GAMAYYAH CHAPTER 13

GAMAYYAH








CHAPTER 13







Zaune suke dukkaninsu gaban boka aqoob dayayi shiru cikin jinjina mataki na qarshe dazai fada musu sbd aljanun dayake aiki dasu sune suke fada masa komai gameda sarauniya mineelik sbd suna cikin maqiyan farko na sarki penya. 5

Kallonsu yayi ‘daya bayan daya
Dukkaninsu kowanne ashirye yakeda karbar matakin qarshe ‘din sbd yanxu sunkai iya maqurar ganin cikar burin sbd Jamal dasukaga yafara shiga hanyarda bazata bulleuba su duka.

Wasu irin qananan wuqaqe farare tas guda shida masu kamar azurfa ya fitar daga wani irin rami ya ajiye agabansu tareda kallonsu yace,

Wannan wuqar dafin jinin penya ce wadda duk duniya ita kadaice zata kashe sarauniya mineelik,
Kowannenku zai soketa da wannan wuqal agurare daban daban saidai kuma dafin zai illatatane bazai kashetaba matuqar ba masoyintane ya soketa da ita kuma ya zamto shine zaiyi mata suka ta qarshe da wannan wuqar to tabbas wannan ne kawai zai kasheta…idan Wanda takeso fiyeda komai bai soketaba to tabbas kusani sukarku zata illatane amma bazat mutuba Wanda kunsan rashin mutuwarta na nufin rayuwarmu mu duka dan haka wannan matakin na qarshe yafi kowanne hadari. 5

Cikin zalama da qosawa kojo yace,

Jamal bazai taba qi hakan ba koya gardama zamuyi amfani da qarfinmu mu sakasa.

To bayan wannan kuma idan ta mutu to masautarta zata bace daga duniya babu Wanda zai sake ganinta saidai idan Wanda take tsananin so ya sadu da ita to tabbas idan ta mutu masarautarta tariga ta bayyana har abada tazama ta bil adama ta tashi daga duniyarsu.

‘Daure fuska amari yayi zaiyi magana da sauri kojo ya dakatar dashi yana cewa,

Munriga munkawo yanzu babu abinda zai gagara yamaida mu baya ga wannan tafiyar Jamal dole zai sadu da sarauniya mineelik.

Wasu sabbin madaurin damtse na wani tsarin boka yabasu kowannensu ya daura tareda ‘daukar wuqa ‘daya na Jamal kuwa cikin fata amari ya nade masa ya soka qugunsa suka miqe.

Yonas dake qoqarin soka tasa cikin takalmin fatar damisarsa yaji hannunsa na wani irin qaiqayi yayi saurin dubawa zai sosa saiyaga rubutu na bayyan a hannun nasa yayi saurin kallon mahaifinsa yaga idanuwansa rufe alamar saqone yake ruboto masa dan sanar dashi wani abin.

Da sauri ya maida kallonsa ga tafin hannunsa yafara karanta saqon.

“” idan buri ya kammala kawai da datti ake ashare komai da komai”””” 1

Jinjina kai yayi cikin rashin tausayi yakalli bayansu kojo dasuka gabansa dan yafahimci saqon meyake nufi yana nufin idan ankammala su kashesu nan take. 1

Suna fitowa qofar gidan boka aqoob sukaga wani irin gini mai matuqar tsawo da kyawu tareda girman dabasu taba ganiba mutanen gari sai fitowa kallo akeyi ana nufar hanyar da ake hango masarautar
Atake cikin gaggawa suka hau raqumansu suka nufi hanya sai tun daga nesa suke hango babu daji sai masarautar kawai da girmanta yasa ta zamto kamar tana cikin ganin ne.

Suna isa bakin qatuwar qofa mai girman gaske suka taru su biyar suka tura qofar tabude suka shige cikin wani irin mamaki mai rikita tunani da nustuwa sbd girma da kyawun masarautar babu kowa koina tsit saidai komai fes tamkar yaune aka ginata.

Harabar gurin suketa rarraba idanu suna kallo cikeda far in ciki mara misaltuwa sbd burinsu yacika saura qiris su mallaki sauran duniyar

Wasu furanni masu qamshi yonas ya tsinka ya shinshina ya lumshe ido cikin farin ciki ya daka wani tsalle tareda sakin ihun farin ciki.

Kojo kuwa mahaukaciyar qofar daya tabbatar ta fadar da karagar ke cikine ya nufa ya saka hannu biyu yatura qofar ta wangale atake dukkaninsu sukai mutuwar tsaye ganin karagar dake wani irin daukar ido duk da kasancewarta kalar baqa mai adon zan zinari.
Girman fadar suka kallon cikin wani irin farin ciki madaukaki da sauri suka nufi kujerar kusan atare kowanne na burin kaiwa ya hau Jamal yasha gabansu cikin wani irin yanayi na damuwa da bacin rai.
Tsayawa sukayi dukkaninsu kallonsa saidai ganin kamar hawaye cikin idanuwansa yasasu tamvayarsa cikin gaggawa.

Yaja baya tareda zubewa kan gwiwoyinsa murya na rawa yace,

Ina roqonku da karku cutatar da ita domin kwadayin arzikinta kubari zankarbar mana ta hanya mafi lalama da yardar ta. +

Wucesa amari yayi ya nufi karagar yana banzatarda zancensa sbd har abada babu Wanda zai shiga tsakaninsa da wannan taskar arzikin.

Dukkaninsu babu Wanda yabi takansa sbd babu alamar gudu ko ja da baya a wannan alamarin nasu.

Cikin wani irin gunjin kuka ya durqusa a gurin suka waiwayo suka kallesa ajani ne yadawo gabansa ya tsaya cikin kulawa yace,

Meke faruwa munyi alqawarin duba damuwarka idan kafada.

Kallonsu yayi cikin wani irin gunjin kuka mai ciwo ya girgiza kai yana cewa,

Ayau na hada shimfida da sarauniyar aljanu Wanda na tabbarda hakan wata sabuwar qaddara rayuwa ke nufi dani saidai kuma hakan y juyar da ra’ayina bazan iya cutatar da itaba sbd a duniyarsu hakan wani babban alamari mai tsananin girma yake nufi dan haka ta tafi wani gurin bauta bazata dawoba sai bayan kwana uku sbd abinda yashiga tsakanina da ita zatajene domin dawowa duniyata gaba daya dan haka nake roqonku karkuyi abinda zai barmu da masifar da bazata tsaya akanmuba kawai. 2

Cikin tsananin farin ciki da jin dadi suke kallonsa atake dukkaninsu suka sheqe da dariya mai qarfi cikeda farin cikin ganin komai ya tabbata qiris yarage. 1

Kallonsu yake daya bayan daya yana mamakin dariyarsu cikeda fargaba.

Sake kutsawa cikin masarautar mai girma sosai sukayi kowanne na taba abinda ya burgesa duk wata zalamarsu da kwadayinsu ya fito nan suka ringa shiga dakuna da gurin shaqawata da sassa daban daban babu tsoron komai aransu.

Shikuwa ke6e kansa yayi daga garesu yana zullumi da tunanin manufarsu daya kasa ganowa yadai San dole sunada qudirin cutatar da ita.

Ranar data cika kwana uku a makeken lafiyyan dakinta dake turakarta ta bayyana lokacin yana zaune tsakiyar daki cikin tsananin tashin hankali da damuwa.

Kallonsa take cikin tsananin farin ciki da wani irin yanayin jin dadi takira sunansa cikin qauna da soyayyarsa.Da sauri ya miqe tareda juyowa bata tsaya bata lokaciba ta rungumesa da qarfi tana sake ajiyar zuciya cikin farin cikin kasancewa dashi har mutuwarsu.

Rintse ido yayi sbd tuno abinda yafaru ayau tsakaninsa da ‘yan uwansa.

Wuqar da boka yabasu suka fitar masa da yasa suka basa tareda yimasa bayani yayi saurin wurgi da wuqar yace,

Aikuwa idan har nine Wanda kawai zai iya kasheta har abada bazata mutuba.

Cikin takaici kojo ya kallesa yace,

Baka isa ka rusa mana shirinda muka share shekara da watanni muna sadaukar da rayuwarmuba.

Kabarsa yagama bulayin shirmen son wadda ba jinsinsa idan yagama shirmrn mafarkin zaidawo hayyacinsane lokacinda tagano manufarsa ta aikasa gurinsu dede”””cewar amari dayafi hasala da zancen

Yonas ya sake dauko masa wuqarsa ya saka masa cikin hannunsa yace,

Idan bakayiba mu zamuyita sukarta harsai ta mutu koda zamu dauki shekara dari ne saidai kasani tana warkewa karasa yan uwanka dasune rayuwarka har abada sbd kashemu duka zatayi kuma harda kai aciki.

Ajani dayafi kowa qaguwa dasu mallaki masarautar ya matso gabansa ya tsaya cikin tabbarwa yace,

Zabi yarage naka kazaba ‘yan uwanka ko soyayyarda bazata doreba har abada sbd ba jinsi dayaba dan haka kashirya tana dawowa zamu qarashe aikinmu idan baka yi yanda akaceba kana kallo zata kashemu.
Tafiya sukayi sukabarsa tsaye da wuqar ahannu yana kallo cikeda wasi wasi saidai bazai iya bari yarasa yan uwansaba sbd sune rayuwarsa sunayiwa juna wani irin so da qauna mai qarfi.

Zamewa yayi daga jikinta jin kamar wani abu a gabanta kallo daya yayi mata yayi baya da qarfi cikin wani masifaffen tashin hankali sbd ganin qaramin ciki ajikinta.

Matsosa tayi cikin farin ciki tana Murmushi zatai masa magana yasake ja baya tareda ficewa da sauri.

Dayake safiya ce sosai sauran babu Wanda yatashi suna sassansu kowanne yazabi sashensa sunacan suna hutawa tuni suka samo masu hidima.

A cikin fadar ya shiga ya tsaya jikinsa na wani irin rawa zufa na karyo masa takoina

Ta bayyana a gabansa tareda riqo hannunsa ta ‘dora akan cikin ahankali tace,

Cikine dani kuma……..cak ta tsaya da maganarta jin sukar data sauka ajikinta daga bayanta
Cikin wani irin yanayin azaba ta juyo dan ganin waye taji wata sukar a gefen cikin duka biyun.

Jajayen idanuwanta ta ‘dago cikin radadi da azaba takallesu amari ne da yonas,radadi da azaba takallesu amari ne da yonas, +

Jinine ya fara fitowa daga hancinta ta ‘damqe hannun Jamal da idanuwansa suke zubarda wata irin qwalla da kuka mara sauti,
kojo da ajani tareda haji suka tsaya gabanta tareda ‘daga wuqaqensu suka soketa da qarfi aciki lokaci ‘daya.

Tasake damqe hannun Jamal tareda fitarda wani nishi mai qarfi da wata irin azaba atake Jini ya balle mata mai matuqar yawanda basu taba ganin irinsaba hakama bakinta yafara fitarda jini ta yanke jiki ta zube bakin karagar mineelik tareda kallon Jamal daya fiddo wuqarsa yana hawaye ta lumshe ido cikin tsananin baqin ciki mai tsananin gaske sbd ta tabbatarda cin amanarta da yaudararta sukayi ahankali tabude baki daqyar ta furta,

Duk iya alqawari da soyayyar danake maka meyasa kazabi cuatatar dani.,
Karka kasheni kabarni na rayu kodan cikinka dake jikina nikuma zan maka alqawarin sabuwar rayuwa,
Haryanzu zuciyata nasonka ko ka kasheni bazan daina sonkaba……. 2

A hankali ya ‘daga wuqar ya nufi qirjinta yana kuka yashigarda wuqar qirjinta da qarfi. 2

Atake tasaki wani irin azababen nishi mai qarfi daya amsa masarautar gabaki daya ta kallesa idanuwanta na fitarda wasu irin hawayen ahankali ta bude baki tace,

Meyasa????

Cikin izza ajani yace,

Sbd karagar mineelik.

Kallon Jamal tayi ya juya mata baya yana sake sakin sabon kuka ta kalli karagar tasaka hannu ta debi jininta dake zuba ta zubawa karagar ta lumshe ido sbd wata irin azaba dake ratsata cikin,

Hawayen azaba tace,

Ayau ni sarauniya mineelik ‘yarda,soyayya dakuma amincewa yasa bawa mafi soyuwa a rayuwata ya kasheni ya zubar da jinin ‘dana ko ‘yata dan haka haqqin jinana bazai taba barin bibiyarku ba har qarnin qarshe harsai ranarda jini ya maida jini maimakon jini dan haka nayiwa mineelik baki zata zame muku masifa mara magani da ganewa,,,,daga yanxu jini ya ringa zuba kenan amaimakon jinin ‘dana.

Kallon bayan Jamal tayi lokacinda taji ko maganar takasa sbd tsananin azaba ahankali ta furta nabar maka dukiyata sbd sarauniya bata alqawari ta ‘daga saidai bazakaji dadinta ba…… 1

Cikin rashin imani yonas ya daga wuqar ya soke mata maqogoro atake ta saki numfashi da ajiyar zuciya ahankali jikinta ya saki ta bace 6at.

Zubewa agurin Jamal yayi yana wani irin kuka mai sauti.

Cikin tsananin farin ciki da murna amari ya nufi karagar zai hau boka aqoob ya bayyana gabansa cikin wani irin murmushin mugunta yace,

Nine mai hawa wannan karagar duk Wanda ya……..bai qarasaba sukaga kansa ya fille yafadi qasa.
Kojo sukaga yani a bayansa kenan shine ya fille masa kai
Cikin murna ajani ya nufi kojo zaiyi magana yonas ya sha gabansa cikin tsananin baqin ciki da zafin zuciyar ubansu da aka kashe yana ‘daga wuqarsa zai cirewa ajani kai aka soke masa zuciya daga bayansa saida takobin ta fito ta qirjinsa.

Wanda amari ne yayi wannan aikin.
Haji na ganin haka ya juya da gudu ya fice yace,

Kusani wannan gabace da masifar dazata zo har zuriar zuriar bayanmu. 3

Cikin zaquwa amari ya juya zai hau karaga Jamal ya buge qafafunsa tareda miqewa ya isa karagar kai tsaye ya hau ya zauna tareda kallonsu da jajayen ido yace,

Nine magajin mineelik dan haka nine zanyi sarautar duk Wanda hakan baimasaba yana buqatar hada kwanji dani.

Kallon juna sukayi ga mamakinsa saiyaga sun nuna amincewarsu.

A ranar Jamal ya karbi sarautar mineelik kuma aranar aka dauki masu hidima ‘Dari da hamsin atake masarauta ta cike da mutan gari ko sati ba’a rufa dukkaninsu sukayi auren mataye uku uku lokaci ‘daya, 1

Mineelik cikin qanqanin lokaci tazama masarauta mafi girma da iko a wannan qarnin musamman data zama babban gari mafi girma
Kafin mulkin Jamal yaqare saida mineelik takoma itace a tsakiyar babban birnin Ethiopia sbd cika da garuwan qasar sukayi koina ya cike tazama babbar qasar cin kasuwar jiragen ruwan dake wajen gari.

Mulkin Jamal wani irin mulkine na daukar rayuka ba abakin komaiba,
Suna arziki da yawa da girma babu kamar mineelik a wannan qarnin sbd garin da masarautar take ko zakayi wata daya kana yawo bazaka zagayesaba.

Duk wani burinsu Jamal dasu kojo yacika saidai rashin haihuwar ‘yaya maza daya addabesu daga qarshe har sultan jamal ya rasu bai samu ‘da namijiba sai mata
Bayan saukarsa sultan kojo ya hau shima duk tsawon shekarunsa harya mutu bai haifi namiji ba dukkaninsu sunyi mulki ajani kawai yasamu namiji ‘daya acikin ‘yayansa Wanda bayan rasuwarsa shima dansa sultan amed yahau bayan sultan amed sai sultan nurin,dagashi sai sultan abaass da haka mulkin yayita zuwa qarni qarni so ‘daya akayi assultana Wanda mulkinta karagar tafi ta6ata kasanewarta mace,
Alokacin mulkin assultana ankashe rayukane tamkar dabbobi sbd jini daya yawaita a mulkinta sbd iya zubar jini iya qarawa karagar qarfi qarshe abin taba kwaqwalwarta yayi ta samu tabin hankali ahaka ta rasu.

Da haka ‘daruruwan shekaru suka shide musuluncin gske yashigo cikin qasar suka karbesa sosai inda a yanxu suna cikin qasashen dasukafi yawan musulmai duk da wasu haryanxu suna aladar bin bokaye.

A yanxu muna wani lokacine na waye da ilimin zamani tareda qarni mai dadi sbd rayuwar ilimin boko dana addini daya shiga koina ya wadata.

Sultan abdulshams sarkine mai tsananin son kansa fiyeda duk wani abu a duniya har yayansa har matansa shidai arayuwa kansa yasani shiyasa yadau alqawarin karya alkadarin mineelik domin yaci gaba da mulkinta shikadai sbd shikansa yaxubarda jinin alumma fiyeda qima dan haka yanason mulkin bazai barshiba shiyasa yayi bibiyar yanda zaiyi yagano ma’anar kalmar,

“”””jini ne zai wanke jini domin jini”””” a cikin littafin tarihin masarautar mineelik.

Ma’ana soyayyace tamkar wadda takewa jamal mai hadeda jinin cikinta zata karya wannan masifar shiyasa azamansa da bawansa bulama ya fahimci wata irin qauna da soyayyarsa da matarsa yayi amfani da qarfin ikonsa yasa jakadiya ta ware musu wata ‘daya suna kebantuwa da juna ranarda Jakadiya tagano asma’u ta samu wani cikin tasanarda sultan nan yafadawa sultana zaarah nufinsa bawai danta hanaba saidanta kawo masa asma’u gaban karagar da safe daidai irin lokacinda aka kashe sarauniya mineelik.

Badan sultana tasoba saidan tsananin iko da barazanar sultan agareta ranar wata laraba da safe tashirya tace Jakadiya tasa asma’u cikin ‘yan rakata gurin sultan kai gaisuwa.

Koda suka isa tace asma’u tabita suna shiga suka rararda bulama tsaye yana jiran fitowar sultan nan sultana tashiga gurinsa tabarsu tsaye suka qurawa juna ido cikin qauna da soyayyar junansu ya kalleta cikin nutsuwa yace,

Idan kika haihu ko bananan kisawa yaron suna bilal idan mace ce kisaka mata asma’u.

Murmushi tayi zatai magana sultan da sultana suka fito sultan yakallesu kafin yayi magana Jakadiya tashigo daukeda qaton tray daukeda kofuna guda biyar takai gaban sultana da sultan suka dauka ta juyo ta miqawa bulama ‘daya asma’u ‘daya babu musu suka karba sultan yace,

Wannan taya murnace ga bawana bulama na ‘yantasa daga yau. +

Cikin tsananin farin ciki suka zube qasa suna godia sbd sunsan nesa tazo kusa sunkusa komawa qasarsu kenan.

Cikin tausayi Jakadiya tace,

Kusha kyautar sultan Ku godewa Allah.

Da sauri suka kwankwade lemon suna sake godiya suka miqe suka fice sultana ta sauke numfashin damuwa da tausayinsu tareda baqin ciki da dana sani Wanda take kallon kanta amatsayin wadda takashesu shiyasa take tsananin qaunar yarsu.

Acikin daren bulama ya rasu da ciwon ciki asma’u ma ta rasu da cikinta dabata haifeba Wanda babu Wanda yasan dashi saisu dasukai aikin saidai abinda basu saniba shine kozaku sadaukar da rayukan masoya ‘Dari to masifar mineelik bazata karyeba sai masoyan dasuka kasance sunada jini da masarautar. 9

**
A matuqar gigice ta farka a firgice suka miqe tsaye amatuqar firgice suna watsa ruwan magani sbd basusan a yaya ta farko ba. 1

Maheer dake zaune hannunsa cikin na suhailat ya zare ya miqe ya nufi gadon yana kallon fuskarta dake bawa duniyarsa nutsuwa.Kallonta yayi da idanuwansa dasukai laushi sbd damuwa
Ahankali ya qarasa bakin gadon
Negasi ya bude baki zai dakatarda dashi ya daga masa hannu ahankali cikin mulki da bada umarni ya bude baki yace, +

Ina buqatar ganawa da ita.

Cikin girmamawa suka fara ficewa ammy dake kallon rumanah kamar idanuwanta zasu fado zuciyarta na bugawa da sauri gabaki daya bata cikin nutsuwa so take taji rumanah tayi magana tasan halinda take ciki saidai rumanar idanuwanta a rintse suke
Kowa ya fice sai ammy da suhailat dake bayanta tsaye rungume da abeel zuciyarta na rauni.

Ahankali ya zauna kusada ita bakin gadon ya riqo hannunta ya damqe cikin nasa tareda qurawa fuskarta ido
Ahankali ta bude idanuwanta dasukai jajir ta kallesa zuciyarta na harbawa da sauri,

Zuciyarta qoqarin kallonsa takeyi a matsayin a iyayensa sukayiwa nata iyayen kisar ganganci da rashin imanin abinda ke cikin mahaifiyarta saidai kuma Sam zuciyarta takasa jin sauyi ko tsanarsa dan kuwa itama tana masa wani irin so ne Wanda bazata iya ganin laifinsa akan abinda maifinsa ya aikataba saida kuma batajin zatabar jinin duk Wanda ya zuba ya zube a banza sultan abdulshams zai dandani kalar nata rashin imanin

Juyar da idanuwanta tayi kan ammy dake tsaye tana kallonta da idanuwanta dake bayyanarda tsananin damuwa da tashin hankalinda take ciki.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali idanuwanta na cikowa da hawaye sbd itace ta rasa iyayenta,itace baiwa a dah,itace uwar da aka kashewa ‘da tun kafin tafita daga radadin naqudarsa data wuni tana saidai ba itace abin tausayiba sune abin tausayin sbd yanda take jin zuciyarta dakuma sanin abinda ya samarda karagar mineelik batada tabbaci akanta da abinda zata iya yi sbd wani irin fushi,xafin zuciya, qunci,rashin tausayi da bushewa takeji a zuciyarta dan ita kanta ayanxu tasan tanada hadari sbd yanda takejin tamkar mineelik na cikin jikinta saidai soyayyar wainda take so da qauna tananan daram cikin ranta musamman shi daya zamo tamkar shine fitar numfashinta.

Ahankali ta miqawa ammy hannu.
Cikin tsananin farin ciki da ‘doki ammyn ta qaraso ta zauna gefenta ‘daya tareda kama hannunta cikin tsananin sanyin jiki tace,

Rumanah ki…….

Girgiza mata kai tayi ahankali ta bude baki tace,

Ke uwace agareni kuma zaki cigaba da zama uwata ko wane irin mataki na taka,kome nazama bazan ta6a iya cutatardake ba laifin da aka sakaki kikayi koda badason rankibane wannan tsakaninki ne da ubangijinki bazanso wannan maganar tashiga tsakaninmuba.

Kasa riqe hawayenta ammy tayi sbd kunyar rumanah ta miqe da sauri ta fice hawaye nabin fuskarta.

Qoqarin maida kukanta takeyi saidai takasa sbd radadin datake ji mai zafi na mutuwar da iyayenta sukayi
Da sauri ya rungumeta yanajin zafin ganin yanayinta tasaki wani irin kuka mai ciwo tana qanqamesa.

Suhailat dake tsaye tanason yimata sannu da jiki ta juya ta nufi qofa jikinta amatuqar sanyaye zuciyarta na qoqarin jin zafi saidai tayi saurin kawar da hakan sbd ganin rumanar batada lafiya tana buqatar kulawarsa saidai duk yanda taso dannewa saida idanuwanta suka ciko da hawaye ta qanqame abeel ajikinta tana qara sauri dan isa gefenta.Baice mata komaiba saida tayi kukan iya yanda zuciyarta keso kafin tayi shiru tana sakin ajiyar zuciya ahankali. +

Dago fuskarta yayi yana kallonta ahankali ya shafota cikin sanyin murya yace,

I love you ummu-rumanah bulama maheer abdulshams.

Kallon cikin idanuwansa tayi akaro na farko dataji Kalmar na bata tsoro saidai tasan maheer ‘dinta har abada bazai ta6a iya cutatar da itaba.
Lumshe ido tayi ahankali ta bude tace,

Ummu-rumanah nasonka tun kafin kace kanasonta saidai inason kayi min alqawarin zaka soni a duk halinda nashiga,
Bazaka gujeniba,
Kaine farin cikina soyayyarka itace qwarin gwiwata karka…….

Hannunsa ya dora a bakinta yana mata wani irin kallo yace,

Shihhhhhh get some rest now sbd gangar jiki da ruhi tare suke rayuwa tare suke barin duniya. 2

Kallonsa tasakeyi tasaki wani irin numfashi mai sanyi tareda sake komawa jikinsa ta kwanta.

Da kansa yakaita toilet tayi wanka ta fito tana duba closet dinta taga sabbin royal gowns ‘dinda aka kawo mata ba adadi kowacce da kalar sarqoqinta nakai dana qafafu da hannuwa tareda wuya.

Doguwar English gown tasaka har qasa mara hannu takallesa lokacinda yasake shigowa dakin ya riqo hannunta suka fito palonta na farko har zuwa dining inda aka jera abinci fiyeda kala biyar da mamaki take kallon dining din sbd ganin duk girmansa ancikasa da kalolin abinci da fruits ga masu tsaronta mata da aka kawo tun daga palonta na farkon shigowa har wannan din sai wasu irin samudawan guards da aka zuba tun daga qofar part din dazagayensa har zuwa hanyar dazata rinqa kaita zuwa fada.

Kallonsa tayi yasakar mata wani murmushi ahankali tareda jawo mata kujera ta zauna tana kallonsa fuskarta daukeda qaramin murmushin qarfin hali sbd har lokacin zuciyarta cike takeda radadi sosai takejin kamar ana babbaka jinintane ana qunarsa mai laifi kadan take nema ta dau mataki akansa saidai kasancewarsa tareda ita yasa take iya control din yanda takeji saidai kamar abin nason yafara mata yawa.

Cikin nutsuwa sukaci abincin duk da kadan taci tasha maganinda aka aje kan dining din daga negasi.

Harsuka gama cin abincin idonsa nakanta sbd sosai ya lurada sauyi atareda ita saidai zuciyarsa naqara jaddadawa kanta arayuwa babu abinda zai rabata sonta.

Kasancewar bata fara sallah ba yasa yakaita daki yasake kwantar da ita ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa yace,

Inason sanin abinda yafaru tsakaninki da ammy.

Kallonsa tayi kafin ta dauke kai tana sake sawa zuciyarta qin ganin laifin ammyn kai tsaye tace,

Sultan ya kashe iyayena da taimakon ammy da jakadiya.

Cikin wani irin mugun yanayi na mamaki yake kallonta
Ta zame ta sauka gadon ta nufi bakin window ta tsaya.Gabanta ya zagayo ya tsaya yana kallon cikin idonta ta rintse idon tana dauke kai. +

Ahankali ya bude baki zaiyi magana ta bude idanuwanta dasukai ja ta katsesa cikin sanyin murya da cewa,

Bana maka wani kallo na daban a zuciyata bayan Wanda nake maka na mahadinta ko Allah baya kama wani da laifin wani….

Shiru tayi tana tauna Kalmar dazata fada cikin qarfin hali tace,

Na yafewa ammy sbd Allah da soyayyarta gareni da kasancewarta mahaifiya kuma kaka ga mutane biyu danafiso ayanxu fiyeda rayuwata dakomai,kai YARIMA MAHEER ABDULSHAMS da ABEEL HASSAN……

Cikin sanyin murya dake nuna baqin cikin dayake ciki ya furta,

Sultan f….

Bai qarasaba tace,

Kayi hakuri.

Ta juya masa baya cikin wani irin zafi datakeji a zuciyarta ta rintse ido tasake cewa,

Kayi hakuri.

Kasa motsi yayi sai idanuwansa dasukai jajir yana jujuya kalmarta ta yayi hakuri….zata dauki mataki akan mahaifinsa kenan…. No not possible…tokuma ko Ba itace akan mulkiba tana buqatar justice…..

Ficewa yayi sbd jin kamar numfashi na masa wuyar ja ko gani sosai bayayi sbd tashin hankalin dayake ciki.

Suhailat dake tsaye gaban windonta taga fitowarsa daga sashen na rumanah ta ‘dauke kai tareda barin jikin windon sbd gujewa ganin damuwa. 1

Yana fita ta zauna bakin gado tareda dafe kanta ta rintse idanuwanta kanta na mata wani irin ciwo.

Koda dare yayi duk yanda taso bacci kasawa tayi sbd kewar iyayenta da ‘yayanta.

Koda gari ya waye qarfe goma wata zungureriyar takardar saqo daga alqalamin sauraniyar mineelik ummu-rumanah bulama ta isa hannun sarkin fada haroun inda saqon yake cewa ayau angama karbar duk wani bayani akan asalin sarauniya ummu-rumanah daga baiwa mamani dan haka ayau za’a yanke mata hukunci.

Atake aka buga sanarwa koina ya dauka qarfe goma sha daya jama’a suka taru ana jiran isowar assultana.

Cikin wata irin royal gown tafito red mai adon golden gashinta koina rufe da adon sarqar farin zinari wasu irin samudawan guards ne maza da mata taredasu Jakadiya a bayanta ta fito suka nufi fada.

Cikin nutsuwa na wani irin miskilanci ya yasha gabanta yana kallonta guards din bayanta suka nufosa ta ‘daga musu hannu tareda juyowa cikin nutsuwa ta kalli Jakadiya tace,

Duk Wanda yasake gangancin tare mijina aduk lokacinda yakeda buqatar magana dani yana ganganci da rayuwarsane a sanarda kowa.

Cikin tsananin ladabi dukkaninsu suka sauke kai suna tuba.

Ta juyo ta kallesa cikin nutsuwa tace,

Ina kwana?

Kallonta yayi kafin ya watsawa su jakadiya wani mugun kallo atake suka ja baya sukai ‘dan nesa kadan dasu.

Ya kalleta cikin ido yace,

Bazaki yankewa mamani hukuncin kisaba that’s an order amatsayin na mijinki
Ba mamaniba har kowama bazaki yankewa hukuncin kisaba nin…… 4

Sultan ne bakason a kashe ba mamani ba”””ta fada tana kallonsa cikeda fargabar abinda zaice.Kallonta yayi yana sake kafeta da manyan idanuwansa ransa na qoqarin 6aci da zancenta zuciyarsa na qoqarin hana faruwar hakan ya bude baki zaiyi magana ya fasa ya kama hannunta da qarfi ya jata part din ammy dake kusa
Tsakiyar palon ya saketa tareda kallonta cikin sautin dake nuna bacin ransa yace, +

Me kika fada yanxu?

‘Dauke kai tayi kai tsaye tace,

Kana qoqarin kare sultan ne akan laifukanda yariga ya aikatasu ne cikin son rai da ganganci saidai kuma nariga nayi alqawarin duk Wanda ya cutatar da wani sai anbi masa haqqinsa sbd wannan shine adalcin assultana,wannan shine banbancin mulkin son rai da adalci….duk Wanda ya kashe a kashesa wannan shine hukuncin a musulunce….. 1

Riqota yayi da qarfi ransa na qarasa 6aci yace,

Kina tunanin na hanaki hakane sbd sultan yana nahaifina?
Kisa dai matuqar ina raye kuma da aurena akanki bazan ta6a bari kiyiba ko adama kin kashetane a lokacinda bana kusa da bazan taba bari ki kashetaba and da…..

Qwacewa tayi tana kallonsa tace,

Nice na kashe adama kana qoqarin cemin mai kisa ne????
Bayan kasan mutanen nan sun cancanci kisa tako wane sashe na sharia,
Anyiwa iyayena kisan wulaqanci da son rai,
Anyiwa ‘dana kisar son rai da ganin dama duk basune masu laifiba nice danake shirin qaddamar da adalci wa kaina amma y…….

Idan kina maganar abeel Hussain ne ni mahaifinsa nabarwa Allah duk Wanda keda saka hannu nabarsa shida ubangijinsa maganar iyayenki kuma amatsayina na mijinki nake baki umarnin kibarwa Allah bazaki qara yankewa kowa kisar wulaqanciba ki tabbatarda idan kika sake hakan ni maheer abdulshams mungama zama tare abakin aurenki gabak…… 2

Cikin tashin hankali suhailat dake palon basusan da itaba tayi saurin katsesa da cewa,

Abu abeel ka…..

Shut up and stay out of this suhailat”””””yafada ransa a matuqar 6ace. 1

Rumanah datai mutuwar tsaye tana kallonsa idanuwanta sun kada jajir suna zubo hawaye zuciyarta takai qololuwa gurin tashin hankali da baqin ciki ta bude baki cikin baqin ciki tace,

Basaika datse alaqar dake tsakaninmuba nasan bana ranka ko gabanka kayi qoqarin barina da aurenka har zuwa yanzu da baka sallameni bayan haihuwataba sbd itace amfanina daman shiyasa kace haka sbd sanin sirrin zuciyata saidai……..

Fixgoto yayi da qarfi zaiyi magana ta fixge jikinta tana sakin wani irin kuka mai qarfi da ciwo sbd zancensa ya girgiza duniyarta gabaki ‘daya ya kasheta jitake zuciyarta kamar zata babbake ta kama da wuta sbd masifar dake ci mata zuciya.Cikin tsananin damuwa suhailat ta dauki abeel ta nufi palon qurya tafadawa ammy dake zaune cikin tunani abinda yake faruwa. +

Da sauri ta taso tana shigowa palon ya juya zai fice ammy tayi saurin riqo rumanah dake kuka kamar ranta zai fita takira sunansa ya tsaya cak batareda ya juyowa sbd qaran kukan dake sake hargitsa nutsuwarsa da tafasa zuciyarsa.

Rungume rumanah tayi tana qoqarin rarrashinta saidai kukane takeyi sosai Wanda ke nuna tsananin ciwo da baqin cikin da zuciyarta ke ciki.

Kasa tsayawa yayi ya rintse ido da qarfi ya fice yanajin baqin cikin kukanta da maganganunta.

Suhailat dake tsaye ji tayi jikinta ya qara wani irin sanyi da kukan da rumanah keyi ahankali ta fice daga sashen sbd ganin suna buqatar tattaunawa tsakanin ‘ya da uwa dan jin tayi tazama baquwa acikinsu su duka din har maheer ‘din. 1

Shiru ammy tayi da ita rungume a jikinta batareda tace mata komaiba sbd halinda take ciki tana buqatar tayi kukan ko dan ta rage nauyin dake zuciyarta,
Maganar gskia ko ita bazataso rumanah ta zubar da jiniba sbd sauyi suke fatar samu daga gareta…

Itace sarauniya ta farko a tarihin qasar gabaki ‘daya data hau sarauta batareda jinin sarauta a jininta ba bama ‘yar qasarba baquwar haure daga wata qasar,

Qaddara ta koro iyayenta daga gida suka fada wani gari inda daganan Allah yasake jefasu hannun masu kamun bayi aka kamosu zuwa nan qasar aka haifeta amatsayin baiwa
Wata qaddarar tasa ta auri yariman masarautar,

duk wannan qaddarar data koro iyayenta ta zamtowarta cikin lissafin masu mulkin qasar ne wannan kawai ya tabbatarda akwai abinda Allah ke nufi da hakan Wanda suke fatar sauyine na alkhairi mezaisa suso ganinta tana aikata abinda sauran sarakunan suka aikata.

Tasan tabbas maheer yayi hakan ne dan bazai iya bari ya rasataba dan idan ta cigaba da zubarda jinin karagar mineelik zata shiga jikintane sosai ta yanda zasu rasata har abada.

Dakinta tashigarda ita ta kwantarda ita kan gadonta ta rufeta tareda shafa kanta ta fice taje palo ta zauna tareda kallon Jakadiya data shigo duba assultana jin shiru dan tuni aka zagaye sashen ammyn da tsaro kasancewar tana cikin.

Dafe goshi ammy tayi cikin tsananin damuwa da rashin sanin mafita tace,Kije kisanarda sarkin fada haroun assultana ta ‘daga hukuncin zuwa wani lokaci batajin dadi yanxu. +

Cikin girmamawa da jimami tace,

To””ta fice taje ta sanar atake akai sanarwar aka watse tareda tsananta tsaro sashen ammy.

Har dare tana sashen ammy kwance ko motsi bata yi
tayi wani irin sanyi idanuwanta sunyi jajir.

Shigowa ammy tayi cikin nutsuwa ta zauna bakin gadon tareda sauke numfashi ahankali cikin kulawa da sanyin murya takira sunanta.

Bata motsaba ta bude idanuwanta dasuka kumbura batareda ta amsaba.

Duk wani ‘da na halak bazai iya kallon makasan mahaifansa ya qyalesuba matuqar yanada halin daukar mataki ko fansa akansuba..
Saidai kuma dangana da bariga Allah ta wata hanyar shine sasanci da kawo qarshe ga kashe kashen.,
Ummu-rumanah har abada haqqin asma’u da bulama bazai bar ko ‘dayanmuba koda kin yafe mana saidai kuma ina sake roqon yafiyarki a maimakon mu duka ‘din,
Wlh rumanah ina kallonki amatsayin ‘yar dana haifa,
Ina qaunarki da sonki har cikin zuciyata fiyeda wasu daga cikin ‘yayan dana haifa shiyasa bazan iya bari naganki cikin wata muguwar rayuwa.

Kisan bashine mafitaba bashine zaisa kiji sanyi a mutuwarsuba saima lalata rayuwarki dazakiyi ta hakan sbd har abada bazaki yafewa kanki abinda kikayiba zaki tsinci kanki cikin baqin ciki da damuwar da muma muke ciki ayanxu, 1

Mijinki yana miki sonda bazai iya bari ki fada wani mummunan haliba bawai yanayi ne dan karki kashe mahaifinsa saidan yana tsoron hakan zai qarasa gusarda imaninki ne.

Amatsayina na uwa ba sultana matar sultan mahaifiyar maheer ba nake baki shawarar karki kashe mahaifin mijinki ki bar iyayensa da haqqin ran iyayenki wlh Allah zai kamasu sbd baya taba barin haqqin wani akan wani dan haka kiyiwa magana nazari.

Miqewa tayi jiki asanyaye tabar dakin tana fatar rumanar tayiwa zancenta kyakkyawan fahimta.

Qofar da ammy ta fita ta qurawa ido idanuwanta nasake kadawa sbd zancen ya shigeta saidai fadanta da maheer ya kasa barin zuciyarta ta nutsu da daga bakinsa wainnan kalaman suka fito tabbas zuciyarta bazata tsaya wasi wasin daukarsu ba,,

Meyasa zai fada mata kalaman dasukafi dalma zafi gurin tarwatsa kunnuwanta da zuciyarta?????
Meyasa zaiyi fushi ya iya furta mata kalaman rabuwa da ita bayan alqawarin dayayi mata badan mutuwaba dashi da ita bazasu rabeba????
Wasu irin hawaye masu radadi suka gangaro mata ta rintse ido tana qoqarin danne kukan dake qoqarin zuwar mata.
A cikin daren takoma sashenta tareda guards inda ta bada gargadi mai qarfi akan batason ganin kowa.

Kwana biyu tayi bata fito ko qofar part dinta ba..
Abincin safe rana dare haka ake kwashesa bata fitowa saidai ammy tazo dakanta har bedroom tasata cin abinci dole.

Duk iya yanda take jin kewa da soyayyarsa na cin zuciyarta dannewa tayi sbd har lokacin zuciyarta cike takeda zafi da radadin kalamansa shima kwana biyun bai nemeta ba hakan yaqara quntata yanayinta.

Nuratu data rungumi qaddara da hannu bibbiyu akan mahaifiyarta still itace ke kulada rumanar amintacciyar baiwarta duk da da farko anso hanata ko kusantar inda rumanah take saidai rumanar ta hana sbd tasan suna tsananin buqatar juna sbd sukadai suke ganin junansu amatsayin jininsu tunda mamani sunanta matacciya.

Sultan kuwa a rubuce ta aikawa harooun da takardar a tsananta tsaro a sashensa kowama yanxu ta hana yashiga gurinsa
Hakan kuwa akayi nan take aka cika umarninta tareda bada gargadi ga duk Wanda yaje kar abari yashiga.Kwance take kan doguwar royal chair ‘din shaqatawa dake qaramin palonta dakeda manyan qofofi guda biyar dasuke ta bayan garden din shashaqatawarta, +

A rufe idanuwanta suke saidai Sam ba baccin takeba iskar gurin mai sanyi take kado mata ta shara sharen labulayen winduna da qofofin palon dan ragewa kanta zafi da quncin datake ciki.

Ahankali ta jiyo kukan jariri na shiga kunnenta ta bude idanuwanta a hankali sbd tasan kukan abeel ne tunda kaf masarautar babu jariri bayanshi.

Tashi zaune tayi cikeda kewar ‘danta da tausayinsa na rashin ‘dan uwansa dakuma ‘dumin jikin mahaifiyarsa
Miqewa tayi ta nufi qofar bakin window ta tsaya tana hango cikin bedroom din suhailat da itama ta iska ke daga farin labulenta….

Rungume take dashi a tsaye tana jijjigasa cikin tsananin kulawa da damuwar kukan nasa
Ta ‘dagosa tafa duba fuskarsa cikin qaunarsa tayi kissing kumatunsa tana cewa,

Abeel please kayi hakuri mummy bazata sake baka maganin zazzabi ba kaji pls my little prince forgive mummy……

Hawayen datake ruqewane suka gangaro mata na tsananin soyayyar ‘danta da qaunarsa saidai kuma bazata iya karbarsa daga suhailat na….

Tunda ta shigo rayuwarta ta sanadinta ta rasa komai,

Ta rasa jin dadi,kwanciyar hankali da soyayyar mijinta sbd ita,
Ta rasa babynta sbd jin mijinta ya aureta,
A yanxuma ta rasa jemal ne sbd ita Dan ‘yayanta akaso kashewa duka tsautsayi yasa aka kashe mata jemal kuma gashi ta rasa mahaifarta har abada…
Gashi ta riqe ‘dan kishiyar datai sanadin rabata da komai da zuciya ‘daya tana qaunarsa tamkar itace ta haifesa,,,
Wace irin soyayyace takewa maheer??sbd tasan tana tsananin qaunar abeel ne sbd shi ‘din tsotson maheer ne.

Idan suhailat ce a matsayinta na yanxu zata iya kashe mahaifin maheer?

Duk wainnan abubuwan da suhailat ta rasa ta dangana bata riqe kowa araiba gashi tana rayuwarta gwargwadon iyawarta batareda tasaka damuwar duk Wanda ya cucetaba koya tauyeta…..meyasa ita takasa hakan?
Suhailat tafita son maheer ne??? 2

Girgiza kai tayi tareda durqusawa a gurin tana zubarda sabbin hawaye masu radadi da ciwo gabaki ‘daya ta rasa nutsuwarta da sukuninta rashinsa atareda ita jitake tanason zubarda jinin duk Wanda ya cutatar da ita da iyayenta da ‘yayanta SBD kalamansa dasuke yawo cikin kanta suna qona zuciyarta…
Cikin kuka tace,

Bakasan rashinka taredaniba ha’darine dan zan iya aikata abinda bakason dan Allah kadawo gareni maheer.

Suhailat data shigo palon dan kawo mata abeel tagansa sbd ta hangota lokacinda take kallonsu tayi saurin tsayawa cak jin abinda rumanar tace.

Numfashinta taji yaqara gudu tayi saurin juyawa dan ficewa tun kafin rumanar taganta
Saidai tana juyowa tagansa tsaye bayanta idanuwansa sunyi wani irin zurfi ya qureta da ido.

Tsawon kwanaki kenan itama bata sakashi a idoba 6acin ran rumanah duk yashafesu saidai Sam bata damu sosai da rashin ganinsaba sbd tasan irin radadi da zafi da zuciyarsa ke ciki na fada da abinda kafiso fiyeda komai.

Rabasa tayi zata fice sbd ahankali ya kira sunanta ta tsaya cak
Rumanah kuwa tun shigowarsa taji qamshinsa saidai bata juyoba sbd wani irin bugawa da zuciyarta keyi.

Hannu ya miqa ya dawo da suhailat gabansa cikin murya mai bada umarni yace,

Miqa mata ‘danta.

Arikice takallesa itama rumanah a firgicen ta juyo takallesa.

Fuskarsa a matuqar ‘daure yace,

Kibata ‘danta.

Wasu irin hawayen soyayyar abeel da qaunarsa suka gangarowa suhailat takalli abeel din takalli fuskar maheer din taga babu sakewa ko kadan ta juya tana tsiyayar hawaye qafafunta na rawa ta nufi rumanah datai mutuwar tsaye cikeda mamakinsa. 1

Siririn kuka suhailat tasaki tareda ‘daga hannuwanta ta miqawa rumanah abeel.

Cikin rawar murya rumanah ta bude baki daqyar tace,

Nabar miki shi.

Girgiza mata kai suhailat tayi tana wani irin kuka mai ciwo da qaramin sauti.A firgice tasake cewa,

Wlh na barmiki shi….

Girgiza mata kai suhailat tasakeyi tareda ajiye mata shi kan kujera ta nufi qofa da gudu tana toshe bakinta sbd kukan dayaci qarfinta.

Dawo ki daukesa.

Cak ta tsaya tareda juyowa takallesa da sauri

Ki daukesa nabakishi bar abada ‘dankine.

Da sauri tadawo ta daukesa ta rungume tareda dawowa gaban maheer din ta rungumesa cikin tsananin farin ciki tace,

For a moment I thought na rabu da abeel har abada..nagode.

Kallon rumanah data zuba masa ido yayi cikin kulawa yace,

Suhailat idan babu so biyayya na jawo soyayya fiyeda komai,
Idan akwai so rashin biyayya na rusashi komai qarfinsa..
Har abada suhailat matsayinki daban yake cikin zuciyata bazan ta6a daina ganin girma da qimarkiba. 17

Sanyi jikinta yayi masifar yi sbd gane amfani yayi da ita gurin isarda saqo ga rumanah… 54

Wani irin ciwo da radadi taji yana tasowa a zuciyarta akaro na farko data kasa riqe abinda yake zuciyarta tasaki wani irin kuka mai ciwo tareda ficewa tana dafe qirjinta dayake mata zafi sosai. 3

Gabanta ya qaraso ya tsaya yana kallon cikin idanuwanta dake zubard hawayen abinda yayi yanxu dan ta tabbarda ita yake fadawa magana bada suhailat din yake.Marubucin gskia baya rubuta abu acikin labarinsa batareda yayi bincike ko tambaya ba yayiwa abin cikakken sani kusani marubuci ba jahili bane sbd wata tambayar ko comment din tamkar wanka da jirwayene akewa marubuci dan haka kusani ni bana rubuta abinda banida sani akansa. 16

Juyawa tayi tabasa baya zuciyarta na wani irin bugu sbd zafin maganar daya gama fada mata,
Kobai fadaba tasani yafi ganin girma da qimar suhailat sbd ko babu komai itace uwar ‘yayansa kuma macen data girmama dukkanin abinda zaizo mata dashi saidai tasan itama baza’ace bata masa biyayyaba,,,,

Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na sake jiyo mata zafin abin,
Da kishiyarta yake gaya mata maganar bata masa biyayya…sabon ciwon hakan taji ta rintse ido da qarfi tareda girgiza kai ta juya ta nufi qofa tana qoqarin maida kukanta.

Riqo hannunta yayi daidai lokacinda tazo wucesa ya dawo da ita gabansa yana kallon fuskarta data qi kallonsa saidai yanayinta ya nuna jin zafinsa ne cikin ranta.

Kujera ya nufa ya zaunar da ita ahankali kafin shima ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa da kulawa yace,

Kina tunanin wannan itace mafita???
Kina tunanin a halinda muke ciki yanxune lokacinda yakamata mu ringa samun matsala akan abinda nake buqata nakuma baki umarni?….
Kina tunanin sbd kare mahaifina nakeson dakatar dake daga abinda kike shirin aikatawa???

A musulince duk Wanda ya kashe a kashesa amma idan kashewar zata kawo kashe kashen bayin Allah da basujiba basu ganiba to an yarda abar Wanda yayi kisar sai ayi masa wani hukuncin kwatan kwacin zafin abinda ya aikata.

Kina tunanin sultan mahaifanki kawai ya kashe?
Sultan ya bada umarni ankashe mutanen da sukafi mahaifanki abin tausayi,
Ya maida yara qanana marayu babu adadi,
Ya saka mata zaman takaba babu adadi,
Duk kina tunanin yin kansa ne kokuma ra’ayin kansa ne???
Dana barki da tun a shrkaran jiyar kinzama abinda yafi sultan ha’dari dan kuwa da yanxu jinin mutanen da kika zubar yafara ta6a qwaqwalwarki…

Kinga abinda mu bamu ganiba labari kawai mukeji na asalin abinda ya faru har aka samu karagar kuma kinsan duk wata masifa dake bibiyar masarauta nan har yau ankasa samun Wanda zaiyi amfani da tunani da baairarsa domin kawo sauyi domin kuwa tun farko kisar cin amana ce ta samarda karagar kuma har yanxu kisar ce akeyi kina tunanin hakan shine mafita da sauyi tareda jin qan da talakawan qasar ke buqata bayan sune ake kashewa wainda basujiba basu ganiba.,

Kinason yankewa sultan hukuncin kisa bawai dan fadar musulunci ba saidan daukar fansar kisar iyayenka Wanda hukuncinki kwata kwata baiyiba a musulunce sbd kai tsaye fansa ne kika dauka,,
Kafin sultan anyi kashe kashe da dama wainda ma sukafi nasa dan haka…

Ina sonki bazan iya bari kibi hanyar da sauran sukabiba,
Bazan iya bari rayuwarmu ta lalace ba sbd rayuwata zata lalace ne daga lokacinda taki ta lalace dan haka bazan iya bariba,
mahaifina tun tuni naso na kubutardashi daga hakan amma yayi aiki da qarfinsa na zama mahaifi agareni ya nesantani da kansa dan haka bazan sake aikata wannan kuskuren ba sbd ke din ikona ce.
Na auri suhailat shekaru shida zuwa bakwai yanxu…,
A cikin shekaru bakwai dinnan bantaba fada suhailat ta fadaba sbd soyayyarta gareni mai girma ce irin girmanda yake sakata shanye duk wani tauyewa dazai fito daga gareni.,

Kece rayuwata,kece abinda zuciyata tafiso fiyeda komai saidai gaskiyar maganar shine suhailat itace nutsuwata……itace mace mafi girma da qima a idanuwa na bayan mahaifiyata… 6

Rintse idanuwanta tayi da qarfi zuciyarta na tsananta bugawa jikinta na daukar rawa hawayenta na tsananta.Kallon yanayinta yayi cikin damuwa yace, +

I can’t lie to you amma steps dinda kika fara son dauka sun fara ankarar dani babban kuskuren danake shirin aikatawa na barin suhailat ta fita daga rayuwata and idan kika cigaba da qoqarin binsa to tabbas zaki rasani…… 1

Wani irin kuka ta fashe dashi mai qarfi da shiga zuciya tareda zamewa qasa ta zauna ta cusa kanta cikin qafafunta tana jin sabon nauyi cikin zuciyarta sbd dukkanin rayuwarta ta hargitse ta juya ta zama wani abu na daban,
Tana tunanin zatayi rayuwar aure mai dadai saidai gabaki dayama rayuwar auren data kowama ta lalace tun haihuwarsu masarautar ta hargitse takoma gidan baqin ciki sbd kowa yarasa gane inda aka dosa.

Dafata yayi ahankali tareda furta,

I love you queen ummu-rumanah bulama,
Ina sonki zanci gaba da sonki har numfashina na qarshe.

Miqewa yayi ahankali yabar dakin idanuwansa na qara kadawa zuwa jajir.

Sabon kuka tasaki bayan fitarsa tanajin maraici da baqin cikin wainda sukayi sanadin barowar iyayenta da gida har sukazo nan aka haifeta..wace irin rayuwa tasamu kanta ne aciki..

Tabbas tanason yankewa sultan hukuncin kisa ne badan ya cancanta ba sai dan daukar fansar kisar dayasa akayiwa iyayenta,
kwata kwata zuciyarta takasa yarda tayi masa hukunci akan dukkanin abubuwan dayayiwa bayin Allah kanta kawai da iyayenta take gani Wanda idan tayi masa kisa akan hakan sun zamo daya babu banbanci a tsakaninsu.

Kuka takeyi sosai tanason ko nauyin dake danne da zuciyarta ya sauka amma saima wani sabon qunci dake qara mata nauyi.

Kuka takeyi sosai tareda dafe zuciyarta dake mata tsananin radadi da ciwo,
Kukan datakeyi ayau yafi na ko yaushe sbd duk wani hope datake dashi akan zai sota wata rana ya rusashi dan kuwa ta tabbarda zuciyarsa ba ita takesoba kuma bazata ta6a sontaba.
Taso ta zauna dashi har qarshen rayuwarta sbd qaunarta garesa mai girma da tsafta ce saidai kuma hakan bamai yiyuwa bace sbd tasa zuciyar takai qololuwa gurin son wata
Saisai Bazataga laifin rumanah ba sbd tun kafin aurenta tasan babu soyayyarta a zuciyarsa saidai qauna da girmamawa zuciyarta ta dauki wannan sbd babu wata a zuciyarsa tana fatar tashiga wata rana saidai yanzu dayakeda wadda yakeso rayuwarsu su duka na neman lalacewa sbd soyayyarsa dan haka yau duk wani abinda takeson tabbatarwa ta tabbatar dan kuwa har abada bazai ta6a sonta tunda bai sota sbd ‘yayanta da shekarun dasuka diba ba.

Ahankali ta tsaida kukanta saidai hawayenta dasuka kasa tsayuwa cikin muryar kuka da tsananin karaya tace,

Ka tarwatsa duk wata soyayyarka dake raina maheer. 5

Kallon abeel dake kwance tayi tabbas tana qaunarsa saidai bazata rayu dashiba dan kuwa zama a tsakanin iyayensa ya qare mata har abada.

Hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta share tareda miqewa ahankali ta nufi wardrobe dinta ta bude.

Ahankali ta fidda dukkanin kayanta ta hada na abeel tareda duk wani abinsa dake gurinta.

Acikin daren babu Wanda yayi bacci acikinsu sbd babu Wanda yake cikin nutsuwa kowannensu tunanin step ‘din dazai dauka dan kawo sauyi arayuwarsa mai kyau yakeyi.
Juyawa tayi tabasa baya zuciyarta na wani irin bugu sbd zafin maganar daya gama fada mata,
Kobai fadaba tasani yafi ganin girma da qimar suhailat sbd ko babu komai itace uwar ‘yayansa kuma macen data girmama dukkanin abinda zaizo mata dashi saidai tasan itama baza’ace bata masa biyayyaba,,,, +

Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na sake jiyo mata zafin abin,
Da kishiyarta yake gaya mata maganar bata masa biyayya…sabon ciwon hakan taji ta rintse ido da qarfi tareda girgiza kai ta juya ta nufi qofa tana qoqarin maida kukanta.

Riqo hannunta yayi daidai lokacinda tazo wucesa ya dawo da ita gabansa yana kallon fuskarta data qi kallonsa saidai yanayinta ya nuna jin zafinsa ne cikin ranta.

Kujera ya nufa ya zaunar da ita ahankali kafin shima ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa da kulawa yace,

Kina tunanin wannan itace mafita???
Kina tunanin a halinda muke ciki yanxune lokacinda yakamata mu ringa samun matsala akan abinda nake buqata nakuma baki umarni?….
Kina tunanin sbd kare mahaifina nakeson dakatar dake daga abinda kike shirin aikatawa???

A musulince duk Wanda ya kashe a kashesa amma idan kashewar zata kawo kashe kashen bayin Allah da basujiba basu ganiba to an yarda abar Wanda yayi kisar sai ayi masa wani hukuncin kwatan kwacin zafin abinda ya aikata.

Kina tunanin sultan mahaifanki kawai ya kashe?
Sultan ya bada umarni ankashe mutanen da sukafi mahaifanki abin tausayi,
Ya maida yara qanana marayu babu adadi,
Ya saka mata zaman takaba babu adadi,
Duk kina tunanin yin kansa ne kokuma ra’ayin kansa ne???
Dana barki da tun a shrkaran jiyar kinzama abinda yafi sultan ha’dari dan kuwa da yanxu jinin mutanen da kika zubar yafara ta6a qwaqwalwarki…

Kinga abinda mu bamu ganiba labari kawai mukeji na asalin abinda ya faru har aka samu karagar kuma kinsan duk wata masifa dake bibiyar masarauta nan har yau ankasa samun Wanda zaiyi amfani da tunani da baairarsa domin kawo sauyi domin kuwa tun farko kisar cin amana ce ta samarda karagar kuma har yanxu kisar ce akeyi kina tunanin hakan shine mafita da sauyi tareda jin qan da talakawan qasar ke buqata bayan sune ake kashewa wainda basujiba basu ganiba.,

Kinason yankewa sultan hukuncin kisa bawai dan fadar musulunci ba saidan daukar fansar kisar iyayenka Wanda hukuncinki kwata kwata baiyiba a musulunce sbd kai tsaye fansa ne kika dauka,,
Kafin sultan anyi kashe kashe da dama wainda ma sukafi nasa dan haka…

Ina sonki bazan iya bari kibi hanyar da sauran sukabiba,
Bazan iya bari rayuwarmu ta lalace ba sbd rayuwata zata lalace ne daga lokacinda taki ta lalace dan haka bazan iya bariba,
mahaifina tun tuni naso na kubutardashi daga hakan amma yayi aiki da qarfinsa na zama mahaifi agareni ya nesantani da kansa dan haka bazan sake aikata wannan kuskuren ba sbd ke din ikona ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page