GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 37

GIMBIYA SA,ADIYYAH

CHAPTER 37


Tsananin faduwar gaba yasa Kursiyya ta kasa ko da motsi ne. Ita kanta warin kanta takeji. Sosai take kyamar kanta, kawai dai bata da yadda za ta yine.
Tana cikin haka taji motsi ana kusanto dakinta. Da sauri ta juya akalar kallonta zuwa ga bakin kofa. Taga mai martaba tafe da waziri da Khalili, dukkansu hankalinsu a tashe.
Ganin ta da suka yi yasa dukkansu suka yi tsaye, idanuwansu bude cike da mamaki. Da azama mai martaba ya tako zuwa inda take. Da warin da komai ya tsugunna a gabanta.
“Kursiyya ina kika shiga kika sa hankalinmu ya tashi? Ina kikaje tun dazu an bazama neman ki amma ba a gan ki ba?”
Shafya ma manta da bata iya magana. Sai bin shi da kallo kawai da take yi, idanuwan nan
nata sun yi wasu iri da gani an san ta sha azaba.
“Yanzu haka Zabbau na can dakin horo ana hora ta saboda rashin ganin ki. Khalili, maza a
je a dakatar, da ita a sake ta da gaggawa.”
Yunkurin magana Kursiyya ta hau yi amma ta kasa. Ta hau gyada kanta da sakakken baki, sai ga hawaye sharr yana sauka a bisa kumcinta. Yawun daya cika bakinta ne ya hau dalalowa waje, sai ga wannan mugun warin ya daki hancinansu. Da sauri kuwa Waziri dake wurin tsaye ya fice Yanajin yadda Maimartaba ke kwala kiranshi amma bai ko waiwayo ba. Don shi kam ji yake tamkar zai yi amai. Jim kadan saiga Khalili biye da shi Zabbau ce data gama dimaucewa duk ta galabaita tamkar ba ita ba. Da gudunta ta iso gaban Kursiyya. Cikin kuka tace, “Ranki shi dade ina ta kaiki? Rashinki yajawo mini bala’i. Na sha azaba kala-kala wai lallai sai na fadi inda na kaiki. Naji dadi da kika dawo. Don Allah ki shaida musu cewa bani bace ba.”
Kursiyya ta hau kakari tamkarza tayi arnai. Azaba takeji sosai wacce bata tabajin irinta ba.
“Wace ce ita? Wace kike magana a kanta Zabba’u? A ina ta kai ku? Kiyi mini bayani yadda
zan gane. Kursiyya bata iya magana.”
Zabba’u sai ta samu kanta da kasa cewa komai. Ba ta san ta inda zata fara labarta musu
komai ba. Hakan yasa ta fara inda-inda tana daddafe bakinta da hannu. “Kiyi magana mana Zabba’u. Watakila idan kika magantu mu samo maslaha ta nan.”
Zabba’u tayi shiru bata iya cewa komai ba. Kursiyya sai gyaran murya take tana kallon ta,
alamun kar ta tona musu asiri. “Khalili wai yanzu mene ne abun yi? Ni kam baki daya kaina ya kulle. Na rasa ta inda zan bullo ma lamarin nan. Ban san ta yaya za a fara nema mata magani ba. Da alama ba ciwon asibiti ba ne ballantana muje can.”
Khalili da ke dode da hancinshi yace “Ni a gani na ranka ya dade, daurewa za ayi a kai ta wurin Mallam Khamis Ciro. Shi kadai ne muke da hope a kansa, saboda ya san abin da yakeyi. Yana da ilimi sosai…”
Bai kai aya ba Sarki Sani ya tari nunfashinshi. “A gabanka, kai kazo da Mallam Khamis Ciro da kyar, ka san abin da ya faru sadda yazo din. Kana tunanin za a sake kiranshi ne yazo? Ba zaizo ba Khalili. Na rasa wace irin rashinjituwa ce a tsakaninsa da Fulani da haryanzu ba
su shiri sam. K0 ina ga tun abin da ya taba faruwa ne ya gaza wucewa a tsakaninsu?”
“Tun shi din ne ranka ya dade. Saboda sadda naje ma abin daya fada mini kenan. Amma dai duk da haka daurewa za a yi a koma wurinshi din. Kawai a dauke ta a yadda take, ita da Zabba’un duk mu tafi tare. ldan ya ga an tafi dasu na tabbata ba zai kiyi musu aiki ba.”
Kursiyya na jin haka ta hau gyada kanta alamun ba taso. Ran mai martaba ya fara baci amma sai ya daure bai nunar mata ba. Yace “Haba Kursiyya. Yanzu idan ba a kai ki wurin Malamin nan ba ina kike tsammanin za a iya zuwa a dace? Dole sai kin cire wannan kiyayyar, ki bari ya miki aiki ko za a dace.” ‘ Duk wannan maganar bata sa Kursiyya ta daina gyada kanta ba.
A cikin wannan halin suka farajiyo taku mai cike da ban tsoro. Da sauri mai martaba ya hau waige-waigen ta inda zai jiyo takun amma sai bai ga komai ba. Ga shi kuma takun sai kara kusanto su yake yi. Sai aka saki kara mai karfi, a take iska mai hade da guguwa ta taso a cikin dakin.
Kursiyya da Zabba’u suna farajiyo haka sai gabansu ya fadi, don jikinsu ya basu ko mene ne.
Jikin mai martaba sai karkarwa yake yi saboda yadda al’amarin yake faruwa dole komai karfin halin mutum sai ya tsorata. Guguwarta cibre wuri guda ta koma fatalwar Sa,adiyya. A gaban mai martaba ta nemi muhalli ta zauna. Yana hada ido da ita sau guda ya kauda kanshi cike da tsoro, banda salati da ambatan sunan Allah babu abin da yake yi.
Kafin komai ya sake faruwa suka ji an banko kofa. Waziri ne a gaba sai Mallam Ciro biye da shi, hannunshi rike da wata jaka, fuskarshi cike da annuri. Waziri ya tura kofar ya datse sannan yabi bayan Mallam Ciro, ba tare da dukkansu sun ga fatalwar Sa,adiyya dake gefe kusa da mai martaba ba. Wani irin sanyin dadi yaji a lokacin da yayi ido hudu da Mallam Ciro. Kamar yasan cewa a yanzu yake da bukatan ganinshi. Tsoron fatalwar yake yi, duk da cewa har yanzu bai gasgata ko mene ne ba.
Ya tashi da gaggawa ya koma kusa da Mallam Ciro yana tattaba shi yana gwada mishi Saadiyya. Malamin yayi mamaki kwarai da ya hada ido da ita kuma ba tare da komai ba. Shi fa koda mutum mai aljannu yayi ido biyu dole ya shiga taitayinsa. To balle kuma aljanin karon kanshi. Amma abun mamaki gashi ga aljana sam ba ta damuba, bata tsorata ba ko kadan.
Hakan yasa ya tashi ya nufi inda take. Jakarshi ya bude ya fito da wata gora, ya zuba ruwan kadan a tafin hannunshi ya watsa ma fatalwar, amma abun mamaki k0 gezau. Ya sake diba har sau biyu yana watsa mata babu abinda ya faru.
Sai ya fara tsorata, ya koma bakin gado ya zauna tare da zuba wa sarautar Allah ido.
Da karfi Sa,adiyya ta fasa wata irin karar, kuka mai hade da dariya. Atake idanuwanta suka
hau zubarda hawayen jini. Dararren bakinta na fitar da hayaki sosai.
Sai a sannan Mallam ya sauke ajiyar zuciya. Ruwan daya yayyafa mata ne yayi aiki. Sai dai abin daya bashi mamaki sosai shine bai taba ganin irin haka ta faru ba sai yanzu. Wannan ya kara tabbatar mishi da cewa ba aljana bace ba a gabanshi. Wata dai halittar ce ta daban “Naji dadin wannan haduwar da aka yi.” Sa,adiyya ta furta cikin gwarancin maganarta. Duk suka daga kai suka kalle ta har Kursiyya
dajikinta keta faman karkarwa. “Wace ce ke? Kuma me kika zoyi?” Mallam Ciro ya fada idanuwanshi kyam a kanta.
“Zan so ku saurare ni sosai, ku daure ma duk abin da kunnuwanku zasu jiye muku. Ni sunana Halimatus-Sa,adiyya. Gimbiya Sa,adiyya kamar yadda mahaifina, mai martaba Sarkin Sani, Sarkin Bilbah ya laka min.” 
Ido bude Sarki Sani ya mike tsaye yana kallon ta. “Karya kike yi, ni diyata Gimbiya Sa,adiyya tajima da rasuwa, shekara goma sha biyar kenan da rasuwarta. Ki fada mana gaskiyar k0 
ke wace ce. Ki fada mana abin da kika zo nema a wurinmu…” 
Mallam Ciro ya dakatar dashi da hannu. “Kar kayi saurin yanke hukunci Mai martaba. Ka bari har mu ji abin da take tafe da shi tukunna. ldan har karya ta mana ni zan gane. Ni kuma zan daukar mata hukunci da kaina.” Ya juyo ga Saadiyya hade da fadin “Ci gaba muna sauraren ki.” 
Ta saki wani irin gumji mai kama da kukan zaki. Sannan taci gaba da magana. “Ni fatalwace, ba mutum ba ba kuma aljana ba. Abba…” 
Ta juya ga Sarki Sani tana kallon shi. “Wannan munafukar matar ita ta raba ni da rayuwata. Itace ta rabani da kai. lta ce azzalunar da ta rabani da ruhina da gangarjikina. Aka saka ni cikin kwalbar sihiri, na dauki tsawon shekara goma sha biyar a cikinta.” 
Har a wannan lokacin mai martaba bai zauna ba. Ya gaza gasgata abin da kunnuwanshi sukejiye mishi, ya gaza gasgata abin da idanuwanshi suke gane mishi. Sai tsananin mamaki da al’ajabin wannan abun yakeyi. Kursiyya kam gumza kawai take yi, da zarar ta yi attempting yin magana sai azaba ta ishe ta a makoshi don dolenta ta yi shiru. 
Saadiyya taci gaba da cewa “Ta yaudare ni a lokacin aurena. Ta nunar maka da tana kaunar aurena da Yerima Abu Sufyan, sai dai daga ni har kai bamu sani ba cewa wani makirci da tuggon take da shirin shirya mana. Ta yaudare ni ta kai ni gidan wani matsafln mutumi, kasurgumin boka. Tun daga nan ban kuma sanin komai ba. Ban kuma sanin abin da yake faruwa ba sai dai na wayi gari naji ya fitO dani daga cikin kwalbar sihirin daya saka ni tsawon shekaru goma sha biyar. Ya fiddo nine ba don komai ba sai fansa da yake so ‘In daukar ma kaina, sannan kuma in daukar mishi a wurin muguwar matar nan Kursiyya. Ya tattara mini duk wani karfinshi har ma dana zobenshi, ga shi nan a hannuna. Yace da ni inyi duk abin daya dace harsai ta fadi inda ta kai min mahaifiyata. Saboda duk a kanta ne 
suka sami matsala shi da ita. Duk gana musu azabar nan da nakeyi ita da Zabba‘u haryanzu sun gaza su tuba. Sunki su tsorata su fada mini inda suka kai min mahaifiyata. Boka Fartsi ya tabbatar min cewa tana 
nan raye, sai dai sun mayar da ita tamkar ba mutum ba. Sannan an katange ta daga ganin shi. 
Ina so ku sani cewa har abada Kursiyya da Zabba’u ba zasu taba samun kansu ba har sai sun fada mini inda uwata take. Duk kudaden da mai martaba zaka kashe a banza, don Kursiyya ba zata taba warkewa ba. ldan ma ta warke din a take zan kumajefa mata wani ciwon da zai tasar mata fiye da wanda aka warkar din. 
A yanzu gani, ga mai martaba, ga Kursiyya da Zabba‘u, ga kuma Mallam Khamis Ciro. Zan sakar ma Kursiyya bakinta tayi magana. Ta fadi gaskiyar inda ta kai mahaifiyata. Ni kuma nayi alkawarin sassauta mata matukar ta fadi inda ta kai ta din.” 


Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page