HASKE CHAPTER 22

 • HASKE

 • CHAPTER 22


 • Haka Haske ta wuni ranar tana kukan, Tausayin Laila yake dawainiya da ita. Tasan tabbas Laila ba barauniya bace kuma she was right. Tsautsayi ne ya gifta mata balle bata dauka ba tunda ta bar masu, kuma ko ita ce aka sakata a halin tsaka mai wuya dole tayi abinda yafi haka. Bata ga laifin Laila akan sharrin datayi mata ba. Dama ance iya ruwa fidda kai kuma

 • ta fitar da kanta babu matsala. Sanin kanta ne Saif baida mutunci kuma zai iya sakin Laila ba tareda yaji bakin zaren ba.
 • Amma Alhamdulillahi Bilal yanada dogon tunani bai dauki mataki ba cikin fushi.
 • Da kyar ta karasa musu abinci wanda white rice ne da stew. Kadan ta iya turawa tana tauna kamar tana hadiye magani. Abinci baya gabanta. Ta kosa Bilal ya dawo ta bashi hakuri. Bai dawo da wuri sai chan wajen goma abinda bai saba ba, Haske ta soma kai shi bango. Kuma yana kyautata zaton zasu samu sabani sosai nan gaba idan bata canza wannan ra’ayi nata ba.
 • Tana zaune a daki tayi tagumi tanajiran sa, yayi mamaki yadda batayi barci ba. Yadda ya ganta cikin damuwa sai yaji babu dadi amma kuma ita taja ma kanta. Duk abinda ya faru da ita tayi kuka da kanta. Murmushi yayi mata saiya karasa inda take. “My dear! Bakiyi barci ba” Hawaye ta soma yi, daga nan ta fashe da kuka. Rungumar ta yayi atleast taga aikin Laila
 • first class. “Dan Allah kayi hakuri ban daukar maka kudi ba!” “Shhh babu damuwa! Karki damu nasan bake bace makiya ne”
 • “Itama Laila ba da gangan tayi ba” Da sauri ya ture ta ya mike tsaye, kunnen sa basu ji me tace da kyau ba. Kamar Haske tanaso tayi defending Laila ne. “Me kika ce?”
 • “Na kira Laila kuma tayi min bayanin dana gamsu, bada gangan tayi ba. Bashi ake bin ta shine nace zanma bata Gold dina ta siyar idan ta samu saita bani”
 • Daga hannu yayi sama yana nuna mata, fushi yayi sosai. ldanun sa suka canza farad daya. Bala’i ya soma cinsa. Tunda yake bai taba ganin dakikanci kamar nata ba. Mamaki fal yakeyi. “Karki ce min kin yarda da karyan data zabga maki”
 • “Ba karya bane, i can feel the pain in her voice. Da gaske take. Kuma tayita damuwa tana tsoron kada ka sake ni” 
 • “Tana tsoro ko tana murnar an sake ki?” “Haba she’s my best friend Fah, meyasa zatayi min haka? Ina ka taba ganin anyi haka? Yasa zan bata Gold din karka damu zata biyani” “Shine zaki dauki Gold din dana siyan maki ki bata? Are you stupid Shamsiyya? Halan a kasa na tsinta kudi da zaki rinka bama wata yar iska abina? Meye matsalar ki? Kinsan yadda na siya Gold din kuwa? Ace ga abu kiri kiri amma ki kasa gani. Ana nuna maki annabi kina 
 • runtse Ido Kuka ta fashe dashi, Bilal bazai fahimci taba. Wanna wani irin tsana ne haka yake bin Laila dashi. Ko kashe mutum tayi bai kamata yayi mata haka ba, balle yar uwansa musulma. Bilal Dan Allah ka bari na taimakawa Laila, she is in dire need of my friend. Almuslim akhi Muslim, koba komai dan darajar ma’aiki ka barni mana. Haba sweet dina !” tace tareda share hawaye, idonta yanzu saura kiris su tsiyaye sabida kuka. Gyara tsayuwa yayi yasa hannu a aljihu, fuska a murtuke ya soma magana” A gaskiya nayi mamakin ki! Kinada kai amma na daukar kaya ne! Bayada wani amfani wajen ki tunda bakya amfani dashi ki ga baki da fari“ hadiye miyau yayi sanadiyar zafin da yaji a Chan makoshin sa. Zuciyar sa daci yake mashi, ldansa ya sake canza kala, asalin Badman Bilal kake gani. Meye matsalar ki ne? Babu yadda banyi ba ki gane halinta amma sai bakina kike gani saboda kin raina ni. Yanzu kin koya shika shikan rashin mutunci kina min rashin kunya akan wata banza, you’re going to lose me. Wallahi bazan dauka ba kuma ban yarda ki bata gold ba kinji na gaya maki” “Haba Bilal ina ce mallaka nane kuma zan iya amfani dashi duk yadda naga dama” “Jibe yadda kike mayar min da martani, ko a shekaru niba sa’anki bane balle kuma ni mijinki ne a haka. Na rantse kika bata a bakin auren ki” Gabanta ya fadi sosai, hannu tasa ta toshe bakinta saboda kuka daya subuce mata. Yanzu ta ina zata taimakawa Laila tunda Bilal ya hanata. What is happening? Rayuwarta yazo karshe. “Wai ta shiga dakina ko ajinki, ko kishina bakya yi baki tambaya meyasa ma tayi hakan ba. A’a kawai tayi maki karya kin yarda. Toh tunda ke kunnen kashi gareki bakya jin magana zan dauki tsartsauran mataki. BAN YARDA Kl SAKE HULDA DA LAILA BA” “Sweet dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan iya rayuwa ba tareda ita ba. Mun shaku sosai karka raba zumunci. Duk wanda ya yanke zumunci Allah fa zai yanke dashi” tana kuka wannan Karon harda tari ta soma kamarzata mutu. Bilal ko gezau baiyi ba, indai akan Laila ne yana kan batunsa. Haka ta gama ta share bakinta, “Ba shakuwa ba naga kashin awaki banji tsoro ba! Suda tare suke fitowa amma kuma suna bushewa kowa ke sabgan gabansa, why do you religiously defend her? Akan ki aka fara kawance? Meye bana maki ? Meye kika rasa? Allah yasan ina kokarin kare amanarda aka bani. Amma ke kam kinaso ki gagare ni. Laila tayi sanadiyar aurena da Banan amma kika ki yarda dani, na lura ko kishi bakiyi ba, kinfi damuwa da meye Laila tayi da wanda batayi ba… Mts” “You’ve lost me Shamsiyya! Kin rasa ni gaba daya” Fita yayi yabar dakin, dakinsa ya koma tareda rufewa da Key, tayi abinci kuma yanajin yunwa amma yaki ci, haka ya shiga ban daki yayi wanka. Yana watsa ruwan dumijikinsa yana karkarwa da tsabaragen bacin rai. Yau da yanada hawanjini dole ya tashi. Ya dade a bayin yana tunani kafin ya fito. Durowa yaje ya dauko jallabiya yasa saiya kwanta. Ranar daga shi har Haske babu wanda yayi barcin kirki. Kowa da abinda yake ayyanawa. Ita abu biyu yanzu yake damunta. Laila da Bilal, rashin ‘jituwar su ana bata mata rai. 
 • Kawai saita yanke shawara akan ta tashi tayi sallah ko zata samu sanyi cikin ranta, AlIah ya kawo mata karshen wannan tashin hankali. Shi kuma Bilal yana ganin aurensa da Haske ya kusan zuwa karshe. Ga saka hannun Laila ga kuma taurin kai irin na Haske. Mamaki yake yadda takeda bala’in dolonci, ga tsautsauran ra’ayi. Bai ma Santa da halin ba. Kwafa yayi tareda buga tsaki mai shegen kara, a daren yayi tsaki yafi sau hamsin. Barci yaki idanun sa. Haka bakin ciki yayita damun sa
 • Da asuba ya tashi ya fita masallaci, ko bi ta kanta baiyi ba wanda abin ba karamin kona mata rai yayi ba. Sanda ya dawo ya wuce kitchen ya kunna kettle, yana tausa ya hada ma kanshi shayi saiya wuce daki ya garke kofa. Tayi wanka ta saka kananan kaya zata wajen sa domin ta bashi hak’uri, aikam taji dakin sa a rufe. Bugun duniya tayi ya basar da ita asalima headphone yasa tareda kunna laptop yana kallon ‘Black Panther‘ Haka ta tafi tareda zallan bacin rai, sai ta wuce kitchen domin tayi kalaci. Anan tayi doughnut mai filling da chocolate ta ciki.Yayi dadi sosai ga kuma ta kawata shi da kyau. Bilal bai fito ba saida tara ta gota, gezner yasa light blue da navy hula, sai bakartakalmi. Ga links masu dankarin tsada ya saka. Ya zuba turare sosai yana kamshi tareda danna 
 • lPhone X dinsa. Gashi tun asuba Mallam Musa ya wanke masa Benz dinsa yana sheki. Tana zaune akan dinning tayi tagumi abin duniya yayi mata yawa, ko kallon gefenta baiyi ba ya zauna akan couch, crossing kafa yayi yana karkadawa a hankali cikin takama. Kana ganinsa kasan wani ne wanda ya isa. 
 • Remote ya dauko yasa BBC lifestyle, yana kallo tareda danna wayarsa a tsakani, sai yaga kirar. lnda ake sanka banan ake ganin kaba, wai mai sanko yaga gashin hammata. Jibe yadda yake bin Haske amma tana mashi fuska bayan Banan kamar taje sama ta fada ma Allah akan soyayyar datake mashi, harda zaiki dauka saiya fasa. A natse cikin gadara ya kara a kunnen sa. “Speak Up” yace cikin takama. 
 • “Ina kwana, ya kake ?” “lau! Me kike so?” 
 • “Dama inaso na tambaya yaushe za’a kawo lefe” “Weekend” “Okay” 
 • Sai su kayi shiru babu abinda suka sake fadi, tsoro takeyi sosai kafin ta fada abinda yafi karfin bakinta. Shine ya yi magana “Okay akwai wani abu ne?” “Dama ina tunanin ko zaka biya wajena anjima ne idan babu damuwa” ta fada a tsorace. 
 • “No, aiki yamin yawa maybe gobe ki ganni, bawai na tabbatar bane” saiya kashe wayansa. Duk abinda sukayi a kunnen Haske. Sai yanzu ta gane tana bala’in san shi. Wani kishin sa ta soma yi. Wai tun kafin ayi auren kenan. Yanzu a haka wai bai ma wani sake da Banan ba balle su kwana shimfida daya. Taji haushin kanta da irin diban albarkan datayi masa. Kaico ta soma yi da hali irin nata. Cizan lebanta tayi ta karasa inda yake. 
 • Ko kallonta baiyi ba harta zauna a gefen sa, langabe kai tayi tareda marairaicewa. Kasa kasa ta soma magana wanda saika mayar da hankali zakaji. “Sweet ina kwana!” tace a sanyaye “uhmmmm” ya amsa mata dashi. ‘kin makara yarinya’ yace cikin ransa. Hawaye ya soma malala mata, meke shirin faruwa da ita ne. Aurenta yana tangarda. Bilal bai taba kallonta da yanayin nan ba, kamar abin wulakanci ya gane sai shan kamshi yakeyi. 
 • “Sweet dan Allah kayi hakuri Just ka Kalle ni” tace saita karasa inda yake ta zauna. Matsawa yayi karta taba shi. Hannun sa da zata rike yayi maza ya janye. Tsoro ya sake mamaye ta. Saita barke da kuka wiwi. 
 • Tsaki yayi saiya ajiye remote din zai fita, da sauri ta tare gabansa, ya karkata itama zatayi, “Matsa min malama” yace cikin ko’in kula “Dan Allah sweet kayi hakuri, karka dauki mugun mataki akai na. Wallahi ina sanka kuma na tuba” matsar da ita yayi da hannun sa sai ya wuce. Baisan hawayen ta amma kuma batajin magana. Zuma saida wuta idan bata ga haka ba bazata yi hankali ba. Anan ta durkusa ta soma kuka, sai kuma ta tashi domin ta kira Laila a waya. Zasu rinka mu’amala amma a sirri yanda Bilal bazai gani ba. Shi kuma ya mance bai dauka car keys ba. 
 • Haske ta juya ma kofa baya ta rapka tagumi tana kiran waya, kawai sai tagansa a bayanta yana huci. Numfashi sama sama yakeyi kamar mayunwacin zaki, idansa ya kada kamar na kwaya. Sakin wayar tayi kasa tareda ja da baya. Nan take duk wani annuri a fuskan sa ya bace kamar bai taba dariya ba. Babu haufi yaga abinda takeyi kuma ga sunar Besty baro baro. Jikinta ya soma rawa zufa ya fara mata anbaliya, kukan ma kasayi tayi tana girgiza kai cikin nadama, ko ba’a fada ba yanzu ta tabbatar batajin magana. Wannan kenan! 

 • Ah haske ah 🤣😠

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page