HARSASHEN SO CHAPTER 2

HARSASHEN SO
CHAPTER 2
Murmushi mai gida yayi ganin shigewar su mama, cikin fushi ya juya inda hoton bashir yake jingine abun rubutu ya dauka sannan ya durkusa jikin hoton ya fara magana kamar bashir din ne a gabansa ba hoto ba! 
Banza ko ajikin hotonka shima kansa hoton ya canja launi, tsoro kwance a cikin kwayar idanuwar ka, jijiyoyinka sun mike tarr, hannunsa yasa a daidai zuciyar mutumin dake cikin hoton sannan ya bushe da dariya yace ashe hotoma zuciyarsa tana bugawa, 
Hahaha ya mike tsaye saida yayi dariya mai isarsa sannan ya sake dukawa jikin hoton ya daure fuskarsa yace ya kaji shalele a gabanka, kana wani wuri daban amma daga ganinsa 
tsaye a gaban hotonka saida naji faduwar gaban ka! 
Mutuwarka, ya soke wasu lambobi daya zana a kasan hoton ya rage yawansu, mutuwarka harna fara jiyo kamshinta, mikewa yayi saida ya kaiwa hoton harbi kusha sannan ya wuce yana surutai masu nuni da yanda zai azabtar da bashir, 
Mama wai waye wannan da mai gida kullum kudirinsa da tunaninsa akansa yake? Waye ya hana farin ciki a zuciyar mai gida waye shi? Ajiyar zuciya mama tayi dan bata san ta yadda zata fara fadawa shalele labarin wannan dadaddiyar gaba ba! lnda mama take zaune ya matsa ya dafa kafadarta sannan yace na rantse da soyayyar da mai gida yake nuna min yau din nan sai bashirya kwana da bakin ciki a gidansa dashi da ahalinsa gaba daya saina sako tsoro a zukatansu ko dabbobin gidansa sai sunsan 
shalale yazo duniya ki daina damuwa mamana, ya karasa maganaryana murmushi, Cikin damuwa mama tace tou shalale ina tare dakai, hannuwa suka hada alamar suna tare ~ ,da sauri shalele ya shige dakinsa, mama tabi bayan shalele da kallo harya shige tare da rufo kofa! 
Toilet ya wuce yayi wanka babu wani dadewa ya fito a gaggauce ya shirya cikin shiri nafita kai hari dan zuwa gidan magaucin mai gida, 
Yana fitowa mama ta mika mishi wata “yar karamar kwarya mai dauke da nonon shanu da dumi duminsa dan sabuwar tatsa ne! Ansa yayi yana taflya yana sha mama tana biye a bayansa saida ya shanye sannan ya juyo ya bata kwaryar, 
Ansa tayi ta koma ciki, shi kuma wucewa yayi ya dauki takobi, cikin shigar daya fito yasa su balaga suka matso da doki cikin sauri, mai gida ne ya fito daga ciki tare da cewa ina zuwa haka shalele? Mai gida zanje ne na kafa tuta ta a yankin bashir sannan kuma zan sanar dasu yanzun kwanakin fafatawa sun fara daga yau, kiyayya da gaba ya dawo a hannuna, idan basu tanka ba shikenan zan dawo amma idan aka samu wani yayi magana a ciki zan yanke masa bakinsa da wannan takobin, ya karasa maganar yana daga takobin tare da kallonsa! 
Wata irin dariyar mugunta mai gida yayi wanda gaba dayan gidan saida ya amsa, bayan ya gama dariyar ya daki kafadar shalele tare da cewa ka nunamin ka haifu ka amsa sunanka jarumin jarumai kaje shalele albarka ta biya har zuwa yankin bashir ka daso masa tsoro a zuciyarsa kamar yanda na gansa yana kyarma a jikin hotonsa lokacin daya ganka tsaye a gabansa, kuje nasara ta biku, 
Tsalle shalele ya daka tare da hayewa saman doki yayi masa kafa yana gaba su balaga na bayansa suma haye a saman dawaki babu abinda ke bi bayansu banda kura kana ganin shalele kaga cikakken jarumi da ya amsa sunansa jarumi amma shekarun jarumtar basu kai ba! 
Gudu sukeyi sosai a hanya a garin duk wanda yaga shalele haye a doki da sauri zai kauce dan duk garin babu wanda baida labarin shalele cikakken jarumin daya fara kashe uwarsa sannan yazo duniya dan ganin bayan makiyin babansa! 
Tun kafin su isa labari ya kaiwa bashir dan haka shima ya hada nasa yaran kowa ya fito da makami bashir ya bada umarnin kisa wa shalele kafin ya girma ya kashe shi yace su gama da labarinsa a duniya ko gawarsa kada a bari mansur ya samu labarinta, Kafin bashirya gama rufe bakinsa akan bayanin da yake bayarwa yaji abu ya taho gabansa suuuuu daga idonsa da zaiyi yaga yaronsa a gabansa kwance da jini jikinsa kallon yaron yayi sosai sannan ya daga kansa ya sake kallon shalele tsaye a gabansa da wani irin shareren takobi yana digar jini ….. 
Yaran bashir sukayo ca akan shalele gaba dayansu, shima da gudu ya tafl dan su hade yaaaaaaaaa, kacau kacau aka fara gabzawa tsakanin shalele da sauran yaran abokin gaban babanshi, lokaci mai tsawo aka dauka ana gumurzu amma duk girman kato duk jarumtarsa saida shalele yakai shi kasa, Gaban bashir yaje yayi tsaye sannan yace ni nine shalale jarumi daya tak a duk fadin kauyen nan, yanki babana nashi ne, yankin ka kuma shine nawa, gaba da kiyayya ta tashi daga hannu mai gida daga yau nine babban makiyinka sannan kuma ina maka albishirda nine MUTUWAR KA, da daya kuma tak daka tura zuwa wata duniya dan tsoron mutuwa gangar j’lkinsa nawa ne nine ajalinsa da kaina zan kamo dan iska a gaban idonka zan yankewa banza kai karnukan gidanmu su cinye banza dan tun ranar dana zo duniya nayi musu wannan alkawarin, tunda ga wannan ranar suka daina cin abinci tausayi suke bani kullum dana fito suke min haushi, kai kuma zan yanke duka hannayenka dan nayi alkawari da zuciyata zan kai gidanmu kullum safiya da naman jikinka dokina zai karya yaci iyakar cinsa sauran na cinna mata wuta, 
Kallo bashir yabi shalele dashi sannan yayi murmushi yace dakyau kyan da ya gaji ubansa duk dan halak yana kishin ubansa, hakika naga jarumta kwance a cikin 
idanuwanka da jikinka, amma ka sani dana yafi karfinka kallo daya idan kayi masa zaka gane babu sauran mazaje a duniya saishi,jarumi yana kasashen waje yana can dan wannan kazamar rayuwar bata dace dashi ba, can dana turashi shine gata kaiko uban naka 
bai nuna maka komai ba sai kiyayya da haukan banza, ni kamin kadan kaje ka tura shi uban naka yazo, 
Cikin bacin rai shalele ya juya tare da kaiwa wani lafiyayen doki suka da wuka ya fadi kasa ya fara harbebe, wani irin halbi yakai wa shalele, shalele ya tafi tangal tangal da sauri ya dafa kasa tare da mikewa tsaye, cikin kunar rai yace kaci sa”a mutuwarka sai nan da shekaru goma sha biyar wannan umarnin mai gidana ne amma da yaune lumfashinka ya zai kare! 
Amma duk da haka sai kayi kwanan bakin ciki, haka shalele ya shiga gidan duk wani akuya doki shanuwa kare kaza agwagwa da zabo duk dai abinda ya shafi abin kiwo saidai shalele ya tabbatar ya mutu sannan ya hau dokinsa mabiya bayansa suka bi bayansa dan tafl gida ……. Wani irin gurnani bashir yayi tare da bin yaransa dake kwance kicin wahala yace tirrr tare da tofar da yawu yace kunyi asara kattin banza wannan dan cakulkulin yaron kuka 
kasa kashewa kuji irin wulakanci daya yazo yayi min har cikin gidana amma kuka kasa kashe minshi “yan iska kattin banza banga amfaninku ba, dawowar mubarak ya zama dole danshi kadai zaiga bayan wannan dan iskan yaron, 
Cikin bakin ciki bashir ya goge hawayen idonsa tunda yake a duniya ko mansur da suke matuwar kiyayyar bai taba tsaya masa a zuciyarsa ba kamar wannan dan iskan yaron, amma ko da yake yace gaba da kiyayya ta dawo a wurinsa, lallai mutuwar yaron nan ta zama dole idan ba haka ba yaci gaba da tayar masa da kura yana karami yayi wannan 
iskanci ina da yakai shekarun ubansa? 
Taflye yake a doki gudu dokin yake yi bana wasa ba, amma sam hankalinsa baya jikinsa 
magana daya tak ta tsaya masa a rai kuma take masa yawo a cikin zuciya, 
Amma ka sani dana yafi karflnka kallo daya idan kayi masa zaka gane babu sauran mazaje a duniya saishi, jarumi yana kasashen waje yana can dan wannan kazamar rayuwar bata dace dashi ba_ 
A daidai lokacin da suka iso gida, dirowa yayi daga saman doki ya wuce ciki, mai gida tunda ya hango su ya ayyana a ransa ga shalele ya ciro kan bashir yazo masa dashi a hannunsa, ta gabansa shalele ya wuce mai gida na masa magana amma hankalinsa baya wurin, mama ma tayi masa sannu da zuwa tare da tambayar an samu nasara amma shalele bayajin mama, toilet ya wuce ya kunna ma kansa shawa, idanuwansa a rufe suke amma maganar bashir tayi masa tsaye a zuciya! 
Amma ka sani dana yafi karf’lnka kallo daya idan kayi masa zaka gane babu sauran mazaje a duniya saishi, jarumin yana kasashen waje yana can dan wannan kazamar rayuwar bata dace dashi ba_ 
Abunda shalele ya kasa ganewa shine, kishi yakeji anfishi jarumta ko kuwa me? Amsar da baisani ba kenan kuma ya kasa bawa kansa amsa, 
Haka ya fito ya shlrya Clkln kayansa, wannan kaya k0 bacci zaiyl dasu yakeyl dan mai gida ya saka masa wani karfe a kirjinsa yace a haka zai rika shiga toilet sannan kuma kada ya kuskura ya cire kayansa a ko ina idan ba toilet ba, wannan karfe da aka tokare kirjinsa dashi kuma ko da yana baccin abokan gaba suka zo zuciya suke saurin kaiwa caka domin itace daidai mutuwa amma saboda karfen daya tokare sa idan sun cakesa bayaji, dan haka 
ya shirya ya kwanta da wannan tunani, 
Can cikin tsakiyar dare shalele bacci ya kauracema idonsa dan haka ya tashi yayi ta safa da marwa a cikin dakinsa, saida ya gaji sannan ya koma ya kwanta kansa na kallon silin din dakin, a bayyane yace jarumin banza ni saina dasa tsorona a cikin zuciyarka, Wata zuciyarta gargade ta da ki kiyaye “yan kasashen waje domin karfi garesu Sunfi “yan kauye karfi domin su tuwon dawa da fura ta kashe musu jiki basu da karfin dukan kowa saina noma, 
Aini bana noma kuma bana cin tuwo bare fura, a bayyane tace hakika nice a gabanka dan iskan nan! Haka tayi ta tunani har Allah ya taimaketa bacci ya daukeshi, 
Koda safe a wurin kalaci suku suku shalele yake, mai gida ya tambayeshi lafiya? Amma sai yace mai gida waye dan bashir? ‘Daure fuska mai gida yayi tare da cewa miye ya shafeka da dansa? Horona ne dole sai ya hada dashi ina san ganin sa ne dan in tabbatar da jarumanta da ubansa yace shi jarumi ne wanda har yakewa lakabi da cewa wai in sani dansa yafi karfina wai kallo daya idan nayi masa zan gane babu sauran mazaje a duniya saishi waye shi waye sunan sa? Ina so na kamoshi da hannuna in kawoshi a gaban uban nashi in cire masa jarumtar dake yawo a jikinsa sannan in yankawa banza tikitin lahira waye Ajiyar zuciya mai gida yayi sannan ya kalli shalele yace hakika bansan dan bashir ba, hasalima ban san sunan sa ba, kuma ban taba ganin sa ba! Da sauri ya mike tsaye tare da dafa daidai zuciyarsa ya rike kugunsa da dayan hannunsa, ajiyar zuciya ya sauke sosai 
sannan yace nemanka ya zama wajibi a gareni AJALI zai tafl nemanka domin daukar ranka, Cikin damuwa mama tace gaskiya mansur ka fitar da shalele daga cikin wannan fltina taku, ku cire “ya”ya yenku a ciki, mama babu ruwanki ni kadai kika haifa dan haka nine kadai kike da iko dani ba abinda na aifa ba, kiyi ikona inyi inkon abinda na kawo duniya, shiru mama tayi tare da bin dan nata da kallo, dauke idonsa yayi daga kanta sannan ya kalli shalele yace dana ina bayanka ka kashe duk wanda ranka yake so kayi abunda ranka yakeso amma ka kiyaye yin hanyar magautarmu kai daya saboda bacin rana…., Na gode mai gida shalele ya fada tare da dan dukawa cikin girmamawa sannan yace ina san sanin waye shi? ……… Na baka dama shalele sunansa da kuma garin da yake zama…. Na baka dama shalele kamannin sa a samo min wanda ya sani kafln ranar haduwa, yana kaiwa nan ya juya ya koma ciki ……… 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page