FARHA CHAPTER 22 THEND KARSHE

FARHA

CHAPTER 22 THEND
KARSHE


Ajiyar numfashi yayi yace “to shikenan naji Allah ya yafe mana baki daya stop crying please” murmushi tayi tayi kissing qirjinsa tace “yawwa adalin Sarki mijin Queen Farha baban Abdallah da….” kallon da yake binta dashine yasata hadiye mgnr ta shige jikinsa tana dariya shima dariyar yakeyi ya jata suka fita suka nufi bangaren Hajiya Fulani shima bangaren cike yake da yan gaisuwa a daki suka tararda Hajiyan suka zauna suka qara gaisawa ta kalli Farha tace “yanzu Amnah tabar nan tace taje ta nemi gafararki kin yafe mata harma kinyi mata kyauta amma tace mijinki yaqi tsayawa ya saurareta ko kallonta bayason yi qarshe ma daki ya shige ya barku”
Murmushi Farha tayi ta ruqo hanunsa tace “ai yanzu yace ya yafe mata ko Hearty?” kawar dakai yayi tare dayin tsaki yace “don Allah ku daina tunamin da wannan matar wlh duk sanda naji abinda ya shafeta zuciya ta tafasa takeyi” murmushi Hajiya tayi tace “dadina dakai Hafeez baka yafiya ita rayuwa hqr akeyi kuma mahaqurci shine mawadacin gobe yanzu sudin da suka cutardamu wacce riba suka tsinta banda tabewa da tarin nadama Hafeez ita rayuwa sai an cutar dakai ake baka hqr kuma idan kayi hqrn me zaka ragu dashi?”
Qasa yayi da kansa ya share hawaye da sauri Farha ta matsa jikinsa sosai tace “don Allah kayi hqr kada kayimin asarar hawayen ka please” kansa ya dora saman kafadarta yace “na godewa Allah daya azurtani da mar’atussaliha wadda takeso na take burin ganin rayuwata ta inganta uwaryayana Ina alfahari dake Farhanah wlh duk abinda kika buqata a duniya zanyi miki shi koma mene saboda haka na yafewa Hajiya Sogiji da Amnah kinji” rungume shi tayi qam ajikinta tana dariya Hajiyan ma dariya tayi tace “Alhmdllh naji dadi sosai Allah yayi muku albarka da zuri’ar ku baki daya”janye jikinta tayi daga nasa ta koma ta zauna kusa da Hajiyan tace “yawwa saura abu na gaba Abban Sarki inason taimakawa Amnah ta hanyar dorata akan magungunan da zata rinqa sha saboda rage mata radadin ciwon da take ciki sannan inason idan babu damuwa zan biya ayi mata surgery na hanunta da qafarta” wani kallo yake mata na tantamar hankalinta” tsugunawa tayi a gabansa duk da nauyin cikinjlkinta tace “na roqeka badan itaba kuma badan niba kada ka hanani wannan aikin ladan da zanyi Abban Sarki bansani ba ko wannan abin shine zai zama sanadin shigarmu aljanna plz kaji”
Duk ta gama daureshi da jijiyoyinjikinsa kada mata kai kawai yayi yace “Allah ya bada sa’a” yana fadin haka ya miqe ya fita tabisa da kallo ‘tana murmushi itama Hajiya murmushin tayi sukaci gaba da hirarsa har dare yayi sosai sannan ya shigo suka tafi suka kwanta. Kwanci tashi cikin Farha ya isa haihuwa cikin dare naquda ta kamata ta tashi ta zauna ciwon kamar wasa ya fara mata tun tana daurewa batason tashinsa har saida takai ga ya farajin nishinta ya tashi da sauri ya ganta durqushe a qasa tana‘a salati da amba‘on sunan kanta takeyi tana cije lebanta gabadaya ya diririce ya rasa abinyi fita yayi da sauri ya kira Jakadiyya kam su dawo har kan babyn ya fito qarasawa yayi da gudu yasa hannunsa ya zaro baby girl din Jakadiyya ta miqa masa towel ya nadeta ya miqa mata ita ya sake komawa gurin Farhan ya fara danna mata cikinta jini ya rinqabin “ta.
Juyawa yayi ya nufl wata qofa a parlourn ya bude ya shiga ya dauko wasu allurai da magunguna da ya dawo lkcn har Jakadiyya ta taimaka mata ta miqe yana zuwa ya rungume ta a jikinsa yayi mata alluran yanata zuba mata sannu Jakadiyya ce ta shiga bathroom ta hada mata ruwan zafl ta taimaka mata ta shiga shi kuma ya gyara gurin sannan ya koma ya dauki Babyn da ta fara kuka ya bude fuskarta ya zuba mata ido yana murmushin farin ciki tare da godewa Allah da wannan kyakkyawar kyauta da yayi masa yarinyar da mamanta take kama dara daran idanunta ne kawai nasa ba kamarsarki ba da komai nasa na mahaifinsa ne rungume ta yayi yace ya Allah” waya ya dauka ya fara daukar hoton yarinyar ya bude data ya turawa Sarki ya koyi sa’a yana online dake su can be dare bane hoton yana shiga kiran Sarki ya shigo wayarsa da zumudi ya daga yace “Hello My Son kaga hoton qanwarka ko? Yanzun nan Momyn ka ta haifa mana ita” ihun murna ya saki yace “Oh My God Dad naso ace nine zan fara ganin yar’uwata Dad Ina cikin farin ciki da kuka samamin yar‘uwa na gde Dad” murmushi yayi yace “amma Momynka tayi mana wayo bata kama damu da ita take kama” daidai lkcn ta fito daga wankan ya zuba mata ido sunata shirmensu da dansa har Jakadiyya ta taimaka mata tasa kayanta.
Komawa tayi ta kwanta ya miqa mata wayar tayi kamar bazata karba ba saboda tasan shirme ne da surutu zai cikata dashi daqyarta karbi wayar tana karawa a kunnenta yace “Momy kinsha wahala ko sannu nasan baby ta wahalar dake amma ni ban wahalardake hakaba ko?” Haushine yasata hadiye takaici tace “ban sani dan qaniyarka tambayi abokin naka yafini sani“ dariya yasa yace “kayy Momy duk wahalar ce tasaki daukar zafi haka?” Takaici ne yasata kashe wayar ta ajiye shima dariyar yakeyi mata ya dauko wayarsa ya rinqa turawa mutane sanarwar haihuwar bai Kira su Hajiya ya fada musu ba ya koma ya kwanta ita da yarta ne sukayi bacci amma shi baiyi baccin ba ko kadan. Saida safe labarin haihuwarya cika gdan sarautar su Hajiya sune suka fara zuwa sukaga yarinya Masha Allah har an shiryata uwarta ma ta shirya tsaf suka rinqa daukan hotuna ana bazawa a duniya a ranar Momyn Kaduna sukazo da Maryam Momy itace take kula da maijego Farha saboda cewa tayi wannan aikinta ne zamanta tayi a Bauchi take kula da yarta Farha da jikarta ana gobe suna Prince Abdallah ya diro 9ja babu wanda yasan da zuwansa saida sukaji gdan ya dauki hayaniyar ga Prince ga Yariman Bauchi yana shigowa ya wucce bangaran Momynsa lkcn tana wanka ya dauki Babyn yana kallonta yanajin qaunarta da tausayin kansa shekara goma sha takwas sannan akayi masa qanwa bude ido Babyn tayi tana kallonsa yayi dariya harda ihunsa yace “Hajiya ta ganeni wlh tasan nine yayanta kinga yanda take kallo na lahhh Hajiya wlh ta sanni wayyoh Allah dadi…” ’
Ranqwashin da yaji an zuba masa ne yasashi dagowa yana ganin Momyn tasu yayi dariya yace “Momy kin qara kyau kamaryar babe gsky Dad na ya iya kiwo” bakinsa ta kaiwa duka ya kauce yana dariya zama tayi tace “meye ya kawoka yanzun sarkin surutu” dariya yayi yace “dadin abin Dad na yace ke na gado a surutu yace ma surutunki shine ya fara birgeshi yawwa gama Dad nan Dad ai haka kace ko?”ya fada yana kallon King Hafeez din da yake shigowa dakin, murmushi yayi yace “wato bakaji ba dana hanaka tahowa shine ka shammaceni ka taho k0?” shafa kansa yayi yace “Am sorry Dad wlh na kasa jurewa inason ganin little sister na shiyasa kawai na taho” bai kuma y masa mgn ba ya matsa gurin Farha yace “Queen ya jikin yanzu meke miki ciwo?” Yatsina fuska tayi tace “jiki yayi sauqi sai kaina da kunne na da yakemin ciwo kuma ba komaine ya kawo hakan ba sai surutunka kaida danka“ dariya sukayi Momy dake shigowa tace “wlh ran uba da da zai baci idan basu fice sun qyalemin yata ta huta ba” juyawa King Hafeez yayi yana cewa “aa niba baqon zafi bane za,a nemi har makwanci na” shima Sarki miqewa yayi da Babyn a hanunsa zai fita Momy tace “kai saholami bani yarinyar nan kada kaje kaji mata ciwo” juyowa yayi idanunsa cike da qwallah yace “yanzu Momy duk girmana na rasa wa zan jiwa ciwo sai wannan tatsitsiyar yar nidai kawai na fahimci kun daina sona ne saboda kunyi sabuwa” ficewa yayi batare da yabada Babyn ba ya shige dakinsa ya kwantar da Babyn ya shiga wanka. Ranar suna akasha bidiri gdan sarauta ya cika ya tumbatsa kowa kagani fuskarsa cike da farin ciki kowa yasan ya halarci sunan Princess Khadijah Hafeez Hambali a wannan satin hotunan iyalan hudu sune kawai suke kara kaina a duniyar yanar gizo King Hafeez Queen Farha Prince Abdallah da yar jaririya Princess Khadijah.
Momyn Kaduna ba qaramin dadin wannan halacci taji ba na sawa yarsu sunanta da sukayi aikuwa bata bar gdan ba saida Princess tayi sati hudu a duniya ranar da zata tafi taga abu kayan da aka rinqa lodawa a motar da zata kaita gda abin har tsoro ya bata ta rinqa yi musu fada akan kayan saidai suyi dariya kawai bayan taflyarta da kwana biyu King Hafeez ya tusa Prince Abdallah a gaba ya mayar dashi Rasha gda ya rage daga Farha sai Princess Khadijah, satin King Hafeez biyu ya dawo lkcn maijego Farha tagama tsumuwa da magungunan da Momyn Kaduna ta kawo mata aikuwa yana dawowa ya fara janta jikinsa tana zuqewa da dare dakinta ta shiga tayi kwanciyarta Princess na gabanta tana feeding dinta da haka bacci ya kwashe ta kasa hqr yayi ya tashi ya nufo dakin ya bude ya shiga tana kwance ko hasken dakin bata kashe ba tayi daidai daga ita sai wata qaramar riga iya cinyarta blue gashinta ya baje saman pillow din fuskarta kamarwadda take murmushi ya jima yana kallonta feeling dinta yana qara bijiro masa tayi wani bala’in kyau ta qara haske ga wata cika data qara duk saita canza masa kamar ba Farhan saba a hankali ya rinqa matsawa harya isa gaban gadon ya dauke Princess a hankali yasata a gadonta sannan ya koma ya kashe sweech din ya dawo ya haye gadon yasa bakinsa ya kama nonon da ta fito dashi take bawa Princess firgita tayi ta bude idonta jin salon shan nonon ya banbanta hanunsa yakai ya kunna lamp din sukayi ido hudu ta saki ajiyar zuciya tasan ko tayi yunqurin hanashi ma ba bari zaiyi ba tunda ya riga ya ritsata hakanan ta sake masa jiki saboda itamma tayi missing dinsa sosai aikuwa taji jiki don ya nuna mata da gaske yayi missing dinta daqyar ta qwaci kanta sukayi bacci.
Sannu sannu lkcn yaketa turawa rayuwar gdan King Hafeez mai dadi abar sha’awa ga kowa suna zaune cikin so da kulawa da tattalin junansu yaransu biyu wanda dagasu Allah bai qara basu haihuwa ba harma sun fidda rai suna rainon wadanda AlIah ya basu shekarar Prince Abdallah 26 ya gama hada karatunsa inda ya tattago aure iyayensu basu jaba da yake abin duka na gdane yarinyar aminin mahaifinsa Nasir yakeso Zahrah aikuwa cikin qanqanin lkc King Hafeez ya nema masa aiki ya samu a Abuja akasha shagalin biki amarya ta tare a gdanta dake Abuja.
Abin al’ajabi kuma a wannan lkcn ne Queen Farha ta fuskacin tanada shigar ciki taso zubar dashi saboda ita a ganinta abin kunya ne danta yayi aure kuma ace tana haihuwa amma kafin ta zubar King Hafeez ya farga aikuwa ya taka mata birki dole ta hqr ta qyaleshi har ya isa haihuwa babu wanda ya fahimta saboda shima King Hafeez kwabarsa tayi akan idan ya fadawa wani saita zubar dole ya kulle bakinsa tun saura wata biyu ta haihu ta tafi England daga lkc zuwa lkc yake zuwa ganota Allah ya taimaka ranar da zata haihu ranar ya dira a qasar England yana zuwa suka tafi asibiti cikin ikon Allah ta haifo yaranta biyu mace da namiji murna gurin King Hafeez ba,a cewa komai har sujjudusshukur yayima ubangiji tun a asibitin ta tubure masa akan cewa to itakam ta hqr da haihuwa ta barwa yayanta yaso ya bijire ta rinqa yimasa kuka tana cewa “yanzu Mai martaba bazaka tausayamin ba kai ko kunya bakaji munada suruka ace muna haihuwa gsky ni bazan iya wannan abin kunyar ba Badan yanaso ba ya qyaleta aka daure mata mahaifar kwanaki uku tsakani suka nufo 9ja tun daga wajan tarosu akayita mamaki shine yaketa washe baki da macen a hannunsa har suka isa gda Hajiya Kilishi da Hajiya fulani sukayita yi musu fadan boye samun cikin da sukayi shidai kallonta yakeyi inda taketa sharar hawaye tace “Allah Hajiya kunya naji matar Sarki taji inada ciki”
Dariya sukayi sukace “sakarcin banza to ai yanzu taji kin haihu ko?” kuka ta kuma rushewa dashi mamaki ya cika su Hajiya shikuwa da ransa ya baci tashi yayi ya fara fada yana cewa “to tunda haihuwar ce bakyaso abin kunyace ki kashesu gasunan a gaban Farhanah bayan takaicin da kika qunsamin na sawa a daure miki mahaifa hakan bai isheki ba sai kin qaramin dana kuka to ga yarannan ai ki mayar dasu inda suka fito tunda kinfi Allah iyawa shida ya bamu bai iyaba…” muryarsa ce ta fara rawa saboda kukan da yake qoqarin kwace nasa dole ya juya ya fice daga dakin, duk sai taji bataji dadi ba Istigifari ta farayi saboda sabon datayi share Mata hawayen Hajiya Kilishi tayi tace “maza jeki lallashi mijinki naga yadau fushi da yawa” komawa tayi ta kwanta kawai ta shareshi tasan zai kawo kansa amma sai taji shiru har dare har safe bai shigo ba Saida ya tashi daga zaman fada taji bazata iya jurewa ba ta nufi part dinsa lkcn ya fito daga wanka budewa tayi ta shiga tare da sallamarta. A ciki ya amsa mata ta tsaya tana jiran taji yayi mgn amma shiru hakanne ya qara sanyaya mata gwiwa taja qafarta a hankali ta matsa gabansa ta tsugunna ta riqe qafarsa me cike da suma tace “Don Allah kayi hqr Abban Sarki ka yafemin bana iya jure fushinka baka sabarmin ba Abban Sarki a zamana dakai tsayin 27 years baka tabayin fushin yini guda dani ba meyasa yanzu zakayi ka fahimceni wlh badon na bata maka rai na fadi hakan …… sai kuma tayi shiru ta sake fashewa da kuka jikinsa ne yayi sanyi ya dagota ya mannata da qirjinsa zuciyarsa na bugawa da qarfi yace “shikenan ya wucce amma kada ki qara Queen hakan sai yake gwadamin kamardanine bakyason haihuw ….. ‘ ‘ Bakinta ta manna saman nashi tana girgiza masa kai saida ta tsotsa sosai sannan ta saki tana ajiyar zuciya tace “sabone wannan Hafeez wana sani a duniya bayan kai bansan kowanne namiji ba saikai kadai tun bansan kaina ba nake tare dakai 15 years aka aura maka ni kuma a lkcn ka sanar dani dadinka ka koyardani soyayyarka me mantarda zuciya kowa da komi wlh duk duniya babu abinda nakeso sama dakai uban yayana ko lkcn dana samu gushewar tunani a zahiri amma a badini zuciyata bata manta dakai ba saboda kaine ka fara budeta kaine kake da mukullinta a hannunka wlh indai wannan ne zaisa ka yarda inasonka to na shirya komawa England a budemin mahaifata nayita zazzaga maka yaya harsai kace ka gaji da kanka kaji mijina”
Wani dadi yakeji a ransa yana gdy ga Allah tabbas Farhanah dabance a cikin matan duniya shi yana tunanin ma itadin hurul’aynee ce bata cikin jinsin matan duniya kawai dai rabon ta kasance farin cikinsa ne yasa aka halicceta a duniya.
Da wannan tunanin sukaji ana taba bell din dakin ya janyejikinsa daga nata yayi peaking goshinta ya dauki doguwar riga ya zura ya nufi qofar Princess Khadijah ce tayi wani tsalle ta rungumeshi shiko Abdallah ya shige ciki ya rungume Momyn su yace “wlh Momy kin iya bada surprise kawai bamu zataba kika bamu twins nama rasa irin murnar da zanyi Momy mun gode da kuka qaramu daga biyu muka zama hudu muna alfahari daku iyayenmu” Ajiyar zuciya sukayi Zahrah matar Abdallah ta shigo ita da Jalal qaninta dauke da twins din tsugunawa tayi zata gaishe da Farha tayi saurin dagota tace “karki soma ni Momynku ce banason surukuta kinji yata” daga mata kai tayi suka rungumejuna nan fah sukayita hotuna harda su Hajiya.
Bayan komai ya Iafa ne Princess Khadijah ta kalli iyayen nasu tace “Dad nifa na zabama twins suna Baby Sunanta Zainab sunan wannan tsohuwarta nuna Hajiya Kilishi ta kalli namijin tace wannan kuma sunansa Usman sunan Baffan Momy da kuma Daddyn Kaduna kaga shikenan an raba ko ke kuma tsohuwa fulani kiyi hqr idan Momy tayi mana auta zamusa mata sunanki Fatima” kabbara suka dauka King Hafeez yace “kamar kin shiga
zuciyata Princess dadina dake kinsan abinda ya dace” turo baki gaba Abdallah yayi yace “to ni kuma da bansan abinda ya dace ba na zaba musu Niknames Ya’eesh da Ya’eeshah” murmushi sukayi sukace Fine zance ya qare Allah yayi muku albarka ya hade kanku amsawa sukayi da amin Jalal ya numfasa yace “yawwa Dad zan taimakawa wannan qwailar na aureta don da wannan rawar kan nata idan bani din ba babu me kwasarta taje tanayi masa miya da Suger” ya nuna Princess Khadijah turo baki tayi ta dauki tumtum ta bishi dashi ya tashi suka fara zagaya dakin dariya kowa dake gurin ya dauka Queen Farha tace “lahhhh games of love nikam na amince da wannan taimako naka Jalal zan biya sadaki ” King Hafeez ne yace “nikuma zan hada lefe” Zahrah tace “wlh zan taimaka da kama event center” kallon Abdallah King Hafeez yayi yace “kaikuma Yaya na qotalo meye taimakonka?” Shafa sumarsa yayi yace “zan taimaka da ruwan gashi cikin dirom don na tabbatajiki zaiyi tsami” dariya suka kuma kwashewa da ita itadai Princess Khadijah kunyace tasata komawa jikin Hajiya Kilishi ta lafe, Hajiya tace “kai kunci gdanku ai qare wasan ku tashi maza kuje kuyi alwalar magrib kai ka dauki matarka ku tafi gdanku kun cikamin qawa da karadi babban kwabo“kawai saida sukayi addu’a sannan suka tashi suka fice.

‘~Tammat bi hamdullah~‘

Nan na kawo qarshen wannan littafi nawa wanda wani bangare na cikinsa ya faru a gaske mu hadu a sabo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page