QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 10

 • QADDARAR SUMAYYAH • CHAPTER 10
 • ‘A WANI DARE’

 • Tun magariba ta shige dakinta kasancewar ba ranar girkinta bane,tun wajejan yammaci take jin ciwon kai da fargaba kadan kadan,hakanne ya sanya tun tana saman abun sallah bayan ta kammala sallar isha’i bacci yayi awon gaba da ita,ko mukhtar da yazo mata sai da safe haka ya sameta,daukarta yayi cak ya maidata saman gado sannan ya ja mata qofar ya fice.
 • Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta,cikin wata iriyar murya ce wadda sam bata ta dadin amo,a hankali ta dinga bude idanunta cikin duhun da ya gauraye dakin nata,tabbas sunanta ake kira cikin wata murya mai kama da amon sautin kukan kare.
 • Idanunta ta ware sosai saboda wata siffa data dinga hangowa ta tokare bangon dakinta daga inda take fuskanta,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarceta take gumi ya rufeta baki daya,jikinta ya hau rawa “Bismillahil lazi la yadurru ma’as mihi shai’un fll’ardi wala fissama‘i wa huwas sami’ul alim” haka ta dinga maimatawa,tun tana yi cikin zuciyarta har ya fito flli,maimakon kiran sunan nata da ake a hankali sai aka koma da sauri sauri,sannu a hankali siffar halittar da take gani jikin bangon ta bace bat.
 • Cikin wani irin hanzari da kuzari ta diro daga saman gadon nata hannunta dauke da waya falo tayo tana ci gaba da ambaton sunan Allah,ta kunna kwan dakin tana mai qarewa falon nata kallo,babu abinda ta gani,cikin sanyin jiki ta zauna kan daya daga cikin kujerunta dafe da kanta.
 • Tsawon mintina ashirin ta dauka a haka sannan ta isa bakin t.v stand dinta,ta dauki ruwan leda guda daya da ya rage wanda tasha dazu,dankwalinta ta cira ta ninka ta shimfida ta daura alwala a kai sannan ta fuskanci gabas. Sallah tayi raka’a hudu sannan daga bisani ta zauna,cikin surorin data haddace ta dinga karantawa daya bayan daya,har zuwa sallar asuba bata samu ta runtsa ba,a nan zaune mukhtar daya shigo tayar da ita sallah ya sameta,yaso ya danyi mamaki amma sanin cewa wani lokaci takan tashi da wuri ya sanya boye mamakin nasa ya fita ya tafi masallaci.
 • Sai kusan biyar da rabi ta koma saman kujerarta ta kwanta a nan bacci ya sureta.
 • Sallamar mukhtar ce ta tasheta,ta miqe tana mutstsike idanunta,a shirye ya shigo da alama kasuwa zaya flta “Laflya kuwa kike sumayya,wani irin bacci yau kike haka sam banji motsinki ba?” Murmushi tayi tana gaida shi ba tare data amsa masa tambayarsa ba “Ni zan fita babu wata matsala k0?” Ya fafa kamar yadda ya saba fadi duk sanda zai fita kasuwa,kai ta girgiza “Babu komai,a dawo lafiya Allah ya bada sa’a” “Amin” ya fada yana kashe mata idanunsa daya tare da cewa “Yau ba rakiya my sumy?” Kai ta kada “Kaima ka sani ba girki na bane,ka kuma san halin fa’iza sarai,ranar girkinta bata son kowa ya rabeka k0?” Kai ya kada “ina ruwa na da ita,tunda kafin na santa ke na sani ko,amma tunda kince haka shikenan,sai na dawo” ya fada yana daga mata hannu kana ya fice. Sai da ya flta da wajen mintina biyar sannan ta miqe,daki ta nufa da nufln shiga,gab da zata shiga din abinda ya faru jiya ya dawo mata tar a kwanyarta,tsayawa tayi jim sannan ta karanto addu’o’i ta shiga.
 • Tsayawa tayi tana bin kowanne lungu da saqo da kallo bata ga komai ba saboda haka ta dauki abinda zata dauka ta fito
 • Ga mamakinta tsakar gida ta taras da fa‘iza zaune saitin window din dakinta zaune,kallon juna sukayi sumayya ta dauke kanta ta nufi bandaki don yin wanka.yayin da fa’izan ta bita da kallo,har ta kammala wankan ta koma daki ta shirya ta fito ta shiga kitchen don samawa kanta abinda zata ci fa’izan na zaune,dim yawanci idan ranar girkinta ne bata baiwa sumayya abin kari,to da yake ita din ma ba gwanar abinci bace hakan baya dada ta da qasa saita hada duk abinda ya samu taci shikenan an wuce gurin. Yauma kamar jiya bacci ya dauketa da wuri,kamarjiyan dai cikin bacci taji ana kiran nata,taji ai wannan karon bude idanunta tai cikin gigita,yau kam siffar macizai take gani tsaye ya mamaye bangon “A’uzu bi kalimatillahit taammati min sharri ma khalaq” ta dinga maimaitawa da qarfinta har bata san tana daga murya ba ko kuma ta manta cewa dare ne,bat abun ya bace sama ko qasa,a bakin qofar ma daga dakin sukaci karo,mukhtar ne yana tsaka da bacci ya dinga jiyo muryarta,jikinsa ta fada gabanta na tsananin duka jikinta na rawa,janyeta yayi zuwa falon suka zauna gefan kujerar yana tofa mata addu’a.
 • Sai da ta samu nutsuwa sannan ya dube‘a ba tare da ya tambayeta me ya faru ba “Muje dakina ki kwanta a can” kai ta kada tana zarejik’mta daga nashi “Kaje kawai babu komai zan iya kwanciya a nan,mafarki kawai nayi kuma yanzun nayi addu’a” idanu ya zuba mata sai ta kada kanta tana son gamsar da shi kan abinda ‘ta fada din,kan doke saboda yadda ta kafe ya sanya shi barinta tare da sake mata addu’a sannan ya fita. ‘ Qarfe tara na safe tuni tayi wankanta tana zaune a falon cikin rashin kuzari da tunani barkatai,a haka mukhtar din ya taddata,bayan sun gaisa ya samu gefanta ya zauna “Sumayya,meke
 • damunki,na tabbata akwai abinda ke damunki,yanayinki jiya ya tabbatar min da haka,kada kuma ki soma cemin babu komai” qasa tayi da kanta don kada ya ga tsoron dake cikin idonta,sai da ta saisaita kanta sannan ta dago “Ya mukhtar,ina zaton akwai maciji cikin dakin nan“
 • “Maciji?” Ya tambaya cikin mamaki,kai ta gyada masa,sai yayi shiru na wasu daqiqu kana daga bisani ya ajjiye jakar dake hannunsa yana mai miqewa “Ina zuwa” ya fada yana ficewa. Minti kusan arba’in da biyar sai gashi ya dawo da wani matashin saurayi,wanda aikinsa shine Fidda maciji kowanne iri,dakinsa ya bude mata yace ta shiga ciki ta zauna tare da kulle dakin,duk abin nan da ake fa’iza na cikin dakinta tamkar bata cikin gidan,shi da matashin suka shiga cikin dakin nata. Duk wani salo da dabara irin tasa da ya gada ta flddo da maciji ko wani mugun qwaro daga bigirensa babu wanda bai gwada ba,saidai ko kusa ko alama babu wani abu da yayi kama da maciji cikin uwar daka da rumfar tata,hayaqi yayi kusan kala uku amma shuru babu maciji,hakan shi ya tabbatar masa babu wani maciji cikin gidan rna baki daya ba dakin ba,yace amma ta sake kula sosai idan ta sake ganin wulgawar wani abu nan da kwanaki uku ta sanar masa zaya dawo,mukhtar ya sallameshi ya tafi.
 • Shi ya taimaka mata suka maida suka kintsa dakin,suka maida komai muhallinsa,bai samu fita kasuwa ba sai azahar ya fice,ita kuma ta nufl bakin fanfo ta tara ruwa zata yi alwalar sallar azahar din. Sai lokacin fa’iza ta f1t0,wani kallo ta yiwa sumayyan kana ta sheqe da dariya
 • “An tara haram an gyara daki dama ta yaya za’aji dadin zama a ciki?,kayan haram ne fa? ……. hhhhhh …… hmmm kadan ma kenan” ta fada tana jan wani shegen tsaki tare da juyawa ta koma dakinta.
 • Cikin mamaki take binta da kallo tare da neman tsari cikin zuciyarta,matar da duk artabun da ake cikin gidan tun safe bata flto ba sai yanzu,watsar da tunanin tayi,me yasa dakinta ya tsone mata ido,koda yaushe bata da magana sai nashi,da bata ce Allah ya sawwaqe ba ta ja bakinta tayi shiru mana.itadai tunda ta riga da tasan cewa tayi addu’a koma meye zaizo ko da QADDARARTA ne sai ya sameta din zaya zo mata da sauqi.
 • Tana kammala sallarta kitchen ta wuce ta soma hidimar dora girki saboda yau girkinta ne ita zata karbi mukhtar din,ita kuwa bata wasa da ranakun girkinta.tana kitcehen taga ficewar fa’iza daga gidan. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page