HARSASHEN SO CHAPTER 17

HARSASHEN SO 
CHAPTER 17
Gyara zamansa yayi tare da rungume duka hannayensa a kirjinsa, ta saman idonsa yake kallonta shi wallahi dariya take bashi idan tana magana, sai ta rikayin magana kullum kamartanayin kuka. 
Kallonshi tayi ganin yaki yayi magana tace Yaya kayi shiru kace wani abu mana, dauke kansa yayi daga kallonta yace to aini bansan abinda zance miki ba, matsowa tayi kusa da kafafuwansa ta zauna sannan tace kawai kace wani abu don Allah. Kallonta yayi tare da cewa to aini komai kin kwabe shi na rasa gane ta yanda zan miki bayani ki fahimceni, Gyara zamanta tayi ta kura masa ido tana cewa kawai zan rika tambayarka da ahankali kana bani amsa ai haka zaka gane k0? 
Dan tabe bakinsa yayi tare da cewa to kila zan iya amsawa, murmushi tayi tare da cewa yawwa, tambayata ta farko itace, fadamin don Allah zaka aureni ne? Shiru yayi baice mata komai ba. Murmushi Shalele tayi, sake kallon Mubarak tayi tace don girman Allah kace zaka aureni koda baza ka aureni ba ka fada min haka inji dadi in samu natsuwa a zuciyata, Suleim mi yasa zanyi karya bayan nasan abinda baya yuwuwa ne gaskiya a rayuwata banajin zan iya aurenki. Na baki amsa ta farko muje ta biyu, 
Shiru Shalele tayi dan zuciyarta ta tsaya cak tama daina aiki, bata sake magana ba, ta 
fada cakwakiyar kokwanto, ajiyar zuciya tayi ta saukewa a jere ba tare data sassauta ba kona minti daya,ba 
A ranta take tunani lallai soyayya kamar Ice cream take, lokacin da take a cike zaka rika jinka kana fankama kana fafa, lokacin data dauko karewa zaka ga kowa ya tarwatse ya barka sai wannan tsinke kawai a hannunka, daga nan kuma sai kokonto ko kuma yama zanyi ne? Shikenan ta fada tashin hankali. ‘ Murmushin karfin hali Shalele tayi tare dayin magana a bayyane cewa wallahi ban fada tashin hankali ba, kallon Mubarak tayi tace kai ni duk duniya bana sanka dan wani dalili baka da abunda zaka bani a duniya bana neman komai kuma bana jiran wani abu daga gareka kai ko gidanku, 
Ko an fada maka ita soyayya sakarace ne? Musamman irin wacce kananun yara sukeyi, itace soyayyar da akeyi wa lakabi da san rakumin yara ko kokarin dafawa rakumi shayi a takaice dai ina nufin bata da wata riba bangare daya kawai take zuwa shine bangaren yarinya itace kadai zata mora ta hanyar siwo min wancan ban kyautar wancan, 
Cire zoben hannunta tayi wanda Mubarak ya saka mata ta gyargyarashi a tsakiyar palon, mikewa tayi tsaye ta tunkari hanyar fita daga palon, shidai bai mata magana ba harta fice daga palon, tana fitowa ta hadu da Mai nasara cikin mamaki yake kallonta yana san yayi magana amma ya kasa cewa komai, Tsaye yayi a wurin yana kallon Shalele harta fice daga cikin gidan,juyawa yayi yakai kallonsa kofar palon cike da mamaki Mubarak ya gani tsaye fuskarsa a hade shima kallon Mai nasara yakeyi.Shalele ce ai nasan ka ganeta k0? Mubarak ya fada haka, gyara baki Mai nasara yayi amma baice komai ba, Mubarak yaci gaba da cewa nan gidan gidana ne Shalele kuma “yar uwata ce zata zo gidan nan a duk lokacin da takeso sannan kuma zata fita a duk lokacin data ga dama, bance karkaje kayi munafirci ba dan kune kuke fadawa Baba komai ina jira Allah yasa yazo gidan nan yace min yaji labari ance masa Shalele tana gidan nan wallahi idan rai yayi dubu na farin ciki a cikin zukantanku daya bayan daya saina saka bacin rai a cikin rayuwar mutum, 
Mai nasara yace nidai wallahi bani bane, Mubarak yace ai nima bance kai bane, yana fadin haka ya juya ya koma ciki, zoben da Shalele ta yada ya dauka ya wuce ciki. Mai nasara kuwa tunani ya fada lallai koba komai Mai gida Mubarak ya iya yaudara ta karshe itama yarinyar nan ya samu ya lashe zuciyarta, sai yanzun hankalinsa ya kwanta tunda ya kaita ya barota, ajiyar zuciya Mai nasara yayi ya tausayawa Shalele sosai gaskiya dan yasan har abadan duniya Mubarak baya aurenta haka dai zaiyi ta bata wahala yana azabtar mata da zuciya babu gaira babu dalili. Tafiya takeyi tare da tunani marar mafita a zuciyarta, lallai tana san tasan dalilin da yasa ake gaba tsakanin gidaje biyun nan, miye ya hada wannan bahagguwar gabar ne wanda bata da ranar karewa? To miye laiflna wanda yasa Mubarak baya sona? Ko dan nayi ma mahaifinsa rashin kunya ne tun farko yasa ya tsaneni har yake buda baki cewa bazai iya aurena ba? Wace irin sigace banda ita? Ina da kyau daidai gwargwado wanda duk namijin duniya zaiyi fatan na kasance mata a garesa! Ina da duk abinda namiji yake so a jikin mace, amma miya shm soyayya da kiyayya? 
Nidai koma dai miye? Ina sanka saboda tsakani na da Allah nake sanka idan ma wani abu kake so daga tsagin dukiyar mahaifina zan iya baka dan ka aureni, kuma idan har abinda nayi ma mahaifinka yasa kakejin tsanata a rayuwarka wallahi banga laifinka ba, dan duk dan sunna yana kishin ubansa kuma zaiji bakin ciki da idan har aka soki mahaiflnsa, kuma zanyi kokarin gano duk abinda kake so game da Hafsat idan na cika burinka zan koma gida inji abinda ya hada uwa daya uba daya sukejin Kiyayyar junansu a zukatansu, daga nan zan fita daga rayuwarka in Allah ya yadda zan ci gaba da hakuri har AHah ya bani 
mijin aure.Da tunani barkatai ta samu napep batayi masa magana ba kawai ta shiga, da hannu take nuna masa hanya har suka isa gidan Hafsat, a bakin get ya ajiyeta ta fice tayi tafiyarta, 
Magana yakeyi mata amma tayi kamar batajinsa da gaskiya, mai gadin gidan ne ya biyo bayan Shalele yajawo hijabinta ta baya, tana juyowa da yayi niyar marinta ne amma kuma saiya fasa, ke bakiji ana miki magana ne? Shiru tayi tana kallonsa sai hawaye da suka biyo daga cikin idanuwanta, tausayi ta bashi don haka ya sake mata hijabi tare da cewa Allah sarki baiwar Allah ashe kurma ce,juyawa yayi da kansa ya sallami mai nepep wato kudin da Shalele bata biya ba. Kai tsaye ta shiga cikin palon, hannu kawai ta daga musu alamar gaisuwa ta wuce, daf da zata shiga ciki ne Hafsa tace shigeya waccan tsinaniyar yarinyar ban kaunarta wallahi da ita da Khadija duk saina kashe su …….Wani fitsarin tashin hankali ya digowa Shalele amma tunda bata“ lallai dole wucewa zatayi ciki, gabanta sai faduwa yake bugun zuciyarta ya karu kamar zata fito saboda tashin hankali, a wani tunanin da tayi kuma sai ta dake dan duk bala”in Hafsa batakai Mai gida iya tashin hankalin ba. A bakin kofa ta labe bata ida shiga ciki ba, mutumin taji yana cewa wai ya kuka kare da saurayin yarinyar nan ne? Yayi maganar ne tare da kauda waccan maganarta kisan Shalele, shiru Hafsat tayi bata bashi amsa ba, sai kuma suka canja fira… 
Dakel Shalele ta isa bakin gado ta zauna, wayarta ta ciro dan taji zutzut na shigowar sako, fiddo wayar tayi tare da duba sakon, Shine nace kada ki cire zoben nan kika cire kika yaddar k0? To yayi miki kyau. Abinda Mubarak ya rubuto kenan, tsaki tayi tare da goge sakon ta mayar da wayarta a inda take ajiyewa. Dare sosai Hafsa ta shigo cikin dakin dan kwanciya gidan duka bedroom daya ne sai kwaton palo madafar abinci da kuma toilet, waya takeyi kuma shigowar ta baisa ta daina ba taci gaba da wayarta hankalinta kwance tunda tasan Shalele a dode take diff, Saida ta gama wayarta sannan ta tashi ta fara cire kayanta danyin wanka, tana shiga toilet Shalele ta tabbatar data shiga kuma harta fara wanka yasa ta tashi zaune, Wayarta ta dauka ta cire layinka ta saka a wayarta gaba daya ta kwashe duk wasu numbobi na cikin wayarsannan ta cire ta mayar da layinka a cikun wayar Hafsat ta makale wayarta a inda take adanawa tayi kwanciyarta. Bata wani dade ba ta fito, shirinta mai kyau tayi sannan ta fice daga cikin dakin, itana ma Shalele ta tashi ta flce daga dakin a hankali take sando harta fita palo, tana shigowa palo ana dauke wuta, gaba daya duhu ya bayyana a gidan, Da sauri Shalele tayi gudu gudu ta flce daga cikin palon, taflya mai nisa ce sosai kafin ka fita bakin hanya rasa yanda zatayi Shalele tayi a rayuwarta dan kwana gidan nan bai ganta ba akwai matsala sosai wallahi wannan dalilin yasa zata gudu tabargidan tun kafin Hafsa ta sauke kudirinta a kanta. Maganar Hafsat taji tana cewa to miye amfanin haska fitulu da kukeyi? Ni nace a kashe wutar gidan sai kuma kuyi tamin haske haske, sai yanzun Shalele ta gane ashe ba wuta aka dauke ba. Kashe wutar gidan akayi, cikin dabara harta isa bakin motar da akejibga kayan 
wanda bata san ko na miye ba ta shige ta boye bayan wani katon kwali. Jikinta sai kyarma yakeyi saboda fargaba, tana labe a ciki har suka gama jibga kayan a cikin motar suka rufe, sukaja suka tafi.Hamdala tayiwa Allah tare da addu”a kuma Allah yasa suje laflya, Daga farko tayi niyar sanar da Mubarak amma saita basar dashi, tafiya sukeyi wanda ita kanta bata san ina za’aje ba amma tunda dai taji ba’a tsaya ba tasan tafiya mai nisa ce sukeyi, 
Tana wannan tunanin ne taji an tsaya, maganar Hafsat tajiyo tana cewa ku sauke 3 anan ku wuce da sauran can, cike da damuwa Shalele ta fara gyarawa tare da neman hanyar fitowa, saida aka fitar da kwali 2 sannan Allah ya bata sa’ar fitowa ta shige cikin gidan da ake shigar da kayan kuma ta sake samun wuri ta kara sakewa. 
Shi kuwa Mubarak yana gida amma ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda wannan zoben da ya bawa Shalele yana dauke da wasu na’urori wanda hade suke ajikin wayarsa idan anyi magana komai zaiji dalilinsa kuwa nayin haka shine yasan dalili. Shalele kuwa ciki sai kara murgudewa takejin kukan wani wanda ake duka tare da tambayarsa cewa ka yadda kaine ka kasheta Eye? Cikin disasshiyar murya yace wallahi bani bane ban kasheta ba kuma bazan amsa laifin da banyi ba. 
Hafsat tace ku bashi daga nan zuwa gobe, daga gobe itace damarka ta karshe idan har baka amsa ba to lallai zansa a ratayeka, mutumin yace ba komai ko bayan bana duniya gaskiya zata bayyana, kuma insha Allah asirinki saiya tonu, nakai kararki wurin Allah sannan kuma Abak zaiji dake. 
Harta juya ta fara tafiya ta tsaya. Nazari tayi sosai hannunta a saman bakinta tajuyo, kai ku kashe sa kawai, idanuwa Shalele ta zaro sosai, daga inda ta boye ta leka tana kallo aka bude bakin mutumin aka cusa wani katon zani duk girman zanin nan saida ta shige a bakinsa, daure hannunsa akayi da igiya ta baya sannan aka sakala igiya a saman wuyansa wani ne ya taka kujera ya hau ya rataye mutumin nan, tunijikin Shalele ya dauki kyarma sai fitsari shah …… ya zubo zufa kyarma hawaye da sauri ta toshe bakinta dan kar kukanta ya fito Kanajin kakarin mutumin nan mai tada hankali harsaida ransa ya fita, sannan Hafsat tace ku sauko shi kuje ku jefar dashi a cikin makarantarsu, tana fadin haka ta fice daga dakin. Shalele tana kallonsu har suka sauko da mutumin nan suka nannade sa a cikin buhu suka fita da gawar daga cikin gidan. 
Suna fita Shalelejikinta na kyarma ta ruga taje ta kama katanga ta dire daga gidan. Cikin rawarjiki ta ciro wayarta ta fara kiran Mubarak saida ta kusa tsinkewa ya dauka, cikin kuka tare da waige waige tace gani nan kazo ka dawo dani ni bansan hanyaba …….. , Kina ta ina ne yanzu? Ni bansan wurin ba kuma bansan sunan wurin ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa kwantar da hankali mene ne ya fitar dake ne? Nidai tsoro nakeji kazo yanzu yanzun nan, 
Cikin fada yace sai cewa kike inzo inzo ina zanzo wai? ltama bata san yanda zatace masa ba dan haka ta kashe wayarta ta fara gudu dan fitar da kanta inda ta sani, shi kuma ranshi ya baci dan duk duniya ya tsani a kashe masa waya saboda yana kallon abun matsayin rainin hankali. Saida ta flto inda ta sani sannan ta kirasa dan ta fada masa waishi a dole yayi fushi bazai dauki waya ba, kiransa tayi tayi saida yaga dama sannan ya dauka, cikin ladabi ta fada masa inda take a wulakance yace ki jirani ina zuwa wurin. 
Ta dade harta fitar da rai bazai zoba sai kuma gashi, da sauri taje ta bude mota ta shiga tare da cewa muje, bai kalli inda take ba yace ina zamuje ne? Shalele tace duk inda yayi maka, Mubarak yace kidai zaba domin ni yau matata zata dawo, da sauri ta dunkule hannunta da niyar kaima bakinsa duka sai kuma ta fasa, cikin bacin rai yace ni zaki daka? Ya nuna kansa, kam aiko yau da kin gane baki da wayau idan da basai na fasa miki kai ba nabi ta kanki da motar nan ba zakice bani ba ne. Cikin rashin zuciya tace kayi hakuri abunne ai babu dadin fada, daure fuskar yayi sannan yace nine ban iya maganar ba ko kuwa matar tawa ce matsalarki? Ko daya kayi hakuri na bata maka rai shedan ne yake so ya hadamu, ta karasa maganar murmushi dauke a saman kyakkyawar fuskarta, tsaki yayi tare da cewa ya akayi ne? Gyara zamanta tayi tana fuskantar Mubarak sosai tace don Allah me Hafsat tayi maka ne? Bani tayi maba wasu bayin Allah ne kuma babu abinda sukayi mata. Shalele tace mene ne akayi ne wai? Fara tafiya yayi da mota sannan ya fara bata labari cewa. 
Kyakkyawar yarinya ce matashiya mai jini a jiki, “yar gayu ce sosai wayayya ajin farko, sunanta Asiya, wani irin so takemin wanda haryanzun babu macen dake min irin wannan son Tun kafun ya rufe bakinsa Shalele tace ai duk duniya babu wanda ya taba maka kwatankwacin son da nake maka a duniya, babu ba’a tabayi ba kuma har a busa kaho babu wanda zai soka kamarni. Murmushi Mubarak yayi tare daci gaba da bata labari. Cikin yanayi na kishi da damuwa Asiya taja da baya ganin Mubarak tsaye dashi da Hafsat suna magana wanda bata iya jiyo abinda suke cewa ba amma daga ganin firansu suna cikin nishadi, daga baya kuma suka nufi wurin motarsa da kanta ta bude masa ya shiga gaba daya sojojin dake wurin saida suka girmama, Hafsat tana daga masa hannu har suka wuce. 
Bayan ya tafi ne Asiya ta tura masa sako cewa, kuma Hafsat ka yayo a rayuwarka? Tou bana rabaka da abinda kakeso rayuwarka, amma kayi hankali Hafsat shika takeyi, Murmushi yayi da gefen bakinsa bayan ya gama karanta sakon Asiya, Allah ya kyauta ya fada. Dan yasan kishi ne
A kullum Asiya bata da magana sai maganar Hafsat tare da fadawa Mubarak cewa “yar iska ce, shidai bai yadda ba saboda ya yadda da natsuwar Hafsat hankalinta da kuma tunani irin nata. Lokaci guda hankalin Mubarak ya tashi daga kan Asiya ya sauka a kan Hafsat saboda tana da kulawa sosai kuma ta cika shishshigin tsiya shi yasa ta samu Mubarak yana kulata sosai har ya yadda take zuwa zance wurinsa. Wannan abu kuwa yayiwa Asiya bakin ciki sosai dan haka ta budewa Mubarak magana cewa Hafsa fa auren dole akayi mata kuma itace ta kashe mijinta har lahira, kuma an sani amma magana yaki fitowa, tunda data kasheshi ta kwashe duk wata dukiyarsa ta gudu ta dawo Abuja da zama. 
Mubarak dai yaki yadda wannan dalili yasa Asiya ta sakawa rayuwar Hafsat ido tare da duk wani motsinta da zatayi dan tayi alkawari saita samu shedar da zata nunawa Mubarak ya gane ba karya takeyi ba. Haka kuwa akayi domin Asiya ta mike aiki sosai dan ta dauki alkawari saita raba Mubarak da Hafsa, ranar wata litinin da marece ita Asiya ta dawo daga kasuwa taga Hafsat a cikin mota ita da wani mutum wanda bata san ko waye ba, da sauri ta juya sitiyarin motarta ta fara binsu. 
Har suka isa inda zasuje, a bakin kofar gidan tayi parking su kuma su Hafsa aka bude musu get suka shige ciki, tun a lokacin Asiya tayi ta kiran Mubarak amma bai dauka waya ba, Fita tayi tare da neman alfarma a wurin mai gadi, daga farko ya hanata amma tace tare suke da Hafsat wannan dalilin yasa ya yadda ya barta ta shiga, leke leke tayi tayi har Allah yakaita ta gano inda suke, hankalinta ya tashi ganin yanayin da suke ciki na sabawa mahalicci, kara matsawa tayi jikin windown da sauri ta ciro wayarta ta fara daukarsu video, 
Tana gamawa daidai yanda yayi mata ta sulale daga gidan, tana flta mai gadin yayi masu waya cewa wata ta shigo a gidansa da alama bata da gaskiya, babu damuwa haka shi kwarton ya fada, hankalin Hafsa ya tashi ta fara kuka duk da bata san wanda ta shigo ba a gidan, 
Kuka takeyi tana cewa kaga abinda nake gudu ko? Rumgumeta yayi a jikinsa tare da kwantar mata da hankalinta ta hanyarcewa karki damu ki bar komai a hannuna zanji da komai, Abinda C C T V Camera ta dauka ya dawo dashi dan dubawa, da sauri Hafsat ta runtse idonta dan ganin hoton Asiya ya bayyana, da bidiyon da tayi musu, sosai taji tashin hankali da damuwa, ba ita kadai ba, danshi kwarton fitacce ne sosai a kasa mutane sun san da yawa ga “ya”ya kuma ga mata, hakuri yayi ta bawa Hafsa tare da lallabata ta tafi. Hukunci mai tsanani yayiwa Asiya domin dai sawa yayi aka kamo masa ita, mai gadin gidansa yasa yayi mata fyade sannan suka kasheta. Ajiyar zuciya Mubarak yayi tare da kallon Shalele danjin abinda zata ce, itama kallonsa tayi sannan tace to kai waye ya fada maka sune suka kashe ta ne? A wurin partyn bikin cika shekarar aihuwarwata kawarsu ne, ita Hafsa tayi ma Asiya magana cewa, Asiya kin bini kinje kin dauko sharri dan yadawa to kin dauka kuma nasan kinyi, dan haka ki saurari matakin da zan dauka, kashe mutumin a wurina yafi min shan ruwa sauki dani dake mu zuwa. Wannan magana na Hafsa shine ya tadawa Asiya hankali dan haka ita Asiya ta fara tattara yanata yanata don tafiya garinsu, saurayinta tayi ma waya cewa su hadu a tashar mota, lokacin da yaje tuni har sunsan yanda sukayi suka kasheta a wurin, shi kuma yana zuwa ya durkusa a gabanta yana kuka, bayan tafiyar su Hafsa suka sanar da hukuma cewa saurayi yayi kisa, babu wani bincike aka kamashi aka tafi dashi, 
Daga baya da kansu sukaje suka anso bilensa suka tafi dashi wanda babu wanda yasan ina suka kaishi. To kai miyasa kace na zauna tare da Hafsa ne? Iyayen shi yaron ne suka ce na taimaka musu na fiddo musu da dansu wallahi bai aikata abinda ake zarginsa dashi ba. 
Shalele tace kai a ina kasan Iyayen shi yaron ne? Kanin matar mai kula da fulawowin gidana ne, suna zama ne a BQ gidana na danni banma san yaron ba sai a lokacin shima karatu ya kawoshi anan garin Abuja. 
Ni kuma miye yasa ka mayar dani kurma ne? Kuma ka hadani zama da Hasatu ne? Saboda lokacin da nayi waya cewa a saki yaron akace min anzo an anshe sa, shi yaron yasan komai tunda Asiya ta tura masa da wannan video shi kuma ya nunawa abokinsa ne, su basu san haka ba suna ganin idan har suka kasheshi asirinsu zai rufu, to wannan dalili yasa nace bakijin magana nace ki zauna a gidan Hafsat dan ko zakiji inda yaron yake ne saboda iyayensa sun shiga tashin hankali. “ Iyakar abinda Shalele ta sani ta fadawa Mubarak har kisan da akayiwa shi wannan bawan Allah,jinjina kai Mubarak yayi tare da cewa sai kije kotu ki bada shaida ……….. Zaro idanuwa tayi cikin tsananin tashin hankali tace haba Yaya wannan kuma wane irin zance ne mara dadi? Mai dadin ji ne, ko kina da sheda ne? Wayarsa ya fiddo daga gaban rigarsa iyar maganar da Shalele tayi yayi record tiryan tiryan taji maganarta amma babu tasa, Mubarak yace zaki fada ma kotu iyakar abinda kika gani idan sun yadda zasu barki ki tafi idan basu gamsu da bayaninki ba zasu tsareki har ranar da gaskiya zata flto. Cikin rarrashi tace haba Yaya haba don Allah? Karka mayar dani abokiyar gaba ni ina sanka so na tsakani da Allah karka jefani cikin halaka rayuwata zata iya salwanta idan harna samu matsala a rayuwata mahaifina yana cikin tashin hankali, kaji tausayina don girman Allah karka zama silar tarwatsewar rayuwata, nasan baka sona wallahi zan tafi na fita daga 
rayuwarka daga yau idan har ka sake ganina ka kasheni. Ni bana kisa kuma bazan fara akanki ba, ya karasa maganartare da dan watsa yatsunsa, yace lallai bayar da shedar kisa yana da babban wahala dan haka ki shirya amsoshin da zaki bawa alkali tun kafin ranar tsayuwarki tayi a gabansa, Kai Yaya wannan wace irin kiyayya ce, me nayi maka haka da yawa ne? Ke saurara ba”a daga murya a gabana idan kika sake cewa uhum saina ce kece kika kasheshi, shiru tayi ta kasa karasa maganar tare da zaro duka idanuwansa, cikin tsoro ta shiga taitayinta bata sake magana ba ta labe kamar kadangare yaga mage. 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page