HUTU CHAPTER 7

HUTUCHAPTER 7
Kausar tana bude kofan taga Hydar tsaye cikin kakinshi na soja da laptop bag dinshi a kafada se wayanshi a hannu yana mata one million dollar smile dinshi, batasan sanda ta fada jikinshi tareda kankanmeshi tana shakan kamshin da ta dade tana muradin sake sakanshi ba, shima din rungumeta yayi sosai a jikinshi yanajin wani sanyin ni’ima na ratsa ko ina na jikinshi saboda yau gashi ga Kausar dinshi after good two weeks it’s not easy, breaking hug din yayi tareda kallonta sannan a hankali yace “I missed you”, murmushi tayi kafin ta amsa mishi ya hade bakinshi da nata wuri daya which she also gave in without thinking twice, kissing juna suke passionately sunma mata kaman a waje suke basu karasa cikin gida ba, bayan sun sake juna ya kalleta tareda cewa “I miss those zippy lips of urs”, murmushi tayi tareda jan hannunshi suka shiga ciki.


Kallon ko ina yakeyi saboda yadda yaga gidan a share ba kura ba datti totally the opposite of what he was expecting, gashi se kamshin abinci yakeji, kallon shi tayi tace “let’s freshing u up, se kazo kaci abinci ka huta”, murmushi yayi a zuciyarshi yace “ai a jikinki zan hutu yau”, sama suka haura bayan ta karba laptop bag dinshi suka shiga dakinshi, nan ma yaga ko ina a gyare murmushi yayi danshi kam he’s a neat freak saboda haka ko kadan bayason ganin kazanta, ajiye bag din tayi sannan tazo ta fara ballemishi buttons dinshi tace “amma daga office ka biya airport koh”, ya kada kai tareda cewa “I can’t wait to see you, shiyasa ina zuwa office nayi abinda zanyi se?”, murmushi tayi tace “awwnn did u miss me that much?”, “I miss u more”, ya bata amsa yanajan da karan hancinta. Har bathroom ta rakashi ta hada mishi wurin wanka sannan ta fito, duk yadda yayi akan seta tayashi wankan ki tayi haka ya hakura, kafin ya fito ta dauko mishi jeans da T-shirt tasawa kayan turare yana fitowa ta tayashi shiryawa sannan suka sauko kasa.

Suna gama cin abinci Binta tayi excuse din kanta ta shige daki dan tayi sallah, Hydar kuwa kallon Kausar yayi tareda jawota ya dorata kan cinyarshi yace “baby u knw I miss u”, murmushi tayi tace “yea I knw”, “so me kika tanadar min”, dariya tayi tace “komai ma”, murmushi yayi yace “da gaske”, tace “uhmm”, yaja kumatunta tareda daukanta bridal style yana cewa “in dat case bari naje na tabbatar koda gaske an tanadar min komai kaman yadda kika fada”, dariya tayi tana rufe fuskanta da hannu, yau dai tasan me mijinta yakeso kuma bazata hanashi ba kodan hakurin da yayi harna tsawon two weeks, apart from that kuma ita kanta tana bukatar mijinta. Be ajiyeta ko ina ba se bedroom dinshi inda ya kwantar da ita kan gado tareda kwanciya kanta batare da ya sake mata nauyi ba, “nidai ka dagani kanada nauyi dayawa”, ta fada cikin wasa tana hararanshi, dariya yayi yace “uhm hmm, bazan dagaki ba harse kin bani sweet lips dinnan naki”, dariya tayi tareda cewa “inna ki fa”, cakulkuli ya fara mata yana cewa “zaki bani ko bazaki bani ba”, dariya take sosai harda hawaye murya a tsarke tace “za…zan ba..baka”, tsayawa yayi da cakulkuli se dariya take tana maida numfashi yace “I’m waiting, konaci gaba”, “a’a dan Allah karkaci gaba”, “toh ina jira”, dagowa tayi a hankali ta hade bakinta da nashi wuri daya tareda zagaye hannuwanta a wuyanshi inda beyi wata wata ba ya kama ya fara kissing dinta cike da kwarewa (ni kuwa nace yau su Hydar soja ba sauki).


Tinda Hydar ya auri Kausar be taba jin dadin s*x kaman yadda yaji na yau ba saboda ta bada hadin kai dari bisa dari ba tareda ta nuna alamun ta gaji ko makamancinshi ba, soyayyar da ya nuna mata a yau ko a daren farkonsu be nuna mata irinshi ba, tattali da tarairaya takesha a wurin Hydar saboda yadda ta faranta mishi, wanka sukayi sukayi sallah sannan aka koma round two wanda sosai Kausar ta wahala da kyar take iya tashi, seda ya taimaka mata ta gasa jikinta suka sake wanka sannan suka shirya dan zuwa gaishe gaishe, Hydar ne ya kalli Kausar dake zaune gaban mirror yace “baby zaki iya zuwa kuwa”, hararan wasa ta aika mishi dashi sannan tace “inma bazan iya tafiya ba ai se ka daukeni tinda kai ka jawo”, dariya yayi yace “ai ko goyaki kikace nayi zanyi”, murmushi kawai tayi ta mike ta dau mayafinta suka sauko, leka dakin Binta tayi tace “zamu fita zakije?”, girgiza kai Binta tayi tace “se kun dawo kai na ciwo”, “subhanallah tin yaushe”, Kausar ta tambaya tana karasawa cikin dakin”, “yanzu”, Binta ta bata amsa, sannu Kausar ta mata tareda bata magani tace ta kwanta ta huta, fita sukayi suka bar Binta wacce tsoron sake haduwa da Hydar ne yasata cewa kanta na ciwo. Gidansu Ummi suka fara zuwa suka gaishe ta sannan sukaje gidansu Mom inda Kausar ta shaidawa Mom tanason a samu mata ‘yar aiki, daga nan kuma suka biya gidan Anty Maryam inda Zeena tace zatabi yayanta ta mishi weekend kafin ya koma, haka Hydar da Kausar suka dauki Zeena inda seda suka biya siyan ice cream sannan suka dau hanyar gida.


Hydar se gab Magrib suka dawo gida, masallaci ya wuce a yayinda sukuma suka karasa cikin gida, a parlor Zeena ta yada zango Kausar kuma dakinta ta shiga ta rage kayan jikinta sannan tayi alwallah ta fito, seda tayi Magrib sannan ta sauko kasa inda taga Zeena na kallo tace “Zee kinyi sallah”, girgiza kai tayi tace “I’m on my period”, “ok, ina zuwa bari na kira Binta”, da haka ta wuce ta bar Zeena na wondering who is Binta. Da sallama ta shiga dakin taga Binta zaune kan sallaya ta jingina kanta da gadon, murmushi tayi ta karasa cikin dakin tareda zama tace “ya jikin?”, “da sauki”, ta bata amsa Kausar tace “muje parlor, ki daina zama kedai kinji”, kada kai Binta tayi, Kausar a iya zamanta da Binta ta fahimci bameson magana bace, fita sukayi suka koma parlor suka zauna Zeena ta kalli Binta tareda cewa “sannu”, “yauwa kema sannu”, Binta tace dariya Kausar tayi dan duk su biyun ba masu son magana bane.


Seda akayi isha sannan Hydar ya dawo gida, a lokacin Binta da Kausar ma sun idar da sallah sun dawo parlor, shima zama cikinsu yayi kan Binta a kasa Zeena ta kalli Hydar tace “Ya Hydar munbar ice cream din a mota”, mika mata key yayi yace “dauko kinga mun manta”, juyowa yayi ya kalli Binta dakeji kaman ta tashi ta koma daki, shikam mamaki ma take bashi dan bata yarda su hada ido, Kausar ya kalla yace “wifey wannan yarinyar taki bata magana”, kallon Binta tayi sannan ta kalleshi tace “I think haka take, ba magananniya bace”, “kice an samu Zeena second kenan”, ya fada yana murmushi, “ai wannan har tafi Zeena”, Kausar ta bashi amsa.Zeena ce ta shigo da leda a hannunta kowa ya bashi ice cream daya daya sauran kuma tasa a freezer, Binta tinda take bata taba shan ice cream ba se yau, dan ko da suke tareda Anwar be taba siyo mata ba, sosai taji dadin shi dan ta riga kowa shanyewa, Hydar dake lura da ita yace “zaki kara”, a hankali tace “eh”, murmushi yayi yace “Zeena karo mata”, tashi Zeena tayi Kausar tace “mine kar sanyi ya mata yawa, kasan na fada maka condition dinta”, “babu abinda ze sameta”, yayi assuring dinta, Zeena ta mika maka amma wannan karon me coconut ne se taji yafi na farkon dadi, haka suka dinga sha suna kallo suna hira, Kausar ta tashi tace “mine zanje na kwanta kafin ka shigo, kasa hankali kan yaran nan kar suyi bacci a parlor”, kada kai yayi sannan yace “muje na rakaki”, har dakinta ya rakata ta canza zuwa nightee dinta sannan ya kaita dakinshi ta kwanta yaja mata blanket tareda cewa “I’m coming for u later, so kiyi bacci yanzu”, bata fuska tayi tace “nidai ka barni nayi bacci na”, dariya yayi saboda yadda tayi da fuska, seda yayi pecking lips dinta sannan ya tashi ya dau laptop dinshi tareda rage mata hasken dakin ya fita. Parlor ya koma kan dinning ya ajiye laptop din sannan ya shiga kitchen yayi warming abincin da sukaci da rana sannan ya fito ya kira Binta da Zeena dan yasan ba mamaki sunajin yunwa, abincin da yasa musu a plate ya mika musu suka kuwa karba tareda zama shikuma ya soma aikinshi kan laptop, se around ten Zeena ta tashi ta cewa Binta zata ta kwanta, sannan tayiwa Hydar seda safe ta wuce dakin Kausar, Binta taso ta tashi itama amma kuma tanaso taga karshen film din da akeyi saboda hausa film suke kallo, haka ta zauna ita tama manta da wani Hydar dan yana chan kan dinning, kallo takeyi har shadaya taki tashi, a haka bacci yayi gaba da ita a wurin kan kujera. Hydar duk a tunaninshi ta shiga daki saboda haka yaci gaba  da aikinshi, bashi ya gama ba se past one, sannan ya kashe laptop din ya wuce parlor dan kashe kayan TVn da suka bari kunne, turus yayi ganin Binta a zaune tana bacci kanta ya karkace, “dama bata shiga ciki ba”, ya fada yana karasawa wurinta, kallonta ya tsaya yi yana contemplating ya tasheta koya dauketa, tsugunnawa yayi ze dauketa se kuma ya tsaya yana kallon face dinta, gashin girarta, idonta, hancinta, bakinta, a hankali ya furta “she’s beautiful”, ba tare da ya sani ba, sa sauri ya buge bakinshi yana astagfurullah, sannan ya shiga tashin ta dan daukanta ma da yayi niyyan yi ya fasa, bude ido tayi tana kallonshi yana kallonta yace “tashi kije ki  kwanta”, mikewa tayi amma maimakon tabi hanyar dakinta se tabi wani hanya daban tana tafiya kaman wacce ta bugu, shi dariya ma ta bashi kuma ba karamin birgeshi abinda takeyi yake mishi ba, maimakon yajata dakin seya tsaya yana kallonta, ganin tana niyyan tsugunnawa a bakin steps da alaman fitsari takeso tayi yasa yayi saurin karasa wurin tareda cewa “me zakiyi?”, ya tambaya, cikin magagin bacci tace “fitsari zanyi”, dariya yayi yace “muje in kaiki inda zakiyi fitsari ba anan akeyi ba”, hannunta ya kama ya kaita daki har toilet ya kaita sannan yace “yi fitsarin ki fito”, sannan ya fita dan ya bata privacy, bata wani dade ba ta fito ya kaita kan gado ta kwanta yaja mata blanket, yanda tayi pouting lips dinta ba karamin kyau ya mata ba, he feels like kissing those lips, amma se yayi restraining kanshi yayi peck din goshinta tareda cewa “good night”, cikin baccinta tace “Ya Anwar”, saboda abinda Anwar ke mata  kenan kuma she feels it sanda yayi pecking dinta saboda haka duk a tsammaninta shine, sedai kumafa duk cikin baccin take wannan shirmen. Hydar kuwa tunani ya farayi waye Anwar ganin ba amsa yasa ya mike tareda rage mata hasken dakin sannan ya dawo parlor ya kashe komai ya haura sama, seda ya fara leka Zeena sannan ya wuce dakinshi inda yaga Kausar se baccinta take hankalinta kwance, zama yayi kusa da ita yana kallonta, haka kurum se yaji be kyauta mata ba saboda yayi pecking din Binta, he feels like yayi betraying dinta, a hankali ya furta “I’m sorry”, yana shafa gashin kanta sannan yayi pecking dinta ya tashi ya cire jallabiyan jikinshi ya kwanta tareda janyo Kausar jikinshi yace “good night”. 

Anwar ya sauka India lfy inda already akwai me jiranshi wanda shine ya kaishi apartment dinda Dad dinshi ya kama mishi online, wanka yayi ya canza kaya sannan ya fita dan neman abinda  zeci saboda yunwar da yakeji, sosai yayi yawo kafin ya siya abinda yaga ze iya ci ya koma gida. Bayan ya gama cin abinci yasa sabon sim dinda ya siya a waya sannan ya fara tunanin ya kira Mom ko karya kirata, ajiye wayan yayi ba tareda ya kirata ya gyara kwanciyarshi kan kujera yana tunanin Binta data tsaya mishi a rai, dogon tsaki yaja tareda tashi ya wuce balcony inda daga nan yana hango sch dinda ze fara zuwa, besan abinda yasa su Mom suka zabi su turoshi India ba, idan suna ganin bayajin magana ne toh ai nan ma se yayi abinda yaga dama tinda ba idon kowa akanshi, dariya yayi yana mamakin stupidity irin na iyayenshi, amma tinda sun riga sun turoshi zeyi using dinshi as an  advantage to forget Binta. 


Kusan a haka Anwar ya kwana yana tunani kala kala wanda da za’a shakeshi ace tunanin me yakeyi shi kanshi bazece ga takamemen abinda yake tunani ba, ga abokin hira, gashi yaki kiran kowa da sabon layin, a haka har gari ya waye yana tunanin rayuwarshi. A haka Anwar yayi spend din weekend dinshi indoor duk ya cika kwakwalwarshi  da tunani kuma har yanzu yaki kiran kowa, Monday morning ya shirya tsaf tareda daukan jakanshi wanda ya kunshi transfer papers dinshi ya fice ya bar gidan, da kafa ya taka zuwa school inda yayi using school map har ya samu ya karasa VC office, bayan gaishe gaishe ya mika mishi transfer papers dinshi akayi processing komai mutumin ya kalleshi tareda cewa “Have a nice time studying here at Indian Institute of Technology Bombay”, murmushi yayi yace “thank u sir”, sannan ya fita.

Maimakon ya shiga present class dinda ya kamata ya shiga seya fara strolling a school din yana kalle kalle, wani garden ya gani yaje ya zauna tareda ciro wayan shi ya kira Mom, sallama yaji an mishi ya amsa Mom jin muryanshi tace “Son kaine, My God u got me worried, meya hanaka kira kace mana ka sauka lfy, kasa duk hankalinmu yabi ya tashi haba Son, Dad dinka har airport yaje aka ce mishi jirginku ya sauka lfy amma kuma se baka kira ba why Anwar”, murmushi yayi one thing he likes about his Mom kenan, in ta kama magana ba fullstop musamman ma idan masifa takeyi. “Mom calm down, ina nan lfy, ban samu siyan new sim bane shiyasa ban kira ba”, ya mata karya, ajiyar zuciya ta sauke tareda cewa “don’t do that again gabadaya kasa hankalina ya tashi, Meenah ma har kuka tasa mana”, wani murmushi ya kuma yi kafin ya sake cewa “Mom kice mata karta damu I’m safe and sound, nasan yanzu ta tafi lesson zan kirata later”, “good ka kirata, ka kira babanka, ka kira yayanka ma”, dariya yayi yace “Allah Mom tsufanki da lbr, anyways duk zan kirasu, zan shiga class yanzu karatunsu yayi nisa dan sunci rabin semester and I need to catch up”, “ok son kayi karatu da kyau kaji, kayi abinda ya kaika banda bin abokan banza dan Allah kaji”, “naji Mom I will  call you later”, “ok bye take care”, “I will Mom”, ya fada tareda kashe wayan.

With the help of school map ya samu ya shiga next class wanda yagani a timetable dinda aka bashi, koda ya shiga ba’a cika ba saboda sauran fifteen minutes class din ya fara, chan bayan aji yaje ya zauna tareda dora kanshi dan desk ai kuwa yana dorawa baccin da beyiba ya kwashe shi. “Dude wake up the lecturer is here”, wani daya zauna kusa da Anwar ya shiga tashinshi amma shiru kukeji, “hey man wake up”, nan ma shiru, seda ya kai mishi duka sannan ya tashi yana mitsitsike ido, dagowan da zeyi yaga all eyes on him, class din ya cika duk an gwamutsa da fararen fata da bakaken fata, lecturer dinne yace “I’ve never seen your face here before, are you new?”, a hankali yace “yes”, ba tareda ya kalli inda lecturer din yake  ba, “do you mind introducing yourself”, kallon lecturer din yayi ya yi murmushi a naija wani lecturer zece maka “do u mind”, to hell with that, mikewa yayi saboda kowa ya ganshi sannan yace “I’m Anwar Ismail by name, I’m 22yrs was studying at Nile university Abuja but unfortunately got transferred by my Dad”, murmushi lecturer din yayi yace “did you just said Unfortunately, well I guess you should find yourself lucky, IITB is a great school and one of the best”, ba tareda ya kulashi ba ya zauna yana wasa da pen din hannunshi.

Story continues below


Chigaba da karatu lecturer din yayi amma har ya gama babu abinda Anwar ya dauka banda guntu guntu tsakin da yakeja akai akai saboda he finds the class boring, har gwara lecturers dinshi na naija they crack jokes while teaching haka students dinma amma nan daga lecturer din har students din kowa ka gani da serious face  sunyi concentrate. Ana gama lecture  ya fita, sauran classes dinma be shiga ba, tafiya yakeyi zashi gida wani BMW yasha gabanshi, kallon motan yakeyi kafin na ciki yayi whining din glass din maza biyu zaune kuma daka gansu kaga hausawa, wanda yake passengers seat ya mika mishi hannu sukayi musabaha tareda cewa “I’m Mukhtar but u can call me MK and this is my friend Jamil, u are Anwar right?”, “nice to meet you and yes I’m Anwar how did u know my name”, “u introduced urself in class”, “oh that’s tru”, MK dinne yace “well mu dinnan Hausawa ne, ni dan Nigeria ne from Kebbi state wannan kuma buzu ne dan Niger ne”, ya fada yana nuna Jamil yana dariya, murmushi Anwar yayi yace “nice one”, Jamil ne ya leko kai cikin Hausanshi da bai gama gogewa ba yace “zamuje muyi lunch, u should join us”, “is that ok with you?”, ya tambayesu a tare sukace “yea cmon hop in”, backseat ya shiga feeling relieved atleast yasan ya samu friends yanzu dukda he’s not sure whether to trust them or not.


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Hydar sosai yaji dadin  weekend dinshi dan ko kadan Kausar bata nuna ta gaji dashi kaman yadda ya saba ba, sedai wannan raggwancin da son jikin nan na nan, kullum Hydar ke fita yana musu takeaway rana da dare, tin abin be ba Zeena mamaki har ta fara wondering ita Kausar bata girki ne, Ita kuwa Binta tasan koda take tareda Anwar siyo abinci yakeyi shiyasa ma bata kawo komai a ka ba, sedai da sun gamaci zata wanke plates din, Sunday da daddare Hydar ya mayar da Zeena gidan aunty Maryam tareda musu sallama saboda washegari ze koma bakin aikinshi, daganan kuma yaje gidan Mom da Ummi duk ya musu sallama sannan ya zarce gidansu Khalil.


Khalil na zaune a compound da laptop dinshi kan cinyarshi yana aiki Hydar ya danno gidan, tin daga nisa Khalil ya fara murmushi, tin zuwan Hydar haduwansu na biyu kenan, karasawa Hydar yayi bayan yayi parking ya mikawa Khalil hannu sukayi musabaha yace “Dr Khalil kenan, when will you ever be free eh, kai kullum cikin aiki se kace wani tireless robot”, murmushi yayi yace “ya muka iya, gashinan su mom sunce se nayi aure zan rage aikin”, dariya Hydar yayi Khalil yace “daga ina haka da daddaren nan?”, “Zeena na kai gidan Aunty Maryam, kasan nace maka gidana tayi weekend”, murmushi Khalil yayi jin an ambaci sunan tauraruwarshi yace “ya take”, tana nan lfy lau”, Hydar ya bashi amsa yana zama tareda cewa “Maza ya kamata kayi settle down fa, 32yrs is not a joke amma acè har yanzu koh girlfriend bakadashi, kai kaman ma aure baya cikin agenda dinka”, shiru Khalil yayi kafin ya nisa yace “wlh ni kuwa keson aure yanzu, amma sedai yarinyar da nakeso yanzu take ss2, idan aka koma school zata shiga ss3”, da mamaki Hydar ya kalli Khalil yace “dama sanda kacemin kai yarinya kakeson aura da gaske kake”, “da chan ancema da wasa nakeyi ne, I damn serious in fada ma”.

Kada kai Hydar yayi sannan yace “toh kun sasanta da yarinyar ne”, nan ne Khalil ya kalli Hydar da sad face yace “batamasan ina sonta ba, dan har yau ban fada mata ba, Infact ma a matsayin yaya ta daukeni”, Hydar ko mamakin Khalil yakeyi, “wace girl ce wannan da har ka kasa tunkarar ta kayi gum, ai gwara muje mu sameta ni nan zan maka jagora mu fayyace mata komai”, murmushi Khalil yayi yace “da gaske zakamin jagora”, “sosai ma kuwa”, Hydar ya fada confidently, dan dariya Khalil yayi yace “promise me u won’t back out inna fada ma”,  “I promise” Hydar yace yana daga hannu daya sama, “ban yadda ba swear”, cewar Khalil dake kokarin kunshe dariyar muguntan dake neman kwace mishi, Hydar kuwa da mamaki yace “I cross my heart”, Khalil a hankali yace “well d girl I love and wish to spend the rest of my life with is no one other than Zeena ur stepsis”, take annurin fuskan Hydar ya canza zuwa na mamaki, Khalil kuwa dariyan yasa tareda cewa “remember you promised and swear to be my dan jagora, saboda haka no backing off”, Hydar ma dariyan yakeyi a halin yanzu amma shi ba dariyan rakiyan da zewa Khalil yakeyi ba a’a,  shi dariyan wai Khalil ya rasa wacce zece yanaso se Zeena, yarinyar da tayi wayo a gabansu, yarintarta duk sunsani, kallon Khalil yayi bayan ya tsayar da dariyanshi yace “wait Khalil like for real, pls tell me u ar nt serious”, “I damn serious general, wlh I’m serious, kuma na dade da fara sonta, tin kafin kayi aure”.

Hydar ganin da gaske Khalil yake se shima yayi serious tareda cewa “I believe you tinda kace da gaske kake, kuma nasan kai mutumin kirki ne bakada makusa sannan nasan Ummi da Abba zasuji dadin kasancewarka surikinsu sedai inda na tabbata zamu samu matsala shine wurin Zeena dan tanada burin yin karatu sannan kuma a matsayin yaya ta dauke ka bana tunanin zata amince”, shiru Khalil yayi yana auna maganganun Khalil a mizanin hankali, dagowa Khalil yayi tareda numfasawa yace “u ar right amma toh ai bazan hanata karatu ba, I can wait for her, kuma naga ai zamu bullomata daga sama”, “meaning?”, Hydar ya tambaya dan be gane Inda Khalil ya dosa ba, “meaning why not in gayawa Dad yaje yawa Abba magana a bani izini in fara zuwa wurinta kaga dat way I think bazatace No ba tinda manya sun shiga maganan”, kada kai Hydar yayi  “hakan ma yayi, Allah ya baka sa’a, amma fa be careful, if u break her heart I will break your bones”, dariya Khalil yayi yace “ni ba wannan ba, gobe zaka koma kuma kace zakamin jagora”, harara Hydar ya aika mishi tareda mikewa yace “better respect urself ko na hanaka mata, kasan I have full rights da zan iya cewa No”, da sauri Khalil yace “tuba nake In law, ni na isa”, dariya sukasa gabadayansu sannan Hydar yawa Khalil sallama ya nufi motanshi tareda rakiyar Khalil, seda ya biya ya siyo ice cream ganin Binta naso sosai sannan ya dau hanyar gida yana duban agogo.

Da sallama Hydar ya shiga gida hannunshi rike da leda, amsa mishi Kausar da Binta sukayi ya karasa ya zauna kusa da Kausar tareda mata peck a kumatu yace “hw’s my angel doing”, bata fuska tayi tace “and where have you been?”, murmushi yayi sannan yace “daga wurin Khalil”, sakin fuska tayi tareda daukan ledan da ya ajiye tace “me ka siyo mana”, “ice cream”, ya bata amsa tareda juyawa wurin Binta yace “Binta ba magana”, kanta kasa tace “sanda zuwa”, yace “yauwa ykk”, “lfy lau”, jiyowa yayi wurin Kausar yace “babe I need u now, kinsan gobe da asuba ne tafiya na”, hankalinta na kan ice cream dinda take mikewa Binta tace “this is just past ten, we can’t just leave the girl all alone, bari in tayi bacci”, kallon Binta yayi da gabadaya hankalinta na kan ice cream dinta, murmushi yayi yace “look, she’s busy, she won’t even notice we are gone”, “nidai a’a cewar Kausar dake gyara kwanciyar ta jikinshi. Se 10:30 bacci ya fara fizgan Binta, da kanta ta tashi ta musu sallama ta shige daki, Hydar tashi yayi tareda daukan Kausar yana cewa “ta tafi yanzu, so u are all mine now”, murmushi tayi tana mamakin jaraba irin na Hydar. 
Washegari tinda Hydar yayi sallan asuba be koma bacci ba, da taimakon Kausar yayi wanka ya shirya tsaf sannan ya zauna kan gado tareda jan hannun Kausar ta zauna gefenshi, kallonta yayi yace “babe this time bana tunanin zan iya dawowa weekend dan akwai abubuwa dayawa dake gabanmu, maybe ma a turamu Niger”, waro ido tayi tareda cewa “Niger!”, yace “yes Niger”, da mamaki take kallonshi tace “me zai kaika Niger, i thought u are to serve your country”, murmushi yayi tareda riko hannunta yace “en kunar bakin wake sun addabe garin, suna tada bomb duk inda sukaga akwai crowd, school, islamiyya, masallaci, kasuwa da sauransu, soldiers dinsu sunyi short saboda an kashesu sosai, so president dinsu ya nemi alfarma wurin president dinmu akan yana bukatan a taimakawa kasarshi, shine ake tunanin za’a turamu, banson ki tashi hankalinki ne shiyasa ban fada miki ba tinda na dawo”, idonta cike da hawaye ta zame hannunta daga nashi tareda cewa “No Hydar I won’t let u, u oath to protect and die for your country not the world, koda an turaku bazaka ba dan kai kanka ka fada an kashe musu sojoji shine kai zaka kai kanka, no ban shirya yi maka takaba ba”, murmushi yayi tareda matso da ita jikinshi ya kwantar yana bubbuga bayanta alaman lallashi sannan yace “Kausar I’m sorry but I have to do this, i know it’s risky but a matsayina na soldier bazan iya zuba ido ina kallo ana kashe innocent souls ba tareda nayi komai ba for my own selfish interest, banaso ki daga hankalinki, addu’a nakeso ki tayani dashi, I’m sure everything will be alright, pls ki daina kuka haka”, amma ina Kausar harta hango mijinta filin yaki, yakin da in sunje basu da tabbas, ko wani soldier in zeje war bayasawa ranshi dawowa amma a haka yake tunanin ita Kausar zata bari yaje, inaa bada ita ba. Kausar ta tsaya ta kafe itafa Hydar kawai ya basu excuse yace baze iya zuwa ba, da kyar da sidin goshi Hydar ya samu ta yarda bayan taci kuka harta koshi, idonta yayi ja kanta harya fara ciwo tin bata samu tabbacin zuwan nasu ba, Binta dake daki jin kukan Kausar  fitowa tayi parlor ta zauna tana tunanin meyasa Kausar kuka haka da asuban fari kaman wacce aka aikowa da mutuwa, tana zaune ta zuba tagumi taga sun fito tareda Hydar dayasa kakinshi sosai ya mishi kyau, suna saukowa ta tashi tareda karasawa kusa da Kausar tace “anty meya sameki?”, Kausar hawayenta ta share sannan tace “Kausar Uncle dinki ze tafi inda bamuda tabbacin dawowanshi, Binta ki rokar minshi kice karya tafi”, da fadan haka ta sake sa wani kukan tareda komawa kan kujera ta zauna, Binta dukda bata gane abinda ke faruwa ba jin Kausar tace ta rokeshi yasa tace “dan Allah karka tafi, kaga anty na kuka kaji”, kallonta yayi da mamaki dan tinda yazo se yau ta mishi magana me tsayi, Kausar tsayar da kukanta tayi dan taji me zece, “I’m sorry Binta bani da choice”, Binta ganin bata gane abinda yace ba yasata kallon Kausar data maida kanta kasa, kallon agogon parlorn yayi yaga 6:30 lokaci na wucewa saboda haka ya karasa wurin Kausar yayi pecking dinta sannan yace “pray for me dear, I’m leaving”, juyar da kai tayi tana hadiye wani kukan, murmushin takaicin barin Kausar a wannan halin yayi sannan yace “take care of urself, Binta and my little one dan nasan akwai ajiyana tare dake”, ganin batayi magana ba yasa ya juya wurin Binta yace “ki kula da antynki sannan ki dinga sani a addu’a”, “toh”, tace yayi murmushi ya fice ba tareda ya sake kallon Kausar ba danshi kanshi karfin hali yakeyi an she’s not making it any better for him har dana sanin gaya mata yayi. Kausar na jin fitanshi ta saki wani kuka mecin rai, Binta a hankali ta karasa wurin Kausar tareda rungumeta cikin sigar lallashi, Kausar rike Binta tayi gamgam kaman za’a kwace mata ita tana kuka harseda ta gaji tayi shiru, daki ta koma tayi wanka tasa gown tareda kwanciya kan  gado ta fada kogin tunani. 

Yau sati daya kenan da tafiyar Hydar kullum yana kiran Kausar su gaisa tin hankalinta baya kwanciya harta kwantar da hankalinta ganin har yanzu ba’a ma maganan tafiyan nasu, sosai ta saki jikinta dan a ganinta sun fasa tafiyan ne, shirye shirye take saboda tanaso ta koma bakin aikinta kuma tanaso ta samawa Binta lesson teacher kafin a koma school ta sata, shiryawa tayi cikin gown na atampa ta gyara fuskanta ta dau abubuwan da zata bukata sannan ta sauko, a parlor ta tarar da Binta  ta samu wuri ta zauna sannan tace “Binta shirya ki rakani”, “toh”, tace sannan ta mike ta shiga dakinta, shiryawa tayi cikin riga da skirt na atampa sannan ta yafa mayafi ya fito, murmurshi Kausar tayi ganin Binta ta fara gogewa ba kaman da ba daseta zaba mata kayan da zatasa, fitowa sukayi soldiers din gidan sukazo da niyyar rakata tace su barshi, ba yanda basuyi ba amma taki yarda haka suka hakura kowa ya koma position dinshi ita kuma ta shiga mota Binta ta shiga passengers seat taja motanta tayi gaba. 

Basu tsaya ko ina ba se saloon inda Kausar tasa akayi musu gyaran gashi, sosai gashin Binta ya bata mamaki dan Binta bata taba kwance gashinta a gaban Kausar ba, daga nan mini super market sukaje Kausar tayi siyayyan kayan abinci wanda babu a gida sannan suka wuce gidan iyayen Binta saboda Mom tace ta samo mata me aiki, da sallama suka shiga parlorn Ya Ahmad dake zaune yana buga ps4 ya amsa musu, zama Binta tayi tareda gaishe shi ya amsa hankalinshi na kan game dinshi Kausar tace “ina Mom”, “dubata bedroom”, bata kara magana ba ta haura sama zuwa dakin Mom dinta, lazimi ta ganta tanayi ta zauna har seda ta idar suka gaisa sannan Mom tace “har yanzu maganan tafiyan Hydar  shiru ko an fasa ne?”, da sad face Kausar tace “wlh Mom wai har yanzu ba’a musu maganan ba, ni Allah yasa kar a turasu dan kullum addu’an da nakeyi kenan”, murmushi Mom tayi tace “Allah ya tabbatar da alkhairi”, “Ameen”, Kausar ta amsa mata dashi Mom tace “amma bana hanaki fitan yamma ba”, shagwabe fuska Kausar tayi tace “fitan yamman ne yafi dadi, yanzu zamuyi sallah muci abinci se mu wuce”, “hala keda Binta kukazo?”, Mom ta tambaya, “eh tare muke”, Kausar ta bata amsa tana mikewa, parlor suka dawo Mom ta kalli Ya Ahmad tace “har yanzu kana gindin game dinnan kayi sallah kuwa”, “Mom nayi”, ya bata amsa, “ina wuni”, Binta ta gaisheta tana saukowa daga kan kujera, “lfy lau Binta, koma ki zauna”, zama tayi a daidai lokacin da Ya Ahmad ya samu yaci goal, wani wawan ihu  yayi har seda Binta ta  tsorata kan kuce me takai bakin kofa fuskanta a tsorace, su Kausar da suka lura da ita me zasuyi inba dariya ba, dariya sukeyi  harda rike ciki duk se sukasa taji kunya, Ya Ahmad daya samu ya tsayar da dariyanshi yace “en mata yi hakuri kinji, dawo ki zauna”, a hankali ta koma ta zauna se dari dari takeyi shikuma yaci gaba da game dinshi. 

Sallah sukayi sukaci abinci sannan suka fara shirin zuwa gida dan har tara tayi, “Mom ina house help dinda kika samomin?”, cewar Kausar tana rataya jakarta, “ba kwana zata dingayi ba, munyi magana da mahaifiyarta dan a garin nan suke da jama, wai mahaifiyarta siyar da abinci takeyi, zata dinga zuwa da safe karfe takwas ta wuce karfe biyar ko shida, albashinta kuwa 25k kinji yadda mukayi da mahaifiyarta”, kada kai Kausar tayi tace “ba matsala Mom, gobe seta fara zuwa kenan”, “shikenan Allah ya kaimu goben zansa driver ya kawota kafin ki tafi aiki tinda kince zaki gobe”, “eh Mom, bari mu tafi seda safe, Ya Ahmad seda safe”, “Allah ya bamu alkhairi”, duk suka amsa mata sannan Binta ta musu sallama suka wuce, koda sukaje gida Binta a gajiye take har mamakin kanta takeyi a kauye setayi aiki tin safe har dare amma bata gajiya, yanzu kuwa tana saurin gajiya kodan a kauye batada halin hutawa koda tanaso ne oho, seda safe tama Kausar ta shige dakinta itama Kausar ta shige nata tana mamakin rashin son magana irin na Binta. 

Washegari da safe aka kawowa Kausar me aiki, yarinyar nada tsafta ba laifi, bayan sun  gaisa Kausar ta lissafo mata aikinta zata dingayi ciki kuwa harda gyaran dakin Hydar dukda tasan bayaso, da kuma girki, a takaice dai tabarwa yar aikin ragamar gidanta gabadaya wanda sosai yabawa yarinyar mamaki dan batayi tunanin harda girki zatayi ba, “ya sunanki?”, Kausar ta tambayeta “Hajara”, ta bata amsa, kada kai Kausar tayi tace “Hajara inaso kisan abu daya, ni dinnan da kike gani inada saukin kai, zamu zauna  lfy dake, abunda dayane banaso shine gulma da munafirci, nida kanwata ne a gidan saboda haka banason ki koya mata gulmace gulmace, idan kinzo kiyi abinda ya kawoki kawai, bance karku gaisa ko karkuyi magana ba, a’a amma kisan irin hiran da zaki dinga mata da fatan kin fahimta”, “Insha Allah hajiya bazaki sameni da wata matsala ba”, cewar Hajara kanta kasa, “Allah yasa, yanzu breakfast zaki hada mana karfe goma zanje aiki”, “toh hajiya me za’a dafa?”, ki dafa anything simple”, kada kai Hajara tayi sannan ta mike Kausar ta nuna mata hanyar kitchen, shiga tayi dan ta fara aikinta se kallon yadda aka zuba kudi a gidan takeyi tana raya inama itace a cikin irin wannan gidan, tabe tabi tayi a ranta tace “masu kudi na morewa, tab wannan gida se kace aljannar duniya”, juyawa tayi taci gaba da aikinta tana sake sake a ranta. 


Story continues below


Kausar dakin Binta ta shiga ta ganta kwance amma ba bacci take ba dan da alama ma tayi wanka, zama kan gadon Kausar tayi amma har a lokacin Binta batasan ta shigo ba da alama dai tunani takeyi, “Binta”, Kausar ta kirata tana bubbuga kafanta, juyowa Binta tayi da sauri ta tashi zaune ta gyara gashinta daya warware, “ina kwana anty”, “lfy lau Binta, ykk, mun tashi lfy”,  “lfy lau anty”, murmushi Kausar tayi sannan tace “tunanin me kikeyi haka”, “ba komai”, Binta ta taba amsa, “a’a Binta karkimun karya fadamin kinji”, kanta kasa tace “kawai tunanin rayuwa nakeyi yadda na taso, da yadda aka kawoni garin nan, gashi basan wani hali Hajiya ke ciki ba kar tayi tunanin ko guduwa nayi, Ya Anwar ma haka, gashi bansan ta ina zan soma neman dagin mahaifiyata ba”, sosai ta bawa Kausar tausayi, Kausar ta kamo hannunta in a comforting way tace “Binta komai kikaga yana faruwa a rayuwar nan kaddararre ne, Kaddarar mu a rubuce take, maganan gidan Hajiya inaso ki dainashi saboda dama wurinta ba wurin zama bane sannan shima Anwar inaso ki mantashi dan shima ga dukkan alamu ba mutumin kwarai bane dan da ace mutumin kwarai ne da baze ajiyeki a gidanshi ba in ba dai yanada wata manufa ba, Binta a halin yanzu inaso ki tsayar da hankalinki wuri daya saboda inaso in saki makaranta dan kiyi karatu ki zama babban mace  yadda ko a wani hali kika samu kanki zaki iya kwatar ‘yancinki, maganan en uwan mahaifiyarki kuma baki da wani wanda kikasani cikinsu balle muce zamuyi cigiya saboda haka inaso ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi, indai Allah ya kaddara zaku hadu toh wata rana zaki gansu kinji”, hawaye Binta takeyi bata taba ganin mace me kirki irin Kausar ba, a hankali tace “anty nagode sosai Allah ya biyaki da gidan aljanna”, murmushi Kausar tayi tace “ameen er kanwata”, sharema Binta hawaye tayi sannan tace “yau karfe biyu wanda ze dinga koya miki karatun boko zezo, zakuyi karatu zuwa karfe hudu, da karfe hudu malamin islamiyya zezo shima karfe shida ze gama, inaso ki mayar da hankali kiyi karatu sosai saboda inaso in za’a kamo makaranta a koma dake”, sosai Binta taji dadi tace “nagode anty nagode, kuma na miki alkawarin zanyi karatu sosai bazan baki kunya ba”, se yau Kausar taga fara’a sosai a fuskar Binta tinda ta kawota, se yanzu ta gane cewar ba magana ne Binta bata sonyi  ba tasa damuwa a ranta ne, gashi yanzu data fito ta fadi damuwarta ta saki ranta kaman ba ita ba turawa sunyi gaskiya da sukace “a problem shared is a problem half solved”, shafa kanta Kausar tayi sannan tace “na samo mana ‘yar aiki, tana kitchen tana aiki, ki fito ku gaisa”, mikewa Binta tayi ranta fari fal suka fito zuwa parlor, har kitchen Kausar ta kai Binta suka gaisa da Hajara daketa faman suyan potato. 


Kausar seda tayi breakfast sannan ta shirya ta sauko kasa, a parlor taga Binta tace “Binta ni zani wurin aiki amma zan da wuri, zuwa biyar na dawo, ki maida hankali idan malamanki sunzo kinji”, da murmushi Binta tace “Insha Allah zan maida hankali anty, allah ya kiyaye hanya”, “ameen”, Kausar tace sannan ta fita, Binta kitchen ta shiga taga Hajara na wanke wanke, karasawa tayi ta fara tayata tana mata daurawa, ba yanda Hajara batayi ba akan Binta ta barshi amma taki haka ta hakura sukayi wanke wanke tare, haka Binta ta dinga taya Hajara aiki tin Hajara tana hanata harta kyaleta sukayi aikin gidan gabadaya kaf, sannan suka dora Indomie sukaci, Binta duk abinda takeyi tanayi tana kallon agogo, she can’t wait taga itama ta fara karatu, 2:05pm teacher dinta yazo, cikin ma’aikatan gidan daya yayi sallama tareda shaida mata, a compound suka zauna an riga an ajiye musu plastic chair biyu da table da marker board, hijab tasa ta fita, zaune ta ganshi ta gaishe shi sannan itama ta zaune yace “what is your name?”, waro mishi ido Binta tayi dan da za’asa mata wuka a wuya a tambayeta me yace batasani ba, murmushi yayi tunawa da yayi ance babu abinda ta sani sannan yace “ya sunanki”, a hankali tace “sunana Binta”, “Fatima kenan”, ta gyada kai yace “sunan mahaifinki fa?”, tace “Tanimu”, ganin sunan yayi wani Tanimu dayawa seya rubuta mata Fatima Tanim tareda cewa “daga yanzu idan an tambayeki sunanki kice “Fatima Tanim”, gyada mai kai tayi sannan ya fara mata lesson din, da ABCD 1234 ya fara mata kuma sosai suke zama akanta, karfe hudu ya mata sallama tareda cewa tayi kokari ta haddace abinda ya koya mata yau sannan ya wuce. 

Seda tayi sallah sannan malamin iskamiyyan ta yazo shima babban darduma aka shimfida musu suka zauna tin daga ا ب ت ث ya fara koya mata kuma tana rikewa, shima karfe shida ya mata sallama sannan ya wuce bayan ya mata alkwarin indai ta rike abinda ya koya mata gobe ze kara mata, a gajiye ta shiga gida ta baje kan dogon kujera, tana shigewa Kausar da dawo, zama Kausar tayi tace “Binta”, a kasalance Binta tace “na’am “, dariya Kausar tayi tace “kin gajine? “, “wlh anty karatu da gajiya”, cewar Binta, murmushi Kausar tayi sannan tace “ai dama karatu beda sauki, amma idan kika daure kikayishi zakiji dadi, yanzu kije kiyi wanka kafin a kira sallah zakiji dadin jikinki”, mikewa Binta tayi ta shiga daki Kausar ta bita da kallo tana murmushi, Hajara dake tsaye tin shigowan Kausar tace “Hajiya na gama zan wuce” juyowa Kausar tayi tace “muje nawa driver magana ya kaiki gida”, cike da jin dadin kirki irin na Kausar tabi bayan ta suka fita waje, a ranan sosai Kausar taga canji a wurin Binta danta saki ranta ta saki jikinta har gaisawa sukayi da Seema a waya, kuma litattafan ta tasa a gaba tanata karatu abinda bata gane ba kuwa ta tambaya har Hydar ya kira Kausar ta wuce daki tabar Binta, se wuraren karfe biyu sukagama waya da Hydar Kausar ta fito dan ta duba Binta amma ga mamakin ta taga idonta biyu ba tana karatu, murmushi tayi ta karasa ta rufe littatafan dake gaban Binta tareda cewa “ya isa haka, karatu kadan akeyi se’a huta dayawa seya zauna dakyau, kije kiyi bacci kinji gobe se ki kara dubawa kafin suzo”, kada kai tayi dan dama ta gaji sannan ta kwashe takardunta tama Kausar seda safe ta wuce daki, Kausar ta kashe fitilu sannan itama ta wuce dakinta. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page