KAWUNA CHAPTER 1

KAWUNA
CHAPTER 1

A gajiye ta k’arasa shigowa cikin madaidaicin falon gidan, daka ganta za ka san cewa ta mugun ɗebo gajiya, ajiye jakar hannunta ta yi kafun ta ajiye longnote dake hannunta duk a kan kujera, wuri ta samu ta zauna tana yamutsa fuskar ta,a hankali ta furta “Wash! Allah ni ‘yar Haleemaa…”

Ba ta k’arasa maganarta ba ta ji k’aninta na kwala mata kira, haɗida rugowa inda take yana kuka yana faɗin:

“Anty! Anty!! kin ga Waleed ya bigeni wai dan na rama shine Yayarsu ta fito ta mareni, har tana ce min banza mara ASALI…”

Ai tun kafin ya gama fadin maganar, ta yi sauri ta mike tare da d’ura wani irin ashar, mahaifiyarsu dake Sallah a can gefensu ta soma “uhum uhum.”

ina ko ta waiwayo ta kalli inda mahaifiyartasu take Aunty ba tayi ba, sai ma finciko hannun ƙaninnata da ta yi, babu inda ta dire sai a tsakar gidan su Waleed, wato makwaftansu, har gaban uwarsu ta je,ba ta jira komai ba ta cafko Yayar Waleed ɗin tare da wanka mata mari, ta fara magana cikin kakkausar murya “kika ce bamu da asali? Sannu mai asali, wacce take da asali idan kin mutu ace yau aljannan ki daban da wanda basu da asali, ko kuma idan kinyi laifi kar a hukuntaki tun da ke ‘yar asali ce. Ina mai baki shawara da ki ji da abin da yake damunki, ba wai ki zauna kina ƙananun maganganu ba, wallahi kika kuma dakan mun ƙani, kika zagesa wallahi haƙoran ki zan ɓarar a waje , banza kawai.” Ta dire maganar tana sakin tsaki.

Yayar Waleed kuwa tsoron Aunty ya kamata, ta ma rasa sanin mai yakamata ta yi, muryar mahaifiyarsu ta ji, wacce ke zaune tana jin duk abin da suke yi, a lokacin ta samu yin magana ta ce:

“Keee! _ABEEDAH_ yanzun mu kike ma wannan rashin kunyar?”

Cikin fushi da d’aga murya Abeedar ta ce “An yi makun, ki nada abin da za ki yi ne? Kun koyawa yaranku rashin tarbiyya, tun suna yara sannan daga baya ku zo kuna ma wasu gorin asali? Toh idan har haka asali yake akoyama ɗa rashin tarbiyya, toh mu dai mun godewa Allah da ba mu samu Asalin ba! And idan kin mutu kice yau aljannar ki daban da wa’inda basu da Asali, aikin banza aikin hofi.”

Ta ida maganar tana balloma mahaifiyarsu Waleed harara, hangame baki kawai Mamansu Waleed ta yi tana mamakin Abeedah, sam yarinyar ba ta ganin girman kowa muddin ka shiga gonarta ko kai waye yaɓa ma abin da ke zuciyarta zata yi .

“Toh Asalin ne daku?da zaki shugo kina mana zage-zage a cikin gida.K’arya Rabi’ar tayi ne?Asalin ne da ku?”

In ran abeedah yayi dubu to ya gama 6aci ji take kaman tayi tsalle ta dira a gaban wannan uwar da wlh babu abin da zai hanata 6a66allata a wajen.Cikin Zafin rai da d’aga murya tace:

“Aa kin manta daga Sama muka fad’o aa daga cikin bola muka fito nan ne Asalinmu,ko daga ina muka fad’o muma mutanene kamar ku,wlh tallahi muddin yaron ki ko ‘yar ki suka k’ara furta wannan kalmar ga ƙannena ko wani nawa idan ba fitar masu da hak’ora zan yiba kice ba sunana Abeedah ba! kin san tsaf zan iya,kin sani sarai zan iya aikata fin haka ma.!

Kafin kace mai a she tuni jama’an gidan sun firfito suna k’are masu kallo.Ta gefen idanu Abeedah ta kallesu taga nuni suke da ita da bakunan su suna wani k’usk’us.Hakan ya kuma k’ular da ita dan haka cikin matuk’ar zafin rai ta cigaba da zage zagenta ta had’e da su mutanen gidan ta zagesu tas ta musu rashin mutunci,taja hannun k’aninta suka bar harabar tsakar gidan zuciyar ta na mugun tafarfasa!

Turus suka ci karo da mahaifiyarsu tana tsaye k’ek’am a bakin k’ofa da Alama ta gama jin duk wani rashin mutuncin da Abeeda taje tama makwaftansu kuma tana tsaye tana jiran dawo warta ne!

Story continues below


Tsayawa Abeedah tayi tana kallan mahaifiyar tasu kafun ta d’an durk’usar da kanta k’asa.Girgiza kai mahaifiyarsu tayi tace: 

“Yanzun Abeedah haka zaki ruk’a jany’omun fitina? Sam ke ba kida hak’uri,in ban da zafin ran tsiya?” 

D’agoda kanta Abeedah tayi ta kalla mahaifiyarsu tace: “mancy kin san Allah,mutanen gidan nan su suka koya mun rashin hak’uri,kuma zan tafi da rashin hak’urin ne har illa ma sha Allah!.Wahalan dana sha ina yariny’a wallahi na sha alwashin k’annena baza su shata ba!” 

Abeedah ta ida maganar tana furza huci,har cikin ranta take jin zafin gorin da a ka ma k’aninta,ta san k’uncin da k’annenta suke shiga muddin a ka masu gorin Asali,dan ita ma da haka ta taso cikin tsangwama da habaicin mutane a kan basu da asali. 

Mancy tace:yanzun ni Abeedah bazan fad’a maki kiji ba?” 

Murmushin tak’aici abeedah tayi tace:”Mancy kiyi hak’uri dan Allah ,ki ruk’a mun adu’a Allah ya ragemun zafin zuciya dan shine silar wanzuwar rashin hak’urina!” 

Girgiza kai mancy tayi cike da tausayin y’arta tace: “Abeedah Allah shi yaye maki zafin zuciya,Allah yayi maki albarka ” 

Cike da jin dad’in adu’ar da mancy ta mata ta amsa da “Ameen ameen mancyn mu ” 

Murmushi su kayi kafun suka k’arasa cikin falan gidan.Kallan k’aninta Abeedah tayi sannan tace: “Haris oya wuce kaje ka shirya islamiya lokaci yayi ” 

Gyad’a kaii Haris yayi ya wuce d’akin su dan sauya kaya zuwa uniform d’in islamiya!

Zama Abeedah tayi a k’asan kafet d’in falon tana jan kulan abincin ta dan yunwa ya fara nuk’urk’usar ta,mancy na zaune gefen ta tana mata daria.Muryar k’anwarta taji a kan ta tana fad’in: 

“Anty Abee sannun da dawowa “! 

Fuskar ta a hade ta kalli kanwar ta. budurwar yarinya wacce ita ke bin ta, tana secondary School ss3 yarinya ce me shiru shiru da sanyin hali tana da matukar hakuri bata fiya son tashin hankali ba.ba kamar Abeeda ba sarkin zafin rai! 

“Dallah rufe min baki mara zuciya wacce bata san mai yake damunta ba!.Ke kina cikin gidan nan har a ma k’aninki gori amman ki kasa fita ki kwace masa y’ancin sa saboda tsoro?,wallahi matsoraci baya ta6a zama gwani a rayuwar duniya,idan har zaki zauna da wannan tsoron naki toh ki tabbata zaki mutu ne a yadda kike,ba zaki ta6a jin dad’in rayuwar ki ba muddin kika kasa kwato ma kanki y’anci kika sany’a tsoro a gaba “

Abeedah ta ida maganarta tana ture kular gabanta had’ida mik’ewa tana fad’in:”Ni kinma sa abincin ya fita a raina mtswwe ” 

Ta ra6a ta gefen k’anwar tata wacce ta kafeta da many’an idanuwanta tana kallanta cikeda tsoro dan ba k’aramin aikin abeedah bane ta kamata ta rangwad’a mata dukan tsiya.Fuuuu Abeedah ta shigewar ta cikin d’akin su tabar Mancy rik’e da baki tana mamakin tsananin zafin hali irin na Abeedah ita har k’annen nata ma bata bari ba kowa ya mata ba daidai ba shima sai ta masa ba daidai ba!

“Ummm Farhanar mancy zo kinji rabuda Anty Abee,zata sauko su Waleed sun 6ata mata raine ,kin san halin y’ar uwar taki da zafin ran tsiya ” 

Gyad’a kai kurum Farhana tayi tana jinjina Zafin zuciya irin ta y’ar uwarta wannan ai sai ta sama kanta hawan jini ko ciwon zuciya.k’aryane a ce yau an wayi gari Anty Abee ba tayi masifa da bala’i ba ko rashin lfy take a ka ta6ota sai ta tanka.

************************************ 

Washe gari 

Sai wajen 9:30 ta gama shirin ta tsaf dan wuce wa makaranta dan yau lectures d’in 10:30am take da shi, hakan ya sata tsayawa ta shirya tsaf ta gyara gidan su ta shirya k’annan ta suka wuce skul.Shigar rigada skirt tayi d’inkin ya amsheta sosai ta d’aura milk hijab akai dan shine kalar da zai fi shiga da kayanta,tattaro handouts d’in ta tayi ta sasu cikin handbag d’inta ta rik’e guda biyu a hannunta dan kar jakar tayi cunkoso,zira takalmin ta tayi kafin ta rataye jakar ta tafi to.

A barandar tsakar gidansu ta iske iyayen ta suna kalaci,murmushi tayi tana mai matuk’ar jin k’aunar iyayen ta har cikin ranta.Bata damu ko kad’an da rashin Asalin da ake cewa iyayenta basu da shi ita tana ƙaunar su a haka ko da kuwa a ce daga sama suka faɗo.k’ara sowa tayi wajen nasu ta durk’usa tana murmushi tace: 

“Abbi ina kwana,mancy barka da safia” 

Murmushi iyayen nata su kayi Abbi yace:”Abeen Abbin ta har an fito za’a d’aukar karatun?” 

Girgiza kai kawai tayi alamun eh,Abbi yasa hannunsa a aljihu ya ciro naira 500 ya mik’a mata yace:”Gashi ki k’ara kan wanda na baki Allah maki albarka ya taimaka a karatu ” 

Murmushi tayi tana fad’in ameen had’ida amsar kud’in da Abbi ya bata ,ta kalla Mancy tace:”Mancy zan tafi Kar ki kula kowa a cikin gidan nan idan sun kawo maki maganar habaici ,ki rabu da su inna dawo zan yi maganin kawunan su ” 

Murmushi mancy tayi dan ita tun tana galihar k’uruciyar ta tana amarya ma lokacin bata kulasu bare yanzun da take da zankad’a zankad’an ‘ya’ya da suka isa zuwa d’akin miji,ina ita ina maida habaici in banda abin Abeedah? 

“Toh Abee naji Allah dawo dake lfy ” 

Mik’ewa tayi tana amsawa da ameen Murmushi sa6e a fuskarta tafi to daga tsakar gidan su,tana kallon yanda ‘yan gidan nasu ke mata kallan uku saura kwata,bata da lokacin tsayawa mayar masu martani dan ta kusa makara amman ta d’au alk’awarin idan ta dawo zasu raina kan su.

“Mancyn yara Abee dai Allah ya nuna manaa ranarda zata daina wannan saurin zafin ran,irin su kam namiji mai halin ruwa ya dace su aura , in ba haka ba da matsala ” 

Murmushi mancy tayi tace:”Hakane Abbin su ,mudai cigaba da mata adu’a dole ta maida Abeen haka ai,mutanen duniyan ne yanzun dole kana yi kana nuna baka tsoro baka shakka ” 

********************************** 

Tana fitowa daga zauren gidan nasu ta iske k’awarta na jiranta .Saurin k’arasowa tayi ta bud’e murfin motar ta shiga ta zauna tana sauke ajiyan zuciya.Kallanta Suhailat tayi tace: 

“Lfy wannan ajiyan lumfashin?” 

Murmushi Abee tayi tace:”Bari kawai mutanen gidan mu ke son samun ciwon zuciya ” 

Ta sauke maganar ta tana yatsina fuska.Murmushi Suhailat tayi ta tashi motar suka soma tafiya .jefa kan motar saman titi tayi ,ta ɗan waigo ta kalla Abeedah wacce ke duba handout d’in hannunta suhailat tace: 

” ke yaufa Sir Salman garemu, lecture d’in Sir salman muke da shi first thing yau.baki ga irin wankan dana d’au ka yau na daban bane?” 

Suhailat ta ida maganarta tana wani kalan yauk’i da rangwad’a zuba k’amshi kawai take.k’are mata kallo Abeedah ta shiga yi sany’e take cikin wani dakakkiyar d’inkin super holland d’inkin yayi mugun yima Suhailat kyau ya zauna a jikinta d’as d’as,taci d’aurin ta irin na Zahrah buhari,ta yane gele a saman d’aurin nata,tayi kyau kam sosai,jin jina kai Abeedah tayi haɗi da ta6e fuska tana ma Suhailat d’in kallan uku saura kwata,bata san lokacinda ta buga wani uban tsaki tace: 

“Mtweeww iska tana wahalar da mai kayan kara ,kuta son mutum ni wallahi haushin sa nake ji ” 

Abeedah ta ida maganar ta,tana balloma k’awarta harara .Suhailat ta juyo ta kalla Abeedar cikin d’an 6acin rai tace:”Abeedah ya zaki ce kina jin haushin sir salman?toh ni son sa nake kuma so na tsakani da Allah nake yi masa,ki sani sabodo sanin cewa yau lectures d’in sa muke da shi kwana nayi jiya ina mafarkin sa.Kin san kuwa yadda nake son shi Abeedah?”…………

Gudun karta fad’ima Suhailat abin da ranta ba zai iya d’auka ba ,yasa Abeedah yin shuru ba tareda k’ara yima Suhailat d’in magana ba!,har suka isa makaranta. 

*BAYERO UNIVERSITY KANO*(BUK) 

Bayin Allah dake cikin wannan jami’ar keta kai kawo a farfajiyar filin makarantar.musamman students d’in da suke da lectures a halin yanzun,kowa nata hanzarin ganin ya shiga aji kafin malami ya shiga.Hakan ne ya kasan cewa su Abeedah bayan Suhailat ta sama wuri tayi parking motar ta ,ta kashe motar suka fito a tare,suka rufe murfin motar Suhailat ta danna remote key d’in motar ta kulle k’ofofin motar.Suka jero a tare suna tafiya cike da natsuwa,Suhailat tace: 

“Sora 10mns Sir Salman ya k’araso department d’in mu kin ga mu hanzarta kar ya hanamu shiga darasin yau,kwalliyata ta tashi a tutar babu.” 

Tale girar sama da k’asa Abeedah tayi  taja tsaki tace:” awww dama ba zuwan Allah da annabi kikayi ba?kin zo nuna ma Sir Salman kwalliyarki ne?mutum da ko kallo babu wacce ta isheshi a kaf jami’ar bayero?wlh watarana muke jama kanmu raini wajen lecturers d’in nan,Ni wlh bazan 6oye maki ba Suhailat na tsani ganin yanda wannan Sir Salman d’in ke disga duk wata mace data furtamai kalaman soyayya ,yazo aji ya disgata kuma ya bata carry over a caurse d’insa.Wlh ki iya takunki kar ya d’agoki ya saki d’aukan carry over a banza ki gaza graduating.Kyawu ai ba hauka bane akwai dubun sa da suka fisa kyau ” 

Tsaki Abeedah ta kuma ja wanda ya riga da yazama jinin jikin ta if batayi tsaki a rana ba toh bata da lafia ne ranar. 

Suhailat tace:” kede kika sani ” 

Idasa k’arasowa cikin department d’in su sukayi suna hanzarin shiga aji dan sun ga giftowan Sir Salman sun san cewa tabbas ya rigaye su shiga lectures theatre toh kuwa ranar baza su sama daman samun wannan darasin ba. 

Nan suka shiga kowacce tama kanta mazauni .students birjik  cikin aji maza da mata,masu aure da marasa aure ,zarawa da bazawarai, kowa na zaman jiran Sir Salman dan fara lectures. 

Wani kekkyawan matashin saurayi ne ya shugo cikin ajin.Suna ganin sa kowa ya soma kama kansa dan sun san halin sa ,sarai bai ɗau kan raini .Yauma kamar kullum ya shugo cikin theatre hall  ɗin dan bai wa students lectures.Fuskan nan tasa a murtuƙe kamar kullum ba annuri.Kekyawane a jin farko ,dogone mai faffaɗar ƙirji ruwan tarwaɗa ne Sir Salman,mai yawan gargasa ,yana da kwanta ciyar saje baqi suluk inka gansa zaka ɗauka ɗan ƙasar Ethiopia ne.Sir Salman kenan saurayi mai ji da kansa ga ilimi ga kuɗi ga yawaitar kwanta ciyar hankali, ga iya ɗau kan wanka yana da son gayu (ɗan kwalisa) kota ina dai wannan lecturer ya kai burin kowacce ƴa mace.mata basu gabansa ko kaɗan ,Ƴan matan jami’an Bayero suna yawan kawo masa farmaki wasu ko kunƴar taya masa jikin su basa yi ,shi kuwa bai ɗaukar wannan ɗabi’ar duk macen data masa haka baya ƙara wani tunani yake disgata ya bata carry over a course ɗin da.Shi yasa dayawa suka shiga taitayin su wasu har rana irin tayau suna gwada sa’ar su ko Allah zai sa su dace Sir Salman ya ɗan kula su. 

Story continues below


A haka ya gama koyar dasu har lokacin fitarsa a ji yayi.Dayawan ƴan matan ajin basu wani fahimci darasin sosai ba ,dan sun luliya duniyan tunanin Sir Salman kowacce da’abin da take ƙissawa a kan Sir Salman. 

Bayan fitan su lecture 

Suhailat ta kalla Abeedah wacce ke dialing lambar mahaifiyar su dan jin yadda ta wuni kira tayi not reachable hakan yasa ta haƙura Suhailat tace:
“Kin san Allah yau kwata-kwata ban fahimci darasin da Sir Salman yayi ba”
Taɓe baki Abeedah tayi tace:”ke kika so hakan ai” 

“Abee Please ki taimake ni ki sanar dani yanda zanyi da soyayyar Sir Salman wallahi ina ƙaunar sa ,Abee zuciyata gab take da tarwatsewa muddin Sir Salman bai amince da soyayyata ba pls tell me ya zanyi?”

Kafe Suhailat da manƴan idanuwanta Abee tayi , tausayin Suhailat ya mugun kamata,she knows cewa tabbas aminiyar ta na mugun son Sir Salman bata tunanin cewa Sir Salman zai amshi tayin soyayyar ta ,dan shi mutum ne ba mai gane gaban sa balle bayan sa, wahala kawai Suhailat zata sha, SO mugun ciwo ne wlh,ita ko kaɗan Sir Salman bai cikin ranta bata ƙaunar sa ,a duniya ta tsani wannan lecturer ɗin saboda zafin kansa , Suhailat kuwa mutuwar son sa take har yazo gaɓan da haƙurinta na naiman ƙare wa .Nisawa Abeedah tayi kafun ta soma faɗin: 

“Ki cigaba da haƙuri Suhailat ki bari har ranar da zamu kammala digree ɗin mu kafun ki amayarwa Sir Salman abin da ke cikin zuciyarki, kar So ya jaki kiyi dana sani kin ga dai yau sora 2wks kawai ya rage mufara jarabawar shiga 3lvl kima kanki Ihsani Suhailat kar wannan mutumin ya kadaki a banza ya saki dawowa ki gyara takardarki ni dai shawarar da zan iya baki kenan” 

Ni sawa Suhailat tayi dan tabbas maganar ƙawarta gaskiya ne Sir Salman baida imani ko kaɗan, gwara ta haƙura ta ruƙa tausasa Zuciyarta har su kammala karatun su lafiya.
“In sha Allah zanbi shawararki Abeedah” 

Gyaɗa kai kurum Abeedah tayi ta cigaba da tunanin ta kaman yadda ta Saba a kullum wanda ya riga da ya zame mata jinin jiki (tunani) 

4pm suka kammala lectures ɗin su, bayan sunyi salla suka wuce inda Suhailat ta faka motarta,suka shiga suka bar harabar makarantar suka kama hanyar gida.Tafiyan kurame suke kowa da abin da yake saƙawa a Cikin ransa ƙarar kasidar murja baba kawai ke tashi a cikin motar.Abeedah kishingiɗe kan kujerar motar ,ta lumshe idanuwanta babu abin da take in ban da aikin tunani, daka ganta zaka san cewa tabbas akwai abin da ke damunta a can ƙasar zuciyar ta wanda ta barwa kanta sani.Suhailat dai ganin shurun yayi yawa ne ta katse Abeedar ta hanƴar kiran sunanta: 

“Abee” 

A gajarce Abee ta amsa da”Na’am” 

Ɗan shiru Suhailat tayi tana tunanin abin da ya kamata tayi dan ganin Abee ta kauda wannan tunanin da kullum ke cinta a rai but taƙi tattaunawa da kowa a kai dan akwai ta da zurfin ciki. 

“Kodai mu biya Sahad store ne?muɗan yi siyayya?” 

Girgiza kai kurum Abee tayi dan tun bayan Sallar azahar take jin jikin ta wani iri tace:”No Suhay ki kaini gida kawai banjin daɗin jikina sam” 

Girgiza kai kurum Suhailat tayi, ta juyar da kan motarta ,ta saitashi hanƴar gidansu Abee (Janbulo) 

Suna isa Abee ta ɓuɗe marfin motar ta fito ta kalla Suhailat tace:”Thanks U Aminiyar ki gaida su Momy” 

Gyaɗa kai tayi tace”ki gaida su mancy as well kice ma Farhana nayi fushi da ita tunda taƙi zuwa gidan na mu” 

Murmushi Abee tayi ta girgiza kai ta rufe mata murfin motar kafin ta juya ta soma tafiya dan shiga gida. 

Suhailat kuma ta juya ta kama hanyar unguwar su (Zoo road) Zuciyarta cike da begen Sir Salman Allah Allah take ma dare yayi gari ya waye ta ganta a skul dan kawai ta sanƴa Sir Salman a kwayar idanun ta.

Ran ta a haɗe tamau ta shugo cikin gidan mutanen gidan su dake ta kai kawo suka soma ƙare mata kallo ba abin kayi mata magana ba,ta zageka tas a wajen amman halin Abeedah na mugun ɓata masu rai bata kallon kowa da gashi inka cire iyayen ta su kaɗai take darajawa.Bata gaida su sam dan basu isheta kallo ba,ba kaman ƙanwarta Farhana ba duk uwar gori da zagi da suke mata babu ranar da zata fito inta iskesu bata gaida su ba koda ko a ce basu amsa mata ba.

Langa langar gidan su da’aka zagaye tsakar gidan su ta ɓuɗe ta shiga.Sune kaɗai suka zagaye tsakar gidan su a duk cikin gidan hayar,hakan ko ya samo a sali ne tun irin tsangwamar da ƴan gidan ke gwada masu .An sasu a gaba ƙiris a ke jira suyi ƴan gidan ko ƴan unguwar sun dinga zagin su suna ce masu :” Banzaye marasa asali dad’in dai mu ansan asalin mu ku kam ba’asan asalin ku ba.Kawai kun faɗo daga wata uwa duniya kuna kama da aljanu D.S.S! 

Haka mutanen unguwa da ƴan gidan su ke mugun tsangwamar su kai kace ba halittun Allah bane tsaba ragen yadda a ke nuna masu tsangwama ƙiriƙiri a bainin jama’a.Hakan yasa Abeedah ta sowa cikin tsangwaman mutane daga ita har iyayen ta.wannan halin da’ake gwada masu shine silar wanzuwar tasowarta da zafin zuciya ko kallan banza kama Abeedah sai ta juyo ta tanka maka/ki ta zage mutum tas.Ba komai ya janƴo Abeedah tasowa haka ba face tasowa da tayi cikin tsangwama tun suna yara ƙiris a ke jira tayi a ce mata”banza wacce ba’asan asalin iyayenta ba ” 

Ita kuma Abeedah ganin hakan na shafan ƙannenta ,ba dama su shiga cikin jama’a an dinga masu gori kenan watarana harda duka a ke haɗa masu.Hakan ya sata pitittiƙewa a na ma ƙannenta abu zata shiga ta rama masu ,kan kace mai tuni Abeedah tayi ƙaurin suna a cikin unguwar su ,ta zama gagarumar mafaɗaciya,a cikin unguwar Janbulo babu wanda bai san ta ba ,harta kai gama mutane shakkar taɓa ta suke yi . kana ce mata kule zata ce maka chas kowaye kai kuwa, hakan ne ya fara Kawo masu sa’ida a cikin unguwar da ma gidansu har su fita su dawo bamai nuna masu yatsa . 

Wannan kenan

Tana shiga falan su ta iske mancy kwance tana karanta hisnulmuslim murmushi tayi tace:”Mancy inata sallama baki jiba” 

A zarihin gaskia zaka ɗauka karanta hisnulmuslim ɗin mancy keyi a baɗini kuwa hankalin ta na chan tana tunanin wani abun daban wanda ke mugun ci mata tuwo a kwarya. 

Firgit ta ɗago tana kallan ɗiyar ta wacce ta kafe ta da idanuwanta tana son karanto halinda uwarta ke ciki ganin hakan yasa mancy saurin tashi zaune tana ƙaƙalo murmushi dan tasan halin ƴarta Abeedah tsaf sai ta karanto damuwar da take ciki dan yarinƴar akwai kaifin basira . 

“Ah Abeen Abbin ta andawo?” 

“Mancy maike damun ki?ƴan gidan nan ne suka taɓaki?ummmm Gaya mun mai suka sake yi maki?” 

Abeedah ta jero ma mahaifiyar ta duka tambayar a lokaci ɗaya, girgiza kai Mancy tayi kafin tace: 
“Aa ko ɗaya babu wanda ya taɓa ni, ya karatu?” 

Sai a nan Abeedah ta saki a jiyar zuciya kafin tace:”ɗauka nayi yau ɗin ma sun sake taɓa ki ne da yau saina zubda haƙoran ko wani mahaluƙi dake a Cikin gidan nan” 

Murmushi Mancy tayi tace:”Aa jeki shirya ki fito kici abinci, yau ki mana tuwon shinkafa miyar eggusi” 

“Tam Mancy let me fresh up” 

Ta ida maganar tana wucewa cikin ɗakin su dan shirya wa. 

*********************************** 

After 3days 

Suna lectures Theatre Yauma Sir Salman ke basu darasi,ajin yayi tsit baka jin motsin kowa face Sir Salman dake tsaye ƙeƙam gu ɗaya yana jawabin darasin sa ga ɗaliban abin.Shurun da ya ɗan yi na wasu sakanni kawai sukaji ta fashe da wani kalan kuka babu abin da kake ji na amsakowa a hall ɗin face kukan Abeedah, kowa ya waiwayo yana kallon ta.Sir Salman ma kallon nata ya tsaya yi abin da bai taɓa yima wata ƴa mace a cikin jami’ar Bayero ba . Suhailat kuwa hankalin ta ya mugun tashi dan dama yau sukuku Abeedar tazo cikin makarantar tamata tambayar duniyar nan a kan maike damun ta taƙi tanka mata. 

Ita kuwa Abeedah babu abin da ya sata wannan kukar in banda tunawa da faɗan da’akayi da wasu maƙotan su jiya wani yaron maƙotan yayi jifa, Wannan jifar bai tashi sauka a ko ina ba in banda akan Mancy wacce ke zaune a tsakar gidan su tana tsifa, kawai taji a bu ya sauka a kan ta tim ,kan kace mai har jini ya ɓalle mata. Toh wannan a bun ya matuƙar tsayawa Abeedah a rai sun kai mahaifiyar su asibiti kuma ta roƙe ta da girman Allah a kan kar tayi magana tabar maƙotan nasu. Ita kuwa wannan maganar da Mancy ta hanata yi yaƙi barin ta ,tayi sukuni dan ita macece wacce bata iya barin a bu a cikin Zuciyarta.Tsananta ƙarfin kukan ta tayi tana shasheƙar kukan ta tana faɗin:

Tsananta ƙarfin kukan ta ta yi tana shesheƙa tana faɗin: “Me yasa zaki ce kar nayi magana Mancy?Mai yasa baki bar ni na ɓarar da haƙoran ɗan banzan yaro ba?Eh Mancy mai yasa kika hanani aikata hakan? kenan wannan jinin da nake gani yana zuba a kan ki zai tashi a banza? Khalifa zai tafi a haka ba tare da anmai hukunci ba kenan? yana sane fa yayi jifar nan cikin gidan mu.Ganin jinin nan da nayi a kanki bazan iya haƙuri ba,Khaleefah shima dole wani sashe na jikin sa ya fidda jini,shima yaji tsananin da ki ka ji” 

Abeedah ba tasan tana wannan sumbatun a bainar jama’a ba.
Kuka kawai take yi na ban tausayi, mutane sun raina su basa kallan su da daraja,duk da abin da Khaleefah ya aikatawa Mancy ba wani a cikin gidan da ya zo ya basu haƙuri ciki ko har da mahaifiyar Khaleefan. 

Gashi Abbi da Mancy sun hanata yin magana da babu abin da zai hanata sumar da Khaleefah. 

  Daga ƙarshe da ta ga kuka bazai amfana mata komai ba ta miƙe da hanzarin ta ,gudu-gudu tabar hall ɗin idanuwan kowa a kan ta.Kowa na mamakin abin da ya sanƴata kuka da sumbatu. 

Ciki ko harda Sir Salman, ya yi kokarin tuno yarinƴar domin fuska na nuni da kamar ya santa
‘she looks familiar to him,’
bai cika tsayawa ya karewa mutum kallo ba 

   Caraf ƙwaƙwalwar sa ya soma labarta mai inda ya san yarinƴar. 

27/08/2017 

  First semester exams

    Bayan sun fito daga Library)suka zarce Notice board dan duba results ɗin su.Abeedah da Suhailat tsaye suna jiran wa’d’anda ke gaban su kammala duba nasu sakamakon , suna barin wajen Abeedah da Suhailat suka soma duba nasu result ɗin ,kaman saukar aradu Suhailat ta tsinkayo muryar Abeedah ta na doka wani uban ashar da sauri ta waiwayo tana kallon Abeedar dan ganin abin da yasa ta wannan zagin: 

  “Kam bala’i kut wallahi yau sai anyi tashin- tashinan hankula a cikin wannan Jami’ar ni zai raina ma wayo?” 

  Ta ida maganar tana juyawa tana furzar da iska da huci,saurin shan gaban ta Suhailat ta yi tace : 

  “Abeedah meye haka ? Me ya faru?” 

  Tsaki! Abeedah tayi tana hura hanci da ka ganta zaka san ranta ya gama ɓaci . 

“Kina gani wai ni wannan lakcara ɗin zai sama absent a course ɗin sa?” 

Cikin mamaki Suhailat tace :”wani lecturer ?” 

“wannan mai baƙin halin mana,Sir Salman ” 

“Auzubillahi” 

Suhailat ta furta tana zaro idanuwanta waje . 

  “Wallahi yau koda Sarkin Aljanu lecturer ɗin nan ke taƙama babu abin da zai hanani tunkaran Sa he most tell me uwar abin da na mai da zai saka mun absent ” 

  Abeedah ta rinƙa surfa masifa da bala’i kowa yazo wuce wa sai ya tsaya ya kalleta , Suhailat ta rinka bata haƙuri ,ƙin sauraran Suhailat ɗin Abeeda ta yi , ta wuce fuuuuuuu! har zuwa offishin Sir Salman,da hanzari Suhailat ta mara mata baya . 

  
  Yana zaune kan kujerar a ofis ɗin sa ya haɗe rai da fuska tamau ,yana marking wasu takardu . Bai ji buɗewar ƙofa ba kawai jin maganar mutum yayi a kan sa 

  “Haba malam mai na maka da zaka samun absent a course ɗin ka?” 

Ɗagowa yayi cike mamaki ya zuba mata lumsassun kwayar idanun sa dake firgita ƴan mata, tare da yi mata kallon tsaf a ran sa yana faɗin :”wannan kuma daga ina?” 

Story continues below


  Daɗa haɗe ran sa yayi tamau ya a jiye biro ɗin da ke rike a hannun sa kafi yace :”Ke kuma daga ina?” 

Ba tsoro a tattare da ita tace :”Absent kasamun a course ɗin ka bayan da ni a ka yi jarabawar ” 

Taɓe baki yayi yace : ” Any prove ?” 

Ranta na mata suya tace : 

  “Yes wallahi a duba records ɗin makaranta babu inda ban yi signing ba” 

Bai ce uffan ba ya sa hannun sa cikin wani loka ya fiddo wani long note yaɗan duba .Tabbas she was present gashi nan tayi sign in, da sign out, but mai yasa bai ga takardar ta a cikin takardun da ya yi marking ba? 

  “U ware present but paper ɗinki absent ” 

  Ran Abeedah ya kuma ɓaci cikin masifa tace :” ya za’ayi ka ce haka bayan kafin na shiga exams hall nayi signing da zan fita nayi submitting nayi signing out yanzun kuma kace takarda ta Absent?” 

  Tunda yake a cikin jama’iar nan babu macen da ta taɓa ɗaga murya ta masa magana haka ,yau ga wannan ƙaramar yarinƴar da ba zata wuce 21 a rayuwarta ba tsaye tana masa masifa ? Abun ya ba shi mamaki da daure masa kai. 

  A fusace yace :” ƙarya aka  maki? da kinyi submitting baza’a yi marking ɗin bane ?” 

  Ita ma cikin fusata tace :” Malam wallahi wannan cuta ce a kan idon kowa nayi submitting paper yanzun kuma a ce wai Absent banyi exam ɗin ba? Kawai salon muguntane irin taku ta lekcarori in kuna da burin faɗar da mutum babu ta yadda bakwa yi” 

  Da ƙarfi Sir Salman ya furta :” Keeee!” 

Suhailat kam jikin ta banda rawa babu abin da yake yi ,”kodai Abeedah ta manta a gaban wa take tsaye ? Sir Salman ne fa ! In batayi wasa ba a yau ɗin nan zai iya sawa a koreta daga jam’iar nan.”

   Irin yadda ya gani ya faɗa ta mayar,ya faɗa ta mayar masa abin da tunda yake a rayuwarsa babu macen data taɓa kallan sa ra’ayul ayni ta faɗa masa magana abin ya ba shi mamaki .Cikin haɗa rai yace : 

  “Get out of my office now !” 

Ya Ida maganar yana nuna mata ƙofar fita. 

  Kaman Abeedah ta ɗora hannun a ka ta kwala ihu haka take ji a wannan lokacin .Sir Salman ya gama kasheta matuƙar ya mata haka shikenan zai ɓata mata result ɗin ta. 

   Cikin ƙunar rai tace :” Nabar ka da Allah in ina da hakkinka zai saka mun” 

  Ta ida maganar haɗi da juya  baya ta wuce fuuuuuuu Suhailat ma sum -sum tabi bayan ta. 

   Tsaki yaja ya koma ya zauna abin sa yana matuƙar jin zafin abin da wannan ƙanƙanuwar yarinƴar ta mai. 

   Koda suka fito ja tayi ta tsaya a bakin show glass door ɗin offishin nasa ,tana ma Suhailat banbamin ta kyaleta.
  
   Abeedah cikin kakkausar muryarta tace :”eeh haka kawai saboda yaga matan makaranta suna bibiyan shi zai zo yana gwadama kowa iko?,ni wallahi tallahi banƙi ko gidan redio inje inyi zayyana ba,a bi mun hakki na” 

  Ta inda take shiga dai banan take fita ba.Shuru yayi yana kallan ta yana kuma jin duk irin maganar da take faɗiwa ƙawarta,ji yayi ran sa ya ɓace shi wannan yarinƴar zata nuna ma hauka? mtsw bari zai nuna mata yafi ta iya hauka. 

  Zai nuna mata halinsu na lakcarori,miƙewa yayi yazo bakin ƙofar ya buɗe ya leƙo yace mata tazo. 

  Da kallan mamaki suka bi shi ganin yayi shigewarsa cikin offishin yasa Suhailat saurin zun gurar ta tace : 

“Bazaki bane ?” 

  Abeedah ta tura ƙofar ta shiga Suhailat kuma ta tsaya tana jiran ta. 

    Nuna mata wurin zama yayi ta zauna, paper ya ɗauka yaɗan yi rubutu kafin ya miƙa mata yace : “Ki amsa duka questions ɗin” 

Story continues below


  Ba tsoro ta amsa ,ta shiga amsa questions ɗin ,tas tagama ta miƙa masa.Ga mamakin sa gani yayi ta amsasu daidai kuma ta amsa duka questions ɗin. 

  Kawai tsayawa yayi ya kalla ya ƙara kalla,marking yayi mata a nan gaban ta ya sa mata 45 over 50 bawai dan bata cancanci cin duka bane a’a dan dai kawai bai sama hanƴar da zai ƙuntata mata bane kawai ya sashi rage mata score. 

  Kallan abin da ya sama ta kawai tayi a zuciyanta tace :”oho dai ko banza na sama A1″ 

  Shi kuwa ce mata yayi “now out” 

Dan ta kuma ƙular da shi tace “Thanks” 

Tayi gaba abin ta. 

Tun yana mamakin yarinƴar har yayi watsi da ita ya ma manta yadda take.Yau kam ya tuna ta shiru yayi yana mai jin tausayin yarinƴar a ran sa yace : 

“Kai wannan yarinƴar fa dama zafin ranta yayi yawa,duk yanda akayi akwai abin da ke damunta ” 

************************************ 

Straight keke napep Abeedah ta tara ta hau tace masa Janbulo,idanuwanta sun kumbura bata jin cewa in bata rama wa mahaifiyarsu abin da ɗan cikin ta yayi mata ba ,zata iya samun sukuni a cikin ranta.Koda ta koma gida ta iske ba kowa a tsakar gidan da alama basu fito ba ko sun tafi unguwa ,buɗe ƙofar tsakar gidan su tayi ta shiga. 

Sallama tayi ta ƙarasa shigowa cikin falon .Mancy na kwance kanta nane da bandeji kan na matuƙar yi mata ciwo shi yasa taɗan kwanta . 

  “Mancy!” 

  Da sauri Mancy ta buɗe idanuwanta ta sauke  su a kan Abeedah da tayi mata tsaye tana kallan ta .Mancy tace: 

  “Abee lfy kika dawo yanzun?” 

   Mancy ta Ida maganar tana yunƙurin miƙewa daga kwancen da take,saurin zama kusa da Mancyn Abee tayi tana mai taimakon Mancyn dan ta miƙe zaune .Mancy ta gyara zaman ta,kanta na mugun sarawa  ta duba Abeedar da duk hankalin ta ke akan ta: 

  “Mancy taya zan iya zama na ɗauka lectures bayan an taɓamun lafiyarki?”
    
   Kallonta sosai Mancy tayi kafin tace : 

“Abee mai ya samu idanuwanki suka kumbura suka sanja launi?wani abun ne ya faɗa a idanun naki?” 

  “Mancy ki amincemun yanzun ba anjima ba na koyawa mutanen gidan nan hankali.Mancy wlh in baki barni najima wannan Khaleefan ciwo ya kwana asibiti, ba zaku Iya samun kaina ba,Mancy wai taya zaki gane cewa ban son komai ya taɓa ki ina ƙaunar ki ina matuƙar son ki a rayuwata.I can’t resist naga anacin duduniyar ki a cikin gidan nan. kawai dan wani zance nasu na rashin Asalin ku keda Abbi da a ke cewa ba kuda shi .Manc………….. 

Kuka ne yaci ƙarfin Abeedar ta kasa ƙarasa maganar ta .Rungume ta Mancy tayi tana ɗan bubbuga bayan Abeedar,zuciyar ta na ƙunci da zafi a yanzun sosai take nadamar barin ahalinta da tayi tazo cikin bare ana gwadamata ƙiyayya ita da ƴaƴanta da mijinta da sun sa cewa ita wacece ko kuɗi a ka basu su aikata mata hakan baza suyi ba.An mata iyaka da sake zuwa wajen ahalinta dole su runguma ƙaddarar su a haka ,Allah yafi su sanin dalilin yi masu hakan. 

   A ranar zazzaɓi mai tsanani ya rufe Abeedah kwananta biyu ba ta zuwa makaranta .Yau kam jikin nata da ɗan sauƙi dan har share gidan su tsaf tayi ,Mancy data farka ta iske Abeedar na shara harma ta kammala tattarawa kawai take ,ta mata faɗa sosai. 

  2:30Pm
Tana zaune kan kujerar falon ɗakin su tana shan magani  tajiyo Sallamar Suhailat amsawa tayi , Suhailat ta ƙaraso cikin falon tsayawa turustayi kafun tace: 

   “Abeedah Usman baki da lafiya ne?jiba yadda kika rame just in 2days.” 

Suhailat ta Ida maganar ta ,tana ƙarema Abeedah kallo.Muryar Mancy suka ji tana cewa: 

  “Yauwa Suhailat faɗa mata dai ,kiga yadda mutum ya rame a kwana biyu kachal kaman wacce a ke tsotse ma jini,ƙawarki nason sama kanta ciwon zuciya fa da hawanjini .ki taimaka ki mata faɗa ta rage wannan zafin zuciyar nata .in taƙi kuma ta sama kanta ciwon zuciya ba mai auran mai ciwo kam” 

  Mancy ta ida maganar tana fita daga falon dan ɗaura sanwar rana kafin su Farhana su dawo. 

  Guri Suhailat ta samu ta zauna tace: 

  “Abee wai dan Allah maike damunki? Duba fa shekaran jia yadda kika ruɗamu ,ana ta cecekucen cewa Aljanu kike dasu shi yasa kike kuka kina sumbatu ,and 2days baki zo lectures ba.Kin san dai mun kusa fara exams ” 

  Kallonta kawai Abee keyi ba tareda tace komai ba kuma da dukkanin alamu ba tada niyyar cewa komi . 

  “Tambayar ki fa nake Abee mai ke damunki?” 

“Niba abin da ke damuna ” 

  “Badai zaki gaya mun abin da ke damunki bane kawai zaki ce ” 

  “Eh bazan faɗa maki ba” 

  Tsaki Suhailat taja tace :”chan dai ta matsemaki ,dama handouts na tattaro maki ,Sir Salman yayi covering duka syllabus ɗin sa jiya ” 

  Ƙarɓa Abee tayi tana jinjina kai,ta ajiye su a gefen ta.Suhailat ta dube ta tace: 

“Kinga Abee ki tsaya ki duba handouts ɗin nan ,ki karance su tas.Yace zai yi tambayar bazata a kan su ,kin san Sir Salman baida mutunci yace minus 20 marks if mutum ya kasa amsa mai.gashi yau sora 5days mufara exams pls kiji sauƙi kixo lectures gbe” 

  Suhailat ta ida maganar tana shagwaɓe fuska.Murmushi Abeedah tayi tace: “Toh sarkin shagwaɓa ngde” 

  Sun ɗan taɓa hira daga bisani Suhailat ta mata Sallama ta wuce.

Haka tawuni ranar sukukuu .Da daddare har tayi addu’a zata kwanta ,ta kasa bacci ta fara tuna abubuwan dake damun rayuwar ta,sam bata son tunanin .hakan yasa ta ɗan waiwayowa idonta ya sauka a kan handouts ɗin da Suhailat ta kawo mata. 

Janƴo handout ɗin tayi ta buɗe tasoma karantawa a hankali tana grapping abin da ya dace .haka dai harta dire karatun handouts ɗin duka.Bayan ta kammala karatun handouts ɗin ta a jiye gefe.gyarawa Farhana kwanciyar ta tayi ,ita ma ta gyara kwanciyar nata haɗida tofe jikinta da addu’a..

  Mafarkin karatun da ta yi ta rinƙa yi a cikin baccin ta. Allah Ya bawa Abeedah wata irin baiwa, duk wani abu da tayi shi last kafin ta kwanta bacci tana yin mafarkin sa. 

Yanzu ma hakan ce ta kasance mafarkin karatun da ta yi ta rinƙa yi, hakan ya taimaka wajen zaunawar karatun sosai a cikin kwakwalwar ta. 

Washegari da ta farka sai ta ji jikin ta ya yi sauƙi sosai, wanka ta yi sannan ta shirya ta fito falo. Abbi da Mancy suna Zaune a cikin falon suna hira. 

Murmushi ne kwance a fuskar Abeedah, yayin da ta ƙaraso wajen iyayenta duƙawa ta yi tana faɗin 

“Abbi Mancy barkan ku da Safiya” 

Abbi da Mancy suka saki murmushi sannan Mancy ta amsa da “Lafiya lau ƴar albarka, ya jikin naki?” Abeedah ta ce “Da sauƙi Mancy” 

“Allah Ya ƙara sauƙi ɗiyar albarka, Ya yi maku Albarka keda ƙannenki, Ya kare ku daga dukkanin wani sharrin aljani da mutane, Allah baki miji nagari Abee na.” 

Abbi ya ida maganar sa yana murmushi. “Ameen Ameen Abbi na, Allah ya ƙara maku tsawon rai tare da lafiya mai ɗorewa kai da Mancyn mu.” Abeedah ta amsa. 

Sosai wannan addu’ar na mahaifinta.ta yi mata daɗi, za ta iya bugar ƙirji tace tunda take a rayuwar ta daidai da rana ɗaya iyayensu basu taɓa buɗe bakin su da sunan sun zage su ba. 

Ko laifi suka yi na faɗa iyaka a yi masu faɗa a ɗora masu da nasiha,”Allah ya shirya ku cikin addinin musulunci.” wanna ita ce addu’ar da suke mana a koda yaushe. 

A tare Mancy da Abbi suka amsa da “Ameen.” cike da jin daɗi. Sallama ta musu sabo, da za ta tafi makaranta.fatan dawowa lafiya su kayi mata, sannan ta wuce. 

Takawa ta yi a ƙafa har zuwa bakin titi dan samun a bin hawa, waɗanda suke wucewa jefi-jefi a layin su sunƙi tsayawa .Tsaki taja ganin tana neman yin latti, tafi mintuna talatin tana jiran a bun hawa kafin ta samu. 

Da kyar ta samu wani ya tsaya tana shiga tace “BUK” ranta duk a jagule dan ta yi latti ba kadan ba. Da sauri-sauri ta shigo harabar makarantar, straight department ɗin su ta shiga. 

Ganin malamin ya riga ya shiga aji har ma ya fara gabatar da lecture yasa cikin ta ɗurar ruwa, domin ƙa’idar sa ne in har ya riga student shiga aji, to haƙuri kawai za ka yi dan ranar ba za ka samu damar shiga lecture ɗin saba. 

Rakuɓewa ta yi a bakin ƙofar theatere hall ɗin abin ta. Cikin hall din kuwa tambayar students ɗin Sir Salman ya shiga yi a kan previous lectures ɗin daya masu. To his surprise gani ya yi ba mai amsa mai question ɗin, kaman bai koyar dasu wajajen ba. 

Ransa ne ya ɓace cikin fushi ya fara magana “Haka kuke daƙiƙai dama? i thought jiya jiya na yi darasin nan? and I told u guys at anytime zan iya yin tambayar bazata a kan handouts ɗin, oh kun ƙi yin bitar sa ko? kun yi zaton ba zan yi tambayar yau ba, hmmmm kun kyauta ina zuwa.” 

Cike da ɓacin rai sir Salman ya fice daga hall ɗin. Students suna ta gulmar sa, duk uban handouts ɗin da ya basu jiya jiya yake tunanin su karance duka a rana ɗaya? And again in summary (a dunƙule) ya yi masu bayani “mtswww sir Salman da matsala ya ke.” cewar wata daliba. 

Haka dai suka riƙa tofa albarkacin bakinsu. Ganin yana tunkarar ƙofar fita na hall ɗin Abeeedah tayi maza ta ɗan ɓoye a bakin ƙofa. Fita ya yi ganin ya tunkari wajen da ya yi parking din motarsa Abeedah ta yi wuf ta shige cikin hall ɗin, ta sama guri ta zauna tana daidaita numfashin ta.

Story continues below


Shigowa ya yi cikin a jin ransa a jagule, ganinta ya yi zaune tana daidaita natsuwarta, mamaki fal ran Sir Salman dan ganin Abeedah yau.Tun kwana biyun da suka wuce ya ke ta mamakin rashin ganin ta da bayayi cikin ajin, yaɗan ta dube-dube ko zai ganta dan yaɗan fara lura da yarinƴar. 

Suhailat kawai yake gani amma girman kansa ya hana shi tambayar ta rashin ganin Abeedar da ba ya yi kwana biyun. Tsintar kansa ya yi yana cewa “Keeee!” 

Cak Abeedah ta tsaya da ciro handout ɗin da take shirin yi a jakarta, tasan da Ita yake dan daidai saitin ta ta jiyo maganar sa kowa a cikin a jin a ka waiwayo ana kallan Abeedah. 

Cikin rashin gaskiya Abeedah ta waigo ta ɗan saci kallon sa, an ci sa’a shima itan yake kallo, hakan ya sa idanuwan su samun damar sarƙewa dana juna. Haka kawai Abeedah taji gaban ta ya buga da ɗan ƙarfi, shima sir Salman a wajen sa hakan ce ta faru. 

Saurin kauda idanuwanta ta yi tare da miƙewa tsaye shima cikin basarwa ya ce “Yaushe kika zo?” miyau ta haɗiye muƙut kafin ta ce “Tun ɗazu.”
   
Duban rashin yarda ya mata sannan Ya ce “Ya akayi ban ganki ba?” Ya ida maganar yana mai kafe ta da idanuwansa, duk ta birkice dan sir Salman akwai kwarjini, in dai ku ka haɗa ido da shi sai ka birkice ka kasa sanin abin cewa.  

“Ammm..uhmm” Abeee ta fara kame-kame, haɗa rai ya yi sannan ya ce “Faɗa min da na shigo cikin a jin nan me na fara tambaya?” Ruɗewa sosai Abee ta yi tana ƙiƙƙifta idanu alaman mara gaskiya ta ce “umm… umm” tanayi tana sosa idanuwan ta yanayin yadda take da idon sai ya ji hakan ya birgeshi. 

“Ummm munafuka” ta tsinci muryarsa yana faɗa  mata. Ai kawai ‘yan ajin suka tuntsure da dariya, ita ma yanayin Yadda ya yi maganar ya bata dariya, kawai sai ta tuntsure da dariyar har kumatun ta na lotsewa can ciki, sai ya tsinci kansa da shagala wajen kallonta. 

Maganar da ta fara ne ta katse shi “Dan Allah malam ka yi haƙuri” ta karasa maganar da murmushi a saman fuskar ta. Murmushin ya yi shima kafin ya ce “Hmmmm toh na haƙura zauna.” 

Zama ta yi shi kuma ya wuce ya tsaya gaban ajin ya fara masu wasu tambayoyin. Nan ma suka yi shiru suka kasa amsawa ran shine ya sake ɓaci, cikin yanayin fushi ya fara cewa “Yanzu dan Allah duk lectures ɗin da nake yi maku a banza nake yi kenan? na muku darasin nan ba wai ban maku ba, but ina maku tambayoyi a kai kun kasa bani amsa?. 

Yanzun waye zai iya amsamun koda questions ɗaya ne? i promise duk wanda na tambaya ya amsamin daga farkon lectures ɗina da mu ka yi a wannan semester har zuwa yanzu zan bashi wannan wayar” 

Sir Salman ya karasa maganar yana ciro wata sabuwar danƙareriyar iPhone 7+ a cikin aljihunsa. Nan aji suka soma cecekuce suna faɗin “Kai malam irin wannan babbar wayar haka za ka kyautar? Ga duk wanda ya amsa maka? malam dan Allah ka ɗaga mana zuwa gobe.” 

Murmushi ya yi ya ce “No garaɓasar ta yaune kaɗai” Suna ta surutai a kai, kowa nason ya ga shi yaci kyautar Sir Salman. 

Shiru Abeedah ta yi tana tuna cewa jiya fa ta duba handouts ɗin nan, tunani ta fara yi dan dama ita duk abin da tayi mafarki a Kai in ta yi tunani tana recalling ɗin shi, nan kuwa tayi recalling komai tas ya dawo cikin kwakwalwar ta. 

Sir Salman ya ce “So now my first question wa zai miƙe ya amsamin?.” Ya ida maganar yana kafe ɗaliban nasa da idanuwan sa. Har ya cire ran ba me amsa masa kawai ya tsinko muryarta tana faɗin “Sir zan amsa.” 

Abeedah ta ida maganar tana miƙewa tsaye idanuwan kowa ya koma kanta, murmushi Suhailat ta yi dan tasan tabbas ƙawarta za ta amsa duka tambayar da Sir Salman zai yi daidai. 

Shima cikin mamaki ya ke kallon ta yace “kin yarda za ki amsa duka tambayar?” Gyaɗa kai Abee ta yi alamun eh, murmushin gefen baki ya yi kafin yace. “In fa ba ki amsamin tambayoyina daidai ba ni zan amshi wayar hannun ki.” 

Story continues below


Dariya duka ƴan ajin suka sa ya cigaba da cewa “Idan kuma ta cinƴe ni ne zan bata wannan wayar, ga ta nan na ɗauka but idan bata ci ba ita zata bani wayar ta, kin yarda?.” 

Sir Salman ya ida maganar yana kallan Abeedar, nan kowa a cikin hall ɗin ya shiga zugata “ah karki yarda Abeedah, tambayoyin zafafa ne ba za ki iya amsasu ba.” 

Murmushi kawai Abee ta yi kafin tace “Sir na yarda” Dan ta rigada tasan abin da ta taka. Murmushi Sir Salman ya yi kafin ya wurgo mata wani zazzafar tambaya, da kowa yacire ran Abee za ta iya amsawa. 

Amma kamar almara suka ji kawai ta fara amsa masa tambayar daidai, kowa cike da mamaki a ka shiga dubanta. Sir Salman kuwa tsananin mamakin ta ya sa shi sake wurgo mata wata questions wanda tafi na farko zafi. 

Nan ma ta amsa masa daidai kawai ji ya yi yana jin daɗin yadda take bashi amsa correctly, nan ya cigaba da wurgo mata tambayoyi tana amsa su. Shi kuwa Sir Salman in dai tabashi amsa sai ya dunƙule hannun sa yana faɗin “Wow!” 

Idan ta ƙara amsawa ya ce “Smart girl bravo… ma sha Allah.” ‘yan a jin kuwa yanayin yadda yake yi yasa suke ta dariya, ji suke dama a ta zama a haka. 

Yau Sir Salman miskilallan malamin nan shine tsaye a gaban su yana wasa da dariya, dama yana wasa? yana fara’a yana dariya? tambayar da suke yiwa kawunansu kenan. 

Musamman Suhailat data lula duniyar tunanin Sir Salman, ina ma ace ya tsaya a haka yafi kyau. Hatta sauran ɗaliban makarantar wadanda ba ‘yan ajin ba ma fitowa suka yi a ka tsaya ta window ana kallon yanda Sir Salman yake wasa yana dariya.” 

Bayan ya kammala tambayoyin sa zai fita ya kalleta kafin ya ce “Ke kam ai kinfi ƙarfin wannan 7+ ɗin, wayar hannuna kinga wannan wayar da yake hannuna? Ita zan baki saboda babu wani student daya taɓa burgeni sama da abin da kika yi na amsa dukkanin tambayoyina. Sabo da haka wayata yanzu zan cire na ba ki.” 

Nan da nan ‘yan ajin suka ruɗe ana ta “Sir X-mas ɗin ka za ka bata?” Kaza da kaza da kaza. Shikam ko kulasu bai yi ba ya cire sim ɗin sa a wayar da duk wani abu muhimmi nasa, ya mayar a cikin sabon wayar da a da yace zai bata. 

Miƙa mata wayar ya yi ita kuma cikin ƙunya tasa hannu da ƙarɓa. ‘Yan aji suka riƙa ihu suna tafi suna faɗin “oh Abeedah kar ki karba sai an muku hoto wannan ai abin tahiri ne.” 

Murmushi Sir Salman ya yi Abeedah ta fito daga wajen mazaunin ta ta ƙaraso wajen Sir Salman ɗin ‘yan aji suka riƙa masu hotuna, Suhailat ta karbi wayar da Sir Salman ya baiwa Abeedar, ta shiga kakkashe masu hotuna.  

Kallon ta ya yi  yana murmushi ya ce “Kiɗan murmusa mana.”
Sai kowa ya fashe da dariya, nan aka riƙa masu hoto wasu unexpected duk a ke masu, Suhailat ta shigo tsakiyar su itama a ka kashe masu hoto tare suna murmushi. 

Ganin malam ya sake ana ta hotuna yasa ‘yan ajin duk shiga aka ɗauki salfie. Abeedah daɗi take taji abin ta wanda bata san dalilin yin hakan ba. Suhailat ma sai daɗin take ji yau ƙawarta tasa masoyinta nishadi. 

********************************* 

Tun daga wannan ranar Sir Salman ya fara kula da yanayin ta, tabbas yana karantar damuwa shimfiɗe a fuskar Abeedah. “Shin me yake damun ta?” ita ce tambayar da yake wa kansa a kullum. 

Yau ma kamar kullum bayan sun kammala lectures ɗin farko fitowa suka yi dan shan iska. Abeedah da Suhailat zaune suna hira a kan jarabawar da za su fara nan da kwana uku, Suhailat ce ta katse hirar tattaunawar tasu da cewa 

“Abeee Ina son Sir Salman da yawa,ina  matuƙar son sa ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba, ban san yadda zan lallashi zuciyata a kan daina son wanda bai son ta ba.” 

Abeee wacce tun fara maganar Suhailat ɗin ,ta kafe ta da idanuwanta tana sauraronta, jin ta kai aya yaɗan sata murmusawa tare da cewa… 

“Allah Ubangiji ya ba ki Sir Salman. Allah ya karkato miki hankalin sa gare ki, Rabbi ya danƙa maki zuciyar Sir Salman duk duniya yaji babu wacce yake ƙauna sama da *Suhailat Yusuf Maitama autar Momy da Daddy.* 

Abeedah ta karasa maganar tana murmushi wanda har sai da kumatun ta suka lotse can ciki fararen haƙoran ta dake ɗauke da wushirya suka bayyana. 

Ba kasafai za ka ga Abeedah na irin wannan murmushin ba, dan ba ɗabi’ar ta ba ne fara’a, balle dariya ko murmushi mai fidda kyawu. 

Dariya sosai Suhailat tayi tana mai jin daɗin addu’ar da Aminiyar ta tayi mata tace “Ameen.. Ummm Abee kina da kyau sosai wani zubin har mamaki nake anya ku ƴan Nigeria ne kuwa? Bakwa kama da ƴan Africa, kun fi kama da Larabawa kaf gidan ku.” 

Ganin Suhailat za ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi yasa Abeedah saurin sauya zancen ta hanyar faɗin “Sir Salman ya yi dacen mata, muddin ya auri Suhailat Yusuf mace tamkar da dubu zarah a cikin wata, kyakkyawar matashiya mai sanyin hali, da kaifin basira. 

Shin wacce aljanar ce take tsolewa Sir Salman idanunsa har baya iya hango Suhailat ɗin sa?, Mace mai ƙaunarsa tsakanin ta da Allah, take yi masa soyayyar gaskiya ba soyayyar da yawan ci yan mata kema samari a wannan zamanin ba.”

Ƙyalƙecewa da dariya Suhailat tayi kafin ta ce “Oh Abeedah yau dai cikin raha kike ko? wannan irin kirari haka” Suhailat ta ida maganar tana ta dariya. 

Abeedah ma na taya ta tun daga wannan lokacin Suhailat bata da magana in banda na Sir Salman, komai Sir Salman dai dai da abinci in za ta ci harda na Salman take siya taci in ta kammala cin nata..Abeedah tayi ta mata dariya.

********************************* 

  Washegari 

Abeedah ta tashi cikin nishaɗi haka kawai ta ji ta tana nishaɗi ƙannenta na tambayar ta yau me a ka mata take ta fara’a kodan an bata kyautar wayane?. Murmushi kawai ta.musu dan bata son abin da zai ɓata mata mood ɗinta. 

Ko a hall yau sai faman zuba murmushi take. Sir Salman na shigowa ya isketa tana wannan murmushin shima murmusawa ya yi, hakanan yaji sa shima cikin nishaɗi dan kawai yaga Abee itama kamar tana cikin nishaɗi yau. 

Jinsa kawai ya yi cikin farin ciki, hakan ya sashi sakewa yau da student ɗin ya soma jan su da hira, yana basu abin dariya. Takawa ya yi yau har zuwa ƙarshen ajin ya tsaya, abun da bai taɓa yi a cikin jami’ar ba. 

In ya shigo aji tsayawa yake ƙiƙam a gaban hall ya haɗe fuska  ya bada darasi in ya kammala ya fita. Duka ƴan a jin suka waiga suna kallon sa musamman ma Suhailat da Abeedah nisawa ya yi yace 

“Wai! Tunda na fara lectures a cikin jami’ar nan yau ne ranar farko dana zo ƙarshen hall ɗin nan.” Dariya suka tuntsure dashi kaman haɗin baki suka ce “Toh sir me ya sa?” 

Shima sir Salman ya yi dariya kafin yace…

Sir! Salman yayi dariya shima, kafin yace:
  
  “Hummm! kun ji ku fa,toh tsoro nake kar ku cinƴe ni” 

Ya ida maganar yana mai satan kallon Abeedah wacce ke taya ƴan uwanta ɗalibai dariyar da suka tuntserewa  da shi. 

   Al’amarin ya sanya kowa  jin daɗi ,yau Malam ya saki fuska ana ta wasa da dariya .Shi kam Sir Salman farin cikin daya gani a tattare da Abeedah shine silar wanzuwar tasa farin cikin ,yaje nan yaje chan yana ta basu abin dariya ana wasa da dariya. 

  In yayi abin dariya sosai Abeedah take ɗarawa ,kawai sai yaga ta tuntsure da dariya itama, hakan kawai yaji farin ciki sosai a cikin zuciyar sa . 

  Hakan ya sa shi cigaba da tsokano abun  dariya dan dai kawai yaga Abeeda tana dariya. 

Tsayawa yake ya kalla yadda take dariya yanajin daɗin hakan a cikin ransa. 

   Sosai ƴan ajin ke mamakin chanzawar Sir Salman ,dan yanzun sosai ya sake da su yana wasa da dariya a cikin hall ɗin.in zai yi lectures fuskan sa a sake yake yi masu,yayi bayani sosai har sai ya tabbata sun fahimta yake fita daga ajin . 

saɓanin a da da  bai damu a kan a gane karatun sa ko kar a gane duk ruwan ka ne ba nashi ba. 

Sosai a ke ta cece- kucen sauyawar Sir Salman farat ɗaya har suna  zargin cewa ,”anƴa  kuwa ba aljanar da ta aure sa ba ce take zuwa cikin hall ɗin tazauna shi yasa yake fara’a da kowa ba?” 

   Ire iren wa’innan zargin dai dukkanin students ɗin keyi.
   
A ranar Sir Salman ya kammala masu komai .yayi masu fatan alkairi dan wannan ne ajin sa na ƙarshe dasu a wannan semester ɗin .Dan farawar exms ɗin su in 2days time 
  ************************************* 

  Sosai Abee ta mayar da hankalinta wajen karatun jarabawar ta.Mancy ce ta dubi ɗiyar ta tace: 

  “Abee ki huta karatun haka mana kizo kici abin ci” 

  Murmushi Abee tayi tace :
“Mancy ai kawai bari na ƙarasa karatun nan gbe fa saura a wanni 15 tayi” 

  Farhana tace: 

  “Anty Abee Kidai ci abincin ta kunnan karatun zai fi shiga ma ” 

  Dariya Abee tayi kafin tace :”Ok Dr Farhanatu”.
  
  Ta ida maganar cikin sigar zolaya.Mancy tace : 

“Kinga Farhana maza miƙe kije ki ɗau Haris a makaranta lokacin tashin su yayi ” 

“Ok Mancy Bari nayi Salla naje” 

*********************************** 

  Washegari su Abeedah suka fara exams ,sosai kowani ɗalibi ke ƙoƙarin ganin ya cike takardar sa suna masu fatan tsari da carry over .

  Yanzun kam Sir Salman yakan yi magana da Suhailat in ta gaisheshi Yana amsawa Shi kuwa yana amsa mata ne kawai dan tana ƙawar best student ɗin shi (Abeedah).Hakan kuwa ba ƙaramin yi ma Suhailat daɗi yake ba nan da nan taji soyayyar Sir Salman na linkuwa a dukkanin sassan jikin ta. 

*********************************** 

Yau suka rubuta last paper ɗin su bayan sun fito daga exams hall suka wuce wurin cin abinci dan su ɗan huta .Suna zaune suna fira Suhailat tace: 

“Abeee wallahi ina mutuwar son Sir Salman barin ma yanzun da yake ɗan kulani yana amsa gaisuwata ji nake kaman na fi sauran mata a duniyar nan sa’a” 

Dariya Abee tayi kafin ta jinjina kai tace:. “I see kin kuwa san mai nayi tunani kuwa Suhai?” 

  Girgiza kai Suhailat tayi kafin tace :”Aa ƙawas ban nasha tunanin mai kikayi ?” 

  Nisawa Abeedah tayi kafin tace:”Tunani nayi ko nace shawara ce nayi tunanin baki a kan Sir Salman “. 

  Gyara zama Suhailat tayi tace :”Ban shawarar mana ke kuwa Aminiyar ” 

   Murmushi Abee ta saki sannan tace: 

  ” Why not muje kawai ki faɗawa Sir Salman cewa kina son sa ? Tunda dai kinga yanzun yana magana damu sannan his friendly zai fahimce mu sosai.koya kika gani?” 

Shuru Suhailat tayi tana nazarin zancen Aminiyar ta .tasan Abee bazata taɓa bata shawara mara kyau ba,a daa ita ke kwaɓar ta a kan karta kuskura ta tunkari Sir Salman da zancen so . Yanzun ita da kan ta tace mata taje ƙila tana hango mata nasara a tattare da hakan ne. 

Bazata bar wannan damar ya suɓuce mata ba. 

  Suhailat tace :”Anƴa kuwa Abee kina ganin zai amsa tayin soyayyata kuwa?” 

  Murmushi Abee tayi kafin tace : 

  “Mai zai hana sa amsar tayin soyayyar ki Suhay?kina fa da kyanki ke kekkyawa ce uwa uba ga ilimi ga tarbiyya .Duk wani abun da namijin kirki ke naima wajen mace toh fa tabbas kina dashi. 

  Murmushi Suhailat tayi kafin tace :”Ngde Abee  nasan bazaki taɓa bani gurɓata ciyar shawara ba ,muje ki rakani na gwada sa’a ta.Allah ya ɗora ni a kan sa.” 

Murmushi Abee tayi tace :”Amin ya Rabbi” 

Miƙewa su kayi suka wuce offishin Sir Salman,Sallama su kayi ya amsa masu haɗi da basu izinin shigowa ciki. 

Shiga sukayi suka samu wuri suka zauna  suka ce : 

“Malam sannu da hutawa” 

Murmushi kwance a fuskar sa ya ɗago ya kalle su kafin yace : 

  “Ah’ah Abeedah Usman ɗan batta da Suhailat Yusuf Maitama ,ya akayi ne ?ya kuke?ya rayuwa? ya naga kuna murmushi ko kunyi hira da samarin ku ne?” 

  Dariya sukayi sosai, da yake yanzun ya saba yi masu wasa da dariya hakan yasa ba suyi mamakin furucin sa ba. 

A tare su kace :” malam dama wani abu ne ya kawo mu”! 

Suka ida maganar su suna kallan junansu ganin hakan ya sashi murmushi yace : 

  “Ina jin ku ƴan mata ku faɗamun ” 

  Duk a tunanin Sir Salman Abeedah tazo faɗa masa cewa tana son sane ,hakan ya sashi maida hankalinsa kacokam wajen su yana jiran jin abin da suke shirin faɗi masa . 

  Tsintar  muryarta yayi tana magana cikin tausasa harshe : 

  “Dama wlh malam Suhailat ce …tace tana son ka wlh tarasa yanda za tayi ……………” 

  Ba haka kunnen sa yaso ji ba.abin da kunnensa ke tsumayin  su jiyo mai daga bakin Abee ba shi take faɗi masa ba. 

ran shine ya ɓaci daka mata tsawa Sir Salman yayi wanda yayi matuƙar razana su .A tunanin su ma ko aljanar shi data auresa ne ya tayar. 

cikin kakkausar muryar sa yace:

  “Look! Ku kalleni dukan ku” 

Suhailat kam sarkin tsoro har jikinta yafara karkarwa da kyar ta iya ɗagowa ta dube shi,itama Abee ta kallesa. 

  Kiran sunan su yayi yace : 

  “Abeedah, Suhailat” 

   Ya ɗan tsaya da maganar sa yana duban Suhailat kafin ya ɗaura da cewa: 

  “Suhailat! dube ki ,kina da  kyau,kina da tsari kina da ilimi ,kina da komai. inaso kiyi haƙuri kina sona Amman ni kuma 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page