QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER8

QADDARAR SUMAYYAH

CHAPTER 8


“Wanne irin aiki kuma,daga dawowar taka?” Ta fada tana duban fuskarsa da maqullin dake hannunsa,girarsa ya dage mata yana fadin “Muje mana,idan muka je ai kya gani” ya fada yana nufar kitchen din,bata sake cewa komai ba tabi bayansa. 
Kayan abincin dake jifge gefe daya na kitchen din ya nufa ya fara daukarsu daya bayan daya yaba zuba cikin locker din sumayya,sai daya gama kwashesu tsaf tana gefe tana kallonshi,ya bude kwadon yana shirin,,,,,”Me kenan?” Sumayya ta tambaya,waiwayo wa yayi yaba dubanta 
“A nan nake son kayan abinci na su zauna,zan baki dan muqulli daya,kada ki soma bawa fa’iza mukullina sai ranar girkinta” “Amma ya mukhtar gani nake wannan ba shine dai dai ba,ka raba ka bawa kowa nasa yafi maslaha,idan yaso ……. “Haka nake da buqata” ya fada yana mai katseta ba tare da ya barta ta gama fadar abinda tayi niyya ba,bata sake cewa komai ba harya gama rufewa ya cire muqullin guda daya ya miqa mata ya zuba sauran cikin aljihunsa. Tana gaban mudubi bayan sallar magariba gab da isha’i tana shafa mai kasancewar yau bata samu tayi wanka da wuri ba,saboda tunda fa’iza ta fahimci wanka zata shiga tayi shigewarta bandakin,bata flto ba sai da aka kammala sallar magariba sannan ta bata gu. 
Wayarta dake kusa da ita taga na haske alamar kira na shigowa,ta miqa hannu ta dauka ganin sunan mukhtar “Kizo daki na ki sameni“ taji yace “To” ta amsa masa sannan a gaggauce ta kammala kwalliyarta,ta shirya cikin doguwar 
rigar atamfa fitted gown mai dogon hannu,ta feshejikinta da turare bayan tayi daurinta wanda ta kafa shi gaban goshi. Adakin ta tadda su yana kan kujera yana rubuce rubuce ita kuma na gefan gadon zaune,ta musu sallama mukhtar ya amsa ta samu gefansa ta zauna,cikin karyar da murya tace “Sannu da aiki yallabai”  salon da ta masa maganar da shi ya sanyashi daga kai ya dubeta,a nan yaci karo da kwalliyar ta wadda ta burgeshi “Masha Allah,yauwa my sumy” wani mugun tsaki sukaji anja,dukansu suka dubeta,mukhtar yace “Kina da matsala ne?” Idanunta na kan sumy tana kafa mata harara wanda hakan bai sanya sumayyan itama kafeta da ido ba duk da cewa ba hararar ita take aika mata ba “Na fuskanci fa wasa wasa ana neman rainani da take min haqina cikin gidan nan,idan banda haka ya za’ayi mace ba girkinta ba komai ba zaka wani daga waya kayi kiranta,tun yanzu ma ina cikin kwanakin amarci na kenan?,to wallahi sam bazan lamunta ba idan hakan yaci gaba wallahi zan kai gaba ne inda za’a qwatar min haqqina ehe“ ta qare maganar idanunta na kan mukhtar “Inda kinsan yadda kike da rashin matsayi a zuciyar wanda kike mawa da baki aikata hakan ba ma wlh”sumayya ta fada cikin zuciyarta amma a sarari sai ta saki wata siririyar dariya tana rausayar da kanta tare dajanye qwayar idanunta daga kan fa’izan wanda hakan ya sake qular da ita,saidai kan ta kai ga cewa wani abu mukhtar ya tari numfashinta ” ba wannan shirmen ya sanya na taraku ba ….. na taraku ne saboda almubazzaranci da na lura an fara min da abincin da nake nemowa da gumi na wanda duk cikinku ko wace na lura ke hakan zan taka mata burki ne,dalili kuwa shine duk wani almubazzari dan uwan shaidan ne,saboda haka bazan yarda a dinga shaidanci da abinda nake nemowa da gumina ba kuma na siyo da halali na,ni ba barawon gwamnati bane bare ace bansan ciwon kudi ko zafin nema ba,ni dan kasuwa ne dake nema cikin inuwa da rana,sanyi da 
zafi hakanne yasa na yanke hukuncin adana kayan abincina ta yadda ya dace”ya dan sarara yana maida numfashi yayin da fa’iza wadda ta cika tayi fam takejira taji qarshen zancan,don gaba daya ta sarrafa maganganun nashi ta aunasu a mizani ta dorasu kacokam a kanta. 
“Na siyi muqulli na kullesu suna kantar sumayya,hakanan mukullin na gurinta,duk wadda ke da girki ta karba ta bude ta debi gwargwadon abinda zaya wadaci kowa yaci ba tare da barna ko almubazzaranci ba….” Yana dire zancan fa‘izan ta miqe ta dubesu kana taja qwafa 
ta fice fuuuu kamar wadda guguwa ke binta. Sumayya ta bita da kallo yayin da shi kuma ya shareta tamkar baiga abinda tayi din ba ya dingajan sumayyansa  da hira,qarshe ma ya janyota cikin jikinsa yana fadin yayi missing dinta,sai data masa wayo sannan ta samu ta gudu dakinta,batasan ya suka kwashe da fa’iza ba. Washe gari sun kammala break fast kamar yadda suka saba yi tare ba tare da fa’iza ba,ta rakoshi tsakar gida kenan aka turo qofar gidan tare da kwado sallama aka shigo,sai da gaban sumayya yayi wata mummunar faduwa,yaya yahanasu ce,ta qaraso tsakar gidan tana binsu da kallo daya bayan daya “Sannu da zuwa” sumayya ta ambata cikin gayyato dakiya da juriya Sannu da zuwa yaya” mukhtar ya ambata yana shirin juyawa zuwa falon sumayyan “Dakata ba shiga zanyi ba” ta fada tana daga masa hannu alamar dakatarwa,sai ya tsaya din ya waiwayo yana dubanta “Ina fa’izar na ganku ku daya a tsakar gidan kuna ta warka jaminku?” Ta fada tana yamutsa fuska,kafin daya daga cikinsu ya bata amsa ta bude qofar dakin nata ta fito. Fashewa tayi da kuka da sauri ta taho gun yaya yahanasun ta fada kafadarta tana fadin “Wallahi yaaya na gaji,na gaji da zaman gidan nan,cikin kwana uku kawai amma baki ga irin wulaqancin da na fuskanta ba,gwara kawai a yita ta qare donni na gaji,tunda nazo ban samu kwanciyar hankali ba,matarsa ta gama da shi sai abinda tace,a haka kuma kuke so na zauna da shi na haifa muku ‘ya’yan?har yau fa ban sanshi a da namiji ba fa,randa aka kawomi kwana nayi muna artabu da shi kan hakan”kafadarta yaya yahanasun ke bubbuga wa,cikin murya mai nuna iso ga wanda ake da iko da shi take fadin 
yi shiru fa’iza,kwantar da hankalinki,ai tunda nazo zance ya qare,ko da baqarjaba take asiri wallahi sai na karya shi …… kai muntari muje …… kema kuma shegiya munafuka muje”ta fada tana dosar dakin fa’izan jaye da hannunta,sai data kai gab da shiga ta waiwayo ta dubi mukhtar wanda ke tsaye idanu jajur saboda bacin rai,sai taga ma sam bai daura aniyar binta ba bare sumayya da taja gefe daya,ta riga ta qudurci indai a dakin fa’izan 
za’ayi shari’ar saidai yaya yahanasun tace ta mata rashin kunya amma babu inda zata je. “Bakaji abinda nace bane?,cewa nayi ka biyoni” kai ya shiga girgizawa cike da bacin rai “Indai ni nake auren sumayya da fa’iza to a dakina nake buqatar ki fadi duk abinda kika zo yin shari’ar a kansa” ya fada yana juyawa zuwa dakinsa bayan yasa maqulli ya bude,basu ce komai ba ta ja hannun fa‘izan suka canza akalarsu zuwa dakin mukhtar sumayya ta rufa musu baya. 
Kuka take har da na qarya da munafunci,da qyaryaya yahanasu ta shawo kanta,yayin da sumayya da mukhtar ke gefe sun zubawa sarautar Allah ido,sumayya na kallon sabon shafin makirci da duniyar kishi ke dauke da shi,sabon darasi kuma sabon karatun da bata san da shi ba a duniyar aure sai yau,yayin da ran mukhtar ke tafasa,wannan har macen aure ce?,matar da cikin kwanaki uku rak! Ta fara birkita duniyarsa da zaman lafiyarsa gaba daya?,cikin kwana uku rak! Har an fara zuwa musu sasanci da shari’a,abinda iyakacin zamansa da sumayya ba’a taba samu ba cikin tarihin rayuwar aurensu. 
Sai da ta kammala shawo kan nata sannan tace ta zayyane abinda aka mata,nan ta baje shafin qarya da gaskiya ta gwamutsata ta mata ado,yadda take tsara laifukan da take ikirari anyi mata kai ka rantse cewa shekara sukayi tare. 
“To yanzu me kike so ke fa’iza?” Yaya yahanasu ta tambayeta “To ni dai yaya gaskiya babban abinda yake cimin tuwo a qwarya shine,abinda aka kawoni nayi gidan nan na zube ‘ya’ya mukhtar bai fa dauko turbarsa ba,don haryau bansan d’a namiji ba wlh” ta fada kanta tsaye ba tare da kunya ba,ita kanta yaya maganar ta mata nauyi,har ta danyi shiru tana nazarin ta yadda zata yiwa mukhtar magana kan hakan,amma dole ta fidda kunya,idan ba haka ba wankin hula ya kaisu dare,mukhtar shi kadai ne d’a namiji acikinsu,saboda haka dole a kawo qarshen wannan tafiya,nan ta rufe ido ta dinga yayyafa masa bala’i,qasa yayi da kansa cike da baqinciki da qunan rai har ta kammala fadanta “Kai muntari,ashe kai ba adalin namiji bane?,to wallahi a daren yau din nan nake so a kawo qarshen komai,kada ka sake ka gama kwanakin ba tare da komai ya afku ba,kuma kada ka kuma bari ta kawomin qararka kan hakan” Ta fada tana kada yatsu,kai ya dago ya watsawa fa’izan wani matsiyacin kallo sannan ya kalli yahanasun “In sha Allahu” ya fadi a sanyaye,sumayya dake gefe kunya duka tabi ta cikata,ga wani takaici da ya cika mata zuciya. Sake juyawa tayi ta kalleta 
“Sai kuma me?” Yauwa yaya zancan bawa waccar maqullin ma’ajiyar abinci,sam ni wlh ban yarda ba a raba a bawa kowa nashi kawai” sai ta sakejuyawa ga muntarin 
“To kai kaji sai ……. ‘ ‘ Cikin fushi da baisan ya taso masa har ya katse yaya yahanasun ba yace “Wannan kuma bata isa ba tayi kadan,iskancin naki naga ya fara samun gindi zama,wacce iriyar shari’ace haka yaya kike?,ita daya ke da abun fada?,ita daya ke da bakin magana,to wallahi ni ba sauna bane da zan nemo abu da zafin gumi na a wulaqanta shi ba,zata iya zama idan taga zata iya zata kuma iya kama gabanta” sarai tasan halin muntarin,akwai sanin ya kamata kawaici da dauke kai,amma fa idan aka taboshi bashi da dadi,tasan cewa har yau bai son fa’iza baison auren gudun kada aje garin neman gira a rasa dukka idanuwa ya sanyata itama hayayyaqo masa cikin salo irin na nade tabarmar kunya da hauka 
“Oh ni yaha,innarmu ta haifawa wata ni kuma na rainan mata,yanzu muntari har kayi riqar da zaka dinga haikemin,qwarai wannan abu yayi kyau,ko da yake baka da laifi wannan baqarjarabar da Allah ya jarabcemu da ita ne,dama ance idan bakayi wasa ba abinda ke baka tausayi wata rana shi zai koma baka tsoro,ita ba amfana ake da ita ba ma baki daya sai ita dake amfana da mutane” haka ta dinga zazzaga,abun da ya sake bata mata rai ganin yadda sumayyan tayi burus a maimakon a baya da idan tana irin hakan take zagewa tayi ta bata haquri wani lokaci har da kukanta. 
Qarshe ta kama hannun fa’iza tace ta tashi suje dakinta tana son ganinta kafin ta wuce,fa’izan ta kalleta “Yanzu na haqura kenan?” “Fa’iza,waccar da kike gani saidai mu hadu muyita taya muntari da addu’a,don idan nayi rantsuwa ko kaffara ba zanyi ba ba cikin hayyacinsa yake ba,ke dinma inaga rabo ne ya rantse shi yasa kika shigo” ta qarasa maganar suna ficewa fa’iza na qunqunai wanda hakan ya sake bata ran mukhtar,ji yake tamkar ya shaqeta ko zayaji sauqin bacin ran dake cin zuciyarsa. Ya rantse sai ya hukunta ta,sai ta gane bata da wayo,’yar bariki ce ita ko mai,zai nuna mata bata iya iskanci ba. Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa “Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba” sai ya tsura mata ido yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsu da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa kansu shi ba sai Allah yaga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta “Kada ki damu sumayya,ina gane komai” yayi kissing goshinta yana fadin 
“Sai na dawo” ya juya ya flta a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma tsaidashi. 
Kai ta kada sannan ta Flto daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key din dakinta,cikin 
falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran rana freedom. 
Tana kammalajin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa’izar,ita daya ta taras da alama yaya yahanasun ta tafl wanda ita sam batasan ta tafin ba “Ga abinci can cikin kitchen na gama” ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka ba,don har da 
yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare. 
Sau biyu suna kacibus da fa’izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana jira botikin ya cika. 
Da sauri taga ta fiIto daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa’izan tayi har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta. 
Wasa wasa har ba fa’iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyarta zauna tana ci gaba da dakon fitowana. Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zuwa tare da jin nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al’adarta ce daya dawo ya sameta tsaf. Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta waiwayo fa’iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake amsa mata,sai sumayyan ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan “Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar daren’ ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai ta saki murmushi sannan tace “Ko?”cikin qufula da ganin yadda maganar bata da data da qasa ba ba yadda taso ba tace ” eh,ko kina musu ne?”kai ta gyada sannan a taqaice tace mata “Zamu gani” ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa taja 
domin bata da amsa ta shige dakin angon nata. Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa’izan,tana wani murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna “Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?” Ta fada tana wani kashe masa ido,ya fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tanka iyaka aka tura mata kulolin ta debi yadda taga zata iya. 
lta da sumayyan kusan tare kowannensu ya sanya Iomar farko a bakinsa,idanu sumayya ta zaro sakamakon wani dan banzan gishiri da ya cika harshenta har zuwa kwanyarta,take qwaqwalwar tata ta tafi tunanin ta yadda akayi hakan ya faru?,a iya saninta lafiyar Allah ta kammala komai ta gyatta shi,amma me ya kawo wannan sauyin?,ko dai harshenta ke 
shirin samun matsala?,. “Qundun uban nan” abinda fa’iza ta fada kenan wanda shi ya tsinke zaren tunanin sumayya,kallon mukhtar suke dukkansu kowanne da tasa manufar a zuciya,zaquwar mukhtar yayi magana ta samu filin baje hajarta da kuma mamakin yadda yaqi maida hankali ga kalamanta da takeyi,cikinsu babu wadda ya kalla saici gaba da sambada lomarsa yake,yayin da sumayya tayi qas da kanta ta daure dukwani abu da takeji kan harshenta itama taci gaba da kai lomarta tamkar babu wata matsala dake waka na. Idanu fa’iza ta dinga binsu da shi,to ko dai harshenta ne kadai ke gaya mata tuggunta yayi dai dai?,ganin sunyi uwar watsi da ita ya sanya ta kasa shiru sai da ta magantu “Wai muntari bakaji uban gishirin dake cikin abincin nan bane?” Bai amsa mata ba sai da ya sake wata Iomar “Wanne abinci fa?” “Na gabanku mana” ta fada tana nuna kwanon da yatsa tare da qanqance idanu “Hala kina da matsalar dan dano k0?” Kafeshi tayi da idanu tana tantama,sai kawai ta miqa hannu ta kwaso miyar gabansa ta kai bakinta,tabbas iri daya ce haka ma dandanon iri daya ne,to tsabar iya asiri ne na sumayya yasa bai fahimta ba ko sun tasamma raina mata wayo ne,fa’iza macace da sam bata da siyasar zamantakewa,hakan ne ya sa ta kasa boye fushinta ta tashi ta fice fuuuu ta bar dakin cike da baqinciki,so tayi yau ya ciwa sumayya mutunci sannan ya janyeshi kuma ta kwana da shi yau ta cusa rnata baqinciki. Idanunta ta dora kan mukhtar fuskarta qunshe da tashin hankali,ta bude baki zatayi magana ya dora yatsansa kan lebansa “Shshshshsh!,kada kice komai,ita ta zuba gishirin kan ido na bayan shigarki wanka,tana zaton bazanci ba,batasan ba maqaryacin so nake miki ba,zan iya cin wanda yafi haka ma,bare ma shekararmu nawa da sumayyaty na santa qwarai wajen iya sarrafa hatsi” yadda ya qare maganar ne ya bata dariya harsai da ta dara din,daga bisani ya wanke mata duk wani damuwa tata suka bige da hira,yace idan ba zata iyaci ba kada ta cuci kanta ta ajjiye ya sama mata wani abu shikam zai iya ci,tace sam tunda har ya iya ci itama sai taci,qarshe dai ramin muguntar gun fa’izar ya koma tunda ko banza ta tashi ciki babu komai. Yau din da kanshi ya mata sai da safe,kishi ya kamata sosai ta dinga rayawa cikin ranta wato zashi yaje yayi abinda anty yahanasun ta umarceshi kenan dazu da safe,ta dingajuyi saman gado ita daya da qyar bacci ya saceta. 
Bata jima da fara baccin ba ta dinga jin ihu sama sama cikin barcinta,a sannu ta bude idanunta tarwai,tabbas ba mafarki bane,ihu ne daga dakin fa’izan kuma muryarta ce cike da gunjin kuka,ta kasa kunne sosai ta dingajin yadda take neman agaji da dauki,runtse idanunta tayi sai kuka ya subuce mata ta sanya hannunta ta toshe dukka kunnuwanta baccin da bata koma ba kenan. Kiran sallar farko na asuba taji an bude falonta,ta kasa kunne sai kuma taji shuru har akayi kiran sallah na biyu,ta sauko daga san gadon da idanunta wadanda sukayi luhu luhu saboda kuka,ta zira hijabinta ta flto daga dakinjiri na dibarta. 
A falon nata taga kamar mutum kwance,gabanta ya fadi da sauri ta koma da baya ta kunna makunni qwan lantarkin falon,haske ya qauraye ko ina,mukhtar ne kwance saman doguwar kujerarta tafin hannunsa dafe da goshinsa. Dauke kanta tayi tamfar ma bata ganshi ba yayin da shi kuma ya bita da ido har ta flce,sai da ta daura alwala ta dawo sannan ya tashi ya fice,tana kan abun sallarta har gari ya soma haske,sallamarsa taji yana shigowa ta runtse idanunta harya qaraso gabanta,ya fuskanci me take nufi domin yana da tabbacin mawuyaci ne idan bata jiyo qarajin fa’iza a jiya ba,saboda shi kadai yasan ta’asar da ga tafka mata da gayya. Muryarsa a tausashe da irin salon dake kwantar da hankali da ratsa sassan jikinta yace “Sumayya,kiyi haquri don Allah,wlh ban shiga dakin fa’iza a jiya don naci fuskarki ko na bata miki rai ba,kiyi haquri idan ranki ya baci,komai nayi nayi ne saboda koya mata saboda ta fice daga rayuwarmu….kiyi haqur ….. “Ya isa ya mukhtar“ ‘ta fada da sauri tana katseshi “Ka daina bani haquri,matarka ce kamar yadda nake matarka,kuma adalcin kenan” ta fada duk da tanajin daci qasan zuciyarta amma hakan ba zaya hanata fadin gaskiya ba. Hannunta ya sake kamawa sosai,kana ganin fuskarsa kasan cikin bacin rai tsantsa yake “Duk da haka nayi da na sanin kasancewa ta tare da ita,fa’iza ……. ‘ ‘ Hannunta ta dora saman bakinsa qwalla da digar mata “Matarka ce bana sonjin komai,don Allah ka tafi ya mukhtar kaji,ka tafi bacci nakeji” da gaske take fadin maganar saboda haka ya saketa ya miqe a sanyaye ya fice,tun tana kukan 
bilhaqqi har ta koma yi qasa qasa,da haka bacci ya sureta. Afirgice ta farka sakamakon hasken rana da ya dalle ta wanda ke alamta mata gari ya waye sarai,da sauri ta dubi agogo,har qarfe goma na safe,gabanta ya fadi data tuna cewa babu abinda yau tayi a gidan,a hankali ta miqe ta isa falo ta yaye labulen window dinta ta duba dakinsa,a kulle yake da muqulli tana jin mawuyaci ne idan bai fita kasuwa ba kenan,dawowa tayi uwar dakin ta tsaya gaban madubi don duba idanunta,bata so ta fita har fa’iza ga fuskanci tayi kuka ko ta fuskanci taji kishi ko ta gane abinda ya faru daren jiya 
cikin gidan har ta raina ta,hudubar anty dije ce boye duk wani abu da zai sa ta gane logonta,bare ta riqeshi ta dinga musguna mata da shi,fuskarta fayau haka ma idanun sun koma babu kumburin,saima haske da suka dada yi,hijabinta ta cire ta daura dankwali saman kanta ta fice tsakar gidan. Sai da ta kammala aikinta tas tana bakin rijiya tana diban ruwan wanka sannan taga fitowar fa’izan,ta daga kai ta dubeta,da qyar take iya tafiya tamkaryaron da aka yiwa shayi yanzu yanzu,idanun nan sun kumbura sunji jazur,hatta da fuskarta a kumbure take,da alamu ba qaramar izaya mukhtar din ya ganawa rayuwarta ba a jiyan,har qasan ranta sai da sumayyan taji ta tausaya mata,amma da baqar zuciya irinta fa’izan sai data iya samun sararin wulla mata harara tare da fadin “Baqar manufarki a kanki zata qare,anyi mai wuyar tunda yazo hannu ko,saiki saurari zuwan ‘yan dagwai dagwai” ita kanta tasan ta fada ne kawai amma ita daya tasan halin da take ciki,dariya ta qyalqyale da shi sannan tace “Wai ….. a hakan,to bamusan gaibu ba” ta juya ta waiwayenta tare da sheqa dariya ta shige daki abinta don bata ga dacewar tsayawa cacar baki da fa’izan ba,ai kuwa ba qaramin qona mata rai dariyartayi ba,sai ta dinga jin duk ta muzanta,ta dinga jin tamkar mukhtarya kwashe duka cin kashin da yayi mata darenjiya ya gayawa sumayyar,ta dingajin kamarya 
gaya mata wace ce ita,jiki a sanyaye dajan qafa ta lallaba ta dibi ruwa ta shiga bandakin. 
Bata fito ba balle ta biye mata suyi sai da ta kammala ta shiga daki sannan tayi nata wankan,tana daki tana shiryawa taji kamar motsi cikin falon ta,bata leqo ba sai data kammala shiryawar,ta fito hannunta dauke da dan kwalinta tana daurawa,fa’iza ce tsaye a falon karo na farko tunda tazo gidan,gaba daya ta shagala da kallon yadda aka tsara falon,babu qarya babu fallasa amma yayi kyau matuqa,komai a tsaftace a killace,sosai baqinciki ya rufe ta na yadda dakin Sumayya yafl nata kyau tsadar kaya tsafta da tsari bugu da qari ga yalwa dai dai gwargwado. 
“Lafiya dai ko?” Sumayya ta fada bayan ta gama kallon yadda take qarewa dakin nata kallo,juyowa tayi cikin jin kunya da bori,ba tare da ta shirya ba abinda ke zuciyarta ta fito “Hmmmm,la|lai kam,kaga masu daki,kin tatsi muntari kin gyara kanki shi yasa kikewa kowa kallon banza ko?ayi mu gani naga ta yadda za’a mora” murmushi sumayyan tayi ba tare da nuna damuwa kan batunta ba “Fadi meke tafe da ke nasan dai ba wannan ne ya kawoki ba”cikin qanqance ido fa’izan tace ” eh,ina abun karina?”ta tambaya cikin gadara,bata san cewa yau sumayyan jinta take dai dai da yadda tazo mata ba,dariyar nan ta rainin hankali tayi mata sannan ta zauna kan daya daga cikin kujerunta “To idan banda abinki fa’iza amarya wanda yayi aika aikar ma ya tsallake ya tafi don me zaki dinga haushin kaza huce kan dami a kaina,ki roqeni kawai na taimaka na baki abinda 
zaki sanyawa cikinki ko?”. Sosai ta hasala harta fara huci,ba shakka da ace da qwarinta babu abinda zai hanata neman dambacewa da sumayyan,sanin cewa babu qarf’ln sai ta buge da nuna ta da yatsa ” ke baki isa ba wallahi qaramar mara kunya,dududu nawa kike da zan nemi alfarma gunki,na fuskanci kanki ya fara rawa ko bakisan wace fa’iza ba,wallahi Sumayya ki kuka da kanki don ke abar tausayi ce nan gaba sai kin zama abarkwatancen wa wasu” “Bakinki ya sari danyan kashi jeki ki duba kitchen ki dauki da’amin tunda duka don shi kike 
wannan dai ko?” Ta fada tana miqewa tayi komawarta uwar dakanta,nan ta barta tana hauka sannan daga bisani ta fice,abu goma da ashirin ga wani baqinciki da ta taras,dakin sumayyan ya kere nata da take taqama da shi,kuma tana da zaton cewa dagajikin mukhtar din ta yaga,tana jin dole ta dau mataki Kafin zuwan yaran da zasu zama silar zamantowar gidan mallakinta. Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page