GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 2

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 2
Zama tayi a gefen da Kursiyya take, ta saka hannunta mai dauke da zara-zaran akaifu ta tallabo kan Kursiyya, ta tsuke fuskar‘ta, yayin da wani irin ruwa mai kama da jini ya rinka furtsowa daga bakinta yana zuba bisa cinyar Kursiyya. Da karfi ta girgiza kanta, hakan ya sa gashin kanta ya sake barbazuwa har bisa fuskarta, abun mamaki, sai ga gashin na zuzzubewa daga bisa kanta yana sauka bisa jikin Kursiyya. Tuni Kursiyya ta gama kidimewa, ta saka tafukan hannayenta ta kare fuskarta dasu. Ko kadan bata son kallon halittar dake gabanta. Ta rasa dame zata alakanta ta dashi. Shin aljana ce ko fatalwa? Tsoron bakar halittar ya gama wanzuwa a cikin zuciyarta. Baki daya gabban jikinta karkarwa suke, yayin da fitsari ya gama wanke kaf ilahirin kafafuwanta. Da ‘yar yatsarta manuniya ta nuna Kurasiyya, sai ga akaifar jiki tayi tsayi sosai har bisa kuncin Kursiyya. Tace
“Kinga wannan ruwan mai kama da jini dake fitowa daga cikin bakina? To haka kema yawu zai dinga dalala daga bakinki a kodayaushe, yawu mai wari, wanda kowa zai kyamace ki a kansa, ciki kuwa har da ‘yar taki da kika zalunce ni saboda ita.Ta runtse idanuwanta, sannan taci gaba da magana, “Kin ga yadda baki daya yalwatacciyar sumar nan ta bisa kaina ta zazzage? Haka taki za tayi kema, sai kanki yayi kwal tamkar na maza. Kursiyya! Kar ki taba tunanin a iya nan abun zai tsaya. Na miki alkawarin gushewar farin ciki daga rayuwarki har abada. Na miki alkawarin sai kin rasa dukkanin walwalarki. Yadda kika raba ni da rayuwata, kema sai na raba ki da taki, ki kasance a wahalce fiye da yadda kika yi mini.”Tana gama fadin haka ta mike, cikin dakikun da basu wuce biyu zuwa uku ba ta bace bat daga dakin. lhu Kursiyya ke son yi, sai dai a banza, saboda babu wanda zaiji ta. Dakin da take kwana yana da tazara sosai da inda mutane suke. Bata san ya zata fasalta halin da take ciki ba, ba tasan yaya zata bada labarin wannan mummunan al’amarin da ke shirin faruwa da ita ba. Abu guda daya tal ta sani, matukar aljanar ta aiwatar da manufarta a kanta lallai tana cikin matsala. Sosai take gwada wa mutane kiyayya musamman ma wanda suke a karkashinta. Ya za tayi idan ta wayi gari ta ganta babu gashi ko dis a kanta, bayan kuma yadda kowa ya santa da ado da gashi duk da tsufar da ta fara? Ya za tayi sadda zata tsinci kanta da dalalar yawu mai wari duk da irin izzar da mulkin da take takama da su? Kuka take sosai a wannan gabar, tana tunanin mafita. A yanzu dai ta tabbatar da ko wacece wannan fatalwar. Ta tabbata cewa Gimbiya SA’ADIYA ce. Saboda a tsayin rayuwarta ta yi zalunci sosai, amma babu wanda tama zalunci kalar na gimbiya Sadiyya. Tun tana cikin mahamyarta take mata munanan abubuwa har sadda ta mallaki hankalinta. Amma me yasa boka Fartsi zai mata haka? Me yasa zai bullo mata ta wannan hanyar a matsayin hanyar da zai dauki fansa a gare ta? Sam bai mata adalci ba. Bata tsammaci hakan daga gare shiBa
Komawa tayi ta kwanta har a lokacin jikinta bai daina karkarwa ba. Fargaba da tashin hankali ba su guje daga zuciyarta da gangarjikinta ba. Da zararta runtse idonta fatalwartake gani tana mata gizo, idan ta bude kuma sai taga tamkartana a gabanta ne. Takamaimai ma ta rasa me zatayi. Duk jikinta ta dukunkune wuri guda cike da tsoro. “ 
‘Fulani Kursiyya!‘ Wani sashe na zuciyarta ya ambata. ‘Kamar ke, duk yadda kike takama da mulki da sarauta amma ace kina tsoron wata fatalwa can ko aljana? Ina! Ba girmanki bane. Barazanar banza ce ake miki, daya daga cikin makircin boka Fartsi ne kawai ya kawo miki wata a matsayin Gimbiya Sadiyya domin ta tsoratar dake. Gimbiya Sadiyya ta riga da ta kare tata. Wannan kwalbar da take cikinta tana da tabbacin ba zata taba fitowa daga cikinta ba.
Cike da kwarin guiwa Kursiyya ta saki dariya, tanajin amincewa dari bisa dari da sashin zuciyarta ya bata. 
Da haka har barci barawo ya sace ta, ba tare da tasan lokacin ba. 
A hankali take dan bubbuga ta, ba tace uffan ba, kamar yadda ita ma Hafsar batace komai ba. 
Takalmanta da suke karkashin hamittarta ta zaro ta aje kasa, sannan cikin daurewar fuska tace, “Gimbiya Hafsana ke dawa? Yau ina lissafi, shekara goma sha takwas kenan rabon da inga digar hawayenki. Yau kuma saiga shi kina kuka. Keda waye haka?” 
Sake fashewa da wani kukan tayi, jikinta sai kyarmar kuka yake yi, Iabbanta na dukan junansu. 
Mai martaba dake zaune yana kallon su baice k0 uffan ba. Sai dai har a cikin zuciyarsa yana tsananin takaicin halayen Kursiyya. lta sam bata damu da damuwar wani ba, tata damuwar kawai ta sani. Bata damu da halin da wanizai shiga ba, halin da zata shiga kawai ta sani. Kursiyya shugaba ce mara adalci kwata-kwata, wacce ta kijinin kowa ya rabe ta. Baigama zancen zucin ba yajiya muryar Hafsa na fadin, 
“Wai akan wa ‘yancan wulakantattun ne Abba yake mini fada, masu tsaron kofa, alhali ba
nice da laifi ba, sune suke yi min rashin kunya…” ‘ Tun bata rufe baki ba taji saukar mari a kumcinta. Tsananin bacin ran da kalamanta suka jefa shi ciki ne yasa ya gaura mata mari ba tare daya san yayi ba. Bambare ta dagajikin Kursiyya ya yiyana kokarin sake kai mata wani dukan ne Kursiyya ta sha gabansa hade da rike masa hannu kyam, babu alamun tsaro a idanuwanta. Baiyi yunkurin kwace hannunsa ba, tsabar mamaki da tuhuma yasa ya tsura nata idanuwa, abinda ko sadda yake yaro ba,a taba yi masa ba. Babu wanda ya taba rike masa hannu ta irin sigar da Kursiyya ta rike masa a yanzu. 
Da karti ta yarfar da hannuwan nashi, cikin izza da takama irin tata, Tace”Yar tawa guda daya tal da Allah ya bani ne zaka nemi cin zarafinta saboda wasu kaskantattun mutane can? Wallahi ba ka isa ba! Karyarka ta sha karya,mai martaba Har a wannan Iokacin baidauke idonsa daga gare taba. Mamaki bai kau daga fuskarsa ba. Wai anya kuwa Kursryya tasan da wanda take magana kuwa?Anya ba tayi makuwa ba? Ko dai ta dauka wani ne wanda ba mai martaba take magana da shi? Zancen zucin da yake yi kenan, kafin ya sulale zuwa mazauninsa ya zauna, yana tunanin abin dake faruwa. Abun dai tamkar a mafarki.”Wallahi duk ranar daka sake dukar min yarinya saboda wasu bayi can daban saina rama mata” “Ya ishe ki Kursiyya…! ” Ya yi maganar dakarfi, ta yaddah ita kanta Kursiyyar sai data tsorata. Hafsa kuwa har faduwa tayi tsabar kidima. Bata tabajin muryar Abban nata kamar haka ba. Ba zata kawo ranar da ta ganshi cikin bacin rai irin wannan ba, wanda harzai saka shiyin wannan kururuwar mai 
tsananin kara haka ba. 
A kaf tarihin wannan masarautar, babu sarkin da aka taba samun matarsa da aikata irin abin da kika yi mini yau. Hakan yasa tun daga sarki AbduI-Hakim wanda ya kasance sarki na farko, wato wanda ya haifi kakan Babana, ba a taba samun wanda ya saki matarsa ba. Sai dai a yau, zan karya wannan tarihin, wallahi Kursiyya ba zan iya zama dake ba. Kije na sake ki saki daya. Zaki iya zama a nan kiyi idda, ko bayan nan ma zaki lya cigaba da rayuwa a masarautar nan. Saboda ke dinma jinin masarautar nance. Sai dai kisani, aure 
na dake ya kare. Babu ni babu ke! Tsantsar mamaki ma bai bar ta ta iya furta komai ba. Sai rike bakinta da tayi tana tunanin yadda aka yi dadadden sihirinta ya kare ga mai martaba. Bata taba tunanin akwai wannan ranar ba. Bata taba tsammanin akwai ranar da asirin nan nata mai tsananin karfizai karye ba. Sai dai kash! Ga shi a yau ya karye, har sarkiya zartar da wannan mummunan hukuncin a gare ta. Bata makara ba ko a yanzu, domin kuwa saki daya zata iya dawowa. Dole ta sake daukar masa wani matakin. Ba tajin zata iya ci gaba da rayuwa ba tare da mai martaba ba. Murmushi ta saki maidauke da ma,anoni kaIa-kala, sannan taja hannun Hafsa suka fice k0 takalminta bata tsaya ta dauka ba.

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page