MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 31

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 31
so . Ya yi murmushi yace
“Lallai kin kawo shawara mai kyau, hakan zan yi don ina bukatar ganinsu a kusa dani matuka”. 
Ganin ta sami shiga a wannan shawarar ya sanya tace
“Yaushe zaka tafi ne Maidugiirin?” 
Ya yi dayi  Jim na wani lokaci, sannan yace
“Idan son samu ne na tafi karshen makon nan,idai an yi albashi k0 kudin ‘kwangilarmu sun .,f1to idan kuma hakan bai ‘ samu ba sai mako na sama insha Allah”. 
Ta ‘so ya tsaida ranar tafiyar, domin bokan yace zasu yi amfani da ranar da zai” taf’i din su samo sa‘a, amma dai zata ci gaba da bibiyarsa har ta ji ranar da zai tafl din. 
Sai dai kamar yasan abin da ta ke shiryawa, kenan juma’a da sassafe ta ganshi yana shirin tafiya. Ta cika da mamaki tace
‘ “Ina kuma za ka?” Yace“Maiduguri na yi sa’a kudin 
kwangilar tamu sun dito, zan tafi yau na dawo ranar lahadi
Bakin ciki ya cika mata ciki tamkar zai kashe ta, wannan wacce irin shammata ya yi mata? Kafin ta kai ga aiwatar da komai ya kammala shirinsa ya fice sai ta fara neman layin wayar boka sai dai ta yi rashin sa’a sabis ya Ki samuwa, takaicinta ya kuma Karuwa, ta yi wurgi da wayar ta fashe da kuka, wai yau tana da rai da lafiya amma Mukhtar ke taflya gurin wata mace kuma har da ‘ya’ya, ba ta mutu ba me yafi wannan bakin ciki, ta kuma rarumo wayar ta ci gaba da neman layin boka, amma dai shiru sabis din yayi tsiyar tasa. ‘ 
‘ Shi kam mai darasu yana fita ya dauki hanyar Maiduguri; amma’b’ai f’ita° daga cikin garin ba ya kirawo wayar Hajiyarsa yana gaya mata idan akwai abin dake faranta mata rai a yanzu bai wuce jin za shi Maiduguri ba, don haka ta ce ya juya gidansu za ta bashi sako. Babu Bata lokaci ya juya motarshi ya nufl ‘gidan nata ya san dai sajon ba zai wucc na su ~Muhammad bai. ‘ 
Bai sami isa garin Maiduguri ba sai wajen tara na dare, idan son samu ace yadda ya ganshi ya wuce can gidan su masaukinsa, amma doki da son ganin yaran nasa ya hana masa samun sukunin haka, idan son samu ne har da Falmata ya gani, sai dai ya yi rashin sa’a yau ne ranar karatun dare da Abba keyi a unguwar, saboda haka da kyar ya sami guri ya tsaya da motarsa saboda layin a cike yake da motoci na masu daukar karatu, duk ranar juma’a yake karatun wa’azi a masallacin gidan nasa, yawan mutane kuwa ba zai ba shi damar isa ga inda Abban yakeba, haka ya sanya dole ya zauna jin lacca din. Abba kam ya iya gabatar da Iacca mai ratsa jikin mutane, yana karatu ne akan tarihin matan sahabbai guda dari. Ana tarihin Sayyada Sauda ne matar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, sai ya ji karatun kamar a kansa aka yi, domin ana fadin yadda manzon Allah yake zaune da matansa ne
Yanayin yadda Manzon Allah ke zaune da iyalinsa abin burgewa ne da sha’awa, sai 
yaje zargin knsa bisa zaman da yake yi da nashi matan, musamman Falmata. Sannu a hankali ya fara tariyo irin zaman da ya, yi da Falmata idanunsa suka kada jajir da ya tuno irin abin da yayi mata, lallai ya cutar da Falmata matuka,‘ sai ya ji gabansa yana faduwa, anya kuwa Falmata zata yarda ta sake zaman aure da shi? 
Wata kila ma ta tsane shi yanzu, shi ya sanya k0 ganinsa ba ta son yi, sai wajen sha daya da mintina aka tashi daga laccar, kai tsaye motarsa ya shiga ya nufl masaukinsa, don ya ga rashin dacewar ya tunkari Abba a wannan lokacin, ya san ya gaji yana bukatar hutu ne. Har ya isa masaukinsa yana tunani mai zurf’i Washcgari sai da ya makara saboda gajiyar da ya yi, don haka sai yamma ya isa gidan malam Abbagana, yau ma ta wancan ‘karon aka yi masa bayan sun gaisa da Abba aka bar shi .da Muhammad da Abba, can ya ~ daure ya kwantar da kanshi yace
“Malam abin da ya faru yana damuna 
matuka, har nake ganm kamar hakkin Falmata ba zai barni na sake ba, don Allah a baiwa F almata hakuri, na rasa abin dake min dadi kwata-kwata”.  Abbagana ya tattara nutsuwarsa ga Mai darasu gaba daya ya ce
“Muntari duk abin dake faruwa na san ba yin kanka ba ne, kuma Allah Ya kaddara hakan sai ya faru, babu makawa idan har kana da laifl guri daya ne, rashin neman tsari da yawaita yin addu’o’in sammu, amma ka cire damuwa daga ranka, komai ya wuce Muntari”. 
Mai darasu ya kara yin kasa da kai, ransa ya yi fari yana jin kamarya ce a kira masa Falmata ita ma ya bata hakuri, amma sai ‘ya kula kamar Malam din bai son haduwarsu, don ya kasa tambayarsa ita din, suka ci gaba da hira, 
Yakura kam da gaske son Mai darasu take don haka tunda taji ya zo gidan hankalinta gaba daya ya tashi, taci kwalliya ta nufl sashin malam, tajima tana neman 
hanyar da zata shiga dakin tana gudun kada malam ya rufeta da fada, ita kuwa tayi shirin yau sai ta gabatar da kanta a gurinshi, domin tun bayan da ya koma wancan zuwan da ya yi ta fara neman hanyar da zata bi ya sota, daga karshe wata qawaeta ta rakata gurin wani malami, babukunya balle tsoron Allah tace a yi mata aiki akan mai darasu. Malamin ko nace boka, ya amshe kudinsa ya hada mata Karya da karairayinsa, ya zuba cikin kwalliya yace ta sanya muddin suka yi ido hudu da Mukhtar shi ke nan zai gigice ya ce duk duniya babu ya ita, dole sai ya aure ta komai za a yi kuwa sai ya aure ta din. Wannan ya sanya tana jin zuwansa ta cancanda wanka da kwalliya cikin irin shigarta ta Turawa, wacce take ganin k0 da ita ma zata iya siye zuciyarsa. ~ 
Wani wandon suwaga ta sanya ya kama ta tsam, ta daura wata riga ita ma ta matse ta tsam-tsam, sai ta yafa siririn mayafl a kanta, hatta barimarhancinta ta gwal ta’ sanya, Kananan kitsonta irin nasu na bare-bari ya zuba a gadon bayanta, da yake duk yaran gidan kyawawa ne sai ta yi kyau ainun; 
Tana nan tsaye ta ji an yi sallama da Abba, ya fita murna ta kuma cikata, don haka Abba yana fita ta kara gyara jikinta, daman tana ta zuba kamshi ta nufl cikin dakin. 
‘ Wani irin kamshi mai dadi ya bugi .hancin mai darasu, ya lumshe ido kafin ya daga kanshi da sauri ya amsa sallamar‘da aka yi masa, babu makawa ya saki jiki Falmata ce, domin muryarsu, iri daya ce da Yakura, ya zubawa kofar ido sai dai ga mamakinsa sai ya ga Yakura ce, sai dai abin da ya daure masa kai bai wuce ganin irin shigar da Yakuran tayi ba, duk da yana da labarin ‘ya’yan Yakolo, ‘ amma bai yi zaton fitsararsu ta kai haka ba Ta”sami guri’ ta zauna tana rangwada ta ce masa. , 
“Sannu da zuwa Muntari, ya ya su Hajiya Mariya?” 
Ya’yi kokarin Boye mamakinsa, yace
“Suna nan laf’lya, sunce a gaishe ku
Abin da take fatan ta samu domin sun hada idon da Mai darasu, sai dai maimakon ya ji sonta ya shige shi, sai ma ya ji tsananin haushinta da tsanarta sun lullube shi, domin ko matarshi Falmata bata taba yi masa irin wannan kallon na kurulla na rashin kunya ba, ita kam Yakura duk sai ta dururuce ta ji gabanta ya fadi tsananin kwarjininsa ya hanata sakat, sai dai tana tunanin yanzu zai fara zubo mata kalaman sOyayya kamar yadda bokansu yace, amma ga mamakinta sai taji yaci gaba da hira da yaransa ya manta da ita a gurin kamar bai san da wata halitta ba, shi kam da zai iya da ya tambayi Yakura ina Falmata, sai dai haushinta da yake ji ya sanya‘ k0 kallonta bai fatan kara yi balle har wata hira ta shiga tsakaninsu. Haka nan ta gaji da zama tana ta mitsika ido, can ta jiyo alamun tahowar Abba ta mike da sauri tana fadin. 
“Sai an jima, zan turo yaro ka bashi lambar wayarka”. 
Ta wuce ciki da sauri ba tare da ta saurari jin ta cewarsa ba. 
Ya bi ta da kallo cike da tsananin 
mamakin me zata yi kuma da lambarsa? Har sanda Abba ya shigo, sai dai a gurguje Abba ya shigo yace maza su daura alwala lokacin sallar magriba ya yi. 
Bayan an idar da sallah ya fito ya jingina da motarsa yana sakawa da kwancewa kamar ance ya daga kansa ya hango Yagana. zata shiga gidansu. Tana sanye da doguwar riga marun kala, ta nade kanta da irin nadin
da Falmata keyi, gabansa ya fadi gaba daya sai yaga kamar Falmata ya gani. Da sauri ya ’ nufe ta yana kiran sunanta. Ta juyo cike da tsananin mamaki baki a bude tana fadin. “Malam yaushe a garin mu?” Ya yi murmushi yace“Inji maqi bako ba tunda kun rikemin mata ai dole ne ku ganni. Yanzu ma Allah ne ya dube ni ya turo mini je, don Allah wahalar dani din ta isa haka, kubani matata mu koma Yagana”. Ta kara shiga mamaki, tace masa, wacce matar kuma? K0 kayi sabon aure a garin namu ban sani bane?” Malam ya yi murmushi yace. 
“Don Allah a daina wajigani haka Yagana, na tuba haka, a kyale ni naga Falmata ko da sau daya ne”. 
. Ta dan saki fuska, domin tagano bai da labarin Falmata bata garin, ta ce. 
“Lallai an sha da kai, wai ba ka san Falmata ba ta Maiduguri ba kenan?” 
Ya cika da mamaki, ido waje ya ce. 
“Da gaske kike Yagana, k0 kuma duk ‘ -hakan yanacikin hukuncin da kuke min ne?” 
Ta yi dan’ya tace, “Haba malam ai .tsakanina da kai babu haka, wallahi da gaske Falmata ba ta Maidugun’, kai ba ma ta Najeriya gaba daya, tana jami’ar musulunci ta Madina, kusan watanninta takwas a can ma”. 
Gabansa ya yanke ya fadi Falmatan tashi ce ta tafl wata kasa tsawon wannan lokacin bai sani ba? Lallai ya yarda Abba ya yi fushida shi. Ya yi shiru ya rasa abin da zaice ma. 
Yagana ta yi murmushi don ta kula da halin da ya shiga na damuwa, cikin zolaya tace . “Naga ka’mar ka damu ba malam bayan ban yi zaton zaka damu ba, ai farin ciki ya dace ka yi na nisanta da Falmata ta yi da kai k0?” Ya kalle ta yana kokarin kakaro murmushi, yace. “Za ku Iya gaya mini komai yanzu Yagana, na kuma shirya jin komai din, amma idan haka zai iya zama shi ne hukuncina da zaku_ yi min bisa Iaifina na gode ma, yanzu ki . taimake ni ki bani lambar Falmata ta can, domin ina yawaita neman layinta daman ba na samu”. ‘ Yagana ta yi dam jim cike da damuwa, sannan ta ce. “Amma don Allah kada kace mata ni na baka malam”. Ya cika -da tsananin mamaki har idanunsa na fitowa waje yace “Wato har ta kai ga sanar da ku kada ‘a ba ni lambarta kc nan k0 Yagana?” 
Yadda ta ga idanunsa sun sauya launi cikin taKi kadan ya sanya ya bata tausayi, amma dai har yanzu zuciyarta ba ta huce daga laifln da ya aikata musu ba, domin ita kanta ta kadu da sakin da malam din ya yiwa F almata, bata taBa tsammanin zata ganshi ta sakar masa jiki haka ba, sai dai ta danganta hakan da tsananin kwarjinin da yakeda shi, da kuma girmansa a idonta. Mutum ne da ba ka isa kallo daya ka raina shi ba, yana da wata HAIBA (Littafin Nasimat) da muhibba irin ta mazan Kwarai . _ Da ta ba shi lambar ma sun jima suna “hira kafin ya nufi masaukinsa, don duk ya cinye. lokacinsa a nan. 
Sai. dai wani abin mamaki duk tsawon lokacin da suka dauka suna hira, Yakura tana laBe tana jinsu, tana kuma jin kamar ta hadiye zuciya ta mutu, musamman da ta ji yana ambatonFalmata. Ta yi zaton ya manta da Falmata yarabu da ita har abada, musamman data ga yazo wancan karon har ya koma bai neme ta ba, sai yanzu. Ashe har yau yana sonta? Lallai dole ta tashi tsaye ta san k0 
Hajjansu ma ba zata kyale wannan abin ba, don haka kai tsaye dakin Hajjansu ta nufa da ta shiga cikin gidan. Ta yi kuma sa’a suna tare da Haija Basma. Hajja Yakolo ta dube ta da kulawa ta ce. “Ya ya dai,1afiya na ganki haka kamar baki cikin hayyacinki?” 
Yakura ta sami guri ta zauna idonta duk ya sauya launi da tsananin bakin ciki,tace. 
“Hajja kin san Muntari na Kano yazo gidan nan, can na ji su a waje suna hira da shegiyar munafukar yarinyar can Yagana, wai . yazo ne zai maida aurensa da Falmata idan har hakan ta kasance tabbas mun shiga uku da gori a gidan nan” Idonta ya fara zubda hawayen bakin ciki. ‘ Hajja Basma ta ce, “Tabdijan! Ai dama Hajja Yakolo na gaya miki, idan har ka ga . kare yana shinshinar takalmi to babu tantama dauka zai yi. Sakacinda kika yi a gidan nan shi ke kawo komai, wallahi muddin hakan ta kasance ke da ‘ya’yanki kun banu gurin Abba da gori, da komai domin kafin auren F almata ya mutu na Yakura ne ya fara mutuwa, ga kuma. Zubaida da take cikin halin ha’ula’i, ita ‘ ba matar aure ba ita ba bazawara ba, mijin bai saketa ba, bai kuma zo ya maidata ba kusan shekara biyu ke nan, amma Abba ya zuba ido yaKi cewa komai, idan har Falmata ta koma kuwa kun hadu da gorin Abba don zai ce su tunda aka sake su mazajensu ba su zo biko ba, ita kuwa ga shi ‘yan watanni kalilan mijin nata ya dawo zai maidata, shi ke nan’ su Yakura sun shiga uku sun kuma kade har ganyensu”. 
_ Hankalin Hajja Yakolo ya tashi ainun, idanunta ‘ suka kankance zuwa tsananin damuwa da masifa, lallai abin da Hajja Basma ta fada gaskiya ne, domin a yanzu babu wanda keyi mata gori akan mutuwar auren yaranta domin da an yi zata maida raddi, idan kuma aka ce Falmata ta koma gidan Muntari ina ta kama, ita da ta sanya a yi mata asirin da zata yi ta zama a haka har abada babu aure domin su a zatonsu asirin da suka yi na farraku tsakanin malam da Falmata ne ya yi tasiri ‘har ya~saketa ga shi kuma bokan yace, Falmata ita da sake yin aure har abada don haka rashin zuwan malam tsawon watannin har Falmata. ta kammala idda ya tabbatar musu-da. haka, .amma.a yanzu sun fara fargaba, kada labari ya sha bambam. Hajja Yakolo ta kula tace. 
“Ni wallahi lamarin mutanen nan ya ishe ni,-kullum muyi ta abu daya amma mun kasa nasara a kansu? Kusan duk abin da na mallaka ya kare akan Iyami da iyalinta amma tamkar ina shuka dusa? Yanzu me ya dace mu yi Basma?” 
Ta kalli Hajja Basma. Yayin da ita din ‘ ma tayi shiru .cike da Bacin rai, can kuma tace. -. 
“Komai dai meye ya dace mu dauki 
mataki a kansu… “Haba tun rannan nace da Hajja a yiwa Muntari aiki sonsa ya dawo kaina ya aure ni. 
wallahi hakan ne kadai zai sanya muyi maganin Iyarni da ‘ya’yanta, har da waccan munafukar Hajja Kaltum din”. 
Yakura ta katse mahaifiyarta cikin kumfar baki. Hajja Basma tace, “Wannan ce kadai ‘ mafita, wallahi abin da zamu yi mu huce ke nan, ai ba haramun ba ne idan har Yakura ta auri Muntari sai Iyami ta hadiyi zuciya ta mutu, balle shegiyar diyarta da ta kwallafa rai a kanta, shi kansa Abba sai ciwon zuciya ya kama shi,‘ wannan ce kadai mafita a gare mu”. Hajja Yakolo ta yi ajiyar zuciya tace “Shi ke nan, saiki fito da gwalagwalanki a fara yin aikin, domin kin san ni duk dan abin hannuna ya kare a kansu”. Zubaida ta fito daga daki a fusace tace. “Hajja gaskiya na gaji da son kanki a gidan nan, na kula kinfi son farin cikin Yakura akan kowa, shekarata kusan biyu a gidan nan kin kasa shawo min kan mijina ya maida ni dakina, ga Abba yana kallo yaKi cewa komai, amma yanzu kinzo da wata 
Hmmm nanfa ake yinta bazasu bar muntari ya huta ba ko kadan ni harya fara bani tausayi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page