MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 33

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 33
“Toh mezan ce maka? Kaga kaima Fateema ka fara aura, kuma ita kake so kafin ni. Toh nima ina sonka amma nafison marigayi dacta nima kaga AN  raba kar wani yaji haushin wani.” Fuskarta yakai dai-dai tata ya hade hancinsu guri d’aya yana rikE da hannunta yace. “No Humaira wannan ba magana bane haryanzu ke yarinya ce. ldan nace zan dinga nuna miki soyayyar Fateema a fili zaki sha wahala tunda kinga ina nuna mata itama zata fallasa nata. While ke kuma idan kika ce zaki fifita soyayyar twinnie a gurina babu abinda zanji sabida yadda muke dashi kuma baya raye bare ya dinga rama miki kamar yadda zamu yi nida Fateema a gabanki. So kidena kawo wannan abun a ranki yanzu ni zaki saka a cikin zuciyarki ba wani ba.” INdo tajuya baya tare da cewa. 
“I love him tayaya zanki fada kawai dan ya mutu? Dama haka soyayya da amana take idan ka mutu a shafe babin rayuwarka? No gaskiya nayi mai alkawarin bazan manta da shiba har karshen rayuwa ta.” 
Rintsa idanuwa Sadeeq yayi, sam Baiyi tunanin zaiji kishi haka ba amma yaji ransa na sosuwa jin yadda take cewa tana son wani mamaci ba shiba. No wonder mutane suke tsoron auran matar mamaci sabida koyaya zaka yi mata abu sai ta fadesa ta nuna maka yafika, shi kam ya shiga uku gashi wani sanyayyan sonta sai sake shigarsa yake. Ba shakka indai haka Abubakar yaji a baya dole ya rikice yace yana sonta a duk yadda take, dole ya kira ta zuciyarsa sabida yadda a yanzu ta kuma shiga cikin tunanin Sadeeq d’in. 
Juyo toh kiji.” Yayi maganar yana kallon bayanta, a hankali ta juyo sai dai idanunta a kulle suke gam yace. 
Zaki bini idan zan koma kwara state? Karki ce min a’a kinga ina son hakan so nake na 
shirya yadda zanyi tun daga yanzu.” “Kai karatuna fa?!” 
“Karki tashi hankalinki kina dani zan dinga yi miki wannan makarantar duk karyar banza ce. Ki bini kigani zaki sha mamaki in a few days.” 
Kunji wayo… Wai makaranta ce karyar banza dan kawai yana son yi mata wayo 
maxa..maza mutanan mu). “Amma kuma fa malam Sadeeq…” Yayi saurin katseta bayan yajanyo ta jikinsa yana zagaye hands dinshi a kirjinta yace. Shhhii “ba anan zaki dinga kirana malam ba sai munje teburin daukar darasi but wannan gurin kam ki dinga kirana da wani sunan special da zai zama kene kike kirana dashi” 
“Kamar irin su honey, sweetie, heartbeat, July juice, mango, touch light, tomato, vest…..” “Ke.. Ke..! Uhm..uhm duk wannan sunan fa, na waye ne.?.” 
“Toh ai lissafo maka nakeyi sai ka zaba a ciki.” 
“Shine harda su Julyjuice, vest, tomato? You ko..” Ya fada tare da ja mata hanci tayi dariya har hakoranta suka fito murya kasa-kasa tace. “Ashe kaima wata ran kanada kirki..?!” 
“Eh dama kece bakya lura but yanzu ai kin fara gani, tashi muje muyi wanka gashi bamu yi sallah ba.” “Toh amma ka fara yi.” “A‘a tare xamuyi tunda komai tare muke yi.” “Innalillahi nidai gaskiya ka fara zuwa kayi.” 
“Yauwa kin tuna min ma, baki gaya min ba zaki bini muje? Kinga a lokacin nake son dana koma na sake bude wani gurin kema ya kasan ce idan muje kina da naki dakin, bana son business a nan sabida sa ido da nan kawai zan dawo gabaki daya.” Shiru lNdo tayi dan a gaskiya bata son zuwa garin tunda yanzu ta fara iya turancinta, itada ba kwarewa ta gama yi ba kawai yajata su tafi sai sun je shima ya sauya mata tana tsoron Allah tana tsoron butulcin dan Adam. 
“Tunda ba gobe zan tafi ba zan kyaleki kiyi shawara kinji?!” “Toh.” Ta fada ya mik’e ya shiga toilet ya tarar musu ruwa ya dawo, da kyarta bari suka je wanka suka yi tare duk da dakyar ta tsaya. 
Sai da suka dauro alwala sannan suka fito yana rike da ita duk asan samunsa na ganin ta aminta dashi ta saki jiki ta kuma yadda da shidin me sonta ne da gaskiya. Riga tasa ta atamfa da skirt sannan ta shimFida musu sallaya ta bishi da kallo ganinsa a zaune bashi da niyar sa kaya tace. 
“Sallan fa, kona yi tawa?!” ldo ya lumshe tare da hura iskar bakinsa yace “wane kayan zansa.?!” 
“Lallai ni ina na sani, ai kasan fa ko hularka babu a cikin gidan nan. Nidai bari nayi tawa sai ka tafi gidan Fateema kayi acan.” 
Tana fada ta fara kokarin tayar da sallah ya mik’e tsaye tare da tsayawa a gabanta yace. “A‘a bari nasa riga ta ai doguwa ce ta rufe min gwiwa.“ “Nashiga uku haka zaka yi babu wando ji kafafuwa a waje a haka zaka yi sallan? 0h ni lNdo…” 
“Eh aini an hallarta min yin hakan kune dai aka haramta muku yin sallah idan baku lullube jikinku duka ba, Allahu akubar‘.“ 
Taji kawai ya tayar. A ranta kawai ta barsa dan tasan sallar malam Sadeeq bata ba. Suna idarwa sai gasu Haleema tayi sauri zata mike ta fita Sadeeq ya rikota suka yiwa juna kallon ciki ido. “Ina zaki?” “Su Haleema nefa ba kaji muryar su ba.” “Naji amma ai baki tsaya kinyi addu’a ba kamar d’azu, zo kiyi addu’a sai ki fita gurin nasu.” 
Komawa tayi ta zauna su kuma sai rangada sallama suke yi jin shiru yasa Aminatu lekawa dakin. 
“Au ashe sallah sukeyi Yaya ma nanan.” 
Guri suka samu a falon suka zauna suna jiran fitowar su. Matsawa yayi kusa da ita tana addu’a saitin kunnanta yace. 
“Kiyi mana addu’a, amma dan Allah karki rokar min mutuwa da gaggawa.” 
Bata juyo ba tayi murmushi jin abinda ya fada. Shi kuwa tsoran irin addu’o’in da takeyi mai a baya ne yasa shi fad’ar haka yanzu tunda sun fara shiryawa . Kuma mikewa tayi ya janyota tare da waigawa yana kallon kofa sannan ya sumbaci saman lip dinta ta fita. “Aunty Humaira ya gida??” Ta zauna tana kallon Haleema sabida itace me kallonta tunda ta fito, INdo tace. “Ke wai meye ne? Sai wani kallon tuhuma kike min.” 
“Kai aunty Humaira, missing dinki nayi fa kinsan kwana hudun nan duk a cikin hostel nayi su, bama haduwa sai naji kamarshekara nayi ban ganki ba.” “Oho ni kuwa banyi wani missing dinki ba sabida kullum idan baki zoba bacci na nakeyi.” “Aisha..” 
Sadeeq ya kira ta ta mike taje dakin, Tsaye ta gansa yana gyaran hular kansa ta dan tsaya nesa dashi ya janyo ta yace. 
“Zan tafi  anjima zan zo muyi sallama.” Tace “Toh sai kazo.” “Is this all abinda zaki ce min kenan?!” INdo ta dan kallesa kafin tace. 
Toh kayi shaving wannan gemun yayi ma yawa.” “Sunnah cefa cutie amma tunda bakya so zan cire.” “Toh sai ka dawo.” “Kin gaji ne? Na tafi na baki guri ko?“ 
“Ah kawai kaga dai su Haleematu na nan ne.” 
“Okey bari naje na dawo, give me good bye hug.” 
Ya fada yana bude mata hannuwa, ya zata yi dole taje ta rungumesa ya matseta a jikinsa kam ya sake ta suka fito tare, ‘yan kannan nasa suka gaidashi sannan ya fita ita kuma ta zauna gurin su suka sha hira har Aminatu ta dafa musu Indomie suka ci. 
Sadeeq kuwa gidan Fateema ya koma, tare suka yi sallan isha sam be nuna mata cewar gidan INdo yaje ba nuna mata yayi yana kai abinci gurin Anas ya wuce. Suna idar da sallahn isha’i yace mata. 
“Baby na bari naje can gidan nayi mata saida safe, daga can zan tsaya nayi aski ki dafa min tea kafin na dawo.” 
Fateema da shagwaba ‘tasan yana son shagwaba tanajikinsa a tsaye tace. “Gaskiya Baby karka yi aski ni dai ka barshi ina son shi yayi ma kyau.” 
ldanuwa Sadeeq ya zarojin ita kuma abinda tace, INdo tace bata so ita kuma tace ya barshi tana so ya shiga uku. 
“Menene naga ka zaro idanuwa haka? Shikenan jeka aske tunda baka son ka barmin kuma ina so.” 
“Ah baby nina isa, tunda kina so ai dole na barshi uwar gida sarautar gida. Bari toh naje na dawo.” Fateema tayi murmushin jin dadi ganin yana yi mata duk abinda take so. Sai da ta raka shi har gate ya juyo yana kallonta bayan yayi kalar tausayi yace. 
“No bye bye kiss ko? Shikenan nayi fushi.” 
Da gudu ta rikosa ganin zai fice tana dariya ta kamo wuyansa ya sunkuyo da kansa tayi kissing dinshi tare da cewa. “Sai ka dawo karka dade.” “Okey as you wish baby.” Sannan ya Fita yana tunanin yadda zai yi musu. Su Haleema kuwa Sai wajan karfe takwas na dare sannan suka tafi gida ya rage sai INdo kawai tayi sallahn isha’i ta cigaba da gyaran littattafanta. 
Jam-luck tasa hakan yasa yana sanya mukulli kofar ta bud’e. Shiga yayi tana jin motsinsa tayi saurin kwanciya tayi baccin karya. Kallonta yayi ganin yadda ta kwanta akan books din gashi ta kudindine fuska cikin bargo, ya karasa kan gadon tare da sanya hannu ya cire mata shi daga fuskar ta. 
“Oh harma bacci kika yi bayan nace miki zan dawo k0?!” 
Yayi maganar cikin kunnanta, INdo tayi mika alamar wai ya tashe ta sannan ta fara mistsike idanuwa murya a shake tace. “Au ka dawo?!” 
“A‘a ina can.” Ya bata amsa yana kallon fuskarta ta wani maze tamkar daga baccin gaske ta tashi. “Shikenan sai da safe in tafi?!” “Eh sai da safe amma 8:00am zan tafi makaranta fa.” Ba nace kin dena zuwa ba?!” 
“Kai malam Sadeeq weekend fa nake zuwa ita kuma Fateema yau da gobe bata da aiki kuma dama acan kake toh kaga ai ba abin hanani zuwa, ni dai gaskiya zani Ina son school din gashi malamin shima yana son yaga na iya wallahi yana da kirki yana sona.” “Yana sonki kuma?!” Cewar Sadeeq a mamakance, cikin rashin fahimtar fassarar dayayi ma maganar INdo tace. “Eh wallahi har extra lesson yake min.” “What…!” 
“Kai malam Sadeeq dafa ace bankai kaina wannan makarantar ba da nasan wallahi har yanzu baxakai marmarin so naba. Toh meyasa yanzu na shiga kake kuma kokarin rabani da ita bayan akan rashin iyawa 
Be bari ta karasa magana ba taji bakinsa cikin nata. lrin deep nd passionate kissing d’in 
nan ya dinga tura mata har jikinta ya kasa daukarta ta shiga biye mai ba tare da tasan ta iya hakan ba. Cikin rashin sani suka sake kasan cewa da juna musamman Sadeeq da sai daya jima sannan ya gano da tabbacin abinda ya sake faruwa. 
“Na barki… Na barki Humaira kiyi karatunki zan cigaba da baki nawa gudun mawar insha Allahu. I love you with all my heart and soul Aisha please say you love me dan Allah….” 
Shiru lNdo tayi ta kasa fadaji take yi tamkar idan ta fad’a tayi karya dan bataji wani love dinsa ba dazai iya sawa ta gaya masa. “In tafi bakya sona k0?!” 
“A’ah ni bance ba, amma ka tafi dare nayi Fateema najiranka.” “Aisha bakya sona ko? Shikenan.” 
“Toh ina sonka, aini bance bana sonka ba.” 
Agogo ya duba yaga sha biyu saura minti goma, da kyar ya tashi yasa kaya lNdo na kwance idanunta a rufe yaje ya sumbaceta sannan ya tafi ya kullo mata gidan da mukulli. 
Yana zuwa ta dinga kallonsa wanda yasa shi tsarguwa yayi murmushi tare da daukar ta suka wuce bedroom. Romance dinta ya dinga yi har sai da ya nuna mata shima fa yana bukata yasan hakan ne kawai zai wankesa daga zargin da ya hango a cikin idanunta, ganin ya fita birkicewa ne kuma ya tayar mata da hankali ta koma bashi hakuri tana lallashinsa 
sannan yace. “Toh baby ya zanyi bari kawai naje nayi wanka amma kwanakin da kikeyi sunyi yawa har 7days.” 
Tana nan kwance yaje yayi wanka ta hada masa tea yasha sannan suka kwanta bacci bayan sun naniki juna kamar za’a sace d’aya. 
Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ranar lahadi da daddare ya koma gidan 
INdo wanda a lokacin sai da tayi rokon zuwan period amma ina sabida cikin jikinta gashi a gurinta kawai yake hucewa tunda ya dawo har ta farajin haushinsa amma baya damuwa 
bare ya nuna ya gane nufinta.
Abu d’aya yake mata ya dauke hankalinta shine zai ce tazo suyi lesson wannan abun kawai yake sawa yaga ta sakar mai jiki har itama takan faranta masa ta hanyar kwanciya ajikinsa. 
Sadeeq kuwa ta karfi da yaji ya zama makaryaci a gurin INdo sabida tace bata son gemun Fateema kuma tana so dole yace wa INdo inda ake mai askin ne suka yi gobara yanzu gyara gurin suke yi sai sun gama, gashi shi baya son zuwa ko’ina idan ba gurin ba. Ita kuma Fateema ya rasa yadda zai sanar mata da cikin INdo domin zata yi mamakin tayaya hakan ta faru shida baya nan hartsawon 3months. 
Ranar Sunday misalin k’arfe 4:30pm Sadeeq da Fateema suna toilet sai rigima suke yi ya rike mata hannuwa yana cewa. “Bake kika hanani yin shaving din ba dan haka yanzu babu abinda zai sa kice sai nayi tunda kina so.” 
“Nidai to yanzu ka rage please, Allah yanzu ta sake yin yawa.” 
Ganin ta kafe ne yasa shi karba yayi ya rage iya yadda yake barinsa sannan suka yi wanka suka fito. Shiryawa sukai ko wannce cikin shigar daya fiso sannan suka fito zuwa gidan lNdo dan can gidan su Mama zai kaisu ana kawo kayan sa ranar Haleematu. 
“Wait anan inje insa ta fito karku shiga ku shantake.” 
Tashi yayi yashiga gidan ita kuma ta zaro phone d’inta ta kunna data kafin su fito. Yana shiga zaune ya tarar da ita tayi shirinta tsab mayafinta a kan cinyarta yayi sallama ta amsa tare da kai idanunta kansa, harya karasa bata dena kallonsa ba ya mik’a mata hannu ta bashi nata ya dago ta tayi murmushi tare da cewa. 
“Ko kaifa da kayi wani kamar tsoho..” “Okey ko shi yasa ma kallon tsufan da kike min yasa kikaki karbar tayin soyayyata?!” “A’a nidai ban fada ba.” 
Yana rike da hannunta ya durkusa yasa gwiwarsa d’aya a kasa dayar kuma ya ajiye ta kamar dai yadda turawa sukeyi yana faman kashe mata narkakkon eye’s d’insa yace. 
“Humaira kina sona?!” 
Ta kallesa ta tuna ajinsa da matsayinsa da kudinsa da martabarsa tun tana cikin duhun kai amma yazo yana rokon ta so shi duk da har yanzu bata kai matarsa ilimi ba amma itama ta waye dan duk wanda ya kalleta sai yayi tunanin ko ta kammala degree ko tana kanyi. Murmushin jin dadi tayi sannan tace. 
“Ina sonka amma sai kayi kokarin wajan Musanya Zuciya ta daga kan doctor domin har 
yanzu yana cikin Zuciya ta bazan munafince kaba.” 
“Aisha…l Are you in your right sence?l’m your husband but kullum sai kin min zancen marigayi why? Please we should help ourselves in one way or the other. Yanzu dai am asking you kina sona??” “Eh ina sonka.. I love you.” 
Yanajin ta fada ya mike tsaye tare da yi mata alama da tazo su wuce. Harya d’an tafi yaji ta rikosa ya kalleta fuskarta a narke ya tsaya yana zaro ido yace. “Menene kuma?!” lNdo tace “kayi hakuri nafa ce ina sonka.” Rikota yayi yana murmushi sannan ya karbi mayafin ya yafa mata suka fito ya kulle falon still yaga tana kallonsa yaje ya rungumeta yana cewa. “Is okay cutie na yadda but sai kin fara nuna min from now on kinji ko?!” “Toh..” Ta fad’a tare da gyara swagger bag d’in hannunta. ltace ta fara fita shi kuma ya tsaya rufe gidan. Zaune taga Fateema tana danna waya a gaba ta yatsina fuska ganin sai dai fa ta shiga baya sannan taje ta zauna suna yiwa juna kallon yake har ya shiga shima ya zauna ya 
tayar da motar suka tafi. Suna zuwa tare suka shiga lokacin har an kawo kayan anata gani. 
‘Dakin Mama suka shiga nan suka ga su Hawwah aikuwa suka had’u suna ta hirar su. Har aka yi magrib suna tare sai da INdo ta cire mayafi ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa 
taga suna kallonta alamar dai sunyi gulmarta Hawwa tayi dariya tare da cewa. “Su aunty Humaira kuma ashe-ashe….” lNdo ta tabe baki cikin rashin fahimta tace. 
“Ashe-ashe me?!” 
“Wallahi matar broth wannan ciki ne, haba shi yasa sai wani shining kike yi sannan kin 
kuma yin kubul-kubul ga shi kuma ya fita.” 
“Toh ai ba haramun bane ko kin manta a gidan miji nake. Allah sister Hawwah keda Hali 
dubu (Haleema) kun saka min ido ya isheku haka.” 
Tunda suka fara magana Fateema take kallon cikin lNdo, tabbas wannan ciki ne ba teba ba. Kirjinta ne ya dinga bugawa yana mata wani radadi hartanajin tamkarzai fasa mata zuciya. Lallai no wonder taji Sadeeq yanzu baya mata zancen yana son yaga ta haihu ashe tuni yaje ya kunsawa lNdo. Babu wanda beyi magana ba a cikin dakin face Fateema domin idan tace zata tanka babu shakka hawaye zata yi har a samu wasu suce bakin ciki takeyi mata, sai kawai tayi shiru dama a kwance take hakan yasa ta lumshe idanuwa har aka kira sallan isha’i sannan ta fita 
basu sake sanya ta a ido ba har Sadeeq yazo d’aukar su…

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page