Makaranta duniya chapter20

Makaranta duniya

              Chapter20

Kamar wasa, kafin tace wani abu ya taho gadan-gadan! Ta yi bayi da gudu, ta shiga sharara shi. ”
. Mamaki ya cika Suleman, ya taso da sauri ya biyo ta, “Daga tayin kifi, sai amai? ‘Meke faruwa ne baiwar Allah?” Ba ta saurare shi ba, sai kakai ri, take yi tare da sabon yunkuri. Ya dafe bayanta yana mata sannu,harta’kare. “ ‘ . ‘
Ya ba ‘ta ruwa ta kuskure baki, ta wanke ‘fuska. Ta mike ‘ta dauki- tsintsiya za ta kora tulin Taliyar da ta amayo Yai. sauri ya amshe, Haba. kamar bani~ a kusa?‘ Kawo jeki kmanta”. Ta wuce a’ ‘.hankali, ’ta dawo gado ta kwanta. ‘
Wurinta ya dawo bayan ya gama wanke bayin, ,
ya zauna gefenta, “Sannu. lna fatan cikin baya ciwo?” Ta gir’giza kai, “To wai me ya sameki ne’yau’?” Tace “Koshi ne ya yi min yawa. Munci Taliyar’ nan har’ da na haram”. “‘ Yayi ‘yar’ dariya yace, “Ai gobe ma ‘kya kara, ko daddawar’ nan ‘ba ta saki amai ba? Tun da cikin ya rairaye, taso mu je kodan lemun ki sha. Akwai’shayi”. Ya dagata suka fito tare ya bude mata lemon, tana sha yana cin kifi da buredi. Duk kaiwa bakin da
zai yi, sai ta ji kyama ta kama ta, amma kuma ta kasa daina kallonsa.
Yace, “Toki ci mana, kina ta kallo na’?” Ya matso da filet din. Ta’zabura, kai tsaye bayi ta yi. ya saki baki galalal”‘Ahl ikon Allah”. Ya yunkura ya tashi ya sake bin ta. Ya yi tsaye kufar bayin; yana ‘yar dariya.
,”Kawai kice Bebina baya son kifi, in daina yi masa tayi”. Ba ta saurare shi ,ba. ta kanta kawai take .yi. Ta wanke baki, ta taso ta wuce-shi ta kwanta, ta _ barshi da‘sake wankin bayi.
Wannan karon’ cikin juyi, ya rinka yi. A . kwancen ya sameta, “lna magana, kin kyale,‘baya son kifi ne?” ,Ta maka masa ‘harara, yana dariYa, ya sake . fadin, “Bebin ‘nan nawa dan. kauye ne, watau daddawa ya ’fiso?”
. Ta shagwabe fuska, “Don Allah Yaya Suleman ka bari; Wallahi ciki na CiWo yake yi”. ‘Yace “Ya zan bari, hayan dama can na kusa. Kullum ki ka ga’na daga hannu, rokon Allah na ke”. ”
Tace “Shi kenan ‘kuma kan ka ‘tsaye ka yanke hukunci’ ldo waje yace, “Dan. me ba zan’ yanke ‘ hukunci ba? Na tabbata shi ne da yardar Allah. Bari . kuma ki. gani‘, a gayawa su Mama. Allah ya raba lafiya ta sauke kai
tana dan murmushi, ita ma take sun abin ya kama ta, har tana taya Suleman addu’ar.
Allah ya sa shine cikin ranta. .
ya je. Ya tada Imam da kyar ya bude ido, yana jaye da shi, yana gyangyadi suka shiga falon Mama. Tana kwance Alhaji Na gefa. tace. “Wuce min da shi ciki don Allah
Ya wuce da shi, ya kwantar bisa gado. Ya fito ya yi dan tsaye jim, kamar zai ce wani‘ abu, sai kuma ya kama hanya zai wuce, yana fadin.
’ “Sai da safe”. Alhaji na lura’ da shi. dun haka; ya kira shi ya dawo, “Kamar ka na so ka yi magana. amma ka fasa. Mene ne?” Ya yi dan murmushi, yana’ shafar kai. ‘YAce  babu komai Baba. dama‘Murja ce ke ta yin amai, ammai kace” . ‘
Alhaji ya katse shi, “Amai? Ba ta da lafiya ne?” Mama ta cafe, “Ai kuwa dazu tace min cikinta ne ke mata ciwo Kar’ dai ace ya tsananta ne?” Ya kada kai yace. “Eh, a’a, tace kadan—kadan-ne wai Taliyar da ta ci nee da yawa shi ne take ‘tasu mata.. Ai ta sha maganin da’na’kawo mata dazu .
‘ Alhaji yace “Ba maganar ta sha magani bane. idan Allah ya kai mu gobe. kuje asibiti a dubata kawai; su zasusan  irin. maganin daya kamata tasha. Ko kuwa’?” Mama tace, Gaskiya ne. kar azo abata maganin daba daidai ba”
‘Yace. “To shi kenan, tunda ba ta da fefa gobe. sai mu je”.-“Yauwa, Allah ya kai mu lafiya”. Ya mike. Mama ma ta tashi suka’fita tare, ta je ta .dubota ta’ dawo cike da al”ajabi,.don ba ta tantama ko shakka
ita ma Murja ciki gareta.
‘ Ta zauna tallafe da haba, tace “Wannan shi ne haihuwar guzuma…” Yace ” ’Ya kwance, uwa kwance. Me aka yi?” Tace, “Ba makawa Murja .ciki gareta, don na tambayeta. yaushe rabonta da al’ada, tace min wai ta manta, sai dai ta san ta jima batayi ba
, Ya kada kai yana fara’a, yace,_”To fa! Shi kenan ga garwar uwa, gata diya”. ta doka tagumi. “Bari fada Alhaji, har kunya ta rufe ni”. Ya bita da kallo Yana dariya. ‘ ‘
“To ya, za ki yi? Haka Allah ya so, ya ba mu haihuwar muna tsofaffi, kuma muna‘yi masa godiya,
muka kara gode masa. Sannan muna rokunsa ya‘
sauke ku lafiya”. Tace “Amin Al‘haji” Tabbas Murja ciki gareta, ’dun asibiti sun tabbatar da hakan, har ya kai wata biyu; Kenan tserayar’ watanni ‘ uku ne . tsakanin su da Hajiya Suwaiba. ” A haka ta karkare’jarabawar’ ta. Koda yake ita tana da lafiya; ba kamar Mamansu ba. Kuma tana cin duk abinda take “sha’awa, sai dai in ma ya zo. haka kawai za ta rinka yinsa. Kifi ne kadai ta tSana a dangin abinci, ko suyan sa ba ta sun ji. –
AyyUkan gida kuwa babu wanda ke gagarar ta’. Maman .ta sha ce ma ta kan  ta rinka zama tana hutawa. Sosai Suleman ke ririta ta, yana nuna mata kulawa kwarai da gaske’. fin da dawa. .
‘Shi- yasa take sharholiyarta, har mamaki ‘Hajiya Suwaiba keyi, idanta ga suna wasan guje-guje
da imam. sai ta rinka yi mata fada. saboda yanzu cikinta ya fara tsufa, yayin da ita Maman take gab da haihuwa.
Anyi girbi, kuma Alhaji ya samu amfanin gona yadda ya kamata. Bayan ya fidda zakka, ya siyar da na siyarwa. ya jibgo na abincin gida. Sai dai wannan ‘ . karon abubuwa za su sake yi masa yawa. ga masu juna biyu har su biyu ga Suleman yana so .ya’koma makaranta. . ‘
‘Haka nan ya rufe ido, ya yi ta maza ya tura Suleman karatun, ‘sauran abin da ya rage, ya siyo raguna guda biyu ya daure, sannan ya cika dakin da suke tara itace da itacen, dun karya yanke
Ya yi wa Allah godiya. Ya dawo shi yake zama cikin shagon Suleman tare da ‘yan buge-buge don. kula da iyalénsa. da karatun Suleman. Ko siyan littattafai da (Handout), a zaune sUke, musamman-irin kos‘din‘sa na‘ chemikal lnjiniyarin.
Ba’a hade kwana ashirin ba. nakuda ta kama Hajiya’, SUWaiba da asuba, .kamar’ almara, cikin hukuncin Ubangiji ko kafin ta sanar wa Alhaji halin da take ciki, haihuwa ta zu gadan gadan
Kawai kukanjariri suka rinka ji, yana tashi a ‘cikin gidan. Kowa ya zaburo suka yi mata cirku—cirku’. Kunyar‘Alh’aji ya sanya murja ta’koma ta yi tsaye daga. waje tana ta tsuma. Alhajin kuwa fadi yake, “Haihuwa ki ka yi Suwaiba?” ” Nan da nan ya taimaka mata ta yanka cibi Yaro santalele tamkar’ Imam. Murja ta dora ‘ruwan wanka. Da kanta tayi wa kanta komai, ruwa yai zafi Murja ta kawo ta wanke yaro, sai kallonsa Marja take yi, bakinta ya ki rufuwa.
Fadi take, “Mamanmu Wallahi wannan ya fi Imam kyau”. Tace “Kin fada, .na ji”; “-Waima ina ‘ yake?’.’ Tace “Yanzu ki’ka tuna da shi? Yana can yana barci”. Ta wuce uwar’dakin da saurinta ta taso. shi. “Tashi sakarai, ka yi kani”;
Nan take idonsa ya wartsake, ya diro daga
‘gado suka fito, ya yi tsaye yana kallon mamaki, kafin yace, “Mamanmu yaushe ,kika daukoshi?” Tace, “Yanzu”. “Yaya sunan sa?”
‘ Tace‘ “Ai‘ Babanka bai rada masa ba”. Yace, “Ni ne zan rada maSa”. Mur’ja ta tallabe masa keya tace. “Sannu uban iya yi, an gaya maka shi ma tsoho ne irin ka?” Ya murmUr’guda mata baki, yace, “Eh :din’, .Da wani katon cikin ta'”.
‘ Suka fara dariya. Mama na fadin, “Yauwa‘, ai gara ka rinka ramawa, duk’sun isheka ita da’mijinta”. Tace “Wa yace asa masa- Sunan tsoho Mamanmu?” Tace, ‘“Albarkace, keMa kin yi biyayya ‘ki samu tubarraki
Haka suka yi ta raha har- Mama ta gama shirya Bebi. Ta mika wa Imam, saboda ya kosa ya‘dauka. Bai ‘ gama gani ba.‘Murja ta laka ce shi, nan da nan haushi ya kama shi‘, ya fara hawaye.
Ta samu abin yi. ta rinka yi masa gwalo tana cewa Don Allah wai kaje ka yi sallah. Kuwa yau tashi kaje kayi ka wuce  makaranta . A fusace yace”Ba za‘a jeba . ‘Dole kake, Mama ta kamoshi tace Muje kyaleta, idan ka‘ yi sallah, kazo in kwatar maka shi da karfin tsiya”. ‘ ‘
Ya yi alwala, yayi sallah kafin ya fito Murjar’ ma ta aje Bebin, ‘saboda. ayyukan da zata’ yi., saboda haka murna kamar ta kashe shi. Yayi ta rikonsa. da’ – kyar ya ‘ajiye shi ya .yi Wanka ya yi shirin makaranta’. sai da’Alhaji ya sa ‘baki, da cewa ya yi ba zai je makarantar ba. ‘
Kowa labarin haihuwar’ya ji kamar daga sama. shi yasa aketa murna tare’da yi wa‘Allah godiya da raba su lafiya. “:Yan barka’suka yita barkowa. ‘Yan-‘ uwa da’abokan arziki.
‘ Kwana biyu tsakani, ya. kama ranar sati~ ne. Suleman yazo ya yi hutun karshen sati, kamar‘yadda ya Saba. Shi kansa’ jaririn ‘Mama ya bashi sha’aWa, sabodar girmansa ,ga’ kyau’. Hakan ya jawo masa zakuwa. cikin zusiyar’sa na‘Son ya ga nasa Bebin hakan.
Yayin da tuni yaro yaci suna (Mudansir) Imam ne ya zabi sunan. wai sunan abokinsa ne a makaranta. Shi kuma Alhaji ya biye maSa, yace tunda ‘ Babansa‘ ya zabi‘ Sunan,’ya yanka‘ rago daya cikin ragunan da Alhaji
ya tanada. Sun kuwa kara girma’ sosai don sun samun kulawa da abinci kwarai da gaske. ‘ ’
Mata sun‘taru kuma an ci,- an sha daidai gwargwado. Mama ta ci-gaba da jego. Murja na‘ tayata kamar yaddata saba. Yayin da fada tsakaninta da Imam akan Bebin kullum yake ci-gaba,
Tana son tsokanar’ sa ya yi’kuka  shi‘ ‘da ita kuwa, .ta kan gaya masa, “Yaro idan‘ na haifi “ya mace kyakkyawa, ba zan ba .ka aurenta ba”. Yana jin haushin lafazinta, amma dun shi ma ya ba ta haushi, sai ya murguda baki, yace “Ba’a sonta”.din
‘Ta mammanganare shi, ya fito da gudu yana mata tsiwa. Mama kam bata da matsalar ‘yan raino; koda shi kadai imam din ne zai iya, domin shekarunsa takwas yanzu. Shi kuwa Mudansir’ kara wayau yakeyi. koda yaushe kamar ana masa famfo.
W‘ata’ uku da kwana biyu bayan ‘haihuwar MudanSir. Da Suleman ya je wani sha’ani a Dutsen Abba, daga’can ya karaso Kaduna ya kwana, dunba – zai iya kwana can ba.
Mur’ja ta ji dadin .zuwansa, domin kwanaki uku kenan tana fama da ciwon baya daga ita sai Imam ‘a daki. Shi kuwa barincinsa yake sha, bata da Wanda za taima shagwaba ‘ya rarrasheta.
A daran yau ma ciwon ya taso mata, kamar yadda takeji’duk tsakar dare.’-Nan’da nan ta tashi Suleman. ya taShi a gigice, yana fadin,’“Ya dai’?” Ta-ce, “Baya na”; Ya tarairayota yace “A kira su Mama?” Ta kada kai tace, ‘A’a, kwana uku kenan haka nake fama da shi, kafin safiya, sai ka ji shiru ciwun ya dauke”. ‘ . ‘
Fuska cike da tausayi yace, “Sannu! Wannan Bebin yana wahalar min, dake ko?” Ta yi lamo, yau,ta samu mai rarrashinta. Sai dai kamar yau- ciwon’yana’ ‘ so ya sauya salo. Karuwa ‘Yake yi kwarai da gaske.. har- yana hadowa da mararta, kamar zata fashe,
Dun haka ta kasa zaune, ta kasa tsaye duk inda tabi, yana biye da ita yana cewa: “A‘ kira  Mamanmu. Mur’ja, dubi fa yadda ‘ki ke zufa, kinrsa“, inda ‘za ki tsoma ranki”. ‘ ~
Ta kuwa kafe, fadi take, “A’a nace”. Kai! Tun tana jin dadin rikon da yakemata, har ta fara’ture shi, dun, sam ba ta Son yawan surutun da yake mata. ganin haka yasa ya fice.
Ya bude kufa ya fito karfe biyun dare, ya buga wa Mama kofa. A gigice ta taso, gaba daya suka fito”: tare da Alhaji. “Yaya dai Suleman?” Duk suka- tambaya. Yace “Murja ce ba lafiya”. .
Mama ta yi azama, ta kutsa kai dakin. Salati Mama ‘ta, hau yi, ganin .yadda jini yatsunke, yake malala bisa leda. Ai ba bata lokaci, ta fito da gudu.‘Alhaji, babu lafiya, jini ya tsinke mata. dole aje asibiti
gaban Suleman ya fadi tamkar yadda Alhaji yake ji. Cikin sassarfa ya kama hanyar waje. Suleman ya biyo shi. “Ina za’a samu mota Baba?” ‘
“.Mu je dai mu gani”. gidan makwabcinsa suka dosa, Suka yi ta dukawa’, sun jima tsaye.’.kafin suka ji mutsi. “Lafiya, wanena?” Yace “Alh.- Abdul—Rasheed ne, dun Allah taimako muke nema, yarinya ce zata haihu, jini ya tsunke mata”. ‘ ‘
‘ da nan ya bude kofa. -“Alhaji,~ Subhanallahi! Wallahi‘ nazaci bata gari ne shi ya sa na jima ina kokwatun bude  ya bude kofar’ Tana ina?”
Yace, “Tana gida, matar Suléman ce’ Yace “Bari a fito da muta” Ya juya da ‘sauri, don dauko
makullai. Kamar matacciya suka fiddo ta. dun ta galabaita Saboda jini dake‘ fita jikinta. bana wasa. bane. Mama kuka take yi, tana‘ sallallami har’ suka isa asibiti.
Anan suka yi iya kakarinsu har ta haihu diya mace, sai dai.‘ Likita na bukatar jini cikin gaggawa. Kamar Suleman zai yi hauka, nan da nan ya bada’ jininsa har’ yana fadin a zuke shi duka. ‘ ‘
‘ ‘ Yadda zai wadace ta. Sun dai ‘dabi’yadda ya dace, aka kara da na Alhaji, domin shi ma na shin ya yi daidai. A daren nan aka yi ta aikin kara mata jinin. Shi ya sa kafin safiya ta dan fara gyagijewa,’har’ akan – yi mata magana, ta bada amsa. ‘ Bayan sallar asuba..Alhaji ya_dawo gida yaje wajen’ makwabcinsa ya kara yi masa godiya
domin shi ya biya kudin gado da alluran da aka rubuta suka siyo. ‘ wasa wasa sai da Mur’ja ta kwana uku a asibiti. Inna
Mairo ce ke zaune a gidan tana kula da hidimar abinci, idan dare ya yi, ta je ta kwana Mama ta dawo gida . sabodajaririnta. ‘
Ba karamar hidimar kudi. aka yi ba,har ta kai” ‘ ga sai da Alhaji ya ciyo bashi, abinda bai taba yi ba. a’ ciki ne ya ba Suleman ya tafi Kankiya, ya gaya masu haihuwah.  ‘ Can. cikin ranta. Hajiya Aliyaa‘tayi murn” amma a fili tunda tace Allah ya raya, bata kara’furta komai ba. Ranar suna.Mata‘da~ yawa’sun -zo sunan daga Kankiya. _ 1 ‘
An sha shagalin sunan (Maryam), watau sunan Inna aka sa mata. Yarinya kyakkyawa, taba. ka lashe Shi ya sa Sulaiman ke jinta cikin ransa. gWaggo Saude matar Malam Sallau ita aka bari ta ci gaba da kula da wankanta,Sannu.a hankali’. Mai-Jago da Bebinta sun murmure’ har,.suka yi arba’in. Gwaggo Saude ta koma. ” ‘ ‘
Ummi ta yi ‘saurin girma da wayau, har’ nema take ta kamo Mudanair. Imam na son daukar ta, amma tsiyar da’Murja take masa, ke ba shi haushi, yake ‘aje mata ‘yar ta.da zaran ya zo daukarta, 2a tace, “Aje ta, ba matarka bace; matar Muda Ce”._Shi ma nan take
zai zungureta yaCe. “Dama wa zai. aureta?” –
                 ***:*****
Bayan wata uku, ta je ganin gida tare suka tafi
da
Imam, kwanaki uku suka‘ yi, suka dawo domin zaman gidan babu dadi. Ga uwarka da Dan-uwanka. ammah. a ko zauna ku yi hirara arziki babu ba za ku farantawa juna rai.ba Dalilin da ya sa kenan, ita ma ba ta marmarin zuwa gida. ‘ wll
Ummi na da wata ‘shida. Mudansir‘na da wata tara. Kwatsaml cikin ikon Allah wani ciki ya bayyana jikin Murja. Kuma sai da ya kai wata hudu a halin da take ciki.
‘ Kamar’ ta dora hannu ta yi ta ihu, haka ta rinka ji’. Suleman ya yi ta rarrashinta, yana kalallamatada
zakin baki. Mama ma ta taima-ka wajen kwantar mata ” ‘da hankali, har ta saduda ta bar wa Allah komai.
Amma tsiya tsakaninta da Sulaman ta ki
karewa. Duk karShén sati ‘idan ya zoda bacin rai yake
komawa, saboda sam ba ta’ sauraronsa, gani take kamar‘wani cikin za ta sake samu, bayan Wannan na jikinta. Ummi ta ci gaba da shan nono, har’ ta samu wata goma; aka yayrta, lokacin cikinta wata takwas’ cif
Koda yaushe tana. wajan Mama, ita da Muda suna wasa tare. ldan ta ga ya mike yana dabo-dabo. ita ma sai ta dafa kujera .ko duk wanda ke kusa da ita ta mike. Kash Anyi rashin sa’a, a ’yan sati. biyu da yayenta. ta ki’lafiya. ciwo yau daban. na gobe daban. Mama ta yi ta jelar asibiti
da ita. Haka Inna kan kawo taimakon na hausa amma ina ba’a dace ba. ~ ‘ ; Shi’kansa Suleman tausayi take ba shi, da hawayensa yashamata kuka, idan yazo ya ganta a karmashe,‘kamar .ba’ita ba. ta shi ta shiga ransa Wannan bai sa’ya wanke kansa a Wajen Murja‘ ba,kara mata haushima take . Sai dai kullum nasa, narrashi ne yana .nuna mata ba’da gangan‘ya yi ba. domin- bashi yake bada ciki ba, hukunci ne na Ubangiji haka Murja ta ‘Sauka lafiya a cikin dakinta, ha kaman yadda take ta farga haka alhaj yasan yaddah yayi ya  kukuta ya yankama jaririyar rago aka sawa yarinya suna Jamila, ’tunda aka haifeta. Murjah tacewa Imam. “ga ‘matarka”.” ya harareta yana tabe baki. Tace “Mane ne haka? Danma sammaka, shine kake wani tabe baki?“ Mama tace, “Ba dole ya tabe baki ba. wacce kika Haifa DA farko ai cewa kikai ba matarsa bace . Shi ma‘ baya So”:- ’Tayi‘ ,dariy.tace”‘Allah’ Sarki Mamanmu. to an basu su duka
A hankali kuwa‘yarinya ke washewa. hanci na kara tsawo Ga shi bakikkirin! Ga tsawo, ldanuwanta‘ dara-daré farare sol Tamkar yadda‘ take fara. Imam yana jin dadi, idan ya ji ana Wasa ‘matarsa cawa ta fi matar Muda kyau.‘ Ko ita ma ciwo ‘ne‘ya dusha ta, ga ta nan daikamar ba’a kai labariba.
Masu_ kemis har. sun san‘Alhaji, Saboda- ita. Koda yaushe yana sabe da ita sunje siyan magani.’ Jamila na da wata hudu, annobar kyanda ‘ta-shigo gari.  ba ta tsallake ba, duk da anyi mata rigakafi. .Dama’ yaya lafiyar kura? Kwana biyér cif! . Ana fama, tace ga garinku nan
Ranar Sulaiman kamar yayi ‘ihu ‘a- dakin jarahawa, shi sam bai ma san me Yake ruhutawa ba. Babu abinda yake tunawa ‘sai kwanaki uku .da suka wuce. . , . . Tana rungume a jikinsa har, tana‘wasa da hancinsa, . Mama na dariya, tana fadin ta ji sauki, yau da, ta ga Abbanta. ~ ~ ‘
‘ Yana gamawa, ya bugo Kaduna,“ sai da .yayi hawaye’da ya ga kayanta an shanya bisa’igiya; Marja kam ta yi, juriya, dun ta jima tana ba‘ Ummi mutuwa. Washe gari da’ ‘sassafe ya dawo Zariya’, yaci gaba da ‘ jarabawa tareda tunanin Umminsa.”’Yan gaisuwa na ta zUWa daga ko’ina. banda Kankiya, saboda sakon bai
can ba. Ko dama Suleman ne ke ‘zuwa. kuma shi
yanajarabawa. . .
Sati biyu tsakani suka kammala. anan ma babu kudin‘mota. Alhaij ya yi ta gagandawa ya hada da cinikin shago, ya tafi rana daya, ya dawo Shi ma dai labarin rasuwar Malam Sallau sulaiman din ya dawo masa dashi,Kwana bakwai kenan; Dole Alhaji ;ya sake fafukukar wasu kudin. Murja ta tafi yo gaisuwa, ita ‘ Imam ya dade bai manta da Ummi ba.‘ kullum sai ya tambaya. _
“Anti ina matar Muda’?” Tace “Kullum ina “gaya maka ta rasu Imam, kuma ina an mutu..ba’a dawowa”. Ya kan yi shiru. ya yi ta dogon tunani.
Amma ba shi zai hana gobe ya sake tambaya ba. shi
yasa koda yausha shi’yake kara taso masu ,da keWar Ummi. ‘
Shirye—shiryen tafiya bautar kasa su Sulaman ke yi. Dan Bauchi aka tura shi, bai san kowa ba a garin balle in yana bukatar wani abu ya dan  nemi taimako_
. Saboda haka yaka bukatar’komai na bukatuwar yau da kullum. Saukinta ma a (NYSE Camp) za’a sauké su.. Tilas, buhunan masara uku da Alhaji ya adana na‘ abincin ‘gida,‘ su aka kwashe‘ aka kai ‘kasuwa. Sulaman ya yi siyayyar, duk abinda yaka bukata. Ya yi sallama da koWa. Ya wuce Bauchi. ‘
Jama’a na ta yi‘masa fatan alkhairi. Hankalin Murja ya kwanta sasai, domin jininta akan kumba yake lol
akan samun ciki. Shi yasa tafiyar Suleman ba ta daga mata hankali ba, illa iyaka tana masa addu’ar samun nasara tare da cin gajiyal‘ karatun.
Sukaci-gaba da sharholiyar su da Imam. ga shi ga matarsa. shi. yake rainonta, .‘ ya’ kama dogon gashinta ya yi ta tufke shi, kamar igiya,waishi yana mata kitsu.
Hakan ya sa yarinyar ta saba da shi kwarai da gaske.da taji sallamarsa. ya dawo makarant‘a‘ zata ‘ rarrafa ta fito da sameshi tana mai tsananin fara’a. Shi
ma haka zai sureta, ta yi ta tsalle’kuma. da zarar ya
ajeta. saboda‘wani dalili‘, ta rinka ‘tsala kuka kenan.
Mama ta kan ce “Lallai wannan aure ya kullu
                       **********
Kwanci, tashi Sulaman , ya kammala bautar kasa shekara daya. Muna iya cewa‘ yayi a sa,a dumin akwai yiwuwar zai samu aiki a ma’aikatar da ya yi bautar kasar.do Ko kafin ma ya baro can, manajan da kansa ya sa shi ya rubuta takardar neman aiki.
” Ya dawo ya tarar da iyalansa cikin koshin laifya da Walwala. Jamila kuwa ta yi katuwa, tana gudunta ko ina. Idan‘ka dube ta sai ka rantse da Allah, itace ta girmi Mudansir, dun ko a fuska ta fi shi wayau.
Kama-kama ‘Suleman ya shafe wata shida a zaune yana jiran kira daga Bauchi. Shi kuwa Alhaji kullum nuna masa yake zai fi kyau ya raba kafa, duk inda ya fara samuwa‘to Falillahil-Hamdu!
‘ Suleman ba shi da wannan ra’ayin, gaba daya ma baya sha’awar zaman Kaduna, dun haka yayi kunnen. uwar’ shegu da zancen Alhaji, illa iyaka yace ’ masa ai zai bincika ya gani.
Ranar wata alhamis Sulaman na kwance yana sharar barcin rana,‘yayin da Alhaji yake zaune cikin dan shagonsu na‘kofar gida. Nazarin Duniyan sa yake yi, yayin da Imam ke kula da masu zuwa neman kayayyaki. Ba’a jima ba. ‘
Muda ya fito rike da hannun Jamila ta‘ kofar falon dake waje. “Yaya  Ta kwalawa lmam kira, ta
kwace hannunta ta ruga gunsa.Mudansir na biye da
ita. Ya kamo hannunta, ya shigo da ita shagon yana fadin.
“Baba, ga karya-jari nan sunzo Yakai  aya ya dubesu, yana dariya, “Ai kuwa Ba ‘zasu zauna ba. Ba su biskit guda-guda, ka maida su gida”. Ya dauko ya mika masu yace.
“Ku zo mu je Mamanmu”. Jamila ta toge, ya san abinda take so, dun haka ya duka yace, “To hau  Nan ‘da nan ta haye bayansa tana murna, ya kama hannun Mudansir; ya wuce da su gida, tana tayi _ masa tsalle a baya .
Yana bada baya, mai raba wasiku‘ ya iso bisa, kiyos din nasu daga gidan waya. anan gidan ya tsaya, yana duba ‘lambar gidan sannan‘ya yiwa Alhaji sallama. Bayan sun gaisa: Ya mika‘ masa ambulan,’ ya ja‘ kekensa ya yi gaba. Alhaji ya dubi wasika, tana dauke. da sunan SUleman ne Bai’ gama karantawa ba. Imam ya dawo. Ya sake mika masa wasika, yace, “Shiga ka kaiwa Antinka’ ta ba Suleman”. Ya karba ya koma. ya , kai sakon. Suleman na barci lokacin, dun haka ta aje tana jira ya tashi tukuna.
-Bai farka ba, sai sallar la’asar, ya yi alwala yana Shirin ficewa masallaci’. Murjar ke gaya masa ya samu sakon‘ wasika. Take nan ya ji. gabansa ya fadi. “Ina” take?”
Ta shiga daki’ ta dauku,ta.mika masa. .Ya jujjuya ta, ya’sake mika mata yace, “Ina ga, bari‘inyi sallah”. Ko a WajEn ma da suka hadu da Alhaji, ya
tambaya shi ya ga wasika? Yace ya gani. amma bai duba ba, sallah yake so ya fara
Ya koma gida. ya bude wasika ya duba. kai abimda ya ganema idonsa yasa ‘ Ya mike zumhur! Baki har kunne”.ya kwalawa Murja Kira tana kan sallaya  ta fito a ‘gigice.lafiya Yayana?” Ya nufo. ta. ya‘na fadin “Ana nema na a Bauchi! lntabiyu Marja”. Ta ware ido tace “Me?” A  allah mun gode maka ka gayama baba DA mama? have a,a yanxu nima nake gani a tare suka fita suka iskesu a falon alhaj yana fada musu abinda me faruwa habawa dadi kashe Su Duk hamdalah suka shiga yiwa Allah. hananyensu sama suna gode masa Allah.harta yara da ba su san me abin nufiba suma ihu suka hau yi tare da tsalle, suna fadin ‘Ye…!” Ranar nan gidan kamar sallah. Shi kuwa uban tafiyar. har ya fara hango kansa a wani mataki na daban. Babu bata lokaci aka hada masa kudin mota da ‘ wanda zai rike na tsaron lalura. ‘ya yiwa Bauchi tsinke a washe garin wannan rana.

lol
my hadu anjima DA dare donjin yaddah lamarin zaici gaba DA kasancewa sulaiman dai aiki ya samu muje zuwa masu karatu sannan dan Allah Ku rinqa comment

naku har kullun

The owner OF LITTAFAN HAUSA ZALLAH PAGE @FCB

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page