MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 3

MATACCIYAR RAYUWA 
CHAPTER 3
Tace“Ni kuwa Hajja Kaltum k0 Falmata nada alkawari a kanta na aurc ne? Don yarinya mai kyau ce da nutsuwa irin wannan ba zata rasa manema ba”. 
Hajja Kaltum tace“Lallai na ga alamar kin 
‘ yaba da nutsuwar diyar tawa, kin ganta nan miskila ce mai zurfin ciki, da tsananin hakuri taki bai wa. 
kowa fuska yazo, bare har a tsaida magana ita ko irin rawar kan nan ta yaran zamani sam Falmata ba ta da ita”. 
‘Hajiya -Mariya ta girgiza kai cike da gamsuwa, a ranta ta fara zabga addu’a.’ 
                             ***
. ‘Washe gari Hajiya Mariya ta harhada kayanta zata wuce Kano, Falmata kam a gurinta zamu iya cewa ga Koshi ga kuma kwana da yunwa. ‘Tana son-zuwanta Kano don kuwa ranar da zasu‘ tafi musabaka‘ kasa bacci tayi don doki  amma tana 
tsoron kada taje a lika mata Muntarin Hajiya ‘MarYam  don haka ta toge akan zata je idan sun dawo daga musabakarsu ta duniya. 
Bayan tafiyarta, Abbagana ‘ ya tattara matansa da ‘yanmatan gidan hudu na hajja Yakolo ‘sai Falmata ta biyar, uku daga cikinsu sun girme mata, wato Yakura da Salima da Zubaida, sai kuma Zahra da suke sa,a‘nni don kwanaki ne
tsakaninsu, duk‘ diyoyin Hajja Yakolo ne
Yaran duk suna qasa kamar gaske sun sha hijabai, yayin da iyayen ke sama. 
Malam Abbagana ya gyara zama, sannan ya ce, “Kamar yadda na gaya muku (ya nuna iyayen mata) abinda ke  tafe da hajiya Mariya shi ne maganar a nemarwa danta Muntari aure, kowa cikinku yasan Muntari, yasan alaqar dake tsakanina da mahaifnsa, don haka na yanke shawarar sanya shi cikin alkawarin da . nayi na aurar daku. Ke Falmata da keda Zahra da babu ku amma na shigo da ku yanzu, don ba zan kuma yarda wata mace taci gaba da karatu a gidan nan ba bayan ta kammala secondary ba, domin na yi akan Yakura da Salima da Zubaida ban ji dadi ba. Don haka ku ma kuna cikin wadanda zan aurar bana”. 
Gaban Falmata ya yanke ya fadi, ta duqar da kai idanunta suka ciko da kwalla, wannan shine tashin hankalin da ba a sanya maka rana. ita kam Hajja Yakolo cika ta yi fam ta batse kamar zata fashe don a ganinta an tsani ‘ya’yanta ne, don matane su kamar yadda Hajja Basma ke zuga ta kullum, 
Amma dai wargi ma ai guri yake sa’mu, sai dai tayi kumburin nata bata isa tace ko qala ba. 
Bai kula du yadda Haijja Yakolo ke cika tana 
batsewa ba, ya ci gaba da bayaninsa. 
Yace“Don haka qofa a bude take daga nan zuwa sati guda, duk wacce keda Wanda ta ke so ta sanar ‘ wa da Hajja Kaltum, k0 ta same ni kai tsaye, idan wannan satin ya cika baku kawo ba, to kuwa zan sanar da Wanda raina ‘ya shiryawa ya shirya ya ‘kawo sadakinsa, wannan ita ce qarshen maganata daku
Hankalin ‘yanmatan gaba daya ya tashi, don sun san duk cikin samarin nasu babu na aure; ‘yan Iove you ne kawai, Zahra ce me dan dama-dama a cikinsu ta kwantar da murya ta ce
“Abba ina da magana ni”. ‘ 
Ya dube ta da kulawa, yace “,Uhm Zahra’u ina jinki” . 
Gaba daya suka tsareta da ido musamman Hajja Yakolo da take tunanin matsiyacin saurayinta zata ambata, sai harararta take yi kamar idonta Zai fadi, amma ko kallon inda taje ba tayi ba. .
 Ta Kara gyara zama, tace, “Abba ni dama 
tun tuni Muhammadu Ligari keta ce mini na tambayo ka za su turo iyayensu, sai nace ya yi hakuri, yanzu na sanar masa kenan?” 
Fuskarsa ta fadada da fara’ a, yace, “Masha Allah, kinga irin abin da nake so kenan, ki gaya masa ya turo kinji k0 Zahra?” 
Dadi ya cikata kamar ta taka rawa don dadi, yayin da Hajja Yakolo kejin kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu don takaici. . 
Haka nan aka tashi daga taron kowa da abin da yake saqawa a cikin ransa. 
Suna isa daki Hajja Yakolo ta dirarwa Zahra. 
“Banza, sakarya, ke barazanar Abba ce ta rude ki da har kika ambata za ki auri matsiyacin yaron nan Ligari? Me na sama yaci balle ya bai wa na qasa? Yaron da ke koyarwa a makarantar islamiyya, dame kike tunanin zai iya riqe ki? K0 kin manta ké ko‘ diyar waye? Ki fito daga wannan babban gidan ki kuma Kare a dan matsiyata dan gargajiya? To wallahi ki sake tunani, sam ban laminci hakan ba”. 
Ta dukar da kai tana fadin, “Ki yi hakuri Umma, amma ni dai shi nake so, ai arziki nufin Allah ne, da Abba Ya ba ni wani da ban sani ba kuma bana so,’ ai gawara shi”. . 
“Kc tafi can, rufc mini baki. Ai k0 da Abbanku’zai bada ku ba zai bada ku ga fakirai ba. Nasan zai zaba cikin dalibansa masu arziqi ne, ana nuna miki Gabas kina runtse idanuwa, sakarya”. Cewar Hajja Basma. 
Yakura ta taBe baki tare da cewa, “Ku kuke wani damuwa da ita, ta je ta yi ta yi, idan dai rayuwar talauci dadi Ce zata ji, ni fa naji takaicin’ qarfa-Karfar. da ake shirin yi mana, yanzu kamar mu da muke karatu a jami’, a ace za a bada mu? Cabdijan wallahi da an cue mu, kuma fa Abba zai iya bada mu ga wadannan daliban nasa masu dangalallun wanduna’ wad’anda ba su san rayuwa ba, amma dai kamin satin nan dole nasan abin yi”. 
“Yanzu Umma babu taimakon da zaki yi mana don Allah?” Zubaida ta fada hankalinta a tashe. ‘ ’ 
Hajja Basma’ ta amShe, “Ni kuwa zan so ace yaron nan ‘dan gidan Hajiya Mariya a dakinki za a zaBar masa mata, domin k0 babu komai ai suna da bala’in kudi; kuma dai ai ba-shi da makusa ko ya ya kika gani Yakolo?” 
Hajja yakolo ta yi dan‘jim, sannan tace, “daya ambaci wannan maganar naji dama cikin ‘ya’yan dakina za a baiwa, amma nasan son rai irin na malam wata qila waccan banzar munafukar yarinyar zai ba wa shi”. 
“Cabdijan, mu kuma zama zamu yi mu zuba musu ido? Ai wallahi tashi zamu yi tsaye mu bi malamai da bokaye har ya fada dakinki, wannan itace damar da zamuyi amfani da ita ta qarshe don idan 
muka bari wannan damar ta fada dakin Iyami zamu sha haushi, ta dinga wannan kwambon da fadin ran taga kamar da gasken tafi kowa, k0 ya ya kika gani?” 
Hajja Yakolo tace “Tabbas wannan haka yake, dole mu shirya zan kira Malam Tanimu a waya anjima na ji yadda zamu yi da shi, to da wa kika ga yafi dacewa a yi aikin da sunanta…?” 
“Dani!” Yakura ta yi saurin amshewa. 
Zubaida ‘ta kalle ta, “Candijan sannunki, , wallahi ba ki isa ba, sai dai a saka sunana”. 
Salma tacc, ‘.‘Eh da yake ni ba mutum ba ce ba, ko Yasin sai dai kowa ya rasa haka kawai”. Ta yi tsaki ta doki cinya.’ , ‘ 
Nan fa rigima ta harke kowacce tana son ace da ita ce za ayi aikin tunda an kwadaita musu Muktari, kuma dai sun sanshi duk da ya jima dai rabonsu da shi, amma sun san shi dan gayu ne mai ilimi kuma. Zahra dai tana gefe cike da takaicin halayyar ‘yan uwa da iyaycnnata, idan tace zata nusar da su kuma a yi kanta kamar za a cinye ta, don haka dole ta zuba musu ido kawai. 
Can Hajja Yakolo tace, “Kinga banzayc ku rufe mini baki, ni k0 kan wa ya fada duk daya ne, zan bada sunanku can duka dai, shi ke nan magana ta wuce. 
Duk da haka basu daina Kananan maganganu ba, kowacce tana ganin ita yafi dacewa ace ta sami Muktari. 
Ita kam Falmata kai tsaye dakinta ta wuce cike da tsananin tashin hankali, ta shiga uku ita kam, don tana ganin gwara kowa da ita, da ace ba ta hadu da Malam mai darasu ba ma da abin zai zo mata da sauki, amma haduwa’ da shi ya sanya ba ta jin har abada zata kuma son wani namiji. Shi kuma ga-shi bai san tana yi ba, wai kunu a wani gida. 
Matuqar tausayin kanta’ ya cikata har ta fara kuka, lallai CiWon so masifa ne, shin k0 kiran malaminsu-zata yi Gwani Muhammad ta sanar da shi gaskiyar «abin da-ke ranta,’ ta kuma roke shi alfarmar ya’rok‘ar’mata Malam mai darasu k0 zai amince ya so ta? Amma tana ganin’ hakan da kamar wuya. 
Ta tashi .-ta fara sintiri a dakima idonta yana zubda haWaye
K0 a makarantar islamiyya da yamma ana musu karatu kasa fahimtar komai ta yi har sanda aka biyo layi kowa ya biya sai ta yi duru-duru cike da fargaba don ba ta ji abin da aka biya bama balle har ta maimaita 
Gwani Muhammad ya tsare ta da ido yana fadin, “Falmata ina hankalinki ya tafi ne, tunda aka 
fara karatu na kula dake sam hankalinki yana wani guri, me ke damunki ne?” ‘ 
Ta dukar da kai idanunta sun ciko da kwalla kamar ta gaya masa abin daje damunta, ganin yadda ‘yan ajinsu suka zuba mata ido ya sanya ta yi saurin waskewa, tace
“Ka yi hakuri Malam, ba xab kuma ba”. 
Sannan aka ci gaba da karatu, amma dai har aka kammala ta kasa samun nutsuwarta. 
Sanda aka tashi suna tafc a hanya Yagana tadube ta da kulawa ta ce, “Kamar akwai abin da ke damunki Falmata, duk da dai nasan kina da zurfin ciki ba komai kike son fad‘awa kowa ba. Ina fatan zaki sanar dani, domin lamarin na yau babba ne _ tunda har ya gaza boyuwa a ranki kamar yadda 
kika saba”  Falmata ta sanya gefen hijab dinta tana goge hawayen daje gangaro mata cikin muryar: kuka ta fara magana. 
“Tabbas ina cikin damuwa Yagana…” 
Ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar mata. * . 
“To ke meye abin damuwa? Kin sha ce mini kina mamakin yadda su Yakwari ke Batawa Abbanku rai, kin yi alkawarin har abada ba zaki Saba masa ba. kuma ga shi ya baku lokaci yace
kowa ya kawo wanda yakc so, idan kina ganin kina tsoron zabin Abban meZai hana ki sanar da shi kina da mai sonki..”. 
Ta kalle ta da mamaki, “Me sona kuma Wayc me son nawa Yagana
Ta dan yi murmushi tace “Ai masu sonki suna da yawa, kinga Malam Bukar ma ai yana cikinsu” . 
‘Taja tsaki ta wucc da sauri tana fadin, “Ke idan ana maganar arziki sai ki dinga soko ta tsiya, kinga tafiyata”. 
Ta bita da sauri, “Wallahi ba maganar wasa bace nasan ke ranki yana kan malam mai darasu, mutumin da bai san kina yi ba, watakila ya ma manta dake, kuma ko a hanya kuka hadu bai sanki ba, bai san wace ce ke ba, don haka gwara ki nutsu’ ki koma cikin hankalinki, kin san Malam Bukar, kin san halinsa, da ki tsaya Abba ya aura miki . wanda ba ki sanshi ba, shin tsoho ne ko yaro ne, mummuna, mai mugun hali ne? Duk ba ki sani ba, a ganina gwara ki auri wanda kika sani tunda ance ita qiyayyar mace tana da lokaci. Amma idan kinga za ki iya bayyanawa wanda kikeso halin da kike ciki, na yi miki alkawarin raka ki ko’ina ne domin cinma burin ranki”. 
Falmata ta dan tsaya jugum tayi sanyi 
qalau, cikin alamun kuka take magana. 
“Wacc mace mai mutumci kika taba ganin ta yi haka a wannan zamanin? Zamanin da ake  gayawa maza ‘ana sonsu ya wuce, wato zamanin Annabawa da sahabbai da tabi’ai, domin su har abada ba zasu wulakanta ki k0 su tozarta ki ba. A wannan zam’anin namijin yaje gidanku yace yana sonki ya auro ki, yana wulakanta ki ma balle ace kece kika furta masa kina sonsa? Ba zan‘ iya ba, ina ga dai zan haqura na sanar da Abba Malam Bukar, ki taya ni addu’a Allah Ya sanya hakan shi ne alkhairi, kuma maslaha a rayuwa,ta amecn”. 
Yagana ta dinga kallonta da tausayawa, tabbas qawar tata tana cikin tsaka mai wuya, sai dai ta tayata addu’a Allah Ya fiddata, a haka suka rabu kowacce zuciyarta babu dadi
Falmata ba ta taBa zaton irin wannan lokacin zaizo a gare ta da ta jima tana nema, wato ace ga ta zata wakilci duniya gasar karatun kur’ani, sannan kuma ace tana cikin damuwa ba, haka ranar ma ta wuni a daki babu walwala, duk da mahaifiyarta tasan diyar tata miskila ce_amma ta kula tun jiya da mahaifinsu ya yi maganar nan ta Kara tsangwamar kanta da damuwa, don haka ta nufi dakinta kai tsaye
A zaune ta tarar da ita akan sallaya da 
alkur’ani a hannunta tana karatu cikin sanyayyar muryarta da kira’arta mai dadin saurare. Ta shiga cikin dakin ta zauna gefen gadonta. 
Tana ganin babar tata ta shigo tasan muhimmin abu ne ya kawota, don haka tana kaiwa qarshcn ayar da ta keyi, ta yi sadakallahul azim,‘ta yi shaida a inda ta tsaya ta ajiye alkur’anin ta fuskanci mahaifiyar tata tace
“Hajja barka da gida”. ‘ 
Mahaifiyae tata tace, “Yauwa barkanki, nazo mu yi wata muhimmiyar magana”. Ce
Ta sake nutsawa ta duqar da kanta qasa tana sauraran mahaifiyar tata. 
“Shin akwai wani da kike sone, k0 kuma kuka yi alkawarin yin aurc?” 
Muryar mahaifiyar tata ta daki kunnenta, gabanta ya hau bugawa, ba tayi zaton abin da ya kawo Hajjan tata kenan ba. 
Amma sai ta dake ta girgiza kai alamar, a’a. Hajja Iyami ta ce “Kinga budw baki zaki yi kiyi mini magana, bana son wannan karatun kurmayen naki”. ‘ 
Ta Kara takurewa cike da kunya, tace “Hajia babu kowa”. . 
“To amma don mahaifinki ya yi miki maganar zai aurar da ke ga almajiransa kika tada 
hankalinki har da su qin cin abinci, eye Ta dago kanta idonta ya ciko da kwalla, tace, “Hajja wallahi ba haka bane ba”. 
,to menwne? Ai ina kula da ke tun jiyan, a tunanina kece ya dace a fara koyi da biyayyar da zaki yi wa mahaifinki, saboda yabonki da yake yi kullum. Don Allah Falmata kada ki watsa mini kasa a idona, kiyi ta addu’a kawai, sannan ki zama mai biyayya ga mahaifinki, sai ki ga Allah Ya sanya miki albarka kinji ko?” 
Ta daga kai tana fadin, “To Hajja, insha ‘ Allah ba zan ba ki kunya ba, ki dai ci gaba da yi mini addu’ar da kike min”. 
“Insha Allahu, Allah Ya yi miki albarka”. 
Tana kaiwa nan ta tashi ta Fice. Falmata ta bita da kallo
 Ranta yana zafi, shin wane irin ciwo ne Allah Ya dora mata haka ne‘? Kuka yana so yazo mata,.amma tana hana shi ta dauko alkur’ani taci gaba da karatunta, muryarta rana rawa tana hawayc gwanin ban tausayi. 
‘ Daren ranar kam baccinta qalilan ne, domin kwana ta yi tana addu’ar Allah Ya zaBa mata abin da zai zama alkhairi a gere ta, da rayuwarta gaba daya‘ don haka da safe sai ta tashi wasai, ta dinga shiri cikin” nutsuwa har zuwa lokacin da mahaifinta ya aiko mata ya shirya 
Suka yi sallama da mahaifiyarta da sauran yan UWanta suka fice a motarshi Su Hajia Yakolo da Basma ana ta zumbura  baki. ‘ ~ Haija Basma ta ce.“Ni fa ban yarda Saudia za ta gasar duniya ba, an yi ne kawai don a aba mu haushi, ubanta ne kawai zai ,kaita ta huta zai wani layance mama”. 
Hajja Yakolo tace “Ai shi munafunci dodo ne, mai shi ya keci Muna nan Allah zai mana sakayya wallahi”. 
A can makarantar islamiyyar tasu ta Elkanemi bara’imul iman suka hadu da babban Yayanta, Yaya Bulama dan gidan Hajja Kaltum, domin a tsarin tafiyar dole ita sai ta tafi da muharraminta tunda doguwar tafiya ceda za, a yi kwanaki, da yakeshi ma Yaya Bulama tsohon gwani ne na shekaru ashirin da daya da suka wuce, shi ne ya daukowa Nigeria lambar farko a duniya, don haka yasan komai akan tafiyar. 
A nan Elkanemi Bara’imul Imana din suka rabu da Abba yana ta yi mata addu’a. Falmata kam tunda suka kebe da Yagana hankalinta ya kwanta, domin har da Yaganar za, a tafi, domin itace tazo ta uku a Jihar Barno. tun kafin a tafi ta qosa gaba daya, sai Alabura da tazo ta biyu, amma ita makarantarsu daban, don haka wannan karon ma dasu za a tafi 
Suna nan sauran suka kammala zuwa har da Alabura, don haka aka dunguma aka wuce Maiduguri International Airpor ta inda daga can za su daga Kasar Saudia. 
SAUDI AREBIA KING ABDUL’AZIZ AIRPORT 
An sauke su a babban hotel din DARTA PVHID, tun daga airport  suke ta kalle kalle, domin wannan shi ne karonsu na farko da suka taBa fita kasar waje kowanne ya rike mamakinsa a cikin ransa. 
Sa’i dai da suka isa masauki suka dinga dariya da maida yadda aka yi, musamman sanda ’ suka keBe a guri daya. 
Kwanakinsu uku aka fara gabatar da musabakar, dukkanin kasashen musulmi sun hallara a gurin, irin su Saudian kanta, su Misra, Iraq, Fakistan da dai sauransu 
An fara gabatar da musabaqar cikin kwanciyar hankali da kowa yana fatan ya zamo na daya a ransa. 
Ita kam Falmata kusan kullum sai taje dakin Allah mai tsarki ta yi ta salloli da addu’o’i, har zuwa wannan lokacin ta gaza mantawa da malam mai darasu . amma ta sani zata iya auren kowa ta zauna da shi bisa biyayyah  da girmamawa, sai dai sonta guda daya yana ga bawan Allan nan Kuma tana samun nutsuwa a ranta duk sanda ta ziyarci dakin Allah, don haka duk sanda bata kai ziyarar ba sai taji ta babu dadi
An dinga gabatar da musabakar daki-daki har zuwa sanda aka zo kashi na karshe, wani abin alfahari da farin ciki a gurin duk wani dan Nigeria da dangin Falmata, domin har wannan lokacin tana kan gaba ba ta yin baya. 
Ana saura kwana guda a gabatar da kaso na qarshe wanda ya rage ita da wata qalibar qasar Saudian, ‘tawa’gar manyan malamai ta iso daga Kasar Nigeria cike da alfahari da jin dadin qokarin da daliban nasu suka yi. 
Shi kam Abdul a mataki na biyun qarshe ya tsaya, wanda idan aka fiddo gwarzo na  daya na biyu shine zai zamo na iki. 
Gwani Muhammad me ya kirasu a waya su isa can masaukinsu, domin su gana da malaman da suka iso. Doguwar riga ce a jikin Falmata, mai tattara daga qirji, mai qaramin hannu, don haka ta dora bakar silk din doguwar abaya mai yalwa. Ta nade kanta da irin nadin nata na Larabawa da silifas na fata mai kyau a qafarta. Kusan su ma duk dogayen bakaken rigunan suka sanya kamar 
baqaken larabawa, suka nufi masaukin nasu. 
Da sallama suka shiga kan Falmata da ma sauran d‘aliban yana qasa, har suka isa inda aka nuna musu su zauna 
Malamai suka fara jawabinsu da qarfafa gwiwa da yabo matuka, bakin Gwani Muhammad da Yaya Bulama yaqi rufuwa don dadi, har bayanin Ya dura akan shehi na qarshe
Da zolaya ya ce “Ina ce an barki kin je Kano din kin gano ‘yan uwan naki?” 
‘ Ko cikin bacci ta ji wannan muryar zata shaidata, don haka ta d‘aga kanta da sauri qirjinta yana wani irin bugu, Yagana ta kula da yanayinta. 
Suka had‘a ido da Malam mai darasu karo na farko da suka yi kallon-kallo, ta yi saurin duqar da 
‘ kanta qasa cike da kunya tana dariya. 
Gaba daya farin ciki ya cika ta, fuskarta ta kasa boye hakan, sai fararen haqoranta ke kyalli, lotsawar  kumatunta (dimple) na dan qara  haskaka fuskarta
Ya ci gaba da jawabinsa duk da shi ma ya dan shiga wani hali, domin tun a wancan karon  muryarta ta girgiza shi, balle yau da yaga fuskarta. Cikin ransa yake fadin “Tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan kyakkya 
war halittar’
“Kin zame mana d‘alibar da zamu yi alfahari  da
Mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen labarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page