HASKE CHAPTER 4

HASKE

CHAPTER 4
A kwana a tashi.

Kwance tashi babu wuya wajan Allah, Kamar yadda Saif yayi tunani zashi wajen kanin mahamnsa haka ko yayi, Chan kauyen su na Danbatta dake jihar Kano yaje duguzum domin ya cimma nufin sa kuma cikin ikon Allah ya samu. Korafi dai yasha wajen Mallam Adamu tareda matarsa Marka. Dama idan bakada arziki ba’a zumunci da kai, sun mashi magana akan hakan inda suke shiga ba nan suke fita ba saboda sun lura shi ne zai karu dasu. Yayi zugudum ya nata basu hak’uri daga nan yabama Mallam dubu 10 ita kuma dubu 2. Yara daya ganin tsakar gida ya basu dari biyar su siya alewa. Mallam yayi masa alkawari zai shiga Kaduna nanda kwana bakwai wajen iyayen Laila.
A hanyar dawowa yake gayama Laila abinda ya wakana banda dai fannin kudin, nan tayi murna ainun tareda masu fatan alheri sannan ta ayyana a ranta koda anyi aure basu zo gidanta ba. Sai tace mashi kada ya mance ya siyan mata tsaraba nasu dankalin turawa sabida tana marmari, kana kuma idan yakai zaria ya siyan mata biredin Bitmas. Bayan nan kuma tace subscription dinta ya kare.
Haka k0 aka yi saboda kashi biyu yayi na tsaraba, na Laila dana Sameera. Yaune yakeso ya fada mata maganar aurensa, duka zuciyar sa keyi kamarjirgin kasa, duk ya tsargu saboda Sameera batada wani laifin dayake yawan fadi. Laila ya fara kaiwa kayan, da azama tasa yara su jida kayan zuwa ciki, saida ya dakatar dasu akan ba duka bane nata. Nan kam tasha kunu kamar sama da kasa zai hadu. Bata iya boye kishin ta ba saida tayi masa magana.
“Rabin raina yanzu wannan gajan harta san biredin Bitmas?” ta fada tana yatsina baki kamartaji warin masai.
Tsunture wa yayi da dariya sabida yaji dadin sunar sosai, yanayi yana tafa hannu kamar dan daudu. “lyye Yar Lelen Saifullahi amaryar gaban goshin sa. Kishin ne ya motsa? To bari kiji ai gajar batakai taci ba, kawai saboda yarana ne, kuma ladan kula dasu kenan. ldan ba haka ba ina ruwana da ita?” tura baki yayi sannan ya daga kafada alamar ko in kula.
“nifa gaskiya bazan iya kishi da ita ba, idan ka siyan min Bitmas ita ka siyan mata biredin kan hanya mara kan gado,kowanne tukunya fa da murfin sa. kuma na shiga gidan nan babu wani raba kwana, ni kadai keda kai. Ehe!”
“Tim na zama dan gayu amarya ta gama magana abinda kikeso shi zanyi” yanayi yana guntun shoki.
Laila taji dadin yadda yabar mata ragamar gidansa, ya nuna yana santa kuma ta dauki alwashin zata canza komai daga yana yin girki da rayuwar da zasu dasa. Zata nuna ma Sameera bata iya zaman aure ba, zata koya mata shikashikan aure.
Gwaggo taga kaya makil an shigo dasu, dama idan basu doya ko dankali ba Laila bata basu, sai dai idan Haske ce ta tilasta akai masu. Laila nada bala’in rowa da san abin hannun ta, gata da kawa zucci akan kayan wani. Aikam Gwaggo taji dadi da batun maganar Laila, yarinya takai 24 anata tsegumi a kauye wai ta sakata a gaba tanata kallo. Wani gonansu na kauye aka ce zaa siyar tunda basuda wani kaddara a birni. Koda Saif yaje gida lokacin Sameera tana kunshi, dama sana’arta kenan Lallen sudan. Ta bala’in iyawa kuma tanada arha. Kowane hannu dari da hamsin takeyi. Dashi take rufawa kanta asiri wanda Saif yake kokarin tonawa a kowane rana. 
Suna zaune kan tabarma a tsakar gida ita tana kan karamin kujera na tsuguno. Hannun karshe kenan takeyi ma uwa da yaranta yanmata biyu. Yau tayi ma mutane wajen 6 ta caska dubu uku da dari shida. Saif ne ya shigo da fara’arsa tinda yau bashida gaskiya, haka ya bude bayan motarsa yayita fita da kayan tsaraba wanda har dasu kayan miya da albasa ya biya ya siyan masu Da murmushi ta dakata da wanda takeyi wanda dama shine na karshen saura bushe wa suke yi. Masu lalle sun gaida shi ya amsa masu a mutunce wanda ba kasafai yake haka ba banda daga masu kai kamar kadangare. Da kansa yace taje ta gama na karshen shi bari yayi wanka tukun. Haka kam tayi bare shi dake dadewa a bayi harta gama mata bai fito ba. Shi 
kam yana bayi yakai mari yakai gwauro yana so yasan ta wani fanni zai fito. Sai wani zuciya 
yace ya hade rai kawai ya gaya mata gatsal tunda ba tsoronta yakeyi ba. Bayan sun fita ta ajiye mashi abinci wanda rabin cefanan nata ne. Ga dakin sai kamshin turaren wuta yake 
wanda ta soma siyarwa tunda ance sana’a goma maganin mai gasa. Tuwon alkama tayi da 
miyan kubewa danya saita hada da fresh fish. Kuma ta kada masu zobo. Yanaci yana murna tunda yasan ba cefanan sa bane, daga gefe tana kallon sa Sadiya tana bayan ta tana rizgan barci su kuma su Mubina da Abul khair anje islamiya. Saida yayi nat yayi gatsa ‘gaaaaaa’ mai uban kara kafin ya soma magana. 
“Maman Abul khair inaso ki natsu ki jini da kaifin basira, dama daga Danbatta nake wajen su Inna Marka” da fara’a tace”Ka barsu lafiya ” 
” Lafiya lau, sunce a gaida ki, gama wancan Gaudah sunce na baki” sai yayi nuni da hannunsa kan wani leda wanda bata bude ba. 
“Nagode Allah ya sanya alheri” 
“Amin summa Amin, yauwa bari kiji abinda yasa Naje, dama na samu yarinya fara, kyakkyawa kuma mai hankali zan aura” yace yana washe baki. 
Kana ganin fuskanta saida ya canza, tunani daya yazo mata, wai ya za,ayi mutum dako cefane saita cika masa shi ne zai kara aure. Ta nuna bakin cikin ta a Fili sabida saida tayi magana. “Aure kuma Baban Abul?” “Eh aure zanyi ko kin isa ki hanani ne?” ya soma mazurai “A’a ba abinda nake nufl bane, naga muna zaune lafia lau ne ai” tace a sanyaye 
“Wannan keya shafa, ni namiji ne kuma ba rago bane, sabida haka dole na sake mata. Infact bafa izinin ki nake nema ba. Sabida nanda wata biyu zan shigo da ita” 
“Mu gani a kar wai ance ma kare ana suna a gidan su” tace tareda murguda baki. Nan ya mike ya soma zare mata ido tareda ashar. 
“Ke nifa ba lusari bane, yanzu zan bibbige ki na karya banza. Kar ki kawo min raini 
sameera” yana nuna mata yatsa. Zugum tayi kafin ya bigeta saiga su Abul Khair da Mubina 
sunyi sallama. Abinda ya ceceta kenan. 
Daren ranar dan hakimci night call sukayi da Saif, Haske taga rashin kyautuwan abin ita 
kam ko gezau. Tanayi tana masa shagwaba wanda yayita biye mata. ldan ran Sameera yayi dubu to ya baci sabida a speaker ya saka, haka ta sungumi pillow ta koma falo kan 3 seater domin tayi barci. Nan ya tuntsire da dariya ya gayama Laila. “Kina ganin mutumiyar ki bata iya tarairayan miji ba kuma dan mugun hali bazata koya ba, shi ne fa ta koma falo domin bakin halinta” 
“Yayarka dai ba mutumiya naba” nan suka yi ta dariya na rashin dalili har wajen uku dare. 
Sameera taci kuka kamar idon ta zai tsiyaya, mamakin sauyawan Saif takeyi. Wani zai ce auren hadi akayi masu bana soyayya ba. Amma da tana ganin gaibu da bata aure shi ba. Sam bashida mutunci ga kuma fadin rai. Sannan uwa uba rashin abinci balle ya siyan maka kaya. Rabon daya siyan mata kaya tun na Lefe da yayi akwati 4 da kit. 
Saidai ta siyan ma kanta ko idan ta haihu danginta da nasa suyi mata. Mamaki take karara 
yanda wata zata yi marmarin auren Da kudi da mota itama yanzu batayi dan zaman yaranta takeyi yanzu. 
Soyayya tsakanin Haske da Bilal babu yabo babu fallasa, ya rage mata diban albarka koda yake baya garin ne. Yana Dubai Abbansa ya aike sa. Gaba daya satin Saif ke kaisu aiki ya dauko su, da safe bayan yakai yaransa makaranta zai biya wajen su. Abin kam yayi ma Laila armashi tana gwalangwatsi tana cika tana batsewa. Koda yake ita take rokon sa akai akai ya siyan masu kayan dadi. Sai dai kuma zulumi fal ranta,yadda take Instagram tana ganin bikin mutane itama tana so ayi mata shigan irin sa koda a talauce ne. Gashi gaskiya tanaso ta siya gas cooker da fridge sannan Kuma tanaso tayi event kwara daya koda kamu ne. Sai dai ta san su Inna basu da halin nan. Wata kawar su wanda sukayi Kaduna Capital School mai suna Wasco (wasila) ta kira. Wasco asalin yar bariki ne, acewarta babu wanda ya kaita iyawa tunda daga mamanta har babanta a club suka hadu sukayi aure. 
Runz gal ce bata Abuja, Lagos, Port Harcourt, Dubai dasu Johannesburg. Kowa yasan abinda takeyi kuma tana iya zama kawaliya. Ko da Laila ta kira ta domin ta ara mata kudi, bayan Wasco tayi dogon ajiyar zuciya tace, “Gaskiya kar nayi maki karya bana bada rancen kudi, balle mai uban yawa haka” 
Da sauri Laila ta katse mata hanzari kana tace, “ Wallahi zan biyaki, idan nayi aure nayi ciki zan rinka kwakulan sa yadda ya dace, kuma ina aiki duk zan tattaro na kawo maki” 
“Hmmm nidai bazan iya ba” Wasco tace cikin rashin aminta. Sai kuma tayi wani tunani “ldan kina so Zan hadaki da Chiefchinedu,yana bunburuntun mai a niger-delta, kuma yanada sakin hannu idan yaji dadin harkan ki” “Babu musulmi ne Wasco” “ke bansan wulakanci! Kudi kike so ko iya shege? An gaya maki saboda gudunmawa na baki shi ki samu kiyi bikin nan cikin armashi” 
“Yi hakuri kawata kin min kokari wallahi” tace da sauri kafin ta bata wasanta da Wasco. Ajiyar zuciya Wasco tayi sai ta cigaba da magana, “Zan maki text din inda zaku hadu, kar ki mance ran Asabar ne” gaban Laila ya fadi saboda Asabar jibi ne kuma ranar za a kawo gaisuwan iyaye da sadaki duka a saka ranar biki. Amma bata isa ta fada ma Wasco ba saboda sai ta hanata gaba daya. Dibara ya fado mata akan taje a hakan zata nemu karyan da zata shapto. 
Sannan idan ma yayi ruwa ta kwace Chief Chinedu a wajen Wasco idan yaso ta bashi number dinta su dinke yayita mata famfon kudi. Balle ma arna basuda surutu barkatai bayan sun gama iskanci dakai. Dama yana zuwa NNPC kai mai ne idan yazo su hade da Wasco. 

Ranar Gaisuwa 

Uku uku gaban Laila ke fadi, Wasco tayi mata text akan zata hadu da chief karfe sha biyu na rana a Hotel Seventeen. Tun safe suka tashi, ranar shara na daban akayi ma gidan har gaban gida akabi aka cire su kwata aka wankel Dama Haske ta bada oda na samosa da meatpie wanda za’a bama baki. Sai kuma kajin hausa biyu da aka soya akayi miya da kuma peppered. Shinkafa yar gwamnati mai dadin ci aka hada da salad daidai gwargwado. 
Haske ta lura da yadda Laila tayi yaushi wani abu yana damunta, datayi mata magana tace kawai tana mamaki wai itama zata dandana aure ne zata soma kashe arna. “Kefa banza ce sam bakida kunya, ko tsoron kada Gwaggo taji ko Mashkura kanwar Laila” 
“wannan kuma kunyar su, bafa karya nayi ba, ai shine auren. A kashe arna safe, rana, dare a hole anayi ana shan lemun kwali” daga nan ta kurba raguwar wanda Saif ya kawojiya watau Chi Exotic. 
Yan matan Gwaggo sunyi kyau abin su, inda Haske tasa purple Lace wanda ya amsa fatar ta, sai tai daurin ture Kaga tsiya, babu make up a fuskanta banda kwalli. Laila ita ma Lace tasa blue kalar bula. Amma ita tayi kwalliya har dasu eye shadow. 
Wajen Sha daya Laila tayi ma Gwaggo sallama zata gidansu Wasco domin ta zauna saboda kar tayi karo da surukai. Dayake Gwaggo batasan waye Wasco ba ta sanya mata alheri. Haske ne tace mata ta zo suje daki domin ta tayata da abu sharp sharp. Bata kawo komai ranta ba tabi sahunta. 
“Ke banda abinki ki rasa gidan zuwa sai gidan tambadarda Wasco” tace a fusace tana huci. 
“Babu ruwanki dani, bansan haka. Idan ke bakida kunya ni ina da shi. Yo so kike nayi karo da surukai na?” “Baga gidan Maman Eemad a kasan layi ba kije ya fiye maki kwanciyar hankali, har Rafin guza wajen Wasco” 
Daukar Jakarta tayi kafin Haske ta shafa mata bakin jini, “Nidai sai na dawo a kula da baki” sai ta fice. A kofar gida ta samu mai napep ya ajiye wata sai ta shiga. Haske na daga daki ta hango ta. Sam jikinta yaki sakewa da Wasco saboda babu alheri a tareda ita. Fata nagari tabi Laila dashi sai ta koma cikin gida. 
Ta dauki alwashin sai bikinta yafina Haske armashi, shi yasa kowane hanya zatabi domin ta samu kudi saita bi. Balle ya za’ayi Haske tazo cin arziki gidansu ace tama fita. Sannu a hankali suka isa hotel din, nan ta kira Wasco aka ce yana presidential suite room 12. Gabanta yana duka uku uku taje tana rokon kada Allah ya hadata da idan sani. Aikam babu wanda ya damu da ita harta kai dakin. 
Murfin kofar ta murda saita shiga tana dariya. Chief zaune yake kan gado da gajeren wando, babu riga banda gashi busu busu baka ganin komai a kirjin sa. Sai kuma rundumemen ciki kamar tulu ko mai juna biyu. Daya bude baki suka gaisa hakora biyu babu sun fita. Nan gabanta ya sake faduwa. 
So na you be the ashawo where dem bring for me, wetin be ur name? (kece karuwar da aka kawo min, ya sunan ki) “ yace yana sakutan hakorar sa. 
“Maryam” tace da sauri. Wayansa ya dauko ya duba, “My friend don’t lie to me, na Lela… 0r wetin she write self” ya kalla yana karantawa. Ita kam ta tsorata dashi ainun, musamman kada yayi kudi da ita. Shikam yana ganinta batayi mashi ba Sam. Tanada haske amma kana gani kasan na bleaching ne, musamman idan ka ga Gwaggo da Baba bakake sidik ita kuma da haske. Shi a duniya baya san farar mace, shi a wajen sa mace iya mace saidai baka. Fatan su duk wuyan duniya baya nunawa, ko na sauro kona ciwo gashi idan ya samu hutu sai yayi kashar kashar. Original kenan ba okrika ba made in aba. Abinda yasa yake san Wasco kenan, ita kuma Wasco ta san Laila baka ce kuma koda tayi bleaching batayi tsammani zatayi pau wanda chief zai tsana ba. 
“you no go remove your clothe? Why you they look me?? (bazaki cire kayanki ba, meyasa kike kallo na?)” 
Haka ta soma sulale kayan jikinta, a hankali kamar babu laka jikinta. Tanaso tace ya kashe wuta amma tana tsoron ya mauje ta. Timbir ta tsaya haihuwa uwa, shikam kallon raini yake mata. 
” see how you straight, you no get anything for body, you sure say you no be boy? Or na you be hausa bobrisky (jibeki a tsaye ba komai jikin ki, kin tabbata keba namiji bane? Ko kene bobrisky din arewa)” ya fada cikin takaici. Anan kam hawaye ya ciko mata, Chief ya gama cin mata fuska amma kuma kudi take nema dole sai tayi hakuri. Bayan Chief ya more, ya hankade ta gefe ya kuma ya hanata wanka saboda Shima bayi zaiyi ba . Haka ta saka kaya duk ta jigata sai raba ido takeyi tana zarewa, tabbas aikin haram akwai wuya. Sai dai daya dauko brief case dinsa saita soma murna tana washe hakora, Balle taga bandir din,1000,500,200, 100,50 da sauran su. Murna fal ranta kila ta tashi da kusan 200k. Aikam wanka ya biya kudin sabulu. 
Fuska a daure Chief ya dauko wrap din 100 ya bata watau dubu goma. Sekeke ta tsaya tana mamaki ya za’ayi ita datazo cin arziki ta bige da 10k. 
“Chief how far? (ya akayi?“ tace cikin rashin kunya. 
“My friend get out before I break bottle for your head? ( fita kona fasa maki kwalba a kai)” da sauri ta sungumijakarta tana kuka ta fita kafin ya fadanra mata kai. 
A hanya tana kuka cikin napep ta kira Wasco, tana mata korafi. Anan ta bata hakuri tace yanzu Chiefya kirata wai Sam baiji dadinta ba tunda shi baya ta’ammali da farar mace ita kuma batace tayi bleaching ba. Nan ta dai bita da baki tareda mata alkawarin zata hadata da wanda zata caska naira 
Anyi taro lafiya cikin mutunci inda aka saka biki sati hudu wanda shi Saif ne ya bukaci
haka, Baban Laila baiga jiran me za ayi ba ya amince. Anan aka karba sadakin ta dubu 
hamsin sai kudin gaisuwa dubu ashirin. Anzo da tabarma guda uku, huhun goro guda daya, pakitin cingam hudu dana sweet haka. 
Shi Saif yana ta wajen ginin sa na cikin gidan inda dama zai saka maman sane amma yanzu ya fasa sai sake mata sabo. Ciki da falo ne manya manya da bayi da kitchen sai karamin store. Ankai har kwano ansa saura su kofa da painti. Koda Laila ta isa gida ta wuce bayi tayi wanka, Haske da Gwaggo sunyi mamaki sabo da duk sun san sau daya take wanka watau na safe. Daga nan ta rama sallolin ta. Abin takaici saida ta shiga dakin Gwaggo taga abinda aka kawo. Gashi biki an matso dashi. Ga yau ta fita babu kasuwa, dubu goma ba fridge dinda zai siyan mata sai dai randa. Wani siririn hawaye ya soma sauko mata komai ya cunkushe mata. 
Haka ta koma daki saiga Saifya mata 5 miss calls, anan ta kira shi kafin tace kwabo ya soma balbale ta. Bata san sanda ta soma bashi hak‘uri ba. Anan ma yace baya so ta rinka zuwa aiki daga yanzu ya soke shi. Zatayi korafi yace shi yanada bala’in kishi bayaso ana ganin masa mata. Ko Sameera tana aikin local government saida ta bari. Nan ya labto mata karya wai Sameera na kiwon kaji ne yanzu haka tanada kaji dubu. ltama idan tanaso zai bata jari. Murna fal ranta dama batasan fita. Amma abinda bata sani ba shine guda 50 ya siyan ma Sameera kuma da kansa zaije ya dauke daya ya yanka kuma bata isa tayi magana ba har saida ya cinye. 
Dadin abin Sameera nada sana’ar hannu inda ta koya lalle wajen makwabciyar su kafin 
tayi aure data dandana Kuren ta. Ta kasa ma masa maganar kayan gaisuwa da aka kawo a tsiyace kawai ta basar tunda taji zata soma kiwon kaji. 
Bayan lsha sun gama cin abinci, Laila sai fadin rai takeyi ta kusan dena kwanan zaure gashi zata shigo gari ga aure ga sana‘a. Bad ya kira Haske sunata waya yadda ya jadadamata gobe zai dawo. Bata kashe wayar da minti biyu ba wani sabuwar number ya kirata. 
Da sallama ta kara wayar a kunne ta, amma kuma sai taji muryan da bazata taba mance irinsa ba. Mai muryan nan yayi mata cin mutunci da bata taba tsammani irinsa ba. Mai muryan nan itace silar shiga duk wani tashin hankali data fuskanta da wani kaskanci. Ta dade tana jiran randa za’a kirata ace an gane cewa kazafi ne ta dawo gida. Mai muryan ta riga ta dauke alwashin saita rabata da duk wani farin cikin ta, da duk wani wanda zai kawo mata Haske a rayuwarta. Ta dauki alwashin gallaza mata fiye da tunanin dan adam. Wanda zata gwammace mutuwa akan zama tareda ita. Muryan Ammi ne watau mahaifiyarta. “Shamsiyya, kizo Abban ku babu lafiya yace yana bukatar ganin ki” 
Ashe bawai an gane gaskiya bane, bawai sun yafe mata bane koda tayi laifin. Yau shekara daya da wata uku kenan rabonta da wani nata koda ta waya ne. Wani zafi da daci kawai yake mata yawo a zuciya, kwakwalwarta ya soma tafasa. Numfashinta na kokarin dauke wa. Gumi ya soma keto mata ta koina. Toh ina ma zata fara zuwa gidan su bayan duk abinda ya faru. Batasan gatan uwa ba,batada bambamci da marainiya sabida tun tana shekara 7 Ammi ta rinka gallaza mata. Wannan kenan! 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page