Makaranta duniya chapter15

Makaranta duniya

        Chapter15

Ya fada motarsa, ya kama hanyar gida. Ko alama furucin Hajiya Aliyaa bai dame shi ba. Ka ji namijin maza! Saboda farin-cikin burinsa ya cika, tunda Alh. Bara’u ya bar wasiyya.
Ko yau ta Allah ta ka sance a kansa, shi baya da fargabar komai a game da auren Suleman- da Murja, wanda shi ne babban dalilin da ya sa yake bin su sau ‘ da kafa.
Shi ya sa koda ya dawo gida, bai gayawa Hajiya Suwaiba irin cin mutuncin da Hajiya Aliyaa ta yi masa ba, don ya tabbata dole ranta ya sosu, ta kara tsanar
Hajiya Aliyaar. illa iyaka ya gaya mata daddadan labarin daya dawo’da shi. Ta kuwa ji dadi ta kumayi addu’ar Allah ya sa ayi da su.
Shi kuwa Suleman uban gayyar’, rasa‘inda zai tsoma ransa ya yi saboda mur’nar jin cewar- ya sami lasisin zuwa ganin sanyin idanuwan nasa.
Tun daga ranar‘ ya fara lissafin’ sauran’ ‘ kwanakin da suka rage wannan watan ya kare. Sai dai matsalar babu kudaden siyayya kamar da. Kuma sai ‘ wannan ya tsaya masa a rai, ya rinka damunsa.
Kullum tunaninsa ina zai samu kudi, ‘kafin karshen wata? A’haka ya kwashe kWanaki’ goma‘ sha  biyu ransa bace, domin‘ .ya rasa mafita, ga shi gobe ne ranan ziyarar ‘yan makarantar.
Ya yi‘tsaki  yau dai‘wuni yayi kwance kamar mai ciwo cikin zuciyarsa.yake~ fadin. “DUk laifin’Baba ne.‘ mutane na zaman zamansu yaxo ,’ya rushe mana jin dadi. ga shi yanzu’ sisi yana neman ya gagari mutum
, Ya ,sake sakin wani dugon tsaki, sai da .ya
’ kusan sakwan biyu bai ‘masa birki ba. Ya gyara kwanciya, yaci gaba da tunaninsa. Yana jin tsayuwar motar Alhaji, amma ya kyale Shi da kansa’ ya fito‘ ya zuge kofar‘ garejin motar‘, wanda nade shi akeyi kamar’ tabarma. ‘ “
Ya dawo ya’ koma cikin mota ya shigar’ da ita  ciki. sannan ya fito ya kwaso wasu- ledoji guda biyu ya jawo murfin ya rufe, ya shiga gida ta kofar garejin kai tsaye
Imam ne ya tarbeshi, yana kokawar amsar ledojin hannunsa. “Kayan nan sun fi karfinka Baba na”. Yace. “Allah zan Iya Baba” “To ga shi nan. dauki
mu gani
Ya sakar masa duk ladojin, sai ga Imam a kasa tijaa Ya fadi dabas Hajiya Suwaiba ta kece da dariya. tana tsaye kofar daki.’Alhajin ma dariyar yakeyi. yana fadin. “Yau Baba na ya sha kasa AI na gaya maka. To mike, sannu ko?” .
‘ Ya sa hannu ya ciccibeshi  Shi kansa dariyar yake wa kansa; Hajiya Suwaiba takaraso’ wajan. ta karbi kayan. tana masa sannu da zuwa. Ya amsa ya kama hannun Imam, suka Wuce ‘daki. Hajiya Suwalba . ta kawo masa ruwa, ya sha.
“Ina Sulaman? Ya fita ne?” Tace “Yana nan a daki kwance, ban san me ke damunsa ba. Nace ko ba shi da lafiya ne. yace a’a”. Yace “Miskilancin  ya tashi kenan Kira min shi. ga wasu ‘yan kaya nan na siyo masa ya kai wa mutuniyar ta sa gobe”. _
. Baki sake take bude ledojin. Confilas ne da  da Seidin da madarar ruwa masu yawa. da mamakl ta dubeshi ta tambaya. “Alhajl Ina ka samu kudi haka? Na dai ‘san ka ‘fita babu kudi a aljihunka
Ya yi murmushl yace “Ikon Allah ya nufe ni da samu. Na fita da tunanin ina zan samu kudi In yiwa Suleman‘ ‘yan siya~siye,don ya kaiwa .Murja? Kwatsam! Ina tafe wajan.(lndifendent Road),
Sai naji anata min horn.ina waigawa naga ashe Sakatarena. ne muka yifakin muka gaisa, ya dauko dubu biyu ya ban.’Kai.tsaya na wuce na yi masa siye-siyan. Kin ji yadda aka yi”. ‘ ,ta”kada kai, tace”To Allah ya amfana. an gode Allah,.tUnda,asiri ya rufu, wata kila shi ma tunanin daya hana shi sukuni kenan”. .Yace, “Ba , mamakl, kira shi inji dalilin kwanciyar”. >
Kofar dakinsa dake gab da zaure, nan ta tsaya ta bubbuga. Ya jima bai’ amsa ba kuma yanaji. Ya taso fuska yamutse ya bude”-Barci ka keyi da yamma?” Ya yi ‘yar mika. yace “Uhm To Babanka ya dawo”. A-haka ya wuce yana yatsina fuska. Ya yi sallama ya shigo “Manya Baka ji shigowata bane?” Yace “banjiba barcine ya kwashe ni. Yace ’Amma ka san barcin yamma bai da kyau ko?” Ya yi shiru. Ya sake fadin. “Mamanku tace a kwance ka wuni,‘me yasA’?”
Yace ba komai kawai jikinane naji duk ya mutu”; Yace “Ina fatan dai ba zazzabi bane?” Ya kada kai “”Shi kanan. ga wasu ‘yan kayayya-ki nan a kaima surukar tawa ko?” ‘
, Ji ya yi kamar’ daga sama,  ya sa ya razana.. ‘ya dube shi”eye Yace”Eh gasu nan a leda. duba ka ~ gani”. cikin zumudi ya jawo ledojin, ya duba; nanda nan ya fara dariya. “
“Wayyo Baba na! Ai kuwa na gode!” Hajiya Suwaiba ta zura masa ido tace“dama na fada, wata kila kuncin rashin abin kaiwa Murja ka ke yi, ko?”
ya shafa kai yace “Ba haka bane Mamanmu”.” “To yaya ne?” Yace‘ Ba komai, ta yi ‘yar dariya tace, “Malam Sule kenan”. Ya kama bincike ledojin. yana fiddo kayan ciki yana ‘yar dariya. ” ‘
Imam ya dau‘wani gwangwanin Geisha daya yace. “Ni ma zan ci! Mamanmu ki bude min!” Saleman yayi. fit! Ya fisge yace, “Me? aiko baka isaba wlh nan ya bude baki. Hajiya Suwaiba tace. .
“Haba‘ Yaya, kai da dan kaninka?” Ya dauresu cikin leda, yana fadin “Ba ‘wani, kawai koyon kwadayi ne. Ba zaka ci shi ba Ya fada yana’zare masa ido.‘ Hakan ya sa shi kara barkewa da kuka sosai. Alhaij ya kamo shi yace
“Bakada gaskiya baBana  Mai taba kayan nan, sai Amina Marja. Taso dai mu je shago in siyo maka wani ;abu Suleman ya harare shir. yace “Dubeshi da idanuWansa irin nawa,. kishi ka kE da ni ko? Wallahi Baba karka sai masa Tsoho kaWai”; Hajiya Suwaiba tace “Wanan kuma babu ruwanka a ciki. ‘Kwashe’ko‘matsanka’, ka ba mu wuri”. Alhaji na dariya ya saba shi, suka fita’ siyo Geisha.
Washe gari da‘sassafe yayi wankan karshe, ya kure a daka ya feshe jikinsa DA turare’ya fito dauke da‘ledojin kayansa,ya fada dakin Mamansu.
ltama ta gama shirya Imam tsaf! da gogaggun shadda suna zaune tana ba Shi shayi yana sha. “Allah yasa ba a shirya ka, ba nayi‘tafiyata”, Tace a shirye yake ai koka tafi kana  isa ita kanta‘ Murjar ba za‘ta kalleka ba.” “Saboda babu wannan’ tsohon?” Tace”Sosai ma!” Yace “Wane ita Mamanmu”. Tana yar dariya
tace. ,
“To shi kenan. dan makullin motar na can, dakin Alhaji ya dan kwanta ne , barci yake” Ya mike ya daukoshi kan T.V. Ta gama‘ da Imam, ta rakasu. ya fiddo motar suka tafi. Mamansu na masa gargadi,_”Kar inji kar in gani! Ka lallaba min Baban mu, kar ka kuskura ka samin shi kuka!”
” Suna tafe. Imam na ta masa surutu, shi kuwa
ko jinsa baya yi, zuciyarsa na can tunanin yadda zai ‘ga’Murjarsa yake ’ya shafe sama da watanni shida bai sanya ta a ido ba. Shi ya sa yake ganin hanyar Kwalejin (Queen Amina).
Ta yi masa nisa. Kusan zai iya cewa ya. riga‘ kowa isowa, domin makarantar babu jama’a sosai. Kai! Murja ta ga abin Mamaki, ba ta ‘san lokacin data. tsaya sake da baki‘tana kallonsa ba. Shi kuwa yashe baki kawai yake yi. , ‘
“Yaya Suleman!” Yace “Ki na mamaki ko? Tomu zauna kar mamaki ya kada min ke”. Da sauri ta wawuri Imam, saboda kunyar data rufe ta “Imam! Kai ‘ne ka kara girma haka?” Ya yi mata zuru, da alama ya
fara manta fuskarta;
Bayan sun zauna, suka gaisa cike da murnar
ganin juna, sannan ya yi mata gaisuWa. “Ya muka ji da ‘ ‘
hakurin su’Nasiru?” Ta sauke numfashi tace’”Mun gode Allah”. “To Allah ya jikansu, shi kuma’Abba Allah ya ba shi lafiya”. Tace”Amin summa amin:’. Yace “Kai! Mun ji mutuwa, sai na rinka ganin lamarin kamar almara”.
Tace “Daina tuna min Yaya Suleman. Ranar‘ da na samu labarin nan, faduwa na yi ban san lnda nakeba, na yi kuka kamar raina zai fita, dole Principal ta sa aka kai ni gida ba shiri
Na dade ina rashin lafiya Yaya Suleman, sai da Umma ta yi da gaske, aka daWo da ni makaranta. Har’ yanzu idan na tunada su, na’tuna halin da Abba ke ciki,“sai in ta. yin kuka ni kadai a kebe
Ya kada kai cike. da tausayinta, yace “Abin sai hakuri dole, ki daina damuwa kin ji? Addu’a kawai za ki rinka yi masu”. Tace “To”. Suka. dan dubi juna suka yi murmushi.
Daga nan ya shiga ba ta labarin yadda Baba suka yi da Abba. Ta jinjina kai tace “Lallai Baba ya. yi‘kokari. Allah ya saka masa-da alkhairi”.
‘ Yana -‘yar” dariya yace “Daga jin wannan addu’ar, ya nuna ke ma ki na farin-ciki ko?” Ta sadda kai tana wasa ‘da hannun Imam. ‘
“Kin cika kunya Murja. To ai shi ma Abban, ya
yi ‘kokari tunda ya cika min alkawari kuma’yaCe koda
babu ransa, bai yarda a tada zancen ba. Kin, ga yayi maganinsu Yaya Mansur mansur masu son a rabamu”, Tace gaskiya ne, har ka sa gabana ya fadi daka tuna min da shi”; “Saboda me?” Tace na tabbata yana tafe Shima. Ban san me gamuwar ku zata haifarba Ya yi ‘yar bazawarar dariya yace, “Me zai‘ tsorata ki? Na farko dai Abba ya riga ya bani lasisin‘ zuwa nan. Na biyu ,kuma bai isa ya yi masu hargowa.a cikin makarantaba, sai Security su gyara masa zama Me zaisa gabanki-ya’fadi? In har kin yarda da ni. Ta langwabe kai tace,‘ “Shi kenan. Nimadai ba  naso naga kuna’ fadane, da zaku shirya’kamar da. wallahi ba karamin farinciki zan yi ba”. ‘ Yace’ “Tani Mai “sauki ne, Yayanki ne, ya fiye zafin rai da zarar ya yi min sallama, zan amsa  ko don saboda Mur’jata. ta yi‘ ‘farin ciki’Ta Sadda kai tana dariyah yana kallonta  da murmushin kauna’ _
‘ Ya fi awa uku da zuwa, suna ta kwarara hirar’ jin dadi. Kwatsam! Suka hango Mansur tafe. Take kuwa gaban nata ya yanke ya fadi, idanuwanta suka
‘ fara-tara ‘“kwalla Shi kuwa Suleman hannu yasa a aljihu, ya toge baqar ledace cike a hannunsa. ,
ganin yayi tsaye bai karaso ba sai ta tashi ta
nufi gunsa. “Sannu da.zuwa ‘Yaya””fuska daure tamau!
Yace “Ungo nan, ni’zan’ koma”.-Tace “Haba‘yaya
daga zuwan ka? Ko gaisawa ba mu yi ba sosai?  Ya jikin Abba da su ‘Umma?”
Yace “Ya ji sauki. Umma na gaisheki”. Ya juya zai Wuce, ta yi azama ta kira shi. “Ya!” Ya’juyo ba tare daya amsa ba. Ta dubeshi cikin sanyin murya, tace “Baku gaisa da Yaya Sule ..
Ya katseta da hananyensa ‘biyu, sannan ‘ya nuna ta da yatsa, “Kar .ki kuskura ki kara ambato sunan nan a gaba na! Kin fini idon ganinsa ne? Ko a zaton ki ina murna da hukUnCin da Abba ya yanke ne? Har abada ni da Umma ba ma tare da wannan iskancin. ,  Haka kuma ba zamutaba bin Alh. Abdul— Rasheed ba! Ina son ki gane wannan, saboda haka’kar‘ ki sake yi min wata magana’akan mutanan da har in mutu bazan daina‘tsine masu ba
Ya juya cikin hanzari ya bar wajen. Ta yi tsaye
’ jigum Na dan lokaci, kafin ta kada kai tace, “Ai shi
kenan Ta bude ledar dake hannunta, ta ga kullin garin rogo da kuli tare da kullin suga ne a farar leda. Ta
‘daWo a ‘salube’ ta zauna, kamar za ta yi kuka.
Suleman ya bita da kallo, ka na yace “Bai- kamata ki bata ranki haka ba, don kawai Yayanki ya ki goyan bayan aurenmu” Kai tsaye ta ba shi amsa. “Dole ne raina ya baci, bayan kai ma kana ganinsa, ka ki taSowa ku gaisa”.
Ya‘ zuba mata ido yace. “Na. karbi laifina, amma zai yi kyau ki gane cewa ko na gaishe ‘shi, ba zai
amsa ba.Ni-kuwa idan akwai abinda na tsana. Wallahi bai-wuca mutum yakunyatani ba so ‘ki karbi uzurina, kar ki min kallan Wani mai girman kai”.
Ta goge’ dan guntun kwallar‘data digo bisa kuncinta tace, “Ai shi kenan”; Ya gyara zama, ya yi ta gyara’ kansa .har ya sauya mata tunani,‘ta daina ganin
nasa laifin. Basu rabu ba, sai bayan sallar aZahar.
. Ya aje mata ledaji biyu cike da kayan ‘dadi. Farin-cikinta ya karu, domin rabonta da samun siye siye irin wannan, tun lokacin da abubuwa suka rikice.
Hakan ya kara dasa mata kaunar Saleman cikin zuciyarta.
                    **********
Tsawon watanni biyu Alh; Abdul-Rashaad bai samu ‘zuwa dubo jikin Alh. Bara’u ba. Sabuda ‘matsalar rashin kudi. Amma duk da haka yana kokarin hada dan abinda ya samu ya ba Suleman. ya kaiwa Murja duk wata. Kwarai abin ya dame shi, koda yaushe hakalinsa yana kan Alhaj Bara’u. yana tunanin ko yaya jikin naSa yake?
‘ Sannan baya so Hajiya Aliyaa ta rinka. kallo,ko furucinta ne ya tsorata, shi ya hana masa’zuwa.‘Yau kam ya yi niyya, domin ya samu ‘yan kudadansa’da ‘yake bi bashi da dama. .
‘ ‘ Da kansa mutumin ya kaWo masa har gida’: a darenjiya juma’a. Naira dubu biyar, kasancewar yau ranar asabar ce tare da Suleman zasu, don shima ya kaiwa surikinsa gaisuwa. ‘ da sassafé Suleman din ya wanke”mota yayi
mata dukkan abinda ya dace
Sannan ya yi mata wanka.. suka dauki hanyar Kankiya. cikin yardar Allah ; suka iso lafiya; Jikin Alh. Bara’u kam sai a hankali ‘ashe har ya kwanta a asibitin kaShi na Kano  ‘ ‘ Hankalin Sulaman ya yi’ mummunan tashi, a yanayin da ya ga Alh. Bara’u. Shi‘ kuwa murna yake yana ta sanya masa albarka. Haka ya riqe hannun Sulaiman, ya kara jaddada masa lallai ya bashi Murja halak malak.
, Nan suka wuni tare da .shi suna ta hirar duniya.
‘bakin-ciki’ kamar ya’ kashe Hajiya Aliyaa. Shi ‘yaSa
abincin da ta kawo masu. Ba su iya cinsa ba. saboda dan banzan’yaji da gishirin data zunbuda. Saida suka fita yin sallar azahar, sannan suka samu fura da nono  suka sha hade da gasasshen nama; ,
Karfe hudu da rabi suka yi sallama da Alhj Bara’u. Kamar’ wancan lokacin. yau ma a tsakar gida suka iske Hajiya Aliyaa tsaye. ‘Sulaman ya rage’tsawo yacE_“Umma za mu koma!” ‘ ” Ta watso masa harara ta watsar. Ya mike jiki
babu‘ kwari, ya‘ yi gaba. Alhaji na kokarin binsa, ta sa baki ta kira shi. Ya ja ya tsaya, yana sauraranta. Fuskarta kamar gobara taShin farko take magana. ‘_‘Na yi maka gargadi. amma bakaji ba ko? Kana ganin kamar ba zan iya aikata maka komai bane A akan sururtun da na keyi, fada kawai na keyi ko? Kai’kana ganin kamar ba zan iya kuntaka maka‘ba wannan abin’ da zan sake  fada inhar kanason ci-gaba da rayuwa toka saurare ni MUddin kafarka ‘bata daina – tako cikin gidan nan ba, .idanuwanka zasu gane maka abin al’ajabi, kunnuwanka zasu jiye maka wani abu mai kama da mafarki. , ‘ Wanda kwakwalwarka ba zata taba iya warware maka shiba. Sai dai ka mutu wajen tunani Mu zuba nida kai,’shege ka fasa”. Ta wuce’ abin. ta ta bar shi anan. ‘
‘_ Shi ma kai tsaya yayi waje, yana kada kai tare da dan murmushin takaici. Ya shige mota suka kama‘
a hanya. Suleman ya yi ajiyar zuciya. yace “Tsanar da Umma take ‘nuna mana ta yi yawa. ina fargaban kar Abba ya mutu su bijire wa maganarsa’ ‘
Alhaji ya yi dan murmushi yace, “Ni kuwa ban  taba kawo wannan a raina-ba. Haka kai ma ba na so ka sanya maganar a cikin ranka, hasalima da yardar Allah Alhaj Bara’u na nan aurenku zai tabbata
_ Ya yi murmushin farin-ciki yace, “Na yarda da Baba na, duk abinda ya furta babu makawa zai faru”. Yace “‘idan Allah ya yarda”. Ya jinjina kai ya amSa. “Haka ne” Ba su wuce Zariya ba, sai da suka shiga Kauran Juli suka gaida gwaggo ‘
inda take gaya masu samarin su Raliya; sun kawo gaisuwa jiya wajen dangin Babansu, har an sanya ‘rana wata biyar. Alhaji yace ,”Amma ba su gama makaranta ba, kafin wannan- lokacin gwaggo?”
Tace “Eh! Ai hakan ba zai hana masu karasawa ba. innarsu ta tabbatar min da hakan. Sannan ta gaya min dalilin yi masu auren yanzu. Ka ga kai ne karfin karatun nasu, ga kuma yadda Allah~ ya sauya al’amarinsa. ~ ‘
Dole a tausaya maka. idan suka yi auren, nauyin ilimin su zai koma wajan mazajensu, kuma Alhamdulillahi kowannansu yana da sana’ar sa daidai gwargwadu
Ya gyarazama yace, “Ba laifi. Allah ya sanya albar‘ka, ya nuna mana lokacin lafiya”. Tace “Amin”. Jim kadan-Suleman ya dawo daga gidan innarsa, tare
suka shigo da Inna Mairon, suka jima‘suna tattaunawa da Dan-uwanta, sannan ta ba shi goro da minti masu yawa, wadanda zai kaiwa Hajiya Suwaiba.
, Tana tauna goran, tana sa albarka. Imam ya fito daga daki ya tashi barci.’Yana isowa minti ya wawusa. Suleman ya danko shi ya kwace. ‘ ‘
“Kawo su maye! Daga fitowa ya kwashi sweet” wa ya ba ka?” Me Imam zai yi inba kUka ba. Hajiya
Suwaiba ta balbale shi,” “Ya isheka Suleman! Ya isheka! Wannan mintin dai ba naka bane, nawa ne.
Yace “Kayan ki, ai nawa ne Mamanmu! Ya zaki bari wannan ‘tshohon ya kwashe?” ,Ta watso masa harara tare da miko hannunta. “Don Allah ban sweet, ka bari a kawo na ka sai ka hana shi sha!” Ya yi ‘yar dariya, “Dama wane shi”. A lokacin Alhaj yasanya baki, “Ba ka son albarka Sule, Bakin tsohu, ai shi kowa
ke so”. ‘
yace “Wanda kuke samin ma ya wadatar‘…” Hajiya Suwaiba ta fisgo mintin daga hannunsa, shi ya katSe sauran kalaman bakinsa. “Ungo imamuna, sha ka sanyawa jikulokinka albarka”.
Ta bare  masa,‘ ta tura masa cikin baki. yayin da yake kwasar harara wajen yayansa. Ya lafe jikinta yace “Mamanmu”:
Tace “Menene Baban mu?” Yace “’bana son Yaya”. Tace “Dama ya za’ayi ka so shi, yana makawulakanci? Ka- bari kawai bayan- bikinsa, ka
rama”. Ya dube ta “Yaushe ne?” Tace “An kusa”. Ya-ce”Zaici gayu?”
‘ Da sauri ta ‘amsa, “Sosai ma”. Yace “Sai na watsa masa‘ruwa”. gaba daya suka kara kecewa da dariya. Suleman na fadin.
“ok! Ka watsa din,.yaro da kwalba zan yi maka kaciya”. Ya makale kafada fuska kunbure, yana hararar
Yayansa.
             ********
BAYAN WATA BAKWAi
watanni ‘biyu da sukawuce kenan suka shA shagalin bikin Raliya‘da Asabe. Kwarai Alhaj; Abdui-Rasheed ya yi ’iya kokarinsa wajen bada gudunmawarsa. .domin ‘dai amfanin gonarsa yayi kyau kuma ya samu Alheri masu tarin yawa.
Da dan abinda‘ ya rage masa ne,_yake shirin “_ tafiya Kankiya dubo Alh. Bara’u, domin dai bai fasa zuwa ba,- duk’ da irinmanyan ‘gar’gadin da Hajiya Aliyaa ‘ take’masa, duk lokacin da ya je din. .
‘barazanarta ba ta yin tasiri a, cikin zuciyarsa. Kamar’ma kara masa azama’take dun koda yaushe da karfinsa yake‘ isa Kankiya. Ko yau din “ma da karfin sa ya iso. .
Mutum na farko daya fara cin karodaShi, shine Mansur. Yana ‘zaune ka san bishiyar mangwaro dake kofar’ gidan. Yana jintsayuwar motar, yazare tagumin daya zabga. ya bi motar ‘da ‘kallo Yana yin arba da Alhaji Abdul Rasheed yayi zumbur .
Ya mike ya bar- harabar’wurin cikin sauri. Alhaji ya fito ‘ya bi shi da kallo  har ya kule. Sannan ya bude
‘buut, ya dauku wani daurin buhu da alama yana da nauyi sosai. Ya aje gefe, ya kulle motar, ya dauki .buhun, da alama doya ce ciki shi yasa nauyin ya yi yawa. . ’ Ya yi sallama sashin’Alh. Bara’u har sau uku ba’a amsa ba. Damaya saba zuwa‘ya‘yi sallama, ba’a amsa ba, saida ya’shigo falon, yake tsinkayar mur’yar
abokinsa yana amsawa. Saboda haka ya’fada’falon tare da wata sallamar ta hudu.’Wannan karon bai ji muryar Alh. Bara’u ba, sai dai Hajiya Aliyaa tana ‘ zaune a felon.“ cikin sakin fuska ya aje buhu. gefe yana fadin. “Hajiya Aliyaa,‘ ba kya jin sallama ne? Ta‘ ja, wani _. mugun dogon tSaki, ta tashi ta bar wajen Ya yi dan murmushi yace a ransa. ‘”Allah ya shirya”; Yawuce dakin ‘abokinsa, kai, jiki fa babu kyan gani:Wani irin numfashi yaké yi mai . kama da haki. Ashe ma yana ta‘, amsa :sallamar; , maganar’ ceba  fita yadda ya kamata.-gaba daya‘Ya dawo fari-ga matsananciyar‘ rama. Da sauri ya’karaso gunsa,‘ gabansa na faduwa Hannanyensa “biyu ya ‘ kama ‘ya runtse tama’ ldanuWanSa cike da ‘kwalla, yace “Alh.” Bar’a’u, jikin kara rikicewa‘ya yi?”.Yace “Yau kwana’ hudu kenan bana cikin sukuni Alhaj. abdulRasheed ‘yace _ -“”Kuma kake zaune ba a‘kaika-aSibiti ba?” ‘Ya .kada kai kwalla‘. Suka gangaro bisa kuncinsa’yace. “Ko mun je, me zasu’ yi’min? Sannan‘ kudin da za’aje dasu din kansu’ aiki ne. Ni a kyaleni kawai, ba tashi ‘zanyi ba, lokaci kadai nake jira”_ ‘Matsanancin tauSayi’ ya lullube Alh. .’Abdul~ Rasheed, tuni. kwallarsa suka sauka. “Kar kace haka Alh. Ba‘ra’u, asibitinma zasu taimaka domin samun sauqin wata lalurar.,Ka amince min,
‘ tunda nazo da mota indaukeka mu wuce asibitin kawai”. ‘ , r ‘
Ya gyada’ kai. yace “Karka damu‘da ni Alhaji. Wata magana kawai na ke so mu yi. ka dagani, ‘ka ban ‘ ruwa in sha”. Nan da‘ nan ya tarairayo shi, ya-ba shi ruwa ya sha’ sosai.‘ Ya jingina shi jikinSa,_— yace; “Sannu”Ya amsa. da kai kafin yace, “Alhj_ Abdul- Rasheed zuwankayau ya yi min dadi fiye da sauran ranakun da ‘ka zo duba ni. Dalili kuwa shi ne; so nake -in aiwatar da auren Suleman da Murja‘da kaina. ldan zai yiwu ku je ku shirya nan da wata daya ku kawu duk
abinda ya samu a daura auren su. In
.cika alkawarin nan. ‘  Kafin na mutu. Ka san a wannan watan aka ce
.zasuyi yi jarabawar gama karamar sakandire. sai ta‘
koma can hannunku ta karasa; karkashin ikon mijinta. Ina fatan ban takura maka ba Alh. Abdul-Rasheed?”
‘ Yace “Ba ka takura min ba, hasalima ka diga ‘
min‘farin-ciki a raina~ Babu abinda zance. face in yi ‘maka godiya tare da addUar Allah. ya nuna mane wannan lokaci, muna cikin koshin lafiya.
Na tabbata Suleman zai yi farin ciki, idan ya’
samu wannan labari, don ba shi da wani buri~daya wuce ya samu murja a matsayin matarsa. Saboda haka a madadinsa, na ke cewa mun gode, mun gode. Allah ya ‘kara maka’ lafiya”. Yace “Amin’summa amin”. ‘
Ya gyara masa kwanciya, yana ceWa, “Na ga Mansur a waje, su ma hutu suke yi?” Yace “A’a, ai sun‘yi sati uku ‘da komawa. Yana jiran kudin rijista ne ga na (Project) da jarabawa.
To babu, shi ya sa yake zauna”. Alhaji yai shiru jim, kafin ya sauka numfashi. Yaca “Allah ya rufa mana asiri.-‘Da ina da kudi da na ba shi, ya koma makaranta‘; Amma idan, na koma zan bubbuga ln ga abinda Allah zai yi”.
Yace”Babu komai Alhaji, kar ka matsawa kanka, duk abinda Allah ya yi game‘ da karatunsa. daidai ne”. Suka yi shiru cike da jimami. Yau kam ba su yi hirar kirki ba, saboda yanayin jikin Alhaji Bara’u. ~ ‘Bayan sallar’ azahar, ya’yi Shirin komawa. ‘ Ba tare’ daya sake ganin Mansur ‘ba. Bayan ‘ sun gama sallama, tare da tofawa_ Alh. Bara’u addu’o’in neman waraka daga Allah. ya bar dakin, idanuwansa cike da kwalla.
Tana tsaye tana jiransa. inda ta saba. Yau kam shi kansa babu walwala a fuskar’sa yace, “Ki yi hakuri Hajiya Aliyaa, ki saduda, ki mika wa Allah al’amarinsa. Wanan abinda ki‘ke yi, tamkar kinaja da nufin Allah ‘ ne. Ya kamata ki gana cewa ba ni da mugun nufi a game ‘da lyalanki”.
Tun ‘daya fara magana take zuba masa kwandon harara har. ya kare. Ta gyara tsayuwa tace, “Ba wa’azinka na tsaya ji ba, don baka yi kalar
Shaihunnaiba, Balle Malamai. Na yausha kuma? An
ce da kuturu Allah ya la’ance ka. har abada kai mugu ne a idona kuma ina nan akan baka na, sai na shayar da kai gubar da zaka yi nadamar rayuwar ka.
Maganar Baban Mansur‘ da ‘yake nan da wata daya za’aba ~wannan .karen’ marar zuciya auren Murja..To ina so ka sani, ba’zamu‘kankara maku komai ba.
kuma Duk abinda akewa “ya mace ita ma sai anyi mata Daidaida gazar .ya zama dole wajibi ku yi shi”. Ya dan kada kai; yacé,’.ki kwantar da hankalinki, da yardar Allah zaki sha mamaki. Duk abinda akewa ‘yar gata da yar‘dar Allah ita ma Murja .za’ayi mata
Taja. guntun tsaki, “Ya rage naka, ‘dama Mu gaya maka ne, don kar ku yi tsammanin za ku ci bulus’ Ne”. Ta, shure takalmanta, ta bashi wuri.~ Bai baice komai ba, shi ma ya kama hanya zai ‘fice. Ji yayi’an Wurgoshi da wani abu mai kama da tarin’kaya.
Ya juya a razane  buhun doyarsa ya hango baje a’ kasa. Juyawa kawai ta yi ta, koma ciki da saurinta. Ya yi tsaye takaici ya kama shi, ai gara Aliyaa ta ci  gaba da ci masa fuska da tawulakanta abinci. Ya koma ya, dauko buhun ya maida shi. saman baranda. sannan ya yi waje. zuciyarsa a kuntace.‘ Yana tafe a, mota yana tunani. wannan ‘ wulakanci ya yi yawa. Kamar Aliya_ta rinka tararsa ido Cikin ido, tana dankara masa magana son ranta‘?’. Kai Me yayi zafi?
Ko kuwa laifinsa ne daya hana Alh. Ba‘ra’u ya gaya wa iyalansa gaskiyar lamarin? Tabbas ya san haka ne, amma yana jin zai iya jurewa, ya cije ya dauki duk nauyin, saboda Suleman ya samu farin-cikin da yake so. ‘ ‘ ‘
Ya numfasa shi kadai a mota, ya sauya tunaninsa ya koma yadda‘zai yi ya fita kunya. Ya dai san a halin yanzu bai aje ba. bai ba kowa ajiya ba. Dan ragowar amfanin gonar sa, ya- aje ne saboda ci. Ya tabbata zai taimaka masa tsawon lokaci bai yi awo ba.
“Allah gamu gareka! ‘Hakika kanaji kana gani;  kuma kai kadai ‘ke maganin komai..Allah na rokeka rufin asiri akan duk lamuran mu”.ya ci-gaba .da tafiya hankali kwance. .
Domin ya danka wa mai kowa mai komai lamu‘ransa. Kamar yadda ya saba, baya iya wuce
Zariya bai biya ya duba Gwaggo ba. yau ma”ya tsaya
wajenta kuma ya shaida mata halin da ake ciki.
Ta jima shiru kafin ta nisa tace. “Shi ma dai‘ Suleman da mayata yake, in banda bakin naci, me zai’
Ci da Mur’ja. Yarinyar da uwarta ba ta, kaunarsa? Wannan ai’ kora da-hali ne, tunda ta san ba mu da shi. ina za mu samu kudin hada lefa nan da wata daya? ga sadaki, ban da hidimar da za ta biyo baya?”
Yace.”Kar‘ ki‘ damu Gwaggo. Allah zai rufa asiri”. Tace “‘Ai shi ma Saiyaje dangin Babansa su
_ taimaka ko?” Ya yi dan murmushi Yace “Gwaggo’
kenan. A zatonki za’a samu wani abu a wajan dangin‘
Babansa ne? Baki Mantawa da Kullum , a babu suke, da ace ma Baban nasa ya bar masa wata ’yar kadara ce sai a sayar a rage wata hidimar, Amma babu komai, za mu ci—gaba da addu’a. insha. Allahu asiri zai rufu”.
Tace “Allah ya sa” Ya amsa da “Amin . ya
taho ya barta cikin ‘tunani, ba’a jima ba, ta yafa mayafi ta nufi gidan lnna Mairo, ta kwance mata jakar, Hankalin lnna ya tashi matuka, ta rasa inda za ta sa ‘ranta. ita kanta babu komai a hannunta. ‘ Don ba ta gama gyagijewa daga bikin yan mata biyu ba. Haka suka rabu ba tare da sun warware bakin zaran ba. Illa iyaka, idan abin yin lefan bai samu ba, sai Suleman ya hakura kawai. Haka lnna Mairo ta ajewa ranta, tunda ta san ba sata za su yi ‘ba. To amma Sulaman zai iya hakura kuwa?
Bakinsa har kunna yake, tun dawowar Alhaji gida har ya zuwa yanzu ‘da yake kwance’ a dakinsa. Baya aikin komai, face tunanin Murjarsa. Abin kamar a mafarki yake zuwa masa, wai aure wata daya
‘tauraruwar ta dawo mallakinsa. Sam ya kasa barci, sai  faman juyi bisa gadonsa. kawai yake.
Tamkar” Alh. Abdul-Rashead dake zaune dangwargwar! Yana-neman mafita, don ya kunyata Hajiya Aliyaa. Ya nuna mata ta Allah ba nata ba, Hajiya Suwaiba ta dube shi karo na barkatai.
Tace “Wallahi hawan jini zai kama ka Alhaji. akan maganar da ba ta zama wajibi ba”. Ya dubeta da kyau yace, “Tabbas maganar‘ ki haka take. sai dai kar ki manta, nunawa’ makiyi gazawarka, wata kofa ce da za ta ba shi damar yi maka dariya.
Na san Alh. Bara’u ba zai bukaci kamai daga gareni ba face: sadaki, amma furucin Aliyaa da take ‘ ‘takenta, yasa zan nuna’mata dan halas neni kuma Suleman dan gata ne, ya WUce ai  masa’ gatse ko a  nemi a kure shi.,da yardar Allah Hajiya Aliyaa sai ta kunyata, domin a gabanta; Tana ji tana gani Suleman zai’ , dauke’Murja” Tayi ‘yar dariya- tace “Alhaji‘kenan, to Allah ya taimake ka bisa kudirinka”. Yace “Amin”. Tace “To ka kwanta ka samu barci, ni kuma tawa bukatar ..’ kenan daga gareka. Ina fatan ba za’a bani kunya ba ni ma?” Yana dariya, ya gyara kwanciya. “Wane ni Abdul-Ra‘sheed, in ba Hajiyata kunya‘”.
KWanaki goma sha hudu kenan Alh. Abdul-
Rasheed na ta fadi tashi, don ganin ya samu kudaden da zai fita kunya; amma abin ya faskara. Shi kansa Suleman din hankalinsa ya fara tashi. 
Duk da ya san koda wadanna kaya ko babu su, tabbas zai Samu auren Murja. Sai dai shi ma sosai . zuciyarsa ta kamu da son a kunyata Hajiya Aliyaa, su ba ta mamaki da abinda ba ta zata ba.- ’,
Shi kansa sadakin da ba’a yanke adadinsa ba.
Alhajin yana so ya! bada daidai yadda ake ba ko wanne
mace cikakkiyar budurwa a wannan zamanin. la,asar ta jima da wucewa, lokacin da Alh. Abdul—Rasheed ya yi sallama, ya shigo cikin gida. ‘
Wasu ‘yara na‘ biye da ‘shi’dauke da setin akwatuna .masu ‘ruwan’siminti Hajiya Suwaiba na tsakar gida ta dinga binsu da kallo‘ har yara Suka gama sauke kayan
ya Sallamesu suka fice. , ‘Ya matsa gareta yace, “Ya‘naganki kin yi. tsaye, maimakon ki karbi ,kayan ki .kai daki?”Ta‘.numfasa dauke da murmushi, tace “guiWoyina ne suka- mace “Alhaji. Setin akwatuna na gani?” Fuskarsa’ cike da an‘nuri yace,” Suwaiba aishi Allah baya barci, na tabbata ba‘za mu kunyata ba,’sai dai uwar . diya taji kunya”Ta shake da dariya‘ tana daga akwatinan. “Alhaji Da alama dai Aliya’a ta kure ka. ban taba ji ka na- korafi a Ranka ba, sai wannan karan”. Yace “Ashe kin ” .gane. Shigo ciki mu yi shawarar”abin yi”;
Sun natsa a falon ta,~tana kallon Alhaji yana fito da damin kudi’dauri dauri, “ta ga kudi. abinda na ke so dake shi ne, ki’rubuta’ duk abubuwan‘ da ake zubawa a lefe, gobe in Allah ya kai mu, ki je ki siyo su. Kin ga wannan daurin? Sadaki ne na ware dubu biyar. Sauran abinda ya’ ‘rage’ a’ kucuncUna su a ‘hidiman
Tace “Ba shakka! Ta Allah” ya nuna ‘mana lafiya, kai kuma allah ya‘saka maka da ’alkhairi”. Ya ‘amsa “Amin summa amin”;.Tace “‘Alhaji kar fa kace nayi
maka tambayar kurulla. don Allah ina ka samu wadannan damman kudin?”‘ Ya dubeta da kyau, ‘ya yi dan murmushi._ “Ai kuwa kin min tambayar kurulla Suwaiba. Zan so ace kin karbi kudin nan ‘bakinki kanin kafarki, ba tare da kin yi bincike ba. Amma ya’zama wajibi inbaki amsar tunda’babu laifi binciken Sukayi jim suna kallon juna, kafin ya ci—gaba. “Kwana uku da suka wuce, na samotata a kasuwa. cinikin bai kaya ba, sai yau Kuma“ Alhamdulillah‘i, tayi. kasuwa, duk da cewa ta fara tsufa.’ Kin :ga kudin nan. ina kyautata zaton zasu ishemu komai dakomai’. Fuskarta dauke . da mamaki .ta‘ tambaya- “Motarka Alhaji ‘Suka kura “wa juna ido. .

Admin is back.
Admin ya dawo. Aci gaba DA gashi crews members abokai.  I luv y’ll😘♡♡♡♡♡♡♡■↘↖

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page