kuka sosai har mun gode Allah, gashi a wannan lokacin mahaifiyata gab take da haihuwa, Baffah Abubukar mutuwar ƙaninsa yayi matuƙar girgiza shi yayi kuka yayi kuka har ya gode Allah, nan ya roƙi mahaifiyata a kan tabasa ni dan Allah tanan ne kawai zai iya samin sauƙin abin da ya aikata wa ƙaninsa, da kyar su Baffah Rufa’i suka yarda Daddy ya ɗauke ni shi ɗin ma sai da ƙanin mahaifinsu dake can rugar mambila ya sanƴa Baki sa’anan suka barsa ya tafi dani, sai dai ina zuwa inwa mahaifiyata sati sai In koma gidan Dady, son duniya Daddy ya ɗauka ya ɗaura min, hakan kuwa ba ƙaramin haushi yake baiwa Hajia Nenne ba,Babu yadda bata yi ba ganin Alhaji ya rabu dani amma na zame ma ta ƙarfe a ƙafa babu yadda ta iya, hakannan ta haƙura ta barni amma daidai da rana ɗaya bata taɓa sona ba, mahaifiyata wajen haihuwa Allah yayi ma ta rasuwa da ita da yaron cikin na ta duk ba su rayu ba. Na zama Maraya gaba da baya kenan, ba uwa ba uba nayi kukan rashin mahaifiyata har na gode Allah, bazan manta ba a satin da ya rage ta mutu naje wajenta In da babu abin da take faɗi min face  “Hammad (Sunan da Mahaifiyata ke kirana kenan, sabida kara ga surukinta Muhammad Giɗadɗo) Inka girma ka malleki hankalinka ina so ka naimo ƴar uwarka a duk inda take, Haleematu bata rasu ba tana nan da ranta, koman daren daɗe wa zata dawo garemu Ni dai kamin alkawarin zaka naimo Haleematu kuma zaka maido Haleematu cikin danginta sa’annan ka shirya su ita da Mahaifinta, saboda muguwar matar babanta tayi ma su katangar ƙarfe ita da Mahaifinta. kamin  alkawari zaka naimo Haleematu Hammad?”. Sa’annan sune ƙarshen tattaunawata da Ummana, kuma na ɗau ma ta alkawarin naiman ki a duk inda kike a faɗin duniyar nan kuma a yau Allah ya cika min wannan burin gani ga Adda Halee. Daddy ne ya zame min uwa da uba sam sam Daddy baya son abin da zai taɓani kullum cikin faranta min yake duk da iriyar hassada da matar sa ke nunawa a kai hakan bai sanƴa Daddy fasa nuna min so da kulawa ba. kin san mai abin mamaki kuwa ? DAddy har rana irin tayau bai muradin haɗa hanƴa da su Kawu Rufa’i baya hulɗa da su samsam har rana irin tayau, shi yasaka ma suka tattara suda iyalansu suka koma Yola. Bayan gama Candy Ina Daddy ya turamin Germany naje Na karanta Computer science Bayan dawo na ne ya ɗaurani kacokan a kan business ɗin sa, a farko bana son fara business ɗin saboda Daddy yayi min abu dayawa a rayuwa, Ni kuma burina bai wuci In dogara dakai na ba. A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min babu iriyar cigiyar da ban miki ba amma babu ke babu labarin ki, har sai ranar da Allah ya sanƴa na haɗu da Abeedah a ranar nayi farin ciki fiye da tunanin mutum. Inda kuma na daukar wa kaina alkawarin maido da farin ciki a cikin zuciyarki In shaallah Sai kin Koma cikin zuri’arki Adda Halee.” Shiru Falon yayi tsit tamkar babu masu rai a cikinsa, sosai labarin da Hammad ya Basu ya tsuma rayukansu musamman Mancy, tunani take kala kala a cikin ranta , ” Hammad bana tunanin komawa Adamawa a yanzun, nafison sai Daddy ya naimeni da kansa yanzun ko naje korar kare zai min” murmushi yayi ya ce ” Hakane, Daddy har yanzun yana kan bakarsa a kan ki, sai dai ina ganin hakan bazai sanƴa ki tsorata ba nan da lokaci ƙanƙani zai nemeki da kansa in sha Allah, amma ina so kimin wani alfarma dan Allah” Hammad ya Ida maganarsa yana mai kai dubansa ga Mancy, murmushi tayi kafin ta ce ” ina jinka faɗi komainene In sha Allah In Bai fi ƙarfina ba Ni mai yi maka shine.” Lumfashi Hammad yaja kafin ya ce ” Nagode kwarai, alfarma ɗaya nake so a wajen ki Mancy, dan Allah ina so ki koma Adamawa nan da kwana 5, akwai gidanki da yake ƙarƙashin kulawata anan Mubi, Ko yola ki zaɓa sai ku koma can da zama dan Allah” Hammad ya Ida maganarsa yana mai nazartar yanayin da Mancy zata amshi maganar. Shiru Mancy tayi tana mamakin Hammad, anƴa ana samin ƴan uwa masu iriyar halin Hammad kuwa har yanzun ? Duk da bai fito ya ce da ita shi ya siya ma ta gidan ba, a shekarunta a kuma tunaninta ya ci a ce tasan shi ɗin ne yayi ma ta hakan shi ya siya gidan ya a jiye ma ta, murmushi tayi kafin ta ce ” Hammad, gidan aure nake a yanzun ka gani bani da ikon barin gidan aure na in je can wani gidan daban in zauna ba tare da izinin mijina ba.” Mancy ta basa amsa a taƙaice, Hammad Sai yaji wani iri ya a kayi baiyi wannan tunanin ba? ai sai Abbi yayi tunanin wani abin daban ko? ya Allah yayi saurin waigowa ga Abbi wanda fuskarsa ke ɗauke da annuri. ” Abbi Dan Allah kayi hakuri….” Bai kai ga ƙarasa maganarsa ba Daddyn ya katse shi, ” a’a Hammad Babu komai, tunanin da kayi ma yana da kyau, In sha Allah zamu koma can Adamawar da zama Allah ya saka hakan shi yafi alkairi, Ubangiji kuma ya kawo mana ƙarshen wannan al’amarin duka”. Dukkanin su suka amsa da Ameen, Mancy taji daɗi har ranta ko banza dai bayan shekaru 22 zata sake shiga garin haihuwarta zata ga Baffanninta koba komai zata rage ka ɗai ci, nan dai suka yanke shawarar gidanta dake Yola nan zasu koma da zama, babu  ɓata lokaci Hammad ya Kira ya ce a soma gyaran gidan nan da 5days su Mancy zasu koma.
************************************************

STORY CONTINUES BELOW


5days later

Abubuwa dayawa sun faru a cikin kwanakin nan biyar, ciki ko harda dawowar Asma’u, Hammad Kuma kwana ɗaya tal yayi dama a Kano ya dawo Adamawa in da ya shiga shirye-shiryen dawowar su Mancy, sosai ya sanƴa a ka gyara musu gidan wanda ke ɗauke da falo biyu, da ɗakuna shida, uku a sama uku a ƙasa, gidan sosai ya haɗu babu abin da Hammad bai sanƴa musu na more rayuwa a ciki ba.

 2

 2

Abee kuwa tana can kanta yayi zafi, sosai ta duƙufa wajen bincike babu dare babu rana, a yau ma tana zaune tana calculating adadin kudaden da suka shiga bank ɗin Secret folks, taji knocking a bakin ƙofarta kai tsaye ta bada umarnin shigowa ba tare da ta ɗago ta kalla waye ba. ” Abeedah!” Taji Muryar Nenne a samar kunnenta, da sauri ta waigo tana kallonta tana kuma mamakin ganin yau Hajiar da kanta a cikin ɗakinta da sauri Abee ta miƙe tana gyara ɗankwalin kanta, ta ce ” Na’am Hajia ke da kanki? ai da kin aiko an kirani, zauna bismalla” ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausarta, kallonta kawai Hajiar tayi ba tare da ta ce ƙala ba ta sami guri ta zauna, ” lissafin mai kike yi haka?” Kallon Hajiar tayi kana ta kai dubanta kan takaddun dake a zube baja-baja a samar gadonta, ɗauke idanuwanta tayi a kan su tamayar kan na Hajia Nenne wacce a ke ƙoƙarin kai hannunta kan wani takadda da ke kan gadon. ” Oh lissafi kike? dama abin da ya kawo ni wajenki kenan,kina ji ba” Hajiar ta faɗa lokaci guda tana a jiye takaddar, kafin takai dubanta kan Abee ” Faruk, yazo min da wata banzar magana wai naira miliyan 60 mukai asara a cikin kayayyakin da muka kai Egpt, shine na ce ban gane ba taya zai bar maƙudan kuɗi har haka su salwanta?” Ita dai Abee shiru tayi kawai bata ce uffan ba, don da saninta kuɗin ya salwanta koma ta ce da saka hannunta wajen salwantar kuɗin, amma kuma a ganinta kuɗin ba salwanta sukai ba tunda cikin asusun bankin Daddy suka mai da kuɗin, yanzun haka lissafin data zauna yi so take ta haɗa komai da komai sa’annan tayiwa Daddy transfer ɗin duka kuɗaɗen dake cikin asusun bankin Secret Folks, Kuma tana gab da yin hakan, don yanzun ita suka baiwa nauyin riƙe kuɗaɗen sai da saka hannunta a ke fice da shige da duk wani dukiya da zai shiga ko zai fita a asusun bankin na su. ” Kina jina kuwa?” Firgigit Abee ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, da sauri ta ce ” eh Hajia, in sha Allah zan duba” hararar ta Hajia tayi ta ce “ki duba mai kenan?” Ɗan zaro idanuwa Abee tayi kaɗan kafin ta ce ” amm, cewa nayi in sha Allah zamu san abin yi” Hajia  ta ce “yo toh mai zamuyi? kina da yadda zamuyi ne? asaeace dai munriga munyisa babu dawowar kuɗi kam, sai dai a kiyayi gaba amma zan shukawa Faruk rashin mutunci wallahi, ki gama kizo akwai abin da zaki min” daga haka ta miƙe tabar ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya Abee ta sauke ta raka Hajia Nenne da idanuwa har ta ɓacewa ganinta, taɓe baki tayi lokaci guda kuma ta koma ta zauna, wayarta ta ɗauka ta danna lamban Mancy don tambayar su ko sun iso, koda ta kira Mancyn ta shaida ma ta sun iso lafiya, hira suka taɓa kaɗan kafin sukayi sallama, Abee ji tayi tamkar tayi fiffike ta ganta a garin yola.

************************************************

11:30pm

Hammad ne zaune Asma’u kuma na a gefensa itama a zaune, shiru ne ya ratsa tsakaninsu, kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa. ASMA’U a gefenta tunanin abin da Hammad zai faɗi ma ta kawai take, don koda ta dawo ya haneta sanarwa Nenne ta dawo sa’annan a guest house ɗin Daddy ya ce ta sauka wanda ke da tazara mai ɗan yawa a tsakanin main house ɗin sa. Kallonta Hammad Yayi a Karo na uku dogon lumfashi ya ja kafin ya ce ” ki rantse ki kuma ɗaukar min alƙawarin faɗamin gaskia a duk abin da na tambayeki, rashin faɗamin gaskia da zakiyi ba zan miki ƙarya ba zaki gamu da fushin Hammad wanda baki taɓa-taɓa cin karo da shi ba, ki natsu ki faɗamin gaskia Asma’u.” Shiru tayi kawai tana kallonsa, lokaci guda kuma cikinta na ɗurar ruwa, mai zantukansa ke nufi wai? wani gaskia yake so ta faɗi ma sa ? Oh Allah wai mai ke shirin faruwa?. Shine Tambayar da Asma’u ta shiga yiwa zuciyarta, a hankali ta kallo sa dan ta sani muddin bata ce komai ba shima bazai sake ce wa da ida ƙala ba dan haka ta ce ” In sha Allah, zan sanar da kai iyakar gaskiar abin da zaka tambayeni i promise you, Na Kuma rantse maka da mahaliccina” murmushi kawai taga yayi kafin ya ce ” bravo! Ngde, tambayar tawa Suna dayawa, amma kifara amsamin wannan tambayar, kin san nasan wanda yayi yunƙurin kashe ni kwanaki ko?” rasras ƙirjin Asma’u ya shiga bugawa a 360 tagaza tantance mai zuciyarta ke faɗi ma ta ma, ya san wa’inda sukayi yunƙurin kashe sa? Kenan ya san yayarta itace tayi ƙoƙarin kashesa, muƙut ta haɗiye zazzafar yawu, muryarta na rawa ta ce ” wallahi, babu  saka hannuna wajen son kasheka da aka yi niyyar yi, hasalima maganin bacci a ka sanƴamin na sha a ranar da suka yi niyyar aiwatar da kisan, don karna kawo masu cikas wajen gudanar da ƙudirinsu a kanka, wallahi wannan shine gaskiar abin da ya faru.” Wani kalan killer smile Hammad ya sakar ma ta ya ce ” Owk  Asma’u duk abin da yayarki take yi ina sane da shi, all her moves a tafin hannuna take Yin su. kawai banga damar exposing ɗin ta bane, na barta take cin karenta babu babbaka, In kina son ranki da rahma ki faɗamin malaman ko na ce bokayen da yayarki ke zuwa wajensu, a iya bincike na da nayi, nagane tana mu’amala da su and na sani sarai ba zaki gaza sanin su ba tun muna mu biyu ki faɗamin  inda suke” wani irin zufa ne ya shiga gangarowa Asma’u a duka jikinta, kardai asirin yayarta ya na gab da tonuwa?, aikin da tayi na shekara 22 suna shirin wargazewa, mai ya kamata tayi? ya kamata ta rufawa yayarta asiri kuwa? Ko kuma ta sanarwa Hammad komai? Ƙila ta haka Allah zai shirya yayarta ta? Anƴa ba tawa Nenne butulci ba kuwa muddin ta sanar wa Hammad komai? karta manta fa itace silar komai na ta arayuwa, ita ce cinta, shanta, suturarta, karatunta komai na ta tun tana ƴar ƙanƙanuwarta take wahala da ita, yau kuma rana tsaka ta watsa mata ƙasa a ido ta tona asirinta? gaskia In ta wa Nenne haka bata yiwa kanta adalci ba. Koma dai mainene Hajia Nenne yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya, ba zata so taga an tozarta ƴar uwarta ba, ta sani sarai matuƙar ta faɗinwa Hammad inda malaman Nenne suke babu makawa tsinke Daddy korar wulaƙanci zai yi ma ta, ta sani sarai Hammad Yana cika musu bujensu da bugun Abuja zasu warware asirin da aka yisa shekara da shekaru komai na Nenne zai mauɗe, asirinta zai tonu, Daddy zai dawo cikin hayyacinsa kuma bata da ko haufi ko Qur’ani a ka bata ta dafa zata dafa Sa’annan ta rantse Daddy zai saki Hajia Nenne!, Toh Ina zasu saka kansu in Daddy ya kore su? Bata shakku da kayan jikinsu kawai Daddy zai barsu su tsira, anƴa zata iya tona asiri kuwa? ƙarshensu ƙauye fa zasu koma. No gaskia aa ba zata tona wa yayarta asiri ba Hausawa sunce naka naka ne koman lalacewarsa, kuma hannunka bazai ruɓe ka yanke ka zubar ba! Wani zuciyarta kuma na kwaɓarta a kan ta faɗi gaskia ko dan Hammad, kenan In har zai naimi ta faɗa ma sa gaskia sa’annan ta rantse zata faɗin in kuma taki faɗa yazo ya gane malaman da kansa ba tare da saninta ba, bazai taɓa son ta ba  kenan? sa’anan hukuncin Nenne zai iya shafanta? A iya saninta In kana son mutum babu abin da bazaka iya sadaukar ma sa ba ko? Kenan In tayi shahada ta sanar wa Hammad komai, ko ba komi zai riƙa darajata ko? ke Asma’u karki faɗa! Wani zuciyar ta sake kwaɓarta, ki faɗa! Wani zuciyar ta sake kwaɓarta. Shiru tayi kawai tana nazari, nazarin abin da ya kamata tayi, wani shawarar zuciyar na ta zata bi? A hankali ta ɗago da idanuwanta ta sauke su a kan Hammad, Wanda Shi ɗin ma ita yake kallo da alamun nazarinta yake, wani iriyar kwarjini taji yayi ma ta a hankali ta ce ” Tabbas  na san komai da komai amma……………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page