RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 7

RIKICIN WANI GIDA


CHAPTER 7Sun gama exams qarfe 12 suka dawo gida, Maysah ta shiga wanka, taci abinci, ta fito da sauri tana yana gyalenta na afta dress, ta kalli mamarta tace Amma naje gurin tsoho, cikin hausarta, akwai dambun name a kitchen ki kai mishi, da sauri ta shiga kichin ta dauko, ta nufa Sassan tsoho.Ta shiga dakin da Sallama, aka amsa ta, ba shi kadai ke dakin ba su biyu ne. tace tsohona ina wuni ya ce cikin sake fuska, Ruma kina lfy? Ya exams? Lafiya Alhamdulilahi, ta kalli wanda suke tsaye tare tace Yazayyad ina wuni yace lfy lau Ruma tayi murmushi, Tsoho yace ki diba bedside na nan tun da safe babanki ya kawo man newspaper nace sai kin dawo zaki karanta man, ta miqe cikin yanayinta ta nufi dakin Tsoho, Zayyad ya bita da ido, ta dauko jaridar ta matso da sofa ta zauna ta shiga karanta mai newspapern nan cikin qwarewa da muryar ta mai dadi. Lumshe ido zayyad keyi sakamakkon jin muryar ta dake ratsa jinin jikinshi cikin kwanyar kansa.Nan take zuciyarsa ta kamu da son Rumaysah, duniyar tunani ya fada, ba tare da sanin ta gama harta shiga dakin Tsoho don dauko mashi magungunanshi,ba Tsoho sai magana yake mai amma inaa hankalinshi baya gareshi, Tsoho yace Kaii Zayyadu,firgigit ya dawo hankalinsa, Naam tsoho, lafyan ka? Yace wlh tsoho Rumaysah ce, me tayi? Yace ba tayi komai ba, Amma wlh na kamu da sonta farat daya, Tsoho ya danyi jimm kafin yace amma kasan dai ba a soyayyah a gidan nan k0? Nike da ikon zabar ma kowannen ku mata, Zayyad yace Tsoho, Ba wai nace ka bani Rumaysah a matsayin mata bane, nidai ina gaya maka ne na kamu da sonta, duk wacce ka zaba mun zan maka biyayya don na san kai Adali ne, ba zaka zabar mana abunda zai cutar damu ba, jikin Tsoho yayi Sanyi, Zayyad ya daure shi da jijiyoyin jlkinshi. Ya daure yace Allah yasa mu dace, Zayyad yace Amin, Maysah ta gama jin zancen Tsoho da Zayyad jikinta ya fara rawa. Kanta a qasa ta shigo parlom tace tsoho bari na koma Sassan mu, yace Rumah daga zuwanki? Ko don kin ganni da wani ne kike kishi? Tayi murmushi tace Aa zan daije na dan duba karatu ne, muna da exams gobe. Yace toh Rumahna Sai da safe. Ta wuce da sauri, Zayyad ya bi bayanta shiko tsoho ido ya rakasu dashi. .ji tayi ana Maysah Maysah, ta tsaya tare da juyowa, Zayyad ne nan jikinta ya soma rawa, Yace Rumaysah bansan yadda zaki dauki maganar nan ba, tunda nake a rayuwata ban taba son wata mace da sunan soyayyah ba, burina na samu na kaina, najira tsoho ya zaba mun mata, nikuma zan sota, muyi zaman aure, amma kuma sai na kamu da sonki tun ranar da muka dawo, na bar abun a raina don kar na zurfafa a sonki kuma a zaba mun matar da bake ba, a yau kuma na ga bazan iyajurewa ba har sai dana fada ma tsoho sirrin dake raina, kuma a ganina ya bani damar sonki don bece kar na soki ba, Maysah ina soki ki bani damar nuna miki son da nake miki, i love u rumaysa’u,jikinta yai sanyi qalaw ta rasa wane yanayi take ciki, bata taba soyayyah ba, amma haka kawai taji Yazayyad ya mata kuma da alamu Tsoho ya amince musu, Bakyasona Ko Maysah? Ta gyada kai Alamar Aa, yace kina sona? Ta daga kai cikin kunya, ya saki ihun murna yace i prmis u wont regret dis…
Cikin Kwana 14 Soyayyah me qarfi ya shiga tsakanin Mu’ammar da Haneefa, Jawad da Bilkisu, Suraj da Fadila, Samir da Islahulkhair, Rumay’sah da Zayyad. Tsoho na sane da su duka, ya dai zuba musu ido ne, ni ko biebee nace tunda sun daidaita kansu ai sai ayi.. Sun gama Jarabawa Lafiya, Tsoho ya hada musu gagarumin Walimar kammalla karatun Sakandire, ko waccensu taci kwalliya, aka gabatar da Walima cikin murna tsoho yaba ko waccensu Kyautar Mota, tare da check din dubu 50, Daga baya kuma a kaci aka sha… Suna zazzaune tun daga matan Tsoho zuwa yaranshi dajikoki, Naima (Amira)tace Tsoho yaushe zaka zaba mana mazajen aurene? Ni fa na qagara nayi auren nan naji abin da akeji, Dukansu sukaji maganar bambaraqwai kunya ta lulube su duka, barin ma babanta baba usman daya daburce dan kunya, haka Amira take, wani lokacin idan tayi magana ji yake
kamar ya nitse, ya rasa me ke damun Amira, gashi ita kadai ce diyarshi, tsoho ya rasa me zaice mata? Haneefa tace kefa banza ce jaka kawai mara hankali, Suraj ya kasa hqr cikin bacin rai yace ke meye haka kike zaginta? Amira bata girmeki ba? Hajia babba ta chafe tace ai naga girmanta kawai tayi ba haihuwana ba, kuma kai meye naka? Ka bari yan,uwanta na jini suyi mata fada ba kai ba jikan mayyu da aljannu, zai yi magana Umma hajja tace Surajj ya isa, dukjikan umma hajja da Hajia Ama sunji wannan zagin, iyayensu sun saba dajin zagin da ake ma mahaifansu shisa abun ya dena damunsu. Amira ta buga tsaki tace Haneefa kinsan ina tausayinki, don wlh na fara jibgarki garada 10 ba zasu iya kwatarki ba, dan kinsan qarfi ne dani kamar shari’ah… Bilkis tama hanifa rada tace kinsan dai bata da hankali ko? Ta fara jibgarki wlh bame iya kwatanki. Tsoho shine kayi shiru k0? Yaushe zaka zaba mana mijin aure? Tsoho ya daure yace Amira aure kike so? Tace Eh tsoho, duk aka juyo ana kallonta ita ko ko a jikinta. Yace kar ki damu da Zaidu ya dawo za a sanar da kowa
madafarshi, tayi shewa yauwa tsoho ni Yazayd din ma nakeso.. ZAYD kuma??

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page