HARSASHEN SO CHAPTER 27

HARSASHEN SO
CHAPTER 27
Yalwataccen gida ne wanda komai yaji a cikin sa banda bala”i, kallo daya zakayi wa gidan kasan mamallakin gidan kusan boko ne, 
Akwai wadatuwar arziki a gidan sosai ma”aikatuwan gidan kuwa basu da zama kowa tsaye yake da gaskiya a bakin aikinsa. 
Tankamemen palon gidan kuwa an kawata shi da kayan burgewa na zamani da daukar hankalin mai karamin imani, 
Tahowa akeyi amma baka ganin mai tafiyar sai karar takalmi kake ji, tafiyar da 
kafafuwan kawai zaka kalla kasan namiji ne yake tafiya domin da karfinsa yake lilo saman kasa. Tafiya yakeyi bai dakata ba, bai tsaya ko ina ba sai bakin wata kofa, tsaye yayi a bakin kofar ba tare daya shiga ba, gyara zaman hular saman kansa yayi irin wanda tsohon shugaban kasa yake sakawa. Yaren kanawa suna kiran hular da mai malfa. 
Hannunsa ya saka a Cikin aljihu ya zaro karan sigari { taba } layterya kunna tare da cinnawa sigarin wuta, mayar da layter yayi a aljihunsa bayan ya kunna tabarsa, mugun ja ………… Yayi wa sigarin tare da cire hular kansa, daga kansa yayi sama tare da sakin hayakin. Waye wannan? ‘MANSUR‘ kenan wato ‘MAI GIDA‘ bude kofar dakin yayi tare da shiga ko sallama babu. 
Mama na zaune a palo saman abin sallah, kallo daya tayi masa ta dauke kanta, dan gajeran tsaki yayi tare da zama saman kujera 3sieter daukar kafarsa yayi daya saman daya ya dora, sai girgiza kafarsa yake tare da dan bubbugata, gyara zaman takalminsa yayi sanciyos, kara karkace hular kansa yayi sannan ya sakejan sigarinsa, dukowa yayi daidai 
fuskar Mama sannan ya fara magana, yana magana hayakin sigarin yana fita daga cikin bakin sa da kuma hancin sa. 
Mama tsakani da Allah ni ba”amin adalci a gidan nan gaskiya, wannan ai tsabar kiyayya ne sai kace ni shege nake a gidan nan? Kawai ki fadamin idan agolanci kika zo dani sai in tafi neman ubana, 
Da gefen hijabinta ta dode hancinta tare da cewa kaga fitarmin anan ni bana san warin sigari kuma kullum na fada maka amma baka tashi shaye shayen iskancin tabarka sai kazo gabana, dariya Mansur yayi sosai tare da kara jan sigarinsa yace, ai bakiga komai ba madamar ba”amin abinda nake so ba na rantse da Allah kema babu zaman lafiya sai kin bani amsata. 
Cikin damuwa Mama tace kaje ka samu Babanku, cikin daga murya Mansur yace da Allah dakata, wane naje nayi masa magana bayan a gaban idonki, kinsan komai kuma duk kece kika kulla komai wannan ai rashin tsoron Allah ne saishi a daukeshi kawai a turasa kasar waje ace acan zaije ya rikayin kasuwanci? Duk garin nan wane ne ya tafi? Saishi, 
Idan gaskiya ne abun a hadamu dukanmu a tura mu mana. 
Cikin rarrashi Mama tace haba dan auta na, kayi hakuri kaima zaka je, Mansur yace 
wallahi babu wani, bayan haka kikace ni dan iska ne? Kinsha banji ki ba? Ina jinki kikace, ai kin dauka bacci nakeyi idona biyu kyaleki nayi kuma idan dai har ana san zaman lafiya a dawo dashi ko kuma a hadamu mu dukanmu mu tafi yana can yayi kudi kullum sai yazo 
yana wani daddagawa mutane kai shi dan kasar waje. 
Shigowar Baba yasashi ya maida maganar gunguni, abinda yake cewa a maganar tasa shine, Allah ya sakamin Allah yasa ma baku ne kuka haifini ba, yana maganar yana kada kansa irin na yanajin masifa. 
Cikin bacin rai Baba yace, wallahi da nafi kowa farin ciki dan duk uba na gari yana san da na gari nidai haihuwar ka Mansur ban dace ba, da ana canzo da a duniya na rantse da Allah dana canzo ka, cikin rashin kunya Mansur yace Eyyy a canzonin mana, nima dana samo iyaye masu adalci. Ya karasa maganar yana turo baki tare dajan tabarsa. 
Tsoki Baba yayi tare da cewa Allah ya shiryeka, yana fadin haka yayi gaba abunsa ……. , Mama tace Mansur ka daina irin wannan dabi”un bana so na fada maka, mikewa tsaye yayi yana cewa ai dama dole kice bakisan haka tunda kin samu an turashi yaje can ya samu 
kudinsa an kawo miki madara da bredi an toshe bakin fadin gaskiya. 
Fita yayi daga cikin dakin yana gunguni, dakin matar babansa ya nufa, wannan da suka zauna gidan yari da Shalele, itama babu sallama ya shiga, palo ya zauna saman kujera tare da fara kiranta, gwaggo ………………. , da sauri ta fito daga ciki tare da cewa lafiya Mansur? 
Gwaggo nifa ba”amin adalci a gidan nan fa, wai taya za’ayi a dauki Yaya Bashir ace shi kadai za’a tura kasar waje saboda ni an rainamin hankali, banda ko sisi ban ajiye ba, ban bawa kowa ajiya ba, idan na tambayi kudi a gidan nan an fara tambayana me zanyi dasu sai kace karamin yaro? Yanzun abun Allah ya amsa idan barayi sukazo gidan sukace na basu kudi wallahi gwaggo idan nace banda su wallahi tsinannan duka zasumin fa, 
Murmushi gwaggo tayi tare da zama saman kujera lsieter tace haba Mansur dina yaushe zaka daina wannan halin iye dana? Idanma barayi sun maka duka ai sai Allah ya saka maka. Kuma ma kake maganar Bashir dan uwanka ne fa, idan ya samu ai kaima ka samu, 
Mansur yace haba gwaggo na samun banza can zaije ya aurojar fata ya manta dani daga shi sai matarsa sai “ya”yansa kawai nima kiyi magana a kaini tunda ke na lura kinfi Mama kirki, 
Gwaggo tace to karka damu zanyi magana in Allah ya yadda, amma ka daina irin wannan 
halin wannan shine ake kira da hassada bana so ka zama mai hassada kaji dana? To naji bani kudi banda k0 sisi don Allah. 
Ba tare da tayi magana ba ta koma ciki ta dauko kudi ta bawa Mansur, godiya yayi tare da cewa Allah ya rayaki gwaggo, nasan idan waccan Mamar ta mutu mun samu sauki, da ganinki zakiyi adalci gwaggonmu Allah yasa kada ayi miki kishiya amma Allah yasa ayima Mama tunda bata tsoron Allah. 
Yana fadin haka ya fice daga dakin, tunda ya fito duk wani wanda ke aiki gidan saida yasha jininjikinsa dan Mansur baida imani haka kuma baida tausayi, kan kowa a kasa saboda masifarsa. 
Wucewa yakeyi can kuma saiya tsaya! Ba tare dayajuyo ba yace kai an baku albashinku kuwa? A, a, suka bashi amsa, Mansur yace to idan an baku ku kawo min kasona dan gaskiya banda kudi, wannan dama shine aikinsa duk wanda aka bawa albashi to fa lallai saiya fitar dashi ……… 
Tou ranka ya dade, ci gaba yayi da tafiya ba tare daya sake cewa komai ba, kowa yabi bayansa da kallo ji sukeyi dama shi aka dauke ba Bashir ba. Dan haka nan kana wucewa ta 
gabansa duk iyakar ladabinka saiya ci mutuncinka ko abinci ka ajiye masa saiya ce baka iya ba. 
Maryam kuwa tana fitowa daga cikin kicin da sauri ta koma baya dan ganin Mansur, a tunaninta bai ganta ba, amma sai taji yace zo nan munafika, cikin ladabi ta taho tare da rike kitsonta guda biyu ta dawo da kitson ta gaba wanda saida ya wuce saitin cibiyarta, kanta a kasa tana rike ta duka kitsonta guda biyun ta durkusa a gabansa cikin ladabi tace 
kayi hakuri wallahi bansan kana tahowa ba, 
Kina da kudi ne? Mansur ya tambayeta, ita dai tasan bata isa tace masa bata dasu ba dan tasan ubanta zaici, cikin ladabi tace bara dai na duba, ke bana san sakarcin banza zan samu ko A, a? Maryam tace banda kudi “yar labai, cakumo ta yayi tare da mikar da ita tsaye ke dan uwarki nine kike fadama baki da kudi ne iye? Ya karasa maganar tare da zaro idanuwa, 
Cikin rawarjiki tace bara na dauko maka, sakinta yayi tare da cewa shegiya kinzo 
agolanci a gidanmu wallahi badan inajin kunyar gwaggo da wallahi dasai kin rika biyan 
kudin haya tunda ba gidan ubanki bane ba. Maza kawo min kuma masu yawa nake so na fada miki, da gudu ta nufi dakin mahaifiyarta wato gwaggo, ba tare da tayi ma gwaggo magana ba ta shiga ta dauko kudi bata bari gwaggo ta gani ba tayo waje ta bawa Mansur, ansa yayi a tsiyace tare da cewa da yawa nace miki amma saboda tsabar kin rainani shine 
kika kawomin dan kadan k0? Kayi hakuri insha Allah zan ajiye maka masu yawa wata rana. Kwafa yayi tare da wucewa, Maryam tabi bayansa da kallo tare da addu”ar Allah ya rabasa da hassada. 
Mansur kuwa duk inda ya zauna baida aiki sai tsinewa uwar Bashir albarka, anyi munafirci an turashi wani kasuwanci munafirci haryanzun bai dawo ba, shi yana can ya samu kudinsa amma shi an barshi nigeria yana shan wahala, Wannan hali nasa Mama tayi bakin kokarinta ta rabashi dashi amma ta kasa, dan haka ta saka masa ido tare da binsa da addu”a, 
Gwaggo kuwa da tayi ma Baba maganar Mansur cewa yayi ta fita daga harkar Mansur idan kuwa ba haka ba zata hadu dashi. Dole ta hakura ta fita daga wannan zance. 
Bayan kwana biyu kuwa Mansur ya samu Mama da maganar tafiyarsa Mama tace baya zuwa k0 ina duk abinda zaiyi yayi dan ubansa, Mansur yace haka kika ce ko? Mama tace Eh ko an fada maka inajin tsoronka ne? Mansur yace to dama ya za”ayi ma kiji tsoro na tunda ni banda kudin sayen madara da tsire, dama tunda naga kina wani kwankwantar da kai idan kikaga wannan munaflkin ai nasan kema an gama dake. Niko dan ubanshi bai isa ya gama dani ba kudi inaji a jikina ni nan da kika ganni wallahi nimai arzikine, wannan abun yasa duniya taki zama lafiya ai neman kudi gareni ya zama wajibi tunda yanzun duk an daina abu domin Allah, idan kana da kudi kaine kake zama uwa ka zana uban iyayenka, nuna Mama yayi tare da cewa daga yau karki sakemin magana don Allah shima Baban idan ya dawo ki fada masa tunda dai duk abin ya zama munafirci. 
Mama tace idan mun daina maka magana ance zamu fasa rayuwa ne? Jinjina kai Mansur yayi tare da cewa ai gidanma zan bar muku gara nayi tafiyata can, nasan idan nayi kudi nan zaki rika cewa don Allah a nemo Mansur dana, shiru Mama tayi ta kyaleshi fita yayi daga cikin dakin ya nufi dakinsa. 
Tattara kayansa ya farayi ya jibga a trolly bag abun matafiya ne yau, haka ya tattara duk abinda yake so ya fito, dakin Baba ya nufa wanda Mama taje ta fada masa, yana zaune saman kujera yana karatunjarida, Mansurya shiga kai tsaye babu sallama, cikin rashin 
kunya yace mufa zamu wuce, Baba yace tou Allah yasa ku sauka lafiya, 
Haka kawai Baba ya fada ba tare daya kalli Mansur ba yaci gaba da karatunsa, gyara tsayuwa Mansur yayi tare da cewa kudin mota zaka bani, Baba yace kaika nemarmin kudin ne? Mansur yace ai saboda ni Allah ya baka kudin, Baba yace su iyayena da Allah ya basu kudinsu ai baro musu abunsu nayi ba nazo na nema nawa? Amma tunda kai dan kararramin dan iska ne bara na baka gudamawa, 
Laluba aljihunsa ya farayi dan basa kudi sukajiyo muryar Bashir yana gaisawa da mutane dan dama idan zai dawo baya fada dawowarsa kawai yakeyi kansa tsaye. Ciro kudin Baba 
yayi ya bawa Mansur tare da cewa ga tawa gudamar na baka a daidai lokacin da Bashir yayi sallama ya shigo, 
Cikin farin ciki ya nufi inda Mansur yake tsaye tare da rumgume dan uwansa, yana cewa kallarni na dawo, banza Mansur yayi masa kamar baiji sa ba, girgiza sa Bashir yayi tare da cewa Mansur ……… Baba yace rabu dashi, cikin damuwa Bashir yace anyi masa wani abu ne. Baba yace shi nan daka gansa turkeni yakeyi wai saina turasa ya isko ka, murmushi Bashir yayi tare da cewa Baba ai babu komai sai mu tafi tare dashi. 
Baba yace ai zamanka da Mansur bazai yuwu ba, murmushi Bashir yayi tare da cewa babu komai Baba, gaisawa sukayi da Baba da Mama sannan yaja hannun Mansur suka fita, har a 
lokacin bakin rai’ yakeyi kamar zaici uwar Bashir, 
Dakin gwaggo suka nufa itama gaisheta sukayi sannan suka fito suka nufa dakinsu. A palo suka zauna Bashir yace dan uwana miye damuwarka? Idan nine nayi maka laifi to kayi 
hakuri insha Allah bazan sake tafiya na barka ba, 
Kayi hakuri kuma ka shirya insha Allah dakai zan koma idan zan tafi har yanzun Mansur baiyi magana ba, amma a ransa yanajin bakin ciki sosai Bashir yayi kudi ya barsa shi yasa 
iyayensa suke sansa amma shi dan baya da ko sisi ake wulakanta sa. 
Duk maganar da Bashir yayi ma Mansur idan bango ya ansa to Mansurya tankawa Bashir, kuma tsarabar daya kawo kowa na gidan yaci amma Mansur kirikiri yaki yaci, nashi 
dana sakawa, baiyi amfani dashi ba. Satin Bashir daya ya tattara dan komawa duk fushin da Mansur yakeyi dashi yaso suje tare amma Mansuryace bazaije ba kowa tashi ta fisheshi, Bashir yayi juyin duniya su tafi amma sam Mansuryace bazaije ba, tunda abun “yar banbanci ne, 
Bashir kuwa daya tashi tafiya kudi masu yawa wanda hankali da tunani baya dauka ya bawa Mansur duk bala”in talaucin da yake kartarsa cewa yayi bazai amsa ba, Bashir baiji dadi ba k0 kadan haka ya hakura ya tafi da wannan tunanin a rayuwarsa. Shi kuwa Mansur ya tashi hankali kudi ko ta ina suzo masa, dan haka yacewa Mama da yasan inda ake tsafin neman kudi wallahi da ita zai bayar a bashi kudi, Idanuwa Mama ta zaro tare da cewa Mansur ni? Yace ke mana wallahi harda Baba zan hada duk a yankemin kawunanku a bani kudi tunda dama kana aihuwar “ya “ya kayi banbanci. Shi Yaya an bashi 
kudi yayi kasuwanci amma ni an barni a haka sai garanranba nake a Cikin gari. 
Kuma da ina da kudi ko dan yatsa babu wanda ya isa ya nunamin amma dan banda shi yasa ake kyamata, dan gajeran tsaki yayi tare da saka hannunsa a aljihu yajawo sigarinsa ya cinna mata wuya yaci gaba da janta abun sa, 
Murmushi Mama tayi sannan tace bakin halinka yaja maka, iyayenka ma baka san darajarsu ba bare kasan darajar wasu, kalli, kalli kacocin dakejikinka, kalli askin kanka dan 
Iska kakalli wandon Jikinka, kullum saidai kaje kajawo mana fitina ka barmu da ramuwa, kana so ayi da kai ka zama na banza? Ka zama na kirki kaga idan Babanku bai gina maka rayuwarka ba, sakaran banza shashasha kidahumi da baka san inda duniya ta nufa ba? Kankance idanuwa yayi ‘tare da cire sigarinsa da sauri daga bakinsa yace ni kike zaki? Mama tace na zageka ko zaka rama ne? Jinjina kansa yayi tare da cewa kici gaba abun kunya nake gudar miki wata rana. Gyara tsayuwarsa yayi tare da dora kafarsa ta baya yaci gaba da shan tabarsa. 
 wata zukekiyar buzuwa ce mai dan banzan kyau na burgewa da daukar hankali tayi sallama tare da shigowa cikin dakin, tunda yaji muryarta ya gano ko wace ce, ba tare daya kalleta ba yace shegiya mayya wato kinji labarin yazo gari har kin wani kwaso jiki kin taho, to ai sai a samu damar komawa ya tafi. Kallonta yayi tare da cewa ni wallahi tunda nake a duniya ban taba ganin karyar mace kamarki ba banza marar aji da kike kwasojiki har gidansu saurayi kizo zance. 
Mama ce tace Hauwa’u sannu da zuwa maraba dake, ranta a cakude ta amsa, shi kuma Mansur ya dake lamba yaci gaba da cewa aifa budurwar dan so tazo dole a ririta ta, dan kar taje ta fadawa Yaya tazo an mata wulakanci mutum yaji didif, wallahi Mama kiji tsoron Allah duk dai abinda zakiyi Allah yana kallonki, 
Bata kalleshi ba ta tashi dan kawowa Hauwa”u ruwa tasha, saida ta kawo mata ruwa da lemu, Mansurya duka ya dauki lemun tare da balle murfin yayi hanyar fita yana cewa lemun daya ne kike ta boyo ai naga wanda zaki bata tasha ina nan kofar gida yau saina ga yanda za”ayi kuma idan ta fito waje ta sameni inci uwarta wallahi, dan daga ita har Yayan ni banajin tsoron kowa. Raba idanuwa Mama tayi, tayi dan bata da wani lemun shikenan ya rage mata a duniyar nan, dole ta hakuri tadan basartanajan Hauwa”u da fira, ita kuwa Hauwa batajin firar hankalinta ya tafi wani wuri daban tana tunanin yanda zataci uwar Mansur dan sai tayi maganin sa, idan kuwa ta kuskura ta shigo gidan Bashir a haka tasan aurensu babu inda zaije domin shidai yana san dan uwansa, sannan bai hada Mansur da kowa ba kuma kullum idan Mansur yayi mata abu ta fadawa Bashir cewa yakeyi tayi hakuri Mansur yaro ne, shi bai taba dauka iskanci bane kawai dai yana barin abun a matsayin yarinta, dan idan ba yarinta ba ya zaka rika jin hassadar dan uwanka uwa daya uba daya, ajiyar zuciya ta sauke tare da daukar kudiri a rayuwarta. Ruwan ta dauka tasha tare da cewa Mama zan tafi, cikin damuwa Mama tace tun yanzu? Hauwa’u tace wallahi kuwa a daidai lokacin data mike dan ko gaisuwa basuyi ba, Mama ta 
tashi tabita dan rakata kar Mansuryayi mata wani abu, 
Mansur kuwa yana tsaye da bokitin ruwansa yana jiran zuwan Hauwa”u yayi mata wanka dashi, Mama tana gaba Hauwa”u na bayanta, Mama tana isa kusa da Mansur ta faffala masa mari tare da cewa kasan Allah na kusa tsine maka albarka, cikin fushi Mansur yace to ki tsine nace ki tsine albarka daga tsinewar sai kuma akayi me? Yana maganar 
yanayi kamar zai kai dukawa Mama, Saida Mama ta rikesa sannan Hauwa”u ta fita da sauri daga gidan, shi kuma daga murya 
yayi yana cewa zan kamaki shegiyar nan wallahi koba yauba saina ci uwarki na kara ganinki gidanmu, 
Mama bata masa magana ba ta shige ciki ta barshi yana ta zage zagensa, da gudu Maryam tazo ta wuce ta gabansa yace zo nan dan ubanki, wato labewa kikayi kika kalla ana 
dukana ko? Kin tsayawa tayi ta ruga da gudu dan tasan duka zai mata bana wasa ba. 
Fita yayi daga gidan ya nufi dandalin abokansa suma dai duk “yan tashar ne kamarsa, wuri ya samu ya zauna tare dayin jigum yana nazarin duniya, Abas ya kallesa tare da gaggabewa da dariya yace maza sunji guyama, nazo zan shiga cikin gidanku na ganka ana marinka, daure fuska Mansur yayi tare da shafa inda Mama ta maresa sannan yajinjina kansa yace ai bari idan na kama yarinyar nan wallahi uwarta zanci, Abas yace mudin kuma? 
Ai harna zane shegiya kaga takalmanta nan ma na kwace, 
Shiru Mansur yayi bai sake magana ba, Abas yace nifa rashin kudi ya fara isata, Mansur yace nima dai, Abas yace to miye mafita? Mansur yace mafitar dai daya itace aka saba itace kuma ita za”ayi, dan dama haka sukeyi idan suka rasa kudi wai sai suce anyi garkuwa da Mansir sai Baba ya bada kudi a ansoshi. Wannan shine sana’arsu duk bayan wata biyu, tun abun yana damun Baba harya daina damuwarsa. Tashi Mansur yayi ya nufi gidansu Abas, su kuma suka shiga cikin gidansu da gudu suna kuka wiwi kamar anyi musu wahayi da sakon zare lumfashinsu. 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page