MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER36

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 36
Gurin dayar nurse din ta karasa ta bawa baby boy din kafin ta dawo gurin ta kalli Sadeeq dake shafar kan INdo yana hura mata iskar bakinsa ganin bata bude ido ba. 
“Angon karni leave us please kafin a gama shirya ta.” Da kyar Sadeeq ya iya yin magana ba tare da ya kalli nurse d’in ba yace. “Ki fara duba ta tukunna naga tayi haka bata kifta idanuwa sosai.” 
“Ah karka damu wannan ba wani abu bane ba, kawai wahalar haihuwa ce kadan bamu guri tunda kaima ka bamu gudun mawa.” 
Tashi Sadeeq yayi yana kallon INdo wadda idanunta ke a rufe sannan ya fita. Maman Sayyid makociyar su da suka zo tare ta kallesa tana zaune ta mike duk da cewar tajiyo kukan jariri tace. 
“Malam Sadeeq yaya ita din?!” 
“Sun ce zasu gyara sune but ni banga ita Aishan tana wani abu ba da zai nuna min cewar komai normal ba.” 
“Insha Allah komai lafiya lau karka damu shi yasa banso ka shiga cikin ba naso ace kawai sai dai a kiraka ace kazo ka gansu.” 
Numfashi yaja tare da yi mata godiya sannan ya wuce masallacin dake cikin asibitin kasan cewar anata kiran sallan asuba. Kafin ya dawo daga massalacin an gama kintsa su duk da basu zo da kayan haihuwa ba, nurse d’in da ta karbi haihuwartana siyar da kayan babies ta sanyawa yaron ita kuma INdo ta bata sabon zani wanda shima itake siyarwa ta daura tare da bata maternity pad da pant. Resting room aka maida su Maman Sayyid na zaune kusa da ita tana mata barka lNdo kuwa ji take wani girim‘girim ganin cewar wai yau itace ta haihu ga dama har tana bashi yana sha. 
Sadeeq kuwa sai daya gama sharara addu’a sannan ya fito daga massallacin har gari ya dan fara yin haske. Yana shiga reception yaga Fateema tana kalle-kalle tanajuyowa kuwa ta ganshi dai-dai lokacin nurse ta fito ta nuna mai d’akin da aka kaisu. 
“Baby ina kwana? Ya su Aishan?!” 
Ta fad’a tana kallonsa kai da ka ganta kasan itama tunda ya sanar mata suna asibiti bata samu wani ishasshen bacci ba. Hannunta ya kama ganin babu mutane suka shiga cikin dakin dasu INdo ke kwance Maman sayyid na ganin su ta mike daga bakin gadon tana musu murna. 
Rufe idanuwa INdo tayi dan wata irin kunya takeji azo aga ta haihu. Yaron Fateema ta karba tana kallonsa yana ta bacci yasa yatsansa babba a cikin bakinsa, ta karasa wajan Sadeeq dake zaune a wajan lNdo ya riko hannunta yana murmushi ganin yadda taki bude ido. Jaririn ya karba yayi mai hud’u ba sannan ya ciro wayarsa, su Mama ya kira ya sanar dasu yayin da Fateema ta kuma karban yaron ta zauna kusa da Maman sayyid. Yaron jawur dashi 
Me kyau kirjinta ya dinga bugawa tana dannewa sabida jinsa take inama taga nata cikin ya fito sai dai baza ka gane hakan ba sabida tayi nasarar fun karfin zuciyarta. 
“Wai cutie wa kikejin kunya a gurin nan da kika ki bude idanuwanki.?!” 
Kada kai tayi still idanta a kulle yayi murmushi tare da mikewa ya fita. Gurin doctor yaje dan yana son a basu sallama su tafi gida dan kar a cika asibitin. 
“Mu wuce gidan Mama Fateema.” 
Ya fad’a bayan ya dawo d’akin. Da sauri INdo ta juyo tana yin kamar zata yi kuka tace. “Gidan Mama kuma? Ni dai wannan karan baza ni gidan Mama ba can gida za’a maida ni.” “Aisha wane gidan za’a maidake bayan haihuwar fari ce.?!” 
Sadeeq ya tambayeta bayan ya mikar da ita zaune. Na”Sani, ni dai can zan tafi gaskiya.” 
“Au lallai gidan namu ne bazaki zauna ba?!” 
Shiru tayi tana tutturo baki su Fateema sukayi dariya kafin tace. 
“Gaskiya ranka ya dade a al’adance haka akeyi, a kaita gida har tayi arba’ln ko sittin sannan sunyi kwari ita da baby sai a dawo dasu.” “Haka ne kam.” 
Maman sayyid ta sake gasgata zancen, Sadeeq ya shafa kai lallai akwai kwarbai kenan duk da ba zama yake yi ba ai zai so ya zauna dasu ko na d’an wani lokaci ne tayaya zai bari su wani tafi kauyan Sani. 
Account number din nurse din ya karba dan zai tura mata kud’in kayanta sannan ya siya magungunan mejego suka wuce can gidan INdon kasan cewar tak’i yadda ya kaita gidan Mama wannan karan da hankalinta dan haka bazata yadda taje gidan sirikai wankan jego ba. 
Suna komawa kuwa ‘yan uwa suka fara zuwa dole tasa Sadeeq kwasar yanashi-yanashi na gidan ya tafi dasu gidan Fateema. 
“Allah sarki, dama rabon wannan yaron ne Allah ya dauke Habu. Gashi daga tafiyarsa har 
Allah ya bada arzik’in yaro zukeke tubarkallah.” 
Cewar kanwar abban su Sadeeq da tazo ganin d’ah. Hakama duk mutane suka fada duk wanda yaji labarin haihuwar wanda hakan sai da yasa lNdo yin kuka sabida surutun mutane da tada mata da baya. 
Haka aka dinga zarya zuwa gidan INdo da niyyan idan anyi suna za‘a maida ita sani bayan Mama ta nunawa Sadeeq amfanin komawartata tunda tafi son can. Ba karamin kokari Sadeeq yayi ba wajan ganin ya fita kunyar mejego da baby harma da mutane, Fateema ma be barta haka ba sai da yayi mata na fitar suna sannan itama dasu Ummanta sunyi rawar gani sunyi musu kayan barka tamkar ba kishiya ce ta haihu ba. 
“Cutie me jego, naga alamar haihuwar nan wata wawuyar kunya ta sanya miki why?” 
INdo ta tura mai baki ya sanya hannunsa yajasa tayi ‘yar k’ara tare da d’an dukan hannunsa. Rungumeta yayi kafin yace. 
“Toh me ake buk’ata na gobe wanda ba‘ayi ba.?!” “Ba komai hakan ma mun gode.” 
“Toh gobe dai nasan ganinki zai min wahala sabida mata dan ba shigowa zanyi ba, idan ma kuna son wani abun ki kira Mubasheer ko khaleefa sai ki sanar musu.” 
lNdo ta kallesa, wani irin tausayinsa takeji sabida ganin hidimar da yayi tundaga kan abincin sunan da za’aci zuwa kayan rabo na sunan da ragunan da za’a yanka ga kayan barka dayayi musu yace. 
“Allah yasa ayi taro lafia cutie, please karkiyi fushi da kowa kinga duk wanda kika gani zuwa yayi dominki domina domin marigayi infact dai kowa yazo ne dan tayamu farin cikin samun karuwa. Na tafi sai gobe zuwa dare zan samu mu had’u.” 
Kai ta daga sannan yajuya zai tafi, da sauri tasa hannu ta rikosa sabida wani sassanyan sonsa daya kuma shigarta a dan tsayuwar da suka yi. Rungumesa tayi shima yasa hannu ya rikota yana shafar bayanta murya na rawa yaji tace. 
” ‘I love you’ Sadeeq forever, I’m also wishing you all the best in your life. You are always by side, to share simplejoys and each Nd every need and now with out your loving presence I’m very lonely indeed I love u with all my life my husband…” 
A yadda yaji tana fitar da words d’in ba k’aramin tsumashi suka yi ba, a hankali ta dinga jerosu dan ba karamin kok’ari tayi ba. Kokarinta da kuma son ganin tayi abu yake k’ara sanya shi cikin k’aunarta, ya d’ago da fuskarta cikin lumshe ido ya zura bakinsa cikin nata. Kissingjuna sukeyi cikin wani irin shauk’i har Sadeeq yaji yana neman fita a hayyacinsa sannan ya kyaleta da kyar ya shafi fuskarta sannan ya bar d’akin da sauri sabida yasan mutane na nan sun sawa dakin ido suga mintuna nawa zaiyi a ciki. 
‘Yan saye duk sunje da ‘yan uwan Inna daga dawakin tofa su Uwani, Sahura, Rukayya, su Maryam haka ‘yan kauyan sanin nan suka yo mota guda suka zo duk da ance su bari zata dawo amma wasu suka ce ai daman basu san gidantaba dan haka sai sunje. 
Washe gari suna yaro yaci sunan Abubakar dan haka ko ajikin kalandu da key holders da sauran abubuwan da akayi aka sanya mai Abubakar (Ayman) wanda Fateema ce ta zabi lak’anin yace wa INdo yana son ta bari a sanya mai tunda dama shima uban sunansa ne 
dan ayi mata kara. 
‘Yan kauyan nan an samu shinkafa dasu zobo lemukan jarka da sauransu suka dinga lodawa cikin jakunkunan su, gidan ya cika mak’il da al’umma su sai nan-nan ake da little Sadeeq (ayman) duk nacin yayya Nabee ta hanata d’aukarsa sai dai ta kallesa a hannunta. ‘Yan yan bankinhausa novels fad’ar yawansu bazai musaltuba suma sai salfie suke da mejego dan a samu na sawa a status da dp, taro yayi sweet mejego an yi fitar suna ta kece raini. Yamma nayi ‘yan sumaila suka kama hanyar komawa bayan sunjajjada ma INdo cewar ta 
taho musu da naman sunan su. 
K’arfe tara na dare Sadeeq yazo k’ofar gidan yana fitowa daga mota mutane dake wajan suka dinga mai barka fuskarsa cike da farin ciki. 
“Yaya Sadeeq kenan kwana biyu.“ Yaji an fad’a cikin noke murya, kallonta yayi bayan ya zare glass din idansa. Sanye take cikin wani fitinannan material anyi mata dinkin riga da skirt sun d’ameta sosai, gashi kwan lantarkin kofar gidan ya haske su ya zabga mata harara cikin tsuke fuska yace. “Chuchu wai banace ki dena yin irin wad’annan banzayen din kunan ba? Wallahi Zan je na 
samu uncle Ahmad d’in wata k’ila baya lura da yadda kuke rayuwarku.” “Kai Yaya Sadeeq yanzu nan meye na rashin dai-dai a cikin rayuwata..?!” 
Tayi maganar tana d’aga mayafinjikinta, tsaki yaja tare da kara wayarsa a kunne taji yana cewa. 
“Cutie lallabo kizo waje ina mota.” 
Mayar da wayar yayi cikin aljihu tare da komawa cikin mota chuchu ta matsajikin murfin ya 
kalleta tare da cewa. “Matsa ki bani guri.” 
“Kai Yaya Sadeeq dan Allah, wai kana nufin kace har yau baka gane inda Zuciya ta take ba akan ka? Please Yaya Sadeeq tun kafin na mallaki hankalin kaina nake sonka amma sai wani shareni kake yi ko banyi maka ba Yaya Sadeeq?!” “Ke! Zaki matsa ki bani guri anan ko sai nayi ball dake.” Turo baki tayi tana sake matsawa kusa dashi, cikin nuna izgilanci tace. 
“Hmmm Yaya Sadeeq duk matanka nasan tarihinsu kuma duk cikinsu babu wacce takaini komai ba kamar wannan aunty Aishan mejego, ita da ko wayewar ma anan gurinka tayi ‘yar kauye da…” 
Kwaf… Taji ya kwade mata baki da phone din daya dakko, dai-dai kuma lokacin lNdo ta fito tayo gurin motar Sadeeq yace. 
“Chuchu bar gurin nan kafln raina ya kuma baci, k’atuwar banza sakarya kawai.“ 
Kuka tasa ganin harda jini ya fito INdo taga ta tafi tana kuka ta shiga motar shima ya kulle suka kalli juna tace. 
“Me kuma ya sanya chuchu kuka my super glue? Allah yasa dai ba wani abun kayi mata ba tana da kirki.” 
“Cutie rabu da ita rashin kunya takemin. Kinga bama wannan ba ya taro hope kunyi komai cikin jin dad’i da wal~wala..?!” 
Hancinsa INdo taja tana murmushi jin dadi sannan tace. 
“Kana sona mijina Allah ya shi albarka ya kara bud‘a maka hanyoyin samu, mu kuma Allah ya bamu ikon yi maka biyayya kamaryadda kake iya k’ok’arin ka wajan ganin ka faranta mana.” 
“Amin Ummi ayman inajin dad’in yabon nan da yake fitowa daga bakinki. Ina dana baki taho min dashi ba, kinsan yaufa tun asuba rabona dashi.” 
Dariya tayi sannan ta zugejakar hannunta ta fito da kudadan ciki wanda duk na barka ne. Mik’a mai tayi be karba ba ya kallesu tare da cewa. 
“Uhmm k’arin bayani tukunna cutie ai bakya mikon Kud’i haka ba bayani ba.” 
“Toh ka karba mana ai zan maka bayani, kudin da mutane suka bani ne na barka ne. Ka karba 
kayi amfani dasu kaga akwai kananu nima sai nayi wani abun ko idan za’a nema.” 
Dariyar shima yayi zuciyarsa fara kal, chuchu na can gefe a tsaye tana gunguni sauran ‘yan uwa na mata sannu amma idanunta suna kan motar Sadeeq haushi kamar zata hadiye motar. 
“Cutie wannan ai naki ne, ni babu abinda zan karba Allah yayi miki albarka ya albarkaci yaron da kika Haifa min Ina alfahari dake Ina sonki har cikin kahon Zuciya ta.” 
Kowa dadi yakeji sun dade a cikin motar kafin ya duba agogo ya kalleta cikin yanayi 
nasan nuna rashin son abinda zai fada yace. 
“Zan tafi, gobe insha Allah ance za’ayi suyar nama acan gida kinga kar a batawa masu gidan idan an kammala za’a kawojibi idan Allah ya kaimu za’a kaiku sumaila sai kuma kinyi arba‘in.” 
“Ko baka son na tafi ne..?!” 
Yayi murmushin yake domin harga Allah baya son suna rabuwa amma ya zai yi ko ta zauna fitina zai dingajawa kansa gashi kuma zai koma kwara Fateema baza ta bishi ba wannan karan sabida zasuyi wani taro a makarantar da take aiki dole ya barta taje. Hannunta ya kamo tare da cewa. 
“Cutie karki damu kije ki dawo hmmmm zaki shaaaa.” Da sauri ta bude motar suna dariya bata bari ya karasa,ba lekensa tayi sunata dariya yace. “Idan kin shiga kicewa Fateema ta fito mu tati.” 
Baki ta turo ya shafa kansa ganin harta mai fassara ya kashe mata ido d’aya sannan ta tafi, tasan komai shi kenan yanzu shida Fateema zasu cigaba da zama sai taji wani iri a cikin zuciyarta da kyar ta iya fadan sakon sannan Fateema ta fita, chuchu na ganin haka ta kalli su Haleema tace. 
“Kuzo muje wajan Yaya Sadeeq ya rage mana hanya duk da munyi fad’a.” 
Tashi suka yi da sauri suka karasa wajan motaryana kokarin tadawa suka rokesa, sai da ya fara dankarawa Chuchun harara kafin yace. “Ku shiga amma wallahi badan halinku ba sakarkaru kawai.” 
Shiga suka yi ya dingajan Fateema da hira dan ya denajin muryoyinsu musamman ta Chuchun da take kamarta gyare kyar-kyar-kyar. Yana zuwa suka fita chuchu ta kallesa shi kuma yaki bari su had’a idanuwa sabida mugun haushinta yakeji sabida yadda yaji zata taba mai mutuncin matarsa uwar dansa. 
Washe gari bayan anyi suyar nama an kasa kowa an bashi. INdo ta kimtsa musu kaya itada ayman da Nafeesah da daddare Sadeeq yazo gidan ya kuma siyo mata wasu abubuwan da zata bukata na ayman sannan ya tafi. 
Washe gari da kanshi ya shirya zuwa kaisu sumaila tun a hanya suka farajin kewarjunan su sai dai yayi mata alk’awarin zuwa duk sanda ya dawo kano. 
Yana kaisu ya juyo dan INdo har kuka tamai wanda da kyar ya lallaba ta sannan ya tafi bayan ya bata kudi taki karba sabida akwai na barkar data samu a hannunta… 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page