HARSASHEN SO CHAPTER 14

HARSASHEN SO 
CHAPTER 14
Gudu Shalele takeyi sosai kamar zata cire lumfashinta, a bayanta kuwa motar “yan 
sanda ce ta saka jiniya wasu “yan sanda kuma suna binta a kasa da kafafuwansu. 
Gudu bana wasa ba Shalele takeyi tana kuka ita babban tashin hankalinta Mai gida yaji wannan zance tasan kashinta ya bushe dan mai gida yaji wannan labarin wallahi har kasheta yana iya yi. 
Juyawa tayi bayanta ta hangosu sun kusa cimmata dan haka ta mayar da hankalinta 
gabanta taci gaba shararar gudu bakinta dauke da addu”a, 
Ki tsaya idan ba haka ba zamu harbar miki kafa, daga farko tayi niyan tsayawa sai kuma taga gara kawai ma ta gudu su harbeta ta mutu ta huta da wannan bakar rayuwa, ina zata 
samu wata miliyan biyara duniya? 
Wayyo Allahna na shiga 3 a haka Shalele take gudu tana fada, wani lungu ta kurda 
wanda bata san ko ina ne ba tunda ba garinsu bane, garin aro aka kawota. 
Tana kurdawa cikin lungun ta samu tayi gudu sosai har Allah ya hadata da wata katuwar bishiya jikinta na kyarma ta kama ta haye can sama sosai ta dade bakinta dan kar wani yajikukanta k0 lumfashinta. 
Tana gama hawa “yan sanda sukazo da gudu, daidai bishiyar sukayi cirko cirko, wani dan sanda ne yayi magana cewa wallahi yarinyar nan bata isa wucewa ta wurin nan ba, wani yace gaskiya ta gudu, 
Kai karyane wallahi duk inda ta boye ta boye tana nan wurin ku nemota, wani kuwa cew yayi mudai bita da gudu zamu kamata, babban cikinsu ne yayi dan gajeran tsaki tare da cewa koma daga farkon inda ta shigo ka biyomin sahun kafarta. Shalele najin haka “yan cikinta suka kada, amma ta dake bata sauko ba kuma batayi magana ba, shi kuwa fara bin sahun kafar shalele ya farayi ya biyo sahun hardaidai gaban wannan icce.
“Yar labai tana nan saman bishiyar nan,jinjina kansa yayi tare da cewa sauko maza ki sauko, Shalele tayi shiru, shi kuma yaci gaba da cewa ki sauko da kanki babu wanda zai hawo bishiya idan kuwa ba haka ba tou fa lallai zan  kunnawa bishiryar nan wuta. Shiru Shalele tayi dan bata da niyar saukowa, ke idan har kika bari na hawo saman bishiyar nan wallahi saina wurgoki daga sama ki fado kasa duk sai kin watse. Baza ki sauko ba? Nayi rantsuwa zaki hadu da fushina mai tsanani, ku hawo ku wurgota yanzun nan, da sauri Shalele tace ku jirani ina saukowa, a hankali ta fara saukowa daga saman bishiyar harta sauko  
Gaban dan sanda taje ta durkusa cikin kuka tace gani, wani irin mari yayiwa Shalele wanda saida ta wurwura ta luliya kamar anyi wurgi da kwallo sannan ta tashi da sauri tare da rike inda yayi mata marin, Bindiga ya ansa yasa kasan bindiga yayi ta dukan Shalele dashi harsai da ya tabbatar yay mata dukan fitar hayyaci sannan ya barta tare da cewa tashi muje yanzun ma ki gudu. Jiki a sabule Shalele ta mike ko gabanta bata gani haka nan take hasashen hanya har a wurin motar “yan sanda ta shiga suka tafida ita zuwa Office dinsu dan gabatar da bincike bincike idan sun tabbatar tayi zasuyi mata hukunci idan bata aikata ba su saketa, Bayan sunje Office dinsu sunyi bincike sosai kuma sun tabbatar da Shalele ta lashe wannan makuden kudaden da ake zarginta dasu, dan haka suka tura Shalele zuwa gdan yari. Matsaloli sosai ta fara fuskanta a gidan yari dan tunda aka kaita ta taka wata bata gani b dan haka sukayi mata dan banzan duka harsai da tayi amai, dan ita bata san ana rama duka ba a gidan yari dan data san ana ramawa aradu duk da sai taci uwasu. Kai ………. Mai gida ya fada tare da runtse idanuwansa kamar an caka masa wuka zufa ta keto masa lokaci daya yayin da Asma”u ta gama mishi bayani abinda ya faru da Shalele, cin bashin da tayi tare da neman asiri akan ta auri Mubarak, Cikin tsananin bacin rai Mai gida yace ina tattama ke diyata ce dana haifa a cikin ciki na, saboda dan makiyina kike so ki tattago min fitina kin cinye min dukiyata ki talautani ki maidani fakiri matsiyaci matalauci wallahi na rantse da Allah duk iyakar cin tattalin arzikina da zakiyi saboda taya makiyana ganin bayana, tou wallahi duk yanda nayi talauci a duniya bazan kai ‘MAKIYINA‘ Bashir talauci ba, Ina yaron nan yake Balaga? Cikin girmamawa Balaga yace gani Mai gida, dafa kafadar Balaga yayi tare da cewa kuje katsina ku biya wannan kudin sannan ku taho min da Shalele garin nan, Alhaji Abas ne ya fara magana, dan shine ya tiso keyar Asma”u dan ta fadawa Mai gida komai tunda a gabanta aka shirya komai daya faru banda dan banza duka da mahaifinta yayi mata har saida hakorinta daya na gaba ya fita dan ansar hukunci mahaifinta. Alhaji Abas yace wa Mai gida tunda amana ka bani yarinyar nan zan bada rabin kudin nan ka bada rabi, abinda yasa na sanar dakai dan kasan ta ina zaka warware wannan matsalar ne, dan haka ka bayar da miliyan 2 da rabi nine zan cika miliyan biyu da rabi gobe insha Allah zan kawo maka Shalele sannan kuma zan bar Asma”u ta zauna a tare da ita har zuwa lokacin da komai zai daidaita dan zaman nan yafi zaman cikin gari, dan na lura zaman ta can yana nema ya zama hadari a wurinta, tunda gashi har ta fara koyon dabi’un da bata iya ba, 
Sundai dan dade suna tattaunawa daga baya Alhaji Abas da Balaga suka kama hanyar zuwa katsina, Asma’u kuwa aka barta a gidansu Shalele wurin Mama, Suna shigowa katsina kai tsaye suka wuce zuwa Ofishin “yan sanda sun dade sosai ana ta abu daya dan basu bar wurin ba sai 12:32am suka bar wurin, kai tsaye gidan Alhaji Abas Suka nufa da Shalele banda dan banza duka da aka mata a gidan yari duka kwananta biyu amma ta canja kamanninta ….. A daren ranar nan Shalele batayi wani cikakkan bacci ba tana tunani wane irin hukunci kuma zata amsa a hannun mai gida! Shi kuwa Mai gida saida dare ya tsula sosai sannan ya fita daga gida dan tafiya wurin mashahurin bokansa wanda ya taba aiken Shalele a wurinsa, ransa a bace ya isa daidai inda suke haduwa ya zauna a wurin zuciyarsa a cukude. Ya dade yana zaune a wurin yana jiran zuwansa, tunani iri iri dauke a zuciyar mai gida, yana wannan tunanin guguwa ta taso wanda wannan ya tabbatar masa da zuwan boko ne wani irin iska mai tattaro kasa tare da wata irin hayaki ne kamar kasuwa ta taru a wurin. Wani irin zafi ya bayyana a inda mai gida yake zaune kamaryana cikin inda ake gasa bread ,jigiff yaji wani abu ya fado kasa sai kuma wata irin dariya da akeyi wanda ta karade kaf gaba dayan dajin nan. Magana aka farayi daga sama wadda mai gida yaji sautinta kamar tana fitowa ne daga cikin sararin samani,a Mansur ka kwantar da hankali wannan yaro Mubarak baya san diyarka, daga farko yayi tunanin ya kulla alaka da ita ya shiga jikinta sosai daga baya kuma ya balbada mata kasa a ido, har abadan duniya makiyi baya taba zama masoyi, tunda yake a rayuwarsa mata basa gabansa mace bata burgesa amma karo na farko yaji tausayin diyarka, a karo na farko ya shigo gidanka wanda bai tabayi ba danshi bai taba taka kafarsa ba zuwa wurin diya mace ba da sunan wani abu amma akwai abu a dunkule a zuciyarsa wanda yawan ibadarsa ya hana mana ganin cikin zuciyarsa, Da sauri Mai gida ya daga kansa sama tare da cewa yaushe yazo gida na ne? Dariya boka yayi sosai tare da bayyana a gaban Mai gida yace hakika yazo gidanka kuma mahaifiyarka tasan komai shigarsa da fitarsa duka a kan idonta komai ya faru, kuma ya dade a dakin”yarka sunyi mahada amma yazo ita kuma bata zoba wannan dalili yasashi yayi fushi, Tou yana san Shalele ko kuwa baya santa? Saida boka ya sake kecewa da dariya sannan yace baya santa baya kaunarta ita daya take kidanta take rawarta, cikin bacin rai Mai gida yace itafa Shalele wane irin so take masa? Boka yace yanda take sansa ko kai bata so haka 
dan tunaninta da komai nata ta tattara tayi imani dashi. Cikin kunar zuciya Mai gida yace ka goge min tabon sansa ka mantar dashi a cikin zuciya Shalelena, boka yace sofa inhar  ya shiga baya fita har abadan duniya, da sauri Mai gida ya kama kafafuwan boko yace ka rufamin asiri ka fitar min da sansa a zuciyar “yata, boka yace wallahi wannan san bazai taba gogewa ba dan ya zamar mata kamar jarabawa ne dani dakai duk wanda yayi gigin shiga huramin wannan haduwa lallai karshensa mutuwa ne, Wani irin ihu Mai gida yayi tare dayin kundunbala cikin kasa baiki a yau din nan mutuwarsa ta riske sa ba, ashe Mama tasan komai hada ita ake munafintar sa, kila ma itace tayi sanadiyar haduwar wannan wulakantacciyar tarayya, yana wannan tunani ne yaji boka yace babu wanda ya hada Allahne ya hada rabuwa kuma har abadan duniya yana fadin haka ya bace bat a wurin. Kai karya ne, karya ne ………….. Tunda Allah ya kagi duniya ya banbance karya sannan kuma ya tace gaskiya, saida ya sauke wani irin wahalallen nunfashi yace zaki zo ki sameni gobe, kasheki ba komai bane a wurina Shalelena, na kwammace inyi rayuwata ni daya a duniyata, haihuwarki ta zamo min fitina masifa bala”i akan aihuwarki nasan jarabta ta rayuwa gara nayi kisan kai nasan makomata k0 a wurin Allah da dai nabar zuciyarki ta rayu da soyayyar dan ‘MAKIYI NA Cikin dacin rai Mai gida ya koma gidansa, rannan nasa a daude yana maijin ciwon aihuwar da yayiwa Shalele a matsayin diya a garesa, shi kansa ya tausayawa Shalele da iril kwandon azabar da zai sauke mata gobe. Tunda aka gama sallah asuba Alhaji Abas suka kamo hanya dashi da Balaga sai kuma Shalele suka taho dan maido Shalele  gidan Mai gida, tunda suka taho banda faduwa babu abinda kirjin Shalele yakeyi. Ta sadaukar kuma tama hakura da rayuwa kwata kwata addu”a kawai takeyi Allah yasa motarsu tayi hadari ta mutu ta huta, Amma cikin hukuncin Allah lafiya qalau suka iso, kallo daya mai gida yayi wa Shalele ya runtse idonsa tare da kauda kansa shi kadai yasan yanda yaji kuma yaji abinda yaji a zuciyarsa, Zazzaune suke dukansu a katon palon mai gida, kowa da kowa yana wurin ba’a rage kowa na gidan ba! Bayan gaishe gaishe wuri yayi tsit, bayan wani lokaci mai gida yayi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka:Shalele nidai bazan miki muguwar fata ba sannan kuma bazan miki tsiniwa ba, ke kina da kangara sannan abinda zuciyarki take so shi kike so, abinda kika ga dama shi kikeyi, to koba komai ni nine ubanki nine nan na haife ki ba wani ba, ci da sha da sutura kula da lafiyarki har zuwa yau din nan da kika bandaremin nine na baki. Duk dan halak yana kishin ubansa sannan kuma yana bin umarninsa matsawar dai bai sabawa Allah ba, Allah shine ya halicceni ya hacciki kuma ya bamu rai mukeyin rayuwa mu dukanmu munsan dalilin abinda yasa mukeyin rayuwa a cikin duniyar nan, 
Dani da Bashir uwa daya uba daya muke duk yanda zaki so sa k0 ki kisa duk baki kaini ba, tunda nake a duniya na tsanin launin fata mai fari saboda ‘MAKIYI NA” ya kasance fari ne shi, haka na tsani rayuwa a cikin birni badan bana so ba, haka na hakura na dawo kauyen nan da zama saboda dan ‘MAIKlYl NA‘ yana rayuwa a cikin birnin Abuja bana so na shaki iskar da makiyina ya shaka a duniya, amma na hakura na dawo kauyen nan nayi gini irin na zamani dan kuma ku tashi cikin jin dadi kuma rayuwarku ta banbanta da mutanen 
cikin kauyen nan, Amma yau kin zama mutum kin girma wai dani zakiyi fada Shalelena? Ya karasa maganar cikin lallausar murya tare da nuna kansa yaci gaba da cewa, duk duniya babu abinda na tsana nakejin bakin cikin lumfashinsa a doron duniyar nan irin Bashir da dansa, ganin dansa ya zama wata tsiya a duniya yasa shi yake alfahari da dagawa dansa ya zama gwannati ya fada min cewa rankatakafa nigeria babu wanda baisan da zaman ‘MUBARAK BASHIR ABAK’ ba, wallahi bana masa bakin ciki dan duk wanda Allah yaso ya zama saiya zama hassada da bakin ciki basa hana mutum yakai inda Allah yayi alkawarin saiya kai, babban dana kawai zan rama kisan wulakancin da sukayi masa wannan bashin saina fanshe sa. Ajiyar zuciya mai gida ya sauke sannan yace kince ‘HARSASHEN SO‘ ne yayi tsalle yazo daidai saitin zuciyarki k0? Hmmm ya wuce fatarjikinki ya tsallake bargo ya wuce tsokar jikinki har kashinjikinki saida ya coka sannan ya shiga cikin ‘ZUCIYAR KI‘ko to yau zan nuna miki iyakar tawa kangarar wanda ke da kanki zaki kai kanki asibiti sai likita ya cire wannan ‘HARSHASHEN SO‘ din da kike tinkaho baya ciruwa. 
Balaga? Mai gida ya kira sunan sa, da sauri ya matsa tare da dan sadda kansa kasa cikin ladabi yace gani Mai gida, wata irin shareriyar wuka mai kaifin tashin hankali ya mikawa Balaga yana mai cewa likita baida maganin “SO’ kuma ya iya cire ‘HARSASHEN‘ bindiga amma bai iya ciro ‘HARSASHEN s0’ ba, ansa wukar nan ka farkamin ‘ZUCIYAR“ Shalele ka fito min da wannan ‘HARSASHEN SO’ din, idan haryaki fitowa to lallai ka ciremin ‘ZUCIYAR TA‘ ni ina da magani ‘SO“ maza maza yau zan dasa ‘KIYAYYA’ sannan zan goge ‘so’ a cikin zuciyarki ni nine likitan dasa ‘KIYAYYA’ kuma nine mutum na farko a duniya dazan goge so na dasa kiyayya ……………….. 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page