MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 24

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 24
Koda sukaje kauyan Sani bakaramin mamaki Fateema tayi ba da ganin gidan su lNdo da kuma kauyan da suke, lallai Allah ya daukakata daya aura mata Abubakar har kuma tashiga wannan uban gidan wanda yafi nata komai da komai. Basu jima ba Sadeeq yace zasu koma ya bada dubu ashirin Inna da malam Hamza suka dinga yi mai godiya amma lNdo fateema kawai tayiwa sallama ta koma gida ‘yan garin suka cigaba da zuwar musu gaisuwa. 
Rayuwa gaba daya ta sauyawa INdo komai yayi zafi tunda ta dawo kauyan Sani komai nata ya canza, tana takaba a gidan su kamar yadda malam Hamza ya bukata sai dai itace inzata bayan gida sai abata sanda da wuka wai ta tafi da ita ko idan zatayi bacci toh ruwanta a buta da wuka wai mijinta yana biye da ita duk da cewar ba’a gidansa takeba. Sannan ta dinga tafiya a hankali karya tadiyeta. wayyace haka ake zaman takaba?wannan ba musulinci ya koyar dashi ba kawai mutanene suka maidashi al’ada har hakan ya fara zama kamar ibada. Satin INdo biyu a gida lokacin sati uku kenan da rasuwar Abubakarsu Mama sukaje garin domin ita sam hankalinta ya kasa kwanciya, a zaure suka tarar dasu lNdo suna tsinkar zogale harta fara komawa kalarta ta dah gashi dai jikinta da kaya masu kyau amma babu tsafta tunda ta dawo sau biyu tayi wanka wai ai duk cikin takaba ne. su Hawwah suka dinga kallonta cikin tsananin mamaki ita kuwa ta kasa boye farin cikinta da ganinsu. 
Bayan sun gaggaisa ne Mama ta kasa yin shiru ta kalli lNdo dake tsakiyarsu Haleema tace. a “Aisha ya naganki haka?duk kinyi wani iri anya kina wanka da kula da lafiyar jikin ki kuwa?” Cikin rashin damuwa tare da ita INdo tace. 
“Ai Mama nida nake takaba ai ance ba’a wanka sai dai a sati sau daya shi yasa ma banayi…” “Subahanallahi inji waye ya gaya miki haka?” 
INdo tace “Su Inna ne.” 
Inna nacan tana kokarin hada dambu ta samu tabasu suci Mama tace. “Zonan Aisha na shiga uku ba haka ake yi ba a musulunci, ba haka qur’ani ya gaya mana ba.” Tashi lNdo tayi zuwa kusa da Mama ta zauna Mama na kallonta cikin tsananin tausayawa ta janyo ta jikinta tace. 
“Mecece Takaba Aisha?!” INdo tayi shiru sai faman wulkita idanuwa takeyi Mama tace. 
“Aisha Takaba dai itace Zaman da mace zatayi bayan rasuwar megidanta na wadansu kwanaki sanannu a cikin gidanta batare da tayi ado da kwalliya ba, ba kuma data kuma yin wani auren ba, ko sanya dukkan abinda zai ja hankalin wani ajikinta ba . Anan Takaba ta sha babban da lddar saki, shi yasa naso a barki a can domin dan zaman da kikayi a gidan mu na gano cewar kinada gyara a cikin rayuwarki. Banda iyayanki sun kafe kancewar gara kitafi babu me zuwa ya zauna dake a cikin gidanki sannan kowa yasan mijinki ya rasu gashi idan kikaga Sadeeq wani tashin hankalin ne da bazan bari ba wallahi yanzu gashi kinzo nan sun kara dilmiyar dake cikin wani duhun kan. Wallahi mahaifinki gaddama garesa Aisha ba yadda ba’ayi dashi ya barki ba yace dasun dawo bakwai za’a tafi dake sabida baya son abinda kikewa Sadeeq. Shin kinsan Gwargwadon kwanakin Takaba a musulunci Aisha?” 
INdo ta girgiza kai alamar a’a Mama ta dago ta daga jikinta tace. “Alokacin da mutun ya rasu, to zai bar iyalin shi ne a dayan hali guda biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to Takabarta itace tayi Wata hudu da kwanaki goma Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bak’ara _Kuma dukkanin mazan dake rasuwa daga cikin ku subar matayan su, to matan zasu zauna wata hudu da kwana goma aya ta dari biyu da talatin da hud’u 234…_ To amma idan ya rasu ya barta dajuna biyu a wannan lokacin karshen Takabarta shine ta sauke abinda take dauke da shi koda kuwa ranar daya rasu ne ma’ana ta haihu ko tayi barin cikin. Misali ya rasu 10:00am na safe ita kuma ta haihu 10:05 na safiyar, shi kenan ta kammala takabarta, idan wani ya gani yace yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya dauru tana karbar gaisuwa ana daurin aure Dalili kuwa shi ne. fadin Allah (s.w. a) a cikin Suratut- aya ta 4_Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauke abinda suke dauk’e dashi_ da kuma Hadisin Subai’a Al-aslamiyyah, Ita ta kasance tana auran Sa’ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir dan Lu’ayy, yana daga cikin wadan da suka halarci yakin Badar, sai ya rasu yabarta a halin bankwana tana da juna biyu, bata kojima ba bayan rasuwar shi saita haihu, a lokacin data kamma biki sai tai kwalliya, sai Abu-Sanabil Dan Ba’akk yazo wurinta, shi kuma ya fitone daga gidan Abduddar, sai yace da ita Lafiya naga kin cancara ado haka, ko kina son kiyi aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yiba, harsai kin yi wata hudu da kwana goma. Sai Subai‘a tace Yayinda ya fada min haka maraice nayi sai na tattara kayana naje wurin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya ban amsa da cewa ai na kamala Takabata tun lokacin dana haihu, ya ban dama da inyi aure a duk lokacin da naga dama. Yanzu ke Aisha kina da ciki?. INdo ta kalli Yaya Hawwah kafin ta maida idonta kan Mama tace “Wallahi ban sani ba nima.” Mama ta sake kallonta sannan tace. “Kinyi al’ada sanda kika dawo?!” 
INdo ta sunkuyar da kai sannan tace, “Ai yanzu ma haka inayi yau kwanana biyu kenan.” 
“Hazbunallahu wani’imal wak’il, yanzu duk da kina wannanjinin Aisha bakya wanka?!” INdo tayi shiru jin yadda Mama tayi magana da alama abin mamaki ya bata da haushi ita kuma ya zatayi tunda ance mata haka akeyi. Inna ce ta shigo tana tayi musu sannu tare da kawo musu ruwa a kwanan shan ruwan malam Hamza, tsabtar kyawun kwanon da yadda ruwan ciki yake garai-garai abin sha’awa shine ya sanya su Haleema shan ruwan gidan. 
Zama Inna tayi suka sake gaisawa Mama tayi gyaran murya bayan tace su Haleema su fita, suna fita tayi murmshi tare da cewa. “Dama munzo ne mu gaida ku sannan zamu tafi da Aisha za’ayi mata wani gwajin ciki sabida shi marigayi yace yasa mata wani abu wanda koda tana da ciki toh bazata dena jinin al’adaba toh yanzu shine zamuje a duba agani kar abar mata abu ba’a saniba ko yana amfani nan da kwana biyu za’a dawo da ita kinsan likitocin nan da kyalekyale.” 
Mama ta kifa Inna domin yanzu so take ta tafi da INdo can. cikin rashin damuwa Inna tace “Allah sarki ai babu komai an zama daya bari na aika a kira malam dama shine ai ke hanawa da yaji yadda takeyi idan taga shi dan uwan marigayin.” Fitowa tayi ta leka waje ta samu yaro yaje ya kira Malam Hamza a gurin sana’ar Sa. Tare da ila suka dawo tunda yaga mota yasan bak’i sukayi yana shiga kuwa Inna tace Maman marigayi ce tazo, dakin ya shiga suka gaisa da Mama Inna kuma ta kawo mata dambu ta kaiwa su INdo ma. A nan Mama ta kuma tsara malam Hamza yayi jim sannan kamar bazai yadda ba sai kuma yayi murmushi yace. “Toh ai dama ni hajiya dalilin daya sa na kafe kan cewar saita dawo nan, gani nayi yadda 
shi Saddiqu suke tsananin kama dashi marigayin. Sannan tun a gurin gaisuwar naji ana 
zance ta fara rikesa tana cewa be mutu ba harma sun fara samun sabani itada Saddiqun wannan dalilin yasa nace dole abani ita mu dawo nan zaman lafiya hajiya ai yafi zama d’an sarki. Amma yanzu tunda akwai wani dalili wanda kuma kune kuke da hakki akai toh saita shirya ku tafi idan an kammala yi mata sai a dawo da ita ai duk an zama guda..”
Wani farin ciki ya lullube Mama sai ta share hawaye gani takeyi tamkar Abubakar din take yiwa a zahiri. Malam Hamza ya dinga bata hak’uri kafin ya tashi ya Fita, gurin su INdo yaje yace ta shirya zasu tafi da ita. Wanka Mama tace tayi sannan tayi tasa kaya Mama ta girgiza kai domin duk kayan na kwalliya ne babu wanda aka ce na takaba ne dole idan sunje tasa a dinka mata wasu marasa style. Babu wanda yasani don Mama tace kar a fad’awa kowa kawai idan an tambaya tana Ina suce tana gidan su marigayi amma karsu sanar da kowa akwai abinda za’ayiwa INdo suka tafi cikin farin ciki da fatan alkairi. 
Tunda suka maida ita Mama ta dakatar da Sadeeq zuwa gidan tace koda itace batada lafiya bata yadda ya shigo ba bare hakan nan. Haka kuwa Mama taci gaba da kula da INdo har aka yi arba’in din marigayi Abubakar sannu a hankali kuma Mama tana bibiyar al’amranta na addini tana gyara mata sannan tana kara nusar da ita abubuwa wadanda mafi akasari suke kara tunawa INdo mijinta soyayyarsa kuwa bata tabajin ta kankare koda digo daya neba, bata komai sai dai taci tasha tayi bacci, idan kuma su Haleema na nan sai suyi hira dan turancin da suke yi jefi-jefi itama ta dan fara tsintar kananun tana hadawa da wanda Dr yake yi mata sai dai dakyar take iya rikewa dan sai tayi take rike kalma d’aya a kwana biyu ko uku sannan take sake fahimtar wata word din. 
Kusan kullum sai Malam Hamza ya bugo musu waya tunda suka zo sadakar arba’in ya karbi number abban su Sadeeq kusan kullum sai ya bugo musu yaji wai ko an cire mata abun sai suce a’a likitocin sun kara musu kwanaki da haka har INdo tayi watannin takabar ta wanda har lokacin Sadeeq baya shiga cikin gidan su dan ma Allah ya temake sa yana tafiya kwara state dan wannan tafiyar tasa da Fateema sukayi sabida yana shan wahala. Ana sauran kwana biyu INdo ta kammala takaba su Sadeeq suka dawo, Fateema ce kawai taje gidan shi kuma su Mama suka fita parking space suka gaisa yajuya Ranar da INdo ta kammala takaba Abba ya kira Sadeeq yaje ya kaisa Sumaila suna zuwa ya samu malam Hamza bayan gaisuwa Sadeeq na mota a zaune ya bugawa Fateema waya suna hirar soyayyar su dan haka suke tamkar zasu cinye junansu Abba ya kalli malam Hamza yace. “Toh malam Abubakar dai Allah ya dauki rayuwarsa a lokacin da yake tunanin ya fara rayuwa, ya tafi yabar matarsa yarinya danya yau gashi Allah yasa ta kammala takabarta kamar yadda addini ya tanadar. A zahirin gaskiya ba wani abu da marigayi ya sanyawa Aisha a jikinta, me dakina ce taga bazata iya barin muku Aishan ba hakan yasa tayi muku dabara kuka bata ita mu kuma duk muka hade muku kai muka nuna cewar eh lallai haka ne abinda ta fada.” 
Malam Hamza yayi murmushi tare da cewa. “Ai munyi mamaki har muna tunanin kila abin kin flta yayi ashe soyayya ce tasa kukayi hakan ai bakomi alhaji mune da godiya da baku nuna kyama a garemu ba, Habubakar shine sila hakan yasa bazan gajiya dayi masa addu’ar samun ni’ima a cikin makwancinsa ba, alhaji Allah yajikansa yayi masa rahama mun gode madallah.” Ba komai malam Aisha ma ai ‘yata ce, sannan kuma babban abinda ke tafe dani shine. Kaf ‘yan uwana da masu dakina suna tausayawa Aisha, yarinya ce danya yau gashi Allah ya jarabce ta idan aka barta zata Shiga layin zawarci, sun hadu sun had’e kai wajan ganin bazasu iya bari matar dansu dan uwansu abokinsu ta zauna a haka ba suna ganin yi mata hakan kamar basu rufawa Abubakar asiri ba hakan yasa ko wannen su yazo min da kokan barar su na cewar mezai hana a mayeta da abokin haihuwar sa, ma,ana mu hadasu aure da Sadeeq domin rufin asirin mu gabaki d’aya sannan munsan Abubakar zai yi alfahari da wannan abun.” 
Malam Hamza yayi shiru kafin yaje ya kira Inna ya kuma kira amininsa malam kallah suka zauna, Abba ya kuma maimaita musu zancen auran INdo da Sadeeq Inna dai bata ce komai ba tace sune maza masu d’aura aure dan haka ita addu’a ce kawai tata. Bayan Inna ta koma gida malam Hamza ya amince wasu mutanan suka zo a gurin aka daura auran lNdo da Sadeeq Abba ya bada sadaki dubu ashirin Sadeeq yana mota a zaune duk wainar da aka toyawa besani ba har Abba yayi sallama da mutanan garin ya shiga mota Sadeeq din ya ajiye wayar suka tafi… 
Hmm ga indo ga malam sadeeq
Marasa aure wai ya sanyinnan ne abinfa ba sauqi sanyin yayi yawa kaiiiiii

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page